Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hallaka dukkan macizan da take taƙama dasu.
Baƙin hayaƙin da ya ƙone macizan ya soma haɗewa a waje guda yana curewa.
Jim kaɗan ya samar da siffar wani mutum dogo mai cikakkiyar kamala da kwarjini.
Kayan jikin wannan mutumi baƙaƙe ne sidiƙ, akansa akwai hular sarauta mai launin baƙi, sannan yana riƙe da zabgegiyar takobi wadda take fitar da baƙin hayaƙi da yake tashi sama yana sanya fararen gajimare komawa baƙaƙe.
Idan ka ƙarewa wannan mutumi kallo zaka fuskanci cewa, ba wani bane illa SARKI SAMUDUL ANSARI.
Amma saɓanin da, wannan sarki Samudul Ansarin a cikin ainihin cikkakiyar siffarsa yake wadda take bayar da tsantsar buwaya da kwarjinin sa.
A fusace Aiyni ta baiwa mutanen dake bayanta wani umarni.
Nan take suka fara ware kansu goma-goma, suna haɗewa a waje guda suna juyewa izuwa manya-manyan macizai.
Kafun a ɗau lokaci tuni dukkansu sun gama juyewa izuwa macizai.
Macizai guda goma suka bayyana a filin yaƙin, ita kuwa Aiyni sai ta sake tashi sama ta zauna akan wannan gajimare sannan ta haɗe hannayenta a waje guda ta fara irin wannan ɗalasimi.
*****
Yau *18/03/2023*
Babi na gaba zaizo *20/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 100: *Kyakkyawan shiri*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra.
*
UMS
*
Sarki Samudul Ansari ya ɗaga takobinsa sama, inuwarta ya cika wannan fili gaba ɗaya.
Macizan na ganin haka suka yi ruri, suka rugo da gudu kan Samudul Ansari suka fara kawo masa sara.
Bakunansu suna furzar da dafi baƙi ƙirim mai tsananin zafin gaske, wanda zai iya narkar da duk abinda ya taɓa.
Sarki Samudul Ansari ya kwarara uban ihu, ya ruga da gudu tsakiyar su, takun sawunsa yana haifar da girgizar ƙasa a wannan filin yaƙi.
Tun kafun Samudul Ansari ya isa inda suke da yawa daga cikinsu suka soma razana.
Ai kuwa yana shigowa tsakiyar macizan ya hau su da mummunan sara da suka da takobin Saif-Al-Barzaƙ dake hannunsa.
Hari guda ɗaya na Saif-Al-Barzaƙ yana hallaka macizai biyu ko uku. Kafun a jima ya kashe dukkan waɗannan macizai guda goma.
Samudul Ansari ya sake kwarara uban ihu shima ya tashi sama cikin iska ya tunkari inda Aiyni ke zaune akan wannan gajimare tana ƙaddamar da ɗalasiminta.
A hankali ta buɗe idanuwanta ta kalle shi, cikin gaggawa ta miƙe tsaye sannan ta zaro takobinta ta afka masa.
Samudul Ansari da Aiyni Gorgon suka buɗe sabon gumurzu a cikin sararin samaniya tamkar sun kasance tsuntsaye masu fuka-fuki.
Takobin Aiyni tana fitar da koriyar walƙiya, takobin Samudul Ansari tana fesar da baƙin hayaƙi.
Nan fa sauran dakarun dake bisa turba suka fara ɗaga kawunan su sama, suna ganin yadda wannan gumurzu ke faruwa.
A duk sa'adda Aiyni ta aikowa Samudul Ansari dunƙulen walƙiya sai yayi amfani da wannan baƙin hayaƙi ya kare kansa.
Harin nasu guda biyu yana haɗuwa a waje guda, sai a kwararo tsawa wadda take haifar gagarumar wuta ta zubo ƙasa.
Nan fa sassa daban-daban na wannan filin yaƙi suka soma kamawa da wuta.
Gumurzun nasu ya soma daɗin kallo.
Ko kaɗan Aiyni bata kuskuren tunkarar wannan baƙin hayaƙi dake fitowa daga cikin takobin Samudul Ansari, saboda ta san illar sa.
Aiyni tana da baƙin zafin nama fiye da tunanin mutum, wataƙila hakan ya samo asali ne sakamakon sirrin walƙiya da take da.
Samudul Ansari yana wannan gumurzu ne a fusace, musamman idan ya tuno cewa, wannan mayaƙiya ta hallaka masa dakaru sannan ta sake haddasa wannan cuta a wannan daula tasa sai ya sake fusata ya afka mata.
Koda aka ɗauki lokaci ana wannan gumurzu sai ran kowa daga cikinsu ya soma ɓaci.
A zahiri harin Samudul Ansari yafi na Aiyni ƙarfi amma tana da mugun zafin nama, bata yarda harin ya kusance balle har ya same ta.
Mafi yawancin lokuta shi kuma tsayawa kawai yake, hare-haren Aiyni su dira a jikinsa amma basa masa komai.
A wannan siffa da Samudul Ansari ya bayyana yafi ƙarfin harin wani bil'adama yayi tasiri a kansa.
Cikakken sarki ne wanda hatta duniyar aljanu take shakkar sa.
Koda aka sake ɗaukar lokaci ana wannan gumurzu babu wani canji, sai Samudul Ansari ya tsaya cak! ya daina motsawa.
Aiyni Gorgon ta taƙarƙare ta tattaro dukkan ƙarfinta waje guda, ta kaiwa Samudul Ansari wawan sara a wuya.
Dukkan mayaƙan dake ƙasa a wannan wuri suna kallon wannan abu.
Tartsatsin walƙiya mai yawan haske ya tunkari mutum mai sanye da baƙaƙen kaya.
Samudul Ansari bai yi wani motsi na kare kansa ko kuma kaucewa wannan hari nata ba.
Har sai da wannan takobi ta dira akan wuyansa.
Tartsatsin walƙiya mai yawan gaske ya tashi a jikinsa sannan ya zubo ƙasa.
Bayan komai ya gama lafawa Samudul Ansari ya bayyana tamkar a wannan lokaci ya fito daga wanka, babu wani abu da ya same shi.
Cikin tsananin razana Aiyni Gorgon ta ja da baya, haka ma sauran dakarunta dake bisa turba.
Lallai Samudul Ansari cikakken hatsabibi ne wanda har yanzu basu gama fuskantar sa ba.
Aiyni tana ja da baya kamar mai ƙoƙarin guduwa, Samudul Ansari na fuskantar haka ya ɓace daga inda yake tsaye.
Ya bayyana a kusa da ita, cikin wannan siffa mai cikar kamala ya ce.
"IDAN NA SARE KANKI, HAKAN ZAI SA SARAUNIYA YILAN TA DAINA AIKO MIN ƘANANUN SHAIƊANU.
"KU NISANCI WANNAN DAULA TAWA, NA FI ƘARFIN KU...
"SARAUNIYA YILAN KU FITA DAGA SHA'ANIN WANNAN DAULA KO KUMA NA KAWO ƘARSHEN KU..."
Samudul Ansari yana gama faɗin haka ya sare kan Aiyni da takobin Saif-Al-Barzaƙ dake hannunsa.
Saurin da yayi amfani dashi wajen sare kan nata yafi gaban misaltawan mutum sai dai abinda kwakwalwa ta wassafa kawai.
Gangar jikin Aiyni Gorgon ta rikito ƙasa, Samudul Ansari ya riƙe kanta sannan ya sauƙo ƙasa daidai inda waɗansu mayaƙanta da suka yi saura guda goma suke.
Jikin mayaƙan na kyarma suka zube a gaban Samudul Ansari suna tuba da neman gafara.
Samudul Ansari ya daka musu tsawa suka miƙe tsaye sannan ya damƙa musu kan Aiyni ya ce, su kaiwa sarauniya Yilan, su ce yaro yayi kadan har yanzu.
Mayaƙan suka karɓi kan sannan suka juya da baya suka falfala da azababben gudu suka fice daga daular suka yanki daji.
Sauran mayaƙan Samudul Ansari da su Zarifa suka rugo gabansa, suka zube ƙasa suka sake jaddada mubaya'ar su.
Bayan gajeren lokaci suka sake komawa cikin birninsa.
A wannan lokaci wannan cuta bata yaɗu sosai ba, saboda wannan ruwan sha da Samudul Ansari yayi tanadinsa domin irin wannan rana.
Amma dukda haka sai da aka sami wadanda suka kamu da wannan cuta, al'amarin babbar daula kamar Shaha ba ƙarami bane.
Bayan sa'o'i kaɗan waɗanda suka kamu da wannan cuta suka soma mutuwa.
Sarauniya Arya ta shaidawa Samudul Ansari cewa, wannnan ruwan sha da suka rarraba a wannan daula ba zai wuce kwanaki uku ba zai ƙare.
Idan kuwa ya ƙare jama'a zasu shiga wani mugun hali wanda zai yi sanadiyar rasa dubbani daga cikinsu.
Bisa wannan dalili ne Samudul Ansari ya yi hawa da kansa ya nufi dajin Ƙaiz inda hadimin sarkin ƙabilar Azbin yake wato boka Ƙaizadu.
Dokin Samudul Ansari na shigowa cikin dajin, siffar boka Ƙaizadu ta bayyana a gabansa.
Bokan ya risina a gaban Samudul Ansari ya kwashi gaisuwa.
Sannan ya shige gaba ya yiwa Samudul Ansari jagoranci izuwa cikin fadarsa.
Bokan ya zauna a ƙasa shi kuma Samudul Ansari a zauna akan karagar mulkinsa.
Ƙaizadu ya risina ya ce, "Ya shugabana! Kazo ne akan batun wannan cuta da ta sake ɓulla a ƙasarka, haka ne?"
Sarki Samudul Ansari ya amsa, "Wannan shi ne abinda ya kawo ni wajenka, ina so nasan a ina zan sake samun irin wannan magani wanda sarkin ƙabilar Azbin ya bani..."
Ƙaizadu ya sake risinawa ya ce, "Duk duniya babu inda za'a sami irin wannan magani, idan ba wajen sarkin ƙabilar Azbin ba..."
"A wanne yanki yake zaune a duniya?" Sarki Samudul Ansari ya tambayi bokan.
"Duniyar Iska!" inji Ƙaizadu. "In dai kana so ka sake haɗuwa dashi, dole ne kaje duniyar iska inda babbar fadarsa take."
Sarki Samudul Ansari yayi gajeren tunani ya ce, "Tayaya zan je duniyar iska, sannan idan naje ta ina zan fara neman wannan basarake?"
Ƙaizadu yayi murmushi ya ce, "Akwai wani tsuntsun tsafi da zan haɗa ka dashi wanda zai kai ka har cikin fadar sarkin ƙabilar Azbin, a cikin kwanaki biyu rak."
Sarki Samudul Ansari ya miƙe tsaye, ya dubi boka Ƙaizadu ya ce, "Yi gaggawar haɗa ni da wannan tsuntsu domin kuwa jama'ata suna cikin wani hali..."
Ƙaizadu ya dafa Samudul Ansari suka ɓace daga cikin wannan fada, suka bayyana a bakin wani zabgegen rami wanda saboda tsananin zurfinsa, basa hango hango abinda ke can ƙasa.
Ƙaizadu ya rufe idanuwansa ya fara karanto ɗalasiman tsafi, faruwar hakan keda wuya wani jibgegen tsuntsu ya sauƙo daga sararin samaniya a bakin wannan rami.
Ƙaizadu ya baiwa wannan tsuntsu umarnin ɗaukar sarki Samudul Ansari ya kaishi duniyar iska.
Tsuntsun ya ranƙwafa a gaban sarki Samudul Ansari shi kuma ya haye bayansa.
Tsuntsun ya buɗe manya-manyan fuka-fukinsa ya tashi sama, ya lulluƙa cikin gajimare ya ɓace ɓat!
****
A can daular Gorgon kuwa, duk wannan yaƙi da ya afku tsakanin sarki Samudul Ansari da mayaƙan Aiyni. Sarauniya Yilan da mahaifinta suna kallo a cikin wani mudubi.
Sarauniya Yilan ta fusata matuƙar fusata. Ganin cewa an hallaka ɗaya daga cikin BES - dirkokin daular Gorgon.
Amma idan mutum ya dubi mahaifinta zai fuskanci cewa, wannan fusata da tayi nafila ce kawai.
Wannan sarki saboda tsananin fusata fuskarsa gatsinewa take tamkar zata zazzago ƙasa.
Cikin fushi ya naushi mudubin da hannunsa, take mudubin ya tarwatse.
Gashin kan sarauniya Yilan da na wannan basarake tuni ya gama juyewa izuwa macizai.
"Ya kai abbana! Ta ya ya zamu kawo ƙarshen wannan hatsabibin, wanda ya addabe mu, yake ta kashe mana mutane?"
Wannan sarki na jin haka ya ce, "Zamu kawo ƙarshensa amma ba yanzu ba, sai mun yi gagarumin shiri na tsahon shekaru casa'in da tara..."
Cikin tsananin mamaki Yilan ta dubi mahaifinta ta ce, "Shekaru casa'in da tara fa, ka ce? Amma wanne irin shiri ne wannan?"
Sarkin ya ce, "Ya ke ƴata, kiyi sani cewa abinda BES suka kasa, ma'abota Bankai suka kasa, ƙananun sarakuna suka kasa. Abu ne mai tsananin wahalar gaske.
"Bana so ace kin shiga wannan faɗa daga yanzu, ina so sai mun gama wannan kyakkyawan shiri wanda nake da tabbaci akan cewa zaiyi tasiri sosai a wannan yaƙi."
Sarauniya Yilan tayi gajeren tunani ta ce, "Abbana! Baka amsa min wannan tambayar da nayi ma ba, wanne irin shiri ne?"
Sarkin ya sake numfasawa ya ce, "Wannan shiri namu, za mu iya kiransa da suna ƘARSHEN TAU'RIN!
"Abinda ake buƙata a atisayen Ƙarshen Tau'rin, su ne abubuwa guda biyu: Takobin hannunki Bankai 100 da kuma takobin taurari ta saurayi Gauhan..."
Sarkin na zuwa nan a zancensa, ya sake samar da wani mudubin tsafi a tsakiyarsu.
Madubin yayi haske sannan ya nuna daidai lokacin da taurarin Gauhan guda biyu, suka dira akan Samudul Ansari har suka sa ya faɗi ƙasa.
"Irin waɗannan taurari zamu iya amfani dasu wajen yaƙi da sarki Samudul Ansari domin a yadda na fuskanta duk duniya, irin waɗannan taurari ne kaɗai zasu yi tasiri akansa.
"Babbar matsalar ita ce, har yanzu waɗannan taurari basu da isasshen ƙarfin da zasu iya tasiri akan sa...
"Dole suna buƙatar a tsuma su a cikin tsumin tsafi na tsahon shekaru saba'in, sannan a tsuma wanda yake da mallakin takobin na tsahon shekaru casa'in.
"Ya ke ƴata! Daga wannan lokaci ba zamu sake tunkarar daular Shaha da yaƙi ba har sai bayan shekaru casa'in da tara.
"Ke, Gauhan da kuma BES guda huɗu da suka yi saura, za mu tsuma ku a cikin tsumin tsafi, bayan kun gama kimtsawa zamu fiddo ku sannan mu kaiwa sarki Samudul Ansari hari.
"Ina da tabbaci bayan shekaru casa'in da tara, sarki Samudul Ansari ya soma manyanta sannan ba lallai ya mayar da hankali akan mu ba, a waɗannan shekarun...
"Kin ga kenan cikin sauƙi, zamu gama da shi."
Koda sarkin ya zo nan a bayaninsa, sai sarauniya Yilan tayi shuru tana ta tunani.
Lokaci mai ɗan tsaho kafun ta ɗago ta dube shi ta ce, "Ya kai abbana! Na fara fuskantar wannan bayani naka, amma har yanzu ban gama gane shi ba. Shin zaka yi min dalla-dalla yadda zan gane?"
Sarkin yayi murmushi kamar ya ji daɗin wannan tambaya da ta yi masa. Aikin da ke gabansu yana buƙatar gamsasshen bayani, idan bata fuskanci abun ba, zata iya yin kuskure, idan kuwa tayi kuskure gaba ɗaya tasu ta ƙare.
"Atisayen ƘARSHEN TAU'RIN yana da matakai guda uku, kamar haka:
"Mataki na farko: Ƙarfafa taurarin Gauhan, wanda zai ɗauki shekaru saba'in.
"Mataki na biyu: Ƙarfafa takobin Bankais' (takobin hannun sarauniya Yilan: Bankai 100) wanda shima zai ɗauki shekaru saba'in.
"Mataki na uku: Sanya gangar jikinki, gangar jikin Gauhan da ta BES guda huɗu a cikin tukunyar Ziyazilu har na tsahon shekaru casa'in da tara.
"Abinda yasa zamu fiddo waɗannan takubba bayan shekaru saba'in shi ne, saboda mu kaisu cikin duniyar ƙanƙara SARKI AIYS'MAN ya saka musu albarka.
"Idan gangunan jikin ku, suka ɗauki tsahon wannan lokaci a cikin tukunyar tsumin zaku sami ƙarfi kwatankwacin na TAU'RIN.
"Babu yadda za'a yi a ce kuna daidai da ƙarfinsa har ku biyar sannan ace kun gagara hallaka shi..."
Haka dai wannan sarki yayi ta yiwa sarauniya Yilan bayani akan wannan atisaye har ta gama fuskantar sa.
Sarkin ya bata umarnin komawa birninta ta taho da BES da kuma Gauhan wanda ke ɗaure a kurkuku.
Sarauniya Yilan tayi girgiza ta ɓace ɓat! daga wannan wuri.
A tsakiyar wata kurkuku ta bayyana.
Kai tsaye sarauniya Yilan ta wuce izuwa bakin wani ƙaramin ɗaki, ta baiwa wata kyakkyawar budurwa dake tsaron ɗakin umarnin buɗe shi.
Budurwar ta risina sannan ta buɗe ƙofar ɗakin, Yilan ta shige cikin ɗakin sannan ta finciko fursunan dake ɗaure a cikin ɗakin.
Abin mamaki wani saurayi ne wanda ba zai wuce sarki Samudul Ansari a shekaru ba, ta jawo shi daga cikin ɗakin.
Saurayin ya dubeta cikin ƙeƙasar zuciya da rashin tsoro ya ce, "Nazo wajen ki domin ki taimaka min, shi ne kike wulaƙanta ni?"
Maimakon sarauniya Yilan ta bashi amsar wannan tambaya, kawai sai jikinta ya juye izuwa jibgegiyar macijiya.
Macijiyar ta wangame bakinta sannan tayi loma ɗaya da Gauhan.
Macijiyar ta faɗa cikin wata ƙatuwar rijiya dake tsakiyar wannan gidan kurkuku.
A cikin wannan baƙin daji ta bayyana wanda ta tattauna da BES akan yadda zasu yaƙi Samudul Ansari harma ta tura Aiyni a matsayin wadda zata saro kan Samudul Ansari.
Daji ne baƙi ƙirim wanda lokaci-lokaci ihu da kururuwar aljanu yake tasowa daga cikinsa.
Sarauniya Yilan tana bayyana ta ƙwalawa BES guda huɗu kira.
Cikin gaggawa waɗannan macizai guda huɗu suka fito daga ƙarƙashin ƙasa sannan suka juye izuwa siffar yan-mata guda uku da saurayi guda ɗaya.
Koda BES suka yi arba da sarauniya Yilan tare da wani mutum wanda baima kasance wannan jinsi nasu ba, sai suka cika da tsananin mamaki.
Cikin biyayya suka jejjeru a gaban sarauniya Yilan sannan suka sunkuyar da kawunansu ƙasa cikin biyayya.
Sarauniya Yilan ta fiddo kan Aiyni wanda waɗannan dakaru guda goma suka bata, ta nunawa BES.
"Abar bauta Ziyazilu ta ɗauki rayuwar Aiyni wadda muka tura farautar Samudul Ansari [tsinanne]"
BES suna jin abinda tace, suka durƙusa kan gwiwowinsu, waɗansu hawaye baƙaƙe suka fara zubowa daga cikin idanunsu.
"Sarki Samudul Ansari shi ne wanda ya sare kanta, kun riga kun san cewa tuni Ziyazilu ta riga ta tsinewa Samudul Ansari...
"Yadda duk muke tunanin ƙarfinsa ya wuce nan, wannan yasa mahaifina da kansa ya kira ni muka yi zama na musamman muka tattauna akan yadda zamu ɓullowa wannan abu..."
Nan take sarauniya Yilan tayi musu bayanin atisayen ƘARSHEN TAU'RIN kamar yadda mahaifinta ya sanar da ita.
Bayan gama wannan tattaunawa sarauniya Yilan da BES da kuma Gauhan suka ɓace ɓat! daga cikin wannan baƙin daji.
Suka bayyana a gaban mahaifinta.
Wannan sarki yayi musu jagoranci izuwa saman dutsen Hajarul Gorgon inda Ziyazilu take.
Kai tsaye suka shige cikin kogon da take rayuwa a ciki.
A saman waɗansu jajayen duwatsu Gauhan yayi arba da Ziyazilu.
Macijiya ce koriya mai jajayen ƙaho guda biyu bisa kanta. Idanuwanta baƙaƙe ne siɗik sannan suna matuƙar kama da na sarauniya Yilan.
Waɗannan duwatsu da take kwance akan su, su ne waɗanda Ƙaizadu ya baiwa su sarauniya Arya umarnin juyawa a shekarun baya.
Dukkansu suka zube a gaban macijiyar suka kwashi gaisuwa, sarauniya Yilan ta miƙe tayi mata bayanin abinda ke tafe dasu.
Ziyazilu tayi musu nuni da kanta izuwa cikin wani ƙaton ɗaki, cikin gaggawa suka ƙarasa cikin ɗakin.
Ɗakin ƙatoton gaske ne sannan akwai ƙatuwar tukunya guda ɗaya a cikinsa wadda take zaune akan iska.
Wani irin tiriri kore sharr yana tashi daga cikin wannan tukunya.
Mahaifin sarauniya Yilan yayi tsafi tufafi koraye masu kaurin gaske suka bayyana akan hannunsa.
Sarkin ya rarrabawa su Yilan duk su sassaka.
A wannan waje Gauhan baya gardamar komai domin sarrafa shi ake.
Suna gama saka tufafin, sarkin ya ƙarasa bakin wannan tukunya ya buɗe marufinta.
Sarkin yazo gaban sarauniya Yilan da Gauhan ya karɓi takubbansu, sannan ya samar da wani tsani yace su hau su faɗa cikin wannan tukunya.
Sarauniya Yilan, Gauhan da BES suka taka wannan matattakala suka haye sama sannan suka faɗa cikin wannan tukunya.
Gangunan jikinsu suna nutsewa cikin ruwan wannan tukunya suka tarwatse, ƙofofin jikinsu suka fara zuƙan sinadaran dake cikin tukunyar.
****
Yau *20/03/2023*
Babi na gaba zaizo *23/03/2023* da izinin ALLAH.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment