Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk inda aka ce SARKI, komai nasa yana da kwarjini sannan yana fitowa dabam.
Auren sarauniya Arya da Samudul Ansari yana da bambanci sosai da auren Zarifa.
Ana tsakiyar shirye-shiryen tafiya, wani mahayi ya shigo cikin birnin Wabisal, inda aka taru domin tarar abokan gaba.
Dama wannan birni na Wabisal shi ne a farko, idan ka shigo wannan daula.
Mutanen wannan daula sun yi imani cewa, lallai ta wannan birni mayaƙan Gorgon zasu shigo wannan daula.
Samudul Ansari ya sha alkyabba irinta manyan sarakuna, yana zaune a tsakanin sarauniya Arya da kuma Zarifa.
A wannan lokaci, idan baka san Samudul Ansari ba, zaka ɗauka wani babban sarki ne na wannan daula gaba ɗaya.
Koda yake me bambancin ma a yanzu?
Dukkan mayaƙan wannan daula, umarninsa suke bi, sannan mijin sarauniya ai sarki ne.
Gaba ɗaya jikin wannan mayaƙi wanda ya shigo wannan wuri a lulluɓe yake da sulke. Sulkensa yasha banban da na sauran mayaƙan wurin, don haka anyi saurin shaida shi.
Babu wanda ya ce da shi uffan sannan babu wanda yayi ƙoƙarin tare shi, har ya iso gaban Samudul Ansari sannan ya faɗi ƙasa yana aman jini.
Cikin gaggawa Samudul Ansari ya tallafo shi, sannan ya fidda hular ƙarfen dake kansa.
Yana ganin fuskar wannan mayaƙi ya cika da tsananin mamaki.
Dukda cewa fuskar tasa tayi kaca-kaca hakan bai hana shi gane wannan mayaƙi ba.
Ba wani bane illa Nurbas wannan wanda suka haɗu lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa tsaunin Hajarul Gorgon.
Samudul Ansari bai san meyasa ba, amma tun daga wancan lokaci Nurbas ya kwanta masa a rai. Yana yawan tunaninsa.
Wataƙila ko domin akwai wani gagarumin alheri wanda zai yiwa Samudul Ansari wanda zai amfani rayuwarsa har zuwa sauran jikokinsa.
Cikin tausayawa Samudul Ansari ya ce, "Abokina! Mene ne abinda ya faru da kai, naga jikinka ya samu muggan raunika haka?"
Nurbas ya yi murmushi mai nuna ƙarfin zuciya da jinjina ya ce, "KAI SARKI NE.. NE. DOLE MU SADAUKAR DA R.. RAYUWARMU WAJEN TAIMAKA MAK..KA" Muryarsa na rawa.
Samudul Ansari ya ce, "Me kake nufi?"
Maimakon Nurbas ya bashi amsa, kawai murmushi ne ya cika fuskarsa. Kamar yana tsananin farin ciki bisa riskar Samudul Ansari bai mutu ba.
Nurbas ya fiddo wata zabgegiyar takobi daga gadon bayansa ya miƙawa ita Samudul Ansari, yana karɓar wannan takobi.
Nurbas ya sake fiddo wani littafi wanda ke ɗauke da zuben rubutu masu yawan gaske, ya baiwa Samudul Ansari.
Idanuwansa suka yi fari fat! babu ko alamar baƙin, ya zube kan hannayen Samudul Ansari.
Fuskarsa cike da murmushin mutuwa a hannun sarki Samudul Ansari.
Samudul Ansari yayi baƙin ciki matuƙa da mutuwar mayaƙi Nurbas sannan da kansa yasa aka yi jana'izar Nurbas aka binne shi.
A wannan rana Samudul Ansari a ɗakin Zarifa ya kwana, saboda ita ya fara aura.
Cikin wani ƙaton ɗaki aka kaita wanda aka cika da gadaje da kayayyaki irin na amarya.
Zarifa tana zaune a tsakiyar wannan ɗaki ta gama shirya musu abincin dare, tana jira Samudul Ansari ya shigo cikin ɗakin.
Yana shigowa ya zauna a gefenta, ba tare da ɓata lokaci ba, suka ci abinci.
Bayan kamar sa'a huɗu, Samudul Ansari ya sauƙo daga kan gadon Zarifa sannan ya matsa kusa da wata aci bal-bal ya fiddo wannan littafi da Nurbas ya bashi.
A wannan lokaci dare ya gama rabawa, komai da komai yayi tsit.
Samudul Ansari ya san cewa, irin wannan lokaci ne zai fi samun nutsuwa, shiyasa ma ya bari saida ya gama da matarsa sannan yazo domin duba abinda littafin ya ƙunsa.
Zarifa tana kwance akan gado cikin tsananin farin ciki. Mafarkin da ta daɗe tana jira, yau ya cika.
Samudul Ansari na buɗe wannan littafi, yayi arba da rubutu cikin yaren wannan daula ta su, kamar haka:
"Na kasance ɗan gagarumin mayaƙi a wannan daula, wanda ake matuƙar ji da shi.
"Mahaifina shi ne sarkin yaƙin wannan daula gaba ɗaya. A duk sa'adda yaƙi irin wannan ya taso, mahaifina ne ke jagoranta.
"Kakana na farko yana da wata takobi wadda yake cewa, za'a ɗauki zamanunnuka masu tsaho kafun a sami takobin da zata fi ta.
"Wannan kaka nawa ya ɓoye wannan takobi tasa a cikin wata rijiya wai ita Barzak a ƙarƙashin wani teku, saboda gudun kada wannan takobi ta faɗa hannun waɗanda basu dace ba.
"Wannan baƙuwar annoba da ta shigo wannan daula, ita ce tayi ajalin babana.
"Nayi matuƙar baƙin ciki bisa rasa mahaifina da nayi, ashe nima ina ɗauke da wannan cuta ban sani ba.
"Tabbas naji daɗin ceton rayuwata da kayi. Saboda bani da buri a duniya wanda ya wuce ɗaukar fansa bisa wannan ta'addanci da aka yiwa mahaifina da ma sauran al'ummar da suka mutu.
"Da farko nayi zaton wannan annoba ce da ta sauƙo daga Ubangiji, ban taɓa tunanin waɗannan shaiɗanu ne suka haddasa ta ba.
"Wannan yasa nayi tafiya izuwa birnin Rasha nayi nutso izuwa ƙarƙashin wannan teku, na shiga cikin rijiyar Barzak na ɗauko wannan takobi.
"A hanyata ta dawowa ne, nayi kiciɓus da irin mutanen Gorgon. Tabbas nayi matuƙar girgiza su, domin ni kaɗai nayi musu mummunan ɓarna, albarkacin wannan takobi dake hannuna.
"Wannan yasa suka fara ɗana min tarkuna domin su raba ni da wannan takobi.
"Na san cewa, sarkin yawa, yafi sarkin ƙarfi. Wannan yasa nayi sauri na taho wannan waje domin na damƙa maka wannan takobi.
"Abin baƙin ciki, a cikin waɗannan mayaƙa akwai wani mutum guda, wanda ga dukkan alamu ba jinsin waɗannan halittu bane.
"Wannan mutum shi ne wanda ya samu nasarar yi min waɗannan muggan raunika da kuke gani. Saboda ta salon yaudara ya ɓullo min.
"Ba domin na ankare ba, da tuni ya raba ni da wannan takobi...
"ABOKINA! NA BAKA WANNAN TAKOBI AMANA, KAYI AMFANI DA ITA KA YAƘI MA'ABOTA BANKAI...
"KA ƊAUKAR MIN FANSAR JININA DA SUKA ZUBAR....
"KA ƊAUKAR MIN FANSAR JININ MAHAIFINA DA SUKA ZUBAR...
"KA ƊAUKARWA DUKKAN SAURAN AL'UMMA FANSA BISA RASA ƳAN UWANSU DA SUKA YI...
"WANNAN TAKOBI TAKA CE, KA YAƘI MA'ABOTA BANKAI!!!"
Sa'adda Samudul Ansari yazo nan a karatun wannan littafi, saiya rintse idanunsa cikin tsananin tausayi.
Tabbas Nurbas ya cika ɗan halak. Bai san wane ne Samudul Ansari ba.
Amma ganin adalcin Samudul Ansari yasa yayi masa wannan gagarumar kyauta.
Samudul Ansari ya sake juya shafin farko na wannan littafi inda ya sake yin arba da rubutu. Cikin gaggawa ya fara karantawa.
Akwai zanen wannan takobi wadda a ƙasanta aka rubuta sunanta; SAIF-AL-BARZAƘ.
Mai rubutun ya fara da cewa.
"Kafun komai ana buƙatar ka fiddo wannan takobi domin zaka fi gane bayananta a haka."
Samudul Ansari na karanta wannan sakin-layi, yaje gefen gadonsa ya ɗauko wannar takobi.
Ya dawo inda wannan littafi yake ya zauna, sannan ya zaro wannan takobi.
Wani irin haske ya bayyana a jikin ƙarfen takobin tsahon daƙiƙu goma kafun ya ɓace.
Mai rubutun ya ci gaba da cewa.
"Shin ko kana da labarin saran takobi mai tafiya, wanda ma'abota Bankai [mataki na biyar] suke amfani da shi?
"Sirrin saran takobi mai tafiya shi ne, rubutun ɗalasiman ɓacewa ake rubutuwa a jikin takobin.
"A duk lokacin da ma'aboci irin wannan takobi yayi amfani da wannan salo, irin wannan samfurin takobi ne take fita daga tsinin takobin nasa sannan taje ta ƙaddamar da aikin da ya saka ta.
"Iya nisan gudun takobin Bankai mai tafiya [mataki na biyar] baya wuce rabin zango.
"Wannan takobi ta Saif-Al-Barzak tafiyanta yana kaiwa tsahon zango goma.
"Sannan saɓanin takobin Bankai wadda tana ƙara gaba tana rage ƙarfi, takobin Saif-Al-Barzaƙ tana ƙara gaba tana ƙara ƙarfi.
"Iya nisar abin harinta, iya ƙarfin da zata ƙaddamar masa."
Samudul Ansari na zuwa nan a karatun wannan littafi, ya sake duban wannan takobi da kyau cikin kallon jinjina da jin daɗi.
Tabbas in dai yana tare da wannan takobi, babu abokan gabar da zaiyi shakka.
Ya sake buɗe shafi na gaba a cikin wannan littafi.
Mai rubutun ya ci gaba da cewa.
"Mafi yawancin takubban duniya da sinadarai guda uku ake haɗa su. Wasu dalma, ƙarfe da wuta. Wasu jini, dalma da ƙanƙara. Hatta takobin Bankai da sinadarai guda huɗu aka haɗa su; iska, sinadarin Reniu [ƙarfin damtse], dalma da walƙiya.
"Ita kuwa, takobin Saif-Al-Barzaƙ da sinadarai guda shida aka haɗa ta; sinadarin Jeeish [ƙarfen dutse], sinadarin iska, narkakkiyar dalma, ƙanƙara, jini da kuma ruwa.
"Takobin Saif-Al-Barzaƙ tana iya juyewa izuwa walƙiya, tana iya juyewa izuwa Jeeish, tana juyewa izuwa ƙanƙara, kowanne irin wuri ka tsinci kanka a duniya zaka iya yaƙi da takobin Saif-Al-Barzaƙ.
"A cikin saran takobin akwai sanyi kamar ƙanƙara, akwai sinadarin jini wanda yake gurɓata dukkan jinin da ya ratsa ta cikinsa, akwai ruwa mai ɗauke da sinadarin tsayar da ruwan dake gudana a jikin halitta.
"Waɗannan kaɗan daga cikin falalolin wannan takobi."
Samudul Ansari na zuwa nan a karatun wannan littafi, ya girgiza kai cikin tsananin jin daɗi sannan ya rungume wannan takobi a ƙirjinsa.
Ya sake buɗe shafi na gaba inda yayi arba da rubutu sakin-layi guda uku.
Mai rubutun ya ci gaba da cewa.
"Saif-Al-Barzaƙ tana iya samar da samfurinta guda dubu casa'in, komai yawan abokan gaba Saif-Al-Barzaƙ guda ɗaya ta ishe su.
"Saif-Al-Barzaƙ bata hana makami yayi tasiri akan mutum, saboda duk wanda makami ba zai illata shi ba, ba cikakken jarumi bane.
"Saif-Al-Barzaƙ zata mulki wannan duniya gaba ɗayanta, wannan shi ne abinda aka rubuta a jikin ƙarfen wannan takobi."
Samudul Ansari ya yi murmushi, dama can shi bai kasance mai shan magunguna waɗanda zasu hana makamai yin tasiri akansa ba.
A can ƙasan wannan littafi ne aka rubuta, "Babu buƙatar ka karanta abinda ke gaba na cikin wannan littafi matuƙar baka taɓa fita yaƙi da wannan takobi ba."
"Saboda haka ana baka shawara, ka fara fita yaƙi da wannan takobi koda sau ɗaya ne, kafun ka karanta abinda ke gaba."
Samudul Ansari na karanta abinda aka rubuta, ya mayar da wannan littafi cikin jakar ajiyarsa, sannan ya rataya wannan takobi a gadon bayansa.
Ya tashi tsaye ya koma gefen Zarifa ya kwanta.
Zarifa na ganin ya dawo ya kwanta, ta tashi ta kwanta akan ƙirjinsa suka ci gaba da barci har gari ya waye.
Bayan Samudul Ansari yayi wanka kuma ya kimtsa, sai yaje gaban kabarin mayaƙi Nurbas ya kai masa ziyara.
Yana durƙushe a gaban kabarin ne, yaji an zauna a gefensa.
Cikin gaggawa ya waiga inda ya kalli ashe sarauniya Arya ce a gefensa.
Samudul Ansari bai ce da ita komai ba, har ya gama addu'o'insa suka tashi zasu tafi.
"Ya ya daren ka na farko?" inji sarauniya Arya.
Samudul Ansari ya yi murmushi ya ce, "Babu laifi, don jiya ban samu wani isasshen barci ba..."
Sarauniya Arya tayi dariya ta ce, "Ka ce jiya kun more amarci kenan?"
"Babu yawa. Na gudanar da nazari akan takobin Saif-Al-Barzaƙ ne..." inji Samudul Ansari a taƙaice.
Sarauniya Arya ta dube shi cikin zolaya ta ce, "Yau rana ta ce. Yau ni ce amarya... Hmm."
A daidai wannan lokaci ne, suka iso inda dubbanin mayaƙa suke.
Samudul Ansari yayi jawabin ƙarfafa gwiwa, sannan ya sanar da su cewa da yamma za'a ɗunguma gaba ɗaya a tafi filin yaƙi inda za'a tari ƙabilar Gorgon.
Mayaƙa suka yi kururuwa suka amsa masa da shirinsu yana tafiya.
Samudul Ansari yana juyawa yayi arba da Zarifa cikin sulken yaƙi, ta rataya takubba guda biyu a gadon bayanta.
Kana ganinta kaga cikakkiyar basadaukiya wadda zata yi matuƙar baiwa abokan gaba ciwon kai.
Tana ƙarasowa ta dubi Samudul Ansari ta ce, "Masoyina! Sarakunan wannan daula ce, suka aiko ni wajenka suna jiranka a gidan mu, domin ku tattauna akan yadda za'a ɓullowa wannan yaƙi."
Samudul Ansari ya gyaɗa mata kai alamar yana zuwa. Zarifa ta juya dokinta ta koma inda ta fito.
Samudul Ansari yana gama yiwa waɗannan mayaƙa bayani, ya kama wani ingarman doki ya hau, ya nufi hanyar da Zarifa ta nufa ɗazu.
Sarauniya Arya tayi sauri ta take masa baya.
Bayan gajeruwar tafiya suka iso wannan gida wanda suka iske dakaru birjik suna tsaro.
Samudul Ansari da sarauniya Arya suka sauƙo daga kan dawakansu suka shige cikin wannan gida, kai tsaye suka ƙarasa ɗakin taro inda waɗannan sarakuna suke jiran su.
Gaba ɗaya sarakunan wannan daula sun gama hallara. Su biyar ne a zazzaune akan kujeru, sarauniya Arya ce cikon ta shidan su.
Kai tsaye ta ƙarasa gefen wani basarake ta zauna.
An tsara wajen zaman nasu, sarakuna uku a hannun dama, sarakuna uku a hannun hagu. A tsakiyar su aka ajiye wata kujera wadda Samudul Ansari zai zauna akanta.
Zarifa tana tsaye a bayan kujerar da Samudul Ansari zai zauna akanta, a wani salon na bayar da kariya.
Samudul Ansari ya zauna akan wannan kujera sannan suka gaisa da sarakunan.
Wani basarake ya dubi Samudul Ansari ya ce, "A matsayinka na wanda zai bayar da umarni a wannan yaƙi. Wanne irin tsare-tsare da kuma dabarun yaƙi zaka ɓullo dasu waɗanda zasu bamu dama akan abokan gabar mu, tunda mun san cewa wannan yaƙi dake gabanmu ba ƙarami bane, kuma bamu san yadda ƙarshen sa zai kasance ba."
Samudul Ansari na jin wannan batu na wannan sarki ya miƙe tsaye, ya dawo gaban wani teburi dake tsakiyar su ya tsaya.
A bisa wannan teburi akwai mutane da aka gina da duwatsu masu yawan gaske, waɗanda ake yawan amfani dasu wajen bayyanar da dabarun yaƙi.
Samdul Ansari ya dubi sarakunan ya ce, "Ina daga cikin waɗanda suka je daular Gorgon suka ga masifun dake cikinta, sannan suka dawo.
"Maganar gaskiya ita ce, yaƙi da waɗannan mutane abu ne mai mugun haɗari. Saboda a kowanne lokaci, mutum zai iya rasa rayuwar sa.
"Na gwabza yaƙi da ƙananun cikinsu [waɗanda basu da Bankai], sannan nayi nasara akansu na fatattaki wasu, wasu kuma sun mutu.
"Babbar illar ƙabilar Gorgon a tunanina da nazarina ba zai wuce abubuwa guda uku ba;
"Abu na farko shi ne, idanuwan Renin-Yilan.
"Renin-Yelin: Waɗansu irin idanuwa ne masu mugun haɗari a duniya. Masana sun ce waɗannan idanuwa suna iya fitar da farin hayaƙi mai ɗauke sinadarin Aiys.
"Sinadarin Aiys na iya juyar da jiki mai jini da tsoka izuwa gunki saboda tsananin sanyin da sinadarin yake da.
"Ma'abota suna da irin waɗannan idanuwa, amma ba kowanne daga cikinsu ne yake da irin idanuwan ba.
"Babban masani ya ce, duk wanda muka kalla da takobin Bankai mai mataki na arba'in yayi sama, yana iya sarrafa irin waɗannan idanu.
"Wannan shi ne babbar ma'abota Gorgon na farko. Watau juyar da jiki izuwa gunki.
"Abu na biyu shi ne, wannan dafi da suke sakawa a cikin ruwan sha wanda yake watsa muggan cututtuka a cikin al'umma.
"Wannan shi ne babbar illar ma'abota Gorgon ta biyu; gurɓata ruwan sha.
"Abu na uku shi ne, TAKOBIN-BANKAI.
"Kamar yadda muka fara samun bayanai, waɗannan shaiɗanu sun yi imani matuƙa da waɗannan takubba nasu masu mugun haɗari.
"Bankai mataki-mataki ne. Akwai mataki na ɗaya zuwa na huɗu, akwai biyar zuwa goma, akwai sha-ɗaya zuwa talatin da tara.
"Akwai arba'in zuwa casa'in da tara.
"Akwai ɗari zuwa dubu.
"Ba'a gudanar da ƙwaƙƙaran bincike akan waɗannan matakai ba, shiyasa bamu samu ƙwararan bayanai akan su ba."
Lokacin da Samudul Ansari yazo nan a zancensa sai yayi shuru, gaba daya mutanen dake cikin wannan ɗakin taro suka yi masa kallo cikin jinjina.
Wani basarake ya dube shi ya ce, "Tabbas kayi bayanai masu gamsarwa akan Gorgon, shin ko zamu iya sanin daga ina ka samu dukkan waɗannan bayanai alhalin ance da kaje daular tasu ma, guduwa kayi?"
Samudul Ansari yayi guntun murmushi ya dubi sarkin ya ce, "Wannan guduwa da nayi tayi amfani tunda a sanadiyarta, na haɗu da sarkin ƙabilar Azbin, sannan a sanadiyarta na samo maganin wannan annoba.
"Duk wanda ya haɗu da sarkin Azbin, yana samun alheri da yawa a rayuwarsa.
"Wannan na daga cikin alheran da na samu wato kyakkyawan bayani akan Gorgon."
Sarakunan suka gyaɗa kai cikin fahimta.
Sarauniya Arya ta dubi Samudul Ansari ta ce, "Babban mayaƙi! Muna buƙatar kayi mana bayanin tsare-tsaren wannan yaƙi da kuma dabarun da ka shirya?"
Samudul Ansari ya sake dubansu ya yi murmushi sannan ya fara bayani.
"Na daga cikin tsare-tsaren wannan yaƙi rashin cakuɗuwa da mutanen ƙabilar Gorgon, saboda idan aka cakuɗu da juna zasu samu kyakkyawar dama ta illa ta mu.
"Mayaƙanmu ba za su na kuskuren tunkarar ma'abota Bankai ba.
"Saboda ma'aboci Bankai guda ɗaya, zai iya ja da mayaƙanmu guda dubu ɗari..."
Cikin rashin fahimta wannan sarki wanda yayi magana da farko ya tashi tsaye ya ce, "Ko kaɗan bamu gane wannan bayani naka ba.
"Ta ya ya za'a yi yaƙi ba'a haɗe a waje guda ba? Anya an taɓa yin haka kuwa?
"Idan har ma'aboci Bankai zai iya ja da mayaƙa guda dubu ɗari ta ya ya zamu iya kawar dasu?"
Samudul Ansari ya dubi basaraken ya ce, "Gaggawar me kuke yi? Ku tsaya nayi bayanin dabarun wannan yaƙi mana."
Ya sake duban su ya ce, "Ina so a bar min dukkan ma'abota Bankai ɗin da zasu zo wannan yaƙi, ni kaɗai zan gama da su.
"Zamu raba dakarun mu izuwa kaso uku. Kaso na farko, zasu tsaya a ɓangaren gabas, kaso na biyu a ɓangaren kudu, kaso na ƙarshe zasu tsaya a ɓangaren arewa.
"Ni da masu taimaka min zamu tsaya a gaban wannan runduna domin kare sauran mayaƙa daga sharrin ma'abota Gorgon.
"Indai muka yi hakan, akwai yiwuwar samun nasara a wannan yaƙi da kaso saba'in cikin ɗari.
"Wannan salon yaƙi ne wanda aka daɗe ba'a yi amfani da shi ba."
Har wannan basarake ya sake miƙewa zai ce wani abu.
Sarauniya Arya tayi gaggawar dakatar da shi ta ce, "Kayi haƙuri ya kai Amnaz. Tun da babban mayaƙi ya kawo wannan dabara, zamu gwadata domin ganin abinda yake hange."
Sauran sarakuna suka gyaɗa kai, alamar sun amince da wannan shawara nata.
Dole sarki Amnaz ya koma ya zauna.
Da wannan suka kawo ƙarshen wannan tattaunawa.
Samudul Ansari ya miƙe ya fice daga cikin wannan ɗaki na taro. Zarifa da sarauniya Arya suka take masa baya.
*****
Yau *04/03/2023*
Babi na gaba zaizo *06/03/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 93-94: *Ruhin Samudul Ansari*
*
***TARIHIN SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
UMS
*
Samudul Ansari, Zarifa da sarauniya Arya suna fitowa daga cikin wannan gida, suka yi arba da wani mayaƙi sanye cikin sulke da hular ƙarfe ya rufe fuskarsa ya nufi cikin gidan.
Dama a wannan lokaci sun bar waɗannan sarakuna guda biyar, suna tattaunawa akan tsare-tsare da dabarun yaƙin da Samudul Ansari yazo da su.
Ga dukkan alamu wannan mayaƙi ma, wata tattaunawa yake so yayi da waɗannan sarakuna.
Samudul Ansari yana ganin cikin idanun wannan mayaƙi ya shaida shi, saboda idanuwa ne da ba zai taɓa mantawa da su ba.
Zarifa tana ganin mayaƙin ta ɗaura hannayenta kan takubbanta guda biyu, tana ƙoƙarin zaro su domin ta afka masa.
Sai da Samudul Ansari ya dakatar da ita, sannan ta fasa.
Mayaƙin ya wuce ya shige cikin wannan gida.
"GAUHAN ANSARI..." inji Samudul Ansari. "Ko meye zai faɗawa waɗannan sarakuna. Oho?"
Sarauniya Arya tana jin haka, ranta ya ɓaci ta juya zata koma cikin wannan gida domin tasa a hukunta Gauhan amma sai Samudul Ansari ya dakatar da ita.
"Ki ƙyale shi, lokacin da za'a yi masa hukunci zai zo." inji Samudul Ansari.
Suka fice daga cikin wannan gida suka tunkari sansanin mayaƙa domin gabatar musu da tsare-tsaren wannan yaƙi sannan a sake baiwa wasu daga cikinsu horon yaƙi.
Tsakanin sarauniya Arya da Zarifa babu wani tsana ko kuma ƙiyayya. Soyayya ce a tsakaninsu mai ƙarfi saboda sun fuskanci cewa dukkansu mijinsu yana ƙaunar su.
Suna isowa sansanin mayaƙan, Samudul Ansari ya kirawo sarkin-yaƙi ya bashi umarnin tara dukkanin waɗannan mayaƙa sannan ya sanar da shi umarnin da zai sanar da su.
Nan take sarkin-yaƙi ya cika wannan umarni.
Kusan sa'a huɗu suka ɗauka suna baiwa dakarun sabon horo, kafun rana ta doshi yamma ta kusa faɗuwa.
A dai-dai lokacin ne, waɗannan sarakuna suka fito daga wannan ɗakin-taro wanda suka tattauna da Gauhan.
Samudul Ansari, Zarifa da sarauniya Arya basu san abinda Gauhan ya sanar da waɗannan sarakuna ba, amma suna fitowa daga cikin wannan ɗakin taro.
Kowanne sarki ya kirawo sarkin-yaƙinsa sannan ya bashi umarnin tara dukkanin dakarunsa.
Sarauniya Arya ta dubi sarakunan ta ce, "Mene ne abinda ya faru? Bayan mun gama tattaunawa akan tsare-tsaren yaƙi. Ya ya za kuzo da sabon abu?"
Sarakunan guda biyar suka yi dariya suka ce, "Idan ke soyayya tasa kin makance, to mu ba zamu makance ba.
"Tsare-tsaren Samudul Ansari babu abinda zasu tsinana mana a wannan yaƙi face mummunar asara.
"Da mu rasa dukiyar mu da al'ummarmu, gwamma mu bi shawarar da Gauhan ya kawo mana.
"Ko ba komai mun ga kan ɗaya daga cikin mutanen Gorgon a hannunsa, wannan ya tabbatar da cewa zai iya yaƙar su..."
Sarauniya Arya ta ce, "Lallai za ku tafka babban kuskure, ba ku san sharrin ma'abota Bankai bane shiyasa.
"Ina mai jan kunnenku da kuyi amfani da wannan shawara da Samudul Ansari ya bamu.
"Ko ba komai shi ne ya shiga har cikin daular tasu sannan ya fito a raye."
Sarakunan suka sake ƙyalƙyalewa da dariya suka ce, "Ke yarinya ce ƙarama shiyasa, da mahaifinki yana nan a raye, ba zai yarda da shashancin wannan yaron ba..."
Sarauniya Arya ta murtuƙe fuska ta ce, "Kada ku kuskura ku taɓa kimar mahaifina..."
Samudul Ansari ya dakatar da ita da hannu ya dubi sarakunan guda biyar ya ce, "A duk lokacin da hankalinku ya dawo jikinku, ƙofa a buɗe take gareni, kuzo mu haɗa ƙarfi-da-ƙarfe mu yaƙi ma'abota Bankai."
Sarakunan suka sake bushewa da dariya, daidai lokacin Gauhan ya ƙaraso wannan waje suka yi kallon-kallo da Samudul Ansari.
"Wai aka ce kaje daular Gorgon, amma baka dawo da alama guda ɗaya da zata

Please Login or Register in order to submit comment