Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ababen sha suka bayyana da yawa a cikin iska, a gaban kowanne ɗaya daga cikin su. Barban ya riƙo kofin shayi mai zafi ya kurɓa sannan yayi musu bismillar cin wannan abinci.
Ba tare da gardamar komai ba, Aymanul Faris, Riya da sarki Dujalu suka ɗauki farantan abinci suka fara ci.
Barban na ganin sun ƙoshi ya sake kurɓar wannan shayi dake hannunsa, sannan yayi gyaran murya ya dube su. "Ku nutsu da kyau domin jin bayanin da duk duniya mutane ƙalilan ne suka sani. Kuyi sani cewa babu mai jin tarihin ƙabilar Aswad face wanda aka yarda da shi."
Yana zuwa nan a zancensa ya juya ya dubi Aymanul Faris da Riya ya ce, "Kuyi haƙuri farkon haɗuwa ta da ku, na ɓoye muku ainihin ƙabilata. Tabbas ni ba ɗan ƙabilar Kuyuru bane. ASWAD sunan ƙabila ta."
Aymanul Faris da jaruma Riya basu yi wani mamaki ba, domin dama can abin yana damunsu. Sun san cewa duk wani wanda ya haɗa jini da Samudul Ansari gawurtaccen sadauki ne, to ya akayi Barban bai kasance sadauki ba?
Tabbas a yau sun sami amsar wannan tambaya, daga bakin Barban ɗin kansa.
Barban ya yi murmushin jin daɗi bisa fahimtarsa da suka yi, ya sake kurɓar wannan shayi dake hannunsa, sannan ya fara jawabi.
"Kimanin shekaru ɗari uku da hamsin baya, akwai waɗansu irin mutane dake rayuwa a gefen wani babban kogi a birnin Shaha. Waɗannan mutane suna da bambanci matuƙa da irin mutanen wannan birni na Shaha.
"Abu na farko da ya bambanta su shi ne, ko kaɗan waɗannan mutane basu kasance jarumai ba, hasalima jikinsu ba shi da bambanci da na matayensu. Abinda ya bambanta su da matansu kawai shi ne mama da kuma fasalin jikin namiji ko mace.
"Waɗannan mutane su ne ƴan ƙabilar Aswad.
"Mutanen garin Shaha basu cika mu'amala sosai da waɗannan mutane yan Aswad ba, saboda na farko basu kasance jarumai ba. A wancan lokaci kuma, babu abinda yayi shuhura a birnin Shaha, idan ba jarumtaka da ƙarfin damtse ba.
"In dai mutum ba shi da jarumtaka ko ƙarfin damtse, to zaman wannan birni zai yi matuƙar ba shi wahala. Saboda tamkar bayi haka za'a mayar da su.
"To, kamar yadda na taɓa faɗa muku a baya. Birnin Shaha babban birni ne, wanda ake ganin yafi ƙarfin a kira shi da birni sai dai daula.
"Duk inda aka samu daula, to tafi ƙarfin mutum ɗaya ya mulketa, wannan yasa sa'adda sarki Al-Khamis ya mutu, aka raba wannan birni gida biyu kamar dai yadda na taɓa baku labari.
"A ƙarshen birnin Shaha-Meher akwai wani ƙaramin sarki da aka baiwa mulkin wannan yanki wanda mutanen ƙabilar Aswad suke rayuwa a cikinsa. Wannan yanki ana kiransa da suna Barban, shi kuma wannan sarki sunansa Halad.
"A taƙaice dai, Barban sunan da nake amsawa sunan wannan yanki namu ne.
"Sarki Halad azzalumi ne mara tausayi. A ɗan wannan wuri da aka bashi yayi mulki zaluntar talakawa kawai yake.
"Babban abinda yafi takurawa talakawansa da shi shi ne, ayyukan gona masu wahalan gaske. Sarki Halad yana da wata ƙatuwar gona wacce ya wareta musamman domin mutanen ƙabilar Aswad suyi masa nomanta.
"Noman ba wai na shekara ɗaya bane, kusan kowacce shekara su suke yi masa aikinta.
"Mutanen Aswad basu da wani ƙarfi na azo a gani saboda haka aikin da sarki Halad ke saka su yasa suka fara galabaita. Wasu daga cikinsu suka fara kamuwa da muggan cututtuka wanda a ƙarshe suke ajalin su.
"Maimakon wannan yasa sarki Halad ya raga musu, ƙara musu tsanani ma yayi. Kafun ka ce me, yara sun fara zamowa marayu, mata sun fara dawowa zaurawa.
"Wannan yasa mutanen ƙabilar Aswad suka yi wata ganawa ta sirri a cikin wani ƙebantaccen gida. Shugaban wannan ƙabila shi ne wanda ya kira wannan tattaunawa.
"Mutanen ƙabilar Aswad suka yanke shawarar zuwa wajen sarki Halad domin sanar da shi matsalar su, wataƙila ko zai raga musu.
"Wannan shugaba nasu shi ne wanda ya jagoranci wannan tafiya ta zuwa wajen Halad. Sun je wajen sarki Halad lafiya amma wulaƙancin da yayi musu yafi ƙarfin a fasalta.
"Dakaru sarki Halad suka kama su ɗaya bayan ɗaya, Halad bai ga girmansu ba. Yasa aka zane su ɗaya bayan ɗaya.
"Bayan an gama zane su, sarki Halad ya kore su daga wannan fada sannan ya ce, gobe yana jiransu a gona domin su zo a ci gaba da aiki.
"Wannan abu da sarki Halad ya yiwa waɗannan mutane, ba ƙaramin ɓata musu rai yayi ba. Saboda mutane ne su masu tsananin kunƴa.
"Babu wanda ya kai wannan shugaba nasu harzuƙa saboda dukkansu yafi su manyanta, kuma ko ba komai ai shi shugaba ne bai kamata a wulaƙanta shi a gaban mutanensa ba.
"Wannan yasa su na dawowa yankinsu ya shiga gidansa, ya tara matansa da yaransa yayi musu sallama ya ce, zai shiga duniya neman ɗaukaka domin gusar da wannan wulaƙanci da ake yi musu.
"Wannan mutumi ana kiransa da suna Anbalu.
"Sarki Halad na samun labarin wannan tafiya da Anbalu yayi, ransa ya ɓaci yasa aka kamo ƴaƴansa da matansa aka kulle su a kurkuku sannan aka yi ta gana musu azaba.
"Anbalu na barin cikin birnin Shaha ya shiga cikin teku ya fara tafiya, ba tare da sanin inda ya dosa ba.
"Dama ya tanadi abincin guzuri mai yawan gaske a cikin jirgin kwale-kwalen nasa. Don haka hanya kawai yasa a gaba yayi ta tafiya.
"Tsahon kwanaki bakwai cir Anbalu ya shafe yana wannan tafiya a cikin teku, ba tare da ya tsaya koda sau ɗaya ba. A duk sa'adda yaji barci kawai kwanciyarsa zaiyi a cikin jirgin.
"A ranar kwana ta bakwai ɗin ne da tsakiyar dare, rakuman ruwa suka sauyawa jirgin Anbalu akala. Da yake yana kwance yana barci ne baisan abinda ke faruwa ba.
"Da sassafe yaji kwanciyar wannan jirgi ya sauya. Tayi sama, tayi ƙasa tamkar zata kife. Wannan yasa ya farka cikin gaggawa domin ganin abinda ke faruwa.
"Anbalu ya tsinci kansa a cikin wata mahaukaciyar teku wadda ruwanta keta hautsinewa a waje guda tamkar zai haɗiye dukkan abinda ke wajen.
"Inda a ce iya wannan ne, to da da sauƙi. Amma wani irin baƙin hadari ne a saman wannan teku wanda ya ɓoye rana sannan waɗansu irin jajayen walƙiya suna ta sukuwa a cikinta.
"Wannan wuri baiyi kama da ko'ina ba a duniya face tekun masifa da bala'i, wanda zuwa wurin kaɗai ya isa ya firgita mutum.
"Anbalu bai kasance sadauki ko jarumi ba, amma bai da tsoro. A imaninsa dukkan abinda ya faru da mutum, dama can an riga an rubuta, ko ya ya mutum zaiyi bai isa ya tsalleka ba.
"Sannan a imanin Anbalu babu kalmar 'ba zai yiwu ba' kwata-kwata. Dukkan duniya babu abinda ba zai yiwu ba, sai dai a gagara yin sa kawai.
"Wannan yasa baya taƙama da komai, ya fito wannan tafiya mai mugun haɗari wanda hatta shi kansa bai san ina zaije da abinda zai nemo ba.
"Anbalu ya tsaya zuru-zuru a wannan wuri ya rasa gaba zaiyi ko kuma baya. Idan ya ce zaiyi gaba, ina yasan zai je? Sannan idan ya ce bayan ma zai koma duk ɗaya ne.
"Tsayawar sa a wuri ɗaya zata iya sawa wannan kwale-kwale da yake cikinsa ya nutse gaba ɗaya. Anbalu ya yi shuru yana tunanin abinda ya kamata yayi, ya ƙurawa wannan baƙin hadari idanu.
"Kafun Anbalu ya gama yanke shawarar abinda ya kamata yayi, yaga wannan baƙin hadari dake sararin samaniya ya soma tsagewa, wani irin baƙin abu mai razanarwa na bayyana daga cikinsa.
"Duk tsananin rashin tsoro irin na Anbalu sai da ya firgita da ya kalli wannan abu. Saboda wannan abu bai yi masa kama da komai ba face baƙin ifritun aljani wanda ganinsa kaɗai ya isa yasa mutum karkarwa.
"Sannu-a-hankali siffar wannan baƙin abu ta ci gaba da bayyana a sararin samaniya, wannan baƙin hadari kuma ya ci gaba da haɗewa a waje guda.
"Jim kaɗan, siffar wani ƙaton aljani baƙi ƙirim ta bayyana a cikin iska saman wannan teku. Aljanin ya tsaya a cikin wannan baƙin hadari ya ƙurawa Anbalu idanu.
"Saboda tsananin baƙin jikin wannan aljani, Anbalu baya iya kallon siffarsa sosai saboda ta saje da kalar wannan hadari dake yawo a sararin samaniya.
"Aljanin ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya wacce sauraron ƙarar aradu yafi ta sauƙi. Ya dubi Anbalu ya ce, ƙarfin zuciyarku yana matuƙar burgeni. Ga shi dai ba ku da jarumtaka da ƙarfin damtse amma sam ba ku da tsoro.
"Wannan yasa na janyo wannan jirgin ruwa taka nan wurin domin na taimaka ka kai wani babban matsayi a duniya. Kai ba ma kai ba, dukkan wani wanda ya haɗa jini da kai sai ya gawurta.
"Anbalu ya kasa kunnuwa sannan ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ya baiwa wannan aljani nutsuwarsa domin jin bayanan aljanin.
"Aljanin ya ce, ni sunana Fairar Zas. Wannan wuri da kazo shi ne inda muke rayuwa ni da sauran yan uwana.
"Tun da baka kasance jarumi ba, kuma baka kasance sadauki ba. Babu abinda ya kamace ka face zamowa gawurtaccen boka wanda aka jima ba'a ga irin sa ba.
"Kayi sani cewa akwai wani babban sirri a cikin jininka wanda ake buƙatar ka farkar da shi. In dai ka farkar da wannan sirri, ba ma kai ba, duk wani ɗan ƙabilar ka sai ya zamo abin tsoro a duniya gaba ɗaya.
"Abinda ake buƙata shi ne kaje birnin Ranayes, ka haɗu da sarauniya Rana kayi ido huɗu da ita sannan ka santa ƴa mace.
"In dai idanunka suka kalli cikin nata daga wannan lokaci kalarsu zai sauya, sannan idan ka sadu da ita, wannan zai sa jininku ya haɗu daga nan babban sirrin tsafi zai na yawo a cikin jikinka wanda zai firgita dukkan bokayen duniya.
"Sannan daga wannan lokaci da kai da dukkan wani ɗan ƙabilarka zaku na samun manyan hadiman aljanu a matsayin masu gidanku.
"Babu wanda zai samu babban hadimin aljani a matsayin maigidansa ba tare da ya ɗaukaka ba.
"Anbalu na gama jin bayanin aljani Fairar Zas ya fara karkawar razana. Ya dubi aljanin ya ce, birnin Ranayes fa kace naje?
"Wurin da ake cewa ba shi da nisa sosai da inda rana take fitowa, sannan kuma, na gana da sarauniya Rana har ma na tara da ita? Anya wannan abu zai yiwu kuwa?
"Aljani Fairar Zas yayi gajeruwar dariya ya ce, wannan ya rage naka, ka san dabarar da zaka yi wajen cika wannan buri. Kayi sani cewa matanka da ƴaƴanka suna kulle a kurkukun sarki Halad.
"Iya daɗewar da kayi a wannan tafiya, iya yawan azabar da zasu sha.
"Wannan jawabi na aljani Fairar Zas ya ɓatawa Anbalu rai matuƙa sannan ya sake ƙarfafa masa gwiwa wajen yin wannan tafiya mai mugun haɗari.
"Shi dai wannan birni da ake kira Ranayes, wani ƙaton birni ne dake can ƙarshen birnin Sin ta ɓangaren gabas. Gaba ɗaya garin a tsakiyar wata makekiyar teku yake.
"Saboda tsananin nisansa da doron ƙasashe ana ganin cewa da wuya a samu wani gari bayan sa. Sannan ya saɓa ƙa'ida, wannan birni idan rana ta fito sa'a biyar kawai take a sararin samaniya take faɗuwa.
"Mutanen wannan gari ana ganin kamar basu cika mutane ba, saboda babu mai iya rayuwa a irin wannan yanki nasu wanda dare yafi yawa a can.
"Ita kuwa sarauniya Rana, babu wanda ya taɓa kallonta amma an bayyana siffofinta a cikin littatafan tarihi da yawan gaske.
"A wasu littatafan ance dalilin da yasa ake kiranta Rana shi ne saboda tsananin hasken jikinta wanda baiyi kama da komai ba face hasken rana.
"A wasu littatafan kuma, cewa akayi wai kalmar 'RANA' a ƙabilarsu tana nufi 'kyawu' shiyasa ake kiranta haka. Saboda sarauniya Rana kyakkyawar gaske ce.
"Koma dai mene ne, jikin sarauniya Rana yana da tsananin haske sannan kyakkyawa ce ta gaban kwatance.
"Cikin tsananin fusata da dakewar zuciya Anbalu ya dubi aljani Fairar Zas ya ce, nuna min hanyar da zan bi na isa garin Ranayes, na rantse da darajar iyalaina sai na kwanta da sarauniya domin na zamo gawurtaccen boka.
"Aljani Fairar Zas yayi murmushi ya saka hannu a cikin jakar tsafinsa ya fiddo kwale-kwale da kuma wani ƙaramin tsuntsu baƙi sidik. Ya miƙawa su Anbalu ya ce, ka shiga cikin wannan kwale-kwalen sannan kayi ta bin bayan wannan tsuntsun.
"Duk inda ya shiga kaima ka shiga, daga nan zai kai ka har cikin birnin Ranayes.
"Anbalu ya karɓi wannan kwale-kwale ya shiga cikinta, shi kuma aljani Fairar Zas sai ya saki wannan tsuntsuwa ta tashi sama ta nufi ɓangaren gabas.
"Anbalu ya fara tuƙa wannan kwale-kwale ya bi bayanta da gudu. Abin mamaki gudun wannan tsuntsu a sararin samaniya yana da ƙarfi sosai, tamkar tauraruwa mai wutsiya haka take gudu.
"Wannan kwale-kwalen da Anbalu yake ciki ma, sai ya fara tsala wani irin azababben gudu wanda yafi gaban tunaninsa da fahimtarsa.
"Babu buƙatar Anbalu ya tuƙa shi ko kuma ya tsayar dashi, in dai idanunsa suna kan wannan tsuntsu an gama.
"Wannan tsuntsu yayi ta ketawa ta saman tekuna masu mugun haɗari, wasu na ɗauke da muggan halittun ruwa amma saboda tsananin gudun kwale-kwalen Anbalu ko kallon sa basa yi.
"Wani lokacin ta gefen tsibirirruka suke wucewa, wani lokacin kuma ta gefen manyan jiragen ruwa amma saboda ƙarfin gudun wannan kwale-kwale babu wanda ke samun damar yiwa Anbalu kyakkyawan kallo balle har ya iya shaida shi.
"Duk tsananin wannan gudu da wannan kwale-kwale keyi, Anbalu na zaune lafiya a cikinta. Iska da hazon kan teku basa damunsa. Kallon hanya yake tamkar wanda yake zaune a ƙofar gidansa.
"Tsahon kwanaki goma sha bakwai Anbalu ya ɗauka yana wannan mahaukacin gudu a cikin wannan kwale-kwale ba tare da ya tsaya ba. Akwai abinci da abinsha na alfarma a cikin wannan kwale-kwale wanda duk ɗebarsa da yake ko alamun ƙarewa baya yi.
"A ranar kwana na goma sha bakwai ɗin ne, Anbalu ya tsinci kansa a wani waje wanda yanayinsa yayi dabam da dukkanin sauran yankunan da ya ratsa kafun ya iso wannan wuri.
"Na farko babu rana wadatacciya a wannan wuri sannan akwai wani duhu da ya lulluɓe wajen, kai kace bayan la'asar ne.
"Wannan tsuntsu ya ci gaba da tsala wannan azababben gudu a sararin samaniya, wannan kwale-kwale na take masa baya.
"Tun da ya shigo wannan wuri, yaji gaba ɗaya gashin dake jikinsa suna mimmiƙewa. Jikinsa ya fara karkarwa wanda hatta shi kansa bai san dalilin yin ta ba.
"Bai ɓata wani lokaci ba yana tafiya a cikin wannan sabon wuri ba, ya soma hango ganuwar wani ƙaton birni a can gaba bisa wani tsibiri.
"Birnin na da ban al'ajabi, idan mutum ya hango shi daga nesa zai ɗauka da zallar tagulla aka gina shi.
"Gaba ɗaya birnin a zagaye yake da doguwar ganuwa wanda aka gina da irin wannan tubali mai kama da tagulla. A ƙofar shiga garin kuma, akwai wasu dogayen husumiyoyi guda biyu waɗanda aka gina ƙofa a tsakiyar su.
"Ƙofar shiga garin da zallar ƙarfen zinari mai kashe idanu aka ginata, sannan babu ko alamun mai gadi guda ɗaya a wajen. Wataƙila hakan ya samo asali ne saboda ƙofar a garƙame take da makullai.
"Kwale-kwalen Anbalu ta ƙarasa ƙofar shiga wannan gari ta tsaya. Anbalu ya sauƙa daga cikinta a hankali, ya tunkari ƙofar shiga wannan gari.
"Wannan ƙaramin tsuntsu baƙi ƙirim ya sauƙo kan kafaɗarsa, ya zauna.
"Idan ka hango Anbalu daga nesa, zaka ga dogon mutum sanye da fararen tufafi ɗauke da baƙin tsuntsu akan kafaɗarsa.
****
Yau *22/12/2022*
Babi na gaba zaizo *24/12/2022* da yaddar ALLAH.
1RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 61: *Sarauniya Rana*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
"Anbalu na ƙarasowa ƙofar shiga birnin Ranayes ya tsaya cak, yana tunanin abinda ya kamata yayi. Wannan ƙofa tana da kafofi guda uku a jere, daga ƙasa suka yi sama. A jikin kowacce kafa akwai ƙaton kwaɗo wanda ko alamun inda za'a saka mabuɗi baiyi da.
"Amma akwai rubutun ɗalasiman tsafi cikin wani irin yare wanda tun da Anbalu yazo bai taɓa kallon mai kama da shi ba, a jikin kowanne ɗaya daga cikin waɗannan kwaɗi.
"Yana tsaye ya gagara yanke shawarar abinda zai yi kenan, ya ga wannan tsuntsu dake bisa kafaɗarsa ya dubi waɗannan rubutu dake jikin waɗannan makullai ya karance su ɗaya bayan ɗaya.
"Nan take wannan ƙatuwar ƙofa tayi wata irin ƙara sannan ta soma buɗewa a hankali. A hankali, a hankali har ta gama wangamewa gaba ɗaya.
"Daga wannan wuri da yake tsaye, Anbalu ya hango cikin birnin Ranayes wanda a ganin sa da wuya a samu birnin da zaiyi rabinsa a kyawu da ƙawatuwa saboda tsananin yadda aka tsara shi.
"Wannan tsuntsu dake bisa kafaɗarsa ya juye izuwa wata zabgegiyar takobi wacce ta bayyana rataye a gadon bayansa.
"Wannan takobi na bayyana Anbalu yaji wani irin ƙwarin gwiwa ya shige shi, kawai sai ya kunna kai izuwa cikin wannan birni na Ranayes.
"Garin a cike yake da irin gine-ginen mutanen birnin Sin, sannan mutanen dake cikin sa gajeru ne sosai domin da wuya a samu wanda zai kai kafaɗar Anbalu a tsaho.
"Yanayin suturar dake jikinsu kuma kamar irin na mutanen birnin Sin ne. Ko kaɗan ba su yi kama da na Anbalu ba.
"Bayyanar Anbalu a cikin wannan gari nasu sai ta zamo wani sabon abu wanda hatta dattijai yan shekaru ɗari biyu da ɗoriya basu taɓa gani ba. Wato bayyanar baƙo a cikin garin.
"Tun da aka kafa wannan birni babu wanda ya taɓa kawo masa ziyara saboda tsananin nisan dake tsakaninsu da doron ƙasashe, sannan kafun mutum ya iso birnin sai ya ratsa ta cikin mahaukatan tekuna masu muggan ababen hatsari.
"Wannan yasa suka ɗan yi shakkar Anbalu basu afka masa karaf ɗaya ba, domin yayi musu kwarjini ainun. Saboda yadda suka ga yanayinsa ko alamun kwarzane babu a jikinsa tamkar daga gidansa ya fito a lokacin.
"Wai shin anƴa ta cikin wannan teku ya ratso kuwa, ya za'a yi ace babu rauni ko guda ɗaya a jikinsa. Wannan ita ce tambayar da mutanen wannan gari suka yiwa kansu amma basu sami amsarta ba.
"Anbalu ya bisu da kallo kawai, ba tare da ya ce da su uffan ba. Ya ci gaba da tafiya a cikin wannan birni cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Kai ka ce a cikin birninsa yake tafiya.
"Waɗannan mutane suka fara ƙus-ƙus a ƙasa-ƙasa suna zaro waɗansu irin mahaukatan makaman yaƙi suna kewaye Anbalu a hankali domin kada ya ankara farat ɗaya ya gama dasu.
"Sannu-a-hankali jaruman cikinsu suka yi ta kewaye Anbalu ba tare da ya sani ba, har kusan mutum ɗari da wani abu suka kewaye shi.
"A sannan ne ya soma ankarewa, don haka tsayawa yayi cak a waje guda ya ƙura musu idanu. Mutum ɗari ɗauke da makaman yaƙi barkatai suka saka shi a tsakiya.
"Anbalu baya taƙama da komai tsakanin jarumtaka ko ƙarfin damtse. Hasalima ko allura bai ɗauka ba sa'adda zai fito wannan tafiya.
"Amma a yanzu yana tare da wannan tsuntsu da aljani Fairar Zas ya bashi wanda a halin yanzu yake matsayin takobi, ga ta nan rataye a gadon bayansa.
"Waɗannan mutane suka fara magana cikin wani irin yare wanda ya yiwa Anbalu kama da irin yadda wannan tsuntsu ya karanta wannan ɗalasiman tsafi dake ƙofar shigowa wannan gari.
"Duk da cewa Anbalu baya jin wannan yare amma ya fuskanci cewa, waɗannan mutane muhawara suke akan su afka masa su kashe shi, ko kuma su kama shi a raye su kaiwa sarauniya.
"Koda fuskantar hakan sai Anbalu yayi murmushi ya zaro wannan baƙar takobi dake rataye a gadon bayansa. Ya ɗaga takobin sama cikin iska sannan ya juyo ya fuskanci waɗannan mutane.
"Takobin baƙa ce ƙirim sannan akwai zanen irin wannan tsuntsu a jikin ƙarfenta. Kallon takobin kaɗai ya isa ya firgita mai raunin zuciya.
"Waɗannan mutane suna ganin Anbalu ya zaro takobinsa, suka kwarara uban ihu suka zabura da gudu suka nufi kansa domin su gididdiba shi.
"Kamar umarni wannan takobi dake hannun Anbalu take bashi, nan take yaji yana sha'awar ya kai musu sara dukda cewa tazarar dake tsakanin su mai yawan gaske ce.
"Anbalu ya kaiwa iska sara da wannan takobi dake hannunsa, waɗansu baƙaƙen tsuntsaye masu yawan gaske suka fita daga tsinin wannan takobi suka yi kan waɗannan mutane.
"Suna riskar mutanen suka soma caccakar idanunsu suna mayar da su makafi, kuma cikin zafin nama wanda yafi gaban kwatancen mutum suke aiwatar da hakan.
"Bisa dole sadaukan dake baya suka tsaitsaya suka gagara ƙarasowa inda tsuntsayen suke, saboda bala'in da suka gani.
"Anbalu ya yi murmushi ya mayar da wannan takobi gadon bayansa, sannan ya juya da niyyar ya ci gaba da tafiya.
"Ba zato ba tsammani yaga wani irin haske mai kama da haske rana, ya dira a wannan wuri. Saboda tsananin hasken abun baya iya shaida koma mene ne.
"Waɗannan mayaƙa na ganin wannan haske suka shiga taitayinsa gaba ɗaya, suka mayar da makaman yaƙin su sannan suka jeru a sahu guda suka sunkuyar da kai.
"Anbalu na ganin haka ya soma wasu-wasi akan wani abu. Ya ce a ransa, anya ba shugabar waɗannan mutane bace ta bayyana.
"Wataƙila hasashen da yayi zai iya yin daidai domin kuwa wannan haske na soma disashewa surar wata kyakkyawar budurwa ta soma bayyana, wadda ga dukkan alamu wannan haske daga gareta yake tashi.
"Anbalu ya cika da tsananin mamaki bisa ganin halitta mai bayar da haske karo na farko a rayuwarsa.
"Sannu-a-hankali hasken jikin wannan mace ya gama disashewa, nan take ta bayyana a matsayin ainihin siffarta. Wannan mace dai ba wata bace illa sarauniya Rana wacce Anbalu ya taso wannan gari kacokam domin ya kalli cikin idanunta sannan ya tara da ita.
"Sarauniya Rana doguwa ce sosai sannan tana da tsananin kyawu na gaban kwatance, fatar jikinta na bayar da haske da sheƙi tamkar mudubi. Idanuwanta dara-dara ne sannan launin shuɗi ne dasu.
"Gashin kanta dogo ne sosai domin har ya zubo gadon bayanta, sannan ba baƙi bane siɗik, akwai ratsi-ratsin shuɗi a cikinsa.
"A wannan lokaci sanye take cikin waɗansu irin kaya wanda baka isa kace da auduga aka ɗinka su ba, idan kace na haske ne za'a ce kayi daidai. Sannan mutum ba zai iya kallon cikin idanunta ba, saboda wata hular sanyi da ta saka wacce ta sauƙo har kan fuskarta.
"Wannan yasa Anbalu bai kalli idanun sarauniya Rana ba, sannan jikinsa ya fara tsuma saboda tsananin razana bisa ganin gawurtacciyar sarauniya a gabansa wacce a take zata iya kama shi sannan tayi masa dukkan abinda take so.
"Sarauniya Rana ta dubi waɗannan dakaru nata tayi musu a cikin wannan yare nasu, nan take dukkaninsu suka risina sannan suka watse suka bar wannan wuri.
"Sauran yan uwansu da suka makance kuma, sarauniya Rana ta nuna su da hannunta guda. A take wani farin haske mai kashe idanu ya fito daga hannun nata sannan ya shige cikin idanunsu, suka sake dawowa yadda suke.
"Su ma sarauniya Rana ta sallame su gaba ɗaya, ya rage daga ita sai Anbalu a wannan wuri. Nan fa suka fara kallon kallo cikin nutsuwa.
"Ita dai sarauniya Rana tana mamakin yadda Anbalu ya shigo wannan birni dukda cewa ba ta ga wata sura ta jarumtaka ko sadaukantaka a tattare da shi ba, sannan tana mamakin yadda ya iya shigowa cikin wannan gari dukda irin kafi

Please Login or Register in order to submit comment