Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga cikin gashin kanta suka sari takobin.
Nan take siffar lamba huɗu cikin yaren wannan ƙabila ya bayyana a jikin wannan takobi.
Budurwar ta sake rugowa da gudu kan Samudul Ansari, wanda a wannan lokaci yana durƙushe akan gwiwowinsa sannan ya caka takobinsa cikin ƙasa domin ya tallafi kansa kada ya faɗi ƙasa.
Idanuwansa suna rufewa da buɗewa saboda wannan dafi ya kusa ya gama baibaye dukkan jikinsa, yana gamawa kuma Samudul Ansari zai mutu.
Wannan budurwa ta daka wawan tsalle sama, ta kawowa Samudul Ansari sara a wuya, da nufin ta tsinke masa kai.
Takobin tana tafe tana wani ƙugi mai razanarwa, wanda ke nuna kaifi da ƙarfin saran.
Tabbas wannan takobi tana zuwa wuyan Samudul Ansari, sai dai wani ba shi ba.
Saura ƙiris ta sare masa kai, Samudul Ansari yayi wani irin juyi cikin zafin nama, ya daka tsalle ya koma bayan wannan budurwa.
Kafun ta juyo ta sake kawo masa wani hari, tuni yasa wannan adda ya fille mata kai.
Kan wannan budurwa yayi tsalle sama, macizan dake kan nata suna wani irin ihu. Dungulmin kan yayi dungure izuwa ƙasa.
Samudul Ansari ya tafi ƙasa a hankali kan gawar wannan budurwa, a wannan lokaci saura ƙiris wannan dafi ya gama zagaye dukkan jikinsa.
Cikin sauri ya tsinko wata salka da ya gani ɗaure a kunkumin wannan budurwa.
Ya buɗeta cikin sauri, sannan ya shanye ruwan dake cikinta.
Ashe ba komai bane a cikin wannan salka face makarin wannan takobi wadda take hannun wannan budurwa.
Su kansu masu irin wannan takobi suna tsoronta, koda bisa kuskure idan ta sari jikinsu wannan dafi yana illa akansu.
Wannan shiyasa suke yawo da irin wannan tsumi wanda suke sha, koda wannan takobi ta sare su bisa kuskure.
Ruwan tsumin na gama shigewa cikin jikin Samudul Ansari wannan baƙin dafi ya soma ɓacewa daga jikinsa.
Samudul Ansari ya soma amayar da wani baƙin ruwa daga cikin bakinsa.
Sauran mayaƙan dake tsaron ƙofar wannan gari, ƙamewa suka yi a inda suke tsaye suka gagara motsawa.
A wannan daula tasu duk wanda aka kalla da takobin Bankai, babban mayaƙi ne wanda yake da dakaru wajen guda dubu hamsin a ƙarƙashin sa.
Duk wanda keda mallakin takobin Bankai, abin bauta Ziyazilu ta yarda da shi, sannan sauran manyan sarakunan wannan daula sun san da zamansa.
Taɓa ma'aboci Bankai guda ɗaya tamkar taɓa kimar abin bauta Ziyazilu ne.
Saboda wannan dalili duk abinda ma'abota Bankai zasu aikata a wannan daula, ba'a hukunta su, sannan duk wanda suka taka a wannan daula ya taku.
Mene ne wannan jarumi yake taƙama dashi, da har zai shigo har cikin daular Gorgon sannan ya kashe ma'abociya Bankai?
Wannan shi ne tambayar da waɗannan mayaƙa amma basu sami amsarta ba.
Suna ganin Samudul Ansari ya sha makarin wannan dafi ya miƙe tsaye, suka juya da baya suka ruga cikin wannan birni.
Samudul Ansari yana tsaye yaji an rungumo shi ta baya, yana waigawa yaga ashe sarauniya Arya ce.
"Tabbas ka cika jarumi kuma namijin gaske, na sallama maka..." inji Arya.
Samudul Ansari ya janye jikinsa daga nata sannan ya jawo waɗannan dawakai nasu dake can baya ya dubeta ya ce, "Yi sauri ki hau dokinki, mu tafi. Kowanne lokaci daga yanzu dubbannin mayaƙa zasu iya hallara a wannan wuri."
Bai gama rufe bakinsa ba, suka jiwo ƙarar busa wani ƙaho wanda ya cika wannan birni gaba ɗaya.
Sarauniya Arya tana jin haka tayi gaggawar hawa kan dokinta, suka yiwa dawakan ƙaimi suka shige cikin birnin Mesa ta wannan ƙofa.
Samudul Ansari ya fiddo wannan taswira dake cikin aljihunsa ya dubata, nan take ya baiwa sarauniya Arya bin hanyar da ta nufi gabas.
Nan take dawakansu suka soma tsala wani irin azababben gudu suka tunkari wannan doguwar hanya wadda tayi gabas.
Tafiyar su da kimanin rabin sa'a kacal, wata baƙar runduna ta ma'abota Gorgons ta bayyana.
Yawan wannan runduna zai kai mutum dubu ɗari uku, sannan akwai ma'abota Bankai guda ɗari a cikinsu.
Wani zabgegen mutum na tsaye a gabansu, rataye da takobin Bankai mai mataki na shida a kafaɗarsa.
Gashin kan wannan mutumi gaba ɗaya kore ne sharr, sannan a kwance yake. Idan baka sani ba, sai kace babu yadda za'ayi macizai su bayyana a kayin nasa.
Ba kowanne lokaci bane waɗannan macizai suke bayyana a gashin waɗannan mutane.
Mafi yawancin lokuta sai sun fusata ne ko kuma sai sun fito yaƙi sannan macizan suke bayyana a kan nasu.
Wannan runduna tayi arba da ɗaruruwan gawarwakin masu gadin garin Mesa kwakkwance fululu a wannan wuri.
Kashe mutum ɗaya a daular Gorgon babban laifi ne balle mutum ya kashe har mutane guda ɗari.
Wannan sarki wanda ke rataye da takobin Bankai mai mataki na shida ya fara dube-dube cikin waɗannan gawarwaki yana ƙwalawa wata budurwa kira.
Ga dukkan alamu abinda ya kawo shi wannan wuri, shi ne duba lafiyar wannan budurwa.
Ya kirata ya kai sau uku amma shuru bata amsa ba. Lamarin da yasa jikinsa ya fara karkarwa kenan.
A can nesa kaɗan ya hango takobin wannan budurwa wadda ita ma ta kasance Bankai.
Yana ganin wannan takobi ƙirjinsa ya buga da ƙarfi, saboda a ƙa'idar Bankai wadda keda mallakinta ba zai taɓa rabuwa da ita ba, kullum suna tare
Ya ya aka yi ya kalli iya Bankai bai kalli budurwar ba?
Yana sake ɗaga idanunsa ya hango kan wannan budurwa a jefe a cikin gawarwaki, har a wannan lokaci jini na malalowa daga cikin kan.
Sarkin ya ƙarasa inda wannan dungulmin kai yake, ya ɗaga shi sama, sannan ya ƙare masa kallo.
Sarkin ya taƙarƙare ya kwarara wani irin wawan ihu wanda ya cika wannan yanki gaba ɗaya, hatta Samudul Ansari da sarauniya Arya da suke tazarar goma sha-shida daga wannan wuri sai da suka jiwo wannan kururuwa.
Samudul Ansari ya dubi sarauniya Arya ya ce, "Ga dukkan alamu sarkin birnin Mesa yayi arba da gawar wannan budurwa..."
Sarauniya Arya tayi ajiyar zuciya ta ce, "Haka ne. Shin mun kusa isowa wannan tsauni ne?"
Samudul Ansari ya sake fiddo wannan taswira dake aljihunsa ya dubata.
Daga bisani ya ce, "Nan da cikar daƙiƙa ɗari huɗu kacal zamu isa wurin..."
Sarauniya Arya ta gyaɗa kai bata ce da shi komai ba, suka ci gaba da tsala azababben gudu mai ban al'ajabi.
Daƙiƙa ɗari huɗu na cika suka iso gindin wani ƙaton tsauni mai tsaho da faɗin gaske.
A tsaye zai iya kamu metan. Akwai bishiyoyi da koguna jefi-jefi a jikinsa.
Ba tare da tsoro ko shakkun komai ba, Samudul Ansari da sarauniya Arya suka yiwa dawakansu ƙaimi suka soma hawa kan wannan tsauni.
Tabbas waɗannan dawakai nasu na da ban al'ajabi domin gudu suke a saman wannan tsauni tamkar akan turbaya suke tafiya.
Sai dai basu yi nisa sosai akan wannan tsauni ba, suka cin karo da mayaƙa jifa-jifa masu tsaron tsaunin.
Samudul Ansari ya sake zaro wannan zabgegiyar adda tasa ya fara yaƙar waɗannan mayaƙa da ita.
Da zarar sun zo wucewa ta gefen mayaƙi, sai ya sunkuyo daga kan dokinsa ya fille masa kai ko kuma ya farke ƙirjinsu.
Tabbas a wannan lokaci Samudul Ansari ya nuna tsantsar jarumtakarsa da kuma tsantsar bajintarsa.
Kafun a jima ya hallaka wajen mutum goma, daga wannan lokaci mayaƙan suka daina bayyana har Samudul Ansari da sarauniya Arya suka hawo saman tsaunin Hajarul Gorgon.
A saman wannan tsauni suka yi arba da wani ƙaton gidan bauta.
Gidan yana da tsaho da kuma faɗi sannan a rufe yake da garƙamemiyar ƙofa wadda waɗansu dakaru guda biyu ke tsaronta.
Ba wai dakarun bane suka baiwa Samudul Ansari da sarauniya Arya mamaki ba, face takubban dake hannunsu.
Ko shakka babu Bankai ne, irin na hannun wannan budurwa wadda Samudul Ansari ya kashe.
Wanda ke tsaye a ɓangaren dama, lamba shida ne a jikin tasa, wanda ke tsaye a ɓangaren hagu kuma, lamba biyar ne a jikinta.
Idan aka haɗa waɗannan lambobi goma sha-ɗaya kenan.
Dakarun guda biyu, fuskokinsu a rufe suke da wata irin hula wadda ba'a taɓa gani ba.
Suna ganin Samudul Ansari da sarauniya Arya suka zaro waɗannan takubba nasu.
Faruwar hakan keda wuya. Iskar da ke kaɗawa a wannan wuri, bishiyoyi da sauran halittun wannan wuri, suka soma biyayya ga waɗannan takubba masu suna Bankai.
Tabbas takobin Bankai mai mataki na biyar zuwa shida babbar takobi ce.
*****
Yau *23/02/2023*
Babi na gaba zaizo *25/02/2023* da yaddar ALLAH.
Chapters are available on WhatsApp for buyers 2348136093283 a N300 kacal.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 89: *Ma'abota Bankai*
*
***HIKAYAR SAMUDUL ANSARI***
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga Zahra...
*
ALLAH KA ZAƁA MANA, SHUWAGABANNI NA GARI...
*
U*M*S
*
Samudul Ansari yayi ajiyar zuciya ya dubi sarauniya Arya ya ce, "Ki koma can baya, ki tsaya. Duk wuya, duk rintsi, kada ki kuskura ki ce za ki shigo cikin wannan yaƙi da zan yi da waɗannan mayaƙan!"
Sarauniya Arya ta gyaɗa kai a hankali sannan ta juya ta koma can baya ta zubawa Samudul Ansari da waɗannan mayaƙa idanu. Zuciyarta na dukan uku-uku saboda ta gama tsorata da lamarin mayaƙa masu irin wannan takobi [Bankai].
Mayaƙan na ganin haka, suka tako a hankali suka tsaya a gaban Samudul Ansari.
"Kai! Bil'Adama, wane ne kai? Me ya kawo ka wannan wuri mai albarka?" ɗaya daga cikinsu ya dakawa Samudul Ansari tsawa.
Samudul Ansari ya ce,"Sanin suna na baida wani amfani a wajenku... Abinda ya kawo ni wannan wuri yafi sanin suna na muhimmanci.
"IDAN KUKA BANI HAƊIN KAI, ZAN ƘYALE KU KU RAYU! IDAN KUWA KUN ƘI; BIYU BABU ZA KU YI..."
Waɗannan mayaƙa suna jin kalaman Samudul Ansari suka yi shuru tsahon ɗan lokaci. Dukda cewa fuskokinsu a rufe suke amma ya gane cewa nazarinsa suke yi, suna so su gano da me yake taƙama?
Tsahon ɗan lokaci, kafun daga bisani ɗaya daga cikinsu wanda ke tsaye a ɓangaren dama ya dubi wanda ke tsaye a ɓangaren hagu yayi masa magana a cikin wani yare.
Samudul Ansari bai san abinda suka tattauna ba, saboda baya jin wannan yare.
Cikin daƙiƙa ɗaya wanda aka yiwa maganar ya ɓace ɓat, sannan ya bayyana a gefen Samudul Ansari ya kawo masa wawan sara a kafaɗa da nufin ya tsarge shi gida biyu.
Kai, idan kace ɓacewar da wannan sadauki yayi yafi walƙiya zafin nama, ba za'a ce kayi laifi ba.
Daga ɓacewarsa zuwa kawowa Samudul Ansari wannan bahagon sara, ko daƙiƙa biyar masu kyau ba'a ɗauka ba.
Tabbas ba don Samudul Ansari ya kasance mai baƙin zafin nama ba, da tuni Bankai ta hallaka shi.
Samudul Ansari yasa wannan adda dake hannunsa ya kare wannan sara da wannan mayaƙi ya kawo masa.
Makaman yaƙin na haɗuwa a waje guda, wani irin nauyi ya bayyana a wannan waje wanda ya danne Samudul Ansari yasa yayi tsalle gefe domin ji yayi tamkar ƙasusuwan jikinsa zasu kakkarye.
Mayaƙin na ganin haka, ya sake kaiwa Samudul Ansari sara da wannan takobi.
Tazarar dake tsakaninsu tana da ɗan yawa, mutum zai yi mamaki idan aka ce masa wannan mayaƙi yayi tunanin kai sara dukda cewa yasan akwai tazara a tsakanin su.
Wani irin fai-fai na haske ya fita daga tsinin wannan takobi yayi kan Samudul Ansari da gudu.
Kafun Samudul Ansari ya gama ankarewa, tuni wannan fai-fai ya isa inda yake.
Take ya doki ƙirjinsa da ƙarfi, Samudul Ansari yayi tsalle ya faɗo can baya a galabaice.
Wani lafcecen sara ya bayyana akan ƙirjinsa mai zurfi. Jini ya fara feshi yana malala a ƙasa.
Babu yadda za'a yi mutum yaga wannan sara akan ƙirjin Samudul Ansari sannan ya tunanin Samudul Ansari zai rayu.
Yanka ne ƙato sannan jini mai yawa nata zuba.
Sarauniya Arya na ganin haka, ta fashe da matsanancin kuka. Tabbas bata so Samudul Ansari ya rasa rayuwarsa saboda ta kamu da tsananin ƙaunarsa.
A hankali, a hankali soyayyar Samudul Ansari ta ɗinga ginuwa a cikin ranta, yanzu har ta gama mamaye dukkan zuciyarta, ta kai matsayin da idan bata tare da Samudul Ansari bata jin daɗi ko kaɗan.
Cikin dakewa da jarumtaka irin ta mazan jiya, Samudul Ansari ya miƙe zaune da ƙyar.
Ya fiddo zare da allura daga cikin jakar guzurinsa, ya sake fiddo wani garin magani ya baɗe wannan ƙaton sara da shi.
Jini ya daina zubowa sannan maganin ya kashe zogin wajen gaba ɗaya. Hakan ya baiwa Samudul Ansari damar ɗinke wannan rauni.
Yana gama ɗinke raunin, ya fiddo wani ruwan magani ya sha.
Waɗannan sadaukai ƙamewa suka yi kamar gumaka, suka zubawa Samudul Ansari idanu kawai.
Saran takobin Bankai da saran maciji tamkar hasan da husaini ne, basu da wani bambanci.
Amma Bankai mai tafiya (irin wanda wannan mayaƙi yayi amfani da ita yanzu) bata da dafi ko kaɗan a cikinta.
Sai dai ƙarfin saranta ya ninka na Bankai sau goma, shiyasa indai aka sari mutum tamkar hari guda biyu aka yi masa a lokaci guda; sara da kuma naushi.
Mafi yawancin lokuta duk wanda aka sara da takobin Bankai mai tafiya jikinsa zaftarewa yake, saboda ƙarfin saran.
Tabbas Samudul Ansari namijin gaske ne, domin shi ne mahaluƙin da wannan takobi [Bankai mai tafiya] bata hallaka a sara ɗaya ba.
Kusan daƙiƙa tamanin Samudul Ansari ya ɗauka yana zaune a ƙasa, yana hutawa sannan ya miƙe tsaye.
A wannan lokaci ya ɗan ji ƙwarin jikinsa ya dawo amma ba kamar da ba, sannan yana jin zogin wannan sara har a wannan lokaci.
Wannan mayaƙi na ganin Samudul Ansari ya miƙe, ya mayar da takobinsa cikin kufe sannan ya fara zane da hannayensa akan iska.
Jim kaɗan, siffar wata zabgegiyar takobi ta bayyana akan iska a matsayin haske.
Wannan mayaƙi yasa hannunsa guda ya kamo mariƙinta, ya juyata a hankali akan iska, ya saita Samudul Ansari da ita sannan ya tura ta a hankali.
Takobin ta taho da gudu ta tunkaro Samudul Ansari wanda ke tsaye a can gefe zata sare shi.
Samudul Ansari na ganin haka, ya dubi wani dutse dake gefensa, sannan yayi sauri ya ƙarashi inda dutsen yake yasa hannayensa guda biyu, ya fara ƙoƙarin cicciɓo dutsen.
Nan fa ƙwanjin maza suka bayyana, jijiyoyin jikinsa suka kumbura suka yi burɗin-burɗin, idanuwansa suka yi jawur.
Wannan dutse idan za'a ajiye shi a ƙasa, sai ƙarti goma sun taru sannan zasu iya raba shi da ƙasa.
Saura ƙiris wannan takobi ta haske ta ƙaraso inda Samudul Ansari yake, ya finciko wannan dutse daga ƙarƙashin ƙasa sannan yayi amfani dashi kamar garkuwa.
Wannan takobi ta haske tana haɗuwa da wannan ƙaton dutse, wata ƙara kamar sauƙar aradu ta sauƙa a wannan wuri.
Takobin ta niƙe wannan dutse gaba ɗaya, sannan itama ta ɓace ɓat!
Tabbas ba don Samudul Ansari yayi amfani da wannan dutse a matsayin garkuwa ba, haka wannan takobi zata niƙe namansa.
Mayaƙan guda biyu suka sake ƙamewa suka ƙurawa Samudul Ansari idanu.
Idan mutum ya kalli girman wannan dutse wanda Samudul Ansari ya fizgo daga cikin ƙasa, da kuma saurin da yayi wajen fizgo dutsen, dole ne mutum ya cika da tsananin mamaki sannan ya sallamawa ƙarfin damtsen Samudul Ansari.
Samudul Ansari ya falfala da azababben gudu kan wannan sadauki wanda ke tsaye a gefe guda kamar gunki.
Mayaƙin bai yi wani yunƙuri na kawowa Samudul Ansari hari a wannan lokaci ba, ga dukkan alamu kamar ya baiwa Samudul Ansari dama ce ya gwada ƙarfinsa akansa.
Samudul Ansari na isowa inda yake ya daka wawan tsalle sama, ya kaftawa wannan mayaƙi sara a kafaɗa.
Rigunan jikin waɗannan mayaƙa masu kaurin gaske ne. An tabbatar da cewa duk duniya idan ba wannan daula ba, babu inda ake samun wannan auduga.
Wannan adda na dira bisa kafaɗar wannan mayaƙi, rigar jikinsa ta farke sannan ta addar ta yanki fatar jikinsa kaɗan.
Jini ya ɗan taru a wajen sannan ya soma zubowa ƙasa.
Wannan mayaƙi ya kwarara uban ihu. Ba wai don zogin wannan sara da Samudul Ansari yayi masa bane.
Abinda yasa yake kuka shi ne, mene ne dalilin da yasa wannan adda zata yi nasara akansa?
Duk wanda ke rayuwa a wannan daula ya yarda cewa, duk wani ma'aboci Bankai, Bankai ce kaɗai zata yi illa akan sa.
Duk makaman duniya baza su yi tasiri a jikinsa ba, kai cewa ma ake ko wannan riga tasu mai kauri makamin ba zai huda ba balle har ya isa fatarsu.
Saboda wannan dalili dole wannan mayaƙi ya kwarara ihun takaici, sannan dole yayi shakkar Samudul Ansari saboda ya karya alƙadarinsa.
Mayaƙin ya daka tsalle ya koma can nesa kaɗan da Samudul Ansari.
Cikin fusata ya sake zaro wannan takobi tasa [Bankai] ya kaiwa iska sara sau uku.
Fai-fan iska guda uku suka fita daga tsinin wannan takobi suka yi kan Samudul Ansari da gudu zasu sare shi.
Gudun waɗannan fai-fan iska yafi gaban tunanin mutum, domin cikin daƙiƙa biyu suke isowa waje, komai nisan sa komai kusan sa.
Kafun Samudul Ansari ya ankara tuni muggan saran takobi guda uku sun bayyana a jikinsa; ɗaya a kafaɗa, ɗaya a daidai saran ƙirjinsa na ɗazu wato an fame wannan rauni da ya ɗinke kenan, ɗayan kuma ya zaftare gefen cinyarsa.
Jini mai tsananin yawa ya fara feshi daga jikin Samudul Ansari, wani irin mugun jiri ya ɗebe shi, bisa dole ya durƙusa kan gwiwowinsa domin ba zai iya tsayuwa ba.
Wannan mayaƙi ya rugo da gudu kan Samudul Ansari, yana isowa inda yake yasa ƙafarsa guda ya doki ƙirjin Samudul Ansari.
Samudul Ansari yayi tsalle sama sannan ya faɗo acan baya, mayaƙin ya ɓace ya bayyana daidai kan Samudul Ansari.
Mayaƙin ya ɗaga Bankai ɗinsa sama zai cakawa Samudul Ansari a ciki.
Ba zato ya jiwo kukan mace acan baya, cikin mamaki ya ɗaga kansa sama.
Nan take ya hango sarauniya Arya durƙushe akan gwiwowinta tana ta rusa kuka.
Mayaƙin ya ƙarasa inda take, ya zana ƙaramar wuƙa akan iska sannan ya sa wuƙar ta farke suturar jikin Arya.
Sarauniya Arya tana kuka wannan ƙaramar wuƙa ta gama farke dukkan surar jikinta, ta bayyana babu wani hijabi a jikinta tamkar yadda uwarta ta haifeta.
Wannan mayaƙi na shirin saka wannan ƙaramar wuƙa ta fara yanke sassan jikin Arya, Samudul Ansari ya ɗago kansa a hankali yaga yadda sarauniya Arya take kuka da cin mutuncin da aka mata.
Ransa yayi mummunan ɓaci, yasa yatsarsa guda a cikin ƙasa ya zana wani ɗalasimi, sannan yasa jinin dake zubowa daga jikinsa a cikin zanen da yayi.
Faruwar hakan keda wuya, wani baƙin hayaƙi mai matuƙar ban tsoro ya fara bayyana a sararin samaniya yana tare hasken rana.
Samudul Ansari na ganin haka ya nuna wannan mayaƙi wanda ke gaban sarauniya Arya da hannunsa guda, jikinsa ya sandare ya daina motsi tamkar ya mutu.
Wannan mayaƙi wanda ke tsaye acan baya da wanda ke cin mutuncin sarauniya Arya suka ɗaga kansu sama, suna kallon wannan baƙin hayaƙi wanda basu taɓa ganin irinsa ba.
Hatta ita kanta sarauniya Arya daina kuka tayi, ta ƙurawa wannan baƙin hayaƙi idanu.
Siffar wani mutum ta bayyana a cikin wannan baƙin hayaƙi, kafun daga bisani ya sauƙo ƙasa.
Suturar jikin wannan mutumi bata da bambanci da wannan baƙin hayaƙi da ya cika wannan waje.
Mutumin baya numfashi, baya motsi, baya murmushi, baya fushi. Jikinsa a tsaye yake cak tamkar itace.
Saboda wannan baƙin hayaƙi dake sauƙa a wannan waje, mutum ko fuskar wannan mutumi ba zai kalla ba.
Mayaƙin dake tsaye a gaban sarauniya Arya ya kaiwa wannan mutumi mai sanye da baƙaƙen kaya sara da wannan Bankai tasa sau uku.
Fai-fan iska suka fita daga tsinin takobin suka yi kan mutumin da gudu.
Suna zuwa suka doki jikinsa sannan suka koma kan wannan mayaƙi da ya harbo su.
Kafun mayaƙin ya ankara tuni fai-fan sun sare shi a ƙirji sau biyu, sannan sai a ƙasan cibiyarsa.
Take kayan cikinsa suka fara zubowa ƙasa, ƙirjinsa ya farke, ya zube ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Wannan mutumi wanda Samudul Ansari ya kirawo ya ƙarasa inda Samudul Ansari yake, ya dafa kansa da hannu guda.
Take wani baƙin haske ya bayyana ya baibaye jikin Samudul Ansari.
Kada a manta, tun bayyanar wannan mutumi jikin Samudul Ansari ya sandare gaba ɗaya ya koma tamkar gunki.
Baƙin haske na gama baibaye jikin Samudul Ansari wannan baƙon mutumi mai baƙaƙen kaya, ya saje a cikin wannan hayaƙi ya ɓace ɓat!
Hayaƙin ya tashi sama a hankali, sannan shima ya fara disashewa har ya gama ɓacewa.
Tun sa'adda wannan mayaƙi ya mutu, sarauniya Arya ta buɗe baki cikin tsananin mamaki.
Bata taɓa kallon irin wannan abin al'ajabi ba. Wane ne wannan mutumi wanda ko siffarsa mutum ba zai gani sosai ba?
Baƙin hasken da ya baibaye jikin Samudul Ansari ya ɓace gaba ɗaya.
Samudul Ansari ya bayyana tamkar yanzu ya fito daga wanka babu ko rauni guda ɗaya a jikinsa.
Duk wannan abu da ya faru akan idanun wannan mayaƙi dake tsaye acan baya ya faru, yaga yadda aka kashe ɗan uwansa da yadda Samudul Ansari ya warke.
Nan take ya ɓace daga inda yake tsaye, maimakon ya kawowa Samudul Ansari hari, kawai sarauniya Arya ya ɗaga da hannu ɗaya sannan yayi jifa da ita ƙasan wannan tsauni.
Samudul Ansari na ganin haka ya kwarara uban ihu, yayi tsalle ya doki ƙirjin wannan mayaƙi.
Mayaƙin yayi tsalle ya hantsila baya.
Samudul Ansari yayi hanzari ya fiddo wata murtuƙeƙiyar igiya daga cikin jakar guzurinsa, ya ɗaure igiyar a jikin wani itace sannan ya ɗaureta da kunkuminsa.
Ya daka wawan tsalle sama, ya faɗa ƙasan wannan tsauni ya bi bayan sarauniya Arya.
Samudul Ansari ya tafi da gudu yayi ƙasa, yana tafiya yana ƙarawa kansa gudu da hannayensa.
Tsahon ɗan lokaci kafun ya hango sarauniya Arya wadda ke kwance akan iska tamkar gawa.
Ƙarfin iskar dake kaɗawa a sararin samaniya ta sumar da ita.
Samudul Ansari yana isowa daidai sarauniya Arya ya rungumota a ƙirjinsa, sannan suka ci gaba da faɗawa ƙasan wannan tsauni.
Saboda tsahon wannan tsauni sai da suka shafe sa'a guda suna faɗawa sannan suka faɗo ƙasa tsaunin.
Dake Samudul Ansari ne a farko, jikinsa ya

Please Login or Register in order to submit comment