Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na auri ƴar babban maƙiyin mu."
Hajriya ta ce, "Kada ka damu ɗana. Wannan buri da kake son cikawa da shi mahaifinka ya mutu. Kuma ya yi baƙin ciki sosai da hakan!"
"Shin kin amince nayi tarayya da ita, harma na aureta?" Aymanul Faris ya tambayi mahaifiyar tasa.
Daga jin muryarsa ka san da gaske yake. Idan tace bata amince ba, zai iya rabuwa da Jaanu. Saboda mahaifiyarsa ita ce komai nasa.
Hajriya ta dubi Riya ta ce, "Na amince zaka aureta amma bisa sharaɗi guda?"
Bata jira ya tambayeta ba, ta ce, "Zaka aureta amma a matsayin matarka ta biyu! Riyalatu ita ce wacce na zaɓa ma, kuma dole ita zaka fara aura!"
Af, tuni ta makara shima Aymanul Faris wannan shi ne a ransa, wato Riya ita ce matarsa ta farko saboda ya yiwa soyayyarta halacci.
Aymanul Faris ya ce, "Na gode mamana. Wannan magana mun riga mun gama da ita. Yanzu tambayoyi nake so nayi miki?"
"Ina jinka?" Mahaifiyarsa ta bashi amsa.
"Shin kina da bayanai akan takobin SAIF-AL-BARZAK?" ya tambaye ta.
Hajriya tayi murmushi ta ce, "Wannan tambaya bata da amsa, babu wanda yasan bayanan komai akan wannan takobi face Samazan. Wannan ɗan tsohon dake rayuwa a yankin birnin Hindu."
Aymanul Faris yayi shuru ga dukkan alamu ya ma rasa maganar meye zai kawo.
Hajriya tana fuskantar haka tayi murmushi ta ce, "Shin ka san dalilin da yasa mahaifinka ya baka wasiyya akan ka kula da mahaifiyarka?"
Aymanul Faris ya ce, "Ko ya faɗa min wannan wasiyya ko bai faɗa min ba. Kula dake ya zamo mini dole?"
Hajriya ta sake yin murmushi ta ce, "Baka amsa min tambayata ba, shin ka sani ko baka sani ba?"
"Ban sani ba," inji Aymanul Faris kai tsaye, don ya fuskanci wani bayani mai muhimmanci take so tayi masa.
Hajriya ta ce, "Shin ka san dalilin da yasa ƙauyen Gazwar yake da albarkar noma mai ban al'ajabi?"
Aymanul Faris ya zaro idanu, sannan alamar bai sani ba.
Tun yana yaro ƙarami yake ganin abubuwan al'ajabi a wannan ƙauye. Ƙauyen ƙarami ne, haka ma gonakinsu amma idan suka yi noma a shekara, suna samun amfani mai yawan gaske.
Hakan ne yasa hankalin duniya gaba ɗaya ya karkato zuwa kansu. Attajirai da dama suna zuwa wannan ƙauye su sayi abinci sannan su tafi ƙasashen duniya daban-daban da shi.
Aymanul Faris bai taɓa tunani akan wannan dalili ba. Abinda ya sani shi ne a shekara suna iya noma abinci mai yawan gaske, sannan wannan shi ne arzikin wannan ƙauye nasu.
Ko sau ɗaya bai taɓa tunani akan akwai wani dalili wanda yasa suke da wannan albarkaci na ƙasa ba.
Hajriya ta ce, "Mahaifina shi ne sarkin noma na wannan ƙauye idan baka manta ba, to ka sani cewa ba wai a iya wannan ƙauye yake sarkin noma ba face duk duniya.
"A zuri'armu akwai waɗansu ɗalasimai da muke gado a wajen manƴan mu. Waɗannan ɗalasimai in dai muka binne su a waje, to wajen zai samu albarkar noma sosai.
"Mahaifina sarkin noma ne sannan yana da irin waɗannan ɗalasimai. Shi ne wanda ya binne waɗannan ɗalasimai a birnin Shaha shiyasa muka shahara sosai a fannin noma.
"Ni kuma ni ce wacce ta binne waɗannan ɗalasimai a ƙauyen Gazwar shiyasa tsibirin ya samu albarkar noma sosai.
"Kada kayi tunanin kamar bani da wani amfani a cikin wannan buri naka, wato burin sake kafa birnin Shaha.
"Kayi sani cewa, sanadiyar wannan yaƙi a birnin Shaha a shekarun baya, jini mai yawa ya kwarara akan ƙasa. Sanadiyar haka albarkar noma ta birnin Shaha ta riga ta karye.
"In dai ana buƙatar ta sake bunƙasa kamar da, dole sai an sake binne irin waɗannan ɗalasimai da mahaifina ya binne.
"Ni ce kaɗai wacce zata iya sake binne waɗannan ɗalasimai duk faɗin duniya. Saboda ni ce kaɗai nayi saura daga cikin zuri'ar mahaifina, sauran yan uwana duk an kashe su.
"Kayi sani cewa, idan jama'a suka sake komawa a birnin Shaha, babu abinda zai riƙe su face wannan albarka ta noma.
"Saboda tsananin yawan mutanen dake rayuwa a cikin birnin ya wuce misali.
"A duk lokacin da ka zamo sarki ni ce wacce zata sake farfaɗo da martabar wannan birni ta noma."
Aymanul Faris na jin haka yayi murmushi ya ce, "Ya ke ummina! Alhalin kula da ke yana ƙarƙashina koda kina da wannan ɗalasimi, koda babu shi. Babu abinda zai hanani kare rayuwarki matuƙar ina numfashi!!!"
Haka dai Aymanul Faris da mahaifiyarsa suka ci gaba da tattaunawa akan al'amuran birnin Shaha da irin ɗalasiman Hajriya har zuwa lokaci mai ɗan tsaho. Jaruma Riya tana zaune a gefe tana kallon su.
Koda Hajriya ta fuskanci akwai magana a bakin Riya amma tana kunƴar idanun Ayman sai ta dube shi ta ce, "Ka je ka samu mai gidan naka, zamu tattauna da matarka!"
Aymanul Faris na jin haka yayi murmushi ya ce, "Kamata yayi muyi sallama domin daga can zan wuce wajen Arya!"
Hajriya tayi murmushin takaici ta ce, "A dawo lafiya, amma kada ka daɗe, sannan duk abinda kuka tattauna da ita zaka sanar dani?"
"Wannan ba matsala bane," inji Aymanul Faris lokacin da ya miƙewa tsaye daga kan wannan kujera.
Jaruma Riya ta bishi da wani irin wani kallo mai nuna tsantsar soyayya har ya fice daga cikin wannan falo.
Aymanul Faris yana fitowa daga wannan ɗaki ya ƙarasa inda Barban yake zaune, ya shaida masa cewa ya gama shiryawa domin tafiya izuwa birnin Damashkar wajen gimbiya Jaanu.
Barban ya yi murmushi ya ce, "Ba tare zamu je ba saurayi! Daga kai sai aljaninka zaku je wannan birni. Nima a wannan wuri zamuyi sallama da kai, idan ka gama zanzo na ɗauke ka, muje wajen maigirma Ranganu domin jin aiki na ƙarshe."
Barban na zuwa nan a zancensa, bai bari Aymanul Faris ya ce wani abu ba, ya ɓace ɓat daga wannan wuri.
Barban na ɓacewa aljani Nara ya bayyana a wannan wuri, ya dubi Aymanul Faris ya ce, "TAU'RIN zo muyi sauri mu tafi, Jaanu tana can tana jiran mu?"
Aljani Nara na gama faɗin haka ya ranƙwafa, Aymanul Faris ya haye gadon bayansa. Cikin gaggawa ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya lulluƙa a cikin gajimare.
****
Tun sa'adda Aymanul Faris ya kaiwa gimbiya Jaanu ziyara a watannin baya, daga wannan lokaci ta ci gaba da tafiyar da harkokin mulkin wannan birni kamar yadda ta saba cikin adalci.
Tun daga wannan lokaci bata taɓa wayar gari da rashin tunanin Aymanul Faris ba. A kullum tana farkawa daga barci babu abinda take fara tunowa idan ba shi ba, hatta mahaifinta kuwa.
Gimbiya Jaanu ta sha yin muggan mafarkai akan halin da mahaifinta yake ciki. Mafi yawancin lokuta ana nuna mata shi a cikin mawuyacin hali.
Ko sau ɗaya hankalin Jaanu bai taɓa tashi ba, saboda ta fuskanci cewa mahaifinta baƙin azzalumi ne wanda zai iya yin komai domin cikar burinsa.
Daga lokacin da yayi mummunan ta'addanci a ƙauyen Gazwar, daga wannan lokaci kimarsa ta zube ƙwarai da gaske a idanunta.
Sau da dama gimbiya Jaanu tana tsananin mamakin yadda aka yi son Aymanul Faris ya shiga ranta, alhalin bata san shi ba.
Tun sa'adda idanuwanta suka yi tozali da fuskarsa a farkon haɗuwarsu a cikin wannan turaka nata, daga wannan lokaci wani abu ya soki ƙahon zuciyarta.
Daga wannan lokaci bata iya shafe lokaci mai tsaho, bata yi tunaninsa ba.
A halin yanzu, Jaanu ta samu watanni huɗu tana mulkin wannan birni.
Tuni jama'a suka fara mantawa da baƙin mulkin mahaifinta, saboda tsananin yadda suke jin daɗin nata.
A wannan rana Jaanu ta tashi da wani irin farin ciki wanda ita kanta bata san dalilin faruwarsa ba. Fuskarta cike da annuri sai murmushi kawai take ita kaɗai.
Baƙaƙen kaya ta saka ta fito fada, inda take tafiyar da harkokin mulkinta. Komai na tafiya kamar kullum ana ta fadanci.
Kwatsam! Ba zato taga wani irin tsuntsu jajawur ya shigo cikin wannan fada. Shigowar wannan tsuntsu yasa wani irin ɗumi ya ziyarci fadar kowa sai da yaji, amma babu mai ikon ganin wannan tsuntsu sai ita kaɗai.
Tsuntsun ya zo ya sauƙa akan hannun wannan karaga na ta, yayi wani irin ihu sannan ya tashi ya fice.
Gimbiya Jaanu bata buƙatar wani ƙarin bayani, ta san cewa lallai tana da baƙo mai muhimmanci.
Ta dubi yan majalisar ƙasar dake zaune a gefe guda ta ce, "Ku ci gaba da tafiyar da harkokin mulki, ina zuwa!"
Ƴan majalisar suka amsa mata sannan ta tashi ta fice daga cikin fadar.
Kai tsaye ta shige cikin wannan yanki nata, a wannan karon ma, kamar wancan karon ne. Gaba ɗaya dakarun dake tsaron wannan yanki nata, suna kwakkwance a ƙasa suna ta sharar barci.
Gimbiya Jaanu ta wuce su gaba ɗaya, ta shigo cikin lambunta.
Daga nesa ta hango Aymanul Faris zaune a gindin bishiya tare da wannan tsuntsu zaune akan kafaɗarsa.
Tun daga nesa suka ƙurawa juna idanu. Shi yana tsananin mamakin wai, ace duk wannan kyawu nata ba na ainihi bane akwai wanda ya ninka shi?
Ita kuma tana mamakin yadda jikinsa ya ƙara cika da kuma murɗewa dukda cewa ba wani daɗewa suka yi sosai da rabuwa ba. Aymanul Faris ya miƙe tsaye ya buɗe hannayensa biyu, Jaanu na ganin haka ta ruga da gudu ta faɗa kan ƙirjinsa suka rungume juna, cikin salo mai nuna tsantsar soyayya.
Sai da suka jima a ƙanƙame da juna sannan Jaanu ta fara janye jikinta daga nasa, ta dube shi fuskarta cike da hawaye ta ce, "Nayi kewarka matuƙa masoyina, tsahon wata biyu ban sake ganinka ba."
Aymanul Faris ya ce, "Dama alƙawarin da nayi miki, bayan watanni biyu ne zan dawo. Kuma ga shi na cika wannan alƙawari. Ya ke masoyiyata akwai magana mai muhimmanci da na taho miki da ita.
"Amma kafun nan mu zauna mu fuskanci juna sosai tukunna!"
Gimbiya Jaanu tana jin haka ta kama hannun Aymanul Faris suka koma wani ɓangare dabam na wannan lambu. Har a wannan lokaci wannan tsuntsu na zaune akan kafaɗarsa.
Suna wannan keɓantaccen waje, suka zazzauna akan waɗansu kujeru guda biyu masu fuskantar juna.
Gimbiya Jaanu ta dubi Aymanul Faris ta ce, "Ina jin ka...?"
Aymanul Faris ya yi ajiyar numfashi ya ce, "Maganganun da zamu tattauna guda biyu ne, kuma a hankali zamu zo gaɓar kowacce magana. Ina so ki bani hankalinki ɗari bisa ɗari domin wannan yana daga cikin dalilan da suka sa nazo."
Gimbiya Jaanu tana jin haka tayi guntun murmushi ta ce, "Zan kasance mai baka nutsuwata ɗari bisa ɗari, yanzu faɗa min abinda zamu tattauna, ina jinka...?"
Aymanul Faris ya ce, "Gaɓar magana ta farko ita ce, magana akan sarauniya ARYA. Shin meye kika sani akan wannan sarauniya da tayi zamani ta shuɗe?"
Gimbiya Jaanu tana jin wannan suna a bakin Aymanul Faris ta ƙura masa idanu cikin tsananin mamaki.
Tun sa'adda ta fara girma ma'ana lokacin da tayi wayo, take yawan mafarkin wata gagarumar sarauniya wadda bata san ko wace ce ba. Bata ɗaukar kwanaki masu tsaho ba tare da tayi wannan mafarki ba.
A kullum a wannan mafarki nata, babu abinda ake nuna mata face ƙarfin mulki da iko irin na wannan sarauniya.
Wani abun al'ajabi da yayi matuƙar bata mamaki shi ne, har ta girma tayi hankali bata taɓa furtawa kowa wannan mafarki ba. Babu wanda ya san wannan mafarki face ita kanta.
Siffofin wannan sarauniya da take gani a cikin mafarki, suna matuƙar kama da siffofinta musamman a wannan lokaci da ta fara girma.
Jaanu bata san ainihin sunan wannan sarauniya ba, amma ta san cewa tabbas tana da nasaba sosai da ita. Bata yarda da kowa a duniya ba, wanda zata furtawa wannan mafarki har ya fassara mata, amma har kullum abin na ranta.
Tabbas a halin yanzu da taji Aymanul Faris ya ambaci wannan suna ta san cewa wannan sarauniya yake nufi.
Yadda take ƙaunar Aymanul Faris a zuciyarta yafi ƙarfin ta tsaya ɓoye masa wani sirri nata.
"Ban san komai akanta ba, amma ina yawan ganinta a cikin barci na. Shin akwai wani abu da ka sani dangane da ita ne?" inji Jaanu cikin sanyin murya.
Aymanul Faris yayi murmushi ya ce, "Kamar yadda na ambata daga farko. ARYA sarauniya ce da tayi zamani a wannan nahiya lokaci mai tsaho da ya shuɗe.
"ARYA ta yi zamani da kakana maigirma Samudu mai ruhin jarumtaka, kuma ance ita ce wadda ya aura.
"Kamar yadda Samudul Ansari yake da magaji, haka ita ma sarauniya Arya tana da magajiya.
"Waɗannan mutane guda biyu, sun yi aure kuma a dalilin wannan aure nasu sun samu ɗaukaka sosai.
"Ni ne magajin Samudul Ansari ke kuma kece magajiyar ARYA.
"Labarin soyayyarmu abu ne wanda aka riga aka gama rubutawa tunda daɗewa."
Gimbiya Jaanu na gama jin wannan jawabi tayi shuru ta ƙurawa Aymanul Faris idanu ta ce, "Zan iya yarda cewa bayanan da ka bani akan sarauniya Arya gaskiya ne, amma batun cewa ni ce magajiyarta zuciyata tana rawa akan hakan.
"Tabbas ina ɗan kama da ita, amma yadda nake kallonta a mafarkina tayi matuƙar ninka ni a kyawu nesa ba kusa ba."
Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "KECE ARYA!!!"
Gimbiya Jaanu tana tsananin ƙaunar Aymanul Faris, duk inda aka samu soyayya ta gaskiya dole akwai kunya a cikinta. Bata so ta tsaya yin jayayya da shi.
"Wacce hujja ce zata tabbatar min da hakan?" inji Jaanu.
Aymanul Faris ya ce, "Bayan mun gama tattaunawa akan gaɓa ta ƙarshe zan tabbatar miki?"
Aymanul Faris ya gyara zama wani gumi ya zubo daga kansa, ya yiwa Jaanu kallon soyayya mai rikirtarwa wadda yasa duniyarta tayi fari yace.
"Shin kin amince za ki zamo matana ta biyu, bayan jaruma Riya?" ya tambayeta cikin sanyin murya tamkar baya so yayi magana.
Gimbiya Jaanu tana tsananin ƙaunar Aymanul Faris, matsafa na ganin cewa kawai an halicceta ne domin ta zamo matar Tau'rin.
Amma dukda haka, sai da waɗannan kalmomi suka tsaya mata a wuya. Mata suna da tsananin kishi irin wanda mutum bai isa ya misalta ba.
Saboda tsananin yadda take ƙaunar Aymanul Faris a baya, mun ji cewa ta amince ya ɗauki fansa akan mahaifinta. Duk wanda zai amince da irin wannan abu, to lallai soyayyar da yake yi gaskiya ce.
Gimbiya Jaanu tana da kyakkyawar alaƙa da jaruma Riya, a baya lokacin da suka yi garkuwa da ita, mun ga yadda suka shaƙu da juna. Har Jaanu tana cewa a ranta wannan wuri, shi ne inda yafi dacewa da rayuwarta saboda tsananin yadda take farin ciki.
Tsahon ɗan lokaci tana ta tunani ba ta baiwa Aymanul Faris amsa ba, daga can ta numfasa ta ce, "Ban isa na yanke hukunci daga yanzu ba, ina buƙatar lokaci domin nayi tunani mai kyau akai.
"Amma kada ka samu damuwa tabbas ba zan baka wata damuwa ba."
Aymanul Faris ya ce, "Bani shakkun komai a kanki, tabbas na san ba zan fuskanci wani tangarɗa daga gareki ba."
Gimbiya Jaanu tayi murmushi mai taushi ta ce, "Na ji. Yanzu sai ka tabbatar min da cewa, ni ce Arya?"
Aymanul Faris yayi guntun murmushi ya saka hannu a cikin wata jaka dake ɗaure a kunkuminsa ya fiddo waɗannan furanni da suka tsinko a lambun Gorgons ya miƙawa gimbiya Jaanu.
Idanuwanta na yin arba da waɗannan furanni, wani irin mugun jiri ya ɗebeta, ta sulale ƙasa sumammiya.
Wani jan haske ya fito daga cikin waɗannan furanni ya lulluɓe jikinta gaba ɗaya tamkar wacce aka saka a cikin bargo.
Tsahon daƙiƙa ɗari da ashirin, kafun wannan jan haske ya ɓace gaba ɗaya.
Jinjina! Ga Ubangijin da ya halicci wannan siffa.
Aymanul Faris ya ja baya cikin tsananin mamaki, lokacin da idanuwansa suka fara arba da kyakkyawar surar.
A hankali gimbiya Jaanu ta miƙe zaune, ta buɗe kyawawan idanuwanta a hankali ta kalli Aymanul Faris.
Idanuwansu na haɗuwa Aymanul Faris yaji wani abu soke ƙahon zuciyarsa. Irin wannan siffa suka ɗinga yawo a cikin ƙwaƙwalwarsa.
Fuskar gimbiya Jaanu a cike take da annuri, tayi fari tamkar wata daren goma sha biyu. Murmushinta kaɗai ya isa ya saka mutum farin ciki, ya manta da duk wata damuwa dake cikin zuciyarsa.
Gaɓoɓin jikinta sun daidaita tamkar wacce aka zana akan takarda daidai yadda ake buƙata.
Gashin kanta ya sauya launi daga ja izuwa ruwan ƙasa.
A wannan siffa ko kallon gimbiya Jaanu, mutum yake ba zai sake baƙin ciki ba. Saboda ya kalli sarauniyar kyawawa ta duniya wadda babu ta ukun ta balle ta biyunta.
Gimbiya ta miƙe tsaye ta tunkaro Aymanul Faris tana cewa, "NI CE ARYA!" Hatta muryarta sai da ta canja.
Wannan tsuntsu dake kan kafaɗar Aymanul Faris ya fara kaɗa fuka-fukinsa yana wani irin kuka, wannan na nuni da cewa lokacin tafiyarsu ya yi.
Aymanul Faris na ganin haka ya buɗe hannayensa, gimbiya Jaanu ta ruga da gudu ta faɗa kan ƙirjinsa suka rungume juna cikin tsananin soyayya wanda ya ninka na farko nesa ba kusa ba.
Ba tare da ɓata lokaci ba, suka yi sallama da juna akan cewa zasu sake haɗuwa ba da daɗewa ba.
Wannan tsuntsu dake kan kafaɗar Aymanul Faris ya rikiɗe izuwa siffar aljani Nara, ya ranƙawafa ƙasa.
Aymanul Faris ya haye gadon bayansa, aljanin ya tashi sama cikin gajimare.
Gimbiya Jaanu tayi ta ɗaga masa hannu har ya ɓace ɓat a cikin giza-gizai.
*****
Yau *26/01/2023*
Babi na gaba zaizo *28/01/2023* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 77: *Bayanan ruhin Samudul Ansari*
*
SADAUKARWA GA MASOYA!
*
@umarsangaru
*
Aymanul Faris da aljani Nara basu yi nisa sosai a cikin gajimare ba, siffar Barban a matsayin haske ta bayyana a gabansu. Barban ya sallami aljani Nara, sannan ya dafa kafaɗar Aymanul Faris suka ɓace ɓat!
Ba su bayyana a ko'ina ba, sai a tsakiyar fadar aljani Ranganu. Fadar tana nan kamar yadda aka santa babu abu guda ɗaya da ya canja. Aljani Ranganu ya ƙame akan karagar mulkinsa.
Barban ya faɗi yayi gaisuwa kamar yadda ya saba, amma shi kuma Aymanul Faris jikinsa sai ya ƙi bin wannan umarni.
A wannan karon bai damu ba, saboda ya soma ɗaukar haske akan dalilin da yasa abubuwa irin waɗannan suke faruwa. Ko ba komai shi magajin Samudul Ansari ne.
Aljani Ranganu ya nuna musu waɗannan kujeru ya ce, su zazzauna akai. Babu musu suka zazzauna akan kujerun, suka fuskanci juna.
Aljani Ranganu ya ce, "Barkan ku da dawowa, wannan fada tawa. A yau zamu tattauna akan Samudul Ansari da kuma ayyukanmu na ƙarshe.
"Da farko Ayman, ina taya ka murnan ganin ainihin siffar masoyiyarka gimbiya Jaanu. Tabbas a halin yanzu kaima tana cikin ranka, kamar yadda kake cikin ranta.
"Shin ka karanta wannan littafi wanda na baka mai ɗauke da bayanan Samudul Ansari?" ya tambayi Aymanul Faris.
Aymanul Faris ya girgiza kai, alamar bai karanta. "Ka ce sai na samu zama, zan karanta. Ni kuma tun daga wannan lokaci ban sake samun zama na nutsu ba!"
Aljani Ranganu ya yi murmushi ya karɓi wannan litttafi daga hannun Aymanul Faris, ya buɗe shi. Ya dubi Aymanul Faris da Barban ya ce, "Ku nutsu da kyau domin jin bayanan ruhin da babu kamarsa a duk faɗin duniya."
Ranganu ya dubi shafi na farko na wannan littafi, sannan ya fara bayani kamar haka:
"Suna: Adawiy Al-Samud Al-Ansar. Wannan shi ne cikakken sunansa, balarabe ne.
"Shekaru: 143.
"Makamin yaƙi: Saif-Al-Barzaƙ.
"Matan aure: 'Arya I' da Zarifa.
"Ƙasashen da ya mulka: Daular Shaha gaba ɗaya."
Aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa sai ya rufe wannan littafi sannan ya dubi Aymanul Faris da Barban ya ce, "Waɗannan su ne bayanan dake kan shafi na farko. Bari mu tattauna akansu tukunna.
"To, shi dai wannan littafi daga hannun wani ɓoyayyen hadimin sarki Samudul Ansari na same shi, hadimin da ma yana ajiye da wannan littafi, yayi alƙawari a duk lokacin da cikakken Tau'rin ya bayyana zai bayar da shi.
"A yanzu babu cikakken Tau'rin kamar Aymanul Faris domin abubuwan da ya cimma, da yawa daga cikin Tau'rins ɗin da suka shuɗe basu cimma sa ba.
"Mene ne dalilin da yasa ake kiransa da suna Adawiy Samudul Ansari?
"Mene ne dalilin da yasa Samudul Ansari ya zamo balarabe, alhalin mutanen da suka biyo bayansa suna da ƙabila mai zaman kanta?
"Ya ya aka yi ya shekara ɗari da arba'in a duniya bai mutu ba?
"Wacce irin takobi ce SAIF-AL-BARZAK?
"Bari na yi muku bayanin waɗannan tambayoyi dalla-dalla.
"Dalilin da yasa ake kiran Samudul Ansari da suna Adawiy shi ne, saboda yana da nasaba sosai da samudawan da suka yi zamani lokaci mai tsaho da ya shuɗe.
"Ance yana daga cikin sirrin ƙarfin Samudul Ansari wato wannan nasaba da yake da, wanda yafi gaban tunanin mutum.
"Kuyi sani cewa Samudul Ansari balarabe ne, amma matarsa ƴar ƙabilar Arya ce. A duk lokacin da ɗan wata ƙabila daban ya auri wadda ba ƴar ƙabilarsa ba. Suna haifar da sabuwar ƙabila.
"Wannan shi ne dalilin da yasa aka samu ƙabilar Kuyuru wato aure tsakanin Samud da Arya.
"Babban dalilin da yasa Samudul Ansari yayi tsahon rai a duniya shi ne, wannan takobi da ya mallaka wacce ake kira Saif-Al-Barzaƙ.
"Ance a shekarar da aka ƙirƙiro wannan takobi sai da aka gwabza yaƙi wanda ya shafi duniya gaba ɗaya.
"Ita dai takobin Saif-Al-Barzaƙ, wata irin rantsatstsiyar takobi ce wadda aka ƙerata da wani irin ƙarfe wanda ake samowa a cikin waɗansu manyan duwatsu dake ƙarshen duniya ta yamma.
"Duk faɗin duniya babu ƙarfe mai ƙarfin wannan, ana ganin cewa, wannan ƙarfe shi ne asalin ƙarfe sauran waɗanda suke duniya jabu ne kawai.
"Babu abinda wannan ƙarfe ba zai huda ba, ko kuma ya fasa. Komai ƙarfin dutse da taurinsa kuwa.
"Wani shahararren mayaƙi ne da yayi zamani a lokacin da sarki Samudul Ansari yake mulki, ya samo wannan takobi. Saboda tsananin adalcin Samudul Ansari wannan mayaƙi ya bashi wannan takobi a matsayin kyauta.
"Wannan na daga jin manyan dalilan da suka sa ake tsoron Samudul Ansari a duniya gaba ɗaya saboda wannan takobi, an san cewa ita kaɗai ta isa ta tarwatsa rundunar mayaƙa komai yawansu kuwa.
"Waɗannan su ne taƙaitattun bayanai akan wannan shafi na farko wanda muka tattauna. Kasancewar ban ji cikakken tarihin Samudul Ansari shiyasa za ku ji bayanan nawa sama-sama."
Lokacin da aljani Ranganu yazo nan a bayanansa, sai Aymanul Faris yayi shuru ya sunkuyar da kansa ƙasa yana tunani.
Tabbas idan ya mayar da hankali yayi abinda ya dace, akwai babban matsayi wanda kowa ke mafarkin samu a duniya yana jiransa.
Abinda yasa yayi shuru yana tunani shi ne tun sa'adda ya haɗu da Barban, basu taɓa kawo masa batun hanyoyin da za'a ratsa a je inda wannan ruhi yake ba.
Kullum magana ɗaya suke kawai, akan matsayin da zai samu idan ya mallaki ruhin.
Aljani Ranganu babban matsafi ne, ana ganin cewa babu mahaluƙin da ya kaishi ƙarfin tsafi duk duniya.
Saboda wannan dalili yana iya ganin abinda ke cikin ran mutum. Wato abinda mutum ke rayawa a ransa.
Aljani Ranganu yaga tunanin da Aymanul Faris yake yi a ransa, saboda haka ya yi murmushi ya ce, "Komai da lokacinsa, kuma a lokacin ne za'a ga amfaninsa."
Aymanul Faris yana jin haka ya ɗago kansa cikin tsananin mamaki da shakkun wannan maganganu na Ranganu. Me yake nufi da haka?
Barban ya ce, "Ya mai girma, muna sauraronka, bayanin aiki na ƙarshen?"
Aljani Ranganu ya yi murmushi wanda yasa Aymanul Faris tattaro hankalinsa domin sauraron abinda zai ce.
"Godiya a gare ku, ya ku waɗannan mutane bisa yadda kuka bamu haɗin kai a ayyukan da muka gudanar a baya. Daga kan ɗauko farin lu'u-lu'u har zuwa

Please Login or Register in order to submit comment