Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na tsafi mai ƙarfi da suka saka a bakin ƙofar.
"Shi kuma Anbalu mamakin tsananin kyawun sarauniya Rana yake da kuma tsananin ƙarfin ikonta wanda yasa shi karkarwa sakamakon arba da hasken jikinta.
"Yana tsaye cikin wannan hali ne yaga ta tunkaro inda yake tsaye, fuskarta a rufe take ballantana ya iya kallon idanunta amma ga dukkan alamu tarau take kallonsa.
"Jikin Anbalu ya ci gaba da irin wannan karkarwa. Zuciyarsa ta yi ta dukan uku-uku tamkar zata faɗo ƙasa saboda tsananin tsorata.
"Anbalu ya tabbatar da cewa, idan fa wannan sarauniya bata ba shi haɗin kai ba, wannan yana nufin matansa da yaransa zasu ci gaba da shan azaba a hannun sarki Halad.
"Tana ƙarasowa gabansa ta fidda wannan hular sanyi da ta rufe mata ta kalle shi da kyau, idanuwanta suka shiga cikin nasa. Nan take yaji wani irin sirri ya ratsa shi tun daga kan gashin kansa har ƙasan ƙafafuwansa. Idanuwansa suka sauya launi suka soma bayar da koren haske mai ɗaukar hankali.
"Sarauniya Rana ta ce, burinka na farko ya cika ko? Ka kalli cikin idanuwan nawa!
"Anbalu ya ji gaba ɗaya tsikar jikinsa ta mimmiƙe wato sarauniya Rana ta san abinda ke tafe da shi. Ya tsaya zuru-zuru a gabanta ya gagara cewa komai, im banda kalle-kalle babu abinda yake yi.
"Tayi murmushi ta ce, zan amince na baka kaina domin burinka na biyu ya cika amma dole sai ka amince da wani babban sharaɗi nawa.
"Bakin Anbalu na karkarwa ya ce, na amince da wannan sharaɗi naki ɗari bisa ɗari.
"A ganin Anbalu babu wani abu wanda wannan sarauniya zata saka shi baiyi ba, in dai zai zamo gawurtaccen boka ya koma yankinsa ayi alfahari da shi sannan ya kuɓutar da iyalansa. Duk abinda zai biyo baya daga baya ne.
"Sarauniya Rana tayi murmushi ta sake saka wannan hular sanyi dake kanta ta dubi Anbalu ta ce, kai da baka ji sharaɗin ba ma, kake cewa ka amince?
"Anbalu ya ce, akan rayuwar iyalaina da jama'ata na yarda na sadaukar da komai nawa. Jin wannan sharaɗi ko rashin jin sa ba zai hana ni amincewa ba.
"Sarauniyar ta sake yin murmushi sannan ta tafa hannayenta sau uku, nan take wata na'ura mai kama jirgin ruwa ta bayyana a gabanta, ta shiga ciki sannan ta yafito Anbalu da hannu shima ya zauna a gefenta yana ta zare idanu domin bai taɓa ganin irin wannan abu ba.
"Sarauniya Rana ta taɓa wani abu a cikin wannan na'ura, nan take ta tashi dasu sama cikin iska suka nufi tsakiyar wannan ƙaton birni na Ranayes. Suna cikin tafiyar ta dubi Anbalu ta ce, akwai buƙatar na baka lokaci kayi tunani mai kyau bayan na faɗa maka wannan sharaɗi domin ka yanke shawarar abinda ya kamata kayi.
"Anbalu ya gyaɗa kai cikin fahimta, sannan ya fara tunanin to wai shin ma wanne irin sharaɗi ne zata zo masa da shi wanda dukda ya amince amma take maganar zata bashi dama ta kwanaki biyu ya yanke shawarar abinda ya kamace shi?
"Anbalu bai samu amsar wannan tambaya ta sa ba. Wannan jirgin ruwa da suke cikinsa yayi ta tsala azababben gudu a cikin gajimare yana kewaye ta saman gine-gine manya da ƙanana.
"Tsahon rabin sa'a cir sannan wannan jirgin ruwa ya dira a tsakiyar wata ƙawatacciyar fada wadda tafi ƙarfin ƙwaƙwalwa ta wassafa ta. Komai na fadar da irin wannan ƙarfe aka yi shi, wanda mutum zai gagara gane tagulla ne ko kuma jan zinari.
"Dakaru na jere sahu-sahu kowanne da irin aikinsa da kuma irin tsayuwarsa da yayi. Suna ganin sarauniya Rana suka durƙusa kan gwiwowinsu cikin biyayya.
"Sarauniya Rana ta kama hannun Anbalu ta tunkari cikin wannan ƙatuwar fada. Anbalu yaji wani irin abu ya ratsa shi, sakamakon haɗuwar fatar jikinsa da na Rana.
"Suna shigowa cikin wannan fada Anbalu ya wangame baki cikin tsananin mamaki domin ya gama zamowa cikakken ɗan ƙauye.
"Wannan fada ƙarshe ce a fagen kyawu, a jikin bangwayenta an saka hatiman hotunan rana ga dukkan alamu su ne shaidar wannan ƙasa.
"Rana da Anbalu suka ƙarasa kan wata ƙatuwar karaga ta mulki ta alfarma suka zauna a tare. Wata hadima ta kawo musu abinci mai daɗin gaske a cikin wani faranti.
"Rana ta karɓi abinci ta ajiye a gabansu, ita da Anbalu suka ci suka ƙoshi.
"Koda taga Anbalu ya samu nutsuwa sai ta dube shi ta ce, ka nutsu da kyau ka saurari wannan sharaɗi nawa domin kaje ka yanke shawarar abinda ya kamata kayi.
"Anbalu na jin haka ya fidda hannunsa daga cikin kwanon abincin sannan ya tattaro hankalinsa gaba ɗaya ya fuskanci wannan sarauniya Rana.
"Sarauniya Rana ta ce, kafun na faɗa maka wannan sharaɗi, ina so ka ɗaukar min alkawari koda ba zaka amince ba, dan Allah kada ka faɗawa kowa.
"Anbalu ya ɗan cika da tsananin mamaki, kafun daga bisani ya gyaɗa mata kai alamun ya amince ya ɗauki wannan alƙawari.
"Idanun sarauniya Rana suka ciko da ƙwalla ta tafa hannayenta sau uku, wata ƙawanya ta haske ta bayyana tayi musu rumfa, yadda babu wanda zai ji abinda zasu tattauna.
"Anbalu na ganin haka ya sake shiga taitayinsa ya tabbatar da cewa lallai wannan sharaɗi da zata zo masa da shi babba ne.
"Sarauniya Rana ta dube shi idanunta na gudun ƙwalla ta ce, SHIN ZAKA YI TAFIYA ZUWA DUNIYAR ISKA DOMIN KARƁO MIN AJIYATA A WAJEN SARKI AZAMU?
"Anbalu ya zaro idanu cikin tsananin mamaki ya ce, duniyar iska fa kika ce. Shin akwai waɗansu duniyoyin ne bayan waɗannan?
"Sarauniya Rana ta ce, shin ka amince ko baka amince ba? Fuskarta babu ko alamun wasa ta tambaye shi.
"Na amince zanje duk inda kike so naje, abinda kawai nake buƙata a gareki shi ne kiyi min bayanin komai dalla-dalla. Shin me zan karɓo a wajen wannan sarki?
"Sarauniya Rana tayi murmushin jin daɗi ta ce, nagode sosai da ka amince da wannan sharaɗi nawa. Kayi sani cewa ba wani abu zaka karɓo a wajen sarki Azamu ba, face allon sihirin da mahaifina ya bashi ajiya.
"Kayi sani cewa daga wannan wuri har zuwa cikin duniyar iska babu abinda zaka haɗu dashi na haɗari. Matsalar ita ce, mutane ƙalilan ne suke suke da ikon zuwa wannar duniya.
"Sannan koda mutum yaje wannan duniya magana da sarki Azamu kaɗai masifa ne, saboda muryarsa tana iya tarwatsa ƙaramin ruhi.
"Ku yan ƙabilar Aswad ba ku da ƙarfi na jiki amma kun fi kowa ƙarfin ruhi (idan ka cire na Samudul Ansari), babu wani abu a duniya wanda zai iya tarwatsa ruhinku saboda tsananin ƙarfinsa.
"Dalilin da yasa nake son a karɓo wannan ajiya shi ne, ina da ɓoyayyun abokan gaba a cikin garin nan. Daga waɗanda suke son aurena, sai waɗanda suke son karagar mulkin da nake kai.
"Idan har ban mallaki wannan allon tsafi ba, daga wannan lokaci zuwa kowanne lokaci zan iya rasa rayuwata da karagar mulkina.
"Ban isa naje duniyar iska ba saboda yanayin rayuwata da tsarin halitta ta bai dace da kowanne irin muhalli ba face nan wurin. Duk ranar da nayi kuskuren barin irin wannan yanki namu, ba zan wuce kwanaki bakwai ba zan mutu.
"Wannan yasa nayi bincike a cikin madubin tsafina akan yadda zan kuɓuta daga wannan abu da ya saka ni a gaba.
"Binciken nawa ya tabbatar min da cewa duk duniya kaine mutum ɗaya wanda zai iya zuwa duniyar iska yayi gaba da gaba da sarki Azamu sannan ya dawo a raye.
"Tun daga wannan lokaci nake ta tunanin yadda zan haɗu da kai.
"Wannan yasa na gudanar da bincike a cikin madubin tsafi domin samun hanyar da zan kuɓutar da kaina daga wannan hali da na tsinci kaina a ciki.
"Bincikena ya tabbatar min da cewa kaine mutum guda ɗaya jal da zai iya zuwa duniyar iska lafiya, ya gana da sarki Azamu sannan ya dawo lafiya.
"Tun daga wannan lokaci nake ta bincike akan yadda zan haɗu da kai, babbar da na fuskanta ita ce ban isa na bar wannan yanki namu sannan bana so na sako wani a cikin lamarin asirina ya tonu.
"Wannan fitowa da kayi nima ta amfane ni tunda a dalilinta zan cika babban burin rayuwata. Batun tarawa da ni kuma ba wani bane, ni idan kaje duniyar iska ma ka dawo na rantse zan aureka.
"Anbalu na gama jin batun wannan sarauniya yaji wani gagarumin farin ciki ya rufe shi, hankalinsa ya kwanta ainun.
"Daga wannan lokaci suka ajiye magana da Rana akan wannan yarjejeniya. Zai yi tafiya zuwa duniyar iska, ita kuma, zata aure shi.
"Anbalu ya ce a take zai tafi zuwa wannan duniya, amma sarauniya Rana dole sai ta bashi waɗannan kwanaki domin yaje yayi tunani.
"Sarauniya Rana a kira wata hadimarta ta bata umarnin a kai Anbalu masauƙinsa sai bayan kwanaki biyu zata neme shi.
"Anbalu yayi sallama da ita, sannan ya bi bayan wannan hadima suka fice daga cikin fadar suka nufi gidan da aka sauƙe shi.
****
Yau *24/12/2022*
Babi na 62 zaizo ranar *26/12/2022* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 62: *Gimbiya Helina*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
MAL. UMAR SANGARU
*
"Tsahon kwanaki biyu sarauniya Rana ta baiwa Anbalu domin ya samu damar yanke shawarar abinda ya kamata yayi. Dukda cewa ya riga ya amince da wannan sharaɗi amma bata amince ba, a ganinta a cikin waɗannan kwanaki zai samu cikakkiyar nutsuwa wacce zata bashi damar yin tunani mai kyau.
"A cikin waɗannan kwanaki biyu, Anbalu bai sake yin arba da sarauniya Rana ba. Im banda hadimar da ke kawo masa abinci babu wanda yake zuwa wannan gida da aka sauƙe shi. Kullum in banda kwanciya yayi ta sharar baci babu abinda yake a wannan gida har waɗannan kwanaki biyu suka shuɗe.
"A ranar kwana ta biyun ne da sassafe Rana ta shigo cikin wannan gida, sanye da waɗansu irin tufafi ruwan-toka masu shara-shara ta tunkari ɗakin da Anbalu ke zaune a cikinsa yana kalaci.
"Tana shigowa cikin ɗakin ya bi ta da kallo kawai ya gagara cewa komai saboda tsananin kyawun surar jikinta wacce bai taɓa ganin mai irinta ba. Anbalu ya gyaɗa kai ya ce, ai ko don na mallaki wannan kyakkyawar surar sai naje birnin sarki Azamu.
"Bayan sun gama gaisawa sarauniya Rana ta sake tambayar Anbalu ya amince da wannan sharaɗi, ya sake jaddada mata cewa ya amince.
"Nan take ta dafa kafaɗarsa suka ɓace daga cikin wannan ɗaki. Ba su bayyana a ko'ina ba sai a ƙarshen wannan gari ta ɓangaren gabas inda wani zabgegen ƙaton rami yake wanda a can ƙarshensa ruwan teku ne.
"Sarauniya Rana da Anbalu suka tsaya a bakin wannan ƙaton rami, Anbalu yana wasu-wasin ta wacce hanƴa ce zai iya zuwa wannan duniya ta iska wadda ko hanyarta ma bai sani ba.
"Ya dubi sarauniya Rana yana shirin tambayarta kenan, ta saka hannu a cikin jakarta dake goye a gadon bayanta ta fiddo wata takarda mai ɗauke da zanen hatimin ƙasarta da kuma sa-hannunta ta dubi Anbalu ta ce, idan kaje duniyar iska wannar ita ce zata zamo shaidar cewa ni ce wacce ta aiko ka.
"Tana gama faɗin haka ta matsa bakin wannan zabgegen rami ta fara karanto waɗansu ɗalasiman tsafi da ƙarfi tamkar wacce take ƙwalawa wani abu kira. Yanayin fasalin harshen ya yiwa Anbalu kama da irin waɗannan rubutu dake ƙofar shigowa wannan gari.
"Koda sarauniya Rana ta sami kamar daƙiƙa ɗari da tamanin tana karanto waɗannan ɗalasimai sai Anbalu ya jiwo ƙarar kaɗawar fuka-fukin wata jibgegiyar halitta daga can ƙololuwar sama, cikin sauri ya ɗaga kansa domin ganin abinda ke sauƙowa.
"Take ya yi arba da wani irin jibgegen ƙaton shaho ruwan-toka na sauƙowa daga can ƙololuwar sama, saboda tsananin girman shahon zai iya shure giwa komai girmanta.
"Kafun ka ce me wannan, wannan jibgegen shaho ya iso gaban sarauniya Rana yana ta kaɗa fuka-fukinsa ya tsaya cak a cikin iska. Sarauniya Rana ta ƙarasa inda yake ta dafa goshinsa da hannu guda ta fara shafa kansa a hankali.
"Wannan jibgegen shaho ya fara lumtse idanu alamun biyayya ga sarauniya. Rana ta juyo ta dubi Anbalu ta ce, wannan ƙaton shahon shi ne zai ɗauke ka ya kai ka wajen sarki Azamu. Dan Allah ka kula da kyau bana son rasa wannan allon tsafi nawa.
"Tana faɗin haka waɗansu hawaye suka zubo daga idanunta ta dubi wannan shaho ta ce, wajen sarki Azamu dake mulkin duniyar iska zaka kai wannan mutumi da muke tare.
"Wannan shaho ya gyaɗa kai alamun yaji wannan umarni na shugabar tasa. Sarauniya Rana ta yafito Anbalu da hannu ta nuna alamar ya zauna akan bayan wannan shaho domin wannan gagarumar tafiya.
"Cikin rashin tsoro da shakkun komai Anbalu ya taho inda take, suka fuskanci juna domin yin sallama. Sarauniya Rana ta rungume shi sannan ta sumbaci goshinsa tayi masa fatan alheri. Anbalu ya haye gadon bayan wannan ƙaton shaho ya zauna ɗare-ɗare tamkar wanda a bayan ingarman doki.
"Wannan jibgegen shaho ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya lulluka cikin gajimare, sarauniya Rana ta yi ta ɗagawa Anbalu hannu har ya ƙulle a cikin gajimare ta daina hango shi, sannan ta juya ta nufi hanyar komawa cikin wannan birni nata.
"Anbalu da wannan jibgegen shaho suka yi ta tsala azababben gudu a cikin sararin sama, suka yi ta tashi sama tamkar zasu ƙure sama.
"Tun Anbalu yana lissafa giza-gizan da suke giftawa har ya daina. Sun gifta ta cikin farin gajimare, jajawur kai har da koraye da shuɗi.
"Tsahon kusan sa'a takwas sannan suka soma shigowa cikin wani irin wurin mai yawan iska. Im banda ƙarar iskar dake kaɗawa da kuma ƙarar fuka-fukin wannan jibgegen shaho babu abinda Anbalu yake ji.
"Saboda tsananin yawan iskar, mutum zai ganta tamkar hayaƙi a wannan wuri. Babu buƙatar tambaya Anbalu yasan cewa sun shigo cikin duniyar iska inda sarki Azamu yake.
"Bai gama wanna hasashe ba, suka soma giftawa ta cikin garuruwan waɗansu mutane. Garuruwan mutanen na da ban al'ajabi ainun, domin komai da komai na garuruwan akan iska yake yawo.
"Gidaje, shaguna, wuraren ibadu da wajajen shaƙatawa duk akan iska suke lilo. Kai hatta su kansu mutanen wannan gari akan iska suke tafiya, sai dai kaga suna tafiya tamkar harba su ake da kibiya.
"Anbalu dake zaune a gadon bayan wannan shaho ya yi ta kallon waɗannan garuruwa cikin tsananin al'ajabi, amma bai ce da su komai ba. Su ma babu wanda ya ce dashi uffan ba, sannan babu wanda yayi tunanin afka masa wataƙila hakan ya samo asali ne saboda tsananin gudun da wannan shaho ke shararawa.
"Anbalu da wannan jibgegen shaho suka yi ta giftawa ta cikin garuruwa daban-daban har tsahon sa'a goma sannan suka tunkari wani babban gari wanda yafi dukkanin waɗannan garuruwa da suka ratsa kyawu da kuma tsaruwa.
"Duk da cewa garin akan iska yake, amma anyi masa katanga da tubalin jan dutse wanda ya kewaye dukkanin garin. A ƙofar shiga garin, akwai ƙofa ƙatuwa ta baƙin ƙarfe wacce aka yiwa samanta ado da tutocin ƙasar.
"A bakin ƙofar shiga wannan gari akwai masu gadi tsaitsaye cikin sulken yaƙi. Masu gadin irin siffar waɗannan mutane dake garuruwan baya ne da su. Sai a wannan lokaci Anbalu ya samu yayi musu kyakkyawan kallo.
"Waɗannan mutane basu da bambanci da sauran mutanen da ke duniyar da Anbalu ya baro. Kai, hannaye, gangar jiki da ƙafafu duk irin na mutane ne dasu, amma a saman kansu maimakon gashin kai kamar na kowanne mutum. Ƙaho guda biyu ne suka kwanta tamkar gashin kan.
"Sannan ƙwayar idanunsu jajazur ne tamkar garwashin wuta. Suna riƙe da makaman yaƙi masu ban al'ajabi.
"Wannan jibgegen shaho na ƙarasowa ƙofar shiga wannan gari, mutanen suka kewaye Anbalu sannan suka zaro makaman yaƙin su.
"Ɗaya daga cikin su ya dakawa Anbalu tsawa ya ce, waye kai? Abin mamaki ba a cikin harshen da Anbalu yake ji yayi wannan magana ba.
"Anbalu ya tsaya zuru-zuru ya rasa me zai ce, tun da baya jin wannan harshe tayaya ya san amsar da zai mayar da amsa?
"Ba zato ya ji wata murya daga gefen kafaɗarsa tayi magana, wato ta baiwa wannan badakare amsa. Yana dubawa yaga ashe wannan baƙin tsuntsu ne wanda aljani Fairar Zas ya bashi a matsayin mai yi masa rakiya.
"Waɗannan dakaru na jin abinda wannan tsuntsu ya ce, suka ja da baya sannan suka buɗewa Anbalu ƙofa, ɗaya daga cikinsu ya shiga gaba yayi masa jagora izuwa fadar sarki Azamu.
"Suna shigowa cikin wannan birni Anbalu ya sake cika da tsananin mamaki kuma ya zamo cikakken ɗan ƙauye domin kalle-kalle ya ɗinga yi tamkar mutumin daji ya shigo babbar birni.
"Idan mutum ya ga wannan birni zai iya cewa Anbalu bai da laifi domin ya tsaya kalle-kalle. Saboda wannan birni dai anyi mugun ƙawatashi, sannan da yake babu turɓaya a cikinsa hakan saiya ƙara masa kyawu.
"Yawancin gidajen wannan gari anyi musu ado da farin tagulla mai sheƙi tamkar gilashi, idan banda ɗaukar idanu babu abinda suke.
"Su Anbalu suka ci gaba da tafiya a cikin sararin samaniya har suka sako wani katafaren gida a gaba wanda duk faɗin wannan gari babu wanda yayi rabinsa a girma da ƙawatuwa.
"Babu tambaya Anbalu ya gano cewa wannan gida shi ne gidan sarautar wannan gari inda sarki Azamu yake.
"Kafun su iso wannan gidan sarauta da tazarar kamu ɗari biyu da arba'in waɗansu irin mutane suka bayyana suka sha gabansu. Maimakon ƙaho biyu dake kan kowanne mutum, waɗannan mutane ƙaho hurhuɗu ne a kansu.
"Mutanen suka sallami wannan badakare da ya yiwa Anbalu rakiya sannan suka kewaye Anbalu suka fiddo waɗansu irin makaman waɗanda Anbalu ya gagara kwatanta su da komai.
"Ɗaya daga cikin su ya dakawa Anbalu tsawa ya ce, ina shaidarka ta zuwa wannan duniya har da zaka tunkaro wannan fada tamu mai albarka?
"Anbalu bai ji abinda mutumin ya ce ba, don haka sai da wannan baƙin tsuntsu ya sake fassara masa. Anbalu yayi murmushi ya fiddo wannan takarda wacce ke ɗauke da zanen hatimin ƙasarta ta bashi.
"Sadaukin ya karɓi wannan takarda ya ƙura mata idanu. Tsahon ɗan lokaci kafun yayi murmushi ya dubi sauran yan uwansa ya yi musu magana a cikin wannan yare, suna gama jin abinda ya faɗa suka watse kowa ya koma mazauninsa.
"Wannan sadauki ya yiwa Anbalu jagora suka tunkari ƙofar shiga wannan fada ta sarki Azamu. Har suka iso ƙofar shiga wannan fada babu wanda ya sake tare Anbalu.
"Sadaukin ya zaro wata kuba ya buɗe ƙofar shiga wannan fada suka kunna kai cikinta shi da Anbalu.
"Suna shigowa Anbalu yaga tamkar cikin wani sabon garin suka shigo saboda tsananin girman wannan gidan sarauta.
"Sai da dakaru kala daban-daban har kala arba'in suka caje Anbalu sannan suka iso asalin fadar sarki Azamu.
"Tsayawa faɗin cewa wannan fada tana da kyau ko bata da kyau ɓata lokaci ne kawai. Amma mutum yayi tunanin fadar babban sarki a irin wannan duniya ta iska.
"Shi kansa wannan sadauki a ƙofar shiga wannan fada aka dakatar da shi sannan wasu dakaru dabam suka yiwa Anbalu rakiya izuwa cikin wannan fada.
"Babu abinda yake taimakawa Anbalu a wurin waɗannan dakaru face wannan hatimi da sarauniya Rana ta bashi, da zarar anga wannan hatimi sai a fara girmama shi.
"Tun daga nesa Anbalu ya hango wani shirgegen mutumi zaune akan wata ƙasaitacciyar karaga ta mulki wacce aka gina da zallar ɗanyen zinari mai kashe idanu.
"Mutumin yana sanye da jajayen kaya waɗanda aka yiwa ado da irin wannan ɗanyen zinari da aka gina wannan karaga da shi.
"Wannan mutumi yana da bambanci da sauran mutanen dake wannan gari. Maimakon ƙaho biyu ko huɗu dake kan kowa, wannan mutumi guda ɗaya ne jal a saman kansa. Sannan idanuwansa haske ruwan ɗorawa suke bayarwa maimakon kalar garwashi irin na kowa dake wannan birni.
"Ba sai an faɗawa mutum matsayin wannan mutumi ba, domin kuwa shi ne shugabansu wato sarki Azamu wanda zai baiwa Anbalu ajiyar sarauniya Rana.
"Sarki Azamu na hango Anbalu ya ɗan haɗe fuska kafun daga bisani ya sake fuskar tasa. Tun kafun Anbalu ya ƙaraso Azamu ya taso ya tarye shi suka rungume juna tamkar wanda yaga wani ɗan uwansa na jini.
"Shi kansa Anbalu sai da ya cika da gagarumin mamaki bisa wannan abu da sarki Azamu yayi, bar ma batun sauran fadawansa dake zaune a cikin wannan masarauta.
"Jikin su na haɗuwa a waje guda Anbalu yaji wani irin sirrin tsafi ya fara ratsa shi, wanda tunda uwarsa ta haife shi, bai taɓa jin sirrin tsafi mai kama da shi ba. Wannan sirrin tsafi na gama ratsa jikinsa yaji wani ƙamshin tsafi da iko na tashi daga jikinsa tamkar gawurtaccen bokan da ya shekara ɗari a cikin halwar tsafi yana tsuma kansa.
"Sarki Azamu ya janye jikinsa daga na Anbalu suka fuskanci juna sosai ya ce, wannan shi ne irin tarbar da nake yiwa manyan baƙina, duk wanda ya samu jikinsa ya taɓa nawa ya gama zamowa gawurtaccen matsafi a duniya saboda kakana na arba'in da tara yana daga cikin matsafan farko da suka fara samar da tsafi.
"Anbalu ya yi ta godiya cikin tsananin farin ciki, ko a wannan wuri kaɗai fitowar da yayi daga gida tayi amfani.
"Sarki Azamu ya sake cewa, mahaifin sarauniya Rana mutumin kirki ne sosai, sa'adda naje cikin duniyarku yayi mini taimako ba kaɗan ba wannan yasa da yazo mutuwa ya bani ajiyar allon tsafinsa, ya ce idan yarsa ta girma na bata wannan allo.
"Tabbas yanzu shi ne lokacin da yafi dacewa Rana ta mallaki wannan allon tsafi domin kuwa tana da maƙiya waɗanda ita kanta ma bata san da su ba. Tun da ta gaji karagar mulkin mahaifinta mahassada suke ta shirya mata tuggu.
"Da naso na baka masauƙi a cikin wannan fada tawa domin ka huta sosai kafun ka koma, amma yanzu abinda yake faruwa a birnin Ranayes yana buƙatar taimakon gaggawa.
"Idan har ba'a yi sauri an kaiwa sarauniya Rana wannan allon tsafi ba, a kowanne lokaci zata iya mutuwa domin kuwa a halin yanzu gagarumin yaƙi na shirin afkuwa tsakaninta da yan majalisar ƙasar masu adawa da mulkinta.
"Sarki Azamu na gama faɗin haka, ya fiddo wani allon tsafi ruwan toka daga cikin jakar tsafinsa ya miƙawa Anbalu ya ce, yayi maza ya koma duniyarsu ya kaiwa Rana wannan allo kada ta rasa rayuwarta.
"Cikin gaggawa da kaɗuwa Anbalu ya karɓi wannan allon tsafin sannan ya juya akalar wannan shaho suka nufi ƙasa suka fara tsala azababben gudu.
"Idan mutum yaga yadda suke keta giza-gizai zai yi tsammani doron ƙasa suke son hudawa saboda tsananin yadda suke sauƙowa da gudu.
"A wannan lokacin ma, sai da suka sake shafe waɗansu sa'o'i guda goma kafun wannan jibgegen shaho ya sauƙa a bakin wannan ƙatoton rami wanda sarauniya Rana ta kira shi a bakinsa.
"Shahon na sauƙa Anbalu yayi maza ya daka tsalle daga kansa ya sauƙa daga sannan ya ruga da gudu izuwa cikin birnin Ranayes. Wannan jibgegen shaho ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya ɓace a cikin gajimare.
"Anbalu na ƙara gudu yana matso wannan birni kenan, ya soma hango hayaƙi tsubi-tsubi yana tashi a cikin birnin, sannan ya soma jiwo kururuwar mazaje da ƙarar karafkiyar ƙarafa. Ga dukkan alamu dai yaƙi mai zafi ake gwabzawa a cikin garin.
"Anbalu ya ƙara azama cikin wannan gudu nasa, har ya soma shigowa cikin wannan birni. Inda ya ɗinga yin arba da gawarwakin dakaru a ƙasa kaca-kaca cikin jini.
"Wannan

Please Login or Register in order to submit comment