Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itaciya ba, lamarin da ya bashi mamaki kenan. A saninsa dai wannan itaciya ba ɓoyayyiya bace, amma da ya tuna ba'a nahiyarsu yake ba, saiya daina mamaki.
Ya ci gaba da kutsa kai cikin wannan daji, har ya fara yin nisa da wannan tanti nasu Firziyya.
Sannu-a-hankali har ya ƙule a cikin ƙungurmin daji, ya ƙule a cikin dogayen itatuwa masu fala-falan ganƴaƴe waɗanda suka sa wannan daji yayi duhu.
Bisa dole Marganu ya ƙaddamar da idanusa na haske, idan ba haka ba babu abinda zai na kallo a wannan wuri. Baiyi nisa ba ya fara jiwo motsi ta can nesa daga inda yake.
Marganu ya zaro takobinsa ya ƙaddamar da hasken wuta a cikin wannan daji wanda yayi sanadiyar ƙonewar dukkanin waɗannan bishiyoyi masu duhuwa da suka saka duhu a cikin dajin.
Komai dake cikin wannan daji ya fito fili ƙarara. Abin mamaki babu dabbobin daji masu yawa a cikin wannan daji, mafi yawa daga cikin su ƙananun dabbobi ne irinsu gada, gafiya da macizai.
Marganu ya ɗan haɗe fuska yana tunani. Tabbas yasan dole akwai wani mugun abun wanda yayi sanadin ƙarancin dabbobi a cikin wannan daji.
Jim ƙadan, ƙasa ta fara tsatstsagewa waɗansu irin gabza-gabzan dodanni suka fara ratsowa ta cikinta suna fitowa.
Jikin waɗannan dodanni babu nama ko guda ɗaya. Gaba ɗaya ƙashi-da-rai ne. Sannan suna da rafkeken kai mai ɗauke da ƙwala-ƙwalan idanu jajaye kamar wuta. Bakunansu kuma kamar bakin guga haka suke saboda faɗi.
A hannayensu suna ɗauke da zabga-zabgan sunguma na duka masu cako-cako. Kai, kallon waɗannan dodanni kaɗai ya isa ya firgita mutum saboda basu yi kama da komai ba face halittun kabari masu sanƴa tsoro a cikin zuƙatan jama'a.
Waɗannan dodanni na ganin Marganu suka kewaye shi gaba ɗayansu, suna wani irin ihu mara sauti sosai tamkar wanda yake tasowa daga tsohon kabari.
Marganu ya ƙaddamar da wani shuɗin haske a matsayin ƙarfen wannan takobi tasa, ya tsaya a tsakiyar waɗannan dodanni suna kallon kallo.
Tsahon wannan lokaci da Marganu ya ɗauka yana tafiya a yayin neman wannan itaciya har ya shigo cikin ɗaya daga cikin dazuzzukan nan dake tsakanin garuruwa uku na farko da huɗu na ƙarshe.
Cikin yarda da kai, Marganu ya kaiwa waɗannan dodanni sara da wannan shuɗin takobi ta haske dake hannunsa. Taurari guda biyu shuɗaye suka fita daga tsinin takobin suka tunkari dodanni guda goma gadan-gadan.
Ko alamun kaucewa waɗannan dodanni guda goma basu yi ba, har waɗannan taurari guda biyu suka dira akan su.
Wani irin shuɗin haske mai kashe idanu ya cika wannan waje, Marganu ya mayar da takobinsa mazauninta ya ɗaureta sannan ya juya ya fuskanci sauran dodanni yana jira yaga firgici a idanunsu sakamakon mugun kisan da ya yiwa ƴan-uwansu.
Ba zato ba tsammani! Marganu yaji an kawo masa duka da wani ƙaton sungumi ta baya. Cikin zafin nama na gaban kwatance Marganu ya daka tsalle gefe guda, wannan ƙaton sungumi ya dira bisa ƙasar wannan wuri. Nan take ƙasar wurin ta ratattake ta haifar da wawakeken rami.
Cikin tsananin mamaki Marganu ya waigo domin ganin waɗannan dodanni. Shi dai a tunaninsa sai dai wasu dodanni ne dabam suka kawo masa wannan hari, amma, ba waɗannan da ya kaiwa hari a ɗazu ba.
Bisa mamaki yaga su ɗinne ba wasu ba, kuma lallai wannan hari ya sauƙa a kansu. Tunda har a wannan lokaci akwai shuɗi-shuɗin haske a jikin ƙwarangwal ɗinsu.
Wannan abu yayi matuƙar baiwa Marganu mamaki, saboda wannan shi ne karo na farko da yaga halittun da wannan takobi bata tasiri a kansu.
Dukda haka bai saduda ba, sai da ya sake ƙaddamar da jan haske a matsayin ƙarfen wannan takobi ya sake kai musu sara. A wannan karon ma, ko kaucewa basuyi ba, har wannan hari ya dira a jikinsu.
Abinda ya faru a farko shi ne ya sake faruwa, ko kwarzane wannan hari bai yi musu ba.
Marganu ya haɗe fuska, ya yanki hannunsa guda da ƙaramar wuƙa, jini ya fara zubowa ya saka wannan jini a jikin wannan takobi. Wannan shi ne yadda ake ƙaddamar da babban ɗalasimin wannan takobi.
Tun da aka ƙirƙiro wannan takobi, ba'a taɓa ƙaddamar da wannan babban ɗalasimi ba, face waɗanda aka ƙaddamarwa sun tafi lahira.
Irin wannan takobi kimanin guda dubu arba'in suka bayyana da yawa a saman waɗannan dodanni, takubba suka fara saƙƙowa ƙasa-ƙasa daidai wuyan dodannin nan.
Cikin yarda da kai da tabbacin samun nasara Marganu ya kaɗa takobin dake hannunsa. Nan take dukkanin waɗannan takubba suka sari wuyan dodannin nan.
Dodannin suka kwarara uban ihu, rugugin masifa da tartsatsin haske ya cika wannan wuri.
Wani irin mugun jiri ya ɗebi Marganu bisa dole ya durƙusa akan gwiwowinsa, sannan ya fara aman jini. Kamar dai yadda sarki Ratanam ya kasance lokacin da ya ƙaddamar da wannan ɗalasimi ya hallaka dukkanin dakarun sarki Kuffuru.
Matsalar wannan ɗalasimi shi ne a duk lokacin da mutum yayi amfani da ƙololuwarsa, to, dole sai wannan mugun jiri ya ɗebi mutum.
Sannu-a-hankali ƙura ta soma lafawa, abubuwan da suke wannan wuri suka fara bayyana. Mutum zai iya cewa Marganu yana da tabbacin cewa waɗannan dodanni gaba ɗayansu sun hallaka tunda anyi amfani da babban ɗalasimi a kansu.
Amma, ba kullum abinda ake hasashe yake tabbata ba. Waɗannan dodanni gaba ɗayansu suka sake bayyana ko ɗaya daga cikinsu bai mutu ba. Amma, akwai alamun duka akan wuyansu.
Marganu ya caka asalin takobinsa a ƙasa ya tallafi kansa ya miƙe tsaye.
A wannan lokaci ne waɗannan dodanni gaba ɗayansu suka rugo da gudu kan Marganu, suna ɗaga sunguman dake hannunsu sama.
Lamarin da ya ɗugunzuma hankalin Marganu kenan, saboda a wannan lokaci jikinsa a galabaice yake sosai sakamakon amfani da wannan ɗalasimi. Da ƙyar ya iya miƙewa tsaye. Tayaya zai yaƙi dubbanin dodanni a haka?
Saboda wannan dalili yasa Marganu ya shafi wannan hatimin-haske dake kan damtsensa domin ya juyar da jikinsa izuwa haske. Bisa mamaki sai yaga babu abinda ya faru, jikin nasa ya ƙi juyewa izuwa hasken.
A daidai lokacin yaji anyi masa wani wawan duka ta baya. Marganu ya tashi sama tamkar wanda aka harba daga cikin majaujawa ya faɗo ƙasa a saman wani ƙaton dutse.
Ƙasusuwan jikinsa suka amsa, yaji tamkar zasu kakkarye. Marganu ya gagara miƙewa koda zaune.
Waɗannan dodanni suka sake rugowa wajen da yake da gudu zasu ƙarasa shi, wani ƙaton dodo ya sake kawo masa duka da sungumin hannunsa.
Mutum zai iya cewa lallai ƙarshen Marganu yazo saboda indai wannan sungumi ya dira akansa, namansa fata-fata zaiyi akan wannan dutse.
Saura ƙiris wannan sungumi ya dira akan Marganu ya mirgina gefe cikin baƙin zafin nama. Ai kuwa wannan sungumi na dira akan wannan dutse yayi daga-daga tamkar an tarwatsa shi.
Marganu ya faɗo ƙasa daga kan dutsen, sannan ya miƙe tsaye ya zaro asalin takobinsa ya riƙeta da kyau.
A wannan lokaci mantawa yayi da wahalar da yake ji a jikinsa, saboda idan baiyi ƙoƙarin kare kansa ba, a banza za'a kashe shi. Sannan bai sake yin gangancin amfani da wannan takobi ta haske ba, asalin takobinsa ya fiddo.
Cikin zafin nama da shammace Marganu ya daka tsalle ya sari wuyan ɗaya daga cikin dodannin nan. Wata ƙara ta tashi tamkar an sari dutsen-wuta. Babu abinda ya sami wannan dodo tamkar mai aka shafa masa a wannan wuri.
Wannan dodo ya kawowa Marganu duka da sunguminsa, Marganu ya daka tsalle gefe guda ya kauce. Sungumin ya dira akan ƙasa ya haifar da wawakeken rami. Dodon ya sake kawowa masa nan ma ya kauce ya sake haifar da wani ramin.
Haka dai ya ci gaba da kaiwa Marganu duka shi kuma yana ta tsalle-tsalle yana kaucewa dukan. Lamarin da yasa ramuka masu yawa suka fara yawaita a cikin wannan daji kenan, domin duk abinda wannan dodo ya samu dagargajewa yake.
Kafun ka ce me wannan, tuni Marganu ya soma haɗa zufa saboda yadda yake yawan tsalle-tsalle. Marganu ya soma gajiya amma wannan dodo ko alamun gajiya bai soma ba.
Sauran dodannin sai suka tsaitsaya suka zubawa gumurzun Marganu da ɗan-uwansu idanu.
Koda Marganu ya fuskanci cewa ya soma gajiya, sai hankalinsa ya soma ɗugunzuma saboda yasan duk tsautsayin da yasa ya gama gajiya, ba tare da ya hallaka waɗannan dodanni ba. Sunansa gawa.
Saboda wannan dalili yasa Marganu ya fara shawarar me zaiyi a cikin ransa. Wacce dabara ya kamata yayi amfani da ita akan waɗannan dodanni?
Marganu ya ƙurawa dodannin idanu yaga gaba ɗaya jikin su babu nama, ƙashi-da-rai ne kawai. Babu yadda za'ayi makamin ƙarfe yayi tasiri akansu.
Idanun Marganu suka kai kan wannan sungumi dake hannunsu, nan take ya ayyana a ransa babu abinda zaiyi tasiri akan waɗannan dodanni kamar wannan sungumi dake hannun su. Saboda wannan dalili ya ayyana a ransa, dole ta kowanne hali saiya ƙwaci sungumi guda daga hannun su.
Marganu na gama ayyana hakan a ransa, wannan dodo ya sake ɗago sungumi ya kawo masa duka. Cikin zafin nama da ƙwarewa Marganu ya ɗan gwace a hankali, wannan sungumi ya doki iska.
Kafun sungumin ya taɓa ƙasa tuni Marganu ya kamo hannun wannan dodo wanda ke riƙe da sungumin yasa gwiwar ƙafarsa ya doki ƙashin-hannun da ƙarfi. Nan take ƙashin ya karfe da ƙarfi, wannan dodo ya kurma wani wawan ihu, baisan sa'adda ya saki wannan sungumi ba.
Caraf! Marganu yasa hannunsa guda ya cafko wannan sungumi kafun ya dira akan ƙasa.
Tabbas Marganu ba ƙaramin sadauki bane, domin wannan sungumi na waɗannan dodanni yana da mugun ƙarfi tamkar ƙaton dutse, amma da hannu ɗaya Marganu ya riƙe shi.
Marganu ya ɗaga wannan sungumi ya dokawa wannan dodo a tsakiyar kansa. Take kan dodon yayi bindiga ya tarwatse, ya faɗi a wannan wuri matacce.
Sauran na ganin haka suka rugo da gudu kan Marganu suka sake ƴanƴame shi. Marganu yayi ta dukan tsakiyar kayukansu da wannan sungumi dake hannunsa, ai kuwa sai suka yi ta mutuwa babu shiri.
Kafun sa'a guda ta shuɗe tuni Marganu yayi musu mummunar ɓarna. Ana cikin wannan hali, wani ɗan ƙaramin tsuntsu baƙi ƙirim, yazo ya wuce ta saman wannan daji yana yin wani irin kuka mai ratsa ƙashi.
Waɗannan dodanni suna jiwo kukan wannan tsuntsu, suka fara fidda fuka-fuki suna tashi sama, suna guduwa daga cikin wannan daji.
Wuya mai sa yaro gudu. Lallai waɗannan dodanni sun ga muguwar masifa da bala'i irin wanda basu taɓa gani ba.
Dodannin na gama watsewa Marganu ya hango wannan itaciya wacce ya fito nema a can nesa. Cikin hanzari ya ƙarasa inda take ya tsinkota sannan ya juya ya nufi wannan tanti nasu Aydenlik da Firziyya.
Yana ƙarasowa ya samu kasko ya haɗa wuta, sannan ya dafa wannan itaciya, ya shafawa Aydenlik, ya shafawa jikinsa, Koda yazo shafawa Firziyya sai ya tsaya cak! Ya ƙurawa kyakkyawan jikinta idanu cikin tsananin mamaki.
A daidai lokacin ta buɗe idanunta, koda taga yadda Marganu ya tsaya kallon jikinta sai taji daɗi a ranta. Marganu na fuskantar hakan yayi sauri ya shafa mata maganin, sannan ya kwanta akan wata shimfiɗa domin ya huta wahalar wannan gumurzu da ya sha.
Dama a wannan lokaci, isha'i ta wuce. Gimbiya Firziyya ta ɗauki bargo ta nufi inda yake kwance, ta lulluɓa masa bargon sannan itama ta shiga ta kwanta a ciki, ta rungumo shi ta baya.
Washe gari da safe Marganu na farkawa yaji mace a bayansa ta rungume shi, a fusace ya janƴe jikinsa daga nata sannan ya daka mata tsawa. A firgice gimbiya Firziyya ta farka.
"Kada ki kuskura ki sake kusantata, ki bari sai ranar da na neme ki da kaina!" ya bata umarni.
Cikin girmamawa da nuna ƙauna gimbiya Firziyya ta gyaɗa masa kai, alamun ta ji.
Tsoho Aydenlik ya farka shima ya dubi Marganu ya ce, "Jiya kam, har ina kaje nema mana magani ne. Domin sau uku ina farfaɗowa amma bana ganin ka a tare damu?"
"Cikin wannan dajin naje, kuma har na ɗan fafata da wasu halittu da bansan ko su wane ne ba?" inji Marganu.
Aydenlik ya miƙe zaune cikin tsananin mamaki ya fara kallon jikin Marganu yana nazarin raunikan jikinsa. Daga bisani ya jinjina kai ya ce, "Ga dukkan alamu da dodanni ka fafata, ya ya yanayin jikinsu yake?"
Marganu ya zayyanewa Aydenlik irin yadda fasalin jikin waɗannan dodanni yake. Aydenlik ya cika da tsananin mamaki sannan ya dafa kafaɗar Marganu ya ce.
"Tabbas ka cika jarumi kuma sadauki. Saboda waɗannan dodanni da ka gani SEDUSAWA ne. Ba kowanne ɗalasimin tsafi bane yake tasiri akansu. Ka san cewa akwai ɗalasiman tsafi dake tasiri akan tsoka da jini kaɗai, kamar ɗalasimin haske da wuta.
"Wannan shi ne dalilin da yasa kaga ɗalasiminka ya ƙi amfani akansu. Saboda ba su da tsoka da jini, shi kuma ɗalasimin-haske jini yake tafasawa, sannan ya narka tsoka."
****
Yau *05/12/2022*
Babi na gaba zaizo *08/12/2022* da yaddar ALLAH.RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 54: *Hatsabibancin Sarki Kuffuru*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Kusan wata guda cir, wannan runduna ta su sarki Kuffuru suna ta tafiya a cikin sararin samaniya, ba tare da sun yada zango ba. Aljani Sheezuwa ya kasance mai tsananin ƙarfin gudu a sararin samaniya, domin tamkar tauraruwa mai wutsiya haka yake gifta wajaje.
A ranar da wata guda ta cika ɗinne, boka Hubbazu ya baiwa aljani Sheezuwa sauƙa a cikin wani ƙaton daji. Sheezuwa ya saki fuka-fukinsa ya dira bisa turba.
Wannan daji da suka sauƙa a cikinsa ya kasance mani'imci, akwai iska mai sanyi dake kaɗawa a cikin dajin tamkar tsakiyar hunturu, sannan akwai hazo mai ɗan kauri da ya lulluɓe dajin.
Boka Hubbazu ya baiwa aljani Sheezuwa umarnin samar da tantuna a wannan wuri saboda zasu ɗan kwana biyu su huta, kasancewar tafiyar dake gabansu mai tsaho ce.
Aljani Sheezuwa ya ɓace ɓat. Jim kaɗan ya sake bayyana ɗauke da itatuwan kafa tantuna. Ba tare da ɓata wani lokaci ba, ya samar da tanti guda biyar, wato kowa da nasa.
Dama a wannan lokaci dare ya soma rabawa, don haka, sai kowa ya shiga tantinsa aka kwakkwanta.
Washe gari da sassafe ma, aljani Sheezuwa ne ya samar musu da abin kalaci tun kafin kowa ya farka daga barci. Suna farkawa suka sami abinci yana jiran su. Bayan kowa ya gama cin abinci, an ƙoshi.
Boka Hubbazu da aljani Sheezuwa suka kira sarki Kuffuru cikin wani tanti domin su tattauna, suka bar sarki Darwazu da sarauniya Rauziyya saboda tattaunawar bata shafe su ba.
Boka Hubbazu ya samar da irin wannan madubin tsafi nasa, ya fara nunawa sarki Kuffuru abinda ke faruwa a cikin madubin tsafin.
Kimanin tafiyar zango goma daga wannan wuri da suke, aka nuno waɗansu mutane guda huɗu tafe a cikin gajimare suna tunkaro inda suke. Abin mamaki biyu daga cikinsu akan shaho suke zaune, sauran guda biyun kuma, akan wata dardumar tsafi suke.
Sarki Kuffuru na ganin ɗaya daga cikin waɗanda ke zaune bisa wannan jibgegen shaho ya shaida shi, domin kuwa, ba wani bane illa sarki Ayubul Zairiy wanda muka ga yaje ya haɗa kai da sarki Kim Sam na birnin Sin.
"Waye nake gani haka?" inji sarki Kuffuru. "Kamar sarki Ayubu da mutanen birnin Sin? Ina suka nufa, su waye suke bi, meye shirin sarki Ayubu?" ya tambayi Hubbazu.
"Ko shakka babu, wannan sarki Ayubu da boka Ruguzan ne na birnin Damashkar tare da sarki Kim Sam da boka Biu Lin na birnin Sin. Kamar yadda binciken mu na tsafi ya tabbatar mana, sarki Ayubu munafukin-ɓoye ne ya jima yana shiri ba tare da kowa ya sani ba.
"Sarki Ayubu na da manƴan burika a duniya waɗanda cika su, ya dogara kacokan akan kamo Barban kamar dai yadda burikan ka suka kasance. Sarki Ayubu ya ɗakko ƙasƙantaccen mutum a birninsa ya girmama shi, saboda yasan waye wannan mutumi. Ruguzan da ba kowa bane a cikin birnin Damashkar, sarki Ayubu ne ya ɗauko shi ya bashi matsayin babban boka, sannan ya bashi dukiya mai yawan gaske. Saboda Ruguzan ya kasance jikan wani gawurtaccen boka da yake da irin sihirin tsafi aljani Barzasa wato samar da taswira.
"Sarki Ayubu ya ɗauko wannan boka sun taho izuwa birnin Sin domin ganawa da sarki Kim Sam akan ya nuna musu hatimin da Barban ya ajiye lokacin da yazo yayi masa sata, amma sarki Kim Sam yace musu ai wannan hatimi ya riga ya salwanta.
"Ruguzan ya bayar da shawarar aje wajen boka Biu Lin domin su haɗa ƙarfi-da-ƙarfe shi da wannan boka domin su samo mafita. Tabbas sun je wajen wannan boka, ya nuna musu dukkanin wata tattaunawa da muka yi kafun tahowar mu wannan aiki. Abinda basu sani ba shi ne, ina sane da cewa suna kallon dukkanin wannan tattaunawa tamu.
"Boka Biu Lin ya basu umarnin biyo bayan mu, su fake mu, idan muka yada zango su yaƙe mu. Su kwaci wannan taswira sannan su tafi farautar Barban da ita.
"Sarki Ayubu ya shirya tsaf domin nuna maka ainihin ƙarfinsa, saboda a wannan lokaci shima yayi maka tawaye kamar yadda sarki Ratanam yayi ma.
"Abinda ba su sani ba shi ne, mun riga mun san wannan shiri nasu kuma har mun gama shirya masa..."
Kafun boka Hubbazu ya gama rufe bakinsa, sarki Kuffuru ya tari numfashinsa yayi ƙwafa sannan ya cije yatsansa. Ya ce, "Wai dan ALLAH, meye waɗannan sarakuna suke taƙama da shi da har zasu ɗinga tunanin yi min tawaye. Sarki Ayubu da nake gani kamar yana da hankali ashe shima munafuki ne?
"Bana taɓa ragawa waɗanda suka yi min tawaye, lallai zan jira sarki Ayubu a wannan wuri har su ƙaraso sannan na sare kansa, kamar yadda na sare na sarki Ratanam."
Aljani Sheezuwa yayi dariya ya ce, "Idan har zaka jira su a wannan wuri, ai zamu ɓata lokaci mai yawa kafun su ƙaraso. Meye amfanin shirin da muka yi ni da maigidana..."
A fusace sarki Kuffuru ya dakatar da shi, ya ce, "Kuna ta maganar wani shiri, shiri, mene ne wannan shiri naku?"
"To ai sai ka jira, mu gama nuna maka abinda ke cikin wannan madubi na tsafi ko?" inji boka Hubbazu lokacin da ya sake shafan wannan madubin tsafi da hannunsa na hagu.
Nan take wannan madubin tsafi yayi haske ya nuna birnin Kufa, ranar da su Barban suka je suka sato wannan takobi ta Saiful Shiradu.
Sarki Kuffuru ya kalli dukkanin abinda ya faru, daga shigowarsu cikin wannan birni, har zuwa lokacin da Aymanul Faris ya ɗauki wannan takobi.
Abin mamaki, ba wannan abu boka Hubbazu yayi niyyar nunawa sarki Kuffuru ba. Amma, kamar umarni aka bawa wannan madubin tsafi, ya nuna abinda hatta shi kansa boka Hubbazun bai sani ba.
Lallai al'amarin Barban da aljani Ranganu abin tsoro ne. Tun daga wannan lokaci har sun fara nunawa su sarki Kuffuru ƙarfin iko, tun kafin ma, su fara amfani da wannan taswira.
Jikin sarki Kuffuru ya fara karkarwa da ƙyarma saboda tsananin fusata. Fuskarsa ta fara karkarwa tamkar zata zazzago saboda baƙin ciki da takaici.
Ko mutanen da suka rayu a zamanin da aka samar da takobin Saiful Shiradu, basu kai sarki Kuffuru sanin wannan takobi ba, domin yana ɗaya daga cikin waɗanda wannan takobi ta taɓa yiwa illa.
Sarki Kuffuru baisan sa'adda ya ɗaga hannunsa zai zabgawa boka Hubbazu mari ba, amma, hannun nasa na zuwa daidai kuncin boka Hubbazu sai ya gagara zabga masa marin, hannunsa ya ci gaba da karkarwa.
"Amma, na rantse, kun cuce ni. Meyasa ba ku nuna min lokacin da suka je sato wannan takobi ba. Na rantse da darajar abin bautata, da babu abinda zai hanani yanke wannan tafiya naje na kamo su. Wawayen banza, wawayen wofi. Kuyi min gamsasshen bayani, idan ba haka kuwa, na rantse sai na yaƙe ku..." inji sarki Kuffuru cikin tsananin fusata irin wanda bamu taɓa gani ba.
Aljani Sheezuwa ya murtuƙe fuska, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata ƙone. Wai, yau har shi za'a ɗinga kira wawa?
Yana shirin afkawa sarki Kuffuru, boka Hubbazu ya harare shi. Nan take ya dawo taitayinsa sannan ya haɗiye fushin sa.
"Yi haƙuri ya shugabana. Kayi sani cewa mu kanmu bamu san sa'adda wannan abu ya faru ba. Ka kwantar da hankalinka kayi sani cewa wannan shiri da muka yi, zai magance dukkanin wata matsala taka. Akwai abinda zamu nuna maka a cikin wannan madubin tsafi wanda ganinsa kaɗai ya isa yasa zuciyarka ta buga ka faɗi a wannan wuri matacce.
"Tabbas a yanzu ganin fusatarka tasa ba zamu faɗa maka wannan abu ba, saboda zaka iya zaucewa idan ka sani."
"KAI!" Sarki Kuffuru ya daka masa tsawa, "Bayani mai gamsarwa nace kuyi min ba kame-kame ba..."
Aljani Sheezuwa yayi murmushi ya ce, "A wannan lokaci ne, sadaukai jinin Infiro zasuyi amfani. Kana da abokan gaba masu yawan gaske. Akwai sarki Ayubu, akwai Aymanul Faris, akwai Marganu, wai waɗanda muka sani kenan. Amma, idan ka tashi sadaukai jinin Infiro ka basu siffarka zasu tafi neman dukkanin wani abokin gabarka su hallaka shi.
"Shirin namu shi ne, zaka tashi sadaukai jinin Infiro guda goma, sannan ka basu irin siffarka. Ɗaya daga cikin su zamu bar shi a wannan wuri ya taryi su sarki Ayub, ya kashe su. Sannan zamu tura ɗaya daga cikinsu ya koma birninka ya ci gaba da gudanar da harkokin mulki. Ɗaya kuma zai tafi farautar Marganu a duk inda yake da waɗanda suke tare dashi ya hallaka su."
Sarki Kuffuru ya tari numfashin sa ya ce, "Wai wanne Marganu ne kuke ta magana akai? Shin akwai wani sabon Marganun da ya sake bayyana ne? Bayan wanda aka kashe a birnin sarauniya Rauziyya?"
Boka Hubbazu ya yi murmushin takaici ya ce, "Marganu bai mutu ba, yana nan a raye...!"
A fusace sarki Kuffuru ya miƙe tsaye ya nufi ƙofar fita yana cewa, "Amma sarauniya Rauziyya ta raina min hankali, ya za'ayi ta ƙi sa wa a kashe Marganu. Bata san cewa rashin kashe Marganu a gare ni, tamkar na kashe maciji ne ban sare kansa ba?"
Kafun ya ƙarasa bakin ƙofa yaji muryar boka Hubbazu, "Tabbas wannan sarauniya ta bayar da umarnin a sare kan Marganu, kuma waɗannan arnan daji sun cika wannan umarni, amma, kafun su sare kan Marganu waɗansu mutane guda biyu suka zo suka cece shi."
Wannan batu na boka Hubbazu yasa sarki Kuffuru ya tsaya a wannan wuri yana ta tunani. Idan har ceton Marganu aka yi, to, su waye zasu cece shi? Bayan in banda shi da amintattunsa babu wanda yasan da batun an kai Marganu tsaunin Barzasa.
Sarki Kuffuru ya rasa amsar wannan tambaya saboda haka ya dawo wajen su boka Hubbazu ya zauna.
"Waye ne ya ceci Marganu, shin zaku iya nuna min dukkanin abinda ya faru a wannan wuri a cikin madubin tsafin ku?" sarki Kuffuru ya tambaye su.
Boka Hubbazu yayi murmushi mai nuna isa ya ce, "Kana tunanin mutanen birnin Hirtoliya ƙananun shaiɗanu ne? Ya za'a yi ka kashe sarkin su, sannan ba zaka tura wakilinka ba, wanda zai na tafiyar da harkokin mulki?
"Ba'a banza Ratanam ya zamo gawurtaccen sarki a wannan nahiya ba. Yana sarrafa aljani kamar yadda kake sarrafa Djinn. Ratanam yana da wani ɓoyayyen hadimi dake rayuwa acan bisa wani tsauni. Wannan hadimi nasa shi muke kyautata zaton ya ceci Marganu."
Sarki Kuffuru ya haɗe fuska ya ce, "Anƴa wannan tafiya tawa, ba zata yanke ba kuwa? Akwai abubuwa da yawa a gabana masu muhimmanci da ya kamata a ce naje na kawar da su."
Aljani Sheezuwa ya dubi sarki Kuffuru ya ce, "Meye amfanin sadaukai jinin Infiro idan har zaka ɗinga wahalar da kanka?

Please Login or Register in order to submit comment