Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sai yau, dad’i ya mamaye zuciyarta ganin irin kishin da Hafiz ke nunawa akanta...

Da k’yar aka raba fad’an Hafiz Alhaji Tanimu saida aka fidda Alhaji Tanimu daga restaurant d’in.. Shiko Hafiz a zuciye ya k’araso gaban Sawwama yana fad’in “Kin gama aiki a restaurant d’in nan, ince damuwarki a d’aura auren ne...?”

Cikin fad’a Sawwama ma tace “Wllhi babu igiyanka akaina baka isa hanani zuwa nan ba...”

A hasale yace “Haka kikace...?”

“Kwarai kuwa haka nace...!” Ta k’arashe tana galla masa harara hannaye a kunkumi...

K’wafa yayi kana ya d’auki mabud’in abin hawansa yayi ficewarsa daga Kantin...


Yana fita Sawwama da Mamanta suka dubi juna suka shek’e da dariya, Magajiya tace “Kinmin daidai yanzu ne zaki fahimci matsayinki a wajensa idan har da gaske sonki yake....”

Sawwama ta murmusa tana mai jijjiga ita kad’ai kana tace “Allah Magajiya ki tsaya ki gani tas saina mallakesa ni kad’ai a tafin hannu na.....”

Shewa suka kuma sakawa Magajiya tana mai rangad’a gud’a....


****

*Kaduna*


Tsaye take tana hangensa sai faman shirya masu dining table yake bayan ya gama dafa masu abinci mai sauk’i dai dai ci da dare, a hankali Siyama ta lumshe idanunta domin kuwa ko shakka babu tayi missing komai nasa...

Juyowa yayi ya ganta tsaye a wajen tana dubansa, kashe mata idanu guda yayi kana ya k’araso ya sureta cak suka nufi teburin cin abincin sai faman cakulkuli yake mata tana zillewa...

Zaunar da ita yayi saman kujera kana ya d’an rank’wafo yace “I’m the waiter here... Mai Queen d’in take son ci...”

D’agowa tai tana dubansa kafin ta saki murmushi tace “Kai Partner... I missed your delicious dishes..”

“I know that’s why I cooked for you honey....”

Murmushi ta kumayi kana ta mik’e tace “I’ll serve....”

Ba musu ya koma ya zauna yana dubanta yanda take serving abincin a hankali, nazarinta yake yana tunanin something is wrong with her, don gaba d’aya ya lura da canzawa da tayi ita kanta ta tsargu da irin duban da yake mata gaba d’aya gani take kaman ya hango abinda tai, mummunar fad’uwan gaba ne ya dirar mata sanda ta jiyo muryarsa na fad’in

“Partner... You know you look like a pregnant woman....Are you sure babu ajiyana a tattaredake....?”

Zaro idanu waje tai tana dubansa ba tareda ta iya ci gaba da serving abincin ba....

Murmushi saman fuskarsa ya mik’e ya k’araso gareta had’ida rungumeta ta baya hannayensa duka biyu d’aure saman shafeffen tummy d’inta...

Kansa saman kafad’anta idanunsa a lumshe yake ci gaba da fad’in “Partner don’t you think is about time mu fara tunanin building namu family d’in....?”

Saurin rintse idanu tai k’irjinta naci gaba da bugu, k’ok’arin saita kanta tayi kana tace “Let’s eat Partner, the food is getting cold already....” Ta k’arashe tana mai cire jikinta daga nashi jin ya soma sumbatar wuyanta....

Zata zauna kujeran gefe ya kuma janyota ta fad’o saman cinyarsa, murya can k’asan mak’oshi yake furta “Honey I missed you... I missed you so much....”

Gaba d’aya sunyi nisa a wata uwa duniya har saida suka jiyo k’aurin k’onewan abincin kafin Siyama tai azamar k’wace kanta ta nufi kitchen d’in ta kashe gasscooker d’in da Sameer ya mance a kunne...

Tsayuwa tai kitchen d’in tana mai maida numfashi, bata isa ta mik’awa Sameer kanta a daren yau ba domin kaw ta mance pills d’inta da a kullum take shan k’waya d’aya a gida....

Bata koma parlorn ba sabida tunanin mai zatai ya kub’utar da ita hannun Sameer yau, ruwan zafi ta hanga cikin electric kettle take ta janyoshi ta d’an bige kad’an ya zube mata a k’afa...

K’ara ta k’walla wanda ya sanya Sameer nufo kitchen d’in babu shiri.....


A hanzarce ya k’arasa ya d’age kettle d’in yayi saurin d’agota yana mata sannu had’ida tambayarta ya hakan ta kasance, kasa ce masa komai tai sai narkewa da tayi cikin jikinsa tanai masa kukan shagwab’a...

Abinka da likitan k’una first aid d’insa ya d’auko bayan ya ciccib’eta ya kaita parlor ya kwantar saman kujera ya shiga mata dressing wajen, fad’i yake

“Sannu Partner, does it hurt..? Sannu koh.. Zai daina yanzu In sha Allah... Barin baki abincin a nan.....?”

Girgiza masa kai tai cikeda shagwab’a kana tace “Bazan iyaci ba na k’oshi please ka kaini d’aki...”

“Alright but ko fruits zaki sha....” Bai jira cewanta ba ya kuma sungumarta ya nufi bedroom da ita kana ya dawo ya d’ibi fruits a bowl ya koma d’akin yana bata a baki a hankali...

Kallonsa kurum take tana ayyanawa cikin zuciyarta da ace yanzu akwai d’iya ko d’a a gidan wannan gata da tarairaya duk bazata gansu ba saidai yayiwa gudan jininsa haka, dole k’aunar da yake mata da tarairayan da yake bata ya ragu a nata tunanin...

Haka Sameer yayita riritata yana mata sannu har bacci yayi gaba da ita tana mak’ale cikin jikinsa....

****


Banda safa da marwa Aunty Lami bata komai cikin tsululun dare ita kad’ai a cikin d’aki, sanin matsayin aminiyar sirri a wajen Ma’aruf ya haifar mata da shakku cewa bata kashe Ma’aruf ba kaman yanda sukayi zaton tayi......




SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_




*22*


*©Sameena Aleeyou...✍🏽*





*Gaisuwa fatan Alheri gareku Ahalin SAN Aminiyar Sirri na gaisuwa ta gode da nuna k’auna🤪🥰*



Da k’yar bacci b’arawo yai gaba da Lami amma fah duk juyi sai fuskan matashin nan mai zubi da Ma’aruf ya fad’o mata, bata fata Mamy tai idanu hud’u da wannan saurayi kaman yanda tai, yanzu babban burinta bai wuce ta samu wata hanya da zata iya nesanta wannan saurayi daga gidan ba, don idanma ba shine Ma’aruf ba shakka babu jikinta na bata shi zai alank’antasu da Ma’aruf....

Washe gari da hantsi Mamy na zaune saman carpet a parlornta tana rage k’umbar hannayenta da k’afafunta, sai sautin karatun sheik Ahmad Sulaiman ke tashi ga wani had’edd’en k’amshin turaren wuta na ratsa sashen nata gaba d’aya, yaran nata duk sun tafi makaranta Aunty Lami tai sallama ta shigo rik’eda ‘yar k’aramar bokati na kindirmo had’ida fura k’ulle a bak’ar keda...

Mamy ta fad’ad’a murmushinta suna gaisawa sanda Aunty Lami d’in ta k’araso ta zauna saman sofa ta sha lullub’i alamun fita zatai....

“Su Marliya duk an tafi makaranta koh...?” Ta tambaya murmushi kwance saman fuskarta,

Mamy ta rage sautin karatun kana tace “Duk sun fice Nabila ma sun koma satin nan....”

Aunty Lami ta kuma murmusawa tana furta “Allah sarki b’angaren namu duk sai yayi shiru, koda shike gidanma gaba d’aya tinda duk sauran yaran ma sun koma...”

Mamy ta jinjina kai tace “Haka ne... Fitane zakiyi...?”

Aunty Lami ta kuma murmusawa kana tace “Eh zanje gidan k’awata Hajiya Tani kinsan an saka bikin d’anta....”

Mamy ta d’an murmusa kana tace “Kai Masha Allahu, Ubangiji Ya sanya alkhairi, ki gaidata idan kinje, lokacin bikin idan Allah ya kaimu ma lek’a...”

Aunty Lami tace “Haka ne.....”

Lokaci guda ta mik’awa Mamy ‘yar bokatin kindirmon da fura tace “Jiya aka kawomin daga gari mai kyau dashi...”

Mamy ta amsa fuska d’auke da murmushi saida tinda taji k’amshin fura fuskanta ya d’an canza, ta shigo tuno d’anta Ma’aruf abinda yafiso kenan a rayuwarsa, kullum idan Abbah ya fice kasuwa sai ya dawo dashi, tinda Ma’aruf ya b’ace kindirmo da fura sukai k’aura ma gidan, shi kanshi Abbah sai ya zamto ko k’anshinsa baiso balle yayi ido dashi....

Aunty Lami tana hankalce da yanayi Mamy dama abinda take son gani kenan....

D’an muskutawa tai kana ta kwantar da murya yawa mutuniyar arziki tace “Mamy rashin Ma’aruf bai kamata yasa rayuwarki ya canza gaba d’aya ba, karki mance shifa Allah na son mai hak’uri da tawakkali, kar ki biye na mijinmu sabida ke kin fisa zuciya mai taushi dukda rauni da zuciyar taki kedashi... Mamy shifa duniya tinda muka zota toh fah duk daren dad’ewa wataran zamu barta, yau shekaru ak’alla talatin ya kamata ki mance komai kici gaba da gudanar da rayuwarki kaman da dukda cewa nasan hakan nada matuk’ar wahala amma daurewa zakiyi....”

Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “Haka ne Lami, kuma na gode da shawarinki masu kyau, tabbas Allah na tareda masu hak’uri da kuma tawakkali... Amma cireshi a zuciya gaba d’aya abune mai matuk’ar wahala, yau da ace naga gawan Ma’aruf da idanuna da abin bazai dameni har haka ba tinda na sani duk mai rai mamaci ne babu babba babu yaro babu tsoho lokaci tanayi dole a tafi.... Amma banga gawanshi ba, shin yana raye ko ya mace, idan yana raye a ina yake rayuwa...? Wane irin addini da tarbiya ya samu, shin a ina yake samun abincinda yakeci har ya rayu ya girma, inane makwancinsa.... Shin idan ya girma yanada iyalai ko baida shi....?” Muryarta ya soma rawa sosai sanda taci gaba da fad’in

“Lami wad’annan tambayoyi sune suka tsaya min a zuciya, sannan duk yanda nakaiga amintar da zuciyata cewa Ma’aruf ya mutu abin yaci tura, zuciyata tak’i amsa tak’i yarda cewa Ma’aruf baya raye a duniyar nan... Zuciyata tafi k’arfafa min cewa akwai ranar da zai dawo gareni ranar da zan kuma tozali dashi, ranar da bak’in cikina zai yaye zuwa akasinsa... Sannan inaji wannan rana gab take da zuwa....” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka wanke mata fuska....”

Kaman daga sama sai jiyo muryar Mamani sukai tana fad’in “Daga baya kenan wai sadaka da bazaura, duk kinsan da wannan kika jajib’esa kikaje kika jefar dashi... Yo waye ma ya sani ko saidashi kikayi tinda babu irin abinda ba’ayi a wannan duniyar tamu, uwa takan haifi d’a ta toni rami ta bisne sabida bata sonsa, uwa takan haifi d’a ta saidashi ma k’ungiyar asiri ta shan jini don ta sami kud’i, munafuncin banza kizo kina damun mutane da bak’in iyayi, bazan daina miki Allah ya isa ba Mariya b’atarmin da jika da kikayi... Algunguma kawai....” Wiwiwiw nan ta shiga rera kuka kaman an kunna injin markad’e...Aunty Lami ta mik’e da sauri ta rik’eta tana bata baki ta fitar da ita zuwa sashenta...

Tinda Mamy ta kifa kanta hawayene kurum ke zubo mata, jiki a sanyaye ta mik’e ta nufi uwar d’aki don yin alwala dama bata gabatar da sallan walha ba kaman yanda yake d’abi’a nata, tuni ta shiga mik’awa ubangijinta kukanta.....

***

*Kaduna*


Yana kishingid’e saman sofa a parlor yana kallon shirin The Dr’s da ake gudanarwa da hantsi ta sauk’o daga saman bene taci uwar gayu kaman ba itace jiya da dare take kwance nasha nasha ba....

Da mamaki Sameer ya d’ago ya dubeta kana yace “Ina zaki da k’afar taki, ko ta daina zafin ne....?”

K’arasowa tai had’ida aje handbag d’inta saman kujera kana ta manna masa sumba a gefen fuskarsa tace “Partner nayi latti, presentation ake jirana zanyi a office....”

Girgiza kai Sameer yayi yana dubanta kana yace “But Siyama k’afarki bata gama warkewa ba kin rufeta cikin takalmi, sannan duka duka fah jiya nazo kuma bazan wuce kwana biyu ba, yau zaki fice office ki barni... C’mon Siyama....”

D’an juya idanunta tai kana ta zauna jikinsa ta kamo hannayensa ta langab’e kai gefe tace “But Partner you know I’m a successful career woman, tun kafin ka aureni kasan da wannan, Sameer so kake na neglecting aikina, please mana... Ko ka mance kai kake supporting d’ina before....”

D’ago face d’inta ya d’anyi kana yace “Siyama ba cewa nake ki ajiye aikinki ba but at least tinda jiya na dawo ai na cancanci a bani kulawa na d’an kwana biyun nan da zanyi... Honey musamman fah sabidake na baro ayyukana na taso nazo, wannan shine tarban da za’a bani....?” Ya k’arashe yana mai kasheta da kallo...

Hannayensa ya kuma rik’owa cikin nata still tana zaune saman cinyarsa kana tace “Partner kasan idan banyi presentation d’in nan yau ba Daddy bazaiji dad’i ba dama yace yanzu Khalid ya fini k’wazo a aiki a company d’in please mana Partner... I don’t want to let Daddy down...” Ta k’arashe kaman zatai kuka...

Jinjina kai yayi kana yace “Fine, it’s alright... Kije, zanje na duba Mummy nima anjima... Take care of yourself ok....” Ya k’arashe yana sakar mata murmushi had’ida gyara mata mayafinta da ya zame ya rufe mata jikinta gaba d’aya...

Dubansa take tsananin k’aunarsa na d’awainiya da ita, lokaci guda ta rungumesa tana furta “I love you Partner...”

“I love you too...” Ya fad’i fuskarsa babu yabo babu fallasa....

Ko takan breakfast batabi ba ta fice cikin sauri tana amsa waya tana fad’in gata nan k’arasowa....

Kallo yabi bayanta dashi har ta fice kafin ya sauk’e ajiyan zuciya ya mik’e ya nufi dining table d’in shi kad’ai kad’aici na d’awainiya dashi, har sai yaji yayi missing Shamsu da Mama dashike idan bazai fice office da wuri ba tare suke karya kumallo gaba d’aya saman dining table.. A hankali ya saki murmushi abincin da bai iya ci ba ya mik’e ya haura upstairs ya shirya tsaf ya nufi nasu gidan....


A kitchen ya tadda Mummy tana directing ma’aikatanta abinda zasu dafa lunch don dama ita d’abi’arta kenan sam bata sakewa ma’aikata girkinta dole sai tana supervising nasu wasu abubuwan ma da kanta take don a wajenta Sameer ya soma koyon girki rabin yinin Mummy a kitchen ne shiyasa shima yasan abubuwa da dama gameda kitchen....

Innani ce ta soma hangosa zatai magana ya mata alamu da ido kan tayi shiru, Mummy naci gaba da fad’in “Ina Zilai tazo ta yanka veggies d’in nan banso a barsu haka nan....” Batakai aya ba saiji tai an rungumeta ta baya....

Ta saki murmushi don tasan mutum guda da zai mata haka, ba tareda ta juyo ba ta d’ago hannu ta d’an dunguri kanshi tana fad’in “Yaushe zaka girma ne wai Sameer, ko sai ka haifo min jikokin nawa ne sannan ka girma ka bar masu jikin nawa su ci gaba da tsalle akai....”

Murmushi kwance saman fuskarsa yace “A wajen Mummy na bazan tab’a girma ba ko yara nawa zan haifa, suje jikin nasu Mummy d’in suyi nima su barmin nawa....”

Murmushi tai cikeda jin dad’i kafin suka soma gaisawa, nan Sameer d’in suka gaisa da ma’aikatan kowa na fad’in yayi kewarsa musamman Innani data jima sosai a gidan tun Sameer d’in na yaro...

Nan kuma aka soma haba haba dashi ana tambayarshi mai za’a kawo masa..

Mummy tace “Innani kina mancewa ne wannan ai saidai ya shiga ya dafa da kansa koda yake k’ila yanzu ya daina tinda yayi aure yanada mai mishi...”

Murmushi kawai ya d’anyi baisan dalili ba amma sai yaji maganar Mummy ya masa wani iri, ko don Siyama bata mishi ne.... Duban Innani yayi kana yace a kawo mishi breakfast...

Mummy ta kalleshi da mamaki kana tace “Ba tun jiya kacemin kazo gari ba, ko yanzu ne sauk’ar naka...?”

Girgiza mata kai yayi kana yace “Tun jiya ne, daga gida nake Mummy....”

Bata kuma cewa komai ba sai d’an sanyi da jikinta yayi, anya wannan aure na Sameer na jin dad’inta kuwa, ace miji yazo gari takannas a kasa dafa masa karin kumallo sai yazo gida...? Ita kad’ai take tambayar kanta cikin zuciyarta, tasan hak’uri irin na Sameer shiyasa kwanaki da suka sami sab’ani da Siyama tabi bayan d’iyar k’awarta Siyama daga baya saida taji bata kyauta wa d’anta ba tinda ita ta tayar dashi ta kuma san sarai Sameer mutum ne mai tsananin hak’uri da kai zuciya nesa toh amma katsalanda a rayuwar ma’aurata ma duk baida wani amfani....

Da kanta ta shiga kitchen ta had’o masa delicious ta dawo parlor ta tayasa zama yana ci suna hira, yana mata hiran abokinsa Shamsu da shima ya tab’a zama gidansu, ya k’arada suna gaishesu gaba d’aya...


Yini zubur yayi a gidan har saida Daddy ya dawo suka gaisa suka b’ige da fira suma... Ba shi ya bar gidan sai bayan isha bayan Mummy ta gama cika mishi ciki da abinci...

A b’angaren Siyama kuwa tuntuni ta dawo donma saida ta biya gida ta d’auko pills d’inta da ta mance sannan ta biya eatery ta sai masu abinci Incase Sameer baiyi ba...

Koda ya dawo ta masa tayin abinci ce mata yayi yaci gidan Mummy, bata damu ba taci nata takai sauran kitchen...

Yau dai kafin ya nemeta tayi k’ok’ari takai kanta dashike tasha maganinta na hana d’aukan ciki...


***


Kwanan Sameer biyu ya tattara ya koma Kano ya bar Partner d’insa da kewarsa...

A b’angaren Khalid kuwa baida buri da ya wuce Daddy ya kuma aikensa Kano, shi ko Daddy bai aikesa ba ma shi zaijeshi da zaran aiki ya ragu mishi, Yesmin tana nan zatai kwana biyu a Kaduna kafin ta koma Abuja don tuni Mummynta ta koma ta barta da hud’uban kar ta kuskura ta dawo Abuja ba tareda ta saye zuciyar Khalid ba...


***

Aunty Lami da Hajiyar Hafiz zaune gaban Malam mai bugun k’asa ana masu duba idan Ma’aruf na raye...

Malam ya buga k’asa yayi wasu zane da yatsun hannunsa guda biyu kana ya d’ago ya dubesu..

Har suna had’e baki wajen cewa “Malam yaya shin yana raye ko ya mutu.....??”


SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_




*23*





*©Sameena Aleeyou...✍🏽*






Malam ya d’ago ya dubesu ba tareda ya furta komai ba, Hajiya tai saurin furta “Malam yaya... Shin kaga Ma’aruf na numfashi a doron k’asa....?”

Kallonta Malam yayi ba tareda ya kuma furta koda kalma ba kana ya iza babbar rigarsa mai tsananin daud’a ya kuma zana layi guda da yatsarsa...

Aunty Lami sai faman yakushin Hajiya take tana k’yafta mata idanu tana fad’in “Ke Haule mu dakata muji ta bakin Malam....”

Gyaran murya Malam yayi kana yace “Abu ne a duhu....”

Suka kalli juna cikeda k’osawa...

Lami ta gyara zama sosai kana tace “Allah gafarta Malam bamu gane ba, kaman yaya abune a duhu...?”

Malam ya kuma sab’a babban garensa kana yace “Kasa bai nuna min komai ba, ban hago tak’aimemen abinda ke wakana ba, zan baku hak’uri ku dawo wani lokaci....”

Cikeda jin haushi Hajiya tace “Yo mai kake nufi kenan Malam, so kake kace muna biyanka a iska, kaga idan bazaka iya duba mana bane sai ka fad’i mana mu tafi wani wajen bawai kace mana bakaga komai ba....”

Duk yanda Aunty Lami ke muskutin Hajiya ta kasa rufe baki sai faman b’araka take...

Malam ya jinjina kai kana yace “Kuna iya zuwa wani wajen a duba maku amma ina mai tabbatar maku K’asa bazata min k’arya ba, duk yanda kukaje iyakacin abinda za’a gaya maku kenan, K’asa da Taurari bazasu min k’arya ba.. Amma tinda kun zab’i zuwa wani wajen sai anjimanku Allah bamu alkhairi...” Ya k’arashe yana k’ok’arin nad’e buzunsa...

Aunty Lami tai saurin katseshi da fad’in “A’a baza’ai haka ba Allah gafarta, yarda da aikinka yasa mukazo nan, tinda kace haka ai sai mu tafi mu dawo wani lokacin....”

Malam ya jinjina kai kana yace “Zan baku rana ku dawo rana itiyau kafin nan na k’irga taurari naga abinda zan iya gani....”

Suka jinjina kai a tare kafin suka mik’e suka masa sallama suka d’au hanyar gida...

Tinda suka fito Hajiya ke sababin cewa wannan bokan neman raina masu hankali yake dama sun nemi wani ne su k’yale tashan wannan gidahumin Malamin...

Aunty Lami tace “Um um Laure mubi a sannu, tinda yace mu dawo ran sati ai sai mu dawo ba wani abu bane....”

Hajiya ta jinjina kai kana tace “Yanzu abinda za’ai kisan yanda zakiyi kisha mana cikin mijinki muji alak’arsa da wannan saurayi da ya firgitaki kin fahimta idan yaso sai musan yanda zamu b’ullowa lamarin....”

Shiru Aunty Lami tai tamkar mai nazari kana tace “Kinfa sanshi kinsan mijina wane irin rikitaccen mutum ne, haka nan yake a tank’ware yawa arnen da, fuskarsa ma kurum bazai bari na iya tambayarsa ba...”

Hajiyar Hafiz ta buga tsaki kana tace “Ai kinji matsalarki shegen tsoron miji, ance ki kai sunansa gaban Malam kin kasa da yanzu kina zuba mulkinki son ranki, ni yanzu kinga duk taurin Alhaji saidai ya ganni ya barni don billahillazi sai nace ayi ayi idan kaw bance ba babu uban da ya isa yi...”

Aunty Lami ta murmusa kana tace “Haule kenan ni fah baso nayi mulki nake ba babban buri na shine na zama tauraruwa a cikin gidana ya kasance kowa ni yake kallo kowa ni yake so wanda da zallan makirci zan iyayin hakan babu taimakon boka balle Malam bawai na mallake mijina na maidashi mijin tace ba, a nan ra’ayinmu yasha banban gaskiya....”

Hajiya ta watsa mata kallo had’ida tab’e baki tace “Ai kinji, wake yayin auren haula bayan kanada masu share maka kuka,ke kikaga zaki iya... Nidai kinsan yanda zakiyi ki binciko mana wannan saurayi musan matakin d’auka akansa.... Ita kuma Aminiyar sirri ba zuba mata idanu zamuyi ba, zuwan takannas zamu mata ta sanar damu abinda tayida Ma’aruf kar mu zama wawaye...”

Da wannan tattaunawa suka rabu, adaidaita guda daman suka d’ale, Hajiya Haule aka soma sauk’ewa kafin aka wuce da Lami....

***

A ‘yan kwanaki biyun da Sameer baya nan saida abin ya dami Abbah, ya lura baya ganinsa a masallaci haka nan ko k’yallin motarsa bai ganin goftawanta a unguwar, ranan dai bayan an ida sallan lisha ya tare Shamsu yana tambayarsa Sameer, abin har saida ya baiwa Shamsu labari, mutumin da a baya babu ruwansa da kowa a unguwar tamkar shi kad’ai yake rayuwarsa dukda Shamsun ma dangin hakan ne amma yana hankalta da dattawan unguwar yanda suke sabo da juna amma banda Alhaji Usman Mailafiya sai gashi lokaci guda sun shak’u matuk’a da Sameer har yana tambayarsa lallai Sameer akwai shi da saurin shiga ran jama’a... Shamsu ya d’an murmusa ya sanar dashi Sameer yaje dubo gida ne...

Jikin Abbah yayi sanyi da ya fahimci ganin iyayensa Sameer ya tafi, da gaske dai wannan saurayi babu abinda ya alank’anta shi da Ma’aruf d’insa...

Ranan jiki a sanyaye Abbah ya koma gida, harta su Mamy saida suka fahimci d’an canzawan nasa na kwana biyu, lokacin da Sameer ya dawo kuwa saida farin ciki ya nuna a tattareda Abbah, lallai bahaushe yayi gaskiya da yace sabo turken wawa....

A satin Hafiz ya d’aga masu hankali da maganan k’arin aurensa, abu kaman wasa wuta wuta aka tambaya sadaki da lefe gidansu Sawwama, wai zo kaga farin ciki wajen Sawwama da Magajiya, duk wani b’uli da suka san cewa ka iya jawo masu matsala musamman mutanen unguwarsu saida suka tosheta don Magajiya ta d’au alwashin wannan shekaran sai d’iyarta Sawwama ta tare d’akin miji ba d’akin saurayi ba kaman yanda tasha yin hakan a baya...

Gidansu Sawwama basu yanke lokaci mai tsawo ba wata guda jal suka yanke dashike dama alla alla suke su mik’ata su huta, shi kanshi Hafiz ba wai d’aukin auren yake ba saidai baisan dalilin da yake matuk’ar so ayi auren wuta wuta ba, baisan ko rashin matarsa Zulfa’u bane yasa yake so ayi bikinshi da Sawwama nan kusa ko zai rage kewar matarsa da yake...

Duk wannan bidiri da ake sam Zulfah bata sani ba, hasalima farin cikin kammala bautan k’asanta take, gashi Aunty B tace da zaran ta gama Iddarta zata samar mata gurbin aiki ya rage mata kewa, yanzu babban burinta bai wuce ta sanya mahaifiyarta da d’iyarta a k’wayan idanunta ba....

***


Kaduna....

“Mummy ya fah wuce duk yanda kike tunani, kawai Mummy kisa a fara maganar auren mu inaga ta haka ne kawai zan samu attention d’insa.... Please Mum talk to your sister...” Ta k’arashe kaman zata runtuma ihu ta cikin wayar...

Daga d’aya b’angaren mahaifiyarta tace “Yesmin are you sure kinyi duk abinda nace kiyi...?”

Cikeda shagwab’a Yesmin tace “Mummy I did everything you asked me to do, amma wllhi Mummy kallo fah ban isheshi ba, I’ve exhausted all my efforts already....”

Cikin kwantar da hankali mahaifiyar tata ke fad’i mata “Ki kwantar da hankalinki ni zanyi maganawa Faridar kinji koh, kedai kawai just focus don’t lose hope kinji koh...”

Yesmin ta jinjina kai a hankali kaman mahaifiyar tata na kallonta kana tace “Alright Mum, take care... Say hello to Daddy for me...”

Daga haka katse wayar tai tana tunanin yanda zata karkato hankalin Khalid gareta...

Kubura dake lab’e bakin k’ofa rungumeda bedsheets zata kai d’akin Mamy nan ta lab’e tana sauraren wayan Yesmin...

Kusan cin karo sukai da Yesmin d’in da batasan Kubura na lab’e jikin k’ofarta ba...

Wani mugun kallo Yesmin ta watsa mata kana tace “Ke wai meye kike bibiyata, lafiya...?”

Kubura ta tab’e baki tace “Yo naga dai hanya ta biyo dani nan, d’akin Mamy zan shige Sirkar kirki...” Ta k’arashe tana d’aga gira samawa Yesmin...

Yesmin ta bitada kallo tana maimaita kalmar sirkar kirki cikin zuciyarta... Gajeren tsaki kurum tai kana ta nufo downstairs...

Hango Khalid da tai zaune tareda Ammi suna fira ya sanyata saurin komawa sama a d’ari ta d’auro makeup saman fuskarta...

Daga yanda take k’arasowa tana iya jiyo muryar Ammi tana tambayarsa..

“Mai kuma zakajeyi Kano....?”

A tak’aice yace da ita “Ammi I’ve unfinished business there...”

Ammi ta kuma dubansa da kyau kana tace “Unfinished business...?”

Jinjina mata kai yayi yana mai ci gaba da canza tasha had’ida furta “Yes Ammi but ba jimawa zanyi ba kwana biyu zuwa uku kawai zanyi...”

Ammi ta jinjina kai kana tace “Ina maganar mu ta kwana...?”

Ya d’an d’ago

Please Login or Register in order to submit comment