Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalma ba sai kallo da yake bin Zulfa’u dashi yana hango wasu abubuwa nasu dake yanayi...
Cikin hawaye tana mai goge fuskarta take fad’in “Dr kamin magana dan Allah... Kace wani abu.... kace zamu iya shiga mu gansu na rok’ek’a dan Allah....”

Kasa furta komai Aunty B tai sai k’ura masa idanu da tayi idanunta na k’ok’arin kawo ruwa.... Cikin sauri ta k’unshe bakinta jin kuka na k’okarin b’alle mata ta fice daga wajen tana mai sakin kukanta, tabbas wannan d’an ‘yar uwartace da ya b’ace shekaru talatin... Allah ya dawo dashi, tabbas ba gizo yake mata ba shid’in ne Ma’aruf ne... Zataso ta zamto mutum ta farko da zata tabbatar da hakan ko don takai wannan labari mai dad’i ga ‘yar uwarta wacce ta rasa farin cikinta da walwalarta shekaru talatin baya....

A tare Hajiya da Aunty Lami suka zame jiki suka fice daga reception din cikin tsananin d’imauta da damuwa... Yanda suke sauk’a daga dakalin k’ofar reception d’in zai tabbatar maka cikin tsananin tashin hankali suke... Aunty Lami hannu biyu dafe da k’irji take fad’in “Haule Haule mun shiga uku abinda muka shuka shekaru talatin shike farautarmu, Haule ba gizo yake mana ba wllhi shine....!”

Cak ta tsaya da kalamanta sanda tai idanu hud’u da Aunty B itama sud’in take duba idanunta d’auke da hawaye......


SameenaAleeyou...📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*47*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Cikin tsananin fuci Aunty B ta tunk’arosu, tana mai gyara fuskarta, murmushin takaici saman fuskarta... Kai tsaye ta fuskanci Hajiyar Hafiz tana mai fad’in “Hankalinki ya kwanta burinki ya cika kin kashe Kausar, nasan da ace kin samu dama tin daga fari da kin kashe Zulfa’u ma amma saidai Allah k’addara mutuwar Zulfa’u hannunki ba.... Shin Haule wace irin ‘yar Adam ce ke...? Shin ashe har zaki iya halak’a jikarki jininki da hannayenki.... Ko zaki musnta min k’unar dasu Kausar sukai ba yinki bane iye....? Kiyi magana mana ya kikai shiru.....???” Ta k’arashe tamkar zata damk’o wuyar Hajiya....

Hajiya ta saki murmushi wanda yafi kama da yak’e kana tace “Bara’atu kenan, k’arfin halinki na mugun birgeni... Yo idan na kashe Kausar sai mai uwar mai zaki iya yi... Ke wacece mai kika isa kiyi.... Banza irinki karan kad’a miya....”

Aunty B da tuni ta gama isowa wuya ta nufo Hajiya gadan gadan zata shak’eta... Tuni Aunty Lami ta shiga tsakaninsu tana fad’in “Haba haba kukuwa... Ya kuke abu tamkar k’anan yara.... Shin da abinda kuke kuna taimaka ma Zulfa’u kenan...? Ya isa haka Bara’atu ki shige ciki Zulfa’u needs you....” Ta k’arashe tana janye Aunty B...

K’uramasu idanu su biyun Aunty B tai kana tace “A juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe....”

Hajiya ta sakar mata murmushi a tak’aice kana tace “Zaifi kyau idan kika daina saka hancinki a abinda bai shafeki ba....”
Aunty B ta kuma murmusawa tana mai dubansu su biyun kana tace “Ko mai kuke b’oyewa ku biyun nan zai fito fili.... Mu zuba mu gani....” Daga haka sa kai tai ta shige....

Aunty Lami da Hajiya suka dubi juna ba tareda sun furta kalma guda ba....

Kasa sanar dasu Sameer yayi dole sai Awwab ne yazo ya masu bayani, Sameer na daga yanda yake yana jiyo sautin kukan ‘yan uwansa.... A hankali ya rintse idanunshi tausayinsu na d’awainiya dashi har saida wata nurse ta iskeshi ta sanar dashi an shirya second patient d’in kafin ya nufi theatre room d’in jiki a sanyaye...

Tin daga k’ofa yake jiyo sautin kukanta cikin tsananin sanyin muryarta tana ambaton ina Kausar take.....
Muryar sounds familiar to him, a hankali ya k’arashe shigowa cikin room d’in sauran nurses d’in na gaidashi.... Cak ya tsaya yana dubanta itace dai domin kaw k’unan wutan bai tab’a fuskarta ba, lokacin da ya soma kuskuransu itada k’aramar yarinya da motarsa ya soma tunowa, ya tuna kuskuransu na biyu da yayi lokacin data watsar da kifin da wancan azzalumar matar Baban nata ta aiketa... Ya tuna last ganinsa da ita a gidan Abbah a parlorn Abbah....
A b’angaren Raihana ma shid’in take duba domin kaw sam bata tab’a mance kamaninsa ba mutumin da ya tab’a defending d’inta so d’aya tak a rayuwarta daga muzgunawa da cin zarafi da Hajiya ke mata... Toh mai yakeyi a nan d’in...? Ta tambayi kanta.... Kafin ta nemo amsar tambayarta taji nurse guda na fad’in “Dr everything’s ready....”

A hankali ya jinjina mata kai still idanunsa naga Raihanah... A hankali ya soma takowa har ya k’araso gabanta....
Jikin Raihanah yai sanyi da irin duban da yake mata dukda zogi da tsananin rad’ad’i da fatarta ke mata.... Duban nurses d’in yai kana yace “Get me the injection...”
Jin an ambaci injection ya sata kuma dubanshi saidai gani tai ya sauya gaba d’aya tamkar bai santa ba haka yayi....
Hannu yasa yana k’ok’arin yaye farin k’yallen da aka rufa mata....
Ta kuma zabura tana dubansa saidai sam shid’in ba fuskarta yake duba ba da alama aikinsa yake k’ok’arin yi....
Tana jin sanda ya rik’o hannunta guda b’angaren da babu k’unan.... Daidai sanda idanunsu ya had’e waje guda, tsananin tsoro da firgici ne zalla cikin idanun Raihanah....
D’auke kai Sameer yai daga barin dubanta ya dawo da idnunsa ga yanda yake k’ok’arin zira allurar... Tana jin sanda yake zira mata allurar cikin tsanaki, hakan bai hanata rintse idanu ba dukda cewa zafin allurar baikai zafin k’unan da takeji a cikin jikinta ba...

Sosai doguwar rigar material d’in ta kame jikinta, dole sai an saka almak’ashi ya iya tsaga rigar a rabata da fatarta....
Ya kuma umarni ma nurses d’in su mik’a masa almak’ashi....
Tsoro da firgici ya cika Raihanah dukda duru duru data soma gani alamun allurar da ya mata ya soma kamata.... Sameer ya kurama fuskarta idanu sanda take fad’i cikin magagi...
“Mai mai zaka min... Mai zakuyimin...? Ina Kausar... Ku fad’a min yanda take.... Ku fad’a min tana lafiya....”

A hankali ya janye idanunsa daga duban fuskarta ya shiga k’ok’arin b’arka rigar jikinta.... Yanajin sanda ta rik’e hannunsa da sauri dukda cewa idanunta a lumshe suke tana fad’in “Nidai ka... ka k’yaleni.... Ni please don’t....!”

Duban bakinta yake yanda take maganar da k’yar... A hankali ya d’ago yana duban nurses d’in guda biyu mata...
Sai kallon kallo suke ganin yanayin likitan nasu yau yasha banban da ko yaushe....
“Dr are you alright...?” D’aya daga cikin nurses d’in ta tambaya... Itama d’in dubanta yai kana ya jinjina kai a hankali alamun yana lafiya kana ya mik’a mata almak’ashin ya masu umarni su farke rigar....

***

Tinda ya shigo gidan yake raba idanu ta ina zaiga d’iyarsa, sosai yarinyar ta shiga ransa har cikin ransa yakejin yarinyar cikin d’an lokaci k’ank’ani da suka kasance tare don tinda Hajiya ta kawota shike rainonta shike d’awainiyarta saidai idan zai fita ne sai ya bartama Sawwama nan ma bada son ransa ba sai don babu yanda ya iya.... Wani shak’uwa mai tsanani ne ya k’ullu tsakanin Hafiz da d’iyarsa Kausar, bai tsamman yana son yarinyar har haka ba kodashike Kausar yarinyace mai tsananin shiga rai ga duk wanda ya lak’anceta balle shi mahaifinta akwai bond mai k’arfi tsakani....

Saman kujera ya aje ledar kayan wasan da ya siyo mata musamman, ya d’aga labulen uwar d’aki ko zai gansu... Nan ma shiru babu Sawwama balle Kausar, toh ina suka shiga...? Ya tamabaya yana mai sauk’e labulen... Saman kujera ya zauna ya shiga fidda toys d’in murmushi kwance saman fuskarsa, danginsu doll baby da sauransu ya tabbata zataso kayan wasan shi kad’ai yake raya hakan cikin zuciyarsa....
Yana a haka ne yaji shigowar Sawwama tana tafe tana amsa waya, sanda ta gansa zaune a parlor turus tai tana dubansa lokaci guda ta canza maganar da take da Alhajinta tana mai fad’in “Karki damu Magajiya ai nace maki zanzo, zanzoni In sha Allah... Yauwa a huta gajiya sai munyi magana...” Ta k’arashe tana mai katse kiran...

Dubanta kurum yake domin kaw ba wai ya yarda da Magajiya ta gama waya ba, tun kwanakin baya jikinsa ke basa wani abu saidai baiso ya jefo zargi cikin zaman aurensu....
Cikin salo ta k’araso ta zauna hannun kujera tana mai fad’awa jikinsa had’ida masa salo take fad’in “Hafizy yaushe ka shigo....?” Birki tai ma kalaman nata ganin kayayyakin dake rik’e hannunsa.... Ta wani yatsina fuska kana tace “Wannan fah... Na zaci kaji ne a ledar ma....?”

Girgiza mata kai yai kana yace “Ba kaji bane.... Ina Kausar...?”
Nan ma yatsina ta kumayi had’ida gyara zama tana wani karkad’e wuyar riga had’ida taunar chewing gum kana tace “Aw baka had’u dasu a waje ba....?”
Duban mamaki ya mata kana yace “Su wane....?”
Tana mai rausaya had’ida jijjiga cikin taunar chewing gum d’inta irinta rik’akk’un ‘yan tasha kana tace “Su Sahariyya mana, ai sun biyo sawu sun d’auki Kausar, tana can ‘Yan turame....” Ta k’arashe kai ka rantse iyakacin gaskiyar ta fad’i....

A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya shiga tattaran kayan yana fad’in “Barin tafi ‘yan turamen na sameta....”

Sawwama tai saurin tare gabansa cikin salo kana tace “Haba Hafizy ina zaka daga shigowa, Kausar dai bazata b’ace ba k’arewa gidanku take ba wani wajen ba, aidai ka tsaya kaci abinci ko Hafizy musamman na maka girki abinda kafi so...” Ta k’arashe tana shafar fuskarta cikin salo...

D’ago kai yai da niyyar magana Sawwama tai saurin d’aura d’an yatsarta saman labb’arsa tana mai furta “Shiiii karkace komai... Zo muje....” Ta k’arashe tana janyoshi har suka komo cikin parlorn... Lokaci guda ta zaunar dashi ta nufi kitchen ta had’o masa abincin da aka gama tsibbace shi da kayan tsibbace tsibbacenta na toshiyar baki...
Zaman dirshan tai tana basa abincin tana shafa kansa tamkar wani d’anta, cikin salo da mad’e taita cika ma Hafiz ciki da abincin da aka kawo mata daga can kantin Magajiya.... Aiko yana ida ci yaji kansa na juyawa kaman mai jin bacci bai wata wata ba dama ta samu tuni ta janyosa d’aki don dama a hannu take don da ace bai dawo ba da tuni ta tafi wajen Alhajinta wa’iyyazu billah.... Ya Allah kai mana tsari daga aikin danasani.... Da yawan matan aure sun halak’a sun fad’aga halak’a da tsananin fushi da tsinuwa ta Ubangiji, zinace zinacen matan aure ba zallan ‘yanmata ba ta yawaita a duniyarmu, mu sani irin wad’annan bala’u suna d’aya daga cikin abinda ke kawo annoba cikin Al’umma... Manzon tsira SAW ya fad’i mana zinace zinace bazatai yawa a doron k’asa ba har ya zamana ana bayyanata face Allah ya jarabci wannan al’umma da cutar da babu wanda ya tab’a sanin irinta... Muji tsoron Allah mu komaga Allah mu gyara tsakaninmu da Ubangijinmu sai Allah yaji k’anmu ya kawo mana d’auki, Allah Ka gafarta mana kaji k’anmu ka shiryamu da zuri’armu ta farkin addininka... Ameen ya Rabbi..!

***

Kan kace mai labarin mutuwar Kausar ya riski kowa idan ka d’auke mahaifinta, duk irin waya da Baba Alhaji mahaifinsa ke masa bai d’aga ba domin kaw tuni Hafiz ya b’ige da bacci, Sawwama na ganin wayar na shigowa saidaima tai tsuka ta katse kiran, k’arshe ma kashe ma kashe wayar tai gaba d’aya ta cilla gefe ta gyarawa Hafiz kwanciyarsa....
Iyakacin b’acin rai Baba Alhaji yakai, har shine Hafiz ke katse masa kira k’arshema ya kashe wayar gaba d’aya, lallai Hafiz ya cika d’ah maras tarbiya... K’wafa Baba Alhaji yai kana ya umarta liman da sauran jama’a dasu k’arasa da Kausar makwancinta domin kaw bazasu tsaya jiran tsammanin Hafiz ba....



SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*48*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Tareda Sameer akai komai, daga nan bai wuce gida ba don ko Siyama batasan da dawowarsa ba, kai tsaye asibiti ya nufa wajen Abbah....
Ya jima yana tsaye k’ofar d’akin yana duban Abbah daga yanda yake kwance k’walla na neman ciko idanunsa.... Sam Abbah baisan da zuwan Sameer d’in ba domin kaw idanunsa a lumshe yake, Sameer ya rintse idanunsa da k’arfin gaske hawaye suka kwaranyo masa domin kaw baisan ta yanda zai soma ba saidai d’ago idanun da zaiyi sukai ido hud’u da Abbah wanda ya masa k’uri babu k’yafta idanu.... Cikin sauri Sameer ya shiga k’ok’arin saita kansa yana goge hawayen da suka wanke masa fuska.... Cikin sauri had’ida d’an sassarfa ya soma shigowa d’akin lokaci guda yake k’ok’arin d’aura murmushin k’arfin hali saman fuskarsa....
K’ok’arin bud’e baki yake da niyyan gaida Abbah saidai kuma Muryarsace yaji ta sark’afe lokaci guda... Daga shi har Abbah kasa daina kallon juna sukai saima sabon hawaye dake k’okarin ciko idanun Sameer.... Lokaci guda bakin Sameer ya shiga rawa... Bai iya furta ko kalma guda ba sai rungume Abbah da yayi cikin wani irin shauk’i yana mai fitar da kukansa gaba d’aya.... Tsananin sanyi jikin Abbah yayi dukda cewa ba k’oshin lafiya bane dashi ga wani irin damk’a da Sameer ya masa yana mai jin kukan Sameer d’in har cikin zuciyarsa da ruhinsa... Gaba d’aya Sameer ya mance da condition d’in Abban, lokaci guda cikin muryar kuka yake furta “Abbah why...? Why Abbah... Meyasa kuka rabu dani, meyasa baku nemeni ba...? Meyasa kuka barni na rayu ba taredaku ba... Why Abbah....?”
Hannayen Abbah suka shiga rawa sosai sanda yake k’ok’arin dafa bayan Sameer cikin tsananin bugun zuciya....
Dukda rawan da hannun Abbah keyi bai hanasa k’ok’arin kamo kafad’un Sameer dake tsanin kuka ya d’agosa ba... Shima Abban kwantattun hawayene saman fuskarsa....
Cikin rawar murya Abbah ke furta “Ma’aruf...! Ma’aruf...!! Ma’aruf d’ahnah....!!!!” Lokaci guda ya kuma rungume Sameer da k’arfin gaske sai bursting cikin kuka da yayi... Suka k’ank’ame juna su duka biyun ko wannensu kuka yake sosai da kuka zuciyarsa....
Cikin kuka Abbah ke furta “Ma’aruf ka dawo...! Ashe zaka dawo garemu... Ashe zan sake ganinka..? Ashe kana nan raye d’ahnah... Mahaifiyarka tayi gaskiya datak’i aminta cewa ka mutu tunda jimawa... Ma’aruf ashe zaka dawo gareni.... Alhamdulillahi Alhmadulillah..! Allah na gode maka daka nunamin rana irin wannan kafin ka karb’i rayuwata... Allah na gode maka na gode...” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai kuma k’ank’ame Sameer cikin jikinsa....
Mamy dake daskare bakin k’ofa tai masu k’uri hawaye naci gaba da gangaro mata, tamkar mutum mutumi take takowa cikin d’akin idanunta basu daina duban Sameer ba tana hango Ma’aruf d’inta tun yana yaro har izuwa lokacin da ya b’ace mata....
Tsananin rawa hannayenta keyi sanda ta shiga shafa bayansa a hankali tana mai ci gaba da dubansa tana tuno rayuwarta da d’anta Ma’aruf, cikin rawar murya take furta “Zuciyata ruhina da gangan jikina bazasumin k’arya ba.... Tin daga randa na soma saka a k’wayan idanuna suka fad’amin cewa kaine.... Kaine Ma’aruf.... D’ah nah.....!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka da rawar jiki tamkar zata zube k’asa.... Cikin sauri Sameer ya tallafota lokaci guda ya rungume mahaifiyarsa su duka biyun suna kuka sosai, babu mai iya cewa komai cikinsu sai kuka da suke sharkaf da hawaye, sun jima a hakan kafin Sameer ya k’arasada mahaifiyarsa saman kujera ya zaunarta had’ida duk’awa gabanta... Ya rik’o hannayenta duka biyu yana dubanta cikeda ai da k’auna murmushi had’ida hawaye saman fuskarsa, lokaci guda ya kifa kansa saman cinyoyinta hawaye suna ci gaba da d’igo masa, itama Mamyn dafa kansa tai da duka hannayenta biyu hawaye naci gaba da d’igo mata....
Cikin sanyin murya yake furta “Mamy nah..! Mamy maiyasa kika bari suka rabani dake...? Why Mamy.... Maiyasa baki nemo d’anki ba, maiyasa kika bari muka kwashe shekaru sama da talatin bama tare Mamy why...?” Ya k’arashe yana mai kuma aje kansa saman cinyarta....
Cikin muryar kuka tana mai girgiza kai alamun a’a take fad’in “Ko kad’an d’ahnah... Ko kad’an bamuso rabuwarmu dakai ba saidai babu yanda muka iya da hukuncin mahaliccinmu, Ma’aruf d’ahnah ban tab’a cire ran cewa bazan sake ganinka ba daidai da rana guda.... A koda yaushe dakai nake rayuwa cikin zuciyata tsawon shekarun nan, d’ah nah ka yafeni ka yafemin....” Kuka yaci k’arfinta...

Sameer ya d’ago yana dubanta hawaye naci gaba da gangaro masa yake share mata hawayenta tsananin tausayi da k’aunar mahaifiyarsa naci gaba da mamaye illahirin zuciyarsa....
Abbah ne ya taso daga saman gadon da yake ya k’araso har gabansu yanai masu duba cikeda shauk’i, tinda yazo asibitin saidai a d’agasa amma sai gashi yau ya mik’e har ya tako da kansa... Haka nan yai tsaye had’ida masu k’uri yanajin yanayin da ya jima baiji irinsa ba a rayuwarsa, gaba d’aya ya had’esu ya rungume su duka ukun suna rungume da juna fuskokinsu d’aukeda hawayen annuri zukatansu cikeda tsan tsan farin ciki da annashuwa had’ida godiyawa Ubangijinsu maras misaltuwa da ya nuna masu rana irinta yau.....

***

“Daddy please zan bika...!” Tai maganar tana mai turo baki gaba had’ida rik’e hannun mutumin data ambato da Daddy....
K’uri ya mata fuskarsa cikeda taananin tausayi don yarinyar sosai ta saba dashi irin sabon da ya kamata tayida mahaifiyarta wacce sam bata samu hakan ba....
A hankali ya duk’a ya kamo hannayenta guda biyu yana mai share mata hawayen da suka kwaranyo mata...
Cikin muryarsa mai cikeda taushi yace “Baby kiyi hak’uri kinji wajenda zanje yara basa zuwa, kiyi hak’uri ki zauna da ‘yan uwanki da kuma Nanny kinji koh...”
Mak’e kafad’u tai sabbin hawaye suna zubo mata lokaci guda take furta “No Daddy I don’t wanna stay.... Please take me with you, I promise I’ll behave kaji please....”

D’an fuzar da iska yayi ba tareda ya kuma cewa komai ba a daidai sanda wani matashi mai kimanin shekaru 35 ya k’araso cikeda risinawa yana fad’in “Sir lokaci na gab da k’ure mana kasan sun maka shaidan mutum mai tsananin mutunta lokaci da cika alk’awari....”
A hankali ya jinjina kansa kana ya k’arada “Alright Akram... Zamu isa akan lokaci In sha Allah....”

Mutumin da ya ambata da Akram jinjina kai yayi kana ya fice, jim kad’an ya fito ya nufi taron motocinsa da ko wanne yana d’aukeda sunan MUTALLAB wajen da ake rubuta lambar mota....

Mutanen sai gaidashi suke kowa na k’ok’arin shigewa mota cikin sauri domin su d’au hanya, kai tsaye ya nufi mota guda wanda nake taammanin tasace, har ya iso jikin motar Akram bai sani ba, idanunsa a lumshe yana sauraren radio....
K’uri yayiwa Akram daga yanda yake tsaye yana duban yanda Akram ke sakin murmushi idanunsa a lumshe... Ya saki murmushi a hankali had’ida girgiza kai kana ya d’an k’wank’wasa gilashin motar da yatsun hannunsa guda biyu....
Cikin sauri Akram ya bud’e idanunsa had’ida d’an zabura kana ya bud’e lock d’in yana mai daidaita kujeran zaman nasa yake fad’in “Sorry Sir... Na d’an sha’afa ne....” Ya k’arashe yana mai sosa k’eya....

Murmushi ya saki a hankali kana yace “Akram kenan.... Mai kake sauraro haka....?”

Lokaci guda Akram ya bud’e sautin radio d’in da a baya ya rage kana yace “Shirin muryar ‘yanci nake saurare... Gaskiya gidan radio d’in suna k’ok’ari wajen sharhi da fashin bak’i kan abindake faruwa a gwabnatancen a k’asar nan.... Sir ya kamata ka fara sauraron shirye shiryen....”

Tak’aitaccen murmushi kurum yai kana yace “Toh banda abinka Akram idan ka saurara ai tamkar ni na saurara, besides kasan ban saba sauraren radio ba...”

Akram yace “Sir ya kamata ka fara sauraren irin wad’annan shirye shiryen domin ta haka ne zaka fahimci yanda siyasarka ta dosa tsakaninka da al’umma....”

Yai shiru tamkar mai nazari kafin ya jinjina kai a hankali ba tareda yace komai ba....
Tafiyar minti talatin sukai kafin suka iso farfajiyan taron siyasan yanda ko ina d’auke yake da manyan hotunansa da sunansa MA’ARUF MUTALLAB.....

****

Suna tafe cikin mota dawowarsu kenan daga gidan cin abinci sannan sun sayowa oga Sameer nasa tinda ya sanar da Siyamar cewa yau zai dawo, ba wai iya girkin tai ba balle ta dafa masa sayowan yafi mata sauk’i da zaran ya iso saidai ta saka a microwave ta d’umama..
Kaman daga sama Yesmin ta hangi motar tamkar ta Khalid na barin k’ofar gidansu Nabila domin goma idan za’a wuce idanunta naga k’ofar gidan ko zata hangi Nabilah... Gabanta yai mugun yankewa ya fad’i badai duk abinda suka turawa Khalid gameda yarinyar nan bai hak’ura da ita bane...? Ta tambayi kanta...

Siyama ta lura da canzawan Yesmin lokaci guda domin taga ta daina amsa mata firanta..
D’an juyowa tai sanda suke k’ok’arin shiga layinsu kana tace “Lafiya cousin.... Ya naga kin canza lokaci guda...?”

Yesmin tai saurin furta “Cousin Khalid na gani..”

“Khalid kuma..?” Siyama tace

Jinjina kai Yesmin ta kumayi cikin sauri kana tace “Wllhi motarsa na gani yanzun nan ya bar k’ofar gidansu tsinanniyan can.... Dan Allah juya motar nan mu koma....”

Kallon mamaki Siyama ta bita dashi kana tace “Mu koma ina...? Badai kince ya tafi ba....”

“Mu koma mu shiga har cikin gidan mui mata wankin babban bargo daga ita har iyayen nata inaga hakan ne kawai zaisa ta fita hanyar Khalid tunda bataji wancan warning d’in ba....”

Siyama ta dara a tak’aice kana tace “Cousin bakida kyau, haka kishinki keda yawa koda yake gaskiyarki domin ko ni ce zAnyi fin haka akan Sameer....” Ta k’arashe tana mai danna reverse.....





SameenaALeeyou📚




*INDA RAI*
_.................DA RABO_



*49*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Sai faman yatsine fuska suke sanda suka shigo gidan, ga k’ofofi kusan guda uku sun rasa wani k’ofar zasu dosa...

Daga can suka hango yarinya tafe ta fito daga wata k’ofar ta nufi wani sashen....
Siyama tai saurin katseta da “Ke d’anzo mana...”
Basma ta dubesu cikeda tsoro don haka kurum suka bata tsoro kana tace “Ni..?”

Muguwar tsuka Yesmin taja kana tace “Eh ke, ko kinga wani a nan ne bayan ke...?”

Basma ta k’araso tana duban cikin idanunsu....
Siyama tace “Dubi yanda take kallon mutane har cikin idanu yanda zaki gane gaba d’aya yaran gidan ba kunya ne dasu ba na rasa uwar da Khalid ya hanga jikin wannan mummunar yarinyar, banda tsiya babu komai a wannan gida...”
Yesmin dake faman toshe toshen hanci tace “Ke ni wllhi banda warin talauci ban iya shak’ar komai tinda muka shigo gidan...”

Basma dai banda binsu data muji bata komai, ta kalli wannan ta kalli wancan...
Siyama ta tsaida dubanta ga Basma kana tace “Ina yayarki...?”
“Wacce cikin yayyena...?” Basma ta tambaya...
Kan Siyama ta sami zarafin magana Yesmin tace “Karuwan can da aka jefeta bakin titi....”
Basma ta fahimci Nabila suke nema, hakan yayi mata don ko babu komai tasan wacece Nabila kuma tasan itace daidai da wad’annan matan....”
Saida itama ta yatsina irin yanda taga sunayi da fuskokinsu kana tace “A iya sanina dai babu karuwa gidan nan, domin kuwa gaba d’aya gidan nan babu mai saka irin suturar dake jikinku... Koma dai wacece kuke nema ku k’arasa wancan k’ofar yanda ake karb’an gaisuwa zaku sameta....” Bata jira cewarsu ba tasa kai ta shige...
Siyama ta bita da kallo kana ta dubi Yesmin tace “Cousin yarinyar nan ‘yar rainin sense ce, wato in directly fad’i mana take mune masu zubin karuwai... Ki dubeta bata wuce cikin cokali ba har tasan ta gaya wa mutane magana....”
“Da kin barni na wawwatsa wa shegiya mari...” cewa Yesmin
“A’a k’yaleta mu sauk’e gaba d’aya kan yayarta... Zo muje...”!Ta k’arashe tana mai janyo hannun Yesmin d’in....

Basma kaw ko saurarensu bata tsaya yi ba ta shige b’angarensu sashen Baffah Ado taje kaiwa ‘yan uwanta rahoto...

Babu ko sallama haka suka banko k’ofar suka shigo, sai faman yatsina fuska suke suna bin mutanen dake zaune verandar da mummunar kallo....
Goggo Laraba k’anwar Baban Mamy ce ta sami zarafin masu magana
“Bayin Allah lafiya, daga ina, wa kuke nema...?” Dattijuwar ta jero masu tambayoyin tana mai dubansu....
“Lafiyar kenan ku jawa Karuwar ‘yarku kunne ta fita daga rayuwar d’an uwanmu wllhi Khalid ko ya rasa mata babu abinda zaiyi da irin wannan gidan...” Cewar Siyama tamkar zata mari tsohuwar...
Gaba d’aya jama’an dake wajen tsananin mamakin rashin ta idon Siyama ya kamasu...
Wata daga gefe tace “Baiwar Allah ki tauna kalamanki ko babu komai zaki daraja furfuran wani ko don a daraja naki...”
“Ke rufe mana baki...!” Yesmin ta katseta... “Matsiyata anga danshi jikin d’an uwanmu ana nema a rab’eshi a dangwali arziki, toh wllhi ko a ‘yar aiki Khalid bazai d’auki wannan kucakar ba....”
Daidai nan Aunty B ta fito daga d’akin yanda suke zaune dasu Nabilah su Zulfa’u tana faman basu baki....
Nabilah taji wasu sabbin k’walla na zubo mata, tabbas tayi gamo da jarababbu wanda sukai karan tsaye wa rayuwarta.... Ace ana karb’an gaisuwar d’iyar ‘yar uwarta ake wannan d’iban albarka duk a ta dalilinta, gaba d’aya sai taji ta kasa daina zuban hawaye zuciyarta na mata zafi sosai...
A fusace ta mik’e ta yunk’ura zata mik’e Marliya tai saurin rik’o hannunta....
Girgiza mata kai tai kana tace “Kada ki fuskancesu Addah Nabila...”
Da raunannun idanunta masu zuban hawaye take duban ‘yar uwar tata kana tace “Shikenan sai na k’yalesu suci mana mutunci Marliya...? Idan rashin mutuncinsu zai tsaya kaina fine, amma bazai yuwu na zuba idanu sucima dangina mutunci ba, what if Addah ta fito daga bayi taji ana wannan zagin d’iban albarkan... Mai kike tunanin zataji bayan rasa d’iyarta da tayi a yau d’in...?” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka zubo mata....

Sosai Marliya ta rik’e hannunta kana tace “Insha Allah

Please Login or Register in order to submit comment