You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
wani irin tsinkewa....
SameenaAleeyou đ
*INDA RAI*
_................DA RABO_
*75*
âWacece ke...?â Kalmar da Raihana taji an fadâi kenan daga dâaya bâangaren... Tamkar wacce aka zabura haka tai zumbur ta ware idanunta, ragowar baccin taji ya watse, lokaci guda ta nemi baccin da takeji ta rasa... Kasa furta komai tayi sai raba idanu da take tamkar mage a tukunya....
Siyama da tuni jikinta ya dâauki rawa sabida tsananin tashin hankali da kishi da suka saukâar mata lokaci guda, cikin wani irin murya mai cikeda kaushi take kuma furta âNace wacece ke...? Sannan mai ya hadâaki da wayar mijina..?!!!â
Jin Siyama ta ambaci wayar mijinta ya kuma sa gaban Raihana fadâuwa, kâirjinta tamkar wacce aka ije mata kâaton dutse... Cikin sauri ta cire wayar daga kunnenta tana duban screen dâin, kâara karanta sunan tai Partner... Da sauri ta rintse idanunta tana mai dafe kanta da jinjna wauta irin tata, sam bata kawo sunanta Partner matarsa ya sakawa ba... Tana jiyowa daga can bâangaren Siyama naci gaba da fadâin hello hello... Bata iya amsata ba sai katse kiran da tayi cikin sauri, ta koma mazauninta da sauri tana mai ci gaba da rarraba idanu don haka kurum muryar matar tasa ya mugun firgitata....
A can kuwa Siyama tsaye ta mikâe tana kuma neman layin Sameer but still baâa dâagawa, kâoluluwan tashin hankali takai, a iya rayuwarta abinda take tsoro ace Sameer ya soma biye biyen mata, a yanda take da muguwar kishin mijinta tabbas tasan zata iya yin komai to keep him all alone for herself.... Aunty Lami ta kafeta da idanu kana ta dâan gyara zama hadâida matsowa kusan Siyama da gaba dâaya bata a hayyacinta kana tace âYa mijin naki....?â
Wani irin duba Siyama ta watsa mata ba tareda tace komai ba....
Aunty Lami ta murmusa, tsaye ta mikâe ta matsoda bakinta saitin kunnen Siyama, cikin sigan radâa take furta âKiyi hattara da ahalin gidan nan suna gab da rabaki da Sameer, amma shawarice idan kin dâauka....â Tana ida fadâin haka ta saki murmushi kana ta fice salin alin.... Kallo Siyama tabita dashi har ta bâace ma ganinta kafin ta fuzar da iska mai zafi...
Muryar wata Dattijuwa ce ya katseta daga duniyar tunanin neman mafitawa rayuwarsu ita da Partner da tai.....
Nabilah na rikâeda Mamani yayinda Mamani taci gaba da dogarawa tana fadâin âWai ina kishiyar tawa takene...? Tinda kishi ya hana ta shigo ta gaidani gani nan ni zan shigo na gaidata da kaina.... Ke Mariya ina kika bâoye min kishiyar tawa ce...?â
Nabilah dake rikâeda ita tana murmusawa take furta âKedai mu shiga daga ciki Mamani kinsan kishiyar taki taci uwar gayu tafiya ma wahala ke mata....â Ta kâarashe maganar sanda take taimakawa Mamani ta zauna saman kujerar gefen Siyama...
Banda huci da tururi Siyama bata komai, sai aikawa Nabilah kallon tsana da take, Nabilah kaw ko ajikinta murmushi ne fal fuskarta....
Gyara zama sosai Mamani tai hadâida kaikaitowa tana fuskantar Siyama, ta kuwa washe baki takai duka hannayenta biyu ta kamo hannayen Siyama, cikeda jin dadâi take furta âAllahu Akbar... Oh ni Halimatu ashe dai rana irinta yau zatazo... Ashe zanga matar Maâaruf kafin na bar duniya... Saura kuma naga dâiyoyinsa.... Sannu kinji âyar nan...â Ta dâanja fasali jin Siyama ta mata dinkim bata amsata ba saima ta mujiya data zuba mata tamkar taga wani halitta daga wani planet....
Juyowa tai ta dubi Nabilah dake kâokâarin kâunshe dariyarta Marliya na girgiza kai wa Nabilar kana Mamani tace âKe Nabilatu Wai bata magana ne...? Kodai kishiyar tawa bihim ce... Ya ina mata magana ta zuba min wannan pici picin idanun nata kaman ni na sammata, wannan badon tsufa danai ba ma nawa idanun sunfi nata girma...â
Ta kâarashe tana mai gwalalo idanunta a fuskar Siyama wacce lamarin Mamani ya soma bata tsoro...
Daga Marliya har Nabilah kasa rikâe dariyarsu sukai...
Mamani ta juyo garesu tana fadâin âKai bani son kâaniya... Ku fadâa min meke faruwa a nan... wacece wannan...? Idan kuma yaren da nake ne bataji kuzo ku mata wanda zataji kafin na tashi na sassabâa maku...!!â
Nabilah tai kâokâarin saita kanta kana tace âMamani kinsan kishiyar taki girman turai ce yawo cikin gajimare kâila dai bata fahimtar abinda kike fadâi ne... Ki canza mata harshe...â
Mamani ta maida dubantaga Siyama wacce ta kasa dâauke idanu daga barin duban Dattijuwar kana tace âAuho kice min dangin nasara Maâaruf ya auro... Ke kaw kinsha bamabam da Haladu yaron arziki... Da kika tashi zuwa cikin danginsa sai ki koyo yaren da suke fahimta... Fiâilin banza da wofi, yo har ni zaâa nunawa yaren jajayen kunne... Ke barikiji na fadâi miki sanda Mammadu na ke raye babu kalan hazon da bai kâetara dani ba... Yo maima kuka samu âyan kâarshen zamani....â
Ganin Mamani ta saki layi ta fara zuba masifa yasa Marliya duban âyar uwarta Nabilah da duniyar tai mata dadâi gamon da takeso Mamani da Siyama, girgiza kai kurum Marliya tai kana tace âMamani Aunty Siyama tana saurarenki kawai dai baki bata dama tayi magana bane tintinin ke kiketa magana tin shigowarki babu ko hutawa..... Kuma zataje gaidaki kenan sai gaki nan kin shigo...â
âKe dalla chan rufe min baki, uwar kinibibi, yo gani zabiya ko mai...? Inyi...?â Tai maganar tana mai tsare Marliya da idanu....
Cikin sauri Nabilah ta kamo Mamani tana fadâin âMamani muje kinji zata shigo har sashenki ta gaisheki idan bata gaisheki a nan ba, wanda zai sata na dole na zuwa....â Ta kâarashe tana mai watsawa Siyama muguwar kallo....
Mamani ta mikâe tana ci gaba da sababi da yabâawa Siyama mugayen maganganu...
Suna tafe sashenta take ci gaba da fadâin âInyi kajimin jaâirar yarinya, yo wannan badon Yayanku yace min âyaruwar Haladu bace sai nace babu abinda ya hadâasa da wannan mai kâirar zabon, Banda Farin fata da dogon hanci banga mai Yayanku ya gani tattareda wannan mai kâirar itacen ba, ko ni nan a haka nafita kyaun gani....â
Nabilah ta gyara mata cushion tanaji Mamanin naci gaba da sababi har ta zauna kana ta umarceta ta nemo wayar salulanta ta kirawo mata Yayansu Maâaruf gashi su Najah sunce shine yaje makaranta ya dâauki Raihanah kuma har yanzu basu dawo ba, ga wannan matar tasa mai suffan karan rake data kuma bâata mata zuciya....
Sake kira Nabilah tai tace da ita wayar bata shiga....
Mamani ta jinjina kai tace âKo wata duniyar yakaimin jika oho.... Kodashike jika na yaron arziki ne bazaiyi wani abu maras kyau ba, Allah sa dai lafiya suke yanda yanzu duniyar tamu ta koma....â
Nabilah ta amsada Ameen dai Mamani, kâila kiran gaggawa akai masa daga can asibitin nasu sai ya wuce da ita....ta kâarada kinason wani abu ne...?â
Dâan dubanta Mamanin tai kana tace âKunna min talabijin na rage takaicin wancan zabuwar matar Yayan taku....â
Dariya ya kusan kufcewa Nabilah, kunna mata TV dâin tai ta silale ta fice don tanaji har lokacin sababi take....
A can parlorn Abbah ma jajen rashin dawowar Sameer dâin da Raihanan suke ga kuma wayarsa da bata shiga, sannan ga matarsa data bayyana wanda sam Sameer dâin bai sanar dasu zuwan nata ba.....
Mamy ta kuma dialing wayar amma bata shiga... Jigum tai tana mai furta âAllah sa dai lafiya suke...â
Abbah dake faman zagaye parlorn hannayensa hardâe a baya iska ya fuzar kana yace âAmma ai koda emergency ne ya taso masa sai ya kira ya sanar damu don kar mu damu, ba ya dâauki yarinya ya tafi da ita...â
Mamy tace âAlhaji Raihanah fah patient dâinsa ce ta yuwu zuwa asibitin da ita ne ya kama shisa ya tafi da ita...â
Abbah yace âWannan duk ba hujja bace....â
Bata kuma cewa komai ba sai sadda kanta kâasa da tai....
Abin magana da bai kasawa a gidan, tuni an soma yayatawa tsakanin sashensu Basma su Sakina, Ya Maâaruf ya dâauki Raihanah daga islamiya baâasan yanda sukaje ba ga matarsa ma nan gidan tana jiransa.... Lami ma tuni tayi waya ta shafawa kâawarta Haule halinda ake ciki.....
Haule kaw tace bataga ta zama ba, dama ya samesu, dole suyi amfani da wannan damar....
Sahariyya da Hajiya ta ida wayar a gabanta bore ta dingayi tana fadâin wllhi sai taci uwar Raihanah muddin bata janye idanunta kan Ya Maâaruf, shegiya kâonanniyar banza....
Najah dai batace uffan ba saima mikâewa da take kâokâarinyi.... Sahariyya ta janyota daga nan yanda take zaune tace âMunafuka hardake kuke hadâe kai da wancan kâonanniyar... Shine dan munafunci ko ki fadâa min shi yaje islamiyar taku ya dâauketa.... Toh wllhi idan zaâa mutu ni ce nan zan aureshi kuma sai na mata iyaka da mijina....â
Najah kallontaâyaruwar tata take kana ta tintsire da dariya tace âAddah Sahariyya kina bani dariya Wllhi, shin duk fah wannan kunfan baki da hura hanci da dâaga jijiyan wuya da kike shifa Ya Maâaruf dâin baima San kinayi ba, kuma ai inaga ba akan Raiha zaki dâaga hankali ba, kan matarsa data iso zaki dâaga hankali, indai Raihanah ce na rantse miki bai dâauketa matsayin komai ba face âyar kâaramar kâanwa kuma patient dâinsa da yai treating dâinta....Ki tada hankali kan Aunty Siyama wacce taji gayu tasha gayu ta kâoshi, ki soma tunanin yanda zakiyi gogawa da ita wajen kishi amma ba Raihanah ba...â Ta kâarashe tana mai janye hannunta hadâida kuma tintsirewa da dariya....
Jikina sanyaye Sahariyya ta sakar mata hannu, tana mai kâarewa kanta kallo maganganun Najah na mata yawo a kwanyarta cewa tai tunanin idan zata gogawa da matarsa wacce take âyar gayu wajen kishi.... Kai dole koda dâingishi ne sai taje taga matar Ya Maâaruf taga kalanta.... Ta dâaga kai tana duban Hajiya dake faman cangwala kâafafu da kâyar tana kuma aza mayafi lokaci guda ta dubi Sahariyyar tace âIdan Alhaji ya dawo kice na tafi can gidan....â Ai bata kai aya ba Sahariyya ta katseta da fadâin âNima zanje Hajiya...â
Haule ta dubeta shekâekâe kana tace âDa wannan kâafar taki da bata ida warkewa ba, idan abin gudu ya biyomu a hanya nayi yaya dake...?â
Sahariyya batako kulata ba ta rarrafa ta dâauko wata sandar gora da Hajiya ke jinginewa bayan kâofa ta dafa tace âWllhi sai naje naga matar tasa naga mai zata nuna min....â
Tsaki kurum Hajiya tai don ta yadda Sahariyya ta gama haukacewa kan Maâaruf, ita batama san a halin yanzu so take ta janye yunkâurin hadâin yaranta da Maâaruf dâin dataso ayi muddin ta sami hanyar salwantar dashi cikin saukâi.... Ko sauraren Hajiya bata kumayi ba ta soma dogarawa tai gaba abinta... Hajiya ta take mata baya cikin cangwala kâafafu itama don dukansu biyu basu warke daga jinyar da suke ba....
Kallo Najah tabisu dashi hadâida girgiza kai tanai masu adduâan shiriya...
Tana zaune Sahariyya ta shigo tana faman kumbure kumbure tana mitan Baba Alhaji ne ya korota yabi Hajiya suka tafi gidan Abbah
Najah dai batace komai ba sai kâunshe dariyarta da tai, Sahariya ta galla mata harara tana fadâin âDariyar mai kike...?â
Najah tace âAllah baki hakâuri ta Ya Maâaruf...â
Wannan suna da Najah ta kira Sahariyya dashi sai taji gaba dâaya bakâin cikinta ya yaye...
***
A can asibiti kuwa tinda ta amsa kiran matarsa mistakenly bata kuma bi takan wayarsa ba, ta matsu baizo sun tafi ba, babu kalan tagumin da batayi ba, alla alla take yazo yakaita gida... Tana nan zaune tana tunanin taji an turo kâofa, muryoyinsu takeji wanda ko baâace ba shida abokin aikinsa ne, tanajin abokin nai masa sallama hadâida masa tinin wani conference na likitoci musamman surgeons da zasu halarta gobe....
shab shikam yama mance da wata Raihanah, har saida ya danno kai cikin Office dâin kafin ya tuna ashe tare sukazo, yai saurin kusto kai cikin Office dâin yana tunanin halinda âyar mutane da ya barta a ciki take....
Aiko tana ganinsa ta mikâe zumbur tamkar wacce aka zabura...
Idanu suka kâurama juna kafin Raihanah tai saurin sadda nata idanun kâasa.... Fuzar da iska ya dâanyi kana yace âSorry na barki jiran office, bansan zan jima haka ba... Aikin ne yazo da complications...â
Cikin sauri ta soma girgiza kai kana tace âAâa babu komai Yaya.... Idanma ka jima ai ceton rai ka tsaya yi, nasan ciwo da radâadâin kâunan wuta wanda bana fata ko makâiyina ne yayi experiencing abinda naji... Da fatan aikin naku ya tafi yanda kuke so....?â
Idanunsa akanta tamkar mai nazari kana ya jinjina kai a hankali yace âIt was successful....â
Yana kallon bakinta yanda take furta âAlhamdulillahâ a hankali....
Kaman babu mai cewa komai cikinsu sai kuma yace âMuje nakaiki gida nasan suma sun damu....â
Tamkar wacce take kan kâaya tai wuf ta nufi kâofa tana mai jinjina kai....
Sameer ya kuma binta da kallo kana ya knarasa table dâinsa ya dâauki wayar salulansa da ya mance nan.... Baiji mamakin ganin tarin kira ba don hakan ne wasu lokuta kan kasancewa dashi idan ya shiga aiki ya mance wayar a kunne... Jefata a ljihu kurum yai kafin ya takewa Raihanah baya ya rufo office dâin....
Suna tafe yana observing dâinta yanda take taka kâafar nata... Sunanta taji ya ambata for the first time wanda ya haifar mata da fadâuwan gaba ta kasa ci gaba da tafiya....
Sameer ya kâaraso bai janye idanunsa daga kâafar nata ba....
âSau nawa Salma ta miki dressing yau..?â Ya tambaya still idanunsa akan kâafar nata wanda ke rufe cikin uniform dâin islamiyarta....
Ba tareda ta dâago ta dubesa ba tace âYau batazo ba dama taje akwai yanda zataje yau dâin bazata samu zuwa ba....â
Jinjina kai yai a hankali kana yace âKenan yau baâai dressing ba...?â
Nanma jinjina masa kai kurum tai still idanunta na kâasa....
Still yai tamkar mai nazari sai kuma yace âBiyoni....â Yai maganar yanabin wata kâofa....
Babu musu ta take masa baya dikda bugu da kâirjinta keyi, tana mai zullumin ina kuma suka nufa...
Dressing room taga an rubuta a kâofar yanda suka nufa, kasancewar dare ne shiyasa babu jamaâa sosai a asibitin, nurses dâinma wanda suke duty basu da yawa kaman na rana, da alama ma babu kowa cikin dâakin.... Offices dâin da suke wajen ya dâan lellekâa ko zai sami wacce zata mata dressing amma shiru bai samu ba...
Ita dai kallon ikon Allah kurum take, tana gani ya isa jikin wasu drawers ya soma dâibo kayan aiki, innalillahi ai nan bugun zuciyar Raihanah ya kâaru, mai Ya Sameer ke kâokâarin yi... Kaman wanda yasan tinanin da take... Idanunsa naga bandage dâin da yake hadâawa yace âTsorona kike...? I can hear your heartbeat.... Donât worry I promise to be gentle....â Ita dai batace komai ba saima kallon hannunsa da take yanda yake shirya kayan dressing dâin... Sameer ya murmusa da gefen bakinsa still idanunsa naga abinda yake yace âNext time idan Salma ta sanar dake bazata sami zuwa ba ki sanar dani right away kinji koh, ya riga ya fara healing idan an bari aiki zai koma baya...â Jinjina masa kai kurum take amma sosai kâirjinta ke bugawa....
Ya dâago idanunsa yana dubanta, sosai tsoro ya wanzu saman fuskarta, idanunta suka kuma firfitowa waje... Tinani take ta yanda zata fara budâe kâafarta gashi kuma wando ne jikinta... Innalillahi itakam balaâin kunyarsa takeji, tsaye yayi yana nazarinta kaman wanda yasan tinanin da take.... Suna a haka muryar Awwab da wata nurse Christian wanda suka fito daga theatre tare ya katsesu... Mamaki ya cika Awwab ganin Sameer a dâakin dressing
âA a Doc you still here, baka tafi ba wai....I thought ka tafi tuntunin.... Wait what are you doing here....?â Sam bai lura da Raihanah dake zaune gefe ba yaketa jerowa Sameer wadâannan tambayoyi...
âKaman muryar Margret naji, ko ba tare kuke ba...? Sameer ya bidâa ba tareda ya amsa dâaya daga cikin tambayoyin Awwab dâin ba....
âEh tare muke sheâs on duty....â Awwab yace yana mai duban Sameer dâin
âAkwai wani abu ne...?â Ya tambaya yana kuma suban Sameer dâin....
Dâan turo baki gaba kadâan yai hadâida duban cikin dâakin yanda Raihanah ke zaune... Le kâasa Awwab yai ya hango Raihanar....
âWhoâs she...?â Awwab ya tambaya yana mai duban Sameer dâin..... Turasa Sameer yai suka fice gaba dâaya yana fadâin âZaka kiramin Margret dâin ne tai mata dressing... Iâve to take this call...â Ya kâarashe yana kâara wayar Abbah a kunnensa
Da fadâa Abbah ya soma masa cewa ina ya dâauki Raihanah ya kaita, ga dare kuma bai sanarda kowa ba....
Sameer ya dâan sosa kâeyarsa kadâan kanshi a kâasa kaman Abban na kallonsa âEm Abbah ai hakâuri, kiran gaggawa na samu daga asibiti, amma gamu a hanya in sha Allah....â
Abbah yace âNaji wannan, matarka kuma fah...? Kasan da zuwanta baka sanar damu ba....?â
Sameer ya ware idanunsa a hankali âAbbah matata kuma...? Kana nufin Siyama tazo gida....?â
Daga dâaya bâangaren Abbah yace âBaka san da zuwan nata ba kenan....?â
Sam baiso iyayensa su fahimci wane irin zama suke da Siyama, kâokâarin saita kansa yai kana yace âOh...Har ta iso kenan... Kuyi hakâuri Abbah ban kawo maku ita da kaina ba amma gani a hanya in sha Allah....â Daga haka sallama sukai da Abban yana mai duban Mamy da tai jigum tana jiran ya ida wayar....
Mamy tace âAsibiti yake koh....?â
Jinjina mata kai kurum Abbah yai kana yace âMariya akwai abinda na fahimta a rayuwar auren yaron nan.... Kaman auren nasa cike yake da tarin matsaloli....â
Ajiyan zuciya Mamy ta saukâe a hankali âNima nayi tunanin hakan tin sanda nai ido biyu da iyalin nasa, kuma bai kawo mana ita duk tsawon lokacin nan ba... Nayi tunanin na tambayesa sai kuma naga ba hurumina bane...â
Jinjina kai Abbah yai a hankali kana yace âWannan hakan matsalarsu tasu ne, ina fata su zamto masu warware matsalolinsu da kawunansu basai wani yaji ba...â
Ta jinjina kai ba tareda ta furta komai ba sai nazarin abin da take....
***
Tsare Akram tai sosai da manyan idanunta tanai masa kallon tuhuma,lokaci guda kuma ta saki murmushi ta mikâe ta nufo yanda yake.... Gefe dashi ta zauna tana wani karkadâa jiki murmushi bai bar saman fuskarta ba....
âAkram Iâm a business woman, sanin kanka ne ban dogara da dukiyar da mijina keda ita ba, inada tawa dukiyar.... Kuma ina mai tabbatar maka I can make you what your boss fails to make you.... Idanma baka son wannan I can offer you something more than that.....â Ta kâarashe tana kashe murya hadâida kashe masa idanu guda....
Mikâewa tsaye yai yana mai murmusawa da gefen bakinsa kana yace âDuk ba sai kinyi wadâannan ba Hajiya, never bazan tabâa cin amanan Excellency irin haka ba, but rest assure auren da mijinki yake nema bazai tabâa yuwa ba.... Here is my plan....â Ziryan ziryan ya zayyano mata yanda abin zai kasance.....
Ta saki murmushin jin dadâi kana tace âWhoâs she... whoâs the girl, sanar dani...â
Nanma murmushin yai da gefen bakinsa kana yace âSanin ko wacece ita to you is not necessary, just trust me, auren bazai tabbata ba....â
Mikâe kâafa guda tai tana mai ci gaba da kadâa kâafar tata take furta âAnd Iâm ever ready to support you financially, duk wani abinda ake bukâata daga lefe zuwa sadaki zan baka kai har gidan da zaka ajeta ni nan zan baka....â
Nanma dai murmushin yai kana yace âKarki damu Hajiya Iâve everything under control, idan bazaki damu ba ni zan wuce....â Ya kâarashe yana mai mikâewa tsaye....
Muhibbah ta kuma sakin shuâumar murmushi kana tace âNaji dadâi da muka kasance on the same page.... And let me remind you this, ka tabbata ka cika alkâawarinka idan ba haka ba, youâll both lose her daga kai har boss dâin naka... Coz when it comes to my husband I can be very dangerous.....â Ta kâarashe murmushi saman fuskarta...
Shidâinma murmushin yake kafin ya dâan tako gabanta kadâan, murmushin bai gushe saman fuskarsa ba hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa na jampa yake furta âYou donât want to have me as an enemy, coz I can expose your little secret... I know exactly the kind of business you run.... So idan baki so mijinki yasan musabbabin yawon kâasashen da matarsa keyi da sunan business trips, kada ki kuskura ki shiga hurumin Zulfaâu...â
Zaro idanu waje tai tana dubansa da tsananin mamaki, ta hadâiyi miyau da kâyar don batai tsammanin Akram zai iya sanin wannan sirri nata da ko danginta basu sani ba...
Bai daina murmushin ba ya furta âJust a piece of advice, do not double cross me...â Daga haka sa kai yai ya fice daga parlorn cikin sauri.....
Muhibbah ta saukâe huci mai zafi ga kanta da ya dâauki chaji lokaci guda... Cikin sauri ta haura sama ta nufi drawer dâinta ta dâauko kâwayar hadâida tsura masa idanu... Lokaci guda ta shiga bâallewa tamkar zararriya haka ta shiga afawa a baki, saida ta afawa kusan hudâu lokaci guda kafin ta zube saman gado hadâida lumshe idanunta....
***
Daga bakin kâofa yaja ya tsaya ganin har Sawwama ta dawo gidan, hularsa a karkace ya hardâe hannaye kâirji hadâida jinginuwa jikin kâofar yana kâare mata kallo, kana ganinshi kasan yau a Hafiz dâinsa ya fito....
Sawwama dake faman goge kayan kallo sam bataji motsin shigowarsa ba har saida ta mikâe zata nufi dâaki nan ta ganshi kâikâam tsaye akanta ya kafeta da idanunsa masu sumar da ita....
Sosai ya mata kyau don tayi kewarsa sosai, tai saurin mikâewa ta nufesa tana mai furta âHafizina bansan kana tafe ba da na girka maka wani abin.... Muje ka kwanta ka huta yanzu zan shiga kitchen na dafo maka abinci mai saukâi, kar ka damu Magajiya ta hadâoni da duk wani abin bukâata....â Kasa kâarashe maganan nata tai jin ko motsasa daga yanda yake ta kasa... Ta dâago tana dubansa da mamaki, ta dâan saki murmushi kadâan....
âLafiya dai Hafizina...?â
âUwarki ne ba lafiya...â
Kalmar data sinkaya kenan daga bakin Hafiz, gabanta ya yanke ya fadâi... Sai yanzu ta tuna babu wani shirin asiri data dawo dashi gidan.....
Ta saki murmushin yakâe âHaba Hafizina na riga na baka hakâuri, nasan muna son junanmu.... Mu baiwa maras dâa kunya muci gaba da zaman aurenmu, nai maka alkâawarin duk wasu abubuwa marassa kyau da nake a baya na dainasu daga yanzu, zan kula dakai yanda baka tsammani Hafizina....â Ta kâarashe tana marairaicewa.....
Tamkar wanda ya tina wani abin ya murmusa da gefen bakinsa, ta gefenta ya rabâa ya shige cikin dâajin yana wani faman kâobarewa.....
Sawwama ta bisa da kallo dikda cewa tasha jinin jikinta da ganin yanayin Hafiz dâin.......
***
A can gidan Abbah kuwa a parlorn Abban Mamani ta ritsa Sameer da iyayensa, ta yanda take shiga bata nan take fita ba, fadâi take âInyi toh Wllhi sam bazata saku ba, wannan ai gubace ba macen zaman aure ba, ni nasan irin wannan matan barikin sam ba kunya bace dasu.....â
Baba Alhaji ya tari zancen da fadâin âHajiya ni dama na gama magana ga kâanwarsa Sahariyya zaune gida babu miji kawai sai a hadâa aurensu don bazamu zuba idanu wannan yarinya da ya auro matsayin mata ta rainamu ba kuma Mamani ina mai tabbatar miki wannan yarinya da kike gani zata iya rabaki da jikanki a karo na biyu, tun kafin abin yakai nan mu aura masa ta gida kinga mun dâauresa....â
Abbah duban Baba Alhaji kurum yai hadâida girgiza kai, yayinda Mamy ta kasa furta koda kalma guda, har lokacin kanta na kâasa...
Sameer dâago kansa yai yana duban wan mahaifin nasa da tsananin mamaki.... A hankali ya furta âBaba ku bani dama nayi magana da Siyama please...â
Mamani ta katsesa da fadâin âYo wani dama, wannan batu naka yayi daidai Alkâali, yanzu basai anjima ba a soma shirye shiryen biki....â
Abbah ya dâanyi gyaran murya kana yace âAmma Yaya, Mamani bawai nakâi maku bane wannan hadâI, kaman yanda Maâaruf ya bukâata a basa dama yayi magana da iyalin nasa... Sannan Yaya baku tunanin abinda ya faru damu baya gameda hadâin Hafiz da Zulfaâu ya maimaita kansa... Ni dai a ganina da an janye wannan batu...â
Haba nan fah Baba Alhaji ya soma kumfan baki yana fadâin âToh kinji koh, Mamani... Kinji abinda dâanki yake fadâi koh, a kullum anaso mutum ya kasance mai kyakkyawan zato amma banda Usman... Minene aibun yara na... Maiyasa zai dinga dawo da abinda ya riga ya wuce....Idan har haka ne wannan ya kuma tabbatar min bai dâaukeni matsayin dâanuwa ba kuma wanda yake gaba dashi... Na tabbata da ace dâaya daga cikin yaran Ado ko Wada ne tsaf zai amince amma dashike dâiyata ce shiyasa zai nuna kâyamarsa... Tinda haka ne ni na cire kaina da ahalina daga wannan zuriâa... Usman daga rana mai kaman ta yau ka mance kanada Dâanuwa mai irin sunana...!â Daga haka yasa kai zai fice...
Mamani dake hawaye tai saurin tare gabanshi tana fadâin âShin sai na mutu ne ku sami jituwa tsakaninku...? Shin bazaku mance komai ku rikâe âyanuwantakarku ba.... Shin kuna tunanin mahaifinku dake kwance a kâasa zaiji dadâi da ace zaâa tayar dashi a nuna masa yaransa sun
Book Chapters
Chapter 40
Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76