Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halina ba wllhi, fitsararriya kawai mai halin uwarta...”

Daga parlor yanda Sakina ke zaune banda dariya bata komai bud’e murya tayi kana tace “Ai sunanki da aka saka mata yasata biyo halinki Mamani...”

“Kai waye a wajen nan maras kunya masu halin iyayensu mata...”

Kafin ta fito Sakina ta mik’e ta fice tana ci gaba da dariya, sauri sauri ta nufi sashensu kai rahoto wa mahaifiyarta Karima matan Baffah Wali....

***


*Kaduna*

A gajjiye ta shigo gidan jaka a hannu mayafi a hannu dogon takalminta a hannu, cikin kasaltacciyar murya take kwad’a masa kira don taga motarsa a parking lot hakan ya tabbatar mata yana gida...

“Partner..! Partner...!! I’m home, where are you....”

“Yes honey I’m here...” Ya amsata daga yanda yake...

B’angaren da tajiyo muryar nasa ta nufa bayan ta zuba tarkacan hannunta a parlor....

Tsaye ta gansa bakin gass cooker yana juya sausage cikin pan ga bread da fresh lettuce a gefe alamun sandwich zai had’a....

Rungumesa ta baya tayi tana fad’in “Umm it smell delicious Partner, ayi sauri a bani naci I’m starving already...” Ta k’arashe tana d’ora hab’arta bisa kafad’arsa....

Murmushi yake yana ci gaba da zuba sausage d’in cikin plate kana yace “Partner kinsan wannan aikinki ne kawai karambani nake maki, don haka zo ki k’arasa ki samu ladanki...”

Turo baki tayi had’ida dad’a matseshi kana tace “But you know I’m not a good cook Partner...”

Juyowa yayi yana dubanta kafin ya d’anja hancinta yace “My wife can’t cook but she can run a company.... Am I right...?”

Jinjina masa kai tayi kana tace “Exactly Partner.... Muje muci before it get cold....”

Bata jira cewansa ba ta soma d’aukan abincin zuwa dining table...

Misalin k’arfe goma da rabi sun gama duk wasu d’abi’unsu da suke kafin suyi bacci tuni ta haye saman gado ba tareda jiran Partner d’in nata ba, dubanta kurum yayi had’ida murmusawa kafin ya jawo computer d’insa ya shiga mail d’insa yana duba abinda yake tsammani... Aiko nan yaga sak’on ya shigo... A hankali ya rintse idanu had’ida sauk’e ajiyan zuciya... Rufe computer d’in yayi kafin ya k’arasa saman gadon yanda Siyama ke kwance tana duba sak’wannin da suka shigo mata a wastapp sai faman hamma take alamun bacci da gajjiya...

Ta bayanta yasa hannayensa ya rungumota kafin ya zame wayar nata a hankali yana fad’in “Partner this is my time a ajiye wannan saida safe kuma....”

Cikin kasaltacciyar murya take fad’in “Partner what are you doing, I’m exhausted please...”

Matseta yayi kana yace “Okay maybe some little massage may help... wouldn’t they....? Or may be some kisses may help too....”

Kukan shagwab’a ta soma masa tana turesa jin abinda yake mata tana fad’in “Partner no.... let go please, not now.. I know exactly what you’re up to....” Rufe bakinta yayi da sumba kafin ya kashe masu side lamp...



*SameenaAleeyou📚*
[25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_.................DA RABO_



*05*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Tafe suke cikin farfajiyan asibitin ko wannensu cikin shiga irinta k’wararrun likitoci, hannayensu rik’eda wasu ‘yan kofi da sukafi kamada disposable saman wasu ‘yan k’anan plates, shakka babu coffee ne ciki kasancewar safiya ce lokacin....

Wajene mai kunshe da mutane wanda yafi kamada a kirasa Cafeteria, can wani table suka nufa suka zauna yayinda wasu nurses ke mik’a masu gaisuwa, Sultan ne kawai mai iya amsawa shi kuwa Sameer saidai ya jinjina kai alamun amsawa...

Hannu Sultan ya nad’e yana duban abokin nasa wanda gaba d’aya yau d’in bai gane masa ba, a hankali ya d’au coffee d’insa yana kurb’a ba tareda ya d’aga idanunsa daga duban Sameer d’in ba, ko ba’a fad’a maka ba yana cikin damuwa da tashin hankali...

Sultan ya d’anyi gyaran murya kana yace “Are you sure you’re alright Sameer, it’s obvious you’re not yourself.... Wai meke faruwa ne.....?”

Sauk’e ajiyan zuciya Sameer yayi kana yace “Sultan I don’t know how to break the news to her, sanin kanka ne I only have a week left here, to be honest with you banason transfer d’in nan domin hakan na nufin rayuwata tana shirin canzawa completely....”

Murmushi Sultan yayi had’ida girgiza kai kana yace “Nasan haka zai faru abokina, bazaka iya tafiya kabar Partner ba koh...?”

Murmushi Sameer yayi da gefen bakinsa kana yace “Ka sani kuma kake tambaya.... Sultan wannan transfer d’in is a disaster to me....” Ya k’arashe yana kurb’an coffee d’insa....

Sultan ya kuma murmusawa kana yace “So tari nakanyi tunanin wane irin so kakewa Siyama... Anya kuwa Sameer wannan nuna soyayya da kulawa taka batai yawa....?”

D’ago idanu Sameer yayi yana duban Sultan kana yace “I love her with all my heart... Bazaka fahimci mai nake fad’i ba sai ka had’u da wacce kake so irin haka....”

Sultan yayi tak’aitaccen murmushi kana yace “Banji akwai wacce zan mata irin wannan soyayyan Sameer, nifah a ra’ayina soyayya duk k’aryace kuma ina maka tsoron watarana da zaka yarda da maganata cewa babu komai cikinta face k’arya da yaudara....”

K’uri Sameer ya masa kafin ya girgiza kai yace “Nida Partner hakan bazai tab’a faruwa damu ba cos we’re Magnets shiyasa nake tunanin transfer d’in nan ka iya kawo tashin hankali ma rayuwata...”

Sauk’e ajiyan zuciya Sultan yayi kana yace “Dr kenan, kai bama tunanin iyayenka da basuda wani d’a kake ba sai Siyama... Besides Kano da Kaduna ai bakida hanci ne idan kaga dama duk bayan kwana biyu kana hanya...”

Girgiza kai Sameer yayi kana yace “Ba kaman idan ina nan ko yaushe ba, nidai gaskiyar magana bud’e sabon asibitin k’una da gwamnatin tarayya tayi a jihar Kano baimin ba...”

Dariya ya kufcewa Sultan kana yace “Haba Sameer nasanka da son taimakon al’umma wannan asibiti da aka bud’e ai sabida al’umma aka bud’eta kuma wayasan d’imbin burn victims da zaka taimaka a jihar Kano, tun had’uwata dakai nasanka mutum ne mai k’aunar aikinsa ba don komai ba sai don ganin ka taimaki al’umma so please kar ka bari wannan k’udirin naka ya gushe akan soyayyar da kakewa matarka don na tabbata itama bazataso hakan ba....”

A hankali Sameer ya sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da iska kafin wata speaker ta soma announcing ana neman Dr Sultan da Dr Sameer sakamakon kawo wata budurwa da akayi k’unan wuta ya mata babu dad’i....

Cikin sauri suka mik’e suka nufi bakin aikinsu don ceton ran wannan budurwa....

****

*Kano*


Shi kad’ai sai wani cika yake yana batsewa, tun bayan gaisuwarta da ya amsa bai kuma bi takanta balle karin kummalon data had’a masa, kallon arziki bata ishesa ba ya k’arashe saka cuff links d’insa, sanin ba magana zai mata ba ko zasu kwana a haka ya sanyata bud’e baki tace “Fita zakayi baka karya ba...?”

Da wutsiyar idanu ya dubi sashen da take kana ya kuma kauda kansa, wani k’atutun bak’in ciki ya tokari k’ahon zuciyar Zulfa’u, wato shiru ma amsa ne.....

K’ok’arin shanye wannan bak’in cikin tayi kana ta kuma yin k’asa da murya tace “Abban Khausar magana fah nake maka...”

A hasale ya maidoda dubansa gareta yana mai darara mata tsawa “Wai meyasa bakida hankaline Zulfah, idan zanci sai nace miki zanci ne, idan nayi ra’ayin ci basai kinmin tuni ba, ko kinfi son cikina ne...? Abincinki ne yau banyi ra’ayin cinsa ba, sai ki ajiye kiyita cinsa har dare don bazan lamunci ayita min almubazzaranci da abincin gida ba....”

Hawaye suka ciko idanunta, tayi k’ok’arin maidasu kana ta bisa da “A dawo lafiya....”

Nan ma bai amsata ba yasa kai ya shige, har ya fice ya dawo da baya yace “Ki tabbata kinje kin baiwa Hajiya hak’uri kafin na dawo....”

Cikin hawaye ta jinjina masa kai yana ficewa kuwa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya domin kuwa tanajin sanda wayarsa tayi k’ara ya d’aga yana sanar da budurwarsa gashi nan tafe a ajiye masa favorite d’insa... Da shike budurwar tasa d’iyar Hajiya Magajiya ce wata mai restaurant a can bayan layinsu, babu yanda Zulfah batayi ba ya rabu da Sawwama d’iyar Magajiya tinda kowa yasan halinta shashasha ce ballagaza maras kamun kai amma yak’i saurarenta, k’arshema mugun kashedi ya kafa mata akan alak’arsa da Sawwama, takai ta kawo Sawwama har nunata suke suna dariya idan tazo zata wuce bakin shagon mahaifiyarta...

Babu yanda Nabilah bataida Zulfah ba kan ta bartada Sawwama zatai maganinta amma fir Zulfah ta hanata shiga maganar, hakan bashike hana Nabilah yab’a masu magana ba muddin tazo wuce k’ofar restaurant d’in....

***

Hajiya na zaune saman tabarma a faranda Khausar na kwance gefenta tana bacci don tunda Raihanah ta goyata take bacci, zab’en safe da ake a gidan radio k’arfe goma shad’aya take sauraro Zulfa’u tayi sallama....

Da gangan Hajiya ta k’ure sautin radio d’inta, jin ba’a amsata ba ya sata k’ara d’an bud’e murya tana kuma sallaman haba nan fah Hajiya ta hayyayak’ota da ruwan masifa don dama ta d’ago muryar nata... “Shegen iyayi da munfurcin banza, an amsa miki bawai ba’a masa ba amma sai nanatawa kike yawa biya karatu... Munafuncin banza kawai...”

Hayaniyar Hajiya ya d’aga Khausar....

Tinda ta soma bala’i kan Zulfah na k’asa, da k’yar ta iya furta “Kiyi hak’uri Hajiya....”

Aiko Khausar najin muryar mahaifiyarta ta nufeta a guje tana mai ci gaba da kuka saidai kafin ta isa Zulfah dake duban d’iyar tata cikin shauk’i da bege tuni Sahariyya da fitowarta kenan daga d’aki don ayi da ita dashike taji zuwan Zulfah, tuni tayi tsalle ta sure Khausar dake kuka tana fad’in “Bazakije ba anan ake koyamiki munafunci.....”

Zulfa’u batasan sanda ta mik’e ta nufi Sahariyya ba sabida tsananin k’una da rad’ad’i da zuciyarta ke mata.... Fincike d’iyarta tayi tana mai furta “Sahariyya kinyi kad’an ki rabani da d’iyata.... Zan lamunci duk wani cin zarafi da zaku min amma banda d’iyata....”

Khausar kuwa tuni ta kwanta cikin jikin Mamanta tana shan zuciya a hankali....

Hajiya da tuni ta saki baki tana kallon ikon Allah mik’ewa tayi had’ida rangad’a gud’a “Eh lallai Zulfa’u kin rik’a kin cika cikakkiya, bari kiji na fad’a miki idan kin mance, Sahariyya tafiki iko da yarinyar nan tunda k’anwar Ubantace, yo aurenki ko mutuwa yayi ba baki Khausar za’ayi ba Sahariyya kuwa za’a mallaka mata Khausar domin kuwa Ubanta ma ita yasha nono ya sake.... Ke Sahariyya karb’i yarinyar nan idan ta cika ta kuma fizgeta.....” Hajiya ta k’arashe tana dukan k’irji alamun fad’a...

Zulfah tanaji tana gani Sahariyya ta fincike Khausar daga hannunta, yarinyar sai kuka take sabida tsananin tsoron Sahariyya da take tamkar zata shid’e lokaci guda kuwa Sahariyyan ke darara mata tsawa wai tayi shiru gaban mahaifiyarta....

Wasu irin hawaye masu d’umi su suka shiga gangarowa Zulfah, batasan sanda ta cukwikuye fuskarta gaba d’aya da hijabinta ba ta fice tana mai jiyo sautin kukan Khausar har cikin k’ahon zuciyarta da yanda Sahariyya ke darara mata tsawa tana fad’in kalaman b’atacin akan Zulfah....

Raiha dake kitchen tana girki ta window take duban Aunty Zulfah har ta fice ga kukan Khausar na tashi, tuni Raiha taji hawaye na gangaro mata, kaman wanda aka turo Hajiya kitchen d’in nan ta hangi Raiha na kuka ga abinci bisa murhu da alama tayi nisa cikin kukan ta bar abinci har ya soma k’auri....

Bata ankara ba batasan da shigowar Hajiya ba sai sauk’an Dundu masu ji da lafiya har guda uku dataji a bayanta....

Raiha ya mik’e a d’ari tana kurma ihu.... Hajiya ta rarumo muciya tana fad’in “Dan ubanki sai na dakeki kiyi kukan da dalili, shegiya munafuka wato salon akai abincin nawa Kasuwa ma Alhaji aji babu dad’i koh... Munafuka algunguma... Wuce ki duba min girki kafin nayi k’asa k’asa dake a nan.....”

Raiha ya shige tana hawaye, Sahariyya dake tsaye bakin kitchen fad’i take “Ai Hajiya da buga mata muciyar kikayi sai ta fad’i uwar da aka mata take kuka...”

Hajiya tace “An b’ata ran uwarta Zulfa’u ta fice tana kuka mana, basu ragema juna komai ba tsinannu munafukai...”

Sahariyya ta k’arada “Wllhi kuwa Hajiya ni dama har kama suke min....”

Jifa Hajiya tayi da muciyar tana mai ci gaba da sababi, Sahariyya ta take mata baya.....


***

Kaman daga sama Sawwama da k’awayenta suka hango Zulfah na tafe fuskarta duk ta dauje alamun taci kuka, idanunta a kod’e...

Sawwama tayi shewa tana jiran k’arasowarta duk a tunaninta akan Hafiz take kukan da shike bai jima da barin Kantinsu ba...

Sawwama ta tab’a k’awayenta suka nufi Zulfah


SameenaAleeyou📚
[25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_................DA RABO_




*06*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*






Kallo guda Zulfah ta masu ta watsar, lokaci guda taji wani k’arfin zuciya yazo mata, tabbas batada lokacin Sawwama balle na k’awayenta, kai tsaye tasa kai zata rab’a ta gefensu ta shige dashike tuni sun tare gabanta...

A tare Sawwama da k’awayenta Sailuba da Zabba’u suka kuma shan gaban Zulfah, sai faman cika Sawwama take tana wani batsewa....

K’ak’aro murmushin k’arfin hali Zulfah tayi kana tace “Bansan kuna biyo mutane har titi ku sanyasu sayen abincinku na dole ba tunda dai naga wannan hanyar wucewace ba kantinku na nufa ba....”

A tare su Sawwama suka kwashe da wata irin shewa had’ida tafe hannaye kana Sailuba tace “Ai munfi k’arfin mu taro mutane saidai su kawo kansu tinda mijin wata ya kawo kansa.....”

Zabba’u tace “Fad’a mata dai k’awata....”

Itako uwar gayyar sai faman jijjiga take tana famkan fankam....

Har cikin ranta taji zafin kalaman Sailuba amma sai ta daure ta murmusa don bataso su gano lagonta... A fili kuwa cewa tayi “Alama ta nuna haka, ko shakka babu mijin wata ku kuka rok’eshi yaci abinci a kantinku amma ba ra’ayinsa bane, sannan ko kad’an banga laifinku ba don kun ara kun yafa domin kuwa abinci kuke nema ku saka a bakin salati wanda baku samu gidan iyaye ba....”

Haba nan fah Sailuba ta harzuk’a, ta yunk’ura zatayo kan Zulfah Sawwama tayi saurin tareta kana tace “Kan me zaki b’ata hannunki, ita tasan wanda zai mata lilis kan wannan magana data furta.... Karki mance a gabanki ya labarta min irin wulak’anci da ya mata itada abincin data girka kafin ya fito kuma kisha kuruminki don yanzu zan kirasa na zayyane masa komai idan ta koma gida sa wanye....” Ta kuma maido da dubanta ga Zulfah kana taci gaba da fad’in “Sunan matarsa kawai kike amma sanin kanki ne Hafiz nawa ne ni kad’ai sai yanda nayi dashi, idan nice ke zan sallamasa na daina fad’a da kishi akansa domin kuwa darajar iyayenku kawai kikaci kike zaune gidansa....”

Izuwa lokacin zuciyar Zulfah ta soma rauni amma ta daure ta murmusa kana tace “Ashe dai inada sunan matar tasa, kuma ko sau goma zan girka abinci baici ba inada lada wajen ubangijina domin kuwa bautarsa nake ba kaman wacce take bautan gardi da babu d’igon lada cikinta ba.... Sannan Alhamdulillah da har nakeda mahaifa na k’warai da zanci darajarsu suka killaceni gidan aure ba kaman wanda aka awatsarsu bakin kwalta suna bautan k’artin banza ba....”

Haba izuwa wannan lokaci Sawwama takai bango banda huci bata komai, tuni ta yaye d’ankwalinta bakin kwalta tana bugan k’irji da zubo nau’i nau’in ashariya tana fad’in a barta ta daki Zulfah... Tuni Zulfah ta wuce don batada lokacin Sawwama ga jama’a da suka soma taruwa ba mutuncinta bane a ganta bakin layi tana dambe....

Su Sailuba sai rik’o Sawwama suke suna bata hak’uri inaa sai ashariya da hauka take bakin layi, kan kace mai ta koma restaurant d’insu a guje ta d’au waya tana neman layin Hafiz....

***

A farfajiyan gidan ta hango Nabila na karatun jarabawa, Sadiya d’iyar Baffah Wali na gefe tana shanya, sam Nabila bataji tab’a gate ba tayi nisa wajen solving equation saida taji muryan Sadiya na gaida Zulfah....

Da mamaki Nabila ke kallon Zulfah yanda fuskarta ta kod’e, ko ba’a fad’a mata ba watsettsen mijin nan nata ko shegun danginsa ne suka mata wulak’ancin da suka saba.... Tattara handouts d’inta da kayan karatunta tayi ta nufi ‘yar uwarta wacce tana k’arasowa ta rungume Nabilan sai kuma ta fashe da wani irin kuka...

Su Sadiya an samu nakai rahoto tuni tabar shanyar da take ta kafesu data mujiya.... Ganin haka ya sanya Nabila saurin janye ‘yar uwarta suka nufi cikin gida don tasan halin ‘yan gidan nasu... Tuni Sadiya ta nufi sashensu kai rahoto....

Aunty Lami da fitowarta kenan daga sashen Abbah ta hangi Zulfah da Nabilah rungume da juna sun shige.... Cikin sauri ta sad’ad’a ta soma binsu a baya, d’akinsu Nabilah suka shige ba tareda sun nufi d’akin Mamy ba...

Aunty Lami tanaji tana gani aka gark’ame k’ofa alamun bazataji komai ba.... Badon taso ba ta wuce sashenta tana neman layin aminiyarta ta sirri....


Cikin hawaye Zulfah ke duban Nabilah kana taci gaba da fad’in “Nabilah na gaji na gaji, I’m giving up.... Bazan iya ba wllhi na gaji da rayuwar k’unci da nake a garin nan, na gaji da auren Hafiz danginsa budurwarsa ga kuma tsangwaman Mamani, gwara na koma Rano wajen kawunaina... Nabilah wllhi I’m tired.....” Ta k’arashe cikin tsananin kuka da rawar murya...

Nabilah da zuciyarta ke faman tafarfasa hannayen ‘yar uwarta ta rik’e kana tace “Addah wllhi ni shaidace kinyi iyaka hak’urin da zakiyi da wad’annan azzaluman mutane, Addah duk hukuncin da kika yanke bazanga laifinki ba, amma Addah Kausar nake jiyewa idan kika tafi rayuwartace zata shiga garari wajen azzaluman nan mussaman idan Ya Hafiz ya auro wannan shegiyar Sawwamar mai zubin zabuwa... Addah kece mai ragar masu nasha fad’a miki duk shegen da ya miki karkiji shayin mayar masa koda Hajiyan Yaya Hafiz ne tinda bata rik’e girmanta ba, ke wllhi baki ragewa Mamy komai ba sai kuyi shiru ayita cutanku ana danne maku hakki, wllhi wanke idanunki zakiyi kici uban duk wanda ya shiga rayuwarki hakan ne kawai zaki samu peace kuma wllhi ko Mamani bance ki ragar mata....”

Duk maganganun da Nabila keyi Mamy na tsaye bakin k’ofa tana saurarensu.... Bata ankara ba sai sauk’an rank’washi dataji a tsakar kanta...

Gaba d’aya suka d’ago suna duban Mamy da babu walwala saman fuskrta, Nabilah na faman sosa kanta dake mata zogi take fad’in “Haba Mamy daga fad’in gaskiya...”

Dak’uwa Mamy ta mata kana tace “Kinci gidanku da fad’in gaskiyar, wawiyar banza, a hakan ne zakici ribar duniya... Tashi ki bani waje baki ragarwa Bara’atu komai ba wannan, wajenta kika gado mugun hali.....”

Nabila ta mik’e tana ture turen baki ta nufi k’ofa tana ci gaba da fad’in “Shikenan Mamy sai muyita zuba masu ido wllhi Allah Mamy ni gaskiya ki daina irin haka...”

“Zakimin shiru ki fice ko sai nazo wajen na k’ara miki, sakarya kawai... Allah dai ya shiryaki.... Ki fice ki rufe mana k’ofa dama...”

Jawo k’ofar Nabilah tayi had’ida yin k’wafa ji take kaman ta shige gidan Baffah Alhaji ta surfa masu rashin mutunci ko taji sanyi....

***

Zama Khalid yayi a kujera mai kallon nata kana yace “Siyaam please magana fah nake....”

Harara ta kuma galla masa had’ida ture files d’in gabanta gefe kana tace “First of all stop calling me Siyaam don mutum d’ayane ke kirana da wannan sunan... Secondly, I’m not signing anything cos I’m pretty sure wasu kud’ad’e kake nema kaje ka had’a party na shashanci kaman yanda ka saba da ‘yanmatan ka... Tun muna saida juna kindly leave my office kafin na kira Daddy na sanar dashi exactly what you’re up to...”

“There you go Sis, you’re hallucinating again.... Ke ko yaushe tunaninki negative, for crying out loud Siyama I don’t even have a girlfriend, please please sister I need you to sign this....” Ya k’arashe yana kashe mata murya

D’aukan takardar tayi tana dubawa kaman zatayi signing d’in Khalid har ya soma murna yana gwad’ata saiji yayi ta watsa masa kayansa a tsakarka tana fad’in “You know what little bro, get out of my office right now... Kun saba kaida Daddy I won’t allow you to drag me into this, oya tashi ka fita bada sa hannuna ba....”

Harara ya watsa mata kana yace “You know.... That’s why I hate you, kuma idan baki sani ba ki sani anyiwa Sameer transfer zuwa wani state d’in, kuma In sha Allah sanadin k’uncinki kenan....” Ya k’arashe yana mata muguwar murmushi...

Sakare ta tsaya kalaman na mata yawo a kwanya, Partner d’inta kai badai Partner ba.... Kai no never babu abinda zai nisantasu... Toh ya akai bai ma fad’a mata ba....

Bata ida tunanin ba wayarta ta soma ringing....

Sunan Partner shine ya bayyana saman screen d’in... Ta jima tana duban screen d’in kafin ta zauna saman kujerarta da k’yar...

Jiki babu laka tai sliding had’ida amsa kiran...

Daga d’aya b’angaren Sameer yace “Hello Partner... Ya kike ya aiki, I can imagine you’re tired already... Can we have lunch together..? .... I’ve something important to tell you... Allah sa bakida aiki sosai....”

Jiki a sanyaye tace “No no banida aiki....”

Jinjina kai yayi kana yace “Good, I’ll pick you up then.... I love you..”

Bai jira cewarta ba ya kashe...

Siyama tayi k’urima wayar tana tunanin da gaske Partner zai iya tafiya wata gari ya barta......

***

Misalin k’arfe biyu da wasu dak’ik’ai Sameer ya iso company d’in, kai tsaye office d’in matarsa ya nufa yayinda sakatariyar tata ta shiga gaishesa ba tareda ta masa sha mak’i da shiga ofishin ba sanin matsayinsa wajen Siyama...

Tsaye take jikin drawers na takardu tana duba wasu documents d’in sanda ya turo k’ofa a hankali ya shigo, riga da skirt ne a jikinta ya zauna d’amas wanda hakan ya kuma bayyana kykkyawar surarta... A hankali Sameer ya lumshe idanu yana mai shak’an k’amshin matarsa da ya kama ofishin, cikin taku da yafi kamada sand’a ya isa ya rungumeta ta baya... A tare su duka biyun suka lumshe idanu cikeda begen juna....

A hankali Siyama ta furta “Part-ner.......”


v

SameenaAleeyou 📚
[25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_...............DA RABO_



*07*





*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Har bakin gate Mamy ta rakota bata daina bata baki ba da nusar da ita ribar hak’uri a rayuwar zaman duniya....

Har cikin ranta Zulfah taji dad’in yanda mahaifiyar nata ta kwantar mata da hankali sai taji gaba d’aya damuwar da take ciki Allah ya yaye mata shi, Mamy ta umarceta ta koma gidanta kuma ta kwantar da hankalinta, da wannan tattaunawa tsakaninsu da Mamy Zulfah ta nufi gida....

Fitowarta daga layin kad’an taga sai manne unguwar ake da sabbin posters na Mutallab, batasan sanda ta saki murmushi ba tana addu’an Allah ya baiwa Mutallab sa’a a zab’en da za’ayi na Gwamnoni mai zuwa domin kuwa Mutallab mutumin mutane ne, mutum ne tuntuni mai taimakon Al’umma, yanada foundations da dama na taimaka ma gajiyayyu marayu musakai da sauransu, tun bayaso ya bayyana kansa har saida al’umma suka fito dashi Allah kuma ya bayyanashi.... Da yawan mutane sabida wannan taimakon nasa ke tsananin k’aunarsa da fatan ya k’arbi ragamar mulki a zab’e mai zuwa da za’ayi, wasu kuwa sabida tsananin kyaun halitta da Allah ya masa suke k’aunarsa bugu da k’ari matashi ne mai jini a jika domin kuwa a shekarunsa ta 40 yake, cikin ‘yan takara masu neman muk’amin kujeran governor kaf babu mai k’arancin shekarunsa... Wannan dalili yasa MUTALLAB yayi k’aurin suna duk yanda ka wuce hotunansa ke shawagi, Zulfah tana d’aya daga cikin magoya bayan Mutallab domin kuwa tanaji a cikin zuciyarta irinsu Mutallab suke kawo sauyi da ci gaban k’asa dama al’umma gaba d’aya...

Murmushi tayi ganin yanda matasan keta aikin lik’a sabbin hotunansa kana ta tare adaidaita ta shige....

***


Hannayenta ya kamo bayan sun gama cin abincin, shinema ya d’an tab’a abincin Siyama kam cakalawa kawai tayi ta bari, ta k’agu taji maganar da Partner ke son sanar da ita shid’inma ya lura da hakan....

“Partner, gameda maganar da nakeso na sanar dake....”

Ido ta d’ago tana dubansa kana tace “About your transfer....”

Da mamaki yake dubanta yaya akayi ta sani....

Murmushi tayi kana tace “Kana mamaki na sani koh....?”

Gira ya d’aga mata cikeda mamaki....

Siyama ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “I just found about it, Khalid ke sanar dani d’azu a office... Partner I thought ni ce ya kamata na soma sani...” Ta k’arashe tamkar zatayi kuka....

Shafe goshinsa ya d’anyi kana yace “I’m sorry Partner, and believe me I was about to tell you bansan ya akai Khalid ya sani ba har ya sanar dake, or maybe Daddy na tareda Uncle nake sanar dashi d’azu, so probably Khalid was there too... Honey I’m so sorry ba haka naso ta kasance ba kinji....” Ya k’arashe cikin sigan lallashi....

Murmushi ta d’anyi kana tace “Shikenan Partner na yarda dakai but ban sani ba idan zan iya rayuwa ba tareda kai ba...”

Girgiza kai yayi kana yace “No Partner ba rabuwa zamuyi ta har abada ba, besides Kaduna da Kano bakida hancine, please karma ki saka wata damuwa ma ranki cos duk yanda zanje soyayyarki bazai tab’a canzawa ba koda zamuyi shekaru bamu tare I’ll still be the same Sameer that fell in love with you kinji koh....”

Murmusawa ta kumayi kana tace “So I shouldn’t worry...?”

Ya kuma kamo hannayenta cikin nasa kana yace “Sameer is all yours, you and only you...”

Kasa daina duban kyakkyawan fuskarsa tayi kana tace “Ancemin matan kano sun iya k’wacen miji so

Please Login or Register in order to submit comment