Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d’aukansa sai sabbin k’walla da yaji suna neman ciko idanunsa...

Marliya takai dubantaga yanda Zulfa’u ke duba ganin ta kasa ci gaba da tafiya... Ganin Ya Hafiz ne ya sata k’ok’arin juyawa da zummar komawa cikin gida amma saidai tuni Zulfa’u ta janyo hannunta sun shige cikin parlorn yanda suka bar Hafiz nan tsaye tamkar wanda ruwa ya shanye....


SameenaAleeyou📚



*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*53*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Marliya ce ta fara yin sallama Zulfa’u na biyeda ita, muryar da ta daki dodon kunnuwan Akram sai yaji tamkar wacce yake saurare a gidan radio, d’ago idanu yai yana duban k’ofan wanda ya sanyasa yin idanu hud’u da mai sallaman domin kaw itama Marliyan su take duba idan ka d’auke Zulfa’u da kanta ke k’asa...

Cikin sauri Hafiz ya take masu baya, bai shiga parlorn ba sai tsayawa da yayi daga bakin k’ofa yana jiyo abindake wakana, haka kurum yaji zuciyarsa sam bai kwanta masa dasu Akram ba musamman da yaga irin wankan shadda da hula da suka zuba....

Bayan sun gaisane Zulfa’u ke fad’in “Saidai ban gane daga ina bane...”

Yusuf ya d’anyi gyaran murya bayan Akram ya d’an dubeshi a kaikaice.... Nan Yusuf yaci gaba da fad’in “Mu wakilan ALHERI Party ne, mun kasance muna matuk’ar k’aunan shirye shiryenki a tasharku ta gidan radio RY, muna kuma jin dad’i sosai yanda kuke k’ok’arin gayyato manyan manazarta masu fayyace gaskiyar abindake faruwa a siyasar k’asan nan da kuma wayarwa jama’a kai a b’angaren abinda ya shafi sanin mahimmancin k’uru’unsu... Wannan dalili yasa Party d’inmu ta wakilcemu a madadin d’aukacin sauran ‘ya’ayanta kama daga shi Eng Ma’aruf MUTALLAB mai neman takaran kujeran gwabna har izuwa sauran ‘ya’yan jamk’iya suka wakiltamu domin mu mik’a gaisuwar ta’aziyanmu na rashin da aka miki... Ubangiji yajik’anta yasa kuma mai ceto ce...”

Gaba d’aya suka amsa da ameen ida ka d’auke Hafiz da k’irjinsa ke tsananin bugu da sauri da sauri, abinda yafi d’aga masa hankali ba komai bane illa ji da yayi Wai Zulfa’unsa ce ta soma aiki a gidan radio ba tareda yasan hakan ba harma wad’annan ‘yan iskan ‘yan siyasan suna saurarenta, watoma gaurayuwa kenan takeyi da maza tana masu interview... Bai ida tunanin nasa ba ya tsinkayo muryarta tana fad’in

“Allah sarki mun gode k’warai da gaisuwarku, Allah Ubangiji kuma yasa a mizani amma saidai ina fata ba sabida siyasarku kukayi haka ba domin ni aikina kwai nakeyi yadda aka umarceni...”

Yusuf ya murmusa yace “A’a Rankishi dad’e ko d’aya bamuyi hakan domin k’arawa jamk’iyarmu martaba sai don kyautata alak’armu da d’aukacin jama’an wannan jiha ina fata hakan bazai kawo wata mishkila ba...”

Kafin Zulfa’u ta sami zarafin basa amsa sukaji an banko labule an shigo.... D’aga kan da zatai tai tozali da Hafiz sai faman huci yake lokaci guda yake nuna Yusuf da Akram da ‘yar yatsa yana fad’in “Idan baku tashi kun fice ba ina mai tabbatar maku zakuga babban mishkila, don mace na aiki a gidan radio hakan bai baku dama ku dinga bibiyan matan mutane ba kuna fakewa da siyasa!” Yanda yake maganan har wani irin zabura yake sabida tsananin b’acin rai...
Zulfa’u ta mik’e a zabure tana fad’in “Ya Hafiz dan Allah ya isa haka... Not now please...”

Tsawa ya daka mata da fad’in “Kimin shiru kekuma, shine sabida tsaban iskanci har aiki kika soma gidan radio kina watsa ra’ayinki na siyasa salon maza su biyoki har gida koh... Toh wllhi kinji na rantse kin gama wannan shegen aikin gidan radio din...” Tinda ya soma magana kuka ya kufce mata yayinda Marliya ta fice a guje ta nufi cikin gida neman d’auki ganin Hafiz ya fice a giya....
Gadan gadan yayi kansu tamkar wanda zai kai masu duka yana fad’in idan basu fita ba zaiyi ajalinsu... Ganin haka yasa Zulfa’u yin kansa a guje tana k’ok’arin janyoshi amma inaa tuni ya bangajeta ta fad’i k’asa...
Sai lokacin Akram ya zabura ya mik’e yayi tsaye gaban Hafiz tamkar k’irajensu zasu gogi juna, In a husky voice Akram ke nunasa da yatsa yake fad’in “Don’t hurt her or else....”
Hafiz na d’aga jijiyan wuya yake fad’in “Or else what...? Mai zakumin, zaku sa a kasheni ne irin yanda ‘yan siyasa irinku sukeyi zakusa ‘yan dabanku suyi ajalina ne ko mai... Ka fad’a mana...!” Ya k’arashe yana kuma d’aga k’irji saman yana sakin huci daidai lokacin dasu Mamy suka shigo babu shiri suna sallalami... Aunty B ce tai k’ok’arin janye Hafiz tana mai baiwasu Akram hak’uri yayinda Mamy ta nufi d’iyarta dake durk’ushe wajen a k’asa tana kuka mai tsuma zuciya....

Har bayan ficewarsu Akram Hafiz bai daina cewa Zulfa’u sabida maza ta soma aikin gidan radio ba, yana fincika daga hannun Aunty B yana fad’in idan k’arya yake ba sabida maza take aikin ba ta tashi ta musa...
Tsananin zafi da zuciyar Zulfa’u keyi batasan sanda ta mik’e tana huci take fad’in “Idan sabida maza nakeyi meye naka a ciki, meye ruwanka a ciki, shin ka mance ni yanzu ba matarka bace... Ka mance hakan Ya Hafiz...? Ka mance inada dama da zan tsaya da duk namijin danaga dama, ka mance inada dama da zan baiwa duk wani namiji mai son aurena k’ofa... Ka mance babu iddarka akaina..? Ka mance babu kome a sakinmu...? Idan har ka mance duka wad’annan, well let me remind you...” Kuka sosai ya kufce mata sanda taci gaba da fad’in cikin rawar murya “Badon kar nace babu sauran alak’a da ya had’amu ba tinda gudan jinin dake tsakaninmu Allah ya karb’i abinsa... Amma saidai kai d’in d’anuwana ne na jini duk yanda naje nazo... Kuma har abada bazan daina baka girmanka na Yaya a gareni ba... Ka tsaya a madakacinka don’t cross your limits...” Tana ida fad’in haka tasa hannu ta goge hawayen da suka jik’a mata fuska kana ta shige cikin gida....
Mamy ta take mata baya cikin sauri yayinda Aunty B ta saki murmushin jin dad’i ganin yanda Zulfa’unta ta takewa Hafiz burki, kallon yayi daidai ta raka Hafiz dashi kana ta shige ta barsa nan tsaye tamkar wanda ruwa ya shanye...
Jiki babu laka ya fice daga gidan abubuwan da Zulfa’u ta fad’i sunai masa yawo a kwanya....

***

Driving yake suna tattauna lamarin Hafiz shida Yusuf, Yusuf yace “A gaskiya da gani tasha wahalan zama da wannan mahaukacin.... Kai kaga yanda yayi jifa da ita kuwa...?”

Akram da zuciyarsa ke masa zogi ya fuzar da iska a karo na babu adadi kana yace “Badon ina tunanin she’s still grieving na rashin ‘yarta da tayi ba wllhi kaji na rantse da na koyawa mutumin nan hankali yanda nan gaba duk macen da ya kasance da ita zai girmamata ya darajata....”

Yusuf ya dara kana yace “Mutumina nasan halinka ai don naga irin duban da kake masa, toh ya kadai ganta hankalinka ya kwanta...”

Sai lokacin Akram ya saki murmushi a hankali sanda traffic light ya nuna masu koren wuta alamun an basu hannu kana yace “Kajika da wata magana... Kaga muje na ajeka na wuce I’m sure oga na can na jirana...”

Yusuf yai dariya yace “His excellency zakace.... Kodashike kaje ganin her excellency na birnin zuciyarka ne don haka bazaka amsa query ba...”
Nan ma murmushin kawai Akram ya kumayi kana ya d’auki hanyar unguwarsu domin sauk’e Yusuf...

***

MUTALLAB’S

Tsaye yake gaban full length mirror yana d’aura agogo a tsintsiyar hannunsa sanda ta turo k’ofan d’akin ta shigo fuska a turb’une....
Kallo take kan faman binsa dashi yanda yayi banza da ita tamkar baisan wata halitta na tsaye wajen ba, yayi kyau sosai cikin jampan nasa mai ruwan toka da ya bita da bak’ar hula zubin damanga.... Sai sassayanyar k’amshinsa dake dakan hancinta tinda ta shigo d’akin wanda babu wai tayi kewarsa sosai....
Ganin zai d’auki wayarsa dake gefen bedside ya sata yin sauri tasha gabansa tana rik’e da kunkumi tana watsa masa mugun kallo take fad’in “Ma’aruf let’s end this game now, wane irin rayuwa kakeyi... Ka sanar dani gaskiya azumi kakeyi kokuwa bin mata ka fara da yasa ka kasa nemata....?”

Idan hulan dake bisa kanshi ya amsa toh shakka babu shima zai amsa.... Duba d’aya ya mata ya d’auke kansa yana k’ok’arin rab’an gefenta d’iyarsa k’arama ta shigo tana fad’in “Daddy nima zan bika... Please don’t say no, kaga Uncle Akram yace gobe dani za’aje....” Ta k’arashe baki a ture....

Rage tsawonsa yayi ya kamo yarinyar ya zauna bakin gado had’ida d’aurata bisa cinyarsa guda kana yace “Yara basa zuwa Kiddy ki zauna a gida kinji koh...”
Mak’e kafad’anta guda tai kana tace “But I don’t want to Daddy, ni banson zama da Mummy bana sonta....”

Zuciyar Muhibba ta kuma yin zafi takaiwa yarinyar dake kwance jikin Babanta harara kana tace “Wannan wane irin wulak’anci ne ina maka magana kayi banza dani kana biyewa yarinya salon a koyawa yara k’in uwarsu tun suna yara...”

Baice mata komai ba sai d’aga Najma da yayi ya mata ‘yan dabaru ta hak’ura ta fice wajen ‘yan uwanta...

Dawowa d’akin yayi ya tadda Muhibba tsaye tana faman huci, dukda zafi da zuciyarsa ke masa hakan baisa yace mata komai ba sai d’aukan d’aya wayar salulansa da yayi ya nufo downstairs....
Cikin tsananin fushi da takaicin yayi banza da ita ta biyo bayanshi tana fad’in “Ni Wllhi sai ka fad’a min wacece shegiyar da kake cin amanata da ita... Wllhi sai ka fad’a min....” Ta k’arashe cikin muryar kuka....

Tsaye yayi yana dubanta don yanzu abubuwan Muhibba sam basa bashi mamaki,
“Ki d’auka a duk yanda ya miki, banida matsala da wannan, duk abinda shed’anin zuciyarki ya raya miki toh ki d’auka a haka, wannan ke ta shafa bani ba... Zan miki kashedi guda d’aya koda wasa kada ki kuskura ki sako yaranmu cikin wannan matsalan, this is between us do not involve them.... Na fad’a miki tun ba yau ba I can take care of them with or without you.... So kada ma ki fara dasawa yara cewa an koya masu tsanarki, ke da kanki kika zab’i hakan.... So na fad’a miki kada ki kuskura idan ba haka zakiga other side d’ina da har yau baki tab’a gani ba.....” Yana ida fad’in hakan yasa kai ya fice cikin sauri zuciyarsa na tsananin masa zafi....
Kallo tabisa dashi had’ida fashewa da wani irin kuka....

***

A can asibiti wajen Abbah kuwa da mamaki yake kuma duban Aunty Lami kana yace “Lami Kausar jikata kike nufi...?”

Aunty Lami ta jinjina kai tace “K’warai kuwa bansan dalilinsu na b’oye maka ba....” Ta k’arashe tana juya idanu...

Abbah ya rik’e bangaren k’irjinsa dake masa zafi sosai, ya sauk’o daga saman gado yana tambayarta ina takalmansa... Har lokacin hannunsa na dafe da k’irjinsa....
Aunty Lami fad’i take “A’ah Alhaji ina zakaje... Ina zakaje a haka... Ka tsaya likita yazo ya sallameka...”

Abbah fad’i yake “A’a Lami ahalina suna buk’atana dole naje na gansu bazan tsaya jiran likita ba....” Ya k’arashe maganan jiri na k’ok’arin aikasa k’asa...
Aunty Lami ta bud’e murya tace “Alhaji..!!”

A daidai lokacin da Sameer ya shigo ya furta “Abbah..!!” Da k’arfin gaske baisan sanda ya isa ya rik’esa ba....

Zaro idanu waje tai k’afafunta na tsananin rawa, yawun bakinta cak ya kafe lokaci guda ganin hasashenta na neman tabbata bata ida karaya ba saida ta sinkayo muryar Abbah na fad’iwa Sameer “Ma’aruf gida zanje...!”

K’iris ya rage Aunty Lami bata saki fitsari a jikinta ba, da za’a tsaga jikinta tabbas da zai wuya a sami jini sabida yanda ta daskare lokaci guda....
A hankali ta furta “Ma’aruuf ne..!!!”

SameenaAleeyou📚





*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*54*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Abbah fad’i yake “Ma’aruf meyasa kuka b’oyemin mutuwar jikata, kan wane dalili.... Na riga na warke maza ka kaini gida... Muje banson na sake yini a wajen nan balle kwana....”
Sameer ya rik’e shi sosai yana fad’in “Calm down Abbah please... Mu jura likita yazo ya duba idan za’a iya sallaman naka... Please Abbah...”
Girgiza masa kai Abbah yaci gaba dayi yana fad’in “A’a Ma’aruf na warke, ka d’aukeni kawai mubar wajen nan...”
Har wannan lokacin Aunty Lami bata dawo cikin hayyacinta ba, abubuwan da suka faru baya suke faman yawo a kanyarta... Ma’aruf ya dawo, yaron da suka salwantar da rayuwarsa da k’arfin gaske gashi Allah ya dawo dashi, tabbas dawowarsa barazana ne ga rayukansu.... Cikin mintoci k’ank’ani tai wad’annan tunanin....
“Lami kirawo likitan ya bani takardan shaidar sallamar, jeki kirashi ya sallameni...”
Sai sannan Aunty Lami ta dawo daga duniyar data tafi... Cikin rawar murya take furta “To...Na’am... To Toh Alhaji ....” Cikin sauri ta fice daga d’akin ba tareda ta dubi b’angaren da Sameer ke tsaye ba, tamkar wacce k’aya ke sokinta haka ta fice daga d’akin...
Sameer ya bita da kallo zuciyarsa na raya masa wani abin musamman da ya fahimci itace ta sanarwa Abbah mutuwar tilon jikarsa....

Sam Aunty Lami batasan yanda take jefa k’afafunta ba, ko kirawo likitan bata iya tayi ba, tsintar kanta tai a bakin kwalta ba tareda sanin ta fito waje ba tsananin rud’ani da tashin hankali had’ida zullumi da fargaba data tsinci kanta ciki....

A daidaita ta tare ta hau cikin sauri ko ciniki bata tsayayi ba tamkar wacce ake biyeda ita a guje haka ta shige adaidaitan....
Da k’yar ta iya lalumo kalamai saman harshenta taceda mai adaidaita ka yanda zaya kaita....

A bakin layin su Hajiya ta sauk’a sai faman zuba haki da gumi take sanda ta fad’a cikin gidan tagajan magajan tamkar wacce aka jehota....
Hajiya na zaune bakin murhu da shike ‘yan gaisuwa sun d’auke k’afa... Firgit ta mik’e had’ida dafe k’irji tana fad’in “Lami lafiya na ganki haka...? Meke faruwa Lami...?”

Naja’atu dake zaune daga can gefe tana wanke wanke kallon mamaki take bin Aunty Lami dashi ganin hawaye kwance saman fuskarta gashi gaba d’aya a birkice take tamkar wacce aka biyota a guje....

Lami naci gaba da waige waige ta kamo hannayen Hajiya cikin daburcewa take fad’in “Haule shikenan... Shikenan mukam Haule tamu tazo k’arshe....”

Hajiya ta waiga taga babu mai kallonsu don ko kulada Najah dake wajen wanke wanke ma batai ba, tai saurin janyo hannun Lami suka shige madafi cikin sauri.....

Naja’atu tai saurin d’auraye hannayenta ta take masu baya had’ida lab’ewa jikin k’ofar kitchen d’in....

Hajiya Haule na muzurai take tambayar Aunty Lami...
“Lami wai meke faruwane ya na ganki haka....?”

Aunty Lami na goge gumin da ya wanke mata fuska take fad’in “Ma’aruf ya dawo Haule... Shikenan kashinmu ta bushe... Haule idan muddin asirinmu ya tonu Alhaji Usman Mailafiya tsireni zaiyi shikenan na rabu da masoyina Haule... Wayyo Allah na wllhi ban tab’a danasani irinta yau ba Haule...” Ta k’arashe murya cikeda tsananin tsoro...

Hajiya ta zaro idanu waje had’ida dafe k’irji tace “Lami kina nufin kicemin hasashenmu ya tabbata wannan likitan shine Ma’aruf...?”

Jinjina kai Lami tai cikeda tsoro kana tace “Haule shine shine dai Ma’aruf ya dawo garemu... Wayyo Allah na Haule, idan Usman ya koreni ina zanje ni ba d’a ba balle jika ba iyaye a raye ba, ina zan dafa Haule...?”

Muzurai Hajiya keyi tana faman sak’e sak’e cikin zuciyarta....
Cikin sauri ta kuma kamo hannayen Aunty Lami kana tace cikin k’asa k’asa da murya “Ki kwantar da hankalinki Lami asirinmu bazai tab’a tonuwa ba... Ni nasan abinda zanyi amma a halin yanzu ki koma kuma kiyi k’ok’ari ki daina bari wannan tsoron naki yana rinjayarki, ki watsar da komai ki nuna tamkar bakisan komai ba....”

Aunty Lami da har lokacin a firgice take ta dubi Hajiya Haule tace “Haule ina zan iya rayuwa gida guda da Ma’aruf..? Gani nake kaman zai tuno fuskokinmu....”

Hajiya tai wata shed’aniyar murmushi tace “Lami bazaki canza ba wannan tsoron naki har yanzu yana nan... Shekarun da yawa Lami na tabbata Ma’aruf bazai fahimci komai ba sannan da ace zai gane wani abu da ya fahimta tinda ya had’u damu tin ba yanzu ba don haka ki kwantar da hankalinki kici gaba da al’amranki kaman da kar ki janyo wani abinda zaisa asirinmu ya tonu... Jeki jeki kawai sai mun had’u mu duka UKUN na tabbata Aminiyar Sirri zatafi kowa gudun tonuwar wannan dadd’en sirrin.... Jeki Lami mijinki zai iya zargin wani abu....” Tana ida fad’in haka ta janyo hannun Aunty Lami suka nufo waje yayinda Naja’atu ta b’ace daga wajen cikin sauri tana mamakin tattaunawan dataji Hajiya da Aunty Lami keyi... Shin waye Ma’aruf shin kodai Yaya Ma’aruf d’an gidan Abbah suke nufi da ya b’ace shekaru da jimawa... Shin kodai akwai sa hannun Hajiyarta a b’acewarsa ne...?” Tambayoyin da suka cika zuciyar Naja’atu.. Dole tabi a sannu don gano wannan sirri da Hajiya ke k’ok’arin bisnewa bayan yana neman tona kansa, ta d’au alwashin bazata kuma bari Hajiya ta cuci wani ba koda kuwa Mahaifinta ne da Hajiyar ta riga ta shanyesa... Da wannan tunani Naja’atu ta koma mawanki jiki a sanyaye.....

***

Koda Aunty Lami ta koma asibitin bata tadda Abbah ba, tayi tunanin hakan ka iya kasancewa don haka kai tsaye gida ta wuce yanda ta tadda gaba d’aya illahirin ahalin gidan suna hallare a parlor, Alhaji Usman Mailafiya na daga center yayinda sauran ahalin ke kewaye dashi, can ta hangi Sameer na zaune k’asa shima kusada k’afafun Abbah...
Gaban Aunty Lami ya kuma tsinkewa musamman data hango kwantacciyar murmushi dake a fuskar Mamy...

Abbah yayi gyaran murya kana yace gaba da fad’in “Kaman yanda kuka sani a gidan nan ko nace a ahalin nan mun kwashe sama da shekaru talatin muna neman d’an uwanku wanda ya b’ace mana a ranar da kikazo duniya Zulfa’u.....”

Zulfah ta d’ago idanunta mai zuban hawaye cikin sauri tana duban Abbah yayinda muryar Abbah ta soma rawa sosai.....
Sameer ya d’ago yana duban wacce aka kirada Zulfa’u... Tsananin tausayinta ya rufesa sanda take fad’in “Abbah Ka samu Yayana ne... Abbah ka sami Yaya Ma’aruf ne....?”

Abbah na murmushi hawaye na gangaro mashi yace “Zulfa’u Allah ya bayyana mana Yayanku ya yaye mana bak’in ciki da muka jima a cikinta....” Idanun Abbah suka sauk’a kan Sameer dake faman bin ‘yan uwansa da kallo d’aya bayan d’aya...
Gaba d’aya suka maida dubansuga likitan wanda azatonsu yana wajen ne kurum a matsayinsa na likitan Abbah...
Murya na rawa Marliya tace “Abbah wannan shine Ya Ma’aruf... Shine Yaya na da ban sanshi ba sai labarinshi....”

Sameer da siririyar hawaye ta gangaro masa a hankali yake furta “Nine Yayanki Ni ne Yayanki da baki sani ba little Sis....” A guje ta tafi gareshi sai kuma taja ta tsaya hawaye sun wanke mata fuska... Murmushi saman fuskokinsu tace “Can I please hug you...?”

Ya jinjina mata kai a hankali murmushi saman fuskarsa yake furta “Of course.... Come here...” Ya bud’e mata hannaye ta tafi a guje ta rungumesa....
Su Nabila da Zulfa’u hawayene kurum suma ke kwaranyowa daga idanunsu...
Sameer ya d’ago ya dubesu kana yace su taho suma...
Gaba d’aya su duka hud’un suka rungume juna suna hawaye
Cikin muryar kuka Sameer ke furta “I have beautiful sisters in the world....” Yana fad’i murmushi mai bayyana hak’wara na fita daga fuskarsa...
Yanda suka rungume juna su duka hud’u suna hawaye yasa Mamy da Abbah zuban hawaye
A hankali Mamy ta isa ta rungume yaranta gaba d’aya tana hawaye take hamdala ga Ubangijinta da ya nuna mata rana irin wannan, ga yaranta gaba d’aya a tareda ita...
Harta Aunty Lami dake tsaye jikin k’ofa saida taji k’walla na neman ciko idanunta, ji tai bazata iya shiga parlorn ba cikin sauri ta juyoda baya tana mai goge hawayen da ya mak’ale mata a idanu... Ido hud’u sukai da Aunty Bara’atu... Sukai tsaye suna duban juna....



SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_



55


*©️Sameena Aleeyou ...✍🏽*



NOT EDITED



Cikin sauri Aunty Lami tasa kai zata shige Aunty Bara’atu ta janyota.... Kallon kallo suke aikawa juna lokaci guda Aunty Bara’atu ta saki murmushi kana tace “Kina mamaki ya dawo ne...?”

Aunty Lami ta waiga gefe da gefe kana tace “Mai kike nufi.....?”

Janyota Aunty B ta kumayi kana tace “Muje, ban yarda dake ba, you must be hiding something....” Lokaci guda ta tura k’eyarta suka b’ace daga wajen Aunty Lami na faman muzurai......

Parlorn yai shiru sanda Sameer ke labarta masu rayuwarsa da mutanen da ya tashi ya gansu a matsayin iyayensa, Mamy da Abbah saida suka zubda k’walla jin yanda iyayen goyon Sameer suka rik’eshi bisa gaskiya da amana ba tareda sunsan cewa ko su waye iyayenshi ba, sun d’au alwashin kaima iyayen rik’on Sameer ziyara ta musamman da kuma mik’a godiyarsu a garesu baki d’aya....
Yanda Mummy ta bashi labarin k’anda akai ya fad’a hannunsu haka ya sanar dasu Mamy, sosai abin ya d’aure masu kai, al’ajabi ya cikasu baki d’aya...
Abbah yace “Wannan yana nuni da cewa tabbas Ma’aruf ba b’acewa kayi haka kurum ba, tabbas akwai mugu a tsakani wanda yaso rabaka damu koma yaso rabaka da rayuwarka baki d’aya....”

Sameer ya jinjina kai kana yace “K’warai Abbah wannan shine abinda nake tunani bayan mahaifiyata ta bani labarin yanda akayi na b’ace daga gareta....”

Zulfa’u datai jigum tana saurarensu sai cewa tayi “Toh Abbah shin wanene zai nemi ganin bayan k’aramin yaro irin haka a wancan lokacin....? Lallai wannan mutumi yakai k’ololuwa wajen rashin imani....”

Abbah ya sauk’e ajiyan zuciya kana yace “Zulfa’u Duniyarmu cike take da mutane iri daban daban, kana tare da mutum wasu lokutan amma bakasan wanene mugu ba, masu iya magana sunce mugu baida kama...”


Nabilah dake zaune gefensa so take ta tambayesa mecece alak’arsa da Khalid amma bata san ta yanda zata soma tambayar nasa ba...
“Ya Ma’aruf ....”
Ta kirawo sunansa a hankali....
D’agowa yayi yana dubanta jin sabon sunan da aka ambace sa dashi...
Itama d’in taji wani iri don ba sabawa sukai ba...
A hankali ta d’an sadda kai kana tace “Sorry... Can we please call you Ya Ma’aruf....?”

Murmushi Sameer yai kana yace “You can call me Ya Ma’aruf or Ya Sameer duka sunana ne zan amsa kinji koh....”
A hankali ta saki murmushi ita da sauran ‘yan uwan nata...
Shigowar Aunty Lami ya hana Nabilah ci gaba da magana..

Murmushi har kunne Aunty Lami ta shigo tana fad’in “Masha Allah.. Masha Allah .... Finally Ma’aruf d’inmu ya dawo.... Alhamdulillahi Allah shine abin godiya....” Ta k’arashe tana mai zama gaban Sameer da yai mutuwar zaune yana duban matar, wacce duba guda ya mata yaji k’irjinsa ya buga dum kaman an aje guduma lokaci guda....

Aunty Lami ta kuma fad’ad’a murmushinta tana fad’in “Ma’aruf...! Ma’aruf ashe zamu sake sakaka a idanuwan mu....!!!?” Lokaci guda kuma ta shiga tattaro bakin zani tana goge hawayen dake zubo mata wanda zakai zaton tsan tsan farin ciki ne....
Sameer duk sau yaji wani iri ganin matar tana sharan kuka gabansa...

Nabilah tab’e baki kurum tai tana kallon salon makircin matar Baban nata

Abbah na murmushi yake fad’in “Lami d’anki Ma’aruf ya dawo garemu... Allah ya dawo mana dashi....” Ya dubi Sameer yace “Ma’aruf wannan itace mamarka Lami abokiyar zama ce ga mahaifiyarka....”

Sameer ya sakar mata murmushi zai bud’a baki tai saurin cewa “Call me Aunty Lami..... Haka k’annenka suke kirana....”

Ya kuma sakin murmushi kana yace “Aunty Lami......”

Ta jinjina kai tana kuma sakin murmushi....
Murmushin yak’e kurum Sameer yake amma har ransa baijin ya sake da matar, sannan yana tuna kaman wani muhimmin abu ya tab’a had’asa da ita a wasu lokuta can masu tsawo....

Sameer bai sami zarafin sanar dasu cewa nada iyali ba har akai masa waya ana neman sa acan asibiti, shi kansa ya mance da sabgan wata Siyama, Farin cikin had’uwa da dangin sa da iyayensa ya sakashi mancewa da duk wani k’unci da Siyama ta jefa sa ciki.....

Yana isa asibiti ward d’in Raihanah ya nufa duk da cewa director na asibitin ne da kansa yake nemansa...

A hankali Sameer ya murd’a handle d’in k’ofar.... Kwance ya hangeta idanunta a rufe alamun bacci take... Ya jima yana dubanta kafin yaji motsin tab’a k’ofan toilet
Cikin sauri ya janyo k’ofar a hankali ya shige don dama kiran nasa director na asibitin ne mai nemansa..
***

Duk saurin da yake gudun kada ya makara ya bar ogan nashi zaman jira saida ya makara sabida holdup mai tsawo data kuma tsareshi, cikin ransa yake ayyana tabbas yasan Boss ya gama shiryawa shi kawai ake jira tinda yasan African time ba tsarinsa bane.... Yana tsaka da tunanin ne wayar d’aya daga cikin tawagan nasu ya shigo masa.... Bai d’aga ba sai k’ara malejin motar da yai, Don ko ya d’aga yasan maganar guda ce His excellency ya shirya shi ake jira....

Aiko yana sako hancin motar cikin gidan yayi arban da taron mutanen nasu, wasu sun shige mota wasu suna tsartsaye cirko cirko a farfajiyan hamshak’in gidan, da yawan mutanen suna mamakin yanda idan za’ai fita ko taron siyasa koma abinda bai shafi siyasa ba yanda duk kaga Engr Mutallab toh fah sai kaga Akram, koda baya nan kuwa sai an jirashi, bai yarda da tuk’in kowa face na Akram, Akram ya zamto tamkar k’ani a gareshi, harta zumunta mai k’arfi saida iyayen Akram suka k’ulla da Mutallab.... Da yawan mutane sunso shiga tsakaninsu saidai Allah bai k’addara hakan ba....

A

Please Login or Register in order to submit comment