Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar da k’yar yana mai k’ok’arin kai hannu don dafe k’irjinsa.... Cikin sauri Sameer ya k’arasa yana fad’in “Take things easy, a halinda kake ciki yanzu hutu ya kamata ka samu....”
Hafiz ya k’ura masa idanu yana mai tunanin tabbas yaga fuskar nan before he lost consciousness... Tabbas ya ga Sameer akansa na k’ok’arin taimaka masa.... Yai shiru suna duban juna shida Sameer d’in...
Baba Alhaji ya k’araso cikin sauri yana dafe hannayen Hafiz d’in yake tambayarsa ya sanar dashi mai ya faru...? Ya akai ya sami accident...?
Hafiz ya dubi mahaifin nasa, ya kuma duban Sameer dake tsaye gefe, ya maido da dubansaga mahaifinsa alamun zai soma magana, caraf ya sinkayo muryar Sameer na fad’in “It was me... Ni ne na bigesa da mota....” Ai bai kai aya ba Baba Alhaji yayi tsalle ya cakumosa yana fad’in “Kashesa kayi niyya, kashesa zakai akan ya saki k’anwarka... Shin kai mai ka sani Ma’aruf...? Fansa ka dawo d’auka....? Ka sanar dani fansa ka dawo d’auka....? Idan fansa ka dawo d’auka ka sani ba akan Hafiz zaka d’auka ba don ba shi yayi sanadiyan b’acewarka ba... Wad’anda zaka d’auki fansa akansu....” Baikai aya ba Hajiya tai wuf ta shiga k’ok’arin janye Baba Alhaji ganin zai saki layi.... Mamani dasu Najah suka shigo a birkice jiyo muryar Baba Alhaji da sukai yana tashi cikin karaji....
Marliya jiki na rawa ta isa tana k’ok’arin janye d’an uwanta ganin yanda Baba Alhaji ya shak’e masa wuya tamkar zai aikasa lahira...
Mamani kam kuka ta saki tana fad’iwa Baba Alhaji ya sakar mata jika ko ta masa baki... Jin haka ne ya sanya Baba Alhaji janye hannayensa daga wuyan Sameer, Hajiya ba haka taso ba, taso ya aikasa lahira kowa ya huta, asirinsu ya rufu ruf rufuwa ta har abada.... Shamsu da shigowarsa kenan ya k’arasa a guje yana mai tallafo abokinsa yake tambayarsa ko yana lafiya....
Hafiz dake tari a hankali yana yunk’urin magana amma ya kasa.... Da k’yar ya iya furta “Baba dan Allah ka k’yale Sameer, babu laifinsa... Laifinane da nake tafiya ba tareda sanin yanda nake zuwa ba... Hasalima ni ya kamaci na rok’eshi gafara halinda na jefashi ciki.... Ya mik’o hannayensa yana k’ok’arin kamo hannayen Sameer lokaci guda yake furta “Ma’aruf ka yafe min please..... Ka yafe min duk wasu abubuwan da na maka.....”
Sameer na sosa wuyarsa yake girgiza kai lokaci guda ya rik’e hannun Hafiz yace “Ka daina fad’in haka Hafiz, bakamin laifin komai ba.... Fatana Allah ya baka lafiya....”

Hafiz da siririyar hawaye ke zubo masa yaci gaba da fad’in “Na gode.... Na gode Sameer, kanada zuciya mai kyau, dan Allah ka tayani rok’on Zulfa’u ta yafemin.....”

Shiru Sameer ya d’anyi kana yace “Wannan tsakaninku ne Hafiz, ba hurumina bane.... Allah ya baka lafiya...”
Hafiz ya jinjina kai a hankali yana mai rintse idanunsa wasu irin hawaye masu d’umi suka kuma zubo masa.... Jikkunansu sukai sanyi gaba d’aya, Baba Alhaji ya fice cikeda borin kunya yayinda Hajiya ta samu ta silale itama ta nufi can gidan Hafiz d’in dubo Sawwama don taji har wani tunanin Zulfah Hafiz ya soma, abinda bata fata ko bayan ranta ace Hafiz ya maidoda Zulfah d’akinta....

***

Akram ya dubi Yusuf a karo na biyu kana yace “Kanaga banyi mata hanzari ba....?”
Yusuf ya kuma karyan raken dake rik’e hannunsa na dama kana yace “Kasanfa hausawa na cewa A bari ya huce shike kawo rabon wani.... Mutumina this is the right time, na tabbata tuni manema sun soma kawo mata hari so gwara kawai ka making move.... Mu k’arasa Atika tai mana iso....”

Akram ya zuba duka hannayensa biyu saman steering wheel kana ya sauk’e ajiyan zuciya kad’an yace “Amma bazataga mun biyota wajen aikinta mun tak’urata ba....?”

Gajeren tsaki Yusuf yai kana yace “Wataran fah kayan haushi ne dakai, idan bazakai amfani da damar daka samu ba kada ka kuma zuwa kanamin zancen wata Zulfa’u ka gane koh... Na fad’a maka ni nan na sanar da Atika ta shirya mana yanda za’ai muga Zulfah lokacin break d’insu, idan kuma baka shirya ganinta bane toh sai naji...”Ya k’arashe yana mai karyan rakensa....

Harara Akram ya watsa masa kana ya kunna motar, Yusuf yaja marfin mota ya rufe kana suka d’auki hanyar station d’in su Zulfah....

Suna tafe ne wayar salulansa dake aje gefe ta d’auki ruri, ya d’an rage speed kana yakai dubansaga screen d’in wayar, ba kowa bane illa boss d’insa Engr Mutallab.... Yai saurin d’agawa cikeda girmamawa, take Engr d’in ke sanar dashi ya bar duk abinda yake yazo Office ya sameshi...
Akram yace “Alright your excellency gani nan zuwa....” Ya k’arashe yana mai karya steering motar, lokaci guda yake furta “Change of plans... Babu gani Zulfa’u yau...”
Yusuf ya tab’e baki kad’an kana yace “Aidai da ka sanar dashi ka tafi neman aurene bazai katse ka ba....”
Akram ya jefo masa harara gajeriya kana yace “Sallah ne kawai bazan katse ba idan his excellency yanada buk’atan ganina... Komai a bayansa yake...”

Yusuf ya kuma tab’e baki yace “Naga alama ai... Kaga barin kira Atika na sanar da ita bazamu samu zuwa yau ba....”

Atika dake faman rarraba idanu a a cafeteria d’in, tana hango ta yanda zataga su Yusuf shiru bata gansu ba, sai faman waige waige take gashi dai sun ida cin lunch d’insu.... Girgiza kai Zulfah tai kana tace “Wai wanine kike jira...? Idan ba jiran wani kike ba kiwa Allah ki tashi mu koma office...”

Hannunta Atika ta rik’e ta kuma zaunarta tana fad’in “D’an k’aramin lokaci kedai....”

Zulfah ta girgiza kai kurum tana mai juya idanu had’ida jan gajeren tsaki... Daidai nan wayar Atika ta d’auki ruri, Yusuf ne mai kiran nata.... Tai saurin matsawa gefe tana tambayarsa mai ya hanasu zuwa har yanzu....
Nan Yusuf ke sanar da ita something came up dole suka canza plan....
Atika da tuni ta shak’i haushi cewa tai “Ni na fad’a maka wannan abokin naka is not serious, da alama Zulfah ba class d’insa bane don harta ogoginmu na nan station suna nuna kulawa akanta, idan baiyi da gaske ba zaiji a salansa....”
Yusuf yace “Ya zakice haka, ogansa ne ya kirasa kedai kici gaba da mana sharan fada kawai please kinji... Yauwa na gode k’anwata...”

Gajeren tsaki tai kana ta dawo taceda Zulfah su koma Office... Zulfah dai dubanta kawai tai kana ta tattari belongings d’inta suka nufi office... Suna tafe Zulfah ke tambayar Atikan ko lafiya take.... Atika tace lafiya lou wani saurayinta ne yace zaizo toh kuma sai yace mata uziri ya rik’esa...
Zulfah batace komai ba sai jinjina kai da tai...
Atika ta d’an dubeta kana tace “Waini Zulfa’u meye shirinki...?”
Zulfah ta d’an dubeta kana tace “Ban gane ba... Shirina kaman yaya...?”

Atika ta murmusa tace “Ina nufin kinada burin aure nan kusa..? don naga da yawan staff d’inmu idanunsu na kanki ne....”

D’an dubanta Zulfah tai kana ta dubi wani gefen, lokaci guda take furta “After what I went through banajin nayi shirin kasancewa da wani namiji kuma...”

Atika tai shiru na tsawon shud’ewan wasu dak’ik’ai kana tace “Does that mean you haven’t moved on from your ex husband... Kina sonshi ne har yanzu....?”

Wani irin duba ta mata kana ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Wasu lokuta mukan tsinci kawunanmu cikin al’amra masu wuyan fasaltuwa, so tari Allah yakan jarabci bawansa da abinda yafi rainawa a rayuwa.... Ko a baya ba auren soyayya nayida Ya Hafiz ba... Idan kika tambayeni ban san wata soyayyan d’ah namiji ba face na iyayena da ‘yan uwana saiko d’iyata da na rasa... Hasalima ni Zulfa’u na taso cikin tsanane a tsakanin danginmu, harta mahaifina da Kakata basa k’aunata kan laifin da sam ban aikata, kan laifin b’acewan d’an uwana Ma’aruf.....To them I was nothing but a curse... Bayan mahaifiyata da k’annena guda biyu no one believes in me, sun yarda cewa mai farar k’afa aka haifoni har saida Allah ya wankeni ya kuma dasa k’aunata cikin zukatansu.... Toh kinga ni bansan wata soyayya ba bansan ya ake jinta ba... Idan nace maki ina son Ya Hafiz na maki k’arya don bansanma ya take ba, the only thing I know shine zaiyi wuya kayi rayuwar aure da mutum sannan a cikin rayuwar har Allah ya baku rabo cikinta kace bazakaji komai gameda mutum ba koda kuwa ace b’angare na tausayawa ne.... A halin yanzu babu wani shiri na aure ko soyayya a gabana, burina shine naci gaba da aikina da kuma samun nasara had’ida kwanciyan hankali.... Kin fahimta....”

Shiru Atika tai tana dubanta har takai aya, tausayin rayuwar da Zulfah tai a baya ya cika mata zuciya, ta saki murmushi a hankali kana tace “Toh kisa a ranki cikin masoyanki harda k’awarki Atika... Sannan na yarda dake na yarda cewa ke ba mai farar k’afa bace kuma in sha Allah a tattareda ke akwai babban al’amari wanda kowa harta masu cewa kinada farin k’afa zasu amfana ta dalilinki....”
Zulfah ta murmusa kana tace “Na gode k’awata nima ina k’aunarki tsakaniga Allah...”
Sukai murmushi su duka biyun kana suka nufi cikin studio....

**

Tin daga k’ofar gidan gaban Hajiya ke bugun tara tara.... Jikinta bai ida sanyi ba saida ta shiga cikin gidan taga bad’alan da ake aikatawa ga hayak’in kayan maye had’ida warinsa ya gauraye gidan gaba d’aya, ta shiga toshe hanci tana tari da k’yar....
Can ta hangi Sawwama sai rawan ‘yan bori take tanayi tana kora barasa ga ‘yan daudu na tayata mai gurmi naci gaba da aikinsa...
Hajiya ta d’aura hannaye duka biyu aka tana nishi da k’yar take furta “Na shiga uku... Na shiga uku ni Haule mai zan gani.....?!!”

***

Kana ganin Muhibbah kasan a d’auke take, Najma ta shigo tana mata kukan yunwa, wani uban tsawa data dararawa yarinyar saida ya sanyata sakin fitsari a wando... Yarinyar ta shiga jada baya jikinta na rawa... Yamutsa fuska Muhibbah take ganin fitsarin da yarinyar ta saki tana mai furta “Oh no no this isn’t happening...” Gashi Engr yasa ta rage ma’aikatan gidan a cewarsa idan tayi niyyan shiryuwa da gaske sai ta fara da kulada iyalanta...
Kira ta shiga dokawa Suwaiba wacce ita kad’ai aka bari harta Cooks d’in gidan Engr ya sallamesu...
Suwaiba ta k’araso a guje tana mai risinawa....
Muhibbah na mata nunida Najma take fad’in “Take care of her... Ta isheni da kuka.... Uban mai kike da har yanzu baki ida lunch d’in ba....?”
Suwaiba tace “Aunty aikin ne sunmin yawa... Kuma ai kaman naji Alhaji yace kece zakike abinci...”

Wani uwar harara data watsawa Suwaiba kana ta isa ta janyo kunnenta guda tace “Na maki kama da mai dafa abinci...? Answer me..!! Na maki kama da mai girki....??”
Suwaiba dake faman tamke fuska alamun taji zafin rik’on cikin sauri take girgiza kai alamun a’a....
Muhibbah ta jinjina kai tace “If you don’t want to get yourself fired toh kiyi duk wasu ayyukan da kikasan ma’aikata keyi gidan nan... Kuma Wllhi saura Engr ya dawo kice masa kece kikai abinci sai nayi d’add’aya dake... Tashi ki bani waje...”
Ta tashi da sauri tana goge hawayen da suka zubo mata... Muhibbah ta kuma kiranta tana mata nuni da Najam tace “Ki gyara wajen nan kafin na dawo....” Tana ida fad’in haka ta haye sama... Najma tai saurin rungumar Suwaiba tana kuka.... Suwaiba ta rungume yarinyar cikeda tausayawa, badon tausayin yaran ba da ganin girman Engr tabbas da tuni ta bar aikin gidan... Matace tamkar ba ‘yar Adam ba ko ma d’iyoyin wasu bazakayi irin wannan rik’on ba balle yaran da ka tsuguna ka haifesu....
Suwaiba ta d’auki yarinyar suka nufi kitchen tare tana mai lallashi had’ida jantada wasa...

Ita kaw Muhibbah tana zuwa d’aki, drawer mai d’aukeda kayan mayenta ta janyo... Ta ciro k’waya guda d’aya ta murmusheshi lokaci guda ta toshe hancinta guda ta shiga shak’a tana mai bubbuga kanta.... Saida taji kanta acan sararin samaniya kafin ta koma gefe tana hango duniyar na juye mata... Tana a haka ta jiyo k’aran shigowar motarsa... Cikin sauri ta mik’e tana k’ok’arin kimtsa kanta dukda cewa k’wayar bai saketa ba, hasalima datasan da wuri zai komo gida da bata sha ba....
Saida ta saita kanta kafin ta sauk’o k’asa....
Akram ne ya soma fitowa rik’eda jakan Engr d’in ya mik’a mata... Tai masa wani duba a yatsine kana tace ya aje a parlor ta k’arada in Engr d’in .... Akram ya bata amsada yana cikin mota...
Tsaye tai tana mamakin mai yakeyi cikin mota, nan dai ta nufi motar...

K’arar radio ta soma jiyowa cikin muryar wata mace mai dad’in sauraro yanda take furta “Toh jama’a masu saurarenmu yauma a nan zamu dasa aya... A shiri na gaba zaku jimu cikin wani sabon shirin... Kuci gaba da kasancewa damu a tasharku kuma zab’inku... A madadin mai kulada shirin da kuma abokiyar aikina tareda ni kaina Zulfa’u Usman Mailafiya muke cewa ku huta lafiya.....”
Muhibbah takai dubantaga mijinta yanda yake kishingid’e jikin car seat idanunsa a lumshe sihirtacciyar murmushi kwance saman fuskarsa....



SameenaAleeyou📚



*INDA RAI*
_................DA RABO_




*66*



Chaaa sukaima Hajiya Haule akai suna tambayarta daga ina take... Haule ta kasa amsasu sai nishi da take saki da k’yar sabida k’ahon zuciyarta dake mata tsananin zogi... D’aya yace “K’ila ‘yar lek’en asirice ma ‘yan hizba tinda makircin ‘yan unguwa ya gagara shine aka turo wannan matar...”
Gaba d’aya suka amsada tabbas maiyuwa hakan ne... “Mai muke jira, mu lakad’a mata na jaki ta yanda gobe zata kuma zuwa wani wajen lek’en asiri ba....” Kan Hajiya ta sami zarafin magana suka shiga sauk’e mata duka ta ko ina, basaji basa gani bugu kurum suke mata har saida hankulansu Sawwama yaje wajen... Ga mamakin Sawwama mahaifiyar Hafiz ake bugu, suka tambayeta ko tasan matar ne, Sawwama tace atafau itama bata santa ba da gaske ‘yar lek’en asirice... Sawwama ta basu go ahead suci gaba da bugun Hajiya...
Hajiya na magagi da mak’yark’yata take furta “Sawwama nice fah... Nice uwar mijinki fah...”
Sawwama ta tinstire da dariya tace “Kuji makira Wai itace uwar mijina... Toh idanma uwar mijina ne sai mai... Ko shi mijin ne ba tsira zaiyi a nan ba balle ke... Wani mijin ma da tuni na basa rasidi... Idan baki sani ba toh ki sani ni Sawwama na gama auren wannan matsiyacin d’an naki mai farin k’afa maza a k’ara gaba....!”

Hajiya ta d’aura hannaye bibbiyu aka tana furta “Wayyo! Wayyo!! Na shiga uku ni Haule... Na d’ibo ruwan dafa kaina... Amma wannan yarinya ke ba ‘yar halas bace... Nayi danasanin aurenki da Hafiz yayi... Matsiyaciya dangin fir’auna a nono kika sh....” Batakai was aya ba taji sauk’ar lafiyayyar mari a k’uncinta... Ta zaro idanu waje tana duban wacce tai marin ba kowa bace illa sirkarta Sawwama... Sawwama na huci taci gaba da fad’in “Ke har kin isa ki zagi mahaifiyata... Kinyi kad’an, kinada sauran azuzuwa kafin ki k’araso yanda nake a bariki...” Ta dubi sauran ‘yantashan nata tace “Kuci gaba da bugunta muddin bata tashi ta nemi hanyar tsira ma kanta ba...”
Haba nan kakeji didim dim dim, sautin bugun dake sauk’a jikin Hajiya Haule... Gashi ihunka banza ne don sautin kid’a dake tashi bazai bari mutan unguwa su jiyo su ceceta ba... Haka Hajiya ta dinga birgima wajen d’ankwali gefe zani gefe sai bugunta suke tamkar an aikosu, itako sai birgima take wajen tana ihu tana neman agaji...
Da k’yar Hajiya Haule ta samu ta arce a guje zani a hannu d’ankwali a hannu ga fuskarta da sumarta duk k’asa ya b’ata yanda tasha bugu... Yara kuwa suna hangota sai su arce a guje suna mata wak’an mahaukaciya, masu adaidaita ma idan ta tare basa tsayuwa don cewa suke mai tab’in hankaline....

Wani adaidaita ne ya nufo yanda take, tai maza ta haye saman kwalta d’in tana saka masa hannaye bibbiyu alamun ya tsaya... Daga mai adaidaitan har passengers d’in dake ciki wasu mata guda biyu, salati suka shigayi suna ambaton Allah, su kansu basu yarda cewa wannan matar ba mahaukaciya bace...
Atika ta zaro idanu waje tana buga siddin mai adaidaitan tana fad’in “Malam kayiwa Allah ka kaucewa mahaukaciyar nan mu bar wajen nan kafin ta mana duka don wannan daga gani tsohuwar kamu ce...” Zulfah kuwa zaune kurum tai cikin adaidaitan tamkar gunki tana kallon ikon Allah...
Hajiya tasa k’arfinta gaba d’aya ta rik’o adaidaitan ganin yana neman zille mata shima, lokaci guda take furta “Kayi wa Allah bawan Allah... Ka ceceni ka fitar dani a unguwar nan kafin su kasheni... Wllhi ni ba mahaukaciya bace... Kaga can gidan mahaukatan na ciki....”

Zulfa’u da hawaye ke kwaranyo mata a hankali ta furta “Hajiya..!!”
Haule tai saurin d’ago idanu tana duban fasinjar data ambato sunanta, ba kowa bace illa Zulfa’u tsohuwar matar d’anta Hafiz wacce ta making rayuwarta impossible a baya ta kuma sanya d’anta ya mata sakin wulak’anci...
Mai adaidaita da Atika har suna had’e baki wajen cewa “Kin santa ne...?”

Zulfa’u na hawaye take jinjina kai... Kan suyi wani aune Hajiya Haule ta fad’i k’asa sumammiya....
Suka shiga karanto innalillahi Zulfa’u na fad’iwa Atika ta taimaka mata su sanya Hajiya cikin napep d’in... Haka suka kwasheta zuwa asibiti....

****

Hankali kwance yake cin abincinsa yaransa na kewaye dashi suna hira cikin jin dad’i da raha idan ka d’auke matarsa da takega yaran tamkar dodanniya... Muhibbah tai tsaye daga can bayan dining table d’in tana duban yanda maigidan nata da yaranta, duk wannan walwala dake tattaredasu tasan tana zuwa wajen shikenan ya k’are, sannan ta lura da yawan jin radio da mijinta keyi wanda a baya ba d’abi’arsa bane, kuma ga dukkan alamu yawan sauraron radio d’in da yakeyi shi ya dad’a bada gudummawa wajen canzasa don dai tasan ba wai zamanta a gidan bane kurum yake jefa Engr cikin wannan farin ciki da annashuwa, shin meye gaminsa da radio..? Shin wane shiri yake yawan sauraro da har ya canzasa haka...? Lallai kuwa dole tai yanda zatai ta nemo wad’annan amsoshi nata...
Lokaci guda tasa kai ta isa dining area d’in...
Tana k’arasowa yaran suka mik’e suna shirin barin wajen....
Cikeda masifa tace “Kai kai ku dawo nan... Ina zaku..? Oh Wato kunga dodo koh... Shine daga zuwata kun wani mik’e zaku shige koh.... Salon munafunci ace ina maku wani abin koh...”
Irfaan babban cikin nasu mai shekaru goma yace “Karatu zanje nayi, monday zamu fara exams...” Bai jira cewarta ba yaron ya shige...
Ita kaw ta biyun cewa tai itama karatu zataje Yayanta ya koya mata... K’aramar ta uku tace wajen ‘yan uwanta zata itama..... Muhibbah ta rakasu da mugun kallo har suka shige kafin ta maidoda dubantaga mijinta wanda yabi bayan yaran da kallo har suka haye sama...
Sai faman kumburi take ta janyo kujera zata zauna.. Lokaci guda shima ya ije spoon d’in dake hannunsa ya d’auki tissues paper ya share bakinsa kana ya mik’e daga kujerar... Muhibbah ta saki baki tana dubansa... Cikin sauri ta mik’e tasha gabansa fuska a narke tace “Kaima tashi zakai ka barni....?”

Bai sami zarafin bata amsa ba wayarsa ta d’auki ruri... Ya d’aga kiran yana mai barin wajen... Muhibbah tabi bayansa da kallo har ya shige... Lokaci guda taji zuciyarta na mata wani irin zafi, taji babu abinda take bid’a tamkar ta shak’i garin hodar ibilis don shine kawai zai mantar da ita bak’in cikin da take ciki a nata tunanin... Allah ka mamu maganin musiban shan kayan maye data addabi al’umma, baga yara ba baga manya ba, baga matan aure ba baga ‘yammata ba... Allah ka kawo mana sauk’i ka kare al’umman musulmi ameen....

***

Farkawan da Hajiya zatai a gadon asibiti ta tsinci kanta, take abubuwan da suka faru suka shiga dawowa kwanyarta, ta tuna cewa tabbas Zulfah ta gani, Zulfa’u dai data tsana tak’i jininta itace ta taimaka mata, don ko shakka babu Zulfah ce ta kawota asibitin nan... Wani irin kuka mai cikeda nadama da kaicon rayuwa ya kufcewa Hajiya... Tinda take a rayuwarta bata tab’a jin nadamar abubuwa da kurakuran data tafka a rayuarta irinta yau ba... Nurse guda ce ta lek’o jin sautin kuka na tashi daga d’akinda Hajiya take... Tai saurin k’arasawa tana tambayarta ko lafiya ko akwai wani ciwo da takeji ta cikin jikinta kuma... Inaa Hajiya bata amsata ba sai ma k’aran sautin kukanta da tayi, nurse ta fice kiran likita da sauri....
Haka likitan ma ba sanar dashi Hajiya tai ba sai faman zabga uban kuka take, da k’yar ta iya saita kanta ta shiga tambayar likita ina yarinyar data kawota nan... Dr yace “A Gaskiya Inaga ‘yanmatan sun tafi, amma guda d’ayar tace tana dawowa don ina tsammani ta tafi sanarda iyalanki halinda kike ciki ne, bata bar nan wajen ba har saida muka tabbatar mata cewa babu wani rauni mai tsanani jikinki kuma nan bada jimawa ba zaki farfad’o...”
Nan ma rintse idanu Hajiya tayi sabbin hawayen takaici da kaico suna zubo mata, duk irin cin mutunci da wulak’anci da cin zarafin da tayiwa Zulfa’u batai tsammanin ko gawarta Zulfah ta gani saman kwalta a tagayyare zata taimaka mata ba, sai gashi ta taimaketa daga hannun matar da take tunanin itace daidai ga d’anta... Hak’ik’a ba Zulfa’u kurum ta zalunta ba harda d’anta Hafiz dake kwance gadon asibiti rai kwaikwai mutu kwaikwai... Ga kuma d’iyarta Sahariyya dake kwance gida tana jinyar karaya... Hajiya Haule ta kuma rintse idanunta tana furta “Wata irin rayuwa na jefa ahalina ciki ni Haule...”
Tana a haka ne Baba Alhaji yayi sallama....
Shi kansa saida ya razana da ganin yanda halittar Haule ya sauya Wai donma ya tadda anyi treating ciwukan nata an kuma d’an kintsa jikin nata ba kaman yanda su Zulfah suka kawota ba...
Zama yai daga gefe yana k’are mata kallo kana yace “Haule ki sanar dani gaskiya, mai kuma kikayi wannan karon...?”
Da gefen idanu ta dubesa kana tace “Ban gane mai kuma nayi ba... Shin ko tambayata jikina bakai ba kawai sai ka hau tambayata mai kuma nayi... Oho wato gani sarkin aikata sharri koh....?”

Huci Baba Alhaji keyi kana yace “Sanin haline da yafi sanin kama....”

K’uri Haule ta masa kana tace “Mai kake nufi....?”

Matsowa kusanta ya kumayi kana ya matso da fuskarsa dab nata, lokaci guda yake furta “Ma’aruf nake nufi... Kinfi kowa sanin nasan komai...”

Kauda kanta gefe tai kana ta kuma maidoda dubanta garesa tace “Haba ai biri yayi kama da mutum, na jima ina kokonton cewa kasan bak’in sirri na, amma ka kasan yin komai akai sabida kaima akwai b’oyeyyen sirrinka, bacin haka da tuni ka koreni daga gidanka da kuma rayuwar ‘ya’yanka.... Fad’a min mai ya faru shekarun can....?”

Shiru Baba Alhaji yayi yana muzurai ba tareda ya furta komai ba... Lokaci guda Haule ta soma murmusawa kana tace “Aminiyar Sirri.....”
Ya d’ago da sauri yana dubanta...
Haule ta kuma jinjina kai tace “Tabbas d’aurin gindi ta samu daga gareka ta fantsamo cikin rayuwarmu da taimakonka... Idan ban b’ata a lissafi ba itace wakiliyarka a wannan bak’in aikin da muka aikata....”
Katseta yayi cikin daka tsawa “Haule..!!!!”

Ko gizau Hajiya Haule batai ba saima murmusawa data kumayi kana tace “Bakaso ka bak’anta kanka a idanun danginka shine kai amfani da aminiyar sirri domin ta d’auki alhakin laifinka.... Ka sani munyi tarayya ne a wannan bak’in laifi kuma dawowar Ma’aruf ba rayuwarmu kurum yake barazanar tarwatsawa ba harda naka rayuwar... Kayi tunani idan d’an uwanka yasan abinda ka aikata ma d’ansa... Shin mai zai d’aukeka....? Kayi tunani idan mahaifiyarka tasan abinda ka aikata ma d’an d’anuwanka shin a wani sahu zata ijiyeka....? Idan ‘ya’yanka suka san wannan bak’in sirri naka shin da wasu idanu zasu kuma dubanka....? Duk wannan abin dubawa ne Alhaji.... Ni dama na riga nasan yanzu Hafiz ya gama tsanata domin kaw a nasa tunanin niceda alhakin gurb’ata masa rayuwa.... Yanzu idan wannan batu ya bayyana ya fito fili shikenan Hafiz zai tsana duka iyayensa, don haka musan abinyi... ‘Ya’yanmu bazasu tab’a sanin gaskiya ba....”

Baba Alhaji yayi shiru yana nazarin kalaman Haule.... Hannayensa hard’e ta baya kansa a k’asa, lokaci guda ya d’ago yana dubanta kana yace “Haule ki sani zuciyata ta cika da kishi da hassada a baya, karki mance yanda mahaifiyarmu keson Usman da d’ansa Ma’aruf, nayi tunanin idan na b’atar da d’ansa hakalinta zai dawo gareni da iyalaina amma koda yaushe mahaifiyarmu tafi fifita d’anuwana sama dani, a idanun danginmu gaba d’aya shi yakeda girman da ya kamata ace nikeda ita....” Shiru yayi na d’an lokaci kana ya kuma d’agowa ya dubi Haule yace “Ban tsammaci cewa Ma’aruf na raye ba harma zai dawo garemu.... Nayi tunanin kun gama dashi tun a wancan lokacin....”

Haule ta murmusa had’ida gyara zama tace “Aminiyar Sirri ita ta yaudaremu gaba d’aya.... Duk munyi tunanin Ma’aruf ya halak’a tuntuni, bata halaka shi ba saima tsiratar dashi da tai... Yanzu abu guda zamuyi mu wanke kanmu mu zame kanmu daga cikin laifin....”
Baba Alhaji ya dubeta yace kaman yaya

Please Login or Register in order to submit comment