Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tayi kana ta furta a hankali “Hajiya ina fatan babu saka hannunki a b’acewar Ya Ma’aruf....” Ta k’arashe tana mai lumshe idanu a hankali kafin ta mik’e don gabatar da sallar la’asar, tana idarwa tayi shirin islamiya abinta, tanajin Sahariyya da Hajiya na d’ibe mata albarka wai ta zama munafuka ta koyo salon munafunci ko kulasu batai ba ta fice abinta tanai masu addu’ar shiriya...
A can islamiyar ta had’uda Marliya yanda Marliya ke sanar da ita cewa an sallami Raihanah ta dawo gida, Najah tace zasu tafi tare idan an tashi ta duba jikin ‘yar uwar tata..,
Sosai abin kewa Marliya dad’i ganin yanda lokaci guda Allah ya shiryi Naja’atu ta dawo daga rakiyansu Hajiya....

***

Abbah da Mamy na zaune parlor suna firansu na mata da miji gwanin ban sha’awa Baba Alhaji yayi sallama, Mamy ta mik’a hannu ta janyo mayafinta ta rufa kafin Abbah ya basa izinin shigowa dukda ba jiran izinin nasa yake ba, da gadara ya shigo yana watsa masu kallo...
Mamy ta gaidashi ya amsa a ciki...
Abbah yace “Yaya kaine a tafe, sannu da shigowa....”
Baikai aya ba Baba Alhaji ya dakatar dashi da fad’in “Dakata Usman kada ka sake cemin Yaya... Ai baka d’aukeni matsayin Yayan ba.... Na tabbata har cikin ranka bakak’i ace kaine d’ah na fari a gidan nan ba, duk wasu d’awainiya da suka kamata ace ni ne nan na d’aukesu ka d’auka ka yafa ma kanka ba don komai ba sai don ka zamto abin tink’aho da alfahari a dangi koh, kana neman ka k’wace girman da Allah ya riga ya bani... Toh duk yinka Usman na rigaka zuwa wannan duniya kuma nine d’ah na fari a wajen iyayenmu kuma kai baka isa kayi komai akan hakan ba....” Ya k’arashe yana mai dukan k’irjinsa cikeda zafin rai....

Abbah bai tankasa ba har ya gama kana yace “Yaya ka zauna mu gaisa tukuna...”

“Aw mahaukaci wanda baima san abinda yake ba ka d’aukeni kenan, kasa su Ado sun rainani duk basu ganin girmana sai Naka shine yanzu bari ka nunawa d’anka Ma’aruf bani da daraja a gidan nan koh, ban tashi sanin cewa ya dawo ba sai yau... Sabida kafi k’arfi ka nuna masa cewa kanada Yaya koh, sabida ka sami d’aurin gindi daga wajen mahaifiyarmu koh...?”

Abbah na girgiza kai yake fad’in “Ba haka bane Yaya... Dama naso na d’aukeka na kai maka shi har gida n......”
Dakatar dashi Baba Alhaji yayi da fad’in “Bana buk’atar bayananka... Ina Ma’aruf d’in yake.....?”
Sai sannan Mamy da kanta ke k’asa tace “Ya fice amma inaji ba nisa yayi ba....”

Baba Alhaji ya kad’a kai kana yace “Dama idan ya dawo maza yaje gida ya sameni....”

Mamy ta jinjina kai tace “In sha Allahu za’a sanar dashi...”
Ko amsa bai basu ba ya fice ya nufi sashen Mamani kaman wani zai kifa....

Aunty Lami dake lab’e ta murmusa cikin zuciyarta tace “Aikin k’awata Haule yayi kyau kenan... Yanzu zan kirata na labarta mata don nasan wannan ba komai bane illa makircinta....” Ta k’arashe tana kuma sakin murmushi...

Mamani ta had’e fuska tayi kicin kicin tana aika masa mugun kallo....
Baba Alhaji yaci gaba da fad’in “Mamani kin kasa gane duk wannan sharrin d’an uwanane, ya rabani dake, ya rabani da ‘yan uwana su Ado yanzu yanaso ya d’auke d’iyata ya rabani da Raihanatu... Tinda an sallameta ta shige mu tafi gida Ta k’arashe jinyar acan.....”

Tsegege Mamani ke dubansa kana tace “Gafara kamin shiru shanyayye wanda Haule da bokayenta suka gama dashi... Toh bazata koma ba, nace bazata koma ba, ince sanda tana asibitin Haule ta hanaka kaje ka dubata sai yanzu ne zakazo kace ta koma gida... Salon Haule da asararrun ‘ya’yanka su k’arasata koh... Toh wllhi kaji na rantse ko bayan rainane ka d’auki rik’on Raihanatu ka maida hannun Haule Allah ya isa ban yafe maka ba....”
Baba Alhaji ya d’ago yana dubanta cikeda mamaki....
Mamani tace “K’wari kaji baninda nace ai... Tashi ka ficemin ka koma wajen Haule ka k’are can....”
Haka Baba Alhaji ya mik’e ya fice yana mai aikawa Raihanah da idanunta ke k’asa mugun kallo

Hawayene ke zuba a idanunta, kalaman Mamani akan mahaifinta yana mata zafi sosai, ko babu komai ko yaya yake tasan mahaifinta ne kuma bazata canza hakan ba....Kuma tabbas kalaman Mamani kayi tasiri a rayuwarsa...

Mamani ta dafata tace “Yaya dai Raihanatu jikin ne.....?”

Raiha ta girgiza kai a hankali tace “A’a Mamani....”
Mamani ta kuma dafata cikeda tausayawa tace “Karki damu kinji bazan tab’a bari Alhaji ya maidaki gaban Haule ba kinji koh....”
Raiha bata iya cewa komai ba sai sadda kai k’asa data kumayi...
Mamani ta mik’e tana fad’in “Ohni Halimatu toh yanzu waye zaike wanke ciwon naki gashi mun riga mun dawo gida, naga lokacin wankin ciwo naki yayi....”

Batakai aya ba suka jiyo sallamar bak’uwar murya, ba kowa bace illa Salma nurse daga asibitin da aka sallami Raihanah....

Mamani ta washe baki tana fad’in “A’a lale lale... Ma’aikaciyar jinyace a gidan namu....”

Salma na murmushi ta ida k’arasowa ciki tana mai gaida Mamani...
Mamani tace “Yanzu kuwa nake jajen waye zai wanke ciwon jikata tinda mun komo gida saiga Allah ya kawoki....”
Salma ta kuma murmusawa tace “Ai Mamani tuni Dr Sameer ya d’aukeni hayar yin hakan....”

Raiha dake zullumin wankin ciwo sabida zafi tayi saurin d’ago kai tana duban Salma...
Salma taci gaba da fad’in “Mamani Dr ko bai biyani ba zanyi duk abinda ya sakani sabida tsananin kirkinsa da ganin ya taimaki duk wanda ke cikin matsala... Balle ace har ya zab’eni na kula da k’anwarsa ai ni abin alfaharine a gareni...” Tanayi tana sassane kai alamun kunya...

Mamani tace “Allah sarki Ma’aruf jikana, ta ko ina yabonsa ake... Allah dai yaci gaba da karemin shi....”

Salma ta amsa da “Ameen Mamani....” Kana takai dubantaga Raiha tace “Raihanah ya jikin... Nazo mu fara koh...”

Murmushi mai kamada yak’e Raihanah ta mata kana tace “Da sauk’i sosai....”
Salma ta murmusa kana ta kwab’e mayafinta ta shiga had’e kayan dressing...

***

Shi kad’ai yake huci yana tururi bayan yaji labarin da Hajiya ta zayyane masa gameda mutuwar d’iyarsa Kausar cewa Zulfa’u da k’anwarta Nabilah su sukazo suka tari fad’a da tashin hankali garin fad’a suka jefa masa d’iya a tukunya... Kada ya zargi kowa da laifin kisan d’iyarsa face Zulfah da danginta....

Ko sallama bai sami zarafin yi ba ya fad’a sashen Mamy yana mai dokawa Zulfa’u kira cikin tsananin karaji da b’acin rai...
Babu shiri Nabilah ta fito jin muryar Ya Hafiz kaman zai d’age gidan....

“Ya Hafiz lafiya kake kiran Addah Zulfah haka....?” Nabila tace tana mai dubansa cikeda mamaki ganin yanda k’wayan idanunsa suka kad’a sukayi jazir....

SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_



58


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Ko zarafin amsa Nabilah bai samu ba yaci gaba da dokawa Zulfa’u kira cikin tsananin karaji...
“Ki fito nan ki fuskanceni Zulfa’u...!!”

A tare Aunty Lami da Zulfah suka k’araso haraban sashen, ganin yanayin Hafiz ya mugun d’agawa Zulfah hankali... Aiko kaman wanda yake jira yayo kanta gadan gadan Aunty Lami tai saurin shiga tsakani....
Fad’i take “Hafiz lafiyarka.... Wai meke faruwa ne l....?”

Yana nuna Zulfah da d’an yatsa cikin tsananin huci yake furta “Bazan tab’a yafe miki ba Zulfa’u, bazan tab’a yafe miki ba... Kin cuceni kin rabani da gudan jinina Kausar.... Why...? Meyasa Zulfah... Sabida na sakeki, sabida baki k’aunata shine bari ki d’au fansa akan d’iyata... Kin cuceni... Ban tab’a danasanin had’a iri dake irinta yau ba.... Kuma wllhi kinj na rantse sai na d’au fansar mutuwar Kausar...!!”

Zulfah dake tsaye hawaye na gangaro mata cikeda tsananin mamaki take fad’in “Ya Hafiz mai kake nufi... Shin kana tunanin zan iya kashe rai balle gudan jinina... Ya Hafiz Kausar rayuwatace, ta yaya zakai irin wannan tunanin....?”

“Shut up...! Rufewa mutane baki munafukar banza....!!” Ya k’arashe yana mai zabura zai finciko Zulfah dake b’oyewa bayan Aunty Lami... A daidai lokacin da Sameer ya shigo... A d’ari yayi jifa da jakar hannunsa ya finciko Hafiz ya watsa shi gefe guda....

Hafiz da baisan ko wanene Sameer ba ya d’ago yana mai ci gaba da huci yayi kan Sameer ya dunk’ule hannu yana k’ok’arin kaiwa Sameer naushi Sameer ya rik’e hannun da k’arfin gaske shima hucin yake su duka biyu suna aikama juna muguwar kallo Hafiz yake furta “And who do you think you’re..? Kai waye da zaka shiga tsakanin miji da mata... Auho d’aya daga cikin ‘yan iskan samarukan nata masu bin matan mutane ne koh... Toh baka isa ba bari kaji na fad’i maka....” Ya k’arashe yana kokawan k’wace hannunsa daga rik’on da Sameer ya masa amma ya kasa ko guzau...

Sameer bai daina huci ba yana kallon cikin k’wayan idanun Hafiz yake fad’in “The moment you intend to hurt my sister again sannan ne zaka san the real meaning of the word pain... I’lol forget we are cousins....!!!!” Ya k’arashe yana mai jifa da hannun Hafiz d’in wanda saida ya kusan fad’uwa k’asa

Gaba d’aya duban Sameer d’in suke da tsananin mamaki don basu tab’a ganinsa cikin irin wannan yanayi ba, babu ya Aunty Lami wacce tuni taji ‘yan hanjinta suna juyawa, yanda taga kalan zuciyar Sameer tabbas duk randa yasan sune sukai sanadiyar rabuwarsa da iyayensa kashinsu ya bushe don sosai ta razana da ganin fushinsa....
Nabilah kaw tamkar ta zuba ruwa a k’asa tasha haka taji... Kame hannaye kurum tai tana kallon yanda yau Yayansu ke karb’awa ‘yar uwarta ‘yanci irin yanda babu wanda ya tab’a tsaya mata...

Hafiz da yanzu ya fahimci ko wanene Sameer mik’ewa yayi yana sakin murmushi mai kamada warning, kana yace “Aw ashe ka dawo kenan... Ka gama yawon barikin naka ka dawo... Sai yanzu ne zaka karb’a mata ‘yanci... Ka makara ai....”
Bai kai aya ba Sameer dake tsananin huci ya tako gabansa a hankali kana yace “Do not try me....!”

Hafiz ya kuma murmusawa kana yace “Your Sister is a monster Ma’aruf... She’s nothing but a curse...!” Wata wawiyar naushi da Sameer ya aikawa Hafiz a baki da hanci ya hanasa ci gaba da magana...
Hankali tashe Zulfah ta shiga janye Yayanta tana kuka sosai take fad’in yayi hak’uri... Aunty Lami ta fice a guje kiransu Mamy a can sashen Abbah don tuni Hafiz ya fad’i k’asa jini na fitowa daga bakinsa da hancinsa...

Mik’ewa yayi a zabure yana fad’in “Your Sister is a killer... She killed my daughter... Ta kashe min d’iyata ta kashe Kausar...!!!”

Sameer na huci Zulfah na kuma janyesa yake fad’in “You take back what you said you imbecile....!”

Daidai lokacin su Najah da Marliya da shigowarsu kenan daga Islamiya ....
Najah da tuni ta soma hawaye ta k’arasa a guje ta rik’e Yayanta Hafiz... Lokaci guda take fad’in “Yaya Hafiz Zulfah batada laifi... Ka daina cewa ita ta kashe Kausar.. Kausar lokacin mutuwarta ne yayi....”

“Shut up Naja’atu you don’t know anything... That monster killed my daughter... Hajiya ta fad’a min komai how my daughter die because of her selfishness...” Ya k’arashe yana nuni da Zulfah dake tsananin kuka....

Cikin kuka Najah ke fad’in “Addah Zulfah batada laifi, idan ma masu laifin kake son sani ba kowa bane illa Matarka Sawwama da k’anwarka Sahariyya, those two are the cause... Su suka jefa Kausar da Raihanah cikin ruwan zafi... Su zaka tuhuma not Addah Zulfah...” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya...
Jikin Hafiz yayi sanyi sosai, hawaye suka ci gaba da zuba masa.... Ya d’ago idanu yana duban Najah wacce itama hawayen take .... Naja’atu ta jinjina kai a hankali kana ta sassauta murya tace “Yaya Addah Zulfah mahaifiyar Kausar ce bazata tab’a kasheta ba... Tana k’aunarta fiye dakai... Rabatada d’iyarta da akai lokacin da take raye ba’a barsu sun kasance tare ba ya isa jefata cikin damuwa.... This is not you Ya Hafiz, na tabbata deep inside kanada zuciya mai kayu....”

Ba Hafiz dake tsaye yana zuban hawaye ba harta Sameer saida yaji gaba d’aya gabb’ansa sun masa sanyi, suna gani Naja’atu ta janyo d’an uwanta suka fice tamkar rak’umi da akala...
Sameer ya dube ‘yan uwan nasa da gaba d’aya sukai tsaye suna dubansa in a strange way.... Dafa Zulfah da har lokacin zuban hawaye take yayi, a hankali ya furta “Everything will be alright kinji koh... I’m here now, bazan kuma barin wani yaci zarafin d’aya daga cikinku ba... Never...”
Zulfah ta rintse idanunta a hankali yayinda Marliya ta k’araso ta janye hannunta suka shige d’aki..
Nabilah ta saki murmushi tana mai kallon Sameer har ya b’ace ma ganinta kana tabi bayansu Zulfah da Marliya...

Aunty Lami data ruga a guje kiransu Mamy ashe ba Mamy ta tafi kira ba lab’ewa tai tana kallon yanda ta kaya tsakanin Sameer da Hafiz... Ta shafe zufan da ya keto mata had’ida sauk’e nannauyan ajiyan zuciya.... Tana ganin sanda Sameer ya nufi sashen Mamani kana ta sad’ad’o ta wuce d’aki ta lalumi waya tana neman layin Hajiya Haule....

***

A tare Hafiz da Najah suka shigo cikin gidan, Najah na gaba Hafiz na biyeda ita... Hajiya dake zaune tsakar gida tana faman sak’e sak’e tana ganin shigowarsu ta mik’e don dama shigowar nasu take jira tunda tuni Lami ta kirata ta zayyane mata komai...
Naja’atu batai aune ba Hajiya ta janyota ta shiga lapta tana fad’in “Shegiya mai halin annamimanci.. Ki rasa ma wanda zaki k’ulla sharri sai ‘yar uwarki ta jini... Wato Zulfa’u da danginta sun fiye maki naki ‘yar uwar munafuka annamimiya...” Ta rarumo muciya zata jibga mata Hafiz ya rik’e muciyar da iya k’arfinsa...
Hajiya ta d’ago tana duban Hafiz shaye da mamaki cikin yanayin da Bata tab’a ganinsa a irinta ba.. Idanunsa sun sauya launi sunyi jajazir gaba d’aya haka nan fatar jikinsa tayi ja, jijiyoyin jkinsa sun mimmik’e banda wani irin muguwar kallo da yake watsawa mahaifiyar tasa...
Hajiya ta soma fad’in “Hafiz kada ka yarda da wannan yarinyar munafukace... Ta guje ‘yan uwanta na jini ta zab’i ‘yan uba... Ka yarda dani d’ahna nice mai fad’i maka gaskiya....”
Bai bari takai aya ba cikin dakewar murya yake furta “Ina take...!!!?”
Hajiya tace wafah....
“Ina Sahariyya Hajiya..!!!?” Wannan karon cikin tsananin daka murya yayi maganar....
Hajiya ta rasata cewa sai inda inda da take...
Fincike muciyar yayi ya soma tafiya yana huci tamkar zai kifa k’asa....
Sahariyya dake kwance saman gado earpiece manne a kunne tana sana’arta ta jin kid’a sai sauk’ar muciya taji a gadon bayanta tamkar sauk’an aradu babu zato balle tsammani...
Sahariyya ta mik’e a gigice sabida wani irin azaban zafi dataji, ta saki ihun azaba had’ida jifa da wayar hannunta...
Hajiya da Najah suka nufo d’akin a guje jin irin k’aran da Sahariyya ta saki....
Kururuwa taci gaba da yi tana fad’in “Yaya Dan Allah kayi hak’uri, Wayyo gadon bayana wayyo k’afata... Hajiya kizo ki ceceni....”
Duk k’ok’arin Hajiya ganin ta janye Hafiz daga bugun da yake wa Sahariyya tamkar wanda ya sami busasshen hatsi amma ta kasa janyesa....
Duk yanda ya samu bugu yake tamkar wanda aka aiko, kai da gani kasan dukan huce takaici yake....
Najah da taga za’a kashe ‘yar uwarta cikin sauri ta tari dukan ta kare Sahariyya tana kuka sosai ta durk’usa a wajen tana fad’in “Yaya Dan Allah kayi hak’uri... Ya isa haka nan please Yaya Hafiz....”

Badon yaso daina dukan ba sai don ganin Naja’atu na kuka durk’ushe gabansa yasa shi jifa da muciyar, ba tareda ya kuma furta koda kalma ba ya fice daga gidan....
Naja’atu tayo kan Sahariyya dake kwance tamkar bata numfashi ta shiga jjjigata tana kirawo sunanta, a guje ta tafi d’ibo ruwa don ta yayyafa mata domin da alama Hafiz ya sumar da ita...

Hajiya ta d’aura hannu aka tana kururuwa tana fad’in wayyo ita Haule ta shiga uku....

***

Sameer na shiga sashen Mamani ya samu Salma zata tafi ta gama dressing ma Raihanah... Ta gaishesa ya amsa sama sama, bata tsaya jan dogon zance ba tai masu sallama ta wuce don ta lura da mood d’in Sameer d’in...

A d’aya daga cikin kujerun parlorn ya zauna yana mai duban sashen da Raihanar take, ita ta soma gaisar dashi ya amsa a tak’aice kana ya mata yaya jiki tace da sauk’i...
Shiru na wasu ‘yan dak’ik’ai ya biyo baya dashike Mamani na k’uryar d’aki bataji shigowar Sameer d’in ba...
Gaba d’aya Raihanah a tsarge take da kasancewarsa a wajen... Ko d’ago idanu ta kasa don wani irin naiuyinsa takeji sosai... Idanunta suka sauk’a kan hannunta da yaketa dunk’ulesu nan ta hangi jini na d’iga a hannun nasa gabanta ya yanke ya fad’i... Kar dai ciwo yaji....


SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_




59




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



NOT EDITED




“A’a Babban Mai gidan an shigo...” Mamani tace sanda take d’age labulen d’akin, Raiha dake k’ok’arin janyo bandage ta saki a hankali ganin Mamani ta fito...
Sameer yai k’ok’arin saita kansa kana ya saki murmushi a hankali yana mai gaida Mamani...
Birki tai ganin jini a hannunsa, ta shiga salati tana sallalami tana tambayarsa mai ya sami hannunsa....
Duk sai yaji wani iri ganin ba wani babban ciwo bane d’an karjewa ne wanda baida shakku dakan bakin Hafiz da yayi ne hak’waransa sukaji masa ciwon...
Ganin hankalin Mamani ya tashi sosai ya sanyashi kwantar mata da hankali da nuna mata ba wani ciwo bane...
Mamani tace “Yo dole in damu mana Maigidan, bakasan ko k’uda banaso ya tab’aka ba balle ciwo.... Bani nan na gani...” Ta k’arashe tana janyo hannun.. Ba wai don Sameer d’in yaso ba, abin na Mamani ya soma damunsa gaba d’aya maidashi take saikace wani jinjiri, kodai don bai girma dasu bane take masa hakan k’ilan...
Raihanah takai dubantaga hannun nasa sanda Mamani ke jujjuyawa...
Ta juyo ta dubi Raiha tace “Dubu bani abin wanke ciwon naki na wanke masa...”
Raiha ta amsada “Toh Mamani tamkar wacce take jira...
Sameer yaga bilhakk’i da gaskiya Mamani take....
Cikin sauri yace “A’a Mamani ai ba sai an wanke ba ciwon ba sosai bane, bendejin ma ya isa....”
Mamani tace “Ka tabbata dai ko...?”
Sameer ya jinjina mata kai, ta amshi bandage d’in hannun Raiha tana k’ok’arin warwarewa amma bata iya ba... Ta yab’e baki tace “Ohni Halimatu ai kaga tsiyar abin nasaran naku, ni ya ake kwancewa....”
Sameer ya saki murmushi da gefen bakinsa ganin yanda take juya bandage d’in...
“Ke Dubu zoki taimaka min, zaki iya tashi aiko...?”
Raihanah ta amsada “Eh Mamani...”
Shiko Sameer kallo ya bita dashi ganin ba k’oshin lafiya bane da ita, idanunsu suka had’e waje guda, Raiha tai saurin sadda nata idanun....
Sameer ya maido da dubansaga Mamani kana yace “Karki damu Mamani zan iyayi....”
Mamani tace “A’a ta yaya zaka iya bayan hannunka guda da ciwo, Dubu maza warware ki d’aure masa barin nemo masa maganin zogi, ina tsamman akwai cikin d’aki...” Ta k’arashe tana mai shigewa d’aki...
Sameer ya tsaya kurum yana kallon ikon Allah wai shi za’a nemowa maganin zogi, k’ila Mamani ta mance shi likitane...
Ya maido da dubansaga Raiha dake durk’ushe gabansa tana warware bandage d’in a hankali tamkar mai tausayin bandage d’in... K’uri Sameer ya mata yana kallon yanda take gudanar da al’amranta cikin natsuwa da tsananin sanyi...
Ya d’anyi gyaran murya a hankali kana yace “Barshi haka nan... Give me that... Jeki ki huta I can do it...”

Ta girgiza kai a hankali kana tace “A’a zan iya Yaya....”
Ya kafeta da idanu kana ya furta “Are you sure...?”
Ta jinjina kai a hankali tana mai k’ak’aro murmushi bacin kaw banda bugu babu abinda k’irjinta keyi...
Mik’ar mata da hannun yayi yana mai ci gaba da duban yanda take zagaye hannun nasa da bandage... Baisan mai yazo cikin zuciyarsa ba amma ba kowa ya tuna ba illa matarsa Siyama, shin ko yaya zata amshi ‘yan uwansa...? Wannan tambaya ya jima yana yawo a kwanyarsa, sanin hali da yanayin matar tasa....
Har Raihanah ta kusan ida zagaye yatsun hannun nasa da bandage d’in kana ta sinkayo muryarsa yana jefo mata tambaya....
“Ya jikin naki...? How are you feeling now...?”
Idanunta naga abinda take tace “Da sauk’i sosai....”
Sameer ya jinjina kai yace “Zogin yana raguwa....?”
Nan ma jinjina masa kai tayi still idanunta naga aikin da take kana tace “Eh ya ragu, bai ciwo sosai saiko da dare....”
Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “You’re lucky skin d’inki nada kyau....”
Wannan karon d’agowa tai suka had’a idanu...
Kawar dakai gefe yayi tamkarma bashi yai maganar ba, daidai sanda ta ida rufe masa ciwon...
Ba tareda ya dubebtan ba yace “Kwanan nan zai warke gaba d’aya In sha Allah kinji koh....”
Ta jinjina kai a hankali...
Duban hannun nasa yayi yanda ta rufe masa tsaf kana yace “Thank you...”
Bata iya cewa komai ba sai k’ok’arin mik’ewa da tayi a daidai lokacin da Mamani ta fito tana fad’in ta nemi maganin nata sama da k’asa ta rasashi taci gaba da fad’in “Yanzu haka Sakina ce ta shigo ta d’auka kai wannan yarinya tayo halin ubanta Ado, haka nan nayi fama dashi sanda yake k’arami, ba dai na aje abin amfanina ba sai na rasashi ga b’arna kaman b’era....”
Sameer ya shafi sumarsa a hankali da d’aya hannun jin Mamani na maganganu da bai kamata suji ba, da gani wannan tsohuwa ansha fama da ita....
Mik’ewa tsaye yayi yana fad’in “Babu damuwa Mamani kar ki damu zan sha inadasu a gida... Yanzu zan zaga ko wane k’ofa ne na gaishesu kafin na wuce gidan Baba Alhaji na masa gaisuwa shima...”
Mamani ta wage baki tace “A’a lallai kaga d’an Albarka... Yawwa nace ba....”
Sameer ya d’ago yana dubanta...
Mamani taci gaba da fad’in “Ya kamata ka dawo cikin gida nan da zama, ga sashen dake gefena nan babu kowa ciki dama Alk’ali ne zai gyare min na koma ciki amma yanzu tinda Allah yayi ka dawo sai ka dawo ciki ka zauna, kaga sai mu samu musan iyalin taka sosai koh....”
Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “Babu damuwa Mamani zan sami Abbah da maganar...”
Mamani ta fad’ad’a murmushinta tana fad’in “Allah sarki ashe dai bazaka k’i gida ba, ai yanda kake d’an gayun nan na zaci bazakazo cikinmu ka zauna ba, Allah Ubangiji dai shi maka albarka yaci gaba da kare mana kai daga duk mai nemanka da sharri...”
Sameer yana mai amsa mata da Ameen yake ficewa amma har ya fice Mamani batai shiru ba tana mai ci gaba da masa addu’an kariya da tsari daga mugu...

***


Shagon Magaji abokinsa ya shige daga gidan Hajiya, yanda Magaji ya gansa yasan wani babban abu na damunsa ga fuskarsa a kumbure...
Magaji ya janyo benchi ya zauna kusan Hafiz kana yace “Duk wanda ya ganka Hafiz yasan kana cikin matsanancin matsala, abokina Dan Allah ka sanar dani meke damunka, naji kace fuskarka had’ari kayi, amma fah Hafiz ba fuskarka kurum ba ga dukkan alamu kai d’in cikin damuwa kake, ni tun bayan rabuwarka da Zulfa’u ban kuma gane kanka ba, ga wannan matar taka da maganganu keta fitowa akanta... Hafiz Wai Dan Allah meke faruwa dakai..... Ko kanaso kacemin har yanzu bakai tawakkali da mutuwar d’iyarka bane...?”

Kafin Magaji yayi shiru kuka mai k’arfi ya kufce wa Hafiz... Jikin Magaji yayi sanyi sosai ganin yanda Hafiz ke kuka da iyaka iyawarsa.... Bai hanashi ba bai kuma furta komai ba sai shiru da yayi yana dubansa cikeda tausayawa... Saida Hafiz yayi mai isarsa kana ya tsagaita....
Magaji ya shiga shago ya kawo masa ruwa mai sanyi kana yace “Sha wannan...”
Babu musu Hafiz ya amsa ya kifa kansa bai d’aga ba saida ya shanye tass...
Magaji ya komo gefe da Hafiz ya zauna kana yace “Kayi hak’uri Hafiz ita rayuwar nan gaba d’ayanta daka gani jarabawace, duk wanda kaga yana taka doron k’asa toh fah cikin jarabwar mahaliccinsa yake walau na jin dad’i koko akasinta, Hafiz duk yanayi da kaga bawa na ciki toh ba komai bace face jarabawa, ta ko ina za’a jarabcemu, ta kasuwancimu ne a’a ta iyalanmu ne koko ta lafiyarmu da dukiyarmu, kai komai da kake gani za’a iya jarabtarmu akai, wasu lokutanma har kayi tunanin ko kai kad’ai ake turoma irin wannan jarabawa... Toh fah ba kai kad’ai bane, hasalima idan kaji halin da wani yake ciki zakace naka ba komai bane... Toh shi haka Allah yake gudanar da al’amaransa tsakanin bayinsa, kai k’ok’ari kaci jarabawarka a duk halinda ka tsinci kanka ciki, ba ina cewa lallai sai ka sanar dani abindake damunka bane, amma ka sani a duk lokacin da kake son yin maganar zaka iya samuna, zan saurareka In sha Allah kuma na baka shawari daidai gawardo... Allah shi mana maganin matsalolinmu...” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye don attending customer...

Hafiz ya lumshe idanunshi hawaye suka kuma zubowa zuciyarsa nai masa wani irin d’aci, tinda yake a rayuwarsa bai tab’a dayasanin auren Sawwama ba irinta yau, baijin zai iya komawa gida ya fiskanceta a yau sabida tsananin zogi da rad’ad’i da zuciyarsa ke masa, yasan idan ya fuskanci Sawwama a halinda yake ciki yanzu komai ka iya faruwa tabbas zai iya kasheta har lahira, toh amma bazaiso yayi hakan ba sabida wa’azin da Magaji ya masa tabbas ya shiga jikinsa, bazaiso ya kuma wani aikin danasanin ba irin wanda ya taptapka a

Please Login or Register in order to submit comment