Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da nai a baya... Haule da d’anta sun sabautar da Zulfa’u ta shiga duniya babu wanda yasan k’anda take, Hafizu ya saki Zulfa’u ya auro Ahalil kitabi... Wayyo ni Halimatu kaicona...

Tinda ta soma magana k’afafun Abbah suka gaza d’aukarsa, tabbas idan akwai babban mai laifi toh fah shine, shine ya tilastawa Zulfa’u auren Hafiz dukda cewa ba sonshi take ba sannan ya mata baki cewa idan ta kashe aurenta saidai ta nemi wani uban bashi ba kuma kadata kuskura ta dawo masa gida daidai da rana guda bai tab’a tuntub’ar yaji wani irin zaman aure d’iyarsa keyi ba, bai tab’a bata dama ta kawo kokenta wajen mahaifinta ba, a koda yaushe Hafiz ne yayi daidai a idanunsa... Shin wane irin mahaifi ne shi, anya hakkin Zulfa’u zai barsa a rayuwa, abu mai kaman wuya kaga hawaye idanun Abbah sai gashi k’walla sun ciko idanun nasa....
Gijif ya zame cikin kujera yana mai furta “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un....” Kalma bayan kalma a hankali can k’asar mak’oshinsa....

“ Kanajina Sarki wllhi Raihanah bazata koma gidanka ba kuma d’anka sai ya nemomin jikata yanda ta shiga ta fita idan kuma ba haka ba kotu ta rabamu....”
Marliya da shigowarta parlorn kenan taji ana zancen Addarta Zulfah ta b’ace don tunda taji Raiha na gidan ta nufi sashen Mamani ta tarar basu a sashen shine ta nufo parlorn Abbah don taji muryar Mamani a nan....
Take idanun Marliya suka kawo ruwa, gabanta yaci gaba da bugawa cikin wane irin kuka ta fice a parlorn ta nufi sashen Mamy tana kuka tana k’wala mata kira...

Daga Mamy har Nabilah da Sameer gaba d’aya mik’ewa sukai suna tambayar Marliya lafiya...
Cikin tsananin kuka Marliya ta fad’a jikin Mamy tana shessheka take fad’in “Mamy Addah Zulfah....!”

Mamy da gabanta ya yanke ya fad’i saurin d’ago Marliya tai tana tambayarta “Addah Zulfah...? Mai ya sami Zulfa’un... Marliya ki sanar dani mai ya sami d’iyata....

Ai Marliya bata kai ga bata amsa ba Raihanah ta shigo a guje tana kuka sosai take fad’in “Abbah ne... Abbah ya fad’i bai numfashi...”

Mamy tama rasa wanne zatai, ai a d’ari Sameer ya fice ya koma sashen Abbah suka d’unguma gaba d’aya kowa bai cikin hayyacinsa sai koke koke da salati kakeji..
Kankace mai Sameer ya shiga k’ok’arin ceto rayuwar Abbah da yai wata irin sumewa dafe da k’irjinsa...
Mamani hannu aka take kuka tana fad’in Baba Alhaji ya fice mata bata koh k’aunar ganinsa, tuni ya cikawa babbar rigarsa iska ya fice yana mai kuma jaddada masu sai ya dawo ya d’auki d’iyarsa....
Dole Sameer ya saka Abbah a mota Mamy na rik’edashi suka fice, suma su Nabilah tuni suka tari adaidaita sukabi bayansu cikin kuka shab’e shab’e....



SameenAleeyou📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*41*


*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



NOT EDITED


Nan da nan babu b’ata lokaci aka soma duba Abbah, daidai da dak’ik’a Sameer bai bar kan Abbah ba taredashi ake komai sanin cewa shima likitan ne....
Su Mamani dasu Nabilah an rasa mai dannan wani cikinsu sai kuka suke shab’e shab’e, dama dama ma Mamy itace mai d’an k’arfin halin juriya da karanto addu’o’i dukda cewa abubuwa da dama ne sukai mata caa cikin zuciyarta, ga Abbah kwance rai a hannun Allah ga kuma maganar b’acewar d’iyarta Zulfa’u, duk juriya da jarumtaka irinta Mamy saida k’walla suka shiga gangaro mata cikin zuciyarta take furta “Ya Allah ka dubemu ya Allah kar ka d’auki mijina yanzu, Allah ka d’aga kafad’unshi ya Allah... Allah kar ka bari bak’in tarihin da ya auku shekaru talatin baya ya maimaita kansa, duk yanda Zulfa’u take ka bayyana mana ita.... Bazan iya jure rashin wata d’iya ba....” Ta k’arashe cikin tsananin kuka wanda yasa Marliya da Nabilah k’arasowa suka rungume mahaifiyarsu suna kukan tare...

Kan kace mai asibiti ya cika da dangi idan ka d’auke zuri’an Baba Alhaji wanda su kad’aine basu a wajen, bayan shud’ewan wasu dak’ik’ai Sameer ya fito daga d’akin da Abbah yake, gaba d’aya suka mik’e suna tambayarsa “Dr wane hali yake ciki...?”

Sameer ya soma calming nasu a hankali “Ku kwantar da hankulanku, his condition is stable now, daga yanzu zuwa ko wane lokaci zai iya farkawa.....”
Gaba d’aya suka shiga jero hamdala suna godiyawa Sameer...
Mamani ta kafesa da idanu tamkar mai tunanin wani abin, hannayen Sameer d’in ta rik’e tana mai furta “Ubangiji ya saka maka da mafificin alheri likita ceton rayuwar d’anah da kayi...”
Sameer ya murmusa a hankali yana mai duban tsohuwar wacce kallo guda ya mata yaji zuciyarsa ya natsu da ita, a hankali yake furta “Babu komai Baaba ai Abbah tamkar mahaifi na d’aukeshi, ku daina min godiya dan Allah...”

Mamani ta jinjina kai tace “Iyayenka sunyi sa’an samun d’ah d’an albarka irinka, kaga ba irin jikana Hafizu ba wanda ya zama shanyayye watsattse shida mahaifinsa....”
Jin zata saki layi yasa Baffah Wada saurin kamota ya zaunarta yana fad’i a hankali “Mamani asibiti muke bai kamata kina maganganu haka ba...”
“Yo sai mai k’arya na fad’i....” Ta fad’i tana watsawa Baffah Wada muguwar kallo ta wafce hannunta ta k’arasa saman benci ta zauna tana mai ci gaba da surutanta...
Shiko Sameer ba tareda ya fahimci maganganun nata ba ya d’an saki murmushi kana ya koma d’akin da Abbah yake....

Kwance ya sameshi idanunshi a rufe na’uran bature naci gaba da aiki....
Zama yayi daga gefenshi had’ida k’ura masa idanu, shi kad’ai yake ayyana abubuwa da dama cikin zuciyarsa, a hankali Sameer ya tsinci kanshi yana mai kai hannayensa saman na Abbah ya dafa a hankali... Hannayen nasa sun jima saman na Abbah kafin daga bisani ya soma k’ok’arin janye su.....
Kaman daga sama yaji Abban ya rik’e hannayensa gam yana mai furta “Ma’aruf kar ka tafi ka barni, nasan zaka dawo garemu... Na jima da ayyanwa cikin zuciyata cewa INDA RAI, DA RABON watarana ka dawo... Kar ka kuma tafiya D’ah nah....”

K’wallan da Sameer ke rik’ewa suka shiga gangarowa, inama ace da gaske shine Ma’aruf d’in da suke nema, inama ace da gaske sud’in ne iyayensa, baiso yasama ransa hope d’in da ba haka bane... A hankali shima ya damk’e hannayen Abbah lokaci guda hawayen Sameer suka d’iga saman hannun Abbah wanda ya sanya Abbah bud’e idanunshi...
K’uri yayiwa Sameer shima Sameer d’in Abbah ke kallo...
Abbah yai k’ok’arin mik’ewa Sameer ya saurin taimaka masa yana mai goge hawayen fuskarsa don baiso Abbah ya fahimci hawayen nasa...

Abbah bai daina nazarin Sameer ba yana mai dubansa... Sameer ya kula da hakan duk sai yaji ya kasa sakewa a hankali ya soma k’ok’arin mik’ewa yana fad’in “Family d’inka gaba d’aya suna nan barin sanar dasu ka farka....”

Mik’ewan da zai yaji Abbah ya rik’o hannunsa guda, ya tsaya cak k’irjinsa naci gaba da bugawa... Abbah na daga kwance yace “Sameer kaima zuri’ata ne, daga sanda Allah ya kawoka cikin rayuwarmu ka zama family kaima, na gode da taimakon ka gareni, da ace baka nan kusa da bamusan abinda zai faru ba....”

Sameer ya juyo a hankali yana duban Abbah kana ya sakar masa murmushi, bai iya furta koda kalma ba sabida wasu abubuwa da yakeji suna fizgar masa lokaci guda...
Abbah yaci gaba da fad’in “Kai hak’uri abubuwan daka tadda suna faruwa damu nida zuri’ata... Nasan akwai abubuwa da dama da bai kamata kaga suna faruwa ba amma ka sani Allah shike gudanar da al’amaran bayinsa yanda yaso, shike jarabtan bayinsa da jarabawa irin wacce basuyi tsammani ba... Kayi hak’uri Sameer....”

Girgiza kai Sameer yai yana mai kuma dafa hannayen Abbah yake fad’in “Abbah kowa a rayuwar nan nada kalan nasa damuwan sannan kaman yanda kace Allah shike jarabtan bayinsa ba tareda shawarin kowa ba, ka daina bani hak’uri kaji Abbah...” Shiru na wasu ‘yan dak’ik’ai suka gifta kan Abbah a k’asa kafin Sameer d’in ya d’an kuma gyaran murya yace “Abbah likita ya tabbatarmin kana buk’atan rage yawan tunani sabida zuciyarka datayi weak, idan har bakai k’ok’arin rage damuwa da tarin tunani ba kana iya samun bugawar zuciya wanda sam bama fata, so try as much as possible kaga ka rage yawan tunani....” Ya k’arashe cikin kwantar da murya mai nitsa zuciya...

Abbah ya d’ago yana duban Sameer d’in kana yace “Anya Malam Sameer zan iya cire tunanin Zulfa’u cikin zuciyata bayan a lokacin da ya kamata na kasance mahaifi na k’warai a gareta ban kasance ba... Na muzguna mata da yawa, na bada gudummawa mai girma wajen ganin rayuwarta ta salwanta... Nabi sharrin shaid’an da son zuciyata, shin kana tunanin Zulfa’u zata yafe min.... Sam ban kasance mahaifin da zatai alfahari dashi ba.... Ni ne jigo na fad’awarta rayuwar k’unci data tsinci kanta ciki a yau... Kaicona...” Muryarsa ta shiga rawa sosai hawaye na gangaro mashi...

Jikin Sameer ya kumayin sanyi da al’amarin Abbah.... Ya zauna gefe dashi kad’an yana bashi baki...
“Abbah ka daina fad’in haka, dukda zamata dakai na d’an lokaci ne k’ank’ani, na fahimci kaid’in mutumin k’warai ne wanda ko wane d’ah zai alfaharin samunka matsayin mahaifi....”
Abbah ya tsareshi da idanu yana mai girgiza kai kana yace “Sameer zan sanar dakai komai, kama daga b’acewan d’anah Ma’aruf har izuwa irin rik’on da na baiwa sauran d’iyoyina da Allah ya damk’amin su matsayin amana na kumayi watsi da wannan nauyi mai girma da Allah ya d’auramin duk a rashin d’ahnah Ma’aruf....”
Shiru Sameer yai yana duban Abbah zuciyarsa bata daina raunana ba, hawaye basu daina zubo masa ba a lokacin da Abbah ke sanar dashi yanda ya watsar da d’iyoyinshi mata duk akan rashin Ma’aruf, sosai ya tausayawa Abbah da rayuwar da ahalin gidansa suka tsinci kawunansu ciki....
Jiki a sanyaye Sameer yace “Shin idan Ma’aruf ya dawo gareku kuna tunanin zai yafe maku k’ask’anta rayuwar k’annensa da kukayi duk a sabida rashinsa...? Shin da wasu idanu zaku duba Ma’aruf da ‘yan uwansa...? Shin meye laifin ‘yan uwan Ma’aruf....?” Tambayoyin da suka kuma sanya Abbah zuban hawaye sosai yayinda shima Sameer d’in ke zuban hawaye....
Aljihun gaban rigarsa Abbah ya zira hannu ciki ya zaro wata hoto ya mik’awa Sameer kana yace “Tsawon rayuwata a koda yaushe Ma’aruf na ajiye gefen zuciyata ban tab’a canzawa hoton nan ma’ajiyi ba daidai da rana guda tun bayan b’acewarsa... Inada yak’ini d’ahnah zai saurareni zai kuma yafemin...”
Duk maganganun da Abbah keyi idanun Sameer naga hoton k’aramin yaro da bazai wuce shekaru biyu zuwa uku ba dake rik’e hannunsa... Hawayensa suka k’aru, k’afafuwansa suna barazanar kasa d’aukarsa...
A hankali cikin rawar murya yaceda Abbah “Shin wannan shine d’anka Ma’aruf...?”
Abbah ya jinjina kai a hankali kana yace “Shine Ma’aruf d’ina....”

“Da ace yana nan zaikai kimanin shekaru nawa a yanzu...?” Sameer ya kuma jefo masa wata tambayar.....

Abbah ya d’anyi shiru kaman mai nazari kana yace “Zaikai kimanin shekaru talatin da uku....”
Sameer ya kuma jin zuciyarsa tai masa rauni tana mai kuma jadadda masa waswasinsa....
A hankali ya mik’e yana k’ok’arin saita kansa kana ya dafa Abbah kaman zai magana sai kuma ya kasa a hankali ya janye hannunsa ya fice cikin sauri sabon k’walla na k’ok’arin ciko idanunsa, abu guda zaiyi ya cire zuciyarsa daga d’inbin waswasin dake k’unshe cikinta, irin yanda yayi da iyayensa na can gida, bazai tunk’ari Abbah da batun ba sai ya tabbatar ma zuciyarsa ya kuma samu hujja mai k’arfi da zai tabbatar da hakan...
Kai tsaye laboratory ya wuce yanda sukayi ganawa ta sirri shida d’aya daga cikin ma’aikatan lab d’in, tuni ya bada sample d’in jininshi ya kuma buk’aci a d’au na Abbah a b’oye a duba idan sun had’a dangantaka ta jini...
Sameer na fitowa ya hangi family d’in Abbah zazzaune suna jiran tsammani, jikinsa ya kumayin sanyi sosai sanin cewa wad’annan zuri’a na iya zama zuri’arsa, idanunsa ya sauk’a kan Mamy tsananin tausayinta ya rufesa, ji yayi kaman yaje ya rungumeta yace mata shine long lost son d’inta, take kuma zuciyarsa ta shiga raya masa yanada buk’atan sanin ya akai ya b’ace ya rabu da danginsa tsawon shekaru shin jefar dashi sukai kokuwa b’acewa yayi...Sannan ya akai ya k’are hannunsu Mummy...? Wad’annan tambayoyi ne da ya kamata yasan amsoshinsu kafin ya yanke wani hukunci... Cikin sauri yasa kai ya shige ba tareda ya bari sun gansa ba...
Kai tsaye bai zarce ko ina ba sai gidansu Shamsu...

A b’angarensu Mamy kuwa haka suka d’unguma suka shiga duba Abbah kowa nason sanin halinda Abban ke ciki har saida Likitoci suka d’an dakatar dasu, ganin jikin nasa da sauk’i sosai yasa su Nabilah Marliya da Raihanah suka nufi gida don shirya abincin da za’a kawo masu asibitin da kuma wasu abubuwan buk’ata...

Adaidaitansu na tsayuwa sai karo da gungun yara sukai cikin layin nasu tamkar wanda suke jiran isowarsu suka ci gaba da wak’e wak’e suna kiran sunan Nabilah cikin aibantawa da tsananin tozarci...

Nabila Raiha da Marliya cirko cirko sukai suna kallon wannan ikon Allah, kan kace mai sunyo kansu suna ci gaba da tafi da wak’e wak’e cewa Nabilah karuwace, ‘yan sa idon unguwan tuni sunyi chaa ga d’oyoyin su Baffah Wadah suma duk sun fito suna kallon wannan bak’on al’amari mai ban mamaki...
Kankace mai yaran nan sun shiga dunbuzan k’asa suna jifan Nabilah dashi.....

SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_




*42*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




NOT EDITED



Cikin tsnanin tashin hankali Marliya da Raihanah suka shiga janye Nabilah wacce ta koma tamkar mutum mutumi suka nufi cikin gida da ita, da k’yar Nabilah ke iya d’aga k’afafunta ga mutane sunyi chaa kuma babu wanda yayi yunk’urin hana yaran abinda suke... Abu mai kaman wuya kaga kukan Nabilah saigashi k’walla sun ciko idanun nata, ta d’ago idanunta da k’yar tana duban mutane a daidai lokacinda ta hangi Siyama da Yesmin zaune cikin motar Siyamar suna faman sakin murmushin cin nasara lokacin guda suna d’aukar tozarcin da akewa Nabilah cikin wayoyinsu, hakan yayi daidai da zubowan k’wallan da suka mak’ale cikin idanun Nabilah, tinda take ba’a tab’a mata cin zarafi irinta yau ba, kalmar karuwa da aka kirata dashi yafi komai d’aga mata hankali, ji tayi duk duniya babu wanda ta tsana irin Khalid, domin kuwa shi ya janyo mata wannan wulak’ancin, da ace bai shigo rayuwarta ba su Yesmin bazasu san da zamanta ba balle su aibatata su mata sharri da b’atanci ga sunanta wanda yafi komai d’aga mata hankali....
Koda suka shiga gida ma d’aki ta fad’a ta kulle kanta ta kifa kanta ta shiga rusa kukanta son ranta, Raiha da Marliya duk jikkunansu yayi sanyi, yau d’in abubuwa ne da dama kekan faruwa cikin ahalin gidansu, haka sukai jigum jigum sunma mance aike suka dawo gidan, tsnanin tausayin Nabilah na d’awainiya dasu....

****

Shamsu ya dubi Sameer a karo na biyu kana yace “Sameer are you sure of what you’re doing....?”

A kaikaice Sameer d’in ya d’an dubesa hannayensa duka biyu rungume da fuskarsa kana ya jinjina masa kai ba tareda ya furta koda kalma guda ba...
Lokaci guda ya mik’e ya suri car keys d’insa, yakai dubansaga Shamsu da raunannun idanunsa kana yace “Da zaran result ya fito, idan har ya tabbata mutanen nan iyayenane zanje can gida Kaduna na tambayi su Mummy gaskiyar al’amari.... I’m confused Shamsu... Abubuwa da dama sun shige min duhu, ina buk’atar haske cikin rayuwata....” Ya k’arashe siririyar hawaye na gangaro masa....

Jiki a sanyaye Shamsu ya k’araso ya d’an dafa Sameer cikeda tausayawa, cikin tausashesshiyar murya yake fad’in “Sameer kar ka damu everything will be alright in sha Allah, komai zai bayyana maka da yardar Allah, na sani is not easy but ka k’ara hak’uri da sannu komai zai wuce....”

Sameer ya d’an dubeshi kana ya jinjina kai yace “Na gode brother....” Daga haka k’ok’arin sa kai ya soma zai shige Shamsu ya take masa baya....

****

KADUNA

Yana kishingid’e saman kujera gefen Ammi tanaci gaba da masa sannu don baijin dad’i kwana biyun, zazzab’i yake fama dashi...
Kubura ta shigo d’auke da bowl na fruit salad ta ije saman stool d’in dake gefensa tana satan kallon yanda ya fad’a ya kuma yin haske a d’an rashin lafiyan kwana biyu da yayi, gaba d’aya tausayinsa ya rufe Kubura, cikin zuciyarta take ayyana inama sunyi aurene da ita ke jinyar kayanta ba Ammi ba, sai faman zuba shagwab’awa Ammi yake ana tambayarsa mai yake sonci yana basarwa, inama ma ita yake wannan shagwab’ar itakaw taita riritatasa kaman jinjirin goye...
Duk wannan tunani da Kubura keyi tsaye take kansa k’ik’am shiko sai faman shafa wayarsa yake baimasan tana tsaye wajen ba...
Ammi ta saki baki tana kallon ikon Allah, har saida ta dakawa Kubura tsawa kafin ta dawo hayyacinta...
“Ke! Lafiyarki kikayiwa mutane tsaye aka....? Badai kin aje abinda ya kawoki ba... Toh tsayuwar kuma ta minene...?”

Kubura ta d’an zabura kad’an tana k’ak’aro murmushi take fad’in “A’a Ammi wai dama nace ko akwai abinda yake buk’ata kuma...”
Girgiza kai kurum Ammi tayi domin ita kanta ta soma fahimtar take taken Kubura kana tace “Jeki idan ya nemi wani abin na kiraki...”

Kai a k’asa Kubura ta amsa tana mai satan kallon Khalid da kacaukam hankalinsa kega wayarsa, da alama sam baima saurari tattaunawarsu da Ammi ba... Ficewa tayi cikin zuciyarta tanai masa fatan samun lafiya...
Shiko Khalid dialing layinta yaketa k’ok’arin yi amma bai shiga, ya d’an saki garen tsuka a hankali had’ida lumshe dogayen idanunsa...
Ammi tace “Saif ka tashi ka sha fruits d’in ko kad’an ne, jibi duk yanda ka rame ina magani zai maka amfani baka cin komai, ko nima so kake ciwon damuwa ya kamani ne...?” Ta k’arashe cikin raunin murya...

D’an duban Ammi yai daga kishingid’en da yake, tausayinta yaji ganin duk yanda itama ta shiga damuwa, a hankali ya mik’e zaune, Ammi tai saurin nufosa zata taimaka masa yana murmushi yace “Haba Ammi zan iya zama fah....”

Ta d’an hararesa kana tace “Don dai bakaga yanda ka rame bane...” Tai maganan tana zuba masa fruits d’in cikin k’aramar bowl ta d’auko d’an spoon d’in tana k’ok’arin bashi a baki...
Nan ma murmushin ya kumayi yana mai girgiza kai had’ida jinjina irin k’aunar da mahaifiyarsa ke masa...
Amsa yai yana fad’in “Haba Ammi stop treating me like a kid again, I’m all grown fah....”
Nanma hararan ta d’an jefa masa kana tace “Toh maza ci na gani....”

Haka ta tasa Khalid a gaba yana tura fruits d’in, saida ta tabbata yaci sosai kafin ta k’yalesa, ya d’anji k’arfin jikin nasa kam ya kuma sami d’an appetite...
Remote d’in dstv ya janyo yana k’ok’arin kamo tashan ball yaji k’aran shigowar sak’onni cikin wayarsa...
A hankali ya mik’a hannu ya janyo wayar yana k’ok’arin dubawa, Whatsapp d’insa ya shiga bud’ewa don ta nan ne aka aiko masa sak’on... Ganin bak’uwar lamba yasa yaji kaman bazai bud’e ba sai kuma ya bud’e yana k’ok’arin dubawa..
Video ce da alama tuni ta bud’e da shike auto download ne wayar tasa...
Sosai ya mik’e ya gyara zama yana kuma kallon video d’in, bai gama tabbatarda abinda yaran ke fad’i ba saida ya hangota tsaye tamkar mutum mutumi ana jifanta ana watsa mata k’asa, sannan duk wajen an rasa mai hana yaran... Yana ganin sanda hawaye suka gangaro mata ‘yanmata guda biyu wanda shakka babu ‘yan uwanta ne suna k’ok’arin janyeta.....
Wani irin mummunar fad’uwan gaba ne ya sauk’arwa Khalid, take ya nemi zazzab’in da yake ya rasa, gaba d’aya ji yayi duniyar na neman juye masa, What’s all this... Ya fad’i a zuciyarsa, ya kuma duban wayar tasa yana jujjuyawa cikin rashin yarda da abinda ya gani... Teddy bear ake kira karuwa...? Karuwa fah....? Khalid ya dafe kansa da ya kuma masa nauyi a hankali, yama rasa tunanin mai zaiyi....
Lambar da aka turo masa video d’in yai k’ok’arin kira saidai bata zuwa... Ya kuma kaiwa kan lambar Nabilah kaman zai dialing sai kuma yaji bazai iya ba, ji yai Kano kawai yake son tafiya...
Kaman wanda aka zabura dukda cewa yamma ce lis hakan bai hanasa tunanin hawa kwalta a daidai lokacin ba....
Sashensa ya nufa ya hau shiryawa gadan gadan...
Ammi da ta fito tana tambayar ko za’a kawo masa fish pepper soup na ta tarar babu Khalid a parlorn...
Tai mamakin daga d’an tashinta har ya sami k’arfin ficewa a parlorn.... K’ila sashensa ya koma ta fad’i hakan cikin zuciyarta had’ida zama cikin sofa tana canza tashan k’wallo da Khalid yakai, ga magungunansa da wayarsa duka a wajen ya bari....

Jim kad’an ana kiraye kirayen sallan magrib Khalid ya fito cikin shiri sai zuba k’amshi yake, Ammi ta saki baki tana kallon majinyaci ya ware lokaci guda...
“Saif masallaci aka nufa ne...?” Ta tambaya tana mai sakar masa murmushi....
Ba tareda ya dubeta ba yana mai ci gaba da d’aura agogon hannunsa yace “Kano zanje Ammi....” Ya k’arashe yana mai d’aukar wayar salulansa dake bisa center table...
Tamkar wacce aka zabura haka ta d’ago tana dubansa...
“Kano...?” Ta maimaita...
Ba tareda ya dubeta ba yana mai ci gaba da abinda yake ya jinjina mata kai alamun eh... Tuni yasa kai yana fad’in “Sai munyi waya Ammi....”

Ai a d’ari ta mik’e ta sha gabansa tana huci take aika masa mugun kallo... Khalid ya tsaya cak yana duban mahaifiyar tasa...
“Wllhi kaji na rantse bazakaje ba....”

Khalid ya d’ago a hankali ya kuma dubanta.... “Amm.....”
Bata bari ya k’arasa ba tace “Na riga na rantse, kan wancan matsiyaciyar yarinyar zaka d’ibi k’afafu ka d’ale kwalta ba isasshen lafiya ne dakai ba ni kuma kawai sabida gani shashasha sai na k’yaleka koh...? Toh bazakaje ba.... Wayasan uwar mai ta sanya maka kaci ka koma haka, tinda ka dawo ma kake rashin lafiya, wayasan kalan asirin data maka.... Toh wllhi wllhi bazakaje ba, sabida tsaban jarbar asirinta a daren nan zata kiraka ka tafi, idan asirinta yayi tasiri akanka ni bazaiyi akaina ba... Ban yarda ka fita a gidan nan da sunan barin gari ba kaji na fad’a maka....” Tana k’arashe fad’in haka tasa kai ta nufi staircase....
A hankali ya lumshe idanunsa ga zuciuarsa dake tsnanin masa zogi da rad’ad’i, a halin yanzu babu abinda yake sonji kaman yaji gaskiyar lamarin nan daga bakin Teddy Bear wanda, maganar tafi k’arfin waya a’a face to face baki da baki yakeson jin komai....
Da k’yar ya iya jan k’afafunsa ya nufi masallaci...
Kubura dake lab’e ta gama jiyo komai duk abinda Ammi ke fad’i dafe k’irji tai tana fad’in “Na shiga uku ni Kubura, wato ashedai ba Yesmin bace kawai ke neman hana burina cika ashe akwai wata can... Harma asirce shi tayi... Tab! Aiko wllhi da sakel, ina nan ina tunanin wannan k’aramar alhakin Yesmin ashe akwai wata gogeggiya mai bin bokaye da malamai.... Toh wllhi bazata saku ba, Khalid nawa ne ni kad’ai sai na nuna mata malumanta sunyi kad’an, abinda banyi a baya ba yanzu zanyi.... Wllhi sai na mallaki Khalid...!” Ta k’arashe tana d’aga yatsa guda sama had’ida juya yatsar cikin salo na juya idanu....

***

KANO

Hajiya ta cika tayi fam tana kuma hararan mijin nata....
“Toh yanzu sai ka baro masu Raihanan....? Kaga Alhaji gidan nan dai babu mai girki idan ba Raiha ba babu mai iyawa da d’awainiyar gidan nan, kawai makasu a kotu zakai dole a baka d’iyarka tinda babu uban da ya haifa maka ita ehe....!” Ta k’arashe tana sakin huci....

Cire hulansa Baba Alhaji yayi yana shafa kansa kana yace “Haule Mamani fah kike nufi nayi k’aranta a kotu....”

“Toh sai mai idan kayi k’ararta ita ta haifa maka d’iyar da zata k’waceta haka kurum, shikenan yanzu tasa d’iyarka bata ganin darajarka, yanzu sam Raiha bazata d’aukeka matsayin mahaifi ba biyayya kuwa saidai tayiwa Manu tinda gidanshi ta koma da zama...” Ta k’arashe tana aika masa harara....

Sauk’e ajiyan zuciya Baba Alhaji yayi yana mai girgiza kai alamun a’a yake fad’in “A’a Haule banda maganar kotu idan an kwana biyu dai lokacin Mamani ta huce zanje na d’auko d’iyata...”

Tsuka Hajiya ta buga had’ida kad’e masa buje ta mik’e tana fad’in “Aikin banza aikin wofi, k’ato da kai ka bari k’aninka da mahaifiyarka suna maka k’ak’a gida, toh wllhi nidai bazan kashe kaina da aikin gidan nan ba, kuma sanin kanka ne ma’aikata basu jure zaman gidan nan don haka duk abinda kaji ka gani kai ka sayo da kud’inka ehe...” Ta wuce fuu kaman zata tashi sama....
Tana isa d’aki ta tadda Kausar tayi kashi jikinta sai tangaririya ake da ita tsakanin Sahariyya da Najah an rasa mai wanke mata kowa cewa take wllhi bazatayi ba...
K’atutun bak’in ciki ya tokari Hajiya don sam basusan d’awainiyar yarinyar ba tinda ubanta ya ajeta gidan sai Raihanah...
Hajiya tai k’wafa tace “Kunsan Allah bazan lamunta wannan sangarci naku ba, kuna gani dai ubanku ya kasa dawo da Raiha gidan nan kun barni a kitchen ina fama da hayak’i da sunan ina maku girki, toh d’awainiyar Kausar d’inma ni ce kukeso na d’auka ko kuwa...?”

Kafin takai aya Sahariyya dake mak’ale da earpiece a kunne tace “Wllhi Hajiya nidai bazan wanke kashin d’iyarda ban haifa ba, ai ubanta na raye maiyasa baza’a maidata gidan ubanta ba matar tasa taje can tai

Please Login or Register in order to submit comment