Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

birkice yana fad’in “How’s my father doing... Tell me, ina mahaifina.... Talk to me....!” Ya k’arashe cikin tsananin d’imauta...
Mutumin yace “Try to calm down Sir, a yanzu haka Babanka yana ICU namu yana samun kulawa na gaggawa... Muna fatan cikin yardar Allah ya tashi kafad’unsa...” Daga haka katse kiran mutumin yai yana mai kuma baiwa Khalid baki had’ida kalaman k’arfafa gwiwa dikda cewa Khalid baima yarda mahaifinsa na raye ba sabida wane irin crack da yakeji zuciyarsa nayi tin daga can k’asa.... Take yaji k’afafunsa sun gaza d’aukansa... Ya zame ya zauna gijif saman kujera yana mai d’aura hannayensa saman bakinsa... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un, abinda yaji zuciyarsa na nanata masa kenan... Lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “A’a Daddy na yana raye... Zai tashi yaga burinsa ya cika... Family d’insa sun had’e waje guda.... My Dad is alive.... Yana nan da rai.... I’m sure of it... Na sani...” Ire iren sumbatu da Khalid keyi kenan... Lokaci guda yaji wani irin kukan da yaketa dannewa na k’ok’arin faso k’irjinsa.... Allah sarki haka Khalid ya kifa kansa ya dinga kuka yana fad’in mahaifinsa na nan da rai, ida ka gansa dole ne ma ya baka tausai... A b’angaren Nabilah haka kurum taji tamkar wani abu na faruwa da Khalid d’in musamman da taga ta kira wayarsa har sau uku bai d’aga ba, tasan dik fushin da zai da ita bazai k’i d’aga kiranta haka kawai har sau uku ba... Take taji zuciyarta ya karaya sosai, tana son sanin halinda mijinta Ke ciki... Baccin data kasa komawa kenan itama taita jero sallolinta....

Washe gari Engr Khalid ya samu da batun don baisan ta yanda zai soma tink’aran Aunty Daula da wannan labari ba, Engr yaita basa baki had’ida k’arfafa masa gwiwa ya kuma sanar dashi shi zai sami Ammah da batun... Koda labarin accident d’in ya isa masu Abbah sai cewa Abbah yai maza su shirya su tafi, Aunty Bara’atu, Aunty Daula da yaranta ,Khalid da kuma Nabila suka d’auki hanyar Abuja bayan Abbah da Mamy sun kumayima Nabilah nasiha mai shiga zuciya, gashi tinda ya dawo makaranta taji wannan batu hankalinta ya tashi sosai, tausayin Khalid d’in ya cika mata zuciya ashe shisa bai sami zarafin d’aga wayarta ba, lallai yana cikin matuk’ar tashin hankali... Taga yanda a kwanakin ya shak’u sosai da mahaifinsa... Dole ma hankulansu ya tashi dan basuga yanayin halinda jikin Daddyn ke ciki ba, fatanta Allah ya tashi kafad’un Daddy ya basa lafiya...Dikda tana cikin yanayi na rabuwa da gida amma halinda mijinta Ke ciki sai yafi d’aga mata hankali, ga Aunty Daula ma wacce batasan soyayyan kowa ba tsawon shekarun nan bayan d’an uwanta Ma’aruf saiko na mijinta, itama dik ta koma abin tausai...
Wannan shine ana wata ga wata dan acan gidan Abban ma yanzu kam hankalinsu ya soma tashi na rashin sanin tak’aimemmen yanda Mamani ta tafi ga girma a tattare da ita, dole hankulansu ya tashi, in Kaga Abbah duk a birkice yake shima... Can gidan gidan Baba Alhaji ma abin babu sauk’i tin sanda Magajiya ta iso gidan a matsayin kishiyar Hajiya Haule abubuwa suka dad’a kwab’ewa... Ga Hafiz ya tada hauka wa mahaifin nasa cewa sai ya saki Magajiya dan bazai dinga shigowa gidan mahaifinsa yana karo da ‘yan daudu ba... Toh a can gidan Engr ma bayan zab’e da ya k’arato sosai maganan b’acewar Akram ya soma d’aga mai hankali a halin yanzu, dan harta Umman Akram d’inma yau sawunta na biyu kenan a gidan tana kuka tana fad’in ya taimaka ya nemo mata d’anta baida kowa sai Engr d’in kuma maraya ne... Kar ya dubi girman laifin da Akram d’in yai masa ya taimaka ya bincika yanda za’a sami Akram...
Engr ya sanarda ita ta kwantar da hankalinta idan ta kama za’ai tracking har layin da Akram yai amfani ya kirasa dashi last... Da wannan batu mahaifiyar Akram ta d’an sami sauk’i... Dole Engr ya had’a binciken da jami’an tsaro....
A b’angaren Sameer kaw yaso ya tafi ya duba jikin Daddy saidai Mummynsa da Daddynsa yau suke dawowa daga k’asar Saudiya yanda aka sallamo Daddyn nasa daga can Saudi German bayan kwashe sama da watanni hud’u yana jinya a can..... Dama tuni sun sanar dashi ta Kano zasu sauk’a...
Tarba na girma suka samu daga iyayen Sameer dikda halin tashin hankalin da suke ciki hakan bai hanasu karrama iyayen rik’on Ma’aruf ba mutanenda bayansu Sameer baida wanda suka fisu, Alhamdulillah jikin Daddy yayi kyau sosai dan Sameer d’in yaji dad’in yanda yaga jikin Daddyn nasa yayi kyaun gani... Allah sarki Sameer da Mummy tamkar su had’iyi juna dan Farin ciki... Mamy da Abbah har rasa kalaman da zasuyi amfani wajen mik’a godiyarsu ga wad’Annan bayin Allah da suka rik’e masu d’a tamkar nasu sukai.... Sai Hawaye kurum da Mamy keyi...
Mummy Fatahiyya ta rungumeta tana fad’in “Hajiya Mariya ai d’ah na kowa ne... Dik wanda kikaga ya rik’i d’an da ba nasa ba a wulak’ance dan kawai bashi ya haifesa ba Toh ki tabbata wannan mutumin baida zuciya a k’irjinsa idan kuma yanadashi Toh fah itada babu dik d’aya ne... Shi d’ah basai ka haifa ba ya zamto naka... So tari zaka haifi d’an baka mora ba wani daban ya moreshi.... Shi wanda baka haifan ba sai kafi moranshi sama da naka.... Haka Allah yake gudanar da Al’amaranshi.... Kin gama min komai da kika haifo min d’ah kaman Sameer cikin Duniyar nan....” Ta k’arashe tana kuma kamo hannayen Mamy da itama hawayen take....
Kirkin mutanen har ya zarta misali, haka kalaman Hajiya Fatahiyya sukaita yawo a kwanyar Abbah, tabbas dik abubuwan data fad’i gaskiya ne... Ko menene Mamani tai a baya ya rik’eshi da duka soyayyarta kuma bata masa rik’on sakainan kashi ba... Idan har ya cika d’a mai biyayya dole ya nemota yanda ta shiga ta fita ya kuma saurara daga b’angarenta....



SameenaAleeyou📚






*INDA RAI*
_...............DA RABO_





*97*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Babu b’ata lokaci Sameer ya soma shirye shiryen bin iyayen nasa zuwa Kaduna a Washe gari, dan hakan ne ya kamata sannan daga can zai biya ya duba jikin Daddy... Nan Abbah ya umarcesa da ya d’auki matarsa ya tafi da ita, babu musu ya amsawa nahaifin nasa, sai sannan su Daddy suke samun labarin k’arin auren da Sameer yai, sukaita mamaki Mummy har tana dungurinshi tana fad’in wato ya tsere ma Babansa, su dai su Mamy sai mamakin yanda Sameer ke matuk’ar wasa da Mummynsa suke, da gani ba k’aramin Sabo da shak’uwa bace tsakaninsu... Sai sannan ake breaking wannan labari wa Raihanah kasancewar zatabi mijinta su tafi... Ita harga Allah abin mamaki yaita bata, Wai itace matar Ya Ma’aruf... Ita Raihanatu itace akai mata aure da Ya Ma’aruf ba Addarta Sahariyya ba... Take taji wane irin rauni kuma can k’asar zuciyarta...Ta sani Ya Ma’aruf mutumin kirki ne da ko wacce mace zatai alfaharin samu a matsayin miji... Amma harga Allah ji take auren yai mata diran sauri, ko da wasa bata tab’a kawowa aurenta na nan kusa ba... Abbah da Mamy sukaita bata baki suna nuna mata in sha Allah Ma’aruf zai zamto alkhairi a gareta kuma bazata kuka da zab’insu ba da izinin Allah... Ita dai kanta kife kurum yake sai Hawaye dake gangaro mata cikin sabon mayafin da Mamy ta rufa mata da kanta, tana jin sallamansa bugun zuciyarta ya k’aru... Zama yai daga gefe kad’an kusan k’afan Abbah...

Abbah ya kuma masu nasiha mai shiga jiki sosai musamman Sameer da yanzu mata biyu Ke gareshi...
Mummy kaw tuni itama ta shiga nan nan da Raihanah, abin sosai yai mata dad’i, ita d’in shaidace yanda D’an nata ya sha wahala da aure, sam zamansu da Siyama rabi a gidansu Siyama tayisa, tabbas taji dad’in wannan aure na Sameer tana kuma fatan nutsuwar da bai samu a baya ba ya samu yanzu...
A d’aki Mamy taci gaba da lallashin Raihanah tana sanar da ita, nan Kano zata zauna... Yanzu rakiya kawai zasuyima iyayen goyonsa amma da zaran al’amara sun daidaita yace nan Kano zai ajeta kusa da gida... Da wannan batu na Mamy Raihanah ta d’an sami sauk’i a zuciyarta...
Da dare suna zaune d’aki itada Marliya tana tayata shiryawa lokaci guda tana ci gaba da zolayarta “A’a ashe dai ashe dai patient ce matar... No wonder dik abinda ya shafi patient Yaya Ke baiwa abin kulawa na musamman ashe dai....”
Raihanah ta galla mata harara tana ci gaba da share hawayenta....
Marliya ta d’an marairaice fuska tace “Allah sarki ki hak’uri mutuniyar gobe war haka ina nan ina kewarki...”
Raihanah dai batace komai ba sai goge hawayenta data ci gaba dayi.... Marliya ta ije rigar da take linkewa kana tace “Toh Wai ma wasu kaya zaki tafi dasu bayan inaji d’azu Ya Ma’aruf na fad’iwa Mamy da zaran kun tafi Kaduna zai maki sayayya... Inye yarinya kin mori miji d’an gayu mai taste...”
Jifa mata rigar dake hannunta tai kana tace “Idan bazaki tayan ba Ki tashi Ki fita.. Na mori miji ta ina bayan wannan matar tasa tsoro take bani harga Allah. kuma yanzu Addah Sahariyya mai zata kirani tinda kinsan yanda ta d’aukaki auren nan... Nidai Allah dan bazan iya musu masu Abbah bane da.....” Kasa ci gaba da magana tai sakamakon sallamansa da suka jiyo daga k’ofa... Marliya tai zumbur ta mik’e tana mai k’ok’arin gaidashi lokaci guda ta fice ta basu waje...
Zuciyarta taci gaba da tsinkewa... Banda sautin dum dum! K’irjinta bai komai, gaba d’aya ma sai ta daburce ta mance mai take, da k’yar ta iya lalumo kalmomi saman harshenta ta soma gaidashi...
Saida wasu dak’ik’ai suka d’an gauta kana ya amsa mata yana mai karantar yanayinta, ita dai dik tsarge take, ko bata d’ago ta dubesa ba jikinta na bata tsareta yai da idanunsa... Har ta ciren ran bazai kuma cewa komai ba ta sinkayo muryarsa na fad’in “Gobe idan Allah ya kaimu before mu wuce akwai yanda zamuje... So ki shirya da wuri ko...”
Jinjina masa kai kurum tai ba tareda ta iya amsawa ba, gaba d’aya sai yaji jikinsa ya masa sanyi... A ‘yan shekaruntan nan ta tari labarin aurenta haka dole abin ya dameta, sosai tausayinta ya cika zuciyarsa... Koda bata d’ago idanunta ba zai iya ta tabbatarwa hawaye take... Gaba d’aya sai yaji babu dad’i, alk’awari ya d’aukarwa kansa koda ace bai sonta zai koya ma kansa yanda ake sonta... Koda ace bai tab’a son wata d’iya mace sama da Siyama ba bazai tab’a bari Raihanah ta fahimci hakan ba sabida ta cancanci fiyeda hakan.... Tana jin ficewarsa yana amsa kira ya sanyata saurin mik’ewa ta nufi bathroom tana mai kuma tintsirewa da sabon kuka... Sameer yana iya sauraro yanda take shesshek’ar kuka daga toilet, ya lumshe idanunsa a hankali yana mai ije ‘yar jakan kayan da ya shigo mata dashi saman gado... Cikin sauri yasa kai ya fice daga d’akin dan kukan nata sosai yake breaking d’insa....


***
A can Abuja kaw tinda suka isa sukaga condition d’in Daddy hankulansu suka kuma tashi, tabbas Daddy yana matuk’ar jin jiki dan ko d’akin da yake ba’a bari a shiga, da k’yar suka k’yale Auhty Daula da Khalid suka shiga bayan sun saka kayan sukuf irinta ma’aikatan lafiya... Haka hawaye ya dinga d’iga masu ganin Daddy kwance unconscious... Addu’o’i sukai masa kana suka fito dan babu halin Kwana ma’aikatan lafiyan basuda buk’atan kowa ya kwana wajensa musamman dashike har yanzu baisan yanda yake ba, na’urar bature ne kawai da buwayar Ubangiji ke aiki akansa....
Haka suka d’unguma suka nufi gida jiki dik a mace, Nabilah da Aunty Bara’atu suke k’ok’arin d’ebewasu Ijlaal kewa musamman Humaira data fara wayo ta fahimci abindake faruwa....

Haka nan sukai dinner babu dad’i gaba d’aya abincin ba wani ci sukai ba, baranma Khalid da sam ko fitowa parlorn baiba tinda suka dawo daga asibiti...

Daga Aunty B har Aunty Daula sun kula da yanda gaba d’aya hankalin Nabilah bai taredasu, mosti ba motsi ba sai ta lek’a k’ofa... Tinda tai wanka ta shirya cikin kayan baccinta mai taushi yalwatacce ta haye gado taredasu Ijlaal amma ga dikkan alamu ba baccin take ba...
Aunty B ta numfasa ta d’an tab’a Daula kad’an tace “Ban tsamman mijinta ya saka wani abu a cikinsa ya kamata ko d’an tea ne takai masa, she cant let him go to bed with an empty stomach, ga kuma halinda yake ciki...” Cikin sigan rad’a tai maganar...

Aunty Daula ta jinjina kai tace “Nima tinanin da nai kenan...”
A tare suka had’e murya suka kirawo sunanta, gabanta ya yanke ya fad’i....
Aunty B taci gaba da fad’in “Nabilah ya kamata Ki lek’a kiga halinda mijinki ke ciki... This is a serious situation for him, Kinga ko abinci baici ba,and you can’t let him go to bed like that....”
Aunty Daula ta jinjina kai tace “Haka ne... Khalid is going through difficult situation, he needs you... Ki tashi kije kitchen and prepare something for him koda tea ne..”
Jinjina kai kurum take a hankali tana mai sauraren Aunties d’in nata, lokaci guda ta mik’e ta sauk’o daga saman gadon a hankali kana ta isa ta bud’e suitcase d’inta ta ciro hijab ruwan madara ta d’aura saman yalwataccen riga da wandon baccin nata...
Aunty Daula tace ta sami Karima tai guiding nata yanda stuff d’in kitchen d’in suke aje... Babu musu ta jinjina mata kai kana ta fice...
Da taimakon Karima ta ida dafa masa ruwan shayin ta had’e saman tray kana ta nufi d’akin nasa dake nan down floor...
Sallama saman bakinta take knocking... Khalid da ida sallansa kenan ya taso yana k’ok’arin bud’ewa dan tuni ya d’ago muryar teddy bear d’insa dikda sanyi da muryar tata tai.... Ya sakar mata sassanyar murmushi na k’arfin hali.... Hanya ya bata kana yace “Come on in...” Ta rab’a a hankali ta shige k’irjinta sai bugu yake...
Haka nan ta zauna cikin d’akin a d’arare sai rarraba idanu take ga sanyin AC da yaima d’akin k’awanya had’ida dadd’an k’amshinsan nan... Jim kad’an ya fito daga closet sanye cikin white inner shirt da ash sweatpants, da alama ya canza jallabiyan data shigo ta tadda jikinsa ne wanda ko ba’ace ba sallah ya ida...
Daga gefenta ya d’an zauna yana mai karantarta... Lokaci guda ya sinkayo muryarta tana gaidashi.. Bai amsata ba sai kamo yatsun hannayenta da yai ya rik’e cikin nasa, lokaci guda ta d’ago tana dubansa.... Sai snn ya d’an amsata a tak’aice kana yai mata alama da ido kan tai serving d’insa tea d’in.... Sarai ta gane mai yake nufi da yai mata alama da idon kan tai serving d’insa amma saidai yak’i sakin hannunta....

Ganin ya kuma mata alama da ido yana duban tray d’in ya sanyata masa alama itama da idanun kan ya sakar mata hannunta, lokaci guda take furtawa a hankali “Can I have my hands back...?”
Murmushi ya sakar mata kad’an kana ya saki hannun nata.... Ta duk’a a hankali tana had’a masa, dik abinda zata zuba sai ta tambayesa, shiko dik wani motsinta ya kasa janye idanunsa daga gareta...
Bayan ta ida had’awa ta mik’a masa cikeda risinawa.... Ya amsa yana mai furta “Thank you teddy bear....!”
K’ak’aro murmushi ta d’anyi ba tareda cewa komai ba, yana sha yana tsareta da idanu... Ya kuwa sha sosai dan baima San sanda tea d’in Ke shige masa ba sakamakon duban fuskarta da yake...
Bayan ya gama ne ta shiga had’a tray d’in tana fad’in bara Takai kitchen...
Kaman mai tsoron idan ta fice bazata dawo ba sai ji tai ya rungumota ta baya yana fad’in “Please stay... Please stay here with me kinji teddy bear....!” Ya k’arashe idanunsa a lumshe....
K’irjjnta yaci gaba da bugu, ta kasa tab’uka komai, tana jin sanda ya dawo dasu baya yai masu masauk’i saman kujeran... Gaba d’aya sai jinta wane iri take... Khalid yaci gaba da furta “I don’t know if I can do this Nabila... I don’t know... Ta ina zan soma sanar da Ammi abubuwan da suka faru... Da Wanne zan soma mata...? Accident d’in Daddy...? Introducing Aunty Daula da yaranta ko kuwa da batun aurena zan soma mata... Nabilah I’m lost..... I don’t where to start... I’m completely lost....!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Tausayinsa ya cika mata zuciya take taji kuka na neman zuwa mata amma sai ta daure dan tasan shid’in na buk’atan juriyarta a halin yanzu.....
Cikin murya irinta lallashi take furta “We are all here for you... You are not alone... Together we can do this kaji... And Daddy zai sami lafiya in sha Allah... Mu ci gaba da masa addu’a kaji, abinda ya kamata muyi focusing yanzu akai kenan kaji.... I’m here... For you....!” Ta k’arashe cikin rawar murya dikda juriya da take k’ok’arin nunawa...
Khalid ya kuma kamo hannayenta yana mai furta “Thnak you teddy bear...!”
Ya k’arashe yana mai kuma janyota cikin jikinsa, saitin kunnenta yake maganar tamkar mai rad’a “Teddy bear... please sleep here beside me....!” Yai maganar yana mai k’ok’arin zame hijabin jikinta... Nabila da gaba d’aya ya gama daburcewa saurin d’agowa tai a d’an razane tana dubansa... Sai kuma ta sadda kanta....
Ya kuma sakale yatsun hannunta cikin nasa kana ya furta “Don’t you want... to sleep beside your bear.... “
Janye hannayenta ta soma a hankali, cikin d’an daburcewa take furta “Zan... zanje karsu fara nemata...”
Murmusawa yai a hankali kana yace “Babu wanda zai nemeki... Alright idan bazaki kwana a nan ba, do me a favor...”
Ya d’an dubesa a hankali.... Still yatsunta cikin nasa yake ci gaba da furta “Stay with me har nayi bacci, idan nai bacci sai ki tafi... I just want you beside me teddy bear that’s all... Please don’ say no... Kinji....” Ya k’arashe kaman wani mai shirin kuka...
Jinjina masa kai tai a hankali kana tace “Alright deal.... Idan kayi bacci zan tafi... You better go to sleep now..!” Ta k’arashe da sigan fad’a...
Khalid ya murmusa cikeda jin dad’i had’ida jinjina kai yace “Deal....! Come here ya k’arashe yana mai janyota jikinsa, yai masu masauk’i saman gadon, Zame jikinta tai had’ida jera pillows tsakaninsu tana mai satan dubansa take furta “Ina kallonka daga nan oya go to sleep...!”
Shidai dariya ta basa sosai hakan yasa yai mata k’uri daga yanda yake kwance, murmushi saman fuskarsa... Idan ta juyo taga yana dubanta saiko ta kuma duk’unk’unuwa cikin hijabinta tana fad’in idan bai juya ba ita zata tafi...
Khalid ya juya yana mai gimtse dsriyarsa had’ida furta “Allah huci ran Princess..”
Yana gani ta soma gyangyand’i ita a dole jiransa take yai bacci... Jim kad’an kaw bacci yai gaba da ita.... Khalid ya janye pillows d’in a hankali kana ya janyota kusanshi ya ja bargo ya rufa masu...Sosai ya lumshe idanunsa yana shak’an dadd’an k’amshinta, a haka shima bacci yai gaba dashi...


***
KANO

Washe gari kaman yanda ya umarceta ta shirya hakan ce ta kasance, daga nan cikin d’aki yanda take tana iya sauraro muryarsa yana gaida Mamy had’ida sanar da ita cewa yanzu zai biya ya d’auko su Mummy suyi sallama dasu....Zuciyarta taci gaba da tsinkewa, addu’an samun strength kawai take cikin zuciyarta tana mai neman agaji da taimakon ubangijinta da ya bata ikon jurewa... Ga tinanin Mamani ya kasa barin zuciyarta, haka zata tafi basuyi sallama ba, sosai wanna abu ya tsaya mata a zuciya, fatanta Allah sa tana cikin k’oshin lafiya a dik yanda take....
Tana ji Mamy tana cewa bara ta shiga ta dubo Raihanar, bugun zuciyarta ya k’aru... Wato dai da gaske shid’in mijinta ne... Ta lumshe idanunta a hankali siriryar hawaye ta gangaro mata, saurin saita kanta tai sakamakon jiyo shigowar Mamy da tai, bazataso Mamy ta danganta cikin yanayin damuwa da tashin hankali ba dan jiyan kusa raba dare tai a d’akin tana bata baki da kuma nasiha... Sai take ga kaman bata kyautawa Mamy ba kar ta d’ago bata son auren D’anta ne.... Mamy ta sakar mata murmushi kana tace “Daughter kin shirya...?”
Ta jinjina mata kai a hankali kana tace “Eh Mamy...”
Jinjina kai Mamy tai kana tace “Toh maza gashi nan yana jiranki a parlor zaku wani wajen before kuzo ku wuce koh...”
Nan ma jinjina kai tai kana tace “Toh Mamy...”
Mamy tace “Allah miki albarka kinji....Idan kun dawo sai ku shiga wajen Abban naku tare kuyi masa sallama ko...” Nan ma jinjina Mata kai tai had’ida amsawa kana ta nufi parlor k’irjinta na matuk’ar bugu idanunta a k’asa...
A tinaninsa bazata saka kayan da ya kawo mata jiya ba sai gani yai ta saka sun kaw mata kyau... Kyakkyawan murmushi ya saki ba tareda ya sani ba, sosai yaji dad’in saka kayan da tai.... Idanunta a k’asa ta k’araso gareshi had’ida risinawa ta gaidashi.. Ya amsa yana mai shagala da duban yanda tai masa kyau sosai.... Shiru ne ya d’an biyo baya har tana dak’ida kana ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Muje koh...”
Babu musu ta risina had’ida bin bayansa... Yanda suka jera dole su birgeka... Yana sanye cikin jampa fara k’al da tai matuk’ar amsar fatarsa saiko bak’ar dara wanda ta k’ara fito da hasken fatarsa, kai da ganshi kaga sabon ango sai watsa k’amshin nan nasa yake... A haka suka nufi motarsa,yau d’in da kansa ya bud’e mata front seat ta shige kana ya zagaya ya zauna a mazaunin driver....
Gidansu Shamsu suka soma zuwa yanda ya kaitawa Maman Shamsu suka gaisa ya kuma sanar da ita yau suke tafiya Kaduna daga nan Abuja zasu shige dan duba jiki Daddyn Siyama... Mama tai masu fatan sauk’a lafiya had’ida saka masu albarka... Daga nan gidan Ammah suka wuce sukai mata sallama itama, har Zulfa’u ma ta fito suka gaisa, gaba d’aya fatan alkhairi sukai masu da sauk’a lafiya had’ida sak’on gaisuwa ga jikin Daddy....
Daga gidan Ammah basu zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Haule, gidan Mahaifin Raihanah.... Bugun zuciyar Raihana ya k’aru, tsoro da firgici suka wanzu sosai saman fuskarta, harga Allah batasan ya yanda zata soma jerawa dashi su shiga cikin gidan da sunan mata da miji ba.... Shi kanshi ya kula da yanda gaba d’aya ta daburce, ya fahimci tsananin tsoron da ya wanzu saman fuskarta... Sai faman rakub’e rakub’e take bayansa ta kasa cimmasa, gashi tin daga waje suke jiyo hayaniyar ‘yan daudu sai faman shewa suke cikin gidan.... Sameer ya d’an dakata kad’an har ta cimmasa, a hankali suke takowa har suka shigo cikin gidan sallama saman bakunansu dikda cewa muryar Sameer ne kawai mai iya fita, itakam Raihanah saima k’ok’arin mak’alewa bayansa da take.... Haba nan fah kallo ya koma kansu, gaba d’aya illahirin jama’an dake tsakar gidan suka bar abinda suke suka zuba masu ta mujiya... Haule dake kokawan k’watan tukunya hannun ‘yan daudu dan idan ta dafa abinci ta bari a nan kitchen saidai tazo ta samu an lashe mata tukunya gardawa sun cinye shisa sam da zaran ta d’aura abinci saidai tai zamanta ta jira ya dafu ta d’auke ta gudu dashi d’aki suci da ‘ya’yanta dan idan ba haka ba to kaw tabbas ma gardawa ta girka, ga Sahariyya ta k’aro wualk’anci tinda aka fasa aurenta da Sameer sai Naja’atu ne ma ke k’ok’arin taimakawa mabaifiyar tata, ga Baba Alhaji tinda yayi Amarya yanaji Haule na drama da ‘yan daudu a waje amma ko lek’owa baiyi, saidaima Magajiya ta fito tana mik’a ta mik’awa ‘yandaudunta sauran takardan tsiren da suka cinye ita da angonta a d’aki... Haule saidai taji hawayen da basu shirya zuba ba suna gangaro mata... A ‘yan kwanaki ukun dik Haule ta fice hayyacinta, kaman ba ita ba....
Tanaji ‘yandaudun nan suna fad’in “Wai Wai Wai bakin ‘yan gayu yau akai a gidan namu... Lale lale barkanku da zuwa... Namu ne ku ko nasu...?” Suka k’arashe cikin salo.... Ita dai Raihanah saima dad’a b’oyewa da tai bayan Sameer abin na kuma basu tsoro had’ida al’ajabi ganin irin wad’annan mutane cikin gidan Baba Alhaji....
Wani mugun kallon da Sameer ya aikama ‘yandaudun suka shiga ja da baya suna kame baki had’ida furta “Wai bari mu matsa kar maza suyi faccakali damu...”
Haule baki sake take dubansu yanda sukai mata bala’in kyau tamkar wasu taurarin cikin film, har malmalar tuwon dake cikin tukunyar hannun Haule ya fad’o Haule bata ankara ba.. Wai Raihanah ce take gani haka kaman wata sarauniya.... Sahariyya dake daga d’aki tana fad’in “Ya kuka daina fad’an kuci gaba man....” Birki tai ma kalaman nata sakamakon hangosu da tai hasken hantsi ya haske masu fuska har wani kashe idanu suke.... Ai take taji wani irin jiwa na d’ibanta... Raihanah da k’irjinta ke bugu ganin irin duban da Addah Sahariyya Ke masu tuni jikinta ya d’auki rawa zata kuma mak’alewa bayan Sameer amma

Please Login or Register in order to submit comment