Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daidai k’ofar babban parlornsa suka had’u...
Akram na sadda kai k’asa yake fad’in “A min afuwa your excellency....”

Engr ya d’an girgiza kai kurum kana yace “Amma sanin kanka ne African time bashi a tsarina, sannan idan nayi alk’awariwa mutane cewa lokaci kaza zanzo toh ko dak’ik’a guda banson k’arawa.... I suppose kasan duka wad’annan by now.....”

Kai a k’asa Akram yace “I’m very sorry your excellency uziri ne ya rik’eni amma In sha Allah hakan bazata kuma faruwa ba...”

D’an girgiza kai kurum yai kana yace ”A dinga kiyayewa....”
Cikin sauri Akram ya take masa baya yana fad’in “In sha Allah...”
A haka suka nufi mota sauran jama’an na hangosu kowa ya mik’e suka nufi nasu motocin....

Suna tafe Engr Ma’aruf na hankalce da Akram, agogon jikin motar ya kalla ya kuma duba wanda ke d’aure tsintsiyar hannunsa, tabbas lokacin gudanar da shirin ne... Ya kai duban sa ga radio din jikin motar da alama yau dai Akram mancewa yayi qilan, samun kansa yayi da kai hannun sa jikin radio d’in motar ya murd’ata....
Akram ya d’an dubeshi cikeda mamaki sanin cewa maigidan nashi ba ma’abocin sauraren radio bane hasalima a baya ko kunna radio din motar baiyi saiko kira’a....
Jin bai kamo channel d’in ba yasa shi d’an duban Akram....
Cikin sauri Akram ya rage speed kana ya d’an dubi maigidan nasa, ya gane tashar Radio ‘Yanci yake nema, baiyi zaci Ubangidan nasa har ya zama attached to shirin ba, ya saki murmushi a hankali kana ya d’anyi gyaran murya yace “Ai kwana biyu ba’a gudanar da shirin sabida wacce ke gudanarwa anyi mata rasuwa, hasalima uzurin da ya rik’eni ta’aziya mukaje mukai mata....”

Engr Mutallab ya dubesa da mamaki kana yace “Anyi mata rashi....?”

Akram ya jinjina kai a hankali yace “Eh ranka shi dad’e d’iyarta ta rasu yau kwana uku kenan....”

_D’iyarta_ Kalmar da Engr ya nanata cikin zuciyarsa, bai tab’a kawowa tana da aure ba, a hankali ya maida duban sa ga window ba tareda ya kuma cewa komai ba... Akram ya d’an dube sa ba tareda yace komai ba, lokaci guda ya kunna masu k’ira’an Alk’ur’ani mai girma cikin muryar marigayi Sheik Jabir....

***

KADUNA

Yau kwanan sa uku a hotel d’in duk wasu savings d’insa ya k’aryar dole ya nemi kudi ya biya kudin d’aki sannan yaci abinci.... Drawer dake gefen gadon ya janyo ya ciro wallet d’insa ya zari credit card dinsa guda da bai baiwa Daddy ba a cewarsa wannan account d’in tsohuwar account d’insa ne babu kwabon Companyn mahaifinsa a ciki....

K’asa ya sauk’o domin yin payment saidai to his greatest surprise Card d’in was declined.... Mamaki ya cika Khalid bai tsamman Mahaifin sa nada access to wannan account d’in ba... Girgiza kai yayi don yasan wannan bazai wuce aikin Siyama ba....Wato dai shi har yanzu a gidan kallon yaro ake masa.... Fuzar da iska ya d’anyi had’i da shafa sumar sa kafin ya amshi card d’insa, idan bai biya ba k’arshe dai dole ya bar hotel d’in don ba barinsa zasuyi ya zauna a bati ba.... Ba don yaso ba ya shiga neman layin Baffah....

Baffah na parlorn Ammi tare da su Siyama suna tattauna lamarin wayar Khalid ya shigo masa.....
D’agowa Baffah yai yana dubansu bayan ya dubi screen d’in kana yai murmushi yace “Kun ganshi nan na kira....”
Ammi tai saurin cewa “D’aga d’aga muji mai zaice....”

Baffah ya jinjina kai kana ya d’aga wayar
Daga d’aya b’angaren Khalid yace “Kana ina ne...?”
“Gida.... Why..?” Baffah ya fad’i a tak’aice

“Can you come over to the hotel please....?” Khalid ya fad’i tamkar wanda baison maganar...

Baffah ya dubesu su d’inma shi suke duba da shike a speaker ya saka wayar... Siyama ta masa ido kan yaci gaba da magana...
Baffah yace “Mai kuma zan maka...?”

Gajeren tsaki Khalid yai kana yace “Idan ba zaka zo ba just tell me na nemi hanyar fita before they kick me out... I can’t believe Daddy can go this far... He canceled all of my cards, I can’t even have access to account d’in da nake da tabbacin baida masaniya da ita....”
Mik’ewa Baffah yayi yana fad’in “Alright alright gani nan zuwa....”

Yana katse kiran Ammi tace maza yaje sa ya duba halin da Khalid d’in ke ciki idan akwai debts sai ya clearing ..... Siyama ta saka shewa tana fad’in “Ammi kin gani ko plan d’in yayi aiki yanzu dole Khalid ya dawo gida tinda baida zab’i....”

Ammi ta murmusa kana tace “Ai gwara da aka saka masa pressure na tabbata yanzu zai nemi hanyar gida.....

Yesmin harda mik’ewa tsaye tana tik’a tsallen murna...
Ammi ta yab’e baki tace “Ke kuma meye haka god’e god’e....”

Yesmin ta cuno baki tace “Kai Ammi, ai dai murna nake at last my Kay zai dawo....”

Ammi batace komai ba sai tab’e baki da tayi kana ta mik’e ta nufi upstairs ...
Siyama na dariya tace da Yesmin... “Kinga zama bata kamamu ba, get me my car keys upstairs...”

Da mamaki Yesmin tace “Ina kuma zamu....?”

Siyama ta murmusa tace “of course we’re gonna follow Baffah.... Kinga yi sauri kafin ya fice....”

Yesmin ta dara cike da jin dad’in kana ya nufi upstairs kaman zata kifa.... Sauri sauri motarsu tabi bayan ta Baffah....

Baffah ne ya gama settling bills d’in Khalid d’in gaba d’aya a counter, ba tare da ya dubi Khalid d’in da tun fitowar su ke duban wani gefen ba ya nufi room d’in Khalid d’in, tattare suitcases d’insa da duk wani belonging d’insa ya dingayi without any hesitation.... Nan ya hangi cellphone d’insa saman gado... Ya d’auka da sauri ya shiga trying nan ya samu tana bud’e, kai tsaye contacts ya shiga yana duba weird suna don yasan yanda abokin nasa yake weirdo haka zai saving lambar Nabila....
Teddy bear ya gani harda hoton bear... Baffah ya girgiza kai had’ida murmusawa a fili ya furta “If not Khalid Mainasara who...?”
Cikin sauri yayi copying lambar Nabilah kana ya fito janye da suitcases d’in.. Kai tsaye ya shige yana mai mik’awa receptionist d’an mabud’in....
Khalid ya tsaresa da kallon mamaki
“Ina kake tunanin zanje....?” Ya tambaya yana duban Baffan....
Janyo sa Baffah ya shigayi da d’aya hannun yana fad’in “You need to end this nonsense right now...”
Ya bud’e mota yana k’ok’arin danna kansa ciki Khalid yace “Ba abinda na kira ka kamin ba kenan, thanks for helping out, but I’m not going back to house.....”
Yanda yayi maganar kana iya hango tsantsan kafiyar sa...

Su Siyama da motarsu ke lab’e gefe suka dubi juna...
Suna gani Khalid yasa kai zai shige ya bar Baffah nan tsaye...
Cikin sauri Siyama taiwa Baffan idanu cewa yabi bayanshi...
Aiko tuni ya soma binsa yana bashi hak’uri yana rok’on sa ya shiga mota su tafi..
Da sharad’in bazai kaisa gidan mahaifinsa ba ya shige motar Baffah, basu zarce ko ina ba sai gidansu Baffan, nan ma bai yarda ya bari mahaifiyar Baffan tasan da zuwan sa don kai tsaye sashen Baffan ya wuce kuma yace baiso kowa yasan da zuwansa..
Hankalin Siyama ya d’an kwanta ganin gidans u Baffah ya koma, Yesmin kam ba haka taso ba taso ya koma gida don tayi kewar sa sosai dukda ba shiga hark’arta yake ba...

***

Kano

Sanye yake cikin pajamas d’insa autarsa Najma na kwance gefe saman makeken gadon nasa na alfarma, shiru yayi had’da k’urama waje guda idanu, zancensu da Akram na kuma dawowa kwanyarsa, akwai tambayoyi da dama da yakeso yayiwa Akram gameda ita.... But what if she’s really a married woman...? Ya lumshe idanu a hankali had’ida furta istigfari a fili... Baisan dalili ba, sau d’aya tak ya saurari program d’inta amma muryarta ya kasa b’acewa daga kwanyar sa, shi ba ma’abocin sauraren radio ba amma rana guda tak da ya saurari shirinta yaji yana son sake saurara, maybe sabida itama tana supporting d’insa ne, maybe program d’in yake son sake saurare ba muryar ta ba, da wannan tunanin yaji ya d’an sami natsuwa cikin zuciyarsa...
Ya karanto addu’a ya tofawa d’iyarsa yana k’ok’arin kwanciya kenan ta turo k’ofa ta shigo...
Ko kallon arziki bata ishesa ba ya juya yayi kwanciyarsa....
Tsegege ta tsaya masa aka tana faman huci...
“Engr....”
Shiru bai amsata ba
“Ma’aruf...”
Nanma shiru bai amsata ba idanunsa a lumshe...
Tasan weakness d’in mijin nata idan akwai abinda ke saurin raunanasa shine yaji mace na kuka, kai shi kuka entirely d’aga masa hankali yake... Take Muhibba ta fashe da kuka had’ida silalewa k’asa...

Ya bud’e idanu a hankali ya sauk’esu kanta, fuskar sa ya d’aura saman hannayen sa guda biyu ba tareda yace da ita komai ba....

Muhibba ta kannare idanu taga ya tashi ya zauna nan ta kuma narkewa tana shak’an kuka...
Kukan nata ya shiga d’aga masa hankali...
Shafe kansa ya shigayi yana furta “That’s enough Muhibba... Ya isa haka nan....”

Haba nan fah ta kuma narkewa...
Engr ya fuzar da iska a hankali kana yakai hannu a hankali ya dafata yana k’ok’arin lallashinta don ya gaji da sauraren kukan nata...
Tamkar wacce take jira ta rungumesa gaba d’aya had’ida kwantawa cikin jikinsa zuciyarta na mata fari don tabi shawarin k’wayenta gwara ta lallab’a mijinta su shirya kar azo a kafa gwamnati yayi aure ya watsar da ita wata tazo ta zama First Lady tana nan ita kuma ta koma ‘yar kallo a cikin gidanta, wata tazo ta rabata dashi da kuma yaranta da tayi imani sune rayuwarsa....

***


A tare Abbah da Sameer suka shigo d’akin da sallama saman bakunan su, Raiha na kwance tana shan fruits da Mamani ta yanka mata an ida mata dressing kenan Sister Salma nurse dake mata dressing ko yaushe...

Mamani baki har kunne take amsa sallaman nasu musamman da taga Abbah ya sami lafia sosai har ya iya fito.....


SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_




56


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*


NOT EDITED



Hawaye suka cigaba da gangarowa Mamani dake rik’eda hannayen Abbah....
Cikin muryar kuka take fad’in “Alk’ali da gaske kake da gaske Ma’aruf ya dawo garemu.....”

Abbah ya zaunarta saman kujera a hankali murmushi saman fuskarsa yake fad’in “K’warai Mamani, jikanki Ma’aruf ya dawo.... Ya dawo garemu.....”

Kukan Mamani ya k’aru, k’ok’arin mik’ewa take tana fad’in “ Alk’ali muje maza kaini na ganshi... Kaini naga jikana.... Shin ya girma koh...? Yayi kamanni dakai koh... Alk’ali ka kaini na gansa kafin wani abin ya kuma gifta tsakaninmu....

Sameer dake tsaye gefe kansa a k’asa hawaye suka zubo masa....

Cikin dabara Abbah ya kuma zaunar da Mamani kana yace “Kwantar da hankalinki Mamani, babu abinda zai kuma gifta tsakaninki da jikanki da yardar Allah...” Ya k’arashe yana mai duban Sameer fuska fal fari’a... Shima Sameer d’in su yake duba....
A hankali ya soma takowa.... Ba Mamani kurum da tai zaune tana duban ikon Allah ba harta Raihanah saida ta tsinci kanta cikin wane irin Shock ganin wannan likitan na k’ok’arin zamtowa Yayanta Ma’aruf da ya b’ace shekaru da dama tun kafin a haifesu....
Har gaban Mamani dake zuban hawaye Sameer ya k’arasa ya duk’a... Ya d’ago idanu suna duban juna, hawaye na zarya a fuskokinsu.... Murmushi saman fuskarsa ya sanya tafin hannunsa yana share fuskar tsohuwar da ta zamto Kakarshi a yanzu....
Mamani ta kasa furta komai sai hawaye dake kwaranyo mata, abubuwa da dama suka dinga dawo mata, ta jima tanajin babban al’amari gameda likitan nan ashe dai shid’in jikantane da yafi soyuwa a gareta, shid’in jininta ne, Ma’aruf d’inta ne.... Lokaci guda hannayenta na rawa ta d’agosu gaba d’aya tana shafa fuskar Sameer hawayen farin ciki na kuma wanke mata fuska.... Cikin rawar murya take furta “Ma’aruf.... Ma’aruf d’ina..,, Da gaske ka dawo garemu masoyina..., Shin da gaske kaine...”

Sameer na jinjina kai yana hawaye ya rik’e hannayenta duk biyu murmushi bai bar saman fuskarsa ba yake furta “Ni ne, ni ne Ma’aruf d’inki Kaka.... Na dawo na dawo cikin ahalina.....” Bai kai aya ba Mamani ta rungumeshi sosai sabon kuka na taso mata, tamkar wacce take tsoron kada a raba tsakaninsu haka ta rungumesa tana kuka take fad’in “Alhamdulillahi Allah mun gode maka, kaine abin godiya.... Allah mun gode maka da wannan babban baiwa daka mana... Ma’aruf...” Ta Kuma fad’i tana mai rungumarsa...
Sameer ya maida mata martanin rungumar a hankali yana mai jin k’aunar tsohuwar da tsananin tausayinta cikin zuciyarsa...
Abbah da Raihanah dake dubansu cikeda tausayawa suka goge k’wallan da ya zubo masu...
Ashe dai mutumin nan d’an uwantane, mutuminda kwatsam lokacin da duk ta fad’a cikin damuwa yake zuwa rescuing d’inta, Allah sarki Allah mai yanda yaso ashe dai sunada babban alak’a ta ‘yanuwantaka.... Ta sauk’e ajiyan zuciya sanda ta sinkayo muryar Mamani tana fad’in “Alk’ali ka fad’imin ya hakan ta kasance, ya akai tuntuni bansan jikana na kusa dani ba....?”

Abbah ya d’an dubi Sameer shima Sameer d’in Abbah ke duba... D’an gyaran murya yayi ya kuma kamo hannayen Mamani kana yace “Mamani you need to rest, ya kamata ki huta sabida a shekaru irin naki ba’aso zuciyarki na d’aukan abubuwa da dama, mubi komai a hankali kinji Kakata, ina nan yanzu babu wani abinda zai kuma rabamu da yardar Allah....” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa hannayensa rik’e cikin na Mamani...

Murmushin itama take tana kuma shafan fuskarsa kana tace “Nidai ina son sanin komai gameda b’acewarka sannan a ina ka girma, su waye suka saceka... Kawo girmanka da karatunka... Su waye suka rabani dakai.... Shin kanada iyalai... Idan kanadasu ina suke.... Inaso naga d’iyoyinka na rungumesu cikin hannayena.....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Sameer ya mik’e daga tsugune ya zauna gefen Mamani ya kuma rik’o hannayenta cikin nasa kana yace “Da sannu zaki san komai Mamani, abinda nakeso yanzu shine ki huta anjima zan sanar dake komai da kaina...”
Mamani ta girgiza kai tace “A’a nidai ka sanar dani yanzu... Ina d’iyoyinka....?”

Sameer ya mata k’uri zuciyarsa na harbawa a hankali don sai yanzu ya tuna baiko sanar da iyayensa nada mata ba, ita kanta Siyamar sai yanzu ta fad’o cikin zuciyarsa....
Saida ya d’anyi gyaran murya ya d’ago ya dubi Abbah kana yace “Abbah I’m sorry I haven’t told you this part of the story....”
Ya maido da dubansaga Mamani kana yace “Inada iyali wacce aurenmu shekara guda kenan.... Amma tukuna Allah bai bamu haihuwa ba....”

Abbah ya dubeshi da kayu kana yace “Kanada mata Ma’aruf....?”

Sameer ya jinjina kai yace “Eh Abbah, inada mata Siyama amma a hanlin yanzu tana can Kaduna shiyasa ban kawo maku ita ba.... Kai hak’uri Abbah ban samu na sanar daku da wuri ba... Abubuwa da dama sun faru ko nace suna kan faruwa...”

Dafasa Abbah yayi kana yace “Babu damuwa Ma’aruf... A hankali zamusan iyalinka, itama a halin yanzu saika natsu ka sanar da ita abubuwan da suka faru... Kar ka damu kaji koh mubi komai a sannu....”
Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “Na gode Abbah....”

Mamani ta yab’e baki tace “Ya kamata dai a kawo mana ita, sashen dake gefena nan za’a gyare maka ka saka iyalin taka ciki...”

Sameer ya murmusa yace “Yanda kikeso Mamani hakan za’ayi....” Cikin zuciyarsa kuwa zullimin yanda Siyama zata amshi nasa family d’in yake balle ace zata zauna a family house d’insu...
A haka Awwab ya shigo daidai lokacin da Abbah ya isa jikin gadon Raihana suna gaisawa...

Awwab ya taddasu gaba d’aya suka gaisa nan yake sanar dasu cewa yau za’a sallami Raihanar ma....Mamani da Abbah sukai hamdala suna godiyawa Allah da fatan ci gaba da samun sauk’iga Raihanah....

Sai sannan Sameer ya d’ago ya dubeta, sukai idanu hud’u... Ta sadda nata idanun k’asa a hankali....
Hannun Awwab ya kama kafin suka fice domin tattaunawa.....

***

Zaune suke saman kujerun SUG da aka k’awata gefen azuzuwan nasu dashi, su Safwan dasu Yusrah na duba test questions d’in da suka fito sai jajanta applied questions d’in da Malamin ya masu suke masu tsananin rikitarwa...
Yusrah tace “Toh Safwan idan kunyi kuka mu kuma muyi mai, ku masu jan ajinma kenan... Gaskiya mutumin nan zaici ubanmu a exams...”

Safwan yace “Karku damu In sha Allah haka zai barmu mu wuce duk iyawarsa... Ni barin k’arasa na amshi folder na a cafe d’in Mouses naga yau k’awar taki ko iya magana batayi Dr KB ya bata tsaraba...” Ya k’arashe teasingly yana mai kallon Nabilah da har lokacin shiru take tamkar wacce ruwa ya shanye....

Yusrah ta maido da dubantaga Nabilah tace “Ke wai lafiyarki...? Na kula kwana biyun nan kaman wani abu na damunki, ko har yanzu jimamin rashin Kausar kike ne....?”

D’an jifanta da gajeren harara tai kana tace “Muje da Allah....”

Rik’e hannunta Yusrah tai kana tace “Nabilah we are not leaving this place har sai kin fad’a min abinda ke damunki... Nasan akwai wani abindake damunki, I know you so well... Na sani idan kina b’oyemin wani abin.... So just tell me please... Kinji k’awata...”

Harara Nabilah ta kuma jifarta dashi kana tace “Stop being silly already... Muje da Allah, nace maki babu komai... Ba komai....”

Yusrah ta kuma rik’o hannunta suna duban juna....

Gajeren tsaki Nabilah tai kana tace “Its pointless, banga amfanin fad’a miki ba, mu tafi dan Allah....”

Yusrah ta kuma rik’e hannunta wannan karon with a serious face tace “Is it about Khalid....?”

Kafin Nabilah ta sami zarafin bata amsa wayarta ta d’auki ruri....

Saurin lalub’ar wayar ta shigayi daga cikin jakarta, ta k’urama wayar idanu ganin bak’uwar lamba ce mai kira....
Kaman bazata d’auka ba har saida ta kusan katsewa kafin ta d’aga cikin sanyin jiki.....

Daga d’aya b’angaren Baffah yai mata sallama kana ya k’arada “Allah sa ina maganane da Nabilah Mailafiya....?”

Kaman wacce batason amsawa tace “Wake magana.....?”

Baffah yace “Sunana Baffah abokin Khalid...”

Gaban Nabilah ya yanke ya fad’i don rabonta da Khalid kusan sati guda kenan... She can’t deny the fact she really wants to hear from him, at least to know about his well being.... Muryar Baffah ya katseta sanda yaci gaba da fad’in “Idan bazaki damu ba magana akan Khalid...”

Cikin tsananin tashin hankali take fad’in “What what happened to him... Mai ya sameshi....” Yanda tai maganar zai tabbatar maka da tsananin damuwa da tashin hankali da take ciki....

Baffah ya sami k’warin gwiwar mata magana... Bai b’oye mata komai ba gameda halinda Khalid ke ciki... Hankalin Nabila idan yayi dubu ya tashi... She couldn’t help but to feel guilty, gani take laifinta ne Khalid ya shiga halinda yake ciki a yanzu... Bazataso fushin iyaye yayi tasiri akan Khalid ba don tasan tabbas fushin iyaye na tareda na Ubangiji...
Idanu rau rau take duban Yusrah kana tace “Yusrah I need to talk to his parents, bai kama suyi fushi dashi har haka ba... I need to convince them cewa bamu tareda Khalid....”

Dafata Yusrah tai kana tace “Ban gane baku tare ba...”

Nabilah ta jinjina kai a hankali tace “Is the truth Yusrah.... Dama tun can ba soyayya muke ba, so I see no reason da zaisa su sallami d’ansu a sabida ni...”

Yusrah tai shiru na d’an lokaci kana tace “Toh what’s your plan now?..”

Nabilah ta fuzar da iska kana tace “Of course I’ll confront his parents and apologize on his behalf tinda shi baisan abinda yake daidai a rayuwarsa ba, ni bazan tab’a rabuwa da nawa family d’in a sabida shi ba don haka shima bazanso ya rabu da nasa a sabida ni ba... Na sani fushin iyaye ka iya tasiri a rayuwarsa....”

Yusrah ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “But this is none of your fault, it’s his decision... Ba ke kikace ya bar gida ba so banga dalilin zuwanki gidansu ba....”

K’uri taiwa Yusrah kana tace “Idan har zuwana zai canza zuciyar iyayen then zanjeni.... I don’t want him to go astray....”

“Toh waye zai kaiki gidansu sannan ta ya zaki fara fad’i a gida....?”

Shiru tai na wasu lokuta kana ta d’ago tamkar wacce aka zabura tace “Aunty Bara’atu..... Aunty Bara’atu will help me... Har muje mu dawo su Mamy bazasu sani ba, zan sanar da Mamy gobe daga sch gidan Aunty B zan wuce idan yaso nida ita sai muje don dai day trip tinda ba wani nisa bane...”

Yusrah tai shiru kana tace “Kenan bazakiyi classes gobe ba...?”

Nabilah ta jinjina kai a hankali tace “Bazan shigo sch ba gidan Aunty B zan wuce, daga nan ma gidanta zamu wuce naje mata da batun don ta kwana dashi although bansan yanda zata d’auka ba....”

Yusrah ta jinjina kai tace “Shikenan Allah ya zab’a miki abinda yafi alkhairi k’awata....”

Nabilah ta amsada Ameen jiki a sanyaye kana suka shige...

Koda suka sami Aunty B da batun da k’yar ta yarda a cewarta bataga dalilin baiwa iyayen Khalid hak’uri da zataje yi ba tinda ba ita tasa ya bijirema buk’atarsu ba... Hasalima zuwan nata ka iya worsen abubuwa... Da k’yar dai Nabila ta shawo kan Aunty B ta amince da buk’atarta...

Har bakin gate Aunty B tai masu rakiya ta kuma basu kud’in abin hawa.... Har sunyi sallama Aunty B ta kirawo sunanta....
“Nabilah...”
“Na’am Aunty...” Nabila ta amsa had’ida juyowa

Takowa Aunty B tai kusanta a hankali kana tace “Yaya Zulfa’u....?”
Dashike tun bayan rasuwar Kausar Zulfah bata dawo gidan Auhty B ba tanacan gidansu...

“Tana nan lafiya, bakuyi waya bane yau....”

Aunty B ta jinjina kai a hankali kana tace “Ki gaidamin ita idan kinje... Yayanku Ma’aruf fah...?”

Nabilah tace “Bai yini a gidan kinsan likita ne....”

Nanma jinjina kai Aunty B kana tace “Allah ya tsare... Yusrah ki gaida Mama kinji koh...”

Yusrah ta amsada “Zataji Aunty mun gode....” Kana suka fice

Jiki a sanyaye Aunty B ta komo cikin gida lokaci guda ta lalumi wayarta dake kan kujera, k’uri taima wani lamba hawaye tab idanunta... ‘Yan uwanta ne batada wanda yafi mata su a rayuwa... Ta sani Yaya Abidah bata ga maciji da Mamy.... Alwashi ta d’au ma kanta In sha Allahu kafin d’aya daga cikin su ukun su bar duniya sai ta daidaita tsakaninsu da taimakon Allah.....



SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_



57




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



NOT EDITED



A motar Sameer suka dawo gida gaba d’aya dashike anyi sallamar, Hajiya Mamani an kasa sakin Sameer gaba d’aya gani take kaman zai kuma tafiya ya barsu... Nan ta shiga ‘yan dube dube a d’akin nata cikin shirginta na tsofi da ba’a rasa ba tana neman abin baiwa Sameer... Shiko Sameer sai aikin murmushi yake zuciyarsa nai masa dad’i bai tab’a kawowa nada babban family irin haka ba, matan su Baffah Ado da d’iyoyinsu sukaita shigowa suna gaida Raiha had’ida barkawa Mamani na dawowar Ma’aruf....
Sameer ya yarda shid’in d’an dangine ganin yanda aketa shigowa ganinsa daga k’ofa k’ofa... Da k’yar ya samu ya silale daga sashen Mamani ya nufi parlorn Abbah yanda ya tadda iyayen nasa gaba d’aya, sai sannan Mamy ke tambayarsa gameda matarsa Siyama....

***

A can gidan Baba Alhaji kuwa Hajiya Haule tayi kicin kicin da fuska tana tunanin yanda akai har Ma’aruf ya rayu ya kuma dawo gida wajen danginsa, ko shakka babu Aminiyar sirri ta yaudaresu, amma idan tasan wata batasan wata ba, lokaci yayi da zata fasa k’wan kowa ya sani tinda dai abin ya zama haka....
Baba Alhaji dake cin abincinsa hankali kwance ta kuma watsawa mugun kallo kana ta karkata tai gyaran murya....
“Alhaji wai ni nace ka kaw san abindake faruwa...?”

D’agowa yayi yana dubanta kana yace “Meke faruwa kuma....?”

Gyara zama ta kumayi kana tace “Bakada labarin dawowan d’an d’an uwanka...?”

Gyara zama ya kumayi had’ida aje cokalin hannunsa kana yace “Ban fahimceki ba Haule....”

Hajiya Haule ta kuma tab’e baki tace “Yo ai bakada amfani a wajensu shiyasa ba’a sanar dakai ba, basu d’aukeka bakin komai ba, sam Usman baya darajaka baya baka girman da ka riga ka fishi, bacin haka ace an doshi sati guda da bayyanar Ma’aruf amma babu wanda ya sanar dakai.....?”

Sauran abincin dake bakinsa ne ya kusa k’waransa... Ya kuma duban Hajiya Haule yace “Haule kinaso kice min Ma’aruf ya dawo gida bayan duk shekarun nan da aka d’iba baya nan....?”

Hajiya Haule ta jinjina kai tace “K’warai kuwa.... Ma’aruf ya dawo...”

Baba Alhaji yai shiru na d’an lokaci kana yace “Shine babu wanda ya sanar dani.... Usman bai fad’a min ba....”

Hajiya ta kuma yab’e baki tace “Toh yaushe kuwa zai fad’a maka tinda ba amfani kakedashi a wajensa ba, ita kanta mahaifiyar taku k’ark’ashin kulawarsa take yo ba dole ba, gaba d’aya ya amshe girman naka, ‘yan uwanku girmansa suke gani ba naka ba tinda ya yanka masu matsuguni a gidansa, yanzu gashi ance Ma’aruf babban likita ne kuma iyayen rik’onsa da alama masu kud’i ne sosai, na tabbata Mamani babu abinda zatai dakai yanzu balle ‘ya’ayanka zaka kuma zama maras amfani a wajenta....” Ta k’arashe tana mai k’ura masa idanu.....

Shiru yayi na wasu lokuta kalaman Haule na kuma tasiri a zuciyarsa... Lokaci guda ya mik’e ya hau zira takalma...
Haule ta mik’e tana k’ok’arin rik’esa take fad’in “Ina kuma zaka....?”
Ba tareda ya dubeta ba yace “Zanje naga d’an d’anuwana....”
Bai kuma saurarenta ba ya fice cikin sauri tamkar zai kifa k’asa, wani abu na yawo cikin zuciyarsa...

Hajiya Haule ta rakasada mugun kallo har ya fice kana ta buga tsuka tayi shigewarta d’aki...
Najah dake zaune can gefe a idonta akayi komai

Please Login or Register in order to submit comment