Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanda bai ba ta taho suyi wankan tare amma tak’i saima dad’a lumewa cikin bargo da tai, Ta janyo k’aramar hotonsu da aka sanya cikin k’aramar frame Wanda Ke aje gefen bed side d’in Engr tana kallo, hotonsu ne da suka d’auka a Maldives Island, ta saki murmushi a hankali dan wannan waje memories ne da bazai tab’a gogewa cikin zuciyarta ba... Wayarta dake gefen bedside d’in ta janyo ta shiga gallery tana kuma kallon pictures d’in da suka d’auka, wasu a bakin beach wasu a wajaje na nan sha’awa... Wasu pictures d’in su duka biyu sunyi funny faces... Harda video da suka d’dd’auka.... Idan ta tina abubuwan da suka faru saidai kawai ta d’an saki murmushi.... Engr k’arshene wajen mantar da mace dik wani damuwar dake damunta, a bainar jama’a gashi nan zaka ganshi very calm and gentle amma idan suka keb’e ita kad’ai tasan mai Gwamnan nata yake juye mata... Ta kuma lumshe idanunta a hankali tsantsan k’aunarsa na azalzalanta.... Kaman daga sama sai jin d’igan ruwa mai d’an d’umi tai a bayanta.... Kan tai aune ya mirgino da ita suna fuskantar juna....
“Tashi muje na wankeki tinda na kula kasalanki da k’iwanki ya soma yawa, idan na biye naki zamu makara....!”
Ya k’arashe yana k’ok’arin janyota jikinsa....
Baki a ture take fad’in “Haba my Governor... Is my presence that necessary, Nidai kawai bazan iya zuwa ba.... Wllhi bacci bai isheni ba....!” Ta k’arashe tana kuma sakin hamma had’ida mik’a tana mai k’ok’arin turasa daga jikinta....
Rausayar da idanunsa ya d’anyi kana yace “Alright idan bazakije ba saidai kada a rantsar dani.... Muyi swearing in d’inmu a nan... Dama nafi san hakan....!” Ya k’arashe yana mai kashe mata idanu had’ida wasu salo nasa na musamman.... Ai a d’ari ta shiga turasa tana fad’in zata tashi, tana k’ok’arin zillewa daga hannunsa....
Saidai mik’ewar da zatai jiri ya d’an taso mata.... Ya dubeta da kyau kana yace “My lady.... Are you sure you’re alright...?”
Jinjina masa kai tai tana mai kuma sakin hamma tareda mik’a take fad’in “I’m fine don’t worry about me... Let me use your bathroom k’iwan zuwa nawa nake...” Ta k’arashe tana mai fad’awa bathroom d’in, shidai Engr kallo ya bita dashi had’ida d’an ware idanunsa kana ya mik’e yana k’ok’arin shiryawa, ya kula kwana biyun ta canza sosai... Yana nan tsaye closet ta fito tana rik’e baki da hanci take fad’in wannan shower jell d’in nasa baida dad’i da alama ya canza....
Dubanta ya d’anyi kana yace “Baby ban canza ba fah... Wannan dai da kike so ne....”
Ta d’an yamutsa fuska kad’an kana tace “Really... Toh gaskiya flavor d’in ya daina min dad’i ka canza wani....”
Jinjina mata kai yai yana mai takowa kusanta, lokaci guda ya d’an kamo k’ugunta yana mai furta “Right away, an gama your Excellency Ma, sai wanda kika zab’a.... But wait, are you sure babu abinda kike b’oye min...?”
D’an zaro idanu tai tana dubansa kana tace “Ni kuma...!”
Ya d’aga mata gira guda still yana rik’eda k’ugunta.... Lokaci guda yakai hannunsa guda saman flat tummy d’inta yana furtawa a hankali “Are you sure babu ajiyana a nan...?”
Zabura ta kumayi tana dubansa, sai kuma maganarsa ya soma ringing a kwanyarta.... Ta d’an muskuta kad’an kana tace “No ni dai babu komai... Just get dressed up kafin ka makara..” Tai maganar tana mai zillewa Daga rik’on da yai mata kana ta nufi k’ofa a d’an guje tana mai shafe cikinta dan tuni taji wani strength yazo mata...
Bud’e murya ya d’anyi yana mai fad’in “Be careful Love... Watch your steps kar kimin asara....!” Ita dai ko kulasa batai ba kayanta ta shige tana mai kuma murmusawa dafe da cikinta...

Langab’e da kai Engr ke dubanta har ta b’acewa ganinsa tsantsan soyayarta na azalzalansa, rayuwarda yaita mafarkin samun irinta a gidansa, yau gashi nan yana experiencing... Ashe dai tabbas yanada RABON hakan.... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai k’ok’arin shiryawa da kayan da Ta fitar masa....

Haka suka d’unguma suka fita shida family d’insa gwanin ban sha’awa....

Da shike akan kunnawa ‘yan prison tv su kalli news a nan Muhibbah take kallon bukukunan rantsar da Engr matsayin gwamnan jiha ga Zulfa’u da yaransu a gefensa gwanin ban sha’awa sun bala’in dacewa da birgewa... Hawaye suka gangaro mata tana mai gogewa a hankali, Allah sarki da yanzu itace nan tsaye gefensa sanda ake rantsar dashi amma sai gashi tana gidan kaso ake rantsar da Excellency d’inta... Kai kaicon aikin danasani.... Shamzy ta dafata a hankali cikeda tausayawa dan dole ne ka tausayawa.. Murmushin k’arfin hali kurum Muhibbah tai tana mai tashi daga wajen dan harga Allah bazata iya jure ci gaba da kallon ba....
Abinda yaiwa Muhibbah dad’i shine ziyara da suka kawo mata har nan prison gaba d’ayansu, sukai nasu murnar tare da yaranta gwanin dad’i, batada abinda zata sakawa Engr dashi sai addu’a...

A haka akaci bukunan rantsar da mai girma gwabna, dangi gaba d’aya an hallara su Mamani su Abbah su Daddyn Siyama Daddyn Sameer, su Mamy su Ammi Aunty B Aunty Daula da dai sauransu, su Nabilah ne dai basu zo ba dasu Siyama su Raihanah tinda wata mai kamawa ake bikinsu Naja’atu da Akram da kuma Shamsu abokin Sameer da Marliya, ga kuma na Dr Awwab da Sahariyya dan tinda yai treating d’inta Allah ya nufa ashe Sahariyya ce matar, Dr Awwab ya tab’a aure amma yanzu basa tareda matar, ya jima babu aure tin bayan rabuwarsu da wancan har saida Allah ya had’asa da Sahariyya a halin yanzu... Da RABON shine mijinta, wannan karon harta su Amarah saida Sahariyya ta gayyata, sukaita murna suna bata hak’urin abubuwan da sukai mata baya...

Daga wajen shagulgulan rantsuwa aka shige da Zulfa’u asibiti dan ta kusa fainting a can yanda aka tabbatar masu tana d’aukeda juna biyu... Wai Zo Kaga murna wajen Engr sai kace ba’a tab’a masa haihuwa ba... Zuri’a tanata Albarka sai san Barka da alama ta ko wanne b’angarorin an sami RABO... Saidai muce Allah shi raba lafiya ya kuma bada masu jin k’an iyayensu wanda zasu amfani Al’umma baki d’aya.....
Tuni Engr ya rarraba muk’amai ciki harda Hafiz, shima ya sami appointment a gwabnatin Engr yanda aka basa SSA to the security matters, Wato Senior Special Adviser to the Security matters dan tinda ya taka babban rawa wajen capke Oga Duna mai girma Gwabna Wato Engr yaga baza’a kyale Hafiz haka nan ba, dole ai tafiyar taredashi dan ya ringa taimakawa ana capko b’ata garin Al’umma....
Su Hafiz an zama babban mutum har wani kamala ya k’ara saidai ko batun aure baiyi, haka Mamani zata tasa sa gaba tana k’are masa tanadi saidai yace oho dai yaji, gani yake kaman garin neman aure zai kuma nemo irin Sawwama shed’aniya jarabebbiya da taso jefasa a halaka...

***

ABUJA

Agogon dake d’aure tsintsiyar hannunsa na hagu ya kuma dubawa yana mai fad’in “Wai ina Shayibun ya tsaya ne, banso muyi missing flight d’in nan, dan idan muka rasa wannan flight d’in saidai mu fasa tafiya Kano...”
Baki a ture take harararsa kana tace “Tab! Aiko wllhi saidai kai ka fasa amma nikam sai naje, biki har uku... Lallai ma ai ko a mota ne sai na tafi...!”

Tsareta da idanu yai fuska a tsare kana yace “Waye zai barki Ki hau titi kije Kimin asara, ai keda tafiya by road sai kin haihu... Ni da ta nine ma bazakije Bikin nan ba kawai dan dai kin dage ne...”
Cuno baki ta kumayi cikeda shagwab’a tana fad’in “Wato baby ne damuwarka bani ba koh....?”
Khalid dake k’ok’arin k’unshe dariyarsa janyota jikinsa yai yana fad’in “Wane ni teddy bear, ai ban isa nace haka ba... No one can ever replace you... Kawai banso kisha wahala ne kinsan ina matuk’ar k’aunarki da dik abinda zai faranta miki...”

Murmusawa tai a hankali tana mai dubansa cikeda k’aunarsa daidai sanda suka soma jiyo alamun bud’e gate Shayibu ya iso d’aukansu zai kaisu Airport.....
A hankali ta furta “I love you... My bear...!”
Ya manna mata kice a hankali yana mai furtawa “I love you more...teddy bear...!”
Lokaci guda ya sakalo hannunsa cikin nata yana fad’in “Shall we...”
Jinjina masa kai tai tana mai shigewa cikin jikinsa suka nufi k’ofa....

***
KANO


Taro yayi taro, zuri’a tai Albarka, an cika iyaka cika a wanann biki.... Kowa ya hallara, su Mamani ba’a sama ba’a k’asa... Ita bama ta ‘yan biki take ba wak’ar nan ta Engr na lashe zab’e da Rarara ya rera masa shi tasa aka k’ure mata sai tik’an rawa take kayanta Goggonayen Kazaure na tayata lokaci guda jama’an dake wajen na darawa cikeda nishad’i.... Su Sadiya sai d’aukarta suke suna fad’in yau sai status d’insu yai kuka.....Lol

A can b’angaren Mamy kaw,su Ammah dasu Aunty Daula, Mummyn Sameer harma da Ammi sune acan suna nasu bidirin harda Aunty Hanne da Yesmin sunzo... Aunty B ce ta shigo tana sanar da Mamy yanda sukaida Major Kabir Kaita mijinta da a yanzu ya kuma samun matsayi ya dawo gareta yana mai bata hak’uri kan cewa ta bisa cen Lagos tinda yanzu tayi settling family d’in nata kaman yanda ta buk’ata daga garesa wanda hakan ne musabbabin samun sab’aninsu dan cewa tai bazata abandoning family d’inta a halin da suke ciki a baya ta bisa ba, hakan yasa sukaita samun sab’ani toh yanzu dai ga Allah ya karkato mata da hankalinsa.... Su Mamy dasu Daula su Ammah sukace k’warai tabi mijinta dan ta cacanci Farin ciki itama bayan d’inbin SADAUKARWAR da taiwa Ahalinta.... Major Kaita ya shigo ya gaisa dasu ya kuma basu hak’uri da jaddada masu cewa zai kula da ‘yar uwarsu ya kuma bata kulawan da bai bata a baya ba... Farin ciki ya lullub’e ahalin Aunty B bayan dik abubuwan da tai masu basusan da mai zasu saka mata ba tabbas addu’arsu ce zaita isa gareta har yanda take... Nan Aunty B tai baiwa mijinta hak’uri itama dan ko shakka babu tana k’aunarsa... Haka sukai sallama da sauran ‘yan uwa ba’a ida Bikin da ita ba tabi Mijinta Major Kaita suka tafi daga can Lagos d’in zasu wuce k’asar Russia yanda zai gudanar da wani course...

Shagalin biki yaci gaba da gudana bayan an gama koke koken sallama da Aunty Bara’atu babu kaman Zulfa’u wacce take ‘yar gidanta.. Aunty B d’in ta jaddada mata da zaran ta haihu in sha Allahu dik yanda take zata baro tazota ganin grandson ko granddaughter d’inta....

Su Zulfa’u, Siyama, Raihanah harmada Yesmin suka d’unguma suka nufi gidan Baba Alhaji zasu taho da amaren gaba d’aya nan wajen Mamani yanda za’a gudanar da family eve, suka shiga gidan kace kace Haule na lale dasu... Ita kam Yesmin can k’ofa aka barta tana faman danna waya, nan taji taci karo da mutum... Ta d’ago dafe da goshinta tana watsa masa harara... Shima fuska a murtuk’e yake dubanta, kan Hafiz yai aune ta shiga silla masa masifa... Da tsananin mamaki yake dubanta kana yace “You watch where you’re going next time....”
Ta kuma hararsa tana fad’i a hankali “he’s so mean...” Tana maganar tana sosa goshinta...
Juyowa yai kad’an kana yace “Mai kikace....?”
Hararsa itama tai kana tace “Kai mai kaji nace..?”

Ga tsananin mamakinta murmushi taga yayi da gefen bakinsa kana yace “Naji kince he’s so handsome that I couldn’t take my eyes off him...!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice yana kuma sakin murmushi...

Tsaye tai tana bin bayansa da kallo har ya b’ace mata murmushin da bata san daga ina bane ya kufce mata....
A haka suka fito da amaren yanda suka nufi hamshak’an motocinsu na alfarma dake jiransu waje tareda jagorancin Matar mai girman Gwamna kuma First Lady Zulfa’u....

Bayan sun isa gidan Mamani ne suka tadda draman Mamani da Khalid ya kasa ya tsare yace matarsa bazatci sha daka da Mamani ta bata ba a cewarsa kar yai affecting babynsa...

Mamani ta dangwari k’eyarsa tana fad’in “Kai Haladu bana san iyayi d’in nan Naka... Wato kaima ka iya felek’e toh sai taci nace sai taci... Ungo d’auka kici, Wato kai ga mai mata da d’ah koh... Ungo Ci shadakanki kai waysan mai akaci da cikinka....” Ta k’arashe tana mai mik’awa Nabilah dake masa gwalo tana fad’in “Yauwa Mamani na yau dai bayana kikabi kin gwansa d’an gaban goshi...”
Mamani tace “Ai kema ba sabida ke na bada ba dan tattab’a kunnena dake cikinki na so ne... Kinsan d’an Haladu dole ya zama na gaban goshi na... Gaba d’aya suka dara daidai sanda Su Mamy dasu Ammi harma dasu Haule dik suka shigo za’ai family pictures, Nan Khalid ya fice kiransu Abbah a cewarsa ya kamata ai gaba d’aya...

Jim kad’an kaw suka shigo gaba d’ayansu mazajen harma dasu Engr dasu Sameer su Hafiz... Gaba d’aya sunsha manyan kaya da huluna masu d’aukan idanu gwanin ban sha’awa saikace sun fito daga sallan idi...

Mamani na tsakiya zuri’arta na hallare gewaye da ita hawaye ya d’igo mata tana ayyanawa cikin zuciyarta yau Ina Mahmud Mailafiya yaga wannan kayan Farin ciki... Ko yanzu tabar duniya Alhamdulillah itakam babu abinda zatace sai godiyawa Ubangijinta...Allahu Akbar Zuri’a tai Albarka... Wai akace INDA RAI DA RABO.... Take camera man ya saita camera d’insa don d’aukan wannan kyakkyawan ahali yayinda nima na aje alk’alamina da nai amfani da ita wajen rubuto maku wannan labari mai cikeda abubuwa iri daban daban ciki nace kai nima dai bara na d’auko maku hoton wad’Annan ahali... Take na saita camera d’in wayata nima na d’aukar maku hoton... Nasan su Ahalin SAN suna nan suna jira suga hoton nan dan ga su Sadiya Auwal su Oum Imaan su Fatee Beni su Bintaa su Laweesa su Mrs Deen su Maman Sadiq su Baby Mahe su Nafisa Wala su Maamah su Halima Mekeke su Oum Noor su Zynab Maude su Maryam Mu’az, Maman Hanan, Yasmeen, Hauwa Muhammad, su Bilkeesu,Raheela, su Maryam Muhammad... Su su su kai kunada yawa duk kunsan kanku masu jiran ganin hoton nan... DA RABON kuga hoton yasa na d’auko maku... LOL

ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!!

A nan na kawo k’arshen wannan labari mai taken INDA RAI DA RABO.....Dikkan yabo da godiya Sun tabbataga Allah da ya bani damar kammala wanann littafi cikin kwanciyar hankali bayan dogon zango da aka kwashe ana rubutunsa... Fad’akarwar dake ciki Ubangiji yasa mu amfana dashi, kurakuren dake ciki Allah ya yafemu gaba d’aya... Ameen!


Jinjina gareku dan kun cancanta...
Engr Sholyngaye
Aunty Hasken Annuri
Aisha Amaal Bappah
Sameena Aleeyou Novels(SAN)
Zauren Biebee Isa(ZBI)

Ubangiji ya bar k’auna🤝

Ina kuke Trio😍 AKA Partners💯 littafin nan d’aukacinsa sadaukarwace gareku... Ko ban fad’i ba ku kunsan namijin k’ok’arin da kukai wajen ganin littafin nan ya kammala... Ubangiji ya bar k’auna... Raliya Garba(Rally), Maimuna Mansoor(Anmunah), Aishatu Dahiru Audi(Shawty)....Sonso fillah❤️

Sameena Ke maku fatan Alheri a dik inda kuke🤝


SameenaAleeyou📚


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment