Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

canzawa lokaci guda, da alama bataso suji wayan nata...
Basu kuma bi takanta ba sukaci gaba da firansu suna cin k’osan...

Koda ta d’aga wayar bata iya cewa komai ba, sannan tunda taji shiru daga d’aya b’angaren tasan shine...
Tsuka tai zata katse kiran tana mai furta “Sai a kira mutum ayi shiru don rashin abinyi, toh ni inada abinyi...”
Khalid ya katseta da fad’in “Don’t think of doing that, no one hangs up on me, wama yace miki ke ake nema, bansan ya akai na kiraki ba amma nasan dama addu’a kike na kiraki d’in, so don’t pretend...”
Tamkar yana kallonta haka ta juya idanu kana tace “Allah kiyaye nayi fatan ka kirani ko na jira kiranka, kada ka mance da bakinka kace bakasan yaya akai ka kirani ba so kaine mai d’okin kaji daga gareni...”
Tinda ta soma magana yake murmushi yana wasada hannun had’edd’iyar shopping bag d’in dake gefensa yana imagining yanda take murgud’a baki da juya idanu...
A hankali cikin kashe murya yace “You haven’t asked about my wound..”
A hasale tace “Toh ni ina ruwana da ciwonka, wai dan Allah baka da abinyi ne sai damuna...”
“You know what your problem is....?”
Shiru tai kurum tana saurarensa sanda yaci gaba da fad’in “You don’t know much about psychological trauma, that’s a serious problem... Ko tun kafin na kuskuri bigeki da mota haka kike...?”
Kasa furta komai tai sabida tsaban takaici gashi ta kasa katse wayar mai yake nufi mahaukaciya ya d’auketa ko mai, for the first time da tai masa magana cikin tsananin raunanniyar murya “Idan ka kira ne just to insult me Dan Allah na rok’eka kada ka sake kirana...”
Khalid yayi shiru yana saurarenta ba tareda ya furta komai ba...
Su duka biyun sunyi shiru, yanajin sanda tai yunk’urin katse wayar... Yai yunk’urin dakatar da ita amma baisan mai zaice ba, hak’uri zai bata ko kuwa, ya ake bada hak’urin shine bai sani ba, tabbas ta d’auki maganarsa da tsananin zafi yana iya gano hakan a muryarta....A hankali ya lumshe idanunsa had’ida fuzar da iska yana kuma bin shopping bag d’in da kallo wanda yasan gobe akwai aiki gabansa muddin ya tunk’areta, kaman ya fasa tafiyar yaji amma b’angare na zuciyarsa tana kwad’aitar masa tafiyar more than ever, a hankali ya shiga d’an buga kansa da hannu yana tunanin maike damunshi gameda al’amarin yarinyar.....
Mik’ewa yayi yana nad’e hannayen longs sleeve d’in dake jikinsa kana ya fad’a bathroom don gwara ya fice ball ko zuciyarsa zata samu sauk’i da tunaninta....
Yesmin kaw da shigowarta kenan ta ajiye masa k’aramar plate anyi wrapping da climfilm wani dad’i ne taji ya mamaye zuciyarta hango shopping bag da tai hadd’add’e kalan mata ajiye saman gadonsa, zuciyarta ta shiga raya mata ma ita zai bada, a hankali ta sad’ad’a tana lek’a cikin ‘yar jakan, bata gama sumewa ba saida taga abinda ke ciki, ita kad’ai ta fad’a duniyar imagination tana murna harda ‘yar tsallenta, jin yana yunk’urin fitowa ya sanyata saurin barin d’akin cikeda jin dad’i...
Shiko Khalid yana fitowa ya hangi abu aje gefen bedside, ko bai tambaya ba yasan aikinta ne, yarinyar nan ta rainashi har d’akinsa take kawo mishi abinci yayi magana Ammi ta tasa shi gaba da fad’a, amma zai maganinta ta yanda ko hanyar d’akinsa aka kuma nuna mata bazatabi ba... Ya k’arashe yana mai yin k’wafa kafin ya d’auki plate d’in ya fice dashi bai dire ko ina ba sai kitchen a cikin sink, Kubura na lab’e tana ganinshi dad’i kaman ya kasheta....

***

A b’angaren Nabilah kuwa tinda tai wayan nan suka kula da canzawanta, gaba d’aya walwalarta ta d’auke k’arshema ce masu tai tafiya zatai..
Aunty B ta tab’e baki tace “K’ila dai sirkin namu ne ya tab’oki...,”
Nabilah ta kuma turo baki gaba tace “Sirki, Sirki fah kikace Aunty... Nidai bani kula kowa kuma banida lokacinsu...”
Aunty B tace “Aiko bazamu zuba miki idanu haka nan ba dole ki kawo mana Sirki...”
Nabilah ta mik’e ta rataya handbag d’inta tana masu sallama, Zulfah ta mik’e da niyyan yimata rakiya koda bakin gate ne don ta lura akwai abindake damun ‘yar uwar tata tana son tambayarta....

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_




*30*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Agogo Siyama ta kuma dubawa ya nuna k’arfe 10:00pm daidai, ba d’abi’arsa bace kaiwa irin wannan lokaci a waje, ko a baya idan yanada surgery da dare yakan sanar da ita ko ya sanar da sakatariyarsa ta kirata ta fad’a mata...
Ko a mafarkinta bata tab’a zaton akwai abinda zatai Sameer yayi irin wannan fushin ba, tinda take dashi duk sab’anin da zasu samu bai tab’a k’in d’aga wayarta ba amma sai gashi yau ta kirashi yafi sau abinda yafi bai d’agawa k’arshema kashe wayar yayi gaba d’aya...
Tana nan zaune wajen har gyangyad’i ya soma d’aukarta taji k’aran tab’a k’ofa...
Ta mik’e zunbur tana mitsike idanu....
Kallon kirki bata isheshi ba yasa kai ya nufi upstairs....
Siyama tabi bayanshi a guje kana tasha gabanshi sanda yake shirin shiga d’aki...
“Partner let’s talk please...” Tai maganar cikin raunanniyar murya...
Baice mata komai ba saima k’ura mata idanu da yayi...
Gaban Siyama ya fad’i sakamakon hango wani sabon tashin hankali da tai cikin k’wayan idnunsa, muryarsa ta jiyo yana fad’in “Ammi ta sanar dake wani abu gameda rayuwata ne...?”
Tambayar ta kuma haifar mata da fad’uwar gaba, kasa furta komai tai sabida tsananin tausayinsa da ya sauk’o mata, tabbas ta lura akwai abinda ake b’oye masa ba’aso ya sani...
“Tell me Siyama, Wannan shine dalilin..? Shine dalilin da yasa kika k’yamaci had’a zuri’a dani.... Was that the reason....?”
K’walla suka ciko idanun Siyama, cikin rawar murya take furta “Partner believe me wllhi bansan komai ba nima.... Ban sani ba...”
Jinjina kai yayi yana murmushi wacce tafi kuka ciwo kana yace “Don’t lie to me again, an jima ana min k’arya ana fooling d’ina... Amma ki sani wannan shine karon k’arshe, Sameer d’in da kike gani tsaye a gabanki ba d’aya yake da wancan Sameer d’in ba who fell in love with you and your lies.... No one, no one would ever fool me again... Sannan ko mai ake rufewa akaina I’d find out...” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige d’akinsa ya bar Siyama tsaye a wajen tana hawaye, ita kanta gaba d’aya ta rasa wasu irin abubuwa ne ke faruwa, duk abinda Sameer ya fad’i gaskiya ne akwai sirrin da ake b’oye masa amma ita kanta bata sani ba gashi yak’i bata chance ta masa bayanin cewa ita kanta batasan mai iyayensu ke rufewa ba....
Jiki a sanyaye ta shige nata d’akin tana tunanin kwana gida guda da Partner ba tareda tayi matashi da k’irjinshi ba....

***

Washe gari sassafe ya fice harta Siyama batasan lokacin da ya fice ba sai tashi tai taga babu motarsa, ta sauk’o k’asa ta hangi dining table d’insu babu komai bisa wanda da a baya ne da yanzu ta tadda breakfast maiji da lafiya, shiryawa tai ta nufi gida don ko office bazata iya zuwa ba...
Tana isa gidan ta tadda Kubura da Yesmin na fad’a don Yesmin taga cookies d’in dataiwa Khalid a hannun Kubura tanaci tana lumshe idanu sannan koda ta tambayeta sai cewa tayi Khalid ne ya bata musamman...
Ta yanda Yesmin ke shiga bata nan take fita ba Kubura ma tak’i yin shiru sai yafa mata maganganu take...
Siyama ta dafe kanta tana fad’in “Waiku dan Allah bazaku tab’a jituwa ba, baku da wani abinyi ne....?”
Yesmin tace “Cousin wllhi sai Ammi ta kori yarinyar nan I can’t stand her anymore...”
Kubura tai shewa kana tace “Wllhi nida Ammi mutu ka raba, haka kikazo kika taddani a gidan nan kuma haka zaki tafi ki barmu ehe...”
A kufule Yesmin tai kanta zata kai mata duka Siyama ta shiga tsakani daidai lokacin da Khalid d’in ya shigo cikin shiri wanda ko ba’ace maka ba fita zaiyi....
Gaba d’aya daga Yesmin d’in har Kuburan suka natsu, sai mugun kallo da suke aikawa junansu...
Ko wacce daga cikinsu hangen d’an paper bag d’in dake hannunsa suke...
Siyama ta dubesu duka biyu tai dariya kana ta maido da hankalinta ga Khalid dake tambayarta Ammi...
Murmusawa tai tana duban ‘yan matan nasa kana tace “Kaga nima zuwana gidan kenan, why not ka tambayi ‘yan gidan...?” Ta k’arashe tana nuna masa su Yesmin da Kubura wacce tuni ta shiga goge table tana satan kallon kyawawan yatsun k’afafunsa dake jere cikin takalmi...
Baice komai ba yasa kai ya nufi cikin parlorn Yesmin na gaisheshi kai a sanne...
Idan jakan hannunshi ya amsa shima zai amsa, batasan yazo wuya da ita ba, baison shishigi sam a rayuwarsa....
Kubura ta kauda kai gefe tana dariyar mugunta, yayinda Yesmin ta had’iyi bak’in cikinta...
Bai k’arasa staircase ba Ammi ta sauk’o tana fad’an tun daga bathroom take jiyo hayaniyan Yesmin da Kubura...
Turus tai ganin Khalid yasha ado jampa da hula wanda ba kasafai yake hakan ba...
Gaisar da ita yayi, ta amsa kana ta k’arada “Babana sai ina kuma...?”
“Kano, inada pending activities acan...” Ya fad’i yana zira wayarsa cikin aljihu...
Mamaki ya kama Ammi, wannan yawan zuwa Kano da Khalid keyi anya na lafiya...
Shiru ta d’anyi kana tace “Khalid ka fad’amin gaskiya mai kake zuwa yi Kano...?”
D’an dubanta yayi kana yace “Ammi yanzu da girmana za’amin wannan tambayar, Ammi aiki ke kaini...”
Siyama kuwa tunda taji yace Kano ta soma tunani koma dai Sameer ya koma ne, idan kuwa haka ne tabbas gwara tabi Khalid taje ta samu mijinta don bazata tab’a bari ko wane irin al’amari ne ya rusa masu rayuwar farin ciki da suka taso cikinta ba....
Jinjina kai Ammi tai kana tace “Toh shikenan Allah taimaka, da fatan dai kayi breakfast...?”
Yace “Nasha tea dai banson cin solid abu idan zan hau hanya...”
Nan ma jinjina kai tai had’ida masa Allah ya kiyaye ya tsare hanya.. Siyama tai saurin cewa zata bishi...
Daga Khalid d’in har Ammi kallon mamaki suka bita dashi...
Khalid yace “Lafiya dai ko...?”
Wani kallo ta aika mashi kana tace “Lafiyar kenan wajen mijina zanje ko laifi ne...”
Ammi ta bita da kallo ba tareda tace komai ba don tasan kwanan zancen...
Siyama taci gaba da fad’in “Kaga zamu tsaya gida na d’anyi parking...”
A d’an kaikaice ya dubeta kana yace “Zaki b’atamin lokaci dai, wllhi 5 minutes zan baki ki shirya duk abinda zaki shirya....”
Sosai take son tafiyar shiyasa bata tsaya tanka Khalid ba...
Yesmin kaw tanata jira taga ma waye Khalid zai mik’a jakar nan sai gani tai ya fice dashi a hannunsa take zuciyarta ta soma zargin Khalid ba aiki yake zuwa Kano ba tabbas watace ke neman k’wace mata shi a can, idan kuwa hakane wllhi bazata tab’a bari hakan ta kasance ba Khalid nata ne ita kad’ai....

***

Momy zaune saman darduma ta ida sallan walha kenan sai ganin Sameer tai tsaye kanta idanunsa sunyi jazir....
Gabanta ya yanke ya fad’i, aje cazbahan dake hannunta tai kana tace “Sameer lafia...?”
Baice komai ba sai dubanta da yake zuciyarsa naci gaba da mashi zafi.... A hankali yake furta “Momy can you please tell me the truth once and for all....”
Girgiza kai Momy tai tana dubansa kana tace “Sameer why are you doubting your own mother... Why Sameer...?”

Cikin zuban hawaye ya d’ago mata takardan dake hannunsa kana yace “I’ve a DNA result that clearly shows Daddy is not my biological father.....”

Wani irin bugu k’irjinta yayi bata tsammanin Sameer zai tsananta binkice irin haka ba, hawaye ne taji suna kwararo mata bata tab’a tsammanin zuwan irin wannan ranar ba ranar da za’ace Sameer d’inta zai fahimci ba ita ta haifeshi ba... Muryarsa ya kuma katseta cikin tsananin rawa sanda yaci gaba da fad’in “Momy why...? Why Momy... Why did you decide to keep it from me..”

Cikin kuka take furta “Because the truth will hurt you Son, Sameer bamu tab’a muzguna maka ba ko wani abu makamancin haka, a ko yaushe burinmu shine ka kasance cikin farin ciki, ka shigo rayuwarmu ka haskaka mana a lokacin da duniya ta mana k’unci....”

Cikin rawar murya ya furta “But don’t you think I deserve to know who my real parents are... Suna raye ko suna mace, idan suna raye ina suke... Idan sun mutu inaso nasan matsayinku a wajensu...?”

Momy ta share hawayen da suka kwararo mata jiki a snyaye ta k’arasa bakin gado ta zauna, tabbas batasan ta yanda zata soma ba, batasan ta yanda zata soma sanar da Sameer ga yanda akayi ya k’are a hannunsu ba, ta tabbata idan ta sanar dashi cewa suma basu san iyayenshi ba hakan sai yafi komai masa ciwo wanda k’uncinshi shine abinda batason gani a rayuwarta...
A hankali idanunta naga wani b’angaren ta furta “Sameer ka fita don Allah and kar ka sake zuwa min da zancen nan....”

Duban tsananin mamaki yake mata kana ya jinjina kai yace “Alright Momy, zan fita kaman yanda kika ce sabida har abada zaki tabbata uwa a gareni koda ace akwai sirrin da kike b’oyemin, but Momy zanci gaba da bincike har sai na gano su waye sukai sanadiyan zuwata wannan duniyar... I’m sorry idan kalamaina sun maki tsanani... I’m sorry Momy...” Daga haka sa kai yayi ya fice zuciyarsa na kuma raunana..
Gida ya koma kana ya soma shirin komawa Kano, abubuwa da dama su suka cunkushe a zuciyar Sameer, yana buk’atar a masa bayani a warware masa komai dalla dalla, da k’yar ya iya driving da taimakon Allah har ya isa garin Kano, daga Mama har Shamsu sam babu wanda ya gane kansa tinda ya dawo, k’arashe ma kulle kansa yayi a d’aki ya kwanta ko baccin dole wanda baiyiba tun daren shekaran jiya zai d’auke sa...

***

Ga tsananin mamakin Siyama suna shigowa garin Kano a toy store taga Khalid ya tsaya, ta juyo tana masa duban mai kuma zasuyi a nan....
Ko takanta baibi ba ya fice ya shiga store d’in, Jim kad’an ya fito da ‘yar jaka a hannunshi....
Back seat ya bud’e ya aje shopping bag d’in kana ya bud’e mazaunansa ya shige...
Ta dubesa a kufule tace “Khalid before ka shige sabganka take me to my husband first...”
“Kinga you can’t be giving me orders cos I’m not driver...”
Ta hararesa had’ida yin k’wafa kana ta juyar da fuskarta ga window dole ta shanye wulak’ancin Khalid tinda motarsa ce kuma shike driving, tasan dama kad’an yake jira akanta yayita rama duk abubuwan da take masa da kafin Daddy ya basa matsayi sosai a company....
Bata kuma tankashi ba duk hira da ya soma k’ok’arin janta dashi, idan ya kalli yanda ta had’e rai saidai ya kauda kai gefe yana murmushin mugunta....
Ganinsu a k’ofar gate d’in babbar jami’ar garin ya kuma sanyata dubansa shek’ek’e kana tace “Khalid wai yawon mai kakeyi dani ne, nace maka ka kaini wajen mijina kafin ka shiga sangan ka haba na gaji da zaman mota...”
Idan kujeran da yake bisa ya amsa shima zai amsa...
A hasale ta mik’a hannu ta danna horn tana fad’in “Khalid magana fah nake maka...”
Ya d’an dubeta a kaikaice yace “Idan kin matsu ki kira mijin naki yazo ya d’aukeki mana...”
Ta galla masa harara had’ida yin k’wafa...

Su Nabilah suna tafe zasu wuce class da wani lecturer ya masu fixing sai ganin kiranshi tai na shigo mata, fuzar da iska tai kana ta saka wayar a silent...
Wata kiran ta kuma shigowa, Yusrah da wata coursemate d’insu Faty da suke tace tare suka dubeta jin sai kiranta ake tak’i d’agawa..
Yusrah tace “Wai bazaki d’aga bane...?”
A d’an dak’ile ta dubeta kana tace “Toh kinsan wanene...?”
Yusrah ta murmusa tace”Khalid ne...”
Nabilah ta d’an rausayar da idanu tace “D’an rainin hankali zakice...”
Yusra da Faty suka dara kafin Faty ta tsaya business center karb’an handouts...

“Dan Allah ki d’aga...” Yusra ta fad’i tana dubanta...
“Na d’aga naji bak’a, kashe wayata ma zanyi...”
Murmushi Yusrah tayi kana tace “Kalan taku salon kenan, amma dai da kin d’aga bakisan mai zaice maki ba...”

Gajeren tsuka Nabilah tai kana tace “Banson nacinki na tsiya Yussy naji zan d’aga....”

A dak’ile ta d’aga wayar ba tareda tace komai ba...

Daga d’aya b’angaren yace “Bana kiran waya ya wuce d’aya ki kiyaye next time...”

Murmushin takaici tai kana tace “And who cares...”

Khalid ya shanye kana yace “Ki k’araso k’asan bishiyar dake gabanku kad’an...”

A hasale tace “And who are you to give me orders....?”

Murya a dake yace “Zan iya binki har cikin class d’in naku har gaban malamin naku ba wani abu ne idan hakan kika zab’a....” Bai jira cewarta ba ya katse kiran...

Sauk’e ajiyan zuciya tai tana duban Yusrah ba tareda tace komai ba, takai dubanta ga location d’in da ya sanar da ita, yana tsaye ya bada baya kansa na k’asa da alama wayarsa yake dannawa....
Huci kurum take tana dubansa ga wani irin yanayi data tsinta kanta ciki bayan hangosa tsaye da tayi...
Hannun Yusrah ta fincika suka nufi yanda yake...
Yusrah na tambayarta ko tsayuwa bata amsa bataiba taci gaba da fizgan hannunta....

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_




*31*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Yana nan tsaye yanda ta hangesa yana ci gaba da shafa wayarsa, sarai yaji k’arasowarsu amma yayi biris yaci gaba da abinda yake, tsaban haushi Nabila taji kaman ta kwab’e takalmin k’afarta ta jefi k’eyarsa dashi, ita kuwa Yusrah shan jinin jikinta tai had’ida matsawa gefe ta basu waje....
Bud’e bakinta kenan da niyyan magana ya juyo yana dubanta, idanunsu suka had’e waje guda, Nabilah ce ta soma kauda nata fuskar kafin Khalid yai murmushi da gefen bakinsa...
“Baki iya sallama bane..?”
Ya fad’i yana takowa kad’an zuwa kusanta...
A kaikaice ta watsa wani kallo da gefen idanu kana “Meyasa bazaka fice a rayuwata completely ba....?”
K’uri ya mata ganin yanzu ta daina masa magana da tsiwa ba kaman farkon had’uwarsu ba....
Gyara tsayuwarsa ya d’anyi gamida hard’e hannayensa ta baya waje guda kana yace “Is that really what you want... You want me out of your life... Kin tabbata daga zuciyarki kike fad’in haka...?”

Saurin d’agowa tai tana dubansa jin tambayoyin da ya jero mata lokaci guda.... Ta kasa furta komai saima k’irjinta dake ci gaba da lugude...
Khalid ya d’an murmusa ganin yanayinta yanda ya canza lokaci guda, gyaran murya ya d’anyi kana yace “Ina saurarenki....”

Murya a raunane tace “Yes abinda nake so kenan, just stay away from me na tsani ganinka....” Ta k’arashe muryarta na sark’ewa...
Khalid ya mata k’uri yana maimaita kalmar na tsani ganinka....
Lokaci guda ya jinjina kai kana yace “Alright, if that’s what you want...”
Shopping bag d’in dake gefe ya d’auko ya mik’a mata ba tareda yace komai ba...
Tabi jakan da kallo cikeda mamaki kana ta d’ago tana dubansa, wannan karon yanayin da bata tab’a ganin k’wayar idanunsa ciki ba ta gani... Jikinta yai wani irin mugun sanyi, a hankali ta shiga girgiza masa kai kana tace banaso bazan karb’a kayi hak’uri....”
“I insist please... be nice for once....” Ya k’arashe yanai mata wani irin duba mai cikeda ma’anoni wanda yasa ta kasa daina dubansa, ganin tunaninta na neman gushewa ya sanyata saurin saita kanta ta koma Nabilarta, cikin hayaniya tace dashi “Nace maka banaso ko ana dole ne....!”

Dariya ya kusa kufcewa Khalid mai hali da hali bazai canza ba Nabila kenan...

Ya d’an gimtse yace “I’m pretty sure zaki so kyautana sabida abinda mata sukafi so ne ciki... Just take it....” Ya k’arashe yana kuma mik’o mata...

Murmushi tai wanda za’a kirasa yak’e kai tsaye, kana ta kuma gimtse fuska tace “And who told you ni kuma inason duk abinda mata ke so.... Nace banaso bazan karb’a, if you may excuse me zan koma class...” Ta k’arashe tana d’aura hannu a kunkumi...

D’an d’aga gira sama yayi kana yace “Oh really.... I’m also surprised that you don’t wear makeup...” Yai maganar yana tab’e baki...

A hasale tace “Are you a fashion credit now....?!!”

Surrender yai da hannayensa kana yace “Easy... you don’t need to yell... Besides I’m not saying you’re ugly, all I’m saying is that ya kamata ki amshi kyutana....”

Banda mugun kallo bata aika masa komai, da fari ya soma acting kaman wani nice guy lokaci guda ya koma Khalid d’insa dama tasan bazai iya minti guda bai nuna halinsa ba....
A hasale tace dashi “You know, why not take that to your girlfriend... I don’t need it....”

Murmushi yai mai bayyan hak’wara for the first time kana yace “I don’t have one...”

Yanda yai maganar ya sanyata d’agowa tanai masa duban mamaki, lokaci guda Khalid yaci gaba da fad’in “Although a lot of girls are after me....”

Nan ma murmushin yak’e tai kana ta kuma gimtsewa tace “Why not go date one of them and leave me alone... Ka tak’ura ma rayuwata...”

“You not sure about that....?” Yayi maganar yana kashe mata idanu had’ida k’ura matasu wanda ya sanyata shiga wani yanayi... Su duka biyu sunyi nisa cikin duban juna dai dai lokacinda Yusra ta k’araso tana fad’iwa Nabilah malaminsu ya shiga aji tuntuni zai iya rufe k’ofa kuma don yanzu Safwan ya kirata...
Nabilah tai saurin saita kanta kana tace “Muje Yusrah...”

Yusrah dake k’ok’arin gaida Khalid Nabilah na janyeta Khalid ya mik’a mata bag d’in yace na Nabila ne....
Nabilah tai k’ok’arin wafcewa zata aje masa abinshi Yusrah tak’i sake mata, a daidai lokacin Siyama da ta gaji da jiranshi ta k’araso wajen tana mitan ta gaji da jiranshi, hango ‘yanmata guda biyu da tai ya sanyata sakin baki tana kallon ikon Allah, ashe kam ga abinda ke kawo Khalid Kano, ita bama wannan ba duk had’uwar Khalid daji da kansa bata zaci a irin wad’annan yaran zai tsaya ba, chabd’i lallai dole Ammi taji wannan batu, sauri ta k’ara don ta samu ta cimmasu saidai tun ‘yammatan sun wuce don da alama su basuma ganta ba, shiko Khalid baibar wajenba har saida yaga shigewarsu zauren karatu...
Siyama ta k’araso wajen da sauri tana raka bayansu da kallon k’ask’anci ta maido da dubanta ga Khalid tana masa duban mamaki kana tace “Wannan shine aikin....?”

Mugun kallo ya aika mata kana yace “So, meye naki a ciki...?”

Siyama ta murmusa kana tace “The whole Khalid Masanawa ashe a nan zai k’are.... Dama akan wannan ne kake wulak’anta Yesmin...?”

Ya kuma danna mata harara had’ida jan garejen tsaki kana ya nufi mota...

Siyama tabisa tanaci gaba da maganganu, saidai sam Khalid bai amsata ba saima bada himma am driving da yayi...
A haka suka iso unguwar da Sameer yake, ta d’ago tana duban Khalid d’in kaman zatai magana sai kuma ta fasa don tasan kad’an da aikinsa ne ya mata banza, Khalid yaja yai parking a k’ofar gate d’in had’ida yin relax cikin kujera alamun yana jira ta fita..
Ta d’ago da dubeshi a dak’ile kana tace “Miye haka, kaja kayi parking... What does this mean...?”

“It means kina iya fita, gidan dake gabanki shine gidan, and kiyi sauri ki fice zan k’arasa masauk’i na huta....”

Siyama tai k’wafa had’ida jinjina kai tace “Wllhi Daddy da Ammi sunji batun nan an gama kuma zigasu zanyi a saka bikinka cikin kwanaki....”
Ya watso mata mugun kallo a kaikaice kana yace “Kiyi fin haka, ni dan Allah ki fice min a mota...”

K’wafa ta kumayi tana watsa mashi mugun kallo kafin ta finciki marfin motar ta fice tana fad’in ya bud’e trunk ta d’auki kayanta.....

Mama na parlor tana kallon tashan Discovery family taji bak’uwar sallama daga bakin k’ofa, ta rage muryar tv d’in a hankali kana ta amsa sallamar had’ida bada izinin shigowa.....
Tabi matashiyar matar da kallo domin kaw bata shaidata ba, da fari’arta tai mata iso...
Siyama ta k’araso ciki murmushi kwance saman fuskarta....
Daga can bakin carpet tai yunk’urin zama Mama tai saurin cewa “A’a dan Allah tashi ki zauna sama, sannu da zuwa...”
Siyama tai godiya murmushi saman fuskarta kana ta zauna saman kujeran...
Gaisar da Mama tayi cikeda d’a’a, Mama ta amsa mata da sakin fuska ta k’arada “Saidai ban gane daga inane ba...”
Nanma murmushi Siyama tai had’ida gyara zaman mayafinta tace “Sunana Siyama, ni ce matar Sameer...”
Nan fara’an Mama ya k’aru aka shiga sabon gaisuwa, Mama ta shiga haba haba da ita, da kanta ta tashi ta shiga kawo mata abin tab’awa musamman da taji sauk’anta garin kenan....
Siyama sai jinjina karamcin matar take, Mama ta zauna daga can gefe suna ci gaba da fira yanda a firan ta fahimci Sameer d’in baisan da zuwar Siyamar ba, a nan ne Mama ta d’an sha jinin jikinta...
Siyama ta kuma tambayanta Sameer d’in...
Mama ta d’an muskuta tace “Eh toh gaskiya inaga tinda ya fita sallar la’asar bai dawo ba, amma bazai wuce yana masallacin ba, anjima kad’an zai dawo...”

Siyama ta d’an kauda kai gefe ta yatsina fuska kafin ta juyo tana sakin murmushi, Mama tai mata iso zuwa d’aki don ta huce gajjiya da kyau, itadai Siyama sai yatsine yatsine take tana duban gidan tana ayyanawa a ranta babu laifi dukda dai bai kai nasu kyau da had’uwa ba k’ila zata d’an iya jurewa ta zauna har ta samu ta shawo kan Partner su shirya....

***

A b’angaren su Nabilah kuwa tunda suka shiga aji Yusrah ta k’agu a bud’e jakan suga menene a ciki, Nabilah ta danna

Please Login or Register in order to submit comment