Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

balcony Raihanah ke lek’ensu gabanta na tsananta fad’uwa... Allah ya sani ko sunan Siyama taji sai gabanta ya fad’i balle ta ganta... Babu shiri ta juya ta koma d’aki a guje Ta fad’a kan gado tana maida numfashi... Take ta kuma d’aure hannu aka tana tino cewa d’azun fah da tai gyaran d’akin Ya Ma’aruf ta mance d’ankwalinta da zobenta a can... Ta rintse idanunta kurum tana karanto innalillahi..!

Bai zarce da Siyama ko ina ba sai d’akinsa... Ya isa ya d’auko first aid na gidan ya soma treating ciwonta fuskarsa a murtuk’e... Ita kaw sai b’alla masa harara take, cikin zuciyarta tana ayyana cewa yanzu haka ya gama cin amanarta da wannan kucakar yarinyar, ga d’akin tas tas yasha gyara na musamman dan shi kansa Sameer d’in saida ya fad’i haka cikin zuciyarsa sanda suka shigo....
Siyama bata ida tinanin ba ta hangi d’ankwali linke saman gadon da k’aramar zobe bisa... Kuka ne kurum taji yana zuwa bakinta.... Da gaske dai Sameer d’inta yanada wata bayan ita... She’s not ready to share him... K’uri tai masa yanda yasha mur sosai yana k’ok’arin rufe ciwon nata da bandage... Zuciyar Siyama taci gaba da tafarfasa... Lokaci guda take ci gaba da fad’in “So she was here... Maybe ma you two spent the night together.... Kai ko kunya bakaji ba Sameer... Just look at yourself...!”
Da tsananin fuci yake dubanta kana yace “I don’t have time for your stupid tantrums... And don’t think sabida naje na d’auki yana nufin mun dawo normal like before bane... Sabida mutum uku nai haka Mummy, Daddy and Raihana...!” Yai maganar yana mai jinjina kai alamun tabbatarwa kana taci gaba da fad’in “Yes Siyama ki gode masu, if you’re still my wife... It’s because of them... And one more thing Siyama... You’re not in any position to question my authority... Wannan ya zama gargad’inki na k’arshe....Treat your wounds yourself.. !!” Ya k’arashe yana mai jifa mata bandage d’in a fuskarta....

Siyama ta saki baki tana binsa da kallo, wane irin kuka na zuwa mata.... Jiki a sanyaye Ta kwanta bisa gadon tana cazgan kuka....

Juyin duniya Mummy tai Siyama ta fito taci abinci tak’i fitowa... K’arshe Raihanah ita ta d’auki abincin ta nufi d’akin Sameer dashi ba tareda Mummy Ta sani ba....
Raihanah tai knocking a k’ofa amma shiru ba’a kulata ba.... Ta sakeyi nan ma shiru.... Har kaman zata juya da abincin sai kuma taji an bata izinin shigowa....

A hankali ta tura k’ofan ta shigo sallama saman bakinta tikda lugude da k’irjinta keyi yawa zai tarwatse tsaban tsoro....

Kallo d’aya Raihanah taiwa Siyama taji gabanta ya wani irin tsinkewa... Siyama sanye take da d’aya daga cikin kayan mijinsu, Black long sleeve check da ya kuma fito da hasken fatarta, gashin kanta mai tsananin tsantsi da shek’i a jik’e yake dik ya kanarnard’e alamun yanzu Ta murjesa da towel, daidai da jeans d’in jikinta na Sameer ne dan jakan kayanta na cikin nata motar bata samu ta d’auko ba bayan accident d’in da ya auku...
Folding hannun rigar taci gaba da yi tana mai k’arewa Raihanah kallo daga sama har k’asa.... Babu Wai tasha jinin jikinta da ganin yanayin halittar yarinyar dan sam bata k’are mata kallo ba sai yanzu... Babu shakka Allah yai mata kyaun diri da Babu d’a namijin a bazaiso mallakar mace irinta ba...
Siyama taci gaba da watsa mata mugun kallo tana mai zagayeta, yayinda Raihanah ta kasa katab’us saima karkarwa da jikinta keyi tana tuhumar kanta anya batayi ganganci shigowa ba....
Wani tsawa Siyama ta darara mata wanda ya sanyata kusan kifa tray d’in dake hannunta....

Siyama taci gaba da fad’in “Munafuncin banza da wofi kin wani d’auko abinci nik’i nik’I kega mai hankali ko..? Idan kinaso Ki nuna min kin cika mai hankali sarkin kirki Toh Ki rabu da mijina shine zan tabbatarda generosity d’inki... D’ago ki kalleni....!”

Kasa d’agowa tai sabida hawaye dake ziraro mata... Siyama ta murmusa a hankali kana tace “Badon cushe ba babu abinda Sameer zai dake... You’re not even his type... Ke ki dubi kanki ki k’are ma kanki kallo Sameer ba daidai ke bane.... Kinga yanda nake sanye da kayansa toh haka muke nidashi Magnets...!” Ta k’arashe tana mai alama da hannayenta lokaci guda taci gaba da furta “Now get out... Wuce ki fita kafin na kwab’a miki abincin nan a fuskarki..!!”

Raihanah dake kuka sosai cikin sauri ta juyo ta fito daga d’akin d’aule da tray d’in... Saidai a daidai staircase Siyama ta kuma kiranta ta tsaida ita... Takowa yanda take Siyama tai. Kana tace “Wait... It was you... So kece kika d’auki wayarsa a asibiti kwanakin baya da na kirasa....?!” Ta kuma murmusawa kana tace “Wato kin jima kina bibiyan mijina har wajen aikinsa...”

Raihanah da hawaye ke gangaro mata girgiza kai tai kana tace cikin rawar murya “Ba bibiyarsa nake ba shine likitan da yai treating ciwona sanda na k’one... Ki yarda dani Aunty Siyama wllhi ba bibiyarsa nake ba....”

Siyama ta kuma murmusawa a hankali kana tace “So you’re even aware of my husband is a plastic surgeon... Barin dad’a k’onaki da abincin nan sai yai treating naki da kyau....!” Ta k’arashe tana mai fatali da tray d’in abincin dake hannun Raihanah... Allah ya rufa asiri abincin babu zafi... Hakan yai daidai da fitowar Mummy... Sosai taiwa Siyama fad’a hardai k’arshe fad’an ya juye ya koma nasiha mai ratsa zuciya....

Mummy taci gaba da fad’in “Siyama this is not you... This is not who you are.... Ina Siyamar da na sani mai taimakon marayu da mabuk’ata...? Don’t allow yourself to get carried away by your emotions... Raihanah batada laifin komai, hasalima k’ok’ari take taga ta kyautata miki... Siyama dik abinda kwanciyan hankali bai badashi ba toh ki sani tashin hankali bazai badashi ba...”

Siyama ta d’ago idanunta masu zuban hawaye kana tace “Mummy maiyasa Sameer zai kawo wata cikin rayuwarmu idan ba daina sona yai ba...” Ta k’arashe cikin rawar murya...

Kamo hannayenta Mummy ta kumayi kana tace “Sameer loves you Siyama... He never stopped loving you... He always does... Da ace bai sonki da bazaije ya d’auko ki ba.... So please kar Ki baiwa mak’iyanku dama su cimma burinsu na ganin sun rabaku kinji...!”

A hankali Siyama ke jinjina kai had’ida kwanciya cikin jikin Mummy hawaye na ziraro mata...
Tabbas idan tana k’aunar Sameer batada zab’in da ya wuce tai hak’uri Ta amshi k’addararta a yanda yazo mata dikda tasan hakan abune mai matuk’ar wahala....

***


KANO

Suna ida waya da inspector Bala wata wayar ta shigo masa... Da tsananin mamaki yake bin wayar da kallo ganin ba kowa bane yakeda wannan layi nasa na musamman.... Dikda bugu da k’irjinsa keyi hakan bai hanasa d’aga wayar ba... Tamkar wanda aka zabura ya kuma mik’ewa tsaye yana furta “Akram.... Akram is that really you....?! Akram tell me mai ya faru dakai....?!”

Da k’yar Akram dake tsananin haki yace “Sir abubuwa ne da dama.... They cannot be discussed over a phone call.... We need your help, I cannot go directly straight to the police... I need back up...!!”

Engr yace ”Where are you now...? Just text me your location....!”

Babu musu Akram yace “Alright Sir, right away...”

Jim kad’an sak’o ya shigo wayar Engr.... Bai nemi kowa ba sai Jalo da ya kira ya sanar dashi ya kira party chairman ya sanar dashi campaign d’in da zasu fita ayi rescheduling d’insa zuwa satin sama... Something urgent came up.... Hakan kaw akayi

Yayinda Bash da Muhibbah suke shirinsu na tarwatsa Engr Ma’aruf....
Sam basuda labarin wannan change of plans na Engr...
shirinsu shine a goben su b’ata masa suna a bainal jam’a su kuma tarwatsa masa rayuwa...

Tareda wasu Jam’ian tsaro guda biyu Engr suka riski Akram.... Ba tareda b’ata lokaci ba Engr ya kirawo family Dr d’insu ya duba Akram a safe house d’in da suka ajesa dan babu wanda yasan Akram d’in ya dawo kuma hakan ne zaisa su cimma burinsu cikin sauk’I wajen capko muggan ‘yan ta’addan nan Babba Duna da yaransa harmada Sawwama da Mahaifiyarta da babu wanda yasan sunada alak’a dasu Babba Duna bacin yanzu da Allah ya toni asirinsu...


Dr ya fito ya tadda Engr zaune a parlor shida jami’an tsaron da alama fitowarsa suke jira....

Engr ya mik’e yana fad’in “Dr how’s he...? Kana ganin jami’an tsaro zasu iya interrogating d’insa a halin yanzu...?”

Jinjina kai Dr yai kana yace “An gode Allah Babu wani deep wounds sosai, a hankali zai healing... He’s stable zai iya amsa dik wani tambayoyinsu Inaga a halin yanzu.....”

Engr ya jinjina kai had’ida mik’awa Dr hannu sukai masabaha kana yace “Na gode Dr... Let me walk you out...”

Dr ya jinjina kai yana mai furta “Aaa babu komai your excellency... Allah dai ya basa lafiya....”
Lokaci guda suka jera a tare suka fito tareda Engr yayinda polisawan suka shiga d’aukan bayanai daga wajen Akram.... Musamman da shike Babba Duna tsohon d’an ta’adda ne da ya jima yana ta’addanci a doron k’asa sama da shekaru masu yawa.....





SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_




*107*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Sanda Engr ya shigo d’akin Akram d’in ‘Yan sandan sun ida tattare duk wasu bayanai da zasu d’auka.... Inspector Bala ya dubi Engr kana yace “Your Excellency mun d’auki dik wasu bayanai da zamu d’auka kuma wannan yak’i ne Babba muke tunk’ara sabida shi wannan d’an ta’adda Duna yanda kasan hawainiya haka yake canza kala, shekara da shekaru wanted ake nemansa, ko wacce gobnati haka take zuwa ta tafi ta bar Duna, sannan babu kalan jami’an tsaro masu tunk’aho da uniform da basuyi azaman kame Duna ba amma Sun gaza, Sabida Duna d’an ta’adda ne mai had’arin gaske, amma yanzu in sha Allah komai yazo k’arshe zamu kamo Duna mu gurfanar dashi gaban Kuliya domin a yanke masa hukuncin duk wasu laifuka na ta’addanci da ya aikata..... A halin yanzu muna buk’atar had’in kanku musamman shi Akram d’in da aka ijesa hostage a wancan dajin.... Sannan rankashi dad’e daga baya nan da Akram yai mun fahimci cewa Hajiya Magajiya sirkar Hafiz kuma matar Baban shi Hafiz d’in sunada saka hannu ita da d’iyarta a wannan ta’addanci.... Zarginka ya tabbata your Excellency...”

Engr ya jinjina masa kai kana yace “Toh yanzu shi Hafiz yana can hannun Duna kenan...?”
Inspector ya jinjina kai kana yace “Kuma rayuwarsa tana cikin had’ari Babba according to Akram’s statement....”
Kakaitowa Engr yai yana duban Akram da hannunsa Ke d’aure cikin bandage, cikin sauri Akram ya sadda kansa k’asa sakamakon nauyin Uban gidan nasa da yake...

Duban Inspector Engr ya kumayi kana yace “Inspector, kenan hakan na nufin babu wani case akan Hafiz a halin yanzu...?”
Inspector ya girgiza kai alamun a’a kana yaci gaba da fad’in “Eh to bazance kai tsaye babu case akansa ba, abu ne da Alk’ali zai hukunci your Excellency... Amma case mafi girma dake kan Hafiz a halin yanzu shine case na kidnapping Akram... Idan Akram yayi filing case against him Toh fah dole ya gurfana gaban Alk’ali domin ya amsa laifinsa na garkuwa da Akram da yai....”

Akram ne ya katsesu da fad’in “Never... Bazan tab’a filing case against Hafiz ba, Hafiz mutumin kirkine da rud’ani na soyayya ya rufe masa idanu bai gane gaba bai gane baya, Hafiz mutumin kirki ne da ya zab’i ceton d’unbin Al’umma sama da rayuwarsa.... Hafiz ya samu chance d’in tserewa daga hannun Duna amma ya zab’i ceton nawa rayuwar data sauran Al’umma.... Hafiz is a total opposite of what you all think of him.... Deep inside his chest there’s heart that’s capable of loving.... He’s not a monster that we all thought he was....Kawai dai ya sami gurb’ataccen tinani ne daga iyayensa, wanda suka haddasa masa gaba tai tasiri cikin zuciyarsa....!”
Tinda Akram ya soma magana Engr Ke dubansa... Lokaci guda Akram d’in ya taso da k’yar sabida jikinsa dake tsananin masa ciwo, ya tako gaban Engr, kansa a k’asa yake furta “Sir, please we need to rescue Hafiz... We cannot allow Babba Duna to have him killed.... Babba Duna fasik’i ne wanda ya d’aura kwad’ayin fasik’ancinsa akan Hafiz, if we don’t act very fast and smart...I’m afraid everything might be possible....!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya....

Dafasa kad’an Engr yai kana yace “Akram I promise you... In sha Allah, zamu karb’o Hafiz daga hannun Babba Duna alive da yardar Allah... Babu abinda zai sami Hafiz da izinin Allah.... Mutumin da ya sadaukarda rayuwarsa ga d’unbin Al’umma Allah zai tsaresa da tsarewarsa... Ka kwantar da hankalinka kaji koh.... Hafiz zai kub’uta..!” Ya k’arashe yana mai dafa kafad’an Akram d’in....
Lokaci guda Akram Ke jinjina kai kana yace “Thank you....Your Excellency....!”

Jinjina masa kai Engr yai kana suka fice tareda Inspector suna kuka tattauna lamarin....

Tsaye Engr yai a waje bayan tafiyar su Inspector Bala yana tinanin rayuwa da abubuwan da suke kan faruwa.... Allah sarki ashe dik yanda suka d’auki Hafiz, mugun mutumi mai son zuciya ba haka bane... Ya zab’i shi ya bada nasa rayuwar dan a capke Babba Duna once and for all d’inbin Al’umma su tsira, tabbas idan har haka ne Hafiz ya cika jarumi wanda yai sadaukarwan da ba kowa zai iya irinta ba... Yana nan a tsaye wayar Detective Najib ya shigo masa... Detective Najib private investigator ne da Engr ya d’auka dan yai masa binciken shagunan ‘yankunnaye da sark’ar zinari na mata da matarsa Muhibbah ta mallaka wanda Engr d’in ke zargin ana tafiyar da hada hadan saida muggan miyagun k’wayoyi masu barazana ga rayuwar Al’umma musamman matasa wanda shan wad’annan miyagun k’wayoyi ya riga ya zama ruwan dare, babu mace babu namiji....
Tsaye yai yana nazari bayan sun ida waya da Detective Najib, the last abinda zaiso shine ace an kama matarsa uwar ‘ya’yansa da wannan mummunar laifi.... Detective Najib ya sanar dashi bai samu wani abu suspicious ba a halin yanzu hakan na nufin kai tsaye bai isa ya tunk’ari Muhibba ba, musamman yanzu da take tsananin fushi dashi, baiso abin yakai ga jami’an tsaro amma baida wani zab’i, muddin Muhibbah bata saduda ba toh fah baida wani zab’i da ya wuce ya sanar da jami’an tsaro dan tsaida wannan b’arna dake wanzuwa, bazaiso ace yau ga nashi d’iyoyin suna ta’ammudi da miyagun k’wayoyi ba, kuma idan har da gaske neman takaran kujerar Al’umma yake Toh ya kamata ya fara proving hakan ta hanyar mik’a natarsa ga hukuma domin a gurfanar da ita gaban Alk’ali ta amsa laifinta... Ya sani wannan abu ne mai matuk’ar wahala daka iya janyo cecekuce tsakanin Al’umma, sannan abu ne dake barazana ga kujerar da yake nema, even his reputation yana barazanar b’aci muddin akace yau an kama matarsa da wannan laifi....!
A hankali ya lumshe gajjiyayyun idanunsa ya kuma bud’esu.... Idan har da gaske yana son kawo canji a wata b’angare na k’asarsa Toh ya kamata yai proving, baida wani zab’i da ya shige ya mik’a Muhibbah da muk’arrabanta ga jami’an tsaro koda hakan na nufin downfall d’insa ne...
Da wannan tinani Engr ya komo ciki wajen Akram, yanda ya tadda Akram d’in kwance tamkar mai bacci idanunsa a lumshe... Daga gefensa Engr ya zauna had’ida masa k’uri kaman mai tinanin wani abin.... Shi kad’ai ya saki murmushi kana ya isa ya janyo bedcover ya rufawa Akram....
Ya jima yana zaune wajen kafin aka soma knocking.... Engr ya tashi ya nufi k’ofar... Umma ce mahaifiyar Akram.... Engr ya bata waje ta shigo tana hawaye, lokaci guda take tambayarsa Ina Akram d’inta.... Bai wata wata ba ya nuna mata d’akin da Akram d’in yake, nan da nan Umma ta fad’a kan d’anta tana kuka sosai tana tambayarsa mai sukai masa.... Akram ya rik’o hannayenta yana mai furta “Ummah na Ki kwantar da hankalinki gani nan gabanki I’m alive... Babu abinda ya sameni sai raunuka....!”
Lokaci guda Umma Ta kuma rungumarsa su duka biyu suna hawaye.... Cikeda tausayawa Engr Ke dubansu kana ya d’an sakala hannayensa cikin aljihun wandonsa, lokaci guda yai gyaran murya kad’an yana mai furta “Umma tinda kinzo Inaga zaifi kyau idan kika tsaya kika kula da Akram...”
Jinjina masa kai tai cikin sauri tana mai furta “Ubangiji dai ya biyaka da gidan Aljannah Gwabna... Yanda kake kula da Akram Allah ya shiga lamuranka kaima...”
D’an murmusawa kad’an Engr yai kana yace “Ummah Akram d’an uwana ne, Ko mai zanyi masa ma kaina nayi.... Sannan a cikin mu biyun shine zan gorzo kuma jarumi mai sadaukar da Farin cikinsa ga d’an uwansa... Mai kula da d’an uwansa ta hanyoyin da D’an uwan nasa bai zato ba balle tsammani....” Ya k’arashe idanunsa kan Akram, shima Akram d’in Engr yake duba kuma tsaf ya fahimci kalamansa, tabbas har cikin zuciyarsa yaji dad’i da Engr ya fahimci shi d’in ba munafukinsa bane.... Ya saki murmushi a hankali k’walla na k’ok’arin ciko idanunsa... Murmushin Engr ma ya sakar masa kana yace “Get some rest... Akwai jami’an DSS guda biyu da aka sanyasu su bibiye Magajiya da d’iyarta Sawwama dan Sune zasu kai Jami’an tsaro ga wannan hideout d’in na Duna da yaransa...”
Akram ya katsesa da fad’in “Sir, Hafiz na cikin had’ari mafi muni... Kuma na mishi alk’awarin zan koma gareshi... Pls ka k’yaleni na koma ma Hafiz....!”

D’an jim Engr yai kana ya d’ago yana duban Hafiz.... Lokaci guda yake furta “Akram, wannan ba aikinka bane, ka barshi wa jami’an tsaro... Probably yaran Duna suna nan suna nemanka, fitarka had’ari ne mai matuk’ar gaske... Kai hak’uri abi shawarin Hafiz, yanda yace Sawwama da Mahaifiyarta su zasu linking Jami’an tsaro dasu Babba Duna... Ni ba jami’in tsaro bane amma nai maka alk’awarin bazan huta ba har sai Hafiz ya kub’uta da izinin Allah...!”
A hankali Akram ya tako gaban Engr kana yace “I trust you... Sir,..”
Lokaci guda Engr ya jinjina kai yana maiyiwa Akram d’in da Ummansa sallama.... Har yakai k’ofa Akram ya kirawo sunansa....
Juyowa Engr yai yana dubansa.... Lokaci guda Akram ya tako gabansa... Murya can k’asa dan baiso mahaifiyarsa taji yake furta “Sir, I have something very important to tell you... It’s about your wife...”
Saurin d’agowa Engr yai yana dubansa, kana Akram ya sadda kansa k’asa a hankali... Matsowa kad’an ya kuma kana yaci gaba da fad’in “I’m sorry idan ban sanar dakai tinda wuri ba.... I don’t know how you’re going to take it Sir, but your wife... Is a drug dealer...!”

K’uri Engr yai masa, shi kansa Akram d’in yasha mamaki ganin baiji wani gizau ba... Saima kafesa da idanuwa da yai kana yace “Since when...? Tin yaushe kasan dika wad’annan...?”

Sadda kansa k’asa Akram ya kumayi kana yace “About 4 to 6 months ago... Sir kai hak’uri idan ban sanar dakai da wuri ba...!”
Girgiza kai Engr yai kana yace “Na fahimceka... Kar ka damu Akram, a halin yanzu ni kaina nasan wacece Muhibbah.... Na kuma san sana’ar da take a bayan fage.... Smuggling miyagun k’wayoyi....Amma in sha Allah bazan rufe idanuna daga ganin gaskiya na k’yale ba, koda ace Muhibbah ta kasance mahaifiya ga yarana... Idan zanyi rantsuwa cewa zan kare Al’ummar k’asata, lafiyar su, rayukarsu da kuma dukiyoyinsu toh ya kamata chanji ya fara daga kaina... I know it is not easy amma zan kwatanta da yardar Allah...!”

Murmushi Akram yai yana dubansa cikeda tausayawa kana yace “Sir, you deserve all the happiness in this world.... Ka cancanci Farin ciki... Kai d’in mutum ne wanda a kullum burinsa ya kyautata wa Al’ummansa, kai d’in mutum da a kullum kake fara kawo matsalolin Al’umma samada naka.... Allah Ubangiji ya yalwata rayuwarka da farin ciki....”

Ameen Engr ya amsa dashi yana mai duban Akram d’in.... Lokaci guda ya janyosa ya rungumesa... Umma dake lek’ensu Ta k’ofa hawaye suka gangaro mata... Tabbas basai kun had’a alak’a ta jini ku zama ‘yan uwan juna ba, haka Allah ke jefa soyayya tsakankanin mutane.... Fatanta Allah yasa wannan zumunci na Akram da Engr yakaisu har Aljannah...

***

A can daji wajensu Babba Duna kaw, wata jahilar mari ya kuma watsawa Hafiz wanda saida jini ya kece daga bakin Hafiz d’in da hancinsa.... Duna ya kuma kamo hab’ar Hafiz da iyaka k’arfinsa yana mai furta “Kai d’an iska... Kai har ka isa... Uban wa yace maka wani zai iya ganin k’arshen mulkin Duna....?!”

Hafiz da bakinsa bai mutu ba yana ci gaba da huci yake furta “Allah shi zai kawo k’arshenka... Kuma ka rubuta ka ajjiye ko yanzu ka kasheni ni ne nan na zama sanadiyar kama ka... Inaso wannan ya zauna cikin tarihin rayuwarka...!!!”
Duna ya kuma d’aukesa da mari kana yace da yaransa su bank’are masa Hafiz.....
Nan da nan yaran Duna sukai yanda ogansu yace.... Kallo Duna ya dinga binsa dashi kana yai wata murmushi yace “Ai kasheka ma a nan yana nufin Duna ya maka rahama kenan... Ai na kasheka gaban matarka daka yarda da ita bayan na gama amfani dakai shine zaifi komai maka ciwo... Wannan mutuwar sai tafi a azaba a gareka kana kallon fuskar mutanen da ka aminta dasu kuma babu abinda zasuyi domin su ceceka.... Ta yanda ko ban kasheka ba zuciyarka zata kumbura Ta fashe sabida bak’in ciki.....!!”
Ya dubi yaransa kana yace “Ku nad’o min shi, taredashi zamu shiga gari...!!”

Babu musu yaran suka kuma yin yanda Babba Duna yace... Hafiz bai daina b’alla masa harara da idanunsa da kaman sun juya ba sabida tsananin bugu da yasha hannun wad’an nan azzalumai... Ko d’aga k’afarsa bai iyawa saima janyota da yake...
D’aya daga cikin yaran Babba yace “Babba shi kuma wancan yaron da ya gudu fah.....?”

Babba yai wata shegiyar murmushi yana shafa tsakiyar malu d’insa da fatar har ta soma yamutsewa sabida tsufa da barbad’anci ga wata siririyar farar fenti a tsakiyar kan an zana doguwar layi da ita daga goshi har k’eya kana yace “Dik yanda ya shige idan cikin tandu ya shige sai mun bincikosa shima mun kashesa....!”
Yaron Babba ya jinjina kai kana yace “Baka saka abu gabanka Kaga kasawa....!”

Babba yai wata k’asaitacciyar murmushi kana yace su fidda da makamai su d’au hanya.....

***

A can gidan Baba Alhaji kaw Magajiya ta tasa shi gaba sun d’auki hanya, yana tambayarta Ina suka nufa ko zarafin amsa shi bata samu ba, Haule na zaune tsakar gida ta rapka uban tagumi suka fito suka shigeta.... Kallo kurum Haule Ta bisu dashi tana mai goge k’wallan da suka ciko idanunta, duniya kenan Wai yau ita Alhaji kema wannan d’anyen aiki... Lallai Ta yarda mulkin duniya mai k’arewa ne Allah shi kad’ai yakeda tabbatacciyar Mulki kuma Mafi adalaci.... Tabbas A DADE ANAYI SAI GASKIYA(Inji Biebee Isa) Itakam ta yarda da hakan dan taga ishara akan nata rayuwar... K’arya fure take bata ‘ya’ya....Ta kuma kamo Bakin zaninta ta goge hawayenta.... Ficewarsu da kad’an gungun ‘yan daudu suka shigo sai hayaniya da kacaniya suke daga mai barandami sai mai tab’arya sai mai adda da gatari, sunbi Sawwama a guje tasha da k’yar dan sin riga sunji sirrinsu Magajiya da Sawwama ashe dik ‘yandaudun da suke b’acewa a nemesu a rasa ashe saidasu ma ‘yan ta’adda suke ayi asiri da sassan jikinsu....

Haule ta mik’e a birkice tana tambayarsu lafiya....? Had’ida dafe k’irjinta...

D’ayan wanda yake rungume da gatari yace “Ina take... Ina shegiyar kishiyar taki take... Wllhi muma yai sai mun cire mata sassan jiki yanda take saida mu ana cire mana namu sassan jikin...!!!” Ya k’arashe yana kuma wasa gatarin a k’asa....
Sahariyya da Najah babu shiri suka fito suka rungume mahaifiyarsu ganin wannan kayan tashin hankali dake aukuwa gidansu....

Haule cikin rawar murya take fad’in “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kunaso ku cemin gasunk’umar’yar ta’adda nake zaune da ita cikin gidan nan... Na shiga uku ni Haule wllhi ko tsuntsu ban tab’a kashewa ba, iyakacin asiri na ban tab’a kashe rai ba... Ma’aruf kawai naso aikatawa hakan shima Allah bai nufa ba dan ya nuna min shikeda cikakken iko akan komai.... Yanzu kunaso kuce matar nan saida mutum take ai tsafi dashi....!!”

D’ayan yace “K’warai kuwa dan ta saida ‘yan uwanmu kuma munji daga bakin d’iyarta sirkarki sannan kema naki d’an abinda suke shirin aikatawa dashi kenan da kuma had’in bakin mijinki...!”

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!! Tashin hankali da ba’a saka masa rana... Take Haule ta soma gani bibbiyu duniyar na juya mata.... Bama tasan sanda ta cire d’ankwalin kanta tana furta “Hafiz...! Hafiz d’ina kuke nufi...?!! A’a badai Hafiz d’ina ba...!” Lokaci guda Haule ta shiga janyo Sahariyya da Najah da tuni sunyi mutuwar tsaye tana fad’in “Kunji koh... Yayanku... Zasu kashe Yayanku.... Na shiga uku ni Haulatu... Ya Allah ka kawo min d’auki ka kare min d’ah na ka tsare min shi.... Ya Allah yanda ka kare Ma’aruf daga sharrin da muka nufesa dashi a baya ya Allah ka kare min nawa d’an daga sharrin wad’annan bayi Naka.....

Please Login or Register in order to submit comment