Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Daddy akaina... Amma Ki k’yale Aunty Daula haka nan... Tanada zuciya mai kyau...”
“Kai dalla cen rufe min baki...! Sun baka a ruwa kasha... Toh kaima ka sani bawai na gama dakai bane da wannan kwashesshen auren naka... Jira nake shi wanda ya had’a wannan Auren shiriritar ya tashi ya kwanceta dan wllhi kaji nai maka rantsuwa ina numfashi baka isa kai zaman aure da yarinyar nan ba...!”
Aunty Hanne Ta k’arashe da fad’in “Yauwa fad’a masa dai yaji da kyau.. Matarsa guda d’aya ce nan gidan Duniyar k’anwarsa Yesmin...!”

Wani irin muguwar kallo Khalid ya watsa mata kana ya mik’e yana bug’e gwiwar wandon jeans d’insa yanda ya duk’a lokaci guda yake furta “Amma dai Aunty ya kamata a d’an ringa dubawa ana kama girma....”

Aunty Hanne ta shiga sallalami tana kame baki “Saifullahi ni kake maida ma martani... Eh lallai na yarda ba haka kawai suka Barka ba....!”

Ammi tai k’wafa kana tace “Nan gaba bama maida martani ba had’emu zai gaba d’aya yace zai zane sabida an tab’a danginsa na asali, matarsa da uwarta... Yayi Khalid... Ya maka kyau... Toh ka dakemu mana kawai sai nasan ka cika...!”
Shidai bai kuma tofawa ga tsananin zafi da k’irjinsa ke masa, tsakaniga Allah he’s tired of all this... Bai kuma cewa komai sai sa kai da yai ya fice gaba d’ai daga cikin asibitin dan hakan ne kawai yafi masa sauk’i a halin yanzu...


***

KANO


Tagumi Haule ta rapka tana duban ‘yandaudu dake baje tsakiyar gidan nasu suna buga lido da karta ga k’aurin hayak’i da ya kaure gidan gaba d’ai....
Dr Awwab ya ida duba jikin Sahariyya ya bata dik wasu magunguna da take buk’ata kana ya dubi Haule yace “Jikin nata da sauk’i sosai k’unan is not that deep so basai an kaita asibiti ba, with the help of these prescriptions zata sami sauk’i cikin yardar Allah....”

Haule ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Likita mun gode sosai...”
Awwab yace “Kuyi godiya ma Allah dan shi ya kiyaye sannan kuyi godiya ma Sameer dan shi ya turoni na dubata....” Yai maganar yana had’e kit d’insa...
Haule da Sahariyya suka dubi juna cikeda al’ajabi... Haule tace kana nufin kace Sameer d’in shine ya turoka ka duba Shariyyar...?”

Awwab ya jinjina kai kana yace “Eh Hajiya Dr Sameer shi ya turoni...”
Wasu sabbin hawaye suka ciko idanun Haule babu shiri....Tasa bakin zaninta tana gogewa.. Lokaci guda take ceda Awwab “Mun gode Ubangiji ya saka da alkhairi... Zamu nemi kud’in aikinka mu biyaka daga baya...!”
Awwab yace “Sameer ya wuce haka a wajena... Magunguna da treatment dik kyauta ne kuma in sha Allah zanke lek’owa ina duba yanayin jikin nata.. Allah shi k’ara afuwa....!” Ya k’arashe yana mai masu sallama kana yai ficewarsa ‘yandaudu na d’aga masa yatsa ko takansu baibi ba....

Sahariyya da Haule suka dubi juna suna mamakin ya akai Sameer ya sani har ya turo abokinsa duba Sahariyya... Najah da shigowarta kenan tace “Ni ce nan na kira Raiha na sanar da ita halinda Addah Sahariyya ke ciki gashi ko tasin kaita asibiti a duba lafiyarta babu ga Baba Alhaji dai yanzu bama gabansa dan ‘yandaudu ma sunfimu ‘yanci yanzu a gidan nan shisa na yanke shawarin sanar da Raiha ita kuma ta sanar da Ya Ma’aruf... Ku gode ma Raihana ku godema Ya Ma’aruf dan bayan dik tilin abubuwan da kukai masu sunada zuciya mai kyau zuciyar yafiya.... Basu k’ullaceku a zukatansu ba....”
Haule da jikinta ya kuma matuk’ar yin sanyi share hawayen idanunta ta kumayi kana tace “Hak’ik’a duniya makaranta ce... Mugunta hassada da k’iyayya ba komai zasu kaika ba sai tarin danasani da d’inbin madama.... Yau ga Ma’aruf yaron da naso salwantarwa tin yana k’arami ya taimaki d’iyata bai k’yaleta ta rub’e a kwance ba, bai k’yaleta ta salwanta kaman yanda naso salwantar dashi ba... Sannan Raihanah yarinyar da tin tasowarta batasan komai daga gareni ba face gallazawa da azabtarwa daga gareni da kuma ita kanta Sahariyya... Sahariyya ita ta k’ona Raihana ta kuma so sake k’onata a karo na biyu Allah ya maida mata mugun nufinta kanta... Gashi yau Raihana Ta taimaketa... Kaicon wannan rayuwa mai cikeda tarin danasani....!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka...

Sahariyya ma kuka take tana furta “Tabbas wannan hakki ne... Hakkin Kausar da kuma Raiha shine ya bini.... Inama Kausar tana raye na rok’eta gafara... Inama na kasance mutuniyar arziki... Kaicon wannan rayuwa...” Ta k’arashe tana kuka mai tsuma zuciya itama.... Naja’atu dake faman share nata k’wallan itama cikeda tausayin mahaifiyarta da ‘yar uwarta Ta shige tsakankaninsu ta had’esu ta rungume suna kuka mai tsuma zuciya...

A haka Lami ta shigo ta taddasu d’aukeda jakkan kayanta... Haule ta shiga goge hawayenta tana fad’in “Lami lafiya na ganki haka... Ina zaki da jakkan kaya...?”

Aunty Lami ta kuma goge ragowar hawayen idanunta dan itama daga gani taci kuka harta gode Allah... Maimakon ta baiwa Haule amsa sai cewa tai “Haule haka gidanki ya koma matattaran ashararru....? Haule haka rayuwa ta juya mana...?”
Haule ta kuma share hawayenta kana tace “Lami abinda muka shuka ne... Yau ga sakamako muna girba.... Ina zakije da kaya...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Lami ta kuma sab’a jaka kana tace “Zuwa nai na miki sallama zan koma can garin mahaifina, zaman garin nan ya gagareni Haule... Kunyar idanun Mariya da Alhaji Usman bazai barni naci gaba da zama k’ark’ashin alfarmarsu ba... Haule zan tafi can garin mahaifina na zauna a k’auyen tukuf dan ya fiyemin wala’alla na sami sauk’in azaban zogin da zuciyata kemin.... Ko jiya da naje gidan Kawu Liti a nan Unguwar rijiyar zaki Zo kiga yanda matarsa da yaransa sukai min cin kashi cewa bazasu amsheni gidansu ba dan labarin abinda mukai ya karad’e ko ina cikin gari... Koran k’are sukai min cewa na tattari makirci na na k’ara gaba ba a gidansu ba.. Kuma banga laifinsu ba Haule tabbas sunyi gaskiya...!”

Haule ta jinjina kai tana mai kuma matsan k’walla tace “Shikenan Lami Allah yaso saduwarmu... Ni kaina banida k’arfin halin fuskantar Mariya da mijinta....Dan bamu cancanci yafiya ba saidai rahamar Ubangiji....!” Lokaci guda suka rungume juna suna kukan nadama wanda basu tab’a irinsa ba...


****


KADUNA

Mamaki ya kuma cikasa, shida yazo shan cikin Sameer yaji ko yanda labarin accident d’in Daddyn Siyama sai ga wani babban surprise da ya tadda daga abokin nasa.... Lallai shi d’in mai sa’a ne... Yanzu kam ya gama samun makamin da zai datse auren Siyama da Sameer rabuwa ta har abada....

Sultan ya kuma gyara zama had’ida aje glass cup d’in dake hannunsa kana yace cikeda mamaki “A’a Wai Sameer haka abotan namu ya koma ne...? Yanzu da ace ban kiraka ba da bazan san Kana nan Kaduna ba kuma da bazan san Daddy ya dawo daga jinya ba, sannan ga babban abin mamaki Wai kaine da mata biyu Sameer... Come on Sameer mai zumunci ya zama ne dan Allah....?”

Sameer ya d’an murmusa kad’an yana mai aje cup d’in hannunsa saman center table shima kana yace “Sultan, everything happened so fast... Wllhi nima daka ganni ban zauna ba, kuma dan dai Mummy ta turo Raihanah ta kawo mana drinks ne.....”
“Da bazan san kayi aure ba ma...!” Sultan ya tari numfashin Sameer d’in da fad’in haka....

Sameer ya d’an murmusa kad’an kana yace “Abokina kenan... Dik yanda zan maka bayanin yanda abubuwa suka kasance bazaka fahimta ba... Amma tashi muje daga waje sai mu tattauna...!”

Sultan ya mik’e cikeda k’osawa yana fad’in “Then you make me understand... Dan ni gaba d’aya ka canza min Sameer, saikace ba abokina aminina da na sani ba... Koda shike kaje Kano kayi sabbin Family sabbin friends da kuma sabon wajen aiki dole ma ka mance ni...”

Gajeren murmushi Sameer ya kumayi, suna tafe yake ci gaba da fad’in “Kaima kasan ba haka bane Abokina... So stop being ridiculous...”
Sultan ya d’an murmusa had’ida sakale hannaye cikin aljihun wandonsa lokaci guda yake ci gaba da jefo tambayoyi na siyayasa ga abokin nasa wanda ya d’auki dukkan yardarsa ya basa... Cikin amsoshin Sameer d’in ya fahimci tabbas Siyama bata da wannan labari na k’arin auren Sameer, don koda yace masa Amarya ce tasa ya mance dashi sai ce masa yai batama tareba tukunna gaban Mummy take yanaso ya soma sanar da Siyama kafin su tare... Hakan yasa Sultan ayyanawa cewa Dama ta sameshi... Shi kad’ai sai sakin murmushin cin nasara yake...

***

Ita kaw Raihana gaba d’aya haka kurum taji ta tsani wannan abokin Ya Ma’aruf d’in dan taga sanda Mummy ya aikota kawo masu ruwa yanda ya kafeta da idanu, gaba d’aya sai taji ta tsanesa bai mata ba.... Suna kitchen ita da Mummy tana taya Mummy aikace aikace da shike Mummy dama chef ce mai zaman kanta dan a wajenta Sameer ya koyi mu’amala sosai da kitchen... Dan tinda suka taho Kaduna Mummy tai mata register a makarantar ta kama daga aikace aikacen kula da tsaftan gida da jiki gayu da girki dik Mummy koya matasu take tamkar wata d’iyarta gashi sosai Allah ya had’a jinin Raihanar da Mummy... Mummy ta k’udura a ranta cewa in sha Allahu sai ta gyarama Sameer d’inta matarsa tsaf ta yanda dik wasu abubuwa da ya rasa a aurensa na baya zai samesu yanzu... Hakan yasa taja Raihanar sosai jikinta dan ta sake da ita....

***


A can Abuja fah....?

Wani Sabon tashin hankali yanda Ammi ta dake ta rufe idanu saidai su tafi gidan Aunty Daula su zauna gaba d’aya, Aunty Hanne naci gaba da zigata cewa gwara suje can duk su tare waje d’aya ta gane ma idanunta yanda kud’ad’en mijinta Ke tafiya... Ammi kaw ta hau kan shawarin Aunty Hanne tace ata fau saidai su d’unguma gaba d’aya su tafi gidan Daula tinda mijinta dai shi ya sayi Gida dan haka babu Uban da ya isa ya hanata zama cikin gidan... Siyama tace tayi daidai hakan za’ai, Yesmin kaw ba k’aramin dad’i hakan yai mata ba dan ko babu komai Yesmin zata samu Ta saka idanu kan Nabilah da Khalid....



SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_



*102*






*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



NOT EDITED


Da tsananin mamaki Khalid Ke duban mahaifiyar tasa, da gaske take gidan Aunty Daula zata tafi... Shin wannan wane irin musiba ne da yak’i ci yak’i cinyewa... A hankali ya soma girgiza kai hannayesa dafe da kunkuminsa yake duban Ammi da Siyama yanda sukai masa k’ebebe aka.... Lokaci guda Khalid ke furta “No Ammi... I won’t allow you to go there, idan san zama cikin mutane kuke ga gidan Aunty Hanne why not bazakuje....” Katsa tai da fad’in “Naga gidan Hanne na zab’i gidan nawa mijin ai.... Kai Khalid bari kaji na fad’a maka... Idan mutuwa kake kana tashi baka isa ka hani zuwa wannan gidan ba... Siyama shige muje....!”
Saurin tare gabanta yai yana fad’in “Ammi please don’t do this... Na rok’i arzikinki kar kije Ki d’aga masu hankali... Idan kinaso ni zan biku dik yanda zakuje but please Ki k’yalesu haka nan....”
Siyama dake faman danna masa mugun kallo tace “Wai Khalid wa Ammi kake dika wad’annan abubuwan... I can’t believe you are doing this to your very own mother... Khalid Wai anya kanaso kai albarka kuwa....?”

Da tsananin mamaki yake kaikaitowa yana mai duban Siyama... Ya karkato sosai yana dubanta kana yace “Really Siyama... What do you even know about albarka... Tell me Siyama, kin baiwa aurenki daraja..? Kin baiwa mijinki daraja...? Kin baiwa mahaifinki dake kwance daraja by disrespecting his own wife... Siyama is that what you call albarka.... Answer me wannan shine neman albarka a wajenki..!!!” Ya k’arashe cikin tsananin b’acin rai jijiyoyinsa na mimmik’ewa....
A zuciye Ammi tace “Khaliiiddd!!!!”
Bai daina kallon Siyama ba yana mai ci gaba da huci yake furta “No Ammi Ki k’yaleni na fad’a mata gaskiya for once in her life idan har ta rasa mai fad’i mata gaskiya ne....!” Bai kai aya ba sai sauk’an mari yaji a k’uncinsa.... Ya d’ago dafe da k’uncinsa yana duban Ammi datai marin tana sakin huci... Lokaci guda taci gaba da furta “Bani address d’in gidan kafin nai maka abinda yafi mari....!”
Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyar tasa yanda tana ganin gaskiya tana rufe idanunta... Tsawa ta kuma daka masa “Zaka bani ko sai na maka baki kabi daji....!!!”

Jiki a mace ya zaro wayarsa cikin aljihu ya rubuta mata address d’in had’ida mik’a mata... Ammi tace da Siyama “Maza amsa ki gani...”
Siyama na watsa masa harara ta finciki wayar had’ida forwarding address d’in zuwa nata wayar.... Ko tsayawa basa wayar hannu da hannu batai ba saima danna masa da tai cikin aljihunsa tana mai aika masa muguwar kallo... Ammi ta buga tsaki kana taceda Siyama “Shige muje Hanne suna jiranmu....”
Babu musu Siyama tabi bayan mahaifiyarta tana mai watsawa d’anuwanta Khalid mugun kallo...

Haka yanaji yana gani har suka b’ace masa bai saki k’uncinsa yana mamakin hali irin na Ammi ba, gaskiya sai yanzu ya kuma tabbatar da k’ok’arin Daddy tsawon shekarun nan da yai da ita a matsayin matarsa... Cikin wane irin yanayi ya nufi Intensive care unit... Ya shiga d’akin da Daddy ke kwance... K’uri ya masa daga nesa yana hangosa idanunsa a lumshe.. A hankali ya isa jikin gadon kana ya kai hannunsa saman na Daddy ya dafa... Saida ya cire nose mask d’in dake mak’ale fuskarsa kana ya soma fad’in “Daddy I’m sorry... But I don’t know if I can take this anymore.... I thought I was strong enough to face all this...But then na fahimci bazan iya ba... You need to get better Daddy... You need to get out of this place please Daddy... I can’t.... I’m sorry...!” Ya k’arashe yana mai kifa kansa saman hannun Daddy guda hawaye suna bin k’uncinsa... Sosai Khalid yake kuka mai ban tausai, saida yai mai isarsa kafin ya kumayi ma mahaifin nasa addu’a ya fice...

****

A can gidan Aunty Daula kaw, kasancewar basu jima da dawowa Daga asibitin ba yasa dik suna parlor bama su haura sama ba tukuna.... Jin k’aran doorbell yasa Nabilah saurin mik’ewa tana fad’in “I’ll get that...!” Dik a zatonta Khalid ne ya dawo.... Da tsananin mamakinta tsaye ta gansu carko carko sai faman cika suke suna yatsina fuska...
Yesmin ta bud’e murya tace “A bamu hanya mu wuce, masu gida sun k’araso....!” Tai maganar tana mai bangaje Nabilah da har lokacin kallon mamaki take binsu dashi...
Suka kuwa kutsa kai suka shigo cikin gidan daidai sanda AuntyB taji shirun Nabilah yai yawa ta k’araso k’ofan itama... Da mamaki take dubansu...
Aunty Hanne tace “What..! Ko korarmu za’ai.....?”

Ga tsananin mamakinsu murmushi sukaga AuntyB ta sakar masu kana ta soma fad’in “Aa Haba dai, ai nan gidanku ne... Nan ya kamata ku sauk’a dama... Ku shigo, ku shigo bismillah....” Ta k’arashe tana kuma basu hanya....
Tuni Aunty Bara’atu ta umarci Karimatu mai aikin Aunty Daula ta taya Kubura haurawa da suitcases d’insu Upstairs... Nabilah ma dai bata kuma zaman parlorn ba ta haye parlorn sama abinta...

Aunty Daula kaw Allah kurum take ambato cikin zuciyarta, ba’a asibiti bane kawai k’addarar had’uwa dasu ya kamasu ashe har gida zasu biyosu... A hankali take furta “Ya Rabb! You know best why you put people through the things they go through.. Give me all the strength to win my battles and to overcome the challenges... Ya Allah..!”
Bud’e idanunda zatai ta sauk’esu kan Ammi dake tsaye gaban k’atoton family picture d’insu tana k’are ma hoton kallo... Ta kuma juyawa tana duban na Daddy da Aunty Daula wanda sukai su biyu.... Take Ammi taji wani irin kukan da babu shiri na kubce mata....
Siyama ta k’araso jiki a sanyaye da dafa mahaifiyar tata, cikin muryar kuka Ammi ta d’ago tana fad’in “Siyaam da gaske Daddynki aure yai ba tareda sanina ba... Siyaam mai nai masa da tsanani... What have I ever done to him to make him hates me like this....Mai nai masa da tsanani... Shin laifi ne dan ina k’aunarsa... Shin ta hakane zai saka min irin k’aunar da nake masa....?” Kuka yaci k’arfin Ammi..
Aunty Hanne Kaw sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Amma dai wllhi Farida mijinki anyi mai budurwar zuciya jibesa a hoton nan geme geme ko kunya Babu rungume da d’iyar cikinsa Wai matarsa....!” Ta k’arashe tana kuma tab’e baki...

Lokaci guda Ammi ta waigo tana dannama Aunty Daula dake tsaye kanta kife wanda ko ba’ace ba hawayene ke zubo mata... A fusace ta isa gabanta tana fad’in “Bakiyi kuka bama munafukar Allah... Ke ko kunya bakiji ba, ki dubi mutum tsofe tsofe Ki auresa, hankalinki kwance sabida tsaban san abin duniya da ya rufe miki idanu.... Ki d’ago kanki ki daina nok’e nok’e ki dubeni tinda har kin iya haifan yara tareda mijina....!”
Wannan karon Aunty Bara’atu ce ta matso ganin cin kashin tai yawa... Lokaci guda take duban Ammi kana tace “Baiwar Allah dik fah wannan bambami da kumfar baki da kike na gaba ya riga da yayi gaba... Mai aukuwa ya riga ya auku... Babu abinda zaki iya canzawa, kuma da ta kama ki amoda bak’in cikin abinda mijinki yai maki bama Daula zakiyi ba... Sai ki jira har randa mijinki ya farka sai ki tarbesa da rashin mutuncin naki dan shi yasan dalilin da yasa bai sanar dake ba... Kije ki binciki halinki da yanayin zamantakewarki da mijinki amma ko da wasa bazan zuba ido kici kashi akan ‘yaruwata ba....!”

Batakai aya ba Hanne ta katseta da fad’in “Ke kul ahir d’inki.... Kada ki kuskura dan da alama bakisan da su wa kike ba....!!”
Jin haka yasa Aunty Daula haurawa sama a guje tana kuka sosai...
AuntyB kaw watsa masu kallo sama da k’asa tai kana tace “A koma islamiya a koyi kishi mai class....!!!”
Haba nan fah Aunty Hanne taci gaba da hura hanci tana bambami... Ita kaw Ammi fincikar hotunan tai had’ida sauk’osu k’asa dan indai tana gidan ba’a isa lank’aya hotunan wad’annan maciya amanan ba...

***

Aunty B tana haurawa Ta tadda Daula zaune a d’aki ta had’e kanta da gwiwoyinta tana hawaye... Dafata tai kad’an saidai Kafin AuntyB takaiga cewa komai Daula ta d’ago cikin hawaye tana fad’in “Gaskiya take fad’i.. Maiyasa zan aure mata miji.... Dik abinda zasumin nayi deserving... She’s the real victim here...” Ta k’arashe tana mai kuma share hawayen idanunta...

Aunty B ta dafata kad’an kana tace “Fatima ko d’aya babu laifinki a nan, kuma Allah yasan dalilin da yasa ya barki ki fuskanci abokiyar zamanki ba tareda taimakon mijinki ba.. Daula ko wane aure na zuwa da obstacles d’insa... Babu ta yanda za’ace rayuwarki a gidan aurenki ya tafi smoothly ba tareda wani tangard’a ba... Kowa da kike gani in one way or the other yanada nasa problem d’in, yanada nasa battle d’in da yake fighting.... Rayuwa gaba d’ayanta jarabawace... Yanzu idan kikaji kalan jarabawar da wata ke fuskanta gidan aurenta sai Kinga naki tamkar a aljannah kike... So karma wannan abin ya dameki.... Mijinki na k’aunarki, sannan ga Khalid yaron kirki, you’re not alone... Dan hakan kici gaba da masa addu’a har Allah ya bashi lafiya kinji koh... This too shall pass...!”
A hankali Aunty Daula ta saki murmushi kana ta rungume Aunty B tana furta “Sai yanzu na kuma fahimtar kyawawan halayyarki da ya sayi zukatansu su Mamy suke matuk’ar k’aunarki.... Ke d’in ‘yaruwace da ko wace ‘yaruwa zatai mafarkin samun irinki... Thank you for being here....!”
Suka rungume juna AuntyB naci gaba da dannarta....

***

A can parlor kaw Aunty Hanne ce ta mik’e zata tafi bayan ta gama ziga Ammi, tace da Yesmin ko zasu tafi gida Yesmin tace wa ai tana nan sai taga abinda ya kwance wa buzu nad’i babu yanda zata... Aunty Hanne tai tafiyarta ta k’yale Yesmin nan gidan Aunty Daula...

Suna zazzaune parlor kowa da abinda yake sak’awa su Ijlaal suka turo k’ofa suka shigo driver ya d’aukosu daga islamiya.... Carko carko yaran suka tsaya suna ganin sabbin bak’in fuskoki a gidansu....

Idanun Ijlaal ya sauk’a kan Siyama da har lokacin bata daina kukan cin kashin da Daddynta yaima mahaifiyarta ba a cewarta, dan auren wannan yarinya da yayi tamkar tozarci ne a garesu....
Da gudu Ijlaal ta tafi ta rungume Siyama tana fad’in “You must be Aunty Siyama Our big sister....I’ve seen your photo before, Ya Khalid ya nuna mana....” D’agowa tai tana duban Siyama da sauran hawaye suka mak’ale idanunta, lokaci guda tace “Are you crying.... kema kina kuka sabida Daddy yana hospital... Ki daina kuka kinji, Malam yace a islamiya we should pray for him... Yace idan Daddy yaga muna kuka he won’t be happy... Daddy zai sami lafia kinji Big sis....!” Ta k’arashe tana mai gogewa Siyama hawayenta da hijab din islamiyarta... Lokaci guda ta kuma rungumar Siyamar ita a dole lallashin Siyama take... Dik yanda Siyama ke so ta janye yarinyar daga jikinta amma ta kasa.... Wane irin sanyi taji jikin nata yai mata lokaci guda.... Ita kaw Humaira dake tanada d’an wayo tsaye tai tana duban fuskokin Ammi da Yesmin da babu alamun annuri tattaredasu saima b’allawa Ijlaal dake rungume da Siyama muguwar kallo da suke, sannan ga hotunansu yasha k’asa gefen k’afafun Ammi, tuni yarinyar tasha jinin jikinta sosai.... Ta isa tana janyo hannun Ijlaal tana fad’i a hankali “That’s enough Ijlaal let’s go upstairs....!”

Da k’yar Ijlaal d’in ta saki Siyama tabi ‘yaruwarta Humaira... Siyama tabi yaran da kallo har suka b’ace ma ganinta... Ammi ce ta doka uban tsaki kana ta mik’e tana fad’in ita zata haura sama... Siyama ta d’an bud’e murya tace “Ammi wane d’akin zaki sauk’a...?”
Wani kallo Ammi ta watsa mata kana tace “Wani d’aki ko ya wuce na mijina.... Ai banida d’akin sauk’a a gidan nan sai nashi....!” Daga haka tasa kai tai hayewarta sama.... Siyama ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai sauk’e idanunta kan hoton dake yashe k’asa... Ijlaal ta k’ura ma idanu tamkar mai tinanin wani abu... Murmushin da batai zato ba balle tsammani taji ya kufce mata a hankali.... Yesmin kaw k’uri taima Siyama cikeda mamaki....

***

A can sama kaw su Ijlaal suna haurawa suka tadda Nabilah zaune tai k’urima window kaman mai jiran isowar wani... Suka isa da gudu sunai mata oyoyo... Nabilah ta rungumesu tana masu sannu da dawowa... Humaira ta dubeta kana tace “Aunty Beels who are those people downstairs...? They seemed scary, I don’t want them here....!” Ta k’arashe tana tura baki....
Karaf Ijlaal tace “No I want our big sis here.... We’re family, after all... Right Aunt Beels....?”

Jinjina mata kai Nabilah tai kana tace “Of course we’re family Princess... And family suppose to love each other... Always remember that kunji koh....” A hankali yaran suka jinjina mata kai.. Nabilah ta murmusa kana tace “That’s my girls... Oya get changed and wash your hands... I’ll serve us dinner here...”
Ijlaal ta katseta da fad’in “No I want to eat downstairs with Aunt Siyama....”
Gaban Nabilah ya yanke ya fad’i... K’ak’aro murmushi tai dan bataso yarinyar ta fahimci komai kana tace “Alright Princess.... We eat downstairs ok... Oya get changed and wash your hands sai muje koh...”
Yaran suka nufi closet sukai yanda tace.....

Suna tafe Nabilah na tsakiyarsu Humaira ke tambayarta “Aunt Beels ina Yaya... Why isn’t home yet....?”
Daidai sanda Yesmin ta k’ara so yanda suke tana jiran taji amsar Nabilah...
Nabilah ta Shafa kan Humaira kana tace “Zai dawo ne Princess... Muje koh....” Suka jinjina mata kai kana suka wuce tamkar babu Yesmin a wajen... Ta saki murmushi tana duban Nabilah kana tace a fili... “Mai waje ne yazo dan haka mai tabarma dole ya nad’e... Matar Khalid ta iso wacce akai fake aure da ita dole ta tattare ya nata ya nata tai gaba....!”
Ko tsayawa saurarenta Nabilah batai ba sabida yaran, dan haka ne ma ta janye hannayensu suka nufo k’asa....

Har lokacin Siyama na zaune parlorn tana shafa wayarta.... Ijlaal ta saki hannun Nabilah ta nufi Siyama a guje ta kuma d’alewa jikinta tana zuba mata surutu, labarin sch islamiya friends d’inta da sauransu... Dik k’in yara irin na Siyama saida ta tsinci kanta da sauraren shiriritar yarinyar nan....
Ita dai Nabilah sai satan kallonsu take daga dining area, tai serving Humy kana tai serving plate d’in Ijlaal ma tana kiranta tazo taci dinner....
Ijlaal kaw ta tafi ta d’auko plate d’in ta dawo parlor wajen Siyama harda d’aukowa Siyama spoon ta aje masu abincin Wai saidai suci tare... Tin Siyama batason amsa yarinyar har dai ta soma amsata da k’yar...
Gyara mata plate d’in tai gabanta kana tace “Oya go ahead and eat.... I had dinner already...!”
Ijlaal ta d’an jinjina kai tace “Is that so... Why didn’t you wait for me...? Toh ki bani a baki..’Please please please!!”

Yarinyar ta soma isan Siyama... Kasa korinta tai sai amsar spoon d’in da tai ta soma bata a

Please Login or Register in order to submit comment