Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba don ita dik tinaninta hakan na cikin shirin Daddy ne na aurawa Khalid Yesmin...

***

A yayinda biki ya rage saura sati guda Sawwama da Hafiz suka isa territory d’in gungun ‘yan iskan...Tafiyar kusan awanni uku ya kwashe su daga gari zuwa cikin dajin ...
Sawwama ta juyo ta dubesa kana tace “Ka tabbatar da abinda kake shirin yi...? Ka shirya mu shiga...?”
Jinjina mata kai yai “I was born ready...”
Sawwama ta murmusa kana tace “Wannan itace Fadar Babba Duna... Shugaban duk wani wanda yai k’auri a fannin garkuwa da Bil’adama a k’asar nan, rashin imanin Babbba Duna ya wuce dik yanda kake tunani, cire kan d’an adam a wajensa ba komai bane... Biyoni muje....”
Hafiz dai sai waige waige yake yana duban k’ungurumin dajin da suka shigo had’ida mamakin ina Sawwama tasan irin wad’annan mutane...




SameenaAleeyou📚





*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*85*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





Wane irin sunk’urumin daji ne da baka jin sautin komai sai kukan tsintsaye, kallo guda zakaiwa Hafiz ka fahimci tsananin tsoro dake tattareda shi, dole ne yai hakan bashida wani zab’i muddin yin hakan zaisa matarsa Zulfa’u ta dawo garesa... Ganin dai bazasu daina kutsa cikin dajin nan ba ya sanyashi janyo hannun Sawwama dake gaba dashi da saurin gaske, cikin k’asa k’asa da murya tamkar mai tsoron kada wani yaji abinda zai fad’i yace “Ke dakata... Wai har yanzu nufinki bamu iso wajen Babba Duna ba, ko kina nufin kice sai munga k’arshen dajin nan ne....? I thought you said mun iso fadarsa... Toh ina Fadar take...”
Murmusawa tai da gefen baki kana tace “Dad’ina dakai saurin karaya saikace ba namiji ba.... Toh banda abinka da nace maka mun iso Fadar Babba Duna ai gabaki d’aya katafarin Dajin nan shi yake mulka... Wai tsaya ka canza zuciyarka ne...? Idan ka canza zuciyarka ne shikenan sai Mu koma....”

Numfasawa Hafiz yai yana mai kame kunkuminsa, shayeda tsananin mamaki yake dubanta “Mamaki nake ina kika san irin wad’annan gaggan ‘yantaddan...?”

K’asaitaccen murmushi Sawwama tai tana mai aika masa duban kama rainani kana tace “Wai da da nace maka inada makullin cin nasararka a hannuna ka zaci wasa nake...?”
Girgiza kai Hafiz yai kaman d’alibi gaban malaminsa kana yace “Ni duk a tunanina ‘Yaniskan cikin gari kike magana ba manyan ‘yan fashi da makami ba....”
Ta kuma murmusawa had’ida gyara tsayuwarta “Bana huld’a da k’anan ‘yan iska.... Biyoni muje...”
Fuzar da iska yai yana mai kuma bin dajin da kallo lokaci guda yake biyeda ita, wasu mutane guda biyu suka soma hangowa jikin wata bishiyar gamji mai tsananin duhuwa ko wannen su rungume da manya manyan bindigogi, murtuk’a murtuk’an mutane bak’ak’e k’irin dasu, haka nan k’wayan idanunsu jajazir babu alamun annuri ko rahama a tattaredasu....
Daga can gefe gefe tsinta tsinta suna hango mutane jifa jifa suma duka rik’e suke da makaman yak’i... Hafiz ya had’iyi miyau da k’yar dan shi zai iya rantsuwa bai tab’a ganin bindiga ido da ido tsirarta ba sai yau da Sawwama ta kawosa wannan waje.... Abinda yake gani a finafinai gashi na faruwa a karan kansa...
Koda suka iso saida mutum guda ya cajesu tsaf kafin ya nuna masu saman wata Dutse yace su jira acan... Babu musu suka k’arasa suka zauna, hankalin Hafiz dai dik ba’a kwance ba yayinda Sawwama ko ajikinta saima taunar chewing gum d’inta take...
Hafiz banda Uwar harara bai aika mata komai, yana ayyanawa cikin zuciyarsa lallai babban kilaki ya aura a matsayin mata... D’an dubansa tai taga yana faman watsa mata muguwar kallo....
Tab’e baki tai kad’an kana tace “Ya dai lafiya ko wani abin ka gani...?”
Girgiza kai Hafiz yai yana mai kuma dubanta kana yace “Ke yanzu tashancin naki bai tsaya a Alhazan gari ba harda ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane kike bi... Tell me Sawwama maza nawa kikai huld’a dasu kafin ni..!!!” Yai maganar yana faman bubbud’e k’irji da hanci saikace bashine ya gama rakub’e rakub’e ba....
Tintsirewa da Dariya Sawwama tai tana dubansa...
Ya kuma harzuk’a “Au dariya ma na baki... Ke ko kunya bakiji ba...”
Dakatar dashi tai da fad’in “A’a Kaga Malam daina min ihu aka, ni nan taimaka maka nake ka samu ka kuma mallakar Matarka Zulfa’u a karo na biyu... Idan kuma kace zaka kawo min rainin hankali wllhi kaji na rantse saidai a maidama Hajiya k’ok’on Kan d’anta dan idan naso sai ai gunduwa gunduwa dakai yanzu a wajen nan...!!” Cikin karaji tai maganar tana kallon yanda alamun tsoro da tashin hankali suka kasa b’oye kansu a fuskar Hafiz dikda k’ok’arin b’oyesu da yake...
Lokaci guda ya kuma tintsirewa da dariya ta shiga shafa fuskarsa tana fad’in “Relax mijina... Karka damu ni d’in har yanzu mai k’aunarka ce so ka kwantar da hankalinka... Kuma da kake cewa har mazan daji Ina bi toh kai kuskure domin kaw babu mata a tsarin Babba Duna... Dama idan kace akasin mata Wato Ina nufin maza...” Tana maganar tana yawo da ‘yar yatsarta a sassan jikin Hafiz had’ida kashe murya irinta gogaggun kilaki....
A firgice Hafiz yajada baya yana mai girgiza kai had’ida duban Sawwama da tsananin mamaki wanda bai tab’a irinta ba....
“Sawwama so kike kice abinda kika kawo ni ayi dani kenan... Sawwama wata irin biladama ce ke.... Ki d’auko mijinki na sunnah ki damk’asa ma ‘yanluwad’i....!”
Bai kai aya ba ta katsesa da fad’in “Kaga Hafiz nifa ka isheni... Idan bakaso burinka ya cika ka dawo da Zulfa’u sai ka tashi ka tafi is not a big deal...”
A zuciye ya mik’e yana aika mata muguwar kallo yake fad’in “I was so stupid da na yarda dake... Na yarda notin kaina sun kwance da har na yarda Ke d’in zaki taimaka min na dawo da matata.... Kafurci na baikai nan ba, bazan aikata wannan laifin ba Sawwama kinga tafiyata....”
Juyawan da zaiyi sai cin karo da bakin bindiga yai an saita k’irjinsa...
K’iris ya rage Hafiz bai saki fitsari ba sabida tsananin firgita, abinda yake gani a fina finai na neman aukuwa dashi....
Mik’ewa Sawwama tai tana mai murmusawa kana tace “Hafizi na kenan... Hafizi na Sawamma haka kuma angon Zulfa’u... Ka kwantar da hankalinka Ina mai tabbatar maka babu abinda zai faru dakai.... Ai ni na maka alk’awari kuma ya zama dole na cika maka.... Babba Duna owes me big time, akwai bashina akansa sabida haka aikin da zai mana baida buk’atan biyan reward ka fahimta....” Ta k’arashe tana sakin murmushi, lokaci guda tai alama ma d’aya daga cikin yaran Babba Duna da yai pointing bindiga a k’irjin Hafiz da ya janye bindigar....
Basu jima ba wasu k’artai biyu da wani d’an tsakurkurin mutumi tsakiyarsu suka nufo yanda suke daga can k’asa da wajensa suke....
Sawwama ta mik’e tana sakarma d’an tsakurkurin mutumin da murtuk’a murtuk’an mutanen nan Ke tsaronsa murmushi....
Daga can tsakurkurin mutumin nan da bai wuce a hure ba ya shiga maida mata maetanin murmushinta yana bud’e hannaye alamun sannu da zuwa yake furta “Barkada zuwa Fadan Babba Duniya... Kyakkyawa mai kyawawan ‘yandaudu..... Fad’i dik abinda kike babu b’ata lokaci za’ai miki... Ki fad’i duk Uban da kikeso a saco miki shi a fad’in k’asar nan.... Idan barikin Soji ne yake yawo dashi matsayin masu tsaronsa Ina mai tabbatar miki sai mun sace miki shi.... Babba Duna bai tab’a saka abu a gabanshi yaga gazawa ba....” Ya k’arashe yana k’ek’yata dariya....

Hafiz da tinda wannan tsakurkuri mai wani irin siffa kaman ba d’an adam ba ya soma magana ya b’oye Bayan Sawwama sai rarraba idanu yake, shi dik a zatonsa zaiga Babba Duna murjeje ne sai yaga wannan k’aramin alhakin.... Amma yayi kama da tsagerun shed’nu matuk’a sannan kallo guda zaka masa ka fahimci shekaru sun fara kamashi ma’ana tsufa ya sauk’o masa, da gani kasan wannan ya jima yana kafurci a duniya....

“Na gode Babba da wannan karramawa taka gareni.... Mijina na kawo, ai masa aiki....” Ta k’arashe tana janyo Hafiz daketa k’ok’arin b’oyewa bayanta...
Babba ya kafe Hafiz da idanu kana yace “Mai ake so ai maka Pretty boy....?”
Hafiz ya kuma hard’e rai jin Babba yana admiring d’insa....
Sawwama ta d’an mintsileshi alamun yai magana...
Babba ya bud’e murya yace “Kar ka damu pretty boy ka fad’i duk abinda za’a maka idan dai a k’ark’ashin alfarman Sawwama ne, bakada matsala... Fad’i ko mai kake so...”
Hafiz ya gyara tsayuwarsa yana hango tsakiyar kan Babba kana ya zaro wayarsa a aljihu ya shafa... Lokaci guda yai taku kad’an zuwa gaban Babba ya nuna masa hoton dake bisa screen d’in....
Babba ya amshi wayar ya k’urama hoton idanu kana wayar ta shiga zaga hannun yaransa, wannan ya kalla ya mik’ama wannan har ta dawo hannun Babba....
“Mai kake so ai masa... Wasu sassa na jikinsa akeso a ciro maka...?”
Saurin girgiza kai Hafiz yai kana yace “Ajiyanshi kawai nakeso na baku na wani d’an lokaci...”
Babba ya murmusa irinta basawa kana yace “Na maka alk’awarin ko tandu nan ya barni wajen iya ajiya.... Amma ina mai tabbatar maka idan ajiyan ya kuskuri kufcewa komai ka iya faruwa....”
Hafiz ya dubi Sawwama, itama d’in shi ta duba kana ta murmusa tace “Wuk’a da nama na hannunka Babba....”
Babba Duna ya jinjina kai kana yace “Yaushe ajiyar taku zata soma aiki...?”
Hafiz yai karaf yace “Nan da kwanaki biyar....”
Babba Duna ya d’aga ‘yan yatsun hannunsa tamkar mai lissafi kana yace “An gama pretty boy angon mai ‘yandaudu....”
Hafiz ya kuma dubansa kana yace “Banaso ya escape...Bana so kuma a samu failure...”

Babba Duna ya tako gabansa kad’an yana mai k’arewa Hafiz duba lokaci guda yake furta “A wannan daji babu wanda ya isa ya fice bada izinin Babba Duna ba muddin ya riga ya shigo fadar Babba toh fah saida amincewarsa ya fice, zaman daji saida shiri pretty boy...”
Tin bayan shigowarsu dajin sai sannan Hafiz ya saki murmushi, tabbas yanaji har cikin ransa Zulfah ta dawo gareshi an gama babu wanda zai kuma shan gabansa....
Koda sukazo ficewa rasa hanya sukai kaman yanda Babba Duna yace, har saida akai masu jagora suka sami hanya,... Wannan dalili yasa suke lak’abi wa Dajin da Fadar Babba Duna,domin kaw dajin kewaye take da shirinsa, hakan yasa ba’a iya kamashi tsawon shekarun da yai yana ta’addanci... Sannan hakan yasa yai k’aurin suna ya shahara a fannin garkuwa da d’anadam....
(Ya Allah ka kawo mana k’arshen wannan ta’addanci ya addabi k’asarmu ya zamto ruwan dare, Allah karka barmu da wayonmu Allah ka kawo mana d’auki Albarkan Annabi d’an gatanka ya Allah) Ameen thumma Ameen..!
***

Muhibbah dake zaune tsakiyar parlor sai faman murmushi take tana ayyanawa cikin zuciyarta yanda Engr zaiji idan yaji labarin auren masoyiyarsa da Babban yaronsa Akram.... Dole ma itace zatai masa breaking wannan news d’in taga kalan reaction d’insa... Babu boka babu Malam babu tashin hankali auren mijinta bazai yuwu ba... Ta kuma murmusawa tana juya glass cup d’in dake hannunta wanda a ido juice ne amma a zahirin gaskiya k’wayoyin maye ne a ciki....
Lokaci guda ya mik’e tana jin kanta a sararin samaniya duniyar na mata dad’i... Takawa ta dingayi har ta isa jikin tapkeken hoton Engr, a hankali ta shiga shafwa tana mai murmusawa “I can’t wait to see your face idan labarin cin amanarda amintaccenka yai maka ya riskeka..... Wannan kyakkyawan murmushi dake bisa fuskarka nasan zai gushe... Sannan babu mai kuma dawo maka da wannan murmushi sai ni Muhibbah... Your one and only wife... You must accept the fact that your home is right here with me...!!!” Ta k’arashe tana mai kuma tintsirewa da dariya tamkar mai tab’in hankali... Cikin tafiya datafi kama da tangad’i take takowa har ta zube saman kujera.. Nan bacci yai gaba da ita... A haka yaran nata suka shigo dawowarsu kenan daga islamiyya suka tadda Mahaifiyarsu nan kwance, idan da sabo hakan yabi jikinsu kasancewar dama tin can basa samun kulawa daga wajenta sunma fi sabo da Murja wacce duk wani d’awainiya da mahaifiya kema d’anta ita take masu...
Murja ta k’urama yaran idanu cikeda tausayawa yanda sukai tsaye suna duban mahaifiyarsu, waima gwamma yanzu suna iya ganin nata, a baya sai su shafe kwanaki basu sakata idanunsu ba, Murja ta k’arasa ta rik’o yaran tana mai saka murmushi saman fuskarta take fad’in “Muje ku canza kayan makaranta kunga Mummy na bacci...” Yaran basu ce komai ba Irfaan ya soma shigewa yayinda Samha ta take masa baya, tabbas murja k’ok’arinta kawai take amma ta sani izuwa wannan lokaci yaran sun soma gane abu tinda sun soma girma... Haka sanda sukaje Abuja gidan Aunty Daula kwanakin baya kaman kar su dawo yanda Aunty Daula Ke nuna masu zallan k’auna irin wanda basu samu daga mahaifiyarsu ba, dan ma Allah yasa mahaifinsu na matuk’ar nuna masu k’auna da kulawa...

***

A can gidan Aunty Bara’atu ake gyaran amaren, sanda Bikin ya rage saura sati biyu dama ta tafi dasu can gidan nata, tuni Zulfa’u ta d’auki hutun wajen aiki yayinda Nabila ce kawai ke ficewa makaranta itama sabida exam ne da suke rubutawa wanda daga shi sai tafiya Industrial training da muke saka ran zatai a garin mijinta da yardar Allah... Sam Aunty Bara’atu bata barinta ta fice ba tareda makarin rufe fuska ba nik’ab, idan Kaga amaren dole Kaso sake kallonsu yanda sukai kyau fatarsu ta kuma murjewa tai santsi alamun suna samun gyara da kulawa na musamman, yaran Aunty Bara’atu kenan, aima dole susha gyara ciki da waje, gyara mai tsafta da babu cutarwa cikinta babu kuma algus...
Yauma dai wani dahuwar kazar Aunty Bara’atu ta shigowa Zulfa’u dashi sanda aka ida mata halawa, sai faman ture turen baki take tana fad’in ita ta gaji da wannan tsirface tsirfacen abubuwan da ko a auren fari ba’ai mata su ba....
Aunty dai jinjina kai tai tace “Na dai ji amma sai kin cinye tas kin shanye roman nan, kinsan ance idan kanada kyau k’ara da wanka...”
Atika na gefe sai k’ek’yata dariyarsu take tana fad’in “Allah dai ya bar mana ke Auntynmu....”
Zulfah kaw saidai ta gallawa Atika harara dan ita ke ziga Aunty Bara’atu a cewarta....
Aunty ta dubi Atika dake gefe tana darawa kana tace “Ki tabbata ta cinye bara naje Ina zuwa...”
Batakai aya ba Atika ta bata amsada “An gama Auntynmu...”
Zulfah ta galla mata harara had’ida yin k’wafa...
Matsowa kusanta Atika tai tana kuma k’ek’yata dariya take fad’in “Aaa gaskiya dole Yaya na Akram ya k’aro sadaki Anty ta gama masa komai....”
Duka Zulfah ta d’aka mata a cinya tana fad’in “Kedai Allah ya shiryaki... Mutum abinda ya iya kenan jin baki...”
Atika ta kuma darawa tace “Allah huci ran amaryar yayana Akrami....” Murmusawa kurum Zulfah tai amma ita kanta batasan meke damunta ba dan gaba d’aya ji take maraban auren da aurenta na fari k’alilan ne, dan idan tace tana k’aunar Akram tayi k’arya, tsakani da Allah bata tab’a jin sonsa a ranta ba saidai batasan dalilin da yasa ta amsa ma auren nasa ba, k’ila sabida azalzalawa da Baba Alhaji da d’ansa Hafiz sukai mata ne... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai tana bin sangalalin k’afafunta da kallo yanda suketa faman shek’i da d’aukan idanu alamun sunsha dilka da halawa... A hanakli ta furta “Allah kaine masanin maiyasa abubuwa suke faruwa yanda suke faruwa, Ya Allah lamurana suna hannunka... Ya ka zamto majib’incinsu...” lokaci guda taji ta samu natsuwa da wannan addu’a.... Gama addu’anta keda wuya wayarta dake jikin socket yai alamun k’aran shigowar sak’o... Hakan ya haifar mata da fad’uwan gaba ba kowa ya fad’o ranta ba illa Mr Unknown....
***
A can makaranta kaw su Nabilah suna fitowa daga exams aka dami Yusrah da kira, gashi dai da alama bata son amsa kiran ne gaban Nabilar... Nabila ta fahimci hakan dan tin fitowarsu a first paper kafin su shiga second paper Yusra Ke k’usk’us a waya... Har suka isa masallaci kira ake Yusrah na sakata a silent.... Nabila kaw yi tai tamkar bata a wajen saima duba question paper d’in jarabawar da suka fito take... Sanda Yusrah ta tafi alwala ta bar wayar saman jakanta gefen Nabilar kasancewar ita Nabilar ba sallar zatai ba shisa ta zauna daga gefen masallacin tana kuma duba takardanta, kaman daga sama wayar Yusrah ya kuma ruri... Kai dubantaga jakan tai lokaci guda ta janyo jakan zata d’au wayar... A d’ari Yusrah ta k’araso ta fuzge jakanta tana fad’in “Nifa banson sa ido...”
Harara kurum Nabilah Ke galla mata kana tai k’wafa tace “Kici gaba, ce miki akai bana lura dake ne a ‘yan kwanakin nan... Sarai nasan akwai abinda kike b’oyemin, kema hardake a shirye shiryen wannan auren munafuncin da ake shiryawa koh... Toh kici gaba Allah ya baki sa’a, dan Allah karki fasa...”
Yusrah na darawa kad’an take fad’in “Haba tawan kema kinsan bazan miki haka ba, dik abinda zai faranta miki shi nakeyi... Haba amaryar oga Bear..”
“Mtsww.. Ke kika sani kuma...” Ta fad’i tana mai aika mata muguwar kallo...
Yusrah ya dara had’ida mik’ewa tana mai ci gaba da fad’in “A daina cika mana baki dai munsan anaso ana kaiwa kasuwa....”
Ko tankata Nabilah bata sami zarafin yi ba, har yanzu ta kasa daina tinanin Wai Khalid baiko kirata ba har wayarta ta lalace ta kuma gyara duk bai nemeta ba... Anya wannan aure mai yuwa ne kuwa... Anya ba ramuwar wulak’anci data masa Farin had’uwarsu yai niyyan mata ba, idan ba haka ba ita ko a wasan kwaikwayo bata tab’ajin labarin ango irin Khalid ba... Takaicin kanta dana Khalid d’in ya kuma cika mata zuciya...
Batai wani gayya ba itakam, harta coursemates d’insu ma ba ita ta basu katin gayyata ba Yusrah ce duk tai wannan, suma ba duka ta bari Yusran ta gayyata ba, daga su Safwan da Al’amin saiko tsiraru cikin matan wad’anda suke mutunci....

***

Yusuf ya mik’e tsaye yana duban mamakiwa abokin nasa....
“Ban gane ba Akram... Toh Wai kana nufin har yanzu invitation card bai isa hannun his Excellency ba...?”

Jiki a matuk’ar sanyaye Akram Ke duban Yusuf kana ya d’an tab’e baki kad’an yace “Yusuf I can’t look him in the eyes.... Wllhi bazan iya mik’a masa katin nan ba.... Bansan da wasu kalmomi zan kare kaina a gabanshi ba... Mutumin da ya kasance Gata a gareni da ahalina.... Shin Yusuf wane irin yaudara da cin amanane wannan...? Ya yarda dani ya aminta dani ni kuma na saka mishi da butulci... Tell me Yusuf am I really doing the right thing....?” Ya k’arashe yana mai ci gaba da juya cards d’in hannunsa....
Fuzar da iska Yusuf yai kana ya d’an duk’a gaban Akram d’in.....
“Akram jibi za’a d’aura maka aure da Zulfa’u... Duk wani tunani da zakai yanzu toh fah ihu ne bayan hari.... Ka sani shi aure muk’addari ne... Allah ya nufa Zulfa’u ba matar his Excellency bace taka ce, so stop blaming yourself for what is happening.... Kar ka mance shi so dangin mutuwa ne bai duba rarrashi, nikam na fahimceka d’ari bisa d’ari ina kuma tabbatar maka His Excellency would understand you even more.... So stop all these ridiculous thoughts, and get yourself together...”
A hankali ya jinjina masa kai kana ya kuma d’agowa yana dubansa, mik’a masa wata takarda yai linke cikin takarda kana ya had’a masa da invitation card d’in yace “Kaine zaka kai masa wannan a madadina....”
Yusuf ya kuma binsa da kallon mamaki...
“Ban gane ba Akram.... “
Mik’ewa tsaye Akram yai yana fuskantar Yusuf d’in yake ci gaba da furta “Kaman yanda na fad’a maka bazan iya kallon cikin idonshi ba.... Nasan zaiji tsananin mamaki idan katin bikina ya riskesa... Hakan yasa nakeso kada ka bashi katin har sai ana gobe d’aurin aure.... Zai tambayeka Ina nake... ko kuma ya kira wayata.... Toh zan kashe wayata, sannan idan ya tambayeka ka sanar dashi nayi tafiya na tafi k’auyen su Umma kuma k’auyen k’auyene tukuf da ko service na waya babu.... Kawai abinda nake so ka sanar dashi shine.... Shi d’in shine Alwalin aure na... Ma’ana shi na wakilta shi zai karb’a min aure.... Promise me zaka isar da sak’ona gareshi abokina....” Ya k’arashe cikin tsananin raunin murya....

Saida Yusuf ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana ya dafa Akram kad’an yace “I promise you, zan isarda sak’onka da yardar Allah....”
Akram ya murmusa a hankali kana ya kuma zaro wata takarda ya mik’awa Yusuf d’in yace “Wannan wa amaryata zaka bada, nasan kwana biyu zataji wayata a kashe kuma zataga ban nemeta ba... Toh idan ta karance wannan takardan Zata fahimceni...” Wannan karon murmushi kwance saman fuskarsa ya k’arashe...
Yusuf d’inma murmushin yai kana suka rungume juna... Akram yana furta “Na gode d’an uwa.... Kai d’in ka wuce aboki a wajena... Kar ka tab’a mance wannan...”
Wannan karon darawa kad’an Yusuf yai kana yace “Kai ango dan zakai aure basai ka bar min wasiyya ba da Allah... Kaga bara naje na amso d’inkuna na d’azu Matazu ya kirani yace ya gama... Ina fata ka amso hulunan fitan angoncin naka...?”
Jinjina masa kai Akram yai yana mai furta “Naka wasa ne... Komai nawa intact yake.... Kaga da Allah ka ajiye takardun nan da mahimmanci and make sure ya isa ga wad’anda aka rubuta dominsu...”
Yusuf yace “Baka da haufi ango... Sai munyi telephone...”
“Alright shikenan sai na jika...”
Sukai sallama Yusuf ya fice....

***

Tin ana sauran kwana biyu biki ake bidiri a gidan Hajiya Haule, daga ita har d’iyarta Sahariyya shige da fice kurum suke, ba k’aramin shiri sukaima wannan biki ba da alama.... Dikda cewa Sahariyya da sandar crutches take dogarawa hakan sam bai hanata gudanar da shagulgulan bikinta ba, bata damu da cewa auren bai gaban angon ba ita dai tinda shid’in zata aura an gama mata komai, jiya ta gudanar da bridal shower gashi yau ma sai shirye shiryen kamu suke, Sahariyya jin kanta take mai babban sa’a cikin k’awaye... Selecting k’awayen ma suke itada Fa’iza sai kin kai a gayyaceki.. Kankace mai k’anan maganganu ya shiga yawo tsakanin k’awaye... Hakan bai dameta ba dama hakan ne takeso ta zama ita d’in dai ake zance....

A b’angaren Sameer bai gari ma ya tafi taron bita (Seminar) na kwana biyu a birnin Ikko, bazai dawo ba sai ana gobe d’aurin aure, Hakan yafi masa sauk’i don dama wannan aure shida babu a wajensa tamkar d’aya ne....Shi gaba d’aya yama mance da ana shirye shiryen biki da wata amarya har saida Shamsu ya kirasa yana zolayan yak’i dawowa ya mak’ale a Lagos ko sai sun biyosa da amaryarsa ce....

Sameer ya d’an mik’e d’aga yanda yake kishingid’e yana murmusawa kana yace “Tinda kana nan zaka wakilceni dan yanzu haka ma wasu team daga Korea kuma zamu tarba cikin satin nan... And my presence is very important, bazan iya katse abinda nake na dawo ba...”
Da mamaki Shamsu ke fad’in “Yanzu mahimmancin abin har ya wuce aurenka....?”

Sameer ya d’an fuzar da siriryar iska kana yace “Auren da na d’aika da mahimmanci a fari ka daiga yanda abu ya sauya mana da Siyama balle wanda sam dama ba har zuciyata bane, kawai na amsa ne dan ganin cewa zuri’armu bata tarwatse ba... So yafi ma da na basu space suyi bukinsu lafiya su gama, naci gaba da taron bitana a nan...”
Murmusawa Shamsu yai “Dr Sameer Faruq Yarima ko na ce Dr Ma’aruf Usman Mailafiya....”
“Duk wanda ka fad’i yayi Architect...” Yai maganan shima yana d’an darawa... Hira ta abokai sukaci gaba dayi Shamsu bai daina zolayarsa ba kana daga bisani sukai sallama....

***

Tafiya yake cikin motar ba tareda sanin tak’amaimen yanda ya nufa ba, shidai kurum yasan ya d’auki hanyar ficewa daga cikin gari, gaba d’aya ji yake zuciyarsa tanai masa d’aci, sam baijin ya kyautawa his Excellency... Zuciyarsa gaba d’aya a jagule take, sai faman fuzar da iska yake yana buga kan steering wheel, ga wani irin gudu da yake falfalwa saman kwalta tamkar mai barin Duniyar.... Yana shige wani check point na sojoji da kad’an wata mota tai masa overtaking.... Bai damu ba yai k’ok’arin canza hanyarsa saidai tuni motar ta kuma yunk’urin shan gabansa... Nan ne fah hankalin Akram ya soma karkata ga tinanin maiyasa wannan motar Ke bibiyarsa.... A hankali yake rage speed dan ganin gudun ruwan masu bibiyan nasa... Rage speed d’insa keda wuya wasu maza guda biyu suka fito suka finciki marfin motar nasa... Suna shiga d’aya da ya zauna daga backseat ya saka masa bindiga a k’eya yana mai furta “Keep moving...”
Hankali tashe Akram Ke karanto innalillahi mai kuke nema wajena..? Su waye ki....?”
Na gefensa ya buga masa k’arshen bindiga a k’eya yana mai furta “You talk too much... Kai abinda muka umarceka idan kanason ci gaba da numfashi....!!”
Tuk’i Akram yaci gaba dayi yana bin duk wani umarninsu dikda dishi dishi da yake gani sakamakon buga masa k’otar bindiga da d’anta’addan yayai....




SameenaAleeyou📚





*INDA RAI*
_.................DA RABO_






*86*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Saida suka saka kan Akram cikin wani bak’in jaka mai kaman buhu kafin

Please Login or Register in order to submit comment