Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“Then learn, learn how to love her... Sabida itace matar dana zab’a maka and no one else...!”

Duban Ammi kurum yake idanunsa na kuma kad’awa... Zuciyarsa cikeda k’una yake girgiza kai bai iya furta komai ba sai ficewa da yayi cikin sauri, k’iris ya rage basuci karo ba shida Yesmin dake tsaye bakin k’ofar kaman an dasata hawaye na gangaro mata alamun taji komai gaba d’aya tattaunawarsa da mahaifiyar sa, tsaye yayi yana k’are mata kallo ga tray a hannunta, itakoh Yesmin tuni ta sadda nata idanun k’asa hawaye naci gaba da kwaranyo mata....
For the first time da yarinyar ta bashi tausayi, baisan mai zai furta mata ba don haka d’an girgiza kai kurum yai yasa kai ya sauk’a k’asar benen cikin sassarfa....

Yesmin tabi bayanshi da kallo hawayenta na k’aruwa, itakoh Kubura dake lab’e k’asan staircase dad’i kaman ya karta ganin yanda Khalid ya gwale Yesmin dake rawar k’afar kai masa dambu... Sosai dad’i ya kama Kubura ta gama amintawa zuciyarta cewa Khalid ba abinda zaiyi da Yesmin, ko shakka babu shid’in rabonta ne...
A hanakali tana mai sakin murmushi take furta “KubsyKhal....” Tai Wani murmushi domin kaw had’in sunayen nasu ya mata, ta lumshe idanu a hankali ta lula duniyar tunani tana hango kalan soyayyar da zasuyi a gidansu, k’aurin k’unan abinci da hancinta ya jiyo mata daga kitchen ya sanyata zabura ta nufi kitchen d’in a guje...

A haka sati ya shud’e Yesmin na tunanin mafita, taji komai taji akwai yarinyar dake neman mata katanga da Khalid, saidai ba garin take ba balle ta tink’areta, menene abinyi...? Take tunanin Siyama ya fad’o mata, gidan Siyama kawai zata tafi tayi zamanta bazata dawo ba har sai ta saita ko wacce shegiya ce ke neman rabata da Khalid d’inta, ta kuwa sami Ammi da batun, Ammi tace tayi dai dai hakan shine mafita, tuni ta saka driver yakai Yesmin har garin Kano, ita kanta Yesmin tasha mamakin gidan da Siyama ke zaune cikinsa, idan ance mata Siyama zata iya zaman irin wannan gidan sai tayi musu...

Jiki a sanyaye ganin yanayin Siyamar Yesmin ta zauna had’ida kamo hannayenta tana kuma k’arema gidan kallo...

“Cousin ya haka.... Wannan ne gidan naku...?”

Siyama ta sauk’e ajiyan zuciya had’ida tab’e baki kana tace “Wai fah... Nidai dan Allah kada ki fad’awa Ammi don wllhi nasan kina fad’a mata aurena da Sameer ya k’are... Ni ban san uwar mai unguwar ke tsinana masa ba, kin gannin tinda nazo unguwar nan ko k’ofa ban tab’a lek’awa ba balle nasan kalan mutanen cikinta, bama zan iya adopting halayyansu da d’abi’unsu ba, daga kallo sai wayata idan ya fice asibiti...”

Yesmin ta jinjina kai a hankali kana tace “Aiko nima bazanso aurenki da Ya Sameer ya k’are ba banci uwar yarinyar da Khalid ke b’ata lokaci kanta ba, saidai fah Cousin zaman gida yanzu bai kamaki ba domin kaw dole ki taimaka min mu samo gidansu yarinyar nan mu saka mata layi...”

Siyama tai dariya a hankali kana tace “Bansanki da tashin hankali ba Yesmin, kodai Ammi ce ta ingizoki...”

Yesmin ta fuzar da iska a hankali tace “Akan My Khalid babu abinda bazanyi ba cousin aidai kinsan yanda nake k’aunarsa, promise kawai you’ll help me...”

Siyama ta kuma murmusawa kana tace “Kar ki damu I got your back ....” Yesmin ta murmusa cikeda jin dad’i kana suka mik’e Siyama na tayata d’aukan kaya zasu kai d’aya d’akin da ba kwana suke ciki ba....

***

A b’angaren Zulfah kuwa yau ne zata soma ziyartan wajen aikinta sannan a jiya laraba ne take fita daga iddarta, d’an zaman da tayi waje guda babu fita har wani haske ta k’ara, sannan yanzu hankalinta ya kwanta babu tsangwaman Hafiz dana danginsa, tinanin iyayenta da d’iyarta ke d’awainiya da ita, tanaji a zuciyarta sunyi kusan kasancewa ita da d’iyarta tare, tai murmushi tana kuma daidaita zaman mayafin abaya dake bisa kanta, Aunty B ta shigo tana sakar mata murmushi ganin yanda tayi kyau tayi kumari kaman ba Zulfa’u wacce Hafiz ya lahanta mata rayuwa ba...

“D’iyata kinyi kyau...” Aunty B tace tana mai kamo hannayen Zulfah...

Murmushi Zulfah ta saki a hankali kana tace “Na gode Auntynah...”

“Muje na soma ijiyeki sai na wuce nawa wajen aikin...” Ta fad’i tana gyara zaman mayafinta tana mai kallon kanta a mirror d’in, car keys d’inta na hannunta...

Jiki a sanyaye Zulfah ta d’au handbag d’inta mai launin shud’i wanda duka Aunty B ta sai mata sabida zata fara zuwa aiki, wadatattun kaya na gayu da kwalliya ta sai mata dukda Zulfa’un ba gwanar pente pente bace a fuska, iyakaci powder ne saiko man leb’e...

Aunty B ta dubeta yanda take tafiya a sanyaye kana tace “D’iyata lafiya kuwa...?”

Murmushi Zulfah ta kuma saki kana tace “Aunty I’m a little nervous, zan had’u da mutane da dama wajen aikina.... Sannan Aunty wai ni Zulfa’u za’ake hasko muryata gidan radio...?”

Aunty B ta murmusa tace “Kowa da haka ya saba Zulfa’u, ki saki jikinki kiyi aikinki da kyau na tabbata sanda mutane suka soma sauraren dadd’an muryarki zasu k’aunaci shirye shiryenki domin kaw ba dad’in sauti da iya kalamai kawai ba harta d’abi’unki gwanin sha’awa ne abin birgewa....”

Zulfah tai murmushi cikeda k’warin gwiwa kana tace “Har kullum bazan gajiya da maki godiya ba Aunty, Ubangiji kema ya faranta miki yanda kike faranta min...”

Aunty na murmushi ta kamo hannayenta suka k’arasa mota tana mai kwab’anta da yawan gidiyan da take mata....



SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_.................DA RABO_



*37*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Tsaye take kansa tanaci gaba da aika masa mummunar kallo, d’aurin kallabi a gefen kai as usual, ga taunar chewing gum da ya zamto d’abi’arta anayi ana hurashi had’ida yin k’as k’as.... Hannaye rik’eda k’ugu bata daina jijjiga ba take fad’in “Kanajina ba damuwata bace idan baka ciniki yanzu koma mai Kantin ne ya amshe kayanshi, wllhi duk yanda kaza ta shiga ta fita sai ka kawo min, ba shinkafa da tuwo aka aura maka ni kake bani ba ehe.... Yau kusan kwanaki uku kenan banci kaza ba jibi duk yanda na rame na d’aid’aice nayi bak’i, kaman ba jazir aka kawoni gidan nan ba....” Ta k’arashe tana juya idanu had’ida danna masa harara tana mai kuma hura chewing gum d’in bakinta.....

Fuzar da iska yayi hannaye bibbiyu ya rafka uban tagumi yana dubanta, ga wata uwar rama da yayi gaba d’aya kayayyakinsa wuyan sun masa yawa, idanuwansa duk sunyi kwarmi sun firfito waje, kaman ba Hafiz duk ya canza...
“Sau nawa zance maki kiyi hak’uri banida kud’in yanzu, kina gani kud’in da zan hau abin hawa zuwa kasuwa banida ita, jiya da na tari Alhaji da zancen ko amsani baiyi ba ya shige gida, wanne kikeso naji dashi Sawwama, shin ke ko tausayamin bakiyi ne....?” Ya k’arashe cikin k’asa da murya...

Wani wawan harara ta kuma aika masa tana mai ci gaba da taunar chewing gum tace “Toh ni ina ruwana don Alhaji bai amsaka ba, Alhaji nake aure ko kai, kai nifa bara kaji na fad’a maka billahillazi babu abinda ya shalleni kaji ne dole ka nemo ka kawomin naci, kuma kasan banacin guda d’aya tak, biyu zuwa uku dole ka kawomin, idanma sata zakai kai ka sani... Malam da Allah ka tashi ka fice min na gaji da ganinka zaune cikin gida....”

Iya wuya Sawwama ta kawo Hafiz.... Ya girgiza kai yana mai tuno Zulfah wacce duk abinda ya kawo gidan da sunan abinci sai tayita masa godiya tanai masa addu’o’in da duk k’iyayyar da yake mata sai yaji natsuwa da kwanciyar hankali cikin zuciyarsa, hakan bashi zai hana ya daddana mata wulak’anci ba, ya zageta ya muzantata ya tozarta iyayenta, daidai da rana guda bata tab’a ramawa ba, wasu lokutan haka yakan barta babu abinci dukda lokacin da take gidan samunsa yafi bunk’asa haka saidai yaje waje ya kashesuwa matan banza ko shaye shayen iska wanda ko d’aya yanzu bai isa ya kwatanta ba, duk wani kayan holewa sun fice masa a rai, toh ma ko yace zaiyi ina kud’in yi d’in, gaba d’aya duniyar tana neman tai masa d’aurin goro...
A hankali ya mik’e ba tareda ya kuma tankata ba ya nufi k’ofa...

Tuni Sawwama ta tare gabansa tana mai ci gaba da fad’in “Wllhi wllhi kaji na rantse maka idan baka dawo gidan nan da k’ullin kaji ba saidai kayi kwanan waje....”

Ya dubeta idanu a raunane gashi sam bai iya mata gardama baisan dalili ba, sukuf sukuf ya fice tamkar wani gajiyayye...

Da k’yar ya samu babur d’in da ya d’aukesa zuwa gidan Abbah da sunan idan ya isa zai bawa mai babur d’in kud’insa, shima mai babur d’in saida sukayita da wajewa yana masa gargad’in kada ya gudu masa da kud’i...

Koda ya shiga gidan ya jima yana hango sashensu Mamy kaman mai tunanin wani abin, jiki a sanyaye ya shige ya nufi sashen Mamani...

Mamani na zaune saman darduma tana gyara cazbahanta da ya hargitse taji sallama kamanta jikanta Hafiz...
Ya shiga wage baki tanai masa lale....
Kallo guda tai masa ai batasan sanda ta saki ‘ya’yan cazabahan dake hannunta ba suka watse k’asa...
“Kalu innalillahi wa inna’ilaihi raji’una... Laa ilaha illahu Mahammadar Rasulillahi.... Hafizu lafiya...? Meye haka..? Ciwo ne kayi.....?” Tayi maganar hannayenta dafe a k’irji...

Banda shafa k’eya Hafiz baya komai...
“Mamani naira d’ari zaki bani na sallami mai babur.....” Ya fad’i yana tsaye kanta...

“Yo ni fah baka amsa min tambayata ba, ita shashashar matarka taka Zulfa’u bata kula dakaine kokuwa...?”

Ambato Zulfah da tai yasa ya kuma kai mata duba had’ida lumshe idanunshi... “Mamani ki bani na sallami mai babur kar ya tara min jama’a...”

Da dafe dafe ta mik’e tanaci gaba da salallami tana tambayarsa ko jinya yayi, can wajen ajiyarta a uwar d’aki ta lalumosa ‘yan hamsin guda biyu ta bashi

“Ungo nan jeka biyashi ka dawo ka sanar dani uwar mai Zulfa’u keyi da ta bari ka lalace irin haka, kahurar yarinya mai halin uwarta, wato bari ta kasheka ta huta, kai wannan yarinya sam babu alheri tattareda ita, tsaban ta shahara ma ni ko a gidan nan na daina ganinta... Toh wllhi har yanda take zanje na sameta naci mata mutunci, haihuwarta yayi sanadiyar salwantar min da Ma’aruf d’ina gashi yanzu tana neman kaima ta aika lahira, toh ahir d’inta saidai ita ta mutu bakai ba, kai wannan yarinya gubarta yafi k’arfin annoba... Ni tin tana k’arama nacewa Manu babu alheri tattareda ita ya kaita bakin kogi aljanai su d’auka yak’i toh yanzu ga irinta waye ya sanima koda maita aka haifota ta lashe Ma’aruf gashi yanzu zata lashe Hafizu... Ohni Halimatu Manu ya haifo mana annoba a dangi....”

Har Hafiz ya sallami mai adaidaita ya dawo Mamani bata daina d’ibewa Zulfa’u albarka ba...
K’uri kurum ya mata don ko k’arfin magana baida ita, kwanuka dake gefe ya janyo ya shiga bud’ewa sauran karin kumallon safiya tuni ya shiga tura soyayyar doyar bakinsa yana had’iya yana muzurai...
Mamani ta rafka uban tagumi ta sanyashi gaba tana kallo, tsabagen tsanan Zulfah ya tsaya mata a rai tama mance kwanakin baya ance mata Hafiz d’in ya kuma aure....
Ta mik’e da k’yar ta kawo masa ruwa tana tambayarsa ko shayine za’a had’a masa, ko amsata bai iya yi ba sai girgiza mata kai kurum da yake alamun a’a...

Bayan ya ida tura sank’ararriyar doyar ne ya kora da ruwa nan yake fad’iwa Mamani wasu ‘yan kud’ad’e yazo ta bashi...
Babu musu ta d’ebo masa cikin bandir d’in ‘yan d’ari bibbiyu da kwanaki Haladu yaron Kirki ya bata...
Ta tasashi gaba tana tambayarshi meke faruwa....
Bai iya amsata ba ya mik’e yana fad’in zai kuma dawowa dama kud’in yazo ta d’an bashi sabida wasu ‘yan matsaloli da suka kunno masa....
Gaba d’aya kaman ba Hafizu mai son gayu da tirare ba, kaman wanda aka canza shi haka ya koma, ko d’an irin hira da yake zama suyi da Mamani yanzu ta lura baima zuwa ita idanba ta fara mantuwa irinta tsofi ba sai tace rabonta da ta skashi a idanunta ya doshi watanni, sam bai zuwa yanzu kaman da, gashi ita ta k’udiri niyyan bazata taka yanda Zulfa’u annoba take ba, amma yanzu kam ya zama dole taje gidan Hafizu tacima Zulfa’u mutunci taji dalilin da yasa ta bar mata jika ya d’aid’aice haka ba, haka tanaji tana gani Hafiz ya fice cikin sauri kaman zai kifa k’asa don d’an doyar da ya samu yaci yasa ya sami kuzari....

***

A gidan Radio Kafar ‘Yanci 96.8 kuwa sosai Zulfah ta sami karb’uwa daga wajen ma’aikatan gidan radion a karonta na farko taredasu, wata budurwa wacce Zulfah zata d’ara mata a shekaru da kad’an mai suna Atika ita taita nunawa Zulfah yanda shirye shiryen nasu ke wakana, ta kuma sanar da ita cewa itace take shirin nan na MU ZAB’I CANCANTA shirin da ake tattaunawa da kuma fashin bak’i gameda jagorancin da ‘yan siyasa suke a k’asar...

Zulfa’u ta zaro idanu waje cikeda jin dad’i tana fad’in “Dama kece Atika Shu’aib dake gudanar da shirin Mu zab’i Cancanta, kai don dai bakisan yanda nake matuk’ar son sauraren shirin nan bane, sam bai wuceni musamman da yanzu zab’e ya kunno kai sosai..”

Atika ta murmusa tace “Gashi yau kin had’u dani kuma nima naji dad’in had’uwa dake gashi Allah ya had’amu wajen aiki guda, ina fata Allah ya dafa mana cikin sana’armu...”

Zulfah ta amsa da amin cikeda nuna jin dad’inta itama, kafin Atika tace “Muje ai inaga Manager ya iso yanzu za’a sake mana lokutan shirye shirye musamman sabida an d’ibi sabbin ma’aikata.....”

Zulfah ta jinjina kai murmushi kwance saman fuskarta tana biye da Atika suka nufi babban d’akin gudanar da shirye shiryensu yanda a nan zasu gana da manager gaba d’aya ma’aikatan gidan Radio d’in....


***

Siyama tace “Gaskiya bansan wace unguwa yarinyar take ba amma a nan BUK take karatu, inaga can ya kamata muje mu fara nemanta kafin mu sami gidan nasu....”

Yesmin dake zaune gefen mai zaman banza ta kad’a kai tace “Hakan yayi, namafi so mu soma samunta a makaranta muci mutuncinta da kyau a bainar nasi kafin mu biyota gidan ubanta mu mata...”

Siyama ta d’an dara kad’an tace “Kallo d’aya nayiwa yarinyar naji bata kwanta min ba, Allah sa ma dai ba asiri ta masa ba don a yanayin danasan Khalid ko maganar fatar baki bazai yarda ya had’asa da irin wannan yarinyar ba balle har ajega batun soyayya...”

Yesmin ta kuma cika tana fad’in “Toh wllhi bokanta yayi kad’an ya mata k’arya, zata gane shayi ruwa ne, zata gane ta d’auko size d’in takalmin da yama yawa.... Muje cousin mu soma nemanta....”

Siyama ta d’an dara had’ida buga kan steering wheel tana fad’in “Dole nayiwa Ammi video don ya kamata taga komai...” Suka saka shewa a tare kafin Siyama taja motar suka wuce...

***

Tuni Mamani tayi shirinta na fita, bata gayyaci kowa ba da sunan rakiya, ta kuwa yi sa’a tana fita ta hangi Mai adaidaita bakin layi nan ta tare had’ida sanar dashi unguwar da zai kaita, ita kad’ai cikin napep sai sababi take gaba d’aya ta cikawa Mai napep d’in kunne....



SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*38*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*


NOT EDITED!


Sun d’au lokaci suna zaga cikin makarantar don ba sanin tak’amaimen yanda zasu sameta sukai ba, gashi ba sanin sunanta sukai ba balle department d’in da take ko kuma course d’in da take karantawa...
Siyama taja tai parking don ita kanta ta gaji da zagaye da kai komo da suke, Yesmin ta d’an dubeta tace “Wai har kin gaji...?”

“A d’an kaikaice Siyamar ta dubeta kana tace “Ba dole ba, kinga we can’t find her that easily, nidai inaga what we should do mu koma gida mu sake tunani...”

Girgiza kai Yesmin tai alamun k’in amincewa kana tace “Haba cousin just think, kiyi tunani a yanda kika ganta da Khalid, baki iya tuna d’an wani sign ba like bishiya haka ko garden ko kuwa dai wani business center da zaki iya tunawa.... Don’t forget as they say a bari ya huce shike kawo rabon wani, na k’agu na ganta ido da ido na kafa mata concrete warning akan My Khalid... Please Cousin kar kice kin gaji please....” Ta k’arashe tana kamo hannayen Siyamar...

Jinjina kai Siyama tai kana tace “Alright fine, let’s see... Idan ban mance ba yanda Khalid yai parking motarsa akwai wata bishiya wajen, sannan akwai wani signboard da ya d’auke hankalina kad’an kaman an rubuta welcome to department of Mathematics and Statistics, something like that...”

Yesmin ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa toh yanzu kinga abinda zamuyi let’s ask where we can find the department, na tabbata from there zamu iya samunta, definitely a department d’in take idanma ba haka ba akwai dai abinda take zuwa yi department d’in kuma zai iya linking d’inmu da ita....”

Siyama ta jinjina kai a hankali kafin tai starting engine suka soma tafiya....
Wasu samari suka tarar zaune saman wasu kujeru a garden d’in SUG nan suka tambayesu yanda zasu sami department of Maths and Stat, nan take samarukan sukai directing nasu har yanda department d’in take, sukai masu godiya kana suka kuma d’aukan hanya...

***

Har suka iso unguwar bakin Mamani baiyi shiru ba... “Inyi yarinya saikace jikanyar ifiritu, duk wani kayan arziki babu shi a tattareda ita, jibi duk yanda yaron nan ya lalace ya koma tamkar bashi ba, inaji dai shima jininsa ta fara zuk’a toh wllhi ta gama cinye zuri’ata tun kan Ma’aruf, saidai taci kanta yanzu kam ehe....”

Duk maganar da Mai adaidaita keyi mata cewa an iso bata saurareshi ba sai balbala masifa take, k’arshe dole ya nemi waje yayi parking ya had’e tagumi yana jiran ta sakawa maganganun nata aya...
Sai bayan wani lokaci ta kula keken ta daina tafiya... Ta saka sandar hannunta ta dunguri k’eyar mai adaidaitan tana fad’in “Yaya haka... Kai dama mashin d’in taka a gajjiye take ne... Ya ka tsaya dani a nan ko ce maka akayi bazan biya kud’inka bane inyi....”

“Baaba tintini naketa ce maki mun iso daidai ina zaki sauk’a amma baki saurareni ba shiyasa naja na tsaya ki gama maganar taki....”

“Aw dama ba saurareta kake ba, wato ka k’yaleni inata magana ni kad’ai ga mahaukaciya koh... Toh ai sai kace min ka kawoni yanda na umarceka ba ka zauna ka had’e tagumi ba kaman wanda anka ka kawowa mummunar sak’o...” Ta shiga k’ok’arin lek’o kai tana ganin unguwar, tsaf ta hangi babbar durumin da take gane gidan dashi dashike a lokacin da Alhaji zai gina mar gidan da Mamani ake zuwa tsaban fitina irin nata da dai akace Zulfa’u za’a aura masa shine ta yanke k’afafunta daga gidan, gata dai duk tsufa da ya sauk’o mata da wuya take mance abu shiyasa gidan sam bai b’ace mata ba...
“Yauwa kaga an iso ajeni nan...” Ta k’arashe tana laluma kud’in adaidaitan a lalitanta... Tana sllaman mai adaidaita ta shiga dogara sandarta sanda ta nufi gidan....

Da sandar hannunta ta dinga bugun k’yauren don ko sallama Zulfah bazata samu daga gareta ba....
Sawwama da tuni bacci ya d’auketa nan cikin baccin nata taji ana bugun k’ofa tamkar za’a b’alla...
Ta buga uban tsuka tana mai kuma juyi cikin gado, abu kaman wasa bugun k’yaure yak’i k’arewa...
Ta mik’e zunbur ta zauna tana tunanin wani shafeffe da man ne ke mata wannan d’iban albarka a k’ofar gida, yo ko bashi ta ciwo a mata bugun a nitse ballanta babu ko d’aya... Duk uban dake mata wannan d’iban albarkan sai yasan ya tada ita daga baccinta ko wanene kuwa kai koda Magajiyace mahaifiyar ta...
A fusace ta fice babu ko kallabi balle mayafi ta nufi k’ofar....

****

Sun kusan shafe awa guda a wajen mutane sahu sahu sai wucewa suke, can suka hangi wasu ‘yanmata guda uku sun fito daga wani babban gini mai d’auke da rubutun ETF nan suka baza idanu kodai zasu iya gano yarinyar ciki, dashike Siyamace ta tab’a ganin fuskar tata nan ta shaidawa Yesmin d’in babu alamunta cikin ‘yan matan, har dai sun cire rai bazasu ganta ba saiko gata ta fito daga ginin itama tafe tareda k’awarta wacce Siyama ta gansu tare...
Cikin sauri Siyama ta shiga nunawa Yesmin ‘yanmatan tana fad’in “Alhamdulillah kinganta gatan can mai red hijab.... Zo muje...”

A tare suka finciki marfin motar suka fice Yesmin sai faman huci take yawa zata tashi sama...
Nabila da Yusrah wad’anda sam basusan da isowar bak’in nasu ba hankali kwance suke tafiya suna firan class d’in da suka fito.... Kaman daga sama sai ganin ‘yanmata guda biyu sukai sun tare gabansu suna binsu da kallon k’ask’anci...
Daga Nabilah har Yusrah tsayuwa sukai suna kallon ikon Allah....
Yesmin ta kuma yamutsa fuska tana dubansu kana tace “Cousin who is she among ‘em...?”
Siyama dake toshe da hanci alamun suna wari da yatsa tai nuniwa Yesmin zuwaga Nabilah....
Wani dariyan rainin hankali Yesmin tai tana nunida Nabilah da yatsarta manuniya daga sama zuwa k’asa... “This thing... Wannan abar, kina nufin kan wannan abar Khalid ke rawar k’afa, toh ai ni banga mace a nan ba....”

Yusrah da zuciyarta ke tafarfasa ta zuciya zatai kan Yesmin Nabilah dake faman murmushi tai saurin kamota ta dawo da ita baya tana fad’in “A’a don’t mind them baki lura ba... She and I aren’t the same scarecrow... So just let them be....” Ta k’arashe tana sakar masu murmushi had’ida janyo hannun Yusrah zasu rab’a su wuce...

Yesmin da tuni ta saki baki cikeda mamakin maganan da Nabilah ta yab’a mata saurin finciko hijab d’in Nabilah tai tana fad’in “Ke you dare call me a scarecrow...Me? A scarecrow.... How dare you...?” Ta k’arashe tana k’ok’arin kai mata mari...

Nabilah da har lokacin murmushi take gyara tsayuwarta ta kumayi tana duban hannun Yesmin da ya daskare tamkar an rik’e...
“Try it... Do it.... Aw bazakiyi ba....?” Yesmin ta kasa amsata sai huci... Kafin tai wani aune taji sauk’an mari masuji da lafiya har guda biyu a fuskarta...
Siyama da abin ya bata tsoro fiyeda zatonta sakin baki tai tana kallon Nabilah shaye da mamaki..
Yesmin ma rik’eda k’uncinta take duban Nabilah, da gaske marinta tai....

“What..? You want more...?” Nabilah ta kuma fad’i tana duban Yesmin d’in wacce ta soma fincika daga rik’onda Siyama ke mata tana fad’in “Cousin ki sakeni na nunawa yarinyar nan k’aramar maras kunyace ita don Allah ki cikni...”

Siyama taci gaba da janye Yesmin tana fad’in “Ke wannan da gani ba mai cikakken hankali bane tinda ta sake ta mareki ba tareda sanin ko wacece ke ba, muje muyi shirin tink’aranta da kyau...” Ta turata suka nufi mota, Yesmin bata daina juyowa tana fad’in “Wllhi Khalid yafi k’arfinki kuma saikinsan kin mareni wllhi kaf danginku sunyi kad’an su k’waceki...”

Huci kurum Nabila keyi sunaci gaba da tafiya, babu mai cewa komai daga ita har Yusran...

Yusrah ta d’an dubeta tace “Nabilah su waye wad’annan...?”

D’an dubanta Nabilah tai still fuskarta a b’ace kana tace “Oho ban sani ba amma dai ga dukkan alamu ‘yanmatan Khalid ne....”

Yusrah tai shiru tamkar mai nazari, tana murna k’awarta ta sami miji ga wani fitinar na neman kunnowa... Sauk’e ajiyan zuciya tai tana duban k’awar tata wacce itama sak’e sak’en take cikin zuciyarta, idanma Khalid shi ya turosu zaiji daga gareta ne... Ita kad’ai sai faman k’wafa take...

A haka har suka fito gate suna neman abin hawa gaba d’aya ran Nabilah a jagule ita bama wad’annan kucakan ne suka tsaya mata a rai ba, Khalid take nanatawa cikin zuciyarta tana k’wafa...
Suna shigewa adaidaitan su Siyama dake lab’e daga angle suka soma bin bayan adaidaitan nasu don binciko yanda Nabilah ke zama dukda da fari sunyi tunanin ko hostel take zama amma hakan bai hanasu jira ba don tabbatarwa...

***

Da k’arfin gaske Sawwama ta tura k’ofar wanda yasa k’iris Mamani bata zube k’asa ba, sandarta ta fad’i gefe k’ofar ta bige mata gwiwa kad’an abinka da jikin girma dama ba wai lafiyan k’afafune ya isheta ba...
Rik’eda gwiwarta take fad’in “Wayyo wayyo k’afata....!” Tana duk’e ta kasa d’agowa sai tamke idanu da take...
Sawwama dake tsaye rik’eda k’ugu tana faman yatsine yatsine wani uban tsuka ta buga kana tace “Sabida tsaban jaraba baran taku ta wuce kuyi a bakin hanya sai kun biyo mutane gidajensu kuna tak’ura masu kuna hanasu bacci ko cewa akai sadakar dole ne iyi... Shegen jaraba da fitina irin taku na tsofin mabarata... Zaki b’ace min da gani ko sai na kuma hankad’aki....!” Ta k’arashe cikin daka tsawa....

Da k’yar Mamani ta d’ago idanu tana duban matar dake mata d’iban albarka wanda tsawon rayuwarta babu wanda ya tab’a kwatanta hakan a gareta... Tirk’ashi! Ta fad’i cikin zuciyarta sanda tai tozali da matar....Tai k’ok’arin janyo sandarta ta mik’e sosai tana duban Sawwama dake faman yatsine yatsinen fuska tana jefa mata mugun kallo....
“Bakiji abinda nace bane ki fice ki bani waje..!” Sawwama tace tana mai kuma yamutsa fuska...

Banda kallonta da Mamani take bata iya komai, toh ita kuma wannan d’in wacece....? Da

Please Login or Register in order to submit comment