Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaman US nakan shiga kitchen na taya Mummy a nan na koya... Daga nan ya zama one of my hubby...”
D’an jinjina kai tai kad’an kana tace “Toh mai kenan matarka zatai ta birgeka if you can cook better than her...?”
Murmusawa ya kumayi kana yace “Naki sai yafi nawa, idan kinyi musamman domin ni sai yafi birgeni, and one more thing... Matarka is your companion, your friend and your partner... She’s not your maid nor your slave....So babu wani aibu dan once in a while ka girka mata abinci... One mistake da nai da Siyama shine na nuna mata nid’in zankeyi shiyasa batayi... Amma yanzu she changed her ways, kuma haka yafi komai min dad’i....”

D’an murmusawa tai kad’an kana tace “You really love her..!”
Ya jinjina mata kai yana mai furta “So much....” Lokaci guda ya kuma kamo yatsun hannunta kana yace “I love you both....!”

Ta murmusa tana mai kwantar da kanta cikin k’irjinsa, sallaman Mamy ya sanyasu janye jikkunansu daga cikin na juna....

***

Masha Allahu, Allah shi ke bada Mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso domin ya jarabci bayinsa... Anyi Election lafiya, sakamako ya fito a Washe gari, yanda aka bayyana Engr Ma’aruf Mutallab a matsayin wanda lashe zab’en ... Gari ya cikada rally da murna, dik yanda ka shiga shagalin murna kawai zakaga anayi, masu adaidaita da masu babura babu yasu... Toh saidai muce Allah shi tayasa rik’o ya basa ikon kwatanta adalci....
Harta gidan mahaifiyarsa saida jama’a suka cika mak’il sai zuwa masu san Barka ake... Su Marliya da Raihanah ma can suka yini sai dare Sameer ya biya ya d’aukesu dan shima yana tare da Engr d’in through out the day... Aunty Bara’atu ma nan gidan Ammahn ta yini suna tayasu amsar bak’i ‘yan murna...

A gajjiye lik’is ya shigo gidan danma da k’yar ya samu ya janye jikinsa daga wajensu party chairman da sauran masu muk’amai a jamk’iyar tasu, ga kuma mutane da tuni Sun soma tururuwar kawo masu barka...

Wajajen k’arfe goma ya shigo gidan yanda ya taddata da Ammah sunata kallon labaru ana hasko zab’en da kuma wanda yai nasaran... Kaman ta mik’e ta haye jikinsa haka taji dan murna amma bazata iya yin hakan ba kasancewar da mahaifiyarsa zaune wajen....

Samha da batai bacci ba tana nan zaune tareda ita ake kallon yana shigowa ta tafi da gudu ta haye jikinsa tana fad’in “Daddy congratulations... I saw it on the news, you won the election....!”Cab’eta yai yana mai furta “Na gode baby... Addu’a zaki min kinji Allah yamin jagoranci...” Ta jinjina masa kai su Ammah da Zulfah na amsawa da Ameen..

Daga nan ya k’arasoga mahaifiyarsa yana satan kallon Zulfah suke gaisawa da mahaifiyar tasa tana mai kuma masa Barka da fatan alheri had’ida ‘yan nasihu dangane da hidiman da ya shafi Al’umma....
Bayan ta d’an masa ‘yan nasihohi ne ta mik’e tana fad’in zata shiga ta kwanta dama isowar nasa take jira... Samha ma mik’ewan tai da niyyan tafiya sai kuma ta d’an juyo tana duban mahaifin nata....
Engr ya d’an bud’e murya yace “Princess akwai abinda kike so ne...?”

K’arasowa kusansa tai kana tace “Dad we’re missing our mum... When are we going to see her... Why isn’t she here with us.... Ba kaci election ba..? She should be here celebrating with us... What happened to our mum....?!”Ta k’arashe cikeda nuna damuwa...

Zuciyarsa Ta tsinke lokaci guda, anzo wajen yanda zai breaking wannan labari mai nauyi ga yaransa... Harta Zulfah dake gefe saida zuciyarta Ta yanke... Engr ya d’an kaikaito yana duban Zulfah dan baisan mai zaicewa yarinyar ba....
K’uri yaiwa yarinyar yana k’ok’arin nemo abinda zai fad’i mata sai ganin hannun Zulfa’u yai ta dafa Samha, lokaci guda take furta “Sweetheart your Dad has something very important to tell you....Amma ba yanzu ba Coz he’s a a little bit tired now... Kuma kema ya kamata kije kwanta sabida ki tashi da wuri ko kin manta we have plans for tomorrow...?” Ta k’arshe tana kashe mata idanu guda....

Saurin jinjina kai tai cikeda murna tana fad’in Ta tina, lokaci guda ta manna masu peck a kumatu tana mai masu saida safe....

Zulfah ta bitada kallo har ta shige murmushi saman fuskarta....
Engr kaw sauk’e ajiyan zuciya yai a hankali yana mai sauk’e gajiyayyun idanunsa kan Zulfa’u... Lokaci guda soyayyarta na kuma ratsa ko wace kafa ta zuciyarsa.... Juyowa tai taga ya tsareta da idanu... Ta d’an sadda kanta tana murmushi.... Hannunta ya janyo yana mai fad’in ta k’araso cikin jikinsa....
Ta matso cikeda d’an jin nauyinsa.... Nan yai mata masauk’i cikin jikin nasa yana mai lumshe idanu.... Lokaci guda yake furta “Everything is stressing out.... All I need right now, is to be with you....!” Ya k’arashe yana mai bud’e idanun nasa had’ida sauk’esu saman fuskarta....
Ta d’an murmusa kad’an ga k’irjinta dake tsananin bugu....

Tallafo fuskarta yai yana kuma dubanta cikin idanu kana yace “I don’t think I can take half of this without you...Thnk you for taking care of my family, my mum and my children....Thank you for being here... Thank you for everything, my number 1...”

Murmushi saman fuskarta take furt “Dan Allah ka daina min godiya saika naji kaman wani abin nayi... Yaranka yarana ne... Sannan Ammah ko baka aurena she’s still my mum, itada Mamy basuda maraba wajena....!”

Murmusawa ya kumayi k’aunarta na fizgarsa... Lokaci guda yake ci gaba da furta “You know, at first lokacinda na soma jin muryarki... I thought na fad’a soyayya da shirin da kike gudanawa ne... Daga bisani sai na zaci da muryarki na fad’a soyayya.... And now that I started to get to know you ... Sai na fahimci ba zallan muryarki bane ba kuma zallan kyaun fuskarki ko na jikinki ba... Zuciyarmu sun jima da had’uwa a wani waje na daban, basu samu damar kasancewa tare ba sai yanzu.... Zulfa’u I want you to know that I love you... So much... I’ve never felt like this for any woman before... A baya nayi zaton moment irin wannan bazai tab’a zuwa a rayuwata ba... Na karb’i k’addarata Muhibbah a matsayin matata... But as they say INDA RAI DA RABO.... Toh yau gashi ina gani, gani nan tareda matarda nakeso, nake kuma fatan na k’arashi rayuwata tareda ita... I’ll love you, take care of you and above all I’l respect you till my very last breath..!”Ya k’arashe cikin wane irin sanyin murya, Zulfa’u kam tuni hawaye sun shiga gangaro mata... She was like is this for real, shin Wai ita Zulfa’un ce yau namiji ke sanar da ita duka wad’annan, Zulfa’u da aka camfata mai Farin sawu... Zulfa’u data sha Uk’uba a rayuwar gidan aure har saida tai tinanin dik mazan duniya halinsu guda ne... Zulfa’un da tai tinanin babu sauran Farin ciki a rayuwarta nan gaba da zata tadda... Ashe irin wannan rana na zuwa da zata samu soyayya da girmamawan miji.... Tabbas ta yarda Allah shine mai canza al’amra a lokutan da yaso.... Ta kuma yarda da wannan kalma da akace INDA RAI to fah shakka babu akwai RABO... Mai rai kar ya zamto mai cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa.... Tana fata da addu’a ga sauran ‘yanuwanta mata da suke experiencing what she went through a gidan aurenta na baya suma kar su cire Rai daga rahamar Ubangiji... Allah ya shirya mana mazajenmu ya sanya masu soyayyarmu da tausayinmu cikin zukatansu... Ya Ubangiji Allah ka zaunar damu lafiya tareda abokan rayuwarmu daka hukunta mana zama taredasu.... Ameen ya Rabbi..!

Ganin tana hawaye ya sanyashi kwantota cikin jikinsa yana lallashinta a hankali lokaci guda yana rikitata da salon k’aunarsa mai cikeda maturity....Yanayin da bazasu so wani abu ya datse masu ba, kaman daga sama wayarsa ta soma ruri... Cikeda jin nauyinsa ta kuma mak’ale kanta cikin k’irjinsa... Tana jin sanda yake amsa wayar da ko ba’a ce ba urgently ake nemansa... Jim ya d’anyi kana yace su tsammacesa nan bada jimawa ba...

Engr ya tallafo fuskarta sanda ya ida wayar kana yace “See, bazasu bar mutum ya huta ba... Wannan kafin ai swearing in a shiga office kenan... Kiyi hak’uri Zulfa’u I’ve to go, wannan shine mijin da kika aura mai hidimar Al’umma... Nasan ya kamata na ware maki lokacin ki... Amma kiyi hak’uri nai miki alk’awarin before ai swearing in lokutana gaba d’aya zan mallaka miki... Kafin na shiga aikin Office gadan gadan....”

Murmusawa ta d’anyi kana tace “I’ll always support you in everything, nasan rabin abubuwan da kake ba dan kanka kake ba... Dan jama’anka kake... Sabida haka, zaka sameni Ina mai k’arfafa maka gwiwa in sha Allah wajen ganin ka kimanta sauk’e nauyin da Allah ya d’aura maka...!”

Wani irin dad’I da sanyi ne ya lullub’e masa zuciya, ya kuma shafar fuskarta yace “What do I do without you.... Allah ya miki albarka....!”

Ta amsa da Ameen tana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye take fad’in suje Ta Mar rakiya... Suna tafe yake fad’in gobe in sha Allah zata taimaka masa su sanar da yaransa batun mahaifiyarsu a natse yanda bazai affecting d’insu ba.. Zulfa’u ta jaddada masa idan dai wanna ne baida matsala... Har k’ofa tai masa rakiya yanda Ta hangi Akram da ‘yansandan da tuni an basa matsayinsa na governor elect sun nufi motoci a hanzarce suna k’amewa...

Akram na hangosu yai saurin sadda kansa dan harga Allah wane irin girman Zulfa’u yake ganina halin yanzu... Dole ne ma yaga girmanta a matsayinta na matar Uban gidansa...
Kai a k’asa ya k’araso harda risinawa yana gaida Zulfa’u, sai saman taji ashe ma Excellency Ma ya ambaceta da... Itakam this too formal for her Meye wani Excellency Ma, Wai ita Zulfa’un ce yau ta zama her Excellency.. Abin sai yanata mata wani banbarak’wai... Sallama suka kumayi da Engr yanda suka nufi mota shida Akram yanda Akram d’in Ke masa bayanin wasu abubuwa...

Zulfa’u kaw har yanzu wannan Excellency Ma da Akram ya ambaceta dashi bai daina mata banbarak’wai a kunne ba saima da Atika ta kirata tana ihu tana kiranta da her Excellency abin ya kuma mata bak’o
Zulfah tace “Zaki sani ne tinda ke yanzu kin zama ‘yar rashin mutunci ko ganinki ba’ayi....”

Atika tace “Allah huci ran her Excellency, zuwa ya zaman min dole ni da zanzo a bani komishina Ta mata...”
Sukai dariya a tare Zulfah na fad’in mai hali bai fasawa... Nan dai suka ci gaba da hiransu Zulfah na tambayarta labarin station d’insu... Gaskiya tayi kewarsu gaba d’aya...
Atika tace zasu hallaro suzo suyi masu murna.... Haka dai sukaci gaba da zance har dai daga bisani sukai sallama...


***


Bayan kwanaki biyu akai zaman kotun su Muhibbah yanda aka yanke masu shekaru goma sha biyar a gidan yari... Allah sarki abin akwai tausayi kam amma wannan shine sakamakon ayyukansu... Sanda za’a wuce da ita prison Engr ya k’araso ya buk’aci a barsu su gana.... Muhibbah ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa lokaci guda take furta “Ma’aruf ka yafe min... Ka yafe min dik abubuwan da nai maka a baya... Gidan yari shi ya kamaceni bayan rayukan mutane da dama da nayi ruining... Hak’ik’a shan miyagun k’wayoyi bazaikai d’an Adam ga komai ba face tab’ewa... Ta’ammudi da miyagun k’wayoyi ya taka rawa wajen sauya min kwanya da tinani har takaiga na ballagazantar da aure na da kuma ‘ya’ya na.... Nayi watsi da rufin asirin da Ubangijina yai min... Yau ga halinda na tsinci kaina ciki... Ina rok’on Allah yasa hakan ya zama wa’azi ga masu hali irin nawa... Ma’aruf yau ina rok’onka gafara dan Allah ka yafe min...!” Ta k’arashe tana mai had’e hannayenta biyu dake d’aure cikin handcuff waje guda alamun rok’o....

Girgiza kai yake hawayen da yake mak’alewa suna kuma gangaro masa lokaci guda ya kamo hannayen nata yana furta “Muhibbah na yafeki duniya da lahira... And about our children zan kula dasu da dikkan iyawata... Fatana shine Allah yasa wannan ya zamto sanadin shiriryarki Muhibbah... Zan dinga kawo miki yaranmu lokaci zuwa lokaci suna kawo miki ziyara... This is a promise... Na fad’a miki bazan abandoning d’inki ba sabida dukanmu ‘yanadam ne masu kure... We will face this together..”

Murmushi ta d’anyi kana tace “Na gode Excellency na....Na manta ban congratulating d’inka ba... Congratulations Allah ya tayaka rik’o dama kai d’in na Al’umma ne... May Allah guide you through...!”

Engr ya amsada Ameen kana yace “You take care of yourself....!”
Jinjina masa kai tai tana murmushi lokaci guda tana share hawayen da suka zubo mata daidai sanda ganduroba mace ta janyota suka shige....

Washe gari akai zaman nasu Baba Alhaji ma yanda Hafiz da ba’ai tsammani ba yaje shi ya bada shaida... Zo Kaga yanda Baba Alhaji yake kuka yana murna, haka ya rungumi Hafiz su duka biyu suna hawaye... Abbah na waje na jiransa, Baba Alhaji yana hango Abbah ya tafi ya rungumesa su duka biyun suna hawaye gwanin ban tausayi... Lokaci ne na yafewa juna... Komai yai tsanani yana tareda sauk’i.... Rahamar Ubangiji ya lullub’esu.... ‘Yan uwan da suka taso cikin sab’ani da juna yau gasu nan k’ark’ashin inuwa guda... Zumunci al’amari ne mai girman gaske... ‘Yan uwa kada muyi wasa da zumunci... Musaka sharri da Alkhairi, mu kuma zamto masu yad’a alkhairi da yafiya had’ida soyayyan junanmu a tsakani....

Haka suka d’unguma suka nufi gida cikeda Farin ciki, k’annensu su Baffah Ado da Baffah Wada suna hango ‘yan uwan nasu suka tafi suka rungumesu suna masu nuna Farin cikinsu, haka Baba Alhaji yaita godiya wa Abbah yana fad’in ya basa girman, kuma ya yarda Allah shike d’aukaka wanda yaso a cikin Al’umma... A gida guda sai Allah ya d’aga k’arami Daga cikinku ya bashi wani mulki ko arziki ba don komai ba sai dan hakan ne yaso ta kasance...

Abbah kaw cewa yai har gobe Baba Alhaji shine dai gaba dashi babban yayansu... Suna nan a haka a k’ofar gidan Baffah Ado da ya ida waya ya k’araso masu da labari mai dad’i cewa an sami Mamani....

SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_............... DA RABO_



*112*



*©️Sameena Aleeyou...*






Daga Abbah har Baba Alhaji har suna had’e baki wajen tambayar Baffah Ado ina Mamanin take... Baffah Ado ya labarta masu yanda akai, ashe gidan d’iyar k’awarta Hajiya Marka ta tafi dashike Ita d’iyar k’awar tata k’awar Matar Baffah Ado ne, kuma Mamani ta rok’esu kan cewa kada su sanar da yaranta ga yanda take ita kaw d’iyar Hajiya Marka taga kullum wannan tsohuwa cikin damuwa da kuka take ga shekaru da suka ja, hakan ba daidai ne ga lafiyarta ba, wannan dalili yasa ta yanke shawarin sanar da yaranta...

Babu b’ata lokaci suka nufi gidan Hajiya Rabi d’iyar Hajiya Marka marigayiya k’awar Mamani.... Mamani tana hango Abbah sabon kuka ya kece mata... Allah sarki shima Abban kukan yake sosai lokaci guda ya tafi ya rungumeta yana kuka sosai yake fad’in “Mamani mai yasa zaki tafi ki barmu... Munsha wahala sosai wajen nemanki... Mai yasa zaki gujemu Mamani na...!”
Cikin muryar kuka Mamani ke fad’in “Usman bansan da wasu idanu zan dubeka ba... Abinda na b’oye maka tsawon rayuwarka abu ne mai girman gaske d’ah na.... Nayi kishi sosai irin na jahilcin zamin da nida mahaifiyarka amma Allah shine shaidata haihuwa itace tai sanadiyar mutuwar Harira... Usman ka yafeni idan na b’oye maka dika wad’annan d’ah na....” Ta k’arashe tana kuka sosai....
Abbah ya kuma kamo hannayenta yana hawaye lokaci guda yake furta “Na yarda dake Mamani, kuma tabbas da ace zaki kashe mahaifiyata da nima kin had’a dani amma kika d’aukeni kika bani duk wani kulawa da uwa ke baiwa d’anta... Shin ta yaya zan mance duka wad’annan... Mahaifiyata haihuwata kawai tayi amma kece duk wani d’awainiyata tin ina tsumman goyo har izuwa girmata, hakan bazai tab’a shafewa a idanuna ba... Zanci gaba da yiwa mahaifiyata addu’an samun rahama har tsawon rayuwata sannan kema zanci gaba da baki matsayin mahaifiya da nake baki tin tasowata... Babu abu guda da zai canza Mamani na....!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa hawaye naci gaba da gangaro masa....
Mamani ta tallafi fuskarsa tana hawaye sosai lokaci guda take furta “Tabbas ba sai ka haifi d’ah ya zamto Naka ba... Na yarda da wannan kalma da hausawa me cewa D’ah na kowa ne... Kada kaga yaro ka wulak’antasa ko Allah ya k’addari rik’onshi ya fad’o hannunka kai masa rik’on sakainan kashi, bakasan waye zaka mora a rayuwa ba, d’an wani sai yai maka abinda Naka d’an bai maka ba... !”

Abbah na hawaye yake jinjina kai kana yace “Mamani tare muke da ‘yanuwana... Zamu d’aukeki mu koma gida gaba d’aya...!”
Mamani ta d’an sarara da kukanta kana tace “Kana nufin harda Alhaji..?”

A hankali Abbah ya jinjina mata kai yana mai duban k’ofa yanda su Baba Alhaji dasu Baffah wada suka sako kai cikin d’akin... Mamani tana ganinsu a haka sabbin hawaye suka shiga zarya a fuskarta... Haka Baba Alhaji ya duk’a yana kuma neman gafarar Mamani harmada Abbah... Allahu Akbar hawayen Mamani suka gaza tsayuwa yau ga ‘ya’yenta a had’e waje guda, gasu nan sun yafi juna, mai yafi wannan Farin ciki, ko yanzu Ubangijinta ya kirayeta ya cika mata burinta taga irin wannan rana.. Yanzu batada buri da ya wuce ta sami Mariya da Zulfa’u ta nemi nasu yafiyar...
Haka su Abbah sukaita godiyawa Hajiya Rabi kana suka d’unguma suka koma gida gaba d’aya cikeda Farin ciki... Kan kace mai labari ya zaga family Mamani ta dawo... Kowa sai murna da San Barka yake... Mamani ta nemi yafiyar Mamy dama yaranta, rayuwa ta koma kaman da harma fiyeda da, Wai zo Kaga murna wajen Raihanah da Sameer, har sai aka rasa wa yafi murna... Su Nabilah ma sunyo waya daga Abuja Khalid yace bai isa ba dole su taho Kano su gaida Mamanin Haladu....Lol

Mamani da kanta taje taiwa su Zulfah murna ta kuma nemi yafiyar Zulfah, Engr da baisan Mamani sosai ba yanata d’an mata surkunta nan ya fahimci Mamani kam babu ruwanta da wani surkunta... Ya cikata da goma na arziki harda kyautar sabuwar mota dal aka dawo da Mamani gida... Sai kuka Mamani take tana fad’in yau dik Ta dalilin Zulfa’u ta samu wannan d’aukaka... Rayuwa kenan, d’an hakin daka raina wataran shike tsone maka idanu... Dik yanda D’an adam yake kada ka rainasa Allahn da ya haliccesa shi Yasan mai ya aje wajen....

Bayan dawowar Mamani Mami Ta rok’i Abbah kan yaje ya maido da Aunty Lami, da fari yak’i yarda da hakan har saida Mamy taita masa magiya tana nuna masa yanda ya yafema kowa itama ta cancanci yafiya tinda ta gane kurenta, sannan dik Abinda ya faru muk’addari ne daga Allah, hakan tuntuni na rubuce...
Da wad’annan batu na Mamy Abbah ya yarda suka tafi har k’auyen su Aunty Lami tareda Mamy...

Aunty Lami ta rame tai bak’i ta fita hayyacinta kaman ba ita ba, zaman k’auye surfe da daka ma kawai sun isheta gashi gidansu mahaifinsu malamin zaure ne wanda bayan rasuwarsa Almajiran basu bar gidan ba sauran matan Babanta da wasu daga cikin yayyensu maza sun ci gaba da kulada almajiran dan haka wahala ce tsantsan ta tadda a wannan gida... Aiko tana ganin su Abbah haka ta duk’a ta dinga kuka tana rok’onsu yafiya musamman Mamy....

Mamy tace “Babu komai Lami Allah ya yafemu gaba d’aya, yasa wannan ya zamto wa’azi a gareki da masu hali irin naki...”
Aunty Lami sai jinjina kai take tana hawaye had’ida da kuma neman gafararsu.... Wani irin kima da darajan Mamy ne suka k’aru a idanunta.... Daga bisani suka d’unguma suka komo gida, har lokacin Aunty Lami a d’arare take....

***

A b’angaren su Zulfa’u kuwa tuni an gama processing visa d’insu, cikin kwanakin suka d’aga zuwa k’asa mai tsarki, kafin su tafi saida Engr ya kaisu duba Muhibbah gaba d’ayansu harda Zulfa’u da yaran... Muhibbah taita masa godiya tana rungumar yaranta, Ta kuma dank’a amanansu hannun Zulfa’u dan batada haufi Zulfa’u zata rik’e mata su da aminci... Haka suka tafi Muhibbah na cikeda kewarsu danma Ta soma karatun Islama a nan prison d’in, idan ka ganta ma bakace ita bace, babu shan k’waya babu ta’ammudi da miyagun k’wayoyi daga ita har Shamzy yanzu sosai suka rungumi sanin addininsu....

Sauk’arsu a k’asa mai tsarki aka wuce da Ammah asibitin ta dan dama tin suna Nigeria an riga an ida dik wani abinda za’ai.... Nan Ammah ta buk’aci Engr ya d’auki matarsa su tafi wani wajen su keb’e tinda ita a nan Gata nan ga yaran ga kuma Hajjah sannan ga Akram ma... Tana ganin zai kyau idan sukai amfani da wannan dama suka d’an tafi wani wajen kafin su koma Nigeria ya soma hidiman office... Tamkar Mahaifiyar tasa Ta shiga ransa, burinsa kenan su d’anyi amfani da wannan tsakani shida matarsa su kasance tare....
Babu wani b’ata lokaci ya sai masu tikitin k’asar Maldives, Akram shi yai masu processing komai cikeda ladabi had’ida girmamawa....
Washe gari suka d’aga zuwa k’asar Maldives..

***
MALDIVES

*Anantara Dhigu Maldives Resorts*

Ita dai tinda suka iso wannan k’asa mai d’inbin Ni’ima take jinta tamkar wani duniyar ta daban suke, Wai dama akwai irin wad’annan wajaje a fad’in duniyar nan... Kai lallai ganin wannan waje ra’il aini ya kuma sanyata tsarkake Ubangijinta a zuciyarta wanda ya k’agi halittar wannan waje da yafi dacewa da a kirasa da Aljannar duniya... Ikon Allah Wai ita Zulfa’u yau dai gata a island nan tsakiyar tsibiri abinda take gani a talabijin da hotuna yau gata cikinsa, Daidai da d’akinda take ciki tsakiyar ruwa yake, ruwanda view d’insa ma kawai kwanciyar hankali yake haifar maka had’ida wane irin natsuwa cikin zuciya.... Ta kuma juyi saman gadon da aka k’erasa da zallan itace akai masa wane irin kwalliya da shell, komai dai a wannan waje abin birgewa ne, ga wani irin ni’imtaccen iska na kad’a dik wani kafa na jikinta.... Laushin bargo da bedsheets ya kuma sanyata lumshe idanu tana sakin wane irin murmushi a hankali... Tinda ya bata kayan da zata sanya idan tai wanka bata kuma ganin gittawansa ba, tadai daure Ta kuma mik’ewa tana duban kanta jikin full length mirror dake nan cikin d’akin wanda akai masa kwalliya da shell shima.... Rigace bak’a doguwa wanda tafi kama data turawa... Ta d’an murmusa kad’an Wato yau irin shigar da yake so ya gani jikinta kenan... Wata zuciya tace “Yanayin wajen bana saka atampa bane k’ila shisa ya kawo miki wannan ki saka.... Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai gyara sumarta ta d’auresa cikin bakin mayafin rigar, ita kanta tasan babu Wai tayi kyau Masha Allah son kowa kin wanda ya rasa... Kyaun da ita kanta bata tsammaci tana da irinta ba.... Tana nan tsaye wayarta ta kuma yin k’ara... A hankali ta isa saman gadon tana duba wayar... Gabanta ne yai wani irin tsinkewa ya fad’i... ‘Mr Unknown..’ Sunan da ya soma zuwa zuciyarta kenan.... Tai saurin bud’e sak’on tana karantawa.... Gabanta ya kuma tsinkewa...
_Nasan kina son sanin ko ni wanene..._ Wannan shine sak’o na biyu da ya shigo....
Zulfa’u har ta soma tsorata tana tinanin toh ko dai gamo Tai ne... Tayi zaton wannan bawan Allah ya daina turo mata anonymous messages d’insa tin ranar aure sai kuma ga wani yau... Ta had’iyi miyau da k’yar dan bata fatan abinda zai kawo mata cikas ga wannan sabon rayuwa mai cikeda Ni’ima data tsinci kanta ciki... Bata ida tinanin ba wani sak’on ya kuma shigo mata...
_Idan har kina son sanin ko ni wanene ki biyo wannan k’ofa da kike hango beautiful ocean d’in nan daga wajen...._

Ta d’an kuma d’ago kai tana waige waige.. Text ya kuma shigo mata... Shin anya bazataje taga waye wannan bawan Allah da ya dameta ta sanar dashi Tanada aure ba, toh ya ma akai yasan tana nan... Wata zuciyar tace toh idan kuma da gaske ba mutum d’in bane fah...? Take dai taji zuciyarta tana k’arfafa mata gwiwa da tajeta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta nufo hanyar da akace tabi...
Wani ikon Allah k’aytaccen waje ta tsinci kanta wanda har saida yafi yanda Ta fito k’ayatuwa.. Tsoro ya soma cikata anya ba birnin mutanen b’oye take ba... Wai meke faruwa ne da ita...? Ta tambayi kanta tana mai kuma waige waige... Sak’on ne ya kuma shigo mata yanda yace ta juyo bayanta kad’an zata hangosa...
Gaban Zulfa’u ya tsananta fad’uwa... Da k’yar take kaikaitowa har dai ta ida jiyowa gaba d’aya yanda ta hangi wani teburi mai d’aukeda fulawowi wanda yasha tsari iyaka tsari harta su wine glass cups gasu nan a jere, saikace wacce ta fito date irin na turawa...Gabanta ya kuma tsinkewa ga wani view na rana da ya kusa fad’i daga can k’arshen teku tana hangowa... Gefe kad’an ta hangi bayansa, sanye yake

Please Login or Register in order to submit comment