Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya ba... A hankali ya mik’e ya isa cikin shagon ya tadda Magaji kana yace “Magaji kamin alfarma d’aya ka barni na kwana a shagon nan naka don bazan iya komawa gida ba....”
Magaji yace “Ka wuce haka a wajena abokina, gidanmu gidanku ne, ka shigo cikin gidanmu ka kwana har iya lokacin da kake so...”
Hafiz ya dafasa kad’an kana yace “Na gode abokina...”
Magaji ya sakar masa murmushi kafin ya janyo masa kujera ya zauna a cikin shagon....

***

Sallamanta na uku kenan a k’ofar parlorn shiru babu wanda ya amsa, kaman zata juya sai kuma wata zuciya tace ta dai tsaya na wasu dak’ik’ai ko za’a amsa sanin halin matar gidan da yanayinta...
Can jimawa kad’an saiga wata matashiyar budurwa wacce da gani kasan ‘yar aikice ta k’araso ta bud’e had’ida amsa mata sallaman tai mata izinin shigowa...
Aunty Bara’atu ta ida shigowa kana ta tambayi yarinyar ko matar gidan na nan..
Yarinyar ta amsa mata eh tana sama kana ta nufi bene kiran matar...
Kaida ganin gidan kasan anyi wasa da naira sabida tsananin tsaruwa da gidan yayi...
Bara’atu ta d’aga idanu tana kuma k’arewa gidan kallo, cikin zuciyarta take ayyana duk wannan girman gida da had’uwarsa babu magaji cikinta lokaci guda ta rintse idanunta tamkar wacce ta tuna wani abin...
Sauk’owar matar daga bene wacce nake tsammanin matar gidan ne ya sanya Aunty B saurin saita kanta had’ida mik’ewa tsaye...

Cikin taku irinta mata masu ji da kansu da isarsu matar ke takowa cikin parlorn, saida ta iso tsakiyar parlorn tana mai ci gaba da k’arewa Aunty B kallo kana tace “Bara’atu mai ya kawoki gidana... Na zaci ta maki iyaka da nan ne kaman yanda na mata iyaka da yanda nake...”

Aunty da kanta ke k’asa ta share k’wallan dake k’ok’arin kawowa idanunta kana tace “Yaya mun yini lafiya...?”
“Baki amsa min tambayata ba Bara’atu...” Matar ta kuma fad’i
Sai sannan Aunty B ta d’ago tana dubanta kana tace “Zuwa nayi na fad’a miki Ma’aruf ya dawo...!!!”


SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_



60



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



NOT EDITED





Cikin wani irin yanayi matar da Aunty B ta kirada Yaya ta d’ago tana dubanta, ta d’auki lokaci mai d’an tsawo tana duban nata kana tace “Ma’aruf...?!!”
Aunty B ta jinjina kai a hankali....
Tak’aitaccen murmushi matar tayi kana tace “Toh mai nawa ciki... Mai ya shafeni da zakizo musamman don ki sanar dani....?”
Tasan hakan ne zai iya faruwa amma batai k’asa a gwiwa ba tace “Yaya karki mance kusanki da mahaifiyarsa, ki dubi girman Allah ki mance komai ki shirya da ‘yaruwarki, ita rayuwar nan babu tabbas, yau kaine gobe ba kai ba.... Kuma nayi imani badon kin mata iyaka da gidanki ba itada zuri’arta da zaki ganta, ko baki ganta ba nayi imani zata turo ‘ya’yanta.... Yaya girma muke ba k’ank’ancewa ba don Allah mu aje komai duk wasu abubuwa da suka faru a baya mu rik’i junanmu don bamu da wanda yafi mana junanmu....”

“Kin gama.....?”
Yaya Abida tace..
Aunty B ta d’ago tana dubanta....
“Toh idan kin gama ki tashi ki fice min a gida....” Cewar Yaya Abida dake hakince saman kujera....
A hankali Aunty B ta duk’a ta d’au handbag d’inta kana ta dubi ‘yar uwar tata tace “Yayah zan wuce... Bazan gushe ba ina rok’onki kimin wannan alfarma guda d’aya....”
Yaya Abidah ta d’ago tana dubanta, Aunty B taci gaba da fad’in “Ki sassauta zuciyarki ki rungume ‘yan uwanki ki tuna bakida wanda suka fisu....” Daga haka Aunty B bata kuma cewa komai ba ta fice ta bar Yaya Abidah nan tsaye tana mai rakatada kallo har ta b’acewa ganinta....

Washe gari sassafe Nabilah ta dira gidan Aunty B, Aunty Bara’atu batai mamakin ganin Nabilar da safe ba don tasan Nabila da kafiya akan duk abinda tai niyya.... Jigum tai a d’aki tana ida shiryawa zuciyarta naci gaba da sak’e sak’en anya tayi dai dai kuwa...? Anya hakan ya dace ta biyewa Nabilah suyi tafiya bada ilimin mahaifanta ba....? Ta lumshe idanunta a hankali tana kuma tunanin lamarin, a hankali ta sauk’e ajiyan zuciya taci gaba da shirinta domin kaw alk’awari ta d’aukarwa kanta da yardar Allah Mamy da ahalinta bazsu kuma shiga k’unci ba matuk’a tana raye wannan shine dalilinta na ajiye Zulfa’u a gidanta a lokacin da suka rabu da Hafiz sannan zatai iyaka k’ok’arinta wajen ganin Mamy da Ya Abida sun shirya koda ace wannan shine abu na k’arshe da zata aiwatar a rayuwarta... Muryar Nabilah ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi... Tai saurin yafa mayafinta had’ida d’aukan jaka da mabud’an motarta kana ta fito ta iske Nabilah a parlor....
“Kinyi breakfast ne....?” Aunty B ta tambaya sanda take gyara zaman mayafinta tana mai duban kanta jikin madubin consul...
Jinjina mata kai Nabilah tai a hankali kana tace “Nayi Aunty... Ke kawai nake jira....”

Aunty B ta jinjina kai a hankali tana mai k’arewa Nabilar kallo kana tace “Nabilah are you sure of this....?”

Sauk’e ajiyan zuciya Nabila tai hawaye na k’ok’arin ciko idanunta take fad’in “Aunty this is the only way....”
Aunty B ta jinjina kai kana tace “Kinaso muje...?”
Nabila ta jinjina mata kai a hankali alamun eh...
Nan ma kad’a kai Aunty B tai kana ta kamo hannayenta tace “I’m here for you kinji koh.... Ko meye zai faru.... You have your Aunt kinji koh....”
Nabilah ta jinjina kai a hankali kana tace “Na gode Aunty....”
Aunty B ta sakar mata murmushi kana suka sa kai.....

***
Da idanu guda take k’are masa kallo yanda yake shiryawarsa cikin tsanaki, babu abinda ya canzu cikin d’abi’unsa saima k’warjini da kyau da ya k’ara mata, ita kanta ta sani tana son Ma’aruf tana tsananin k’aunar mijinta, wasu lokutan takan rasa maiyasa take masa abubuwan da take masa, kodashike abune a fili, mijinta mai son kula da tarairayane ita kuma sam bazata juri wannan ba, mijinta maison nitsartsiyar macece mai kula da duk wani nauyi da hakki na rayuwar aure da Allah ya shar’anta ga duk wata mace mai aure sauk’esu amma ita sam bazata iya sauk’e wad’annan hakkin ba ciki harda kulada yaransa da tarbiyarsu wanda yaran nan yaranta ne amma ta sani sam basu gabanta kuma bazata iya sauk’e masu hakkinsu dake kanta ba a matsayinta na mahaifiyarsu, fita yawonta da gantalinta ma bazasu barta... Mijinta mai son mace mai killace kanta a gidane kaman yanda Alk’ur’ani mai girma yace _Kuma Ku zauna cikin gidajenku kada kuke fita irin yanda jahilan farko suke fita_..... Duk wad’annan abubuwa da mijin Muhibbah keso matarshi ta kasance cikinsu sam Muhibbah ba haka take ba hasalima d’an kwanaki biyu da tayi a gidan ba tareda ta fita ba duk sai taji babu dad’i...

Mik’ewa tai zaune tana faman mutsuke idanu alamun bacci, ganin yaci gaba da sabgan dake gabansa ba tareda ya kulata ba ya sanyata mik’ewa ta tako a hankali ta tsaya bayansa, a hankali ta rungumesa ta baya had’ida d’aura hab’arta saman kafad’arsa guda tana mai kallon fuskokinsu cikin madubi....
Fuska babu walwala yake k’ok’arin kaucewa yana mai ci gaba da abinda yake, lokaci guda yake furta “I’m running late, people are waiting for me....” Ya k’arashe yana mai d’aura agogo a hannunsa....

Fuzar da iska Muhibbah tai tana mai binsa da kallo kana ta k’ak’aro murmushi, lokaci guda ta kuma takowa ta bayansa kad’an tana mai gyara masa zaman suit d’insa had’ida daidaita masa necktie d’insa.... Fuska a shagwab’e take fad’in “Bazakaje dani ba...?”
“Ba taron mata bane....”
Ya fad’i a tak’aice yana mai matsar da ita gefe had’ida d’aukan turare....
Cikin sauri ta rik’e hannun nasa ta amshi turaren tana k’ok’arin fesa masa cikin salo....
Duk abinda take kallon arziki bata ishesa ba, sauri sauri ya ida abinda yake ya fice ya barta nan tsaye....
A parlor ya tadda yaransa sunyi shirin tafiya makaranta, Najma tana hangosa ta taso a guje ta rungume tana fad’in “Daddy good morning...”
Engr ya rungumeta had’ida manna mata peck a goshi “Morning my princess....” Ya kamo hannunta suka nufi dining table din yanda sauran ‘yan uwan nata suke...
Gaba d’aya yaran gaidasa sukai fuskokinsu fal fari’a... Hakan take kasancewa da mahaifinsu sab’anin mahaifiyarsu da sam babu sabo tsakaninsu da ita....

“Daddy yau kai zaka kaimu sch....?” Hanan mai shekaru shida ta tambaya....
Shafa kanta yayi murmushi bai gushe saman fuskansa ba daidai sanda Murja ta k’araso da lunchboxes din yaran...
“Kunaso na kaiku ne...?”
Gaba d’aya yaran suka had’a baki wajen cewa eh...
Fuskarsa d’aukeda murmushi yake fad’in “Alright kowa ya gama cin abincinsa and Daddy will take you to school today...”
Yaran suka shiga murna suna tsalle musamman k’anana guda biyun, shi babban mai shekaru goma dama magana bawai ya faye yinta bane, haka nan yake tamkar wani miskili....
Harta Murja saida taji dad’i cikin ranta don sosai yaran suke bata tausayi musamman idan ta tuna cewa yaran basu nemi komai sun rasa ba face soyayyar mahaifiya...
Muhibbah kaw daga yanda take tsaye tana dubansu ta cika tayi fam, wato sabida tsaban rainin hankali itace zaice mata sauri yake kada yayi latti amma ga yaransa nan ya sakasu gaba yana biyesu k’arewarta ma cewa yayi da kansa zai kaisu makaranta, dad’i da k’arin takaicinta shine yanda daga Ma’aruf har yaransa ita d’in bata gabansu, yaran ko sallama basu mata ba suka fice wanda ta tabbata da ace ubansu ne bazasu fita basu masa sallama ba, wato ma babu wanda ya d’auketa da wani kima da daraja cikin gidan...
K’wafa tai kana ta haye sama tana neman layin Suby aminiyarta

“Hello Suby.... Nifa na gaji Wllhi na gaji da zama waje guda, kinga masu gidanma ba noticing d’ina suke ba, gaskiya ni na gaji da wannan zaman don wllhi ji nake kaman banida lafiya.....”
Daga d’aya b’angaren wacce ta kirada Suby dariya ta tintsire dashi kana tace “Toh Wai ki fito kiyi mai bayan babu business a k’asa.... Kedai kawai kiyi hak’uri na d’an lokaci ki kuma winning mutumin nan over ta haka ne kurum idan yaci zab’en nan zamu samu kasonmu, kuma kinga business d’inmu ma zata kuma bunk’asa tinda ba lallai yasan tak’amaimen kasuwancin da muke ba...”
Muhibba ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana tace “Suby bazaki gane bane akwai matsala....”
Suby ta kuma shek’ewa da dariya kana tace “K’awata nasan matsalarki bazai wuce abin ba, zan turo Jenny ta kawo maki anjima...”
Muhibbah ta murmusa kana sukai sallama...
Ta jima tana tsaye wajen kafin ta nufi bedroom d’inta...
Kai tsaye closet d’inta ta nufa ta janyo wata ‘yar drawer.... Wata ‘yar farar leda mai d’auke da k’waya ta ciro lokaci guda ta saki murmushi.... Hancinta ta toshe da yatsunta guda biyu kafin ta afa k’wayan tana mai rintse idanunta....

***

Basu sha wahalan neman gidansu Khalid ba dashike ba gida ne b’oyayye ba, tinda Nabilah ta d’aga idanu ta kalli gidan gabanta yayi mugun fad’uwa, lallai dole ma su Siyama su nemi datse tsakaninta da Khalid.... Aunty B ta dafata kad’an kana tace “Kina buk’atar na rakaki cikin gidan...?”

Murmushi ta sakarwa Aunty B tana mai girgiza kai kana tace “A’a Aunty, da kika kawoni ma kin gama min komai, this is my war ya kamata na fuskanceta ni kad’ai...”
Aunty B ta jinjina kai a hankali kana tace “Shikenan ina jiranki a nan cikin mota, I know you’re strong enough to do this alone...”

Nabilah ta fuzar da iska tana mai k’arfafawa kanta gwiwa, cikin ranta take furta “I can do this..I know I can...”


***

Fitowarsu daga masallaci Hafiz ya d’auki hanyar gida tamkar wanda ake sinkaransa don ko sallama da Magaji bai sami zarafin yi ba....
Tinda mai babur ya ijesa k’ofar gidan yaji kansa na sara masa, babu abindake azalzalarsa face tsan tsan tsanar matarsa Sawwama, komai ya shiga dawo masa, ya d’aga kai ya kuma duban k’ofar gidan, idanunsa suka sauk’a kan mota k’irar Corolla dake pake k’asar bishiyar delbejiya dake a k’ofar gidan....

***

Kubura ta dubi Nabilah daga sama har k’asa kana tace “Baiwar Allah kikace fah wajen Mai gidan kikazo...?”

Cikin dakewa Nabilah tace “Ko na sake maimaita maki ne...?”

Kubura ta murmusa kana tace “Yo abinne da mamaki wai an baima d’an kura ajiyan nama... Bama kice wajen Hajiya kikazo neman taimako ba sai kice Alhajin d’ungurungum....”

Ammi dake k’ok’arin sauk’owa daga staircase waya manne kunnenta ta katse Kubura da fad’in “ke Kubura Wai keda wayene wajen nan.....?”

Kubura ta bud’e murya tace “Ammi salon bariki nake gani, wannan mai baran Wai wajen Alhaji tazo bama wajenki ba.... Shine abin ya d’aure min kai....”

Ammi taci gaba da sauk’owa daga bene still waya manne kunnenta tana duban yarinyar dake tsaye da Kubura...

Kan Nabilah a k’asa banda bugu babu abinda k’irjinta keyi, batasan idan zata iya d’agowa ta dubi mahaifiyar Khalid ba, batasan idan zata iya ci gaba da abinda ya soma ba.......



SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_



61



*©️Sameena Aleeyou...✍🏻*

NOT EDITED





Tin daga sama har k’asa Ammi ke k’are mata kallo, still waya na manne b’angaren kunnenta na dama... Daga d’aya b’angaren shiru Baffah yai yana sauraren sautin maganganun Kubura dake tashi a wajen.....
Ammi ta k’araso har gaban Nabilah a daidai lokacinda Nabilah ta d’ago suna duban juna.....
Gaban Nabilah ya yanke ya fad’i a karo na farko....
Sosai Ammi take dubanta tana k’ok’arin tuno yanda tasan wannan fuska....
“Baiwar Allah lafiya...? Daga ina kike....? Sannan maiyasa kike neman mijina....?” Lokaci guda Ammi ta jero mata wad’annan tambayoyi....

“Wajen Daddy nazo....” Nabilah tace tana mai d’auke idanu daga duban Ammi....
Kubura taci gaba da tafe hannaye tana fad’in “Oh yau ni naga jaraba, Ammi na fad’i maki Yanzu haka irin masu neman taimakon nan ne da Daddy ke taimaka masu shine suka soma biyo shi har gida... Bani umarnin fitar da ita yanzu kiga aiki da cikawa....” Ta k’arashe tana nannad’e hannun riga tamkar wacce zata sunkuce Nabilar....
Sauk’owan Yesmin kenan daga sama cikin shirin fita da alama da Siyama take wayar cak ta tsaya tana duban yanda su Ammi ke tsaye carko carko, mamakin bai ida kama Yesmin ba saida ta hangi fuskar yarinyar dake tsaye bakin k’ofa Kubura ta mata k’ababa....

Da k’arfi Yesmin ta furta “Nabilah..!!”
Daga Ammi har Kubura harma ita kanta Nabilar d’agowa tai tana duban Yesmin dake sauk’owa daga bene... Daga d’aya b’angaren Siyama tace “Mai kikace cousin... wata Nabilah kenan....?”
Yesmin tana mai k’arasowa garesu idanunta kan Nabilah take ci gaba da fad’i cikin wayar “K’warai kuwa Cousin Nabilah’s here she’s right here in front of me.... Da alama duk wulakancin da muka mata bai isheta ba ta kawo kanta....”

Duk maganganun nan a kunnuwan Baffah... A hankali ya furta “Nabilar Khalid....!” Yai saurin bud’e murya yace “Ammi ba damuwa naji kaman kinada bak’i ki gama abinda kike sai muyi magana...”
Ammi tace “Alright Baffah I’ll get back to you...” Ta kashe wayar tana mai duban Yesmin da kyau kana tace “Explain... Wacece ita... A ina kika santa...?”

Yesmin na murmushi mai k’unshe da Allah sarki idanunta kan Nabilah take furta “Ammi wannan itace yarinyar da Khalid ya d’imauce kanta har ya sab’a umarninku for the first time in his life.... “

Ammi tace “Kina nufin kicemin wannan itace yarinyar... Kan wannan abar Khalid ya bijire mana, ya zab’i ganin k’uncinmu sama da farin cikinmu.... No wonder naga kaman nasan fuskar nata ashe a wancan video d’in na santa, yarinyar da ‘yan unguwa suka had’u suna mata wak’an Karuwa...” Ta kuma maido da dubantaga Nabilah wacce ta kasa d’ago idanunta sabida tsananin k’una da k’irjinta ke mata...
Murmushi Ammi ta saki kana taci gaba da fad’in “Aw shine kika biyoshi har gida, kika taso tin daga uwa duniya kika biyo namiji har gidansu... Eh lallai kin cika cikakkiyar kilaki...”

“Ni ba kilaki bace, kuma ni ba wajen Khalid nazo ba, na sani Khalid doesn’t live here anymore...” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya....

Kubura ta rangad’a guda tana mai tafe hannaye da salallami take furta “Yau naga salo... Ni nan ina tunanin mijin Ammi aka zo k’wacewa har gida ashe nawa mijin aka biyo.... Toh wllhi kinyi kad’an Karuwan cikin gidan ma sunyi sun k’yalesa ballanta ke da na tabbata a naira goma bazai amsheki ba....!”

Ammi ta saki baki tana duban Kubura shaye da mamaki, lallai ta yarda haukan Kubura ya fara yawa dole a nema mata taimako.... Ganin Ammi na mata wani irin duba yasata saurin yin shiru tana mai furta “Yo Ammi ai gaskiya na fad’i su karuwan cikin gidan sun san kansu....”
Yesmin da tuni ta kufula ta yo kan Kubura tana fad’in “Wa kike kira karuwa....”
“A wacce ta tsargu....” Kubura tace tana watsa mata harara....
Ammi ce ta raba tsakaninsu tana fad’in “Banison shashanci da hauka kuna jina koh....”
“Ammi shiyasa nace Kimin iyaka da wannan lunatic maid d’in....” Yesmin ta fad’i fuska a shagwab’e.....

Gajeren tsaki Ammi tayi had’ida girgiza kai kad’an don ta fara gajjiya da fad’an Kubura da Yesmin kan namijin da sam basa gabansa....Ta dubi Kubura tace “B’ace min daga nan, idan bakida aiki kije ki taya Tabawa....”
Ta maidoda dubantaga Nabilah tace “Ke! Kinajina banason salon iskanci da bariki, tun muna shaida juna ki tattari k’afafuwanki Ki bari gidan nan, sannan ki fita daga rayuwan d’ahnah for good don shi ba mijinki bane kin jini koh, kinsan hausawa suna cewa idan kunne yaji toh fah jiki ya tsira, Don haka ki rufa ma kanki asiri kibi ta k’ofan da kika shigo ki fice tun kafin a fiddaki ta wata k’ofar....”
D’agowa Nabilah tai ta dubeta kana ta kuma sadda kanta tace “Kiyi hak’uri Ammi bazan tafi ba har sai nayi magana da Daddy....”

Yesmin ta dubeta shaye da mamaki kana tace “Eh lallai... Kinji koh Ammi, kinga irin salon nata koh.... Kawai ki bani dama na fidda maki ita right this minute....”

Murmushi Ammi tai tana mai duban k’arfin hali irinta Nabilah kana tace “Baza’ai haka ba Yesmin... K’yaleta badai tace Daddy take son gani ba.... Let her come inside and wait...”
Yesmin ta dubi Ammi zatai magana... Ammi ta kashe mata idanu guda....
Lokaci guda Ammi ta sakarwa Nabilah murmushi kana tace “Ki shigo parlor ki jira Daddyn anjima kad’an zai fito daga sashensa, shigo ki zauna, Yesmin tell Kubura to serve her drink...”
Yesmin tai tsaye tana duban mamaki wa Ammi yanda ta janyo Nabilah ta zaunarta saman kujera.... Harda kunna mata tv kana tace ta saki jikinta anjima kad’an mijinta zai sauk’o....

Cikin sauri Yesmin tabi bayan Ammi, a staircase ta tari Ammi tana fad’in “Haba Haba Ammi ya zakiyi haka, ya zaki bar wannan ‘yar iskar yarinyar ta shigo cikin parlornki har ta zauna, maiyasa baki bani go ahead na fiddata ba, ita har ta isa tace Daddy tazo gani...? Ammi kuma fah kinsan I can’t stand the sight of her....”

Banda harara Ammi bata b’alla mata komai, janyo hannunta tayi suka shige d’aki kana tace “Ashe ke banza ce shashasha, banda abinki ce maki akai bansan mai nake bane, wannan shine damarmu da zamuyi amfani da ita mu rabata da Khalid har abada, na tabbata idan har muka nunawa Khalid cewa wannan yarinyar har gida take bin manyan alhazawa tunda gashi ta biyo mahaifinshi tsaf zai yarda cikakkiyar k’aruwa ce, kinga shikenan Khalid ya rabu da ita har abada, zai dawo ya bamu hak’uri ya kuma amince da zab’inmu....”
Yesmin ta zaro idanu tana duban Ammi cikeda mamaki kana ta tintsire da dariya tace “Amma Ammi ban tab’a yarda da hausar nan cewa abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi bazai hanga ba irinta yau, shikenan kuwa Ammi, Wllhi kin kawo shawari, Bara na kirawo Cousin ta baro duk abinda take tazo ayi a gabanta....

**

Tsaye Baffah yai yana dubanshi yanda ya kishingid’a saman kujera idanunsa a lumshe, tausayin abokin nasa ya cikasa, tunani yake ya sanar dashi ne koko kada ya sanar dashi, da alama Nabilar batason yasan taje gidansu, toh idan wani abin yaje ya faru fah tinda yasan ‘yan uwan Khalid da iyayensa sam basa son Nabilah hasalima she’s the reason Khalid yake cikin condition d’in da ya tsinci kansa ciki.... Toh ko dai ya fad’iwa Khalid d’in ne, maybe everything will come to an end.... Da wannan tunanin ya k’araso cikin parlorn, daga can kujeran gefen Khalid d’in ya zauna had’ida k’ura masa idanu....
Khalid ya k’yallara idanu guda yana duban Baffah, gajeren tsaki yayi kana ya gyara kwanciyarsa ya kwanta sosai cikin kujera yana mai furta “Don’t give me that look...”

Baffah ya fuzar da iska yace “Khalid you need to end this for crying out loud... Jibi fah ka duba kaga duk yanda ka wani rame, kaman ba Khalid Mainasara da na sani ba... Haba Dude just put an to this already...”

D’ago Khalid yayi yanai masa wani irin duba kana yace “Wait... Ka gaji da gani na a nan ne... Idan ka gaji da ganina ne just go straight and tell to my face, ba wai ka tsaya kana karanto min lectures d’inka da already na sani ba ka gane.... I’m fed up with you already...” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye zai nufi d’aki...
Baffah ya bud’e murya yace “Do you really want to ruin your life just because of a girl...?”

Cak Khalid ya tsaya kana ya karkato yana duban Baffah... Gajeren murmushin takaici yayi kana yace “Did you just say ruin my life..? Idan baka sani ba... It’s official, my life is actually a complete mess... So ka daina cewa zan ruining rayuwana...” Yasa kai yana mai ci gaba da tafiya..

Baffah ya kuma bud’e murya yace “Kasan cewa tazo Kaduna... Probably tana gidanku....”

Wannan karon sosai Khalid ya juyo yana dubansa, saida ya d’auki dak’ik’a guda kana yace “What do you mean...?”

Baffah ya mik’e tsaye kana yace “I mean Nabilah....”

Kallonsa Khalid yake sosai kana yace “Nabilah kuma... Mai zai kawota gidanmu for what...?”

Baffah ya d’an ciza leb’ensa yace “Khalid I’m sorry... But I told her everything... The situation you’re in right now... Inaga shiyasa tazo maybe to confront your parents....”

Girgiza kai kurum Khalid yake idanunsa suka kad’a sukai jazir ji yake tamkar ya dunk’ula hannu yayita kaiwa Baffah duka... Cikin tsananin b’acin rai ya tako gaban Baffah, yana huci yake furta “How many times do I have to tell you, I hate people intruding into my life.... Why Baffah... Maiyasa zaka sanar da ita... Akan mai...? What if they did something to her...? You know perfectly well basa sonta, they’re capable of anything...”

Baffah na b’alla masa harara yake furta “Because I cant stand seeing you like this.... I don’t want you to go astray, I don’t want you to ruin your life..”

“Just shut up..!!” Khalid ya katsesa kafin yaci gaba da furta “I don’t need your concern.... Kuma na gama zama a nan...” Yana ida fad’in haka ya nufi d’aki kaman zai tashi sama Baffah na biye dashi na kiran sunansa inaa ko sauraronsa Khalid bai tsayayi ba, tuni ya soma parking stuff d’insa....

***

Laila ta dubi Siyama a karo na biyu kana tace “Look princess I’m not saying you should leave him for good, kawai zaki rabu dashi ne na d’an wani lokaci to teach him a lesson and to let him see your worth.... Sometimes dole mu bar abinda mukeso don mu karb’awa kanmu’yanci, kan mai zakije ki zauna cikin talakawa da talauci don kawai Sameer na son zama cikin talakawa, babu dangin iya balle na uba, ya bar gidansu gidan arziki ya koma zama cikin tsiya, idan ba mugunta ba mai hakan ke nufi... Look princess men are so selfish wasu lokutan, ki baro gidanku da aikinki da gatanki da komai ki koma zaman k’unci Wai duk kan soyayya, soyayyar da rana tsaka zaki iya ganinsa da wata macen tinda shi k’ofa uku ya rage masa bayan ke, yes he has the right ya auro Uku bayan ke... while ke kuma on the other hand bakida wannan damar, ya kashe maki kariya ya hanaki aiki... Nan gaba ya auro mai zuwa office da zuba kwalliya ki dawo ‘yar kallo cikin gidanki.... Toh wllhi kiyi ma kanki fad’a tun wuri kafin lokaci ya k’ure maki....”

Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Siyama tai kana tace “Yes princess you’re absolutely right.... Ya kamata na karb’i’yancina daga wajen Sameer I can’t let him control me.... Bazan bar soyayyan da nake masa yaci galaba akaina ba.... I’ve to fight my battles....” Ta k’arashe tana mai hura hanci had’ida duban wani gefe guda....

Laila ta saki murmushi a hankali kana ta kurb’i drink... Tuni Siyama ta suri handbag d’inta sukai sallama da Laila...

****

Tsananin mamakin abinda kunnuwarsa ke sauraro masa daga cikin gidan ne ya hanasa shigewa cikin gidan, banda ele da kacaniyan mutane had’ida wak’okin ‘yan bori baka jiyo komai... Hafiz yai tsaye yana sauraron ikon Allah yanda kasan bayan gari haka gidan ya koma..... Yana nan tsaye mutanen unguwa da fitowarsu kenan daga masallaci suka k’araso sukai masa sallama, da k’yar ya iya amsa sallaman nasu... D’aya daga cikin mutanen ya bud’e murya

Please Login or Register in order to submit comment