Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kuma kai tafin hannunsa ya shafi gefen fuskarta na dama kana yace “I can’t wait for this moment to come... Ina rok’on Allah yasa Yana nan kusa...”
Su duka biyu sukai k’uri suna duban junansu na d’an wani lokaci kana Daddy yace “Ni zan wuce Kaduna, duk yanda abun ya kasance zan kiraki na sanar dake komai, for now inaso ki gama sayyayan duk wasu abubuwa da ake buk’ata,akwai number k’anwar mahaifiyar ita Nabilar da Sameer ya tura min sai ki kirata ku tsara komai ki kuma tambayeta wasu abubuwan...”
Aunty Daula ta jinjina kai tace “Shikenan, zan kirata in sha Allah sai mu tsara komai...”
Hannayensa Daddy ya bud’e mata kana yace “Come here...”
Cikeda kunya ta k’arasa ta shige cikin jikinsa... Suka k’ank’ame juna tamkar su dawwama a haka ba tareda wani abin ya gitta tsakaninsu ba, haka Aunty Daula ta rabu da mijin nata cikeda bege da alhini...

***

Gaba d’aya yau d’in Yusrah bata gane kanta ba, ta kuma zama wata sukuku da ita haka nan, har suka fito daga second class d’in tana nan haka sukuku, babu wani abinda ta fahimta, ganin abin take tamkar a mafarki Wai ita ake batun aurensu da Khalid kuma har an saka rana lokaci guda dana Yayanta Ma’aruf, abinda yafi bata mamaki shine tinda akai maganar auren Khalid bai nemeta ba, bai kuma sanar da ita komai ba.. Mai hakan yake nufi...? Ta lumshe idanunta a hankali tana mai zama bisa carpet d’in masallacin..
Yusrah da tuni ta d’auro alwala zama tai gefenta tana zira safarta dara cire sanda zatai alwala lokaci guda take maganawa Nabilar... Ganin hankalin Nabilah bai tareda ita ya sanyata d’an dungurinta kana tace “Ke Wai meyene haka, tin safe kike haka nan... Wai meke faruwa ne, kinga d’azu a class k’iris ya rage wannan d’an rashin mutuncin bai koreki daga ajinsa ba, wai dan Allah meke damunki....?”

Idanu Nabilah ta zuba mata kana ta sauk’e ajiyan zuciya kad’an tace “Wai aurena ake shirye shirye... Could you imagine...”
“No.... Are you serious...!” Yusrah tace sanda take mik’ewa tsaye cikeda murna harda sakin k’aran murna gaba d’aya ta mance masallaci suke har saida Nabilar ta janyota had’ida d’aka mata duka tace “Ke bafah a class kike ba....”
Yusrah ta zauna tana mai ci gaba da fad’in “Ke Wai da gaske kike....? Aure with who....?” Lokaci guda kuma taci gaba da murmushi tana nunata da d’an yatsa take fad’in “Wllhi da shine... I’m certain dashi ne.... Haladu na Mamani... Wayyo angon teddy bear... Allah yayi, wllhi dama kunyi masifar dacewa...”
D’an tsuka Nabila tai kana tace “Bansan misa Abbah ke hanzarin ya aurar dani ba saikace na tare masa wani abin...Kuma shi d’an rainin hankalin ko wayarsa ban sake ji ba ko ma waye zai jida kai oho....” Tai maganar cikin fad’a...
Yusrah na murmushi ta dafata kana tace “Kan ango yayi zafi toh ki kirasa kiji lafiyarsa mana....”
Wani uwar hararanda Nabila ta b’alla mata ya sanyata had’iye sauran zancen... “Kar Allah sa yayi lafia idan sai na kirasa, kema kinsan idan za’a shekara a haka bazan kirasa ba, kuma bazan nuna masa nasan komai gameda batun auren ba... Ke ni haushi ma yake ban wllhi...” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye da zummar d’auro alwala... Yusrah ta murmusa tace “Ah lallai na yarda abin yazo... Allah huci ran Amarya...”
Harara Nabilah ta galla mata ba tareda ta kuma cewa komai ba don harga Allah wani irin mugun haushin Khalid d’in takeji...

Koda ta koma gida ma Mamy da Aunty B ta tadda nan suna zancen, fuska a tamke ta gaidasu don gaba d’aya har mutanen gidan nasu haushi suke bata, ji take kaman ta nufi parlorn Abbah ta sanar dashi cewa itafah bata amsa auren Khalid ba toh amma rashin kunyar nata baikai nan ba, Koda ta iska Marliya a d’aki tsiya ta dinga mata musamman data fahimci ko labarin Bikin bata k’aunar ayi...
A can parlor kuwa Aunty Daula ce ta kirawo layin Aunty B Dan su samu su tattauna maganar kawo lefe da sauransu...
Da sallama Aunty Daula ta soma cikin siriryar muryarta mai dad’in saurare... Wani irin fad’uwan gaba Aunty Bara’atu ta tsinci kanta ciki ba tareda sanin dalili ba......


SameenaAleeyou 📚



*INDA RAI*
_................DA RABO_



*81*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Sun ida wayar sun samu matsaya kan cewa ranan biki ma’ana ranan d’aurin aure sai su taho da lefen gaba d’aya, wani ikon Allah harta Mamy ma wani irin yanayi ne mai wuyan fasaltuwa ta tsinci kanta ciki sanda tai maganada abokiyar zaman mamar Khalid, muryarta baida maraba data marigayiya mahaifiyarsu, tamkar marigayiyace ke magana haka nan sukaji sautin muryar...
Aunty B ta numfasa ta dubi Mamy tace “Muryar matar nan sai ya min kaman nasan mai irinta amma na kasa gane ina san mai irin muryar...”
Sauk’e nannuyan ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “Muryar Hajja Mama naji a tattareda matar can... Babu abinda ya raba muryarta data mahaifiyarmu....”
Numfasawa Aunty Bara’atu tai kana tace “Allah mai iko, shisa na kasa gane ina nasan mai irin muryar ashe dai irin muryar Mama Hajja gareta, kinsan ni ban wani san Mama Hajja sosai ba ina k’arama Allah yai mata rasuwa....”
Take fuskar Mamy ya soma sauyawa, abubuwan da suka faru a wancan shekarun suka shiga dawo mata, k’walla masu zafin gaske suka ciko idanunta, dafa hannayenta Aunty B tai kaman zatace wani abu sai kuma ta kasa don ko shakka babu dukda juriya irin tata itama d’in sai ta kasa magana, zuciyarta tai rauni sosai, a hankali ta mik’e ta nufi waje ba tareda ta iya furta koda kalma ba....
Aunty Lami dake lab’e tana dubansu, murmushi ta saki a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta “Muddin Aminiyar Sirri tana tsakani bazaku tab’a kasancewa cikin farin ciki ba koda kuwa zaku nunawa duniya cewa cikin Farin ciki kuke, can a k’asar zuciyarku bazai kasance haka ba domin kaw wata gyambo ce da batada magani can k’asar zukatanku...” Ta kuma murmusawa kafin ta juya sad’af sad’af ta koma sashenta...

***

Washe gari ta kama juma’a, tafe suke itada Atika a farfajiyan ofishin nasu, fitowarsu kenan daga d’akin gudanar da shirye shirye, ga tsananin rana da ake kwand’arawa... A gajjiye suka iso d’akin hutun nasu had’ida zubewa saman kujeru a gajjiye.... Atika ta rage mayafinta tana mai gaida Aunty Zilai colleague d’insu dake shirin fita daga d’akin sai zolayarsu take musamman Zulfa’u dashike Aunty Zilai mace ce mai barkwanci da son mutane...
Sauk’e ajiyan zuciya Zulfah tai sanda d’akin ya rage saura su biyu tana mai fifita da takardan dake hannunta a hankali...
Gyara zama Atika tai had’ida tsare k’awar tata da idanu.... D’an dubanta Zulfa’u tai kana tace “Ke kuma fah, wannan kallon na menene... Meke faruwa?”
Atika ta d’an murmusa kad’an kana tace “Ai ke zan tambaya meke faruwa..? Irin wannan ajiyan zuciya da kiketa faman sauk’ewa akai akai tin muna hanya, kodai kiran manager d’in ne bakiso zuwa ba... Ni bakima sanar dani mi ya faru ba... Don’t tell me kin sauya ra’ayi dashi za’ai...?”
Gajeren tsuka Zulfa’u tai kana tace “Ke ai kinga matsalarki kenan, you talk too much, har mutum ya rasa wanne zai amsa miki....”
Atika ta d’an dara kad’an “Zulfa’u mai farin jini mai masoya... Nidai banga aibun Akram ba kuma shima Manager baida wani aibu wllhi, matarsa ma mutuniyar arziki ce takanzo gidan radio d’in nan kwanakin baya, very simple and friendly wllhi...”
Harara Zulfah ta galla mata kana tace “Bazakiyi shaidan mace akan kishi ba, kinsan ance kumallon mata, kibar mace akan mijinta, duk kyaun halinta da kirkinta dole tai kishin abinda take so, ke ni wai ce miki nayi ina sonsa ne ma... Wllhi Atika ni dik kin isheni bari Oga Ameer ya shigo na kaiki sammaci kotunsa....”
Atika ta dara kad’an kana tace “Aunty Zulai ma tayi ta barni, randa dik bana station d’in nan sai kunyi kewata... Kinga tashi mu samu muyi sallah mu koma kafin d’an nacin nan Ameer ya soma kirana, sam banson a had’ani program dashi Wllhi, fidda ficce ne dashi kaman mace...”
Zulfah ta d’an dara tana mai fad’in “Ai Wllhi babu maganin surutun nan naki irin Ameer, jekiyo alwalwa ni na mik’a nawa tintini...” Ta k’arashe tana mai kurb’an bottle water dake rik’e hannunta...
“Aw shine na biyeki naketa zuba, ashe kin riga liman tintini, ai sai kimin bayani...” Tai maganar tana mai d’an jan skirt d’inta sama kad’an, kana ta nufi d’auro alwala...
Tab’e baki kad’an Zulfah tai murmushi saman fuskarta take furta “Ke dai kika sani kuma, uwar ‘yan zuba...”
Wani ajiyan zuciyar ta kuma sauk’ewa tana tunanin encounter da jiya ta samu da Hafiz, ta tina abinda ya fad’i mata cewa bazata tsere masa ba dik rintsi sai ta dawo gareshi, he would make sure of that, ita d’in tasa ce shi kad’ai and no one else... Fuzar da iska mai d’umi tai a hankali, daidai nan wayarta ta soma ringing.... Takai dubantaga wayar dake aje saman table, lamba ce babu suna, ta d’an d’auki lokaci tana duban lambar har saida ta kusan tsinkewa kana ta d’aga da sallama... Shiru ba’a ce mata komai daga d’aya b’angaren ba, ta kuma yin sallama a karo na biyu nan ma shiru ba’ace komai ba, toh waye wannan mai kiranta yai shiru, tin kwanaki hakan ke faruwa da ita tin tana gidan Aunty Bara’atu, sai a kirata ai shiru kuma kaman da different lines ake mata hakan, da ace da layi guda ne tabbas da tai noticing layin ta daina d’agawa... D’an tab’e baki tai kana ta katse kiran tana mai addu’an neman tsari daga duk mai nemanta da sharri cikin zuciyarta.... Katse kiran keda wuya taji sautin shigowar message a inbox d’inta, saurin bud’ewa tai da niyyan karance sak’on, saidai abinda ta gani cikin sak’on ya bala’in d’aure mata kai had’ida bata mamaki...
_Sallamarki kad’ai ta wadatarda zuciyar dake k’ishin ruwan sauraren muryarki_
Ta karance sak’on yafi sau abinda yafi, ta lura dik ranar da ba itace on duty na gudanar da shirin da take yi ba sai mai kiran nata ya kirata a ranan, dik randa itace da duty ta gudanarda program toh ko shakka babu mai kiran nata bazai kira ba... Toh waye wannan...? Tambayar daya tsaya mata a Rai, a haka Atika ta k’araso ta sameta, bata b’oyewa Atika komai ba harta sak’on saida ta nuna mata...
Atika ma sosai abin ya bata mamaki, Toh ko waye shi kuma wannan sai Allah.... Dafa Zulfa’u Atika tai kana tace “Karkisa komai ma ranki k’awata, ci gaba da fawwalla wa Allah lamuranki da sannu zai rik’i ragamar al’amranki... Ki kwantar da hankalinki kinji koh... Dikda bamusan wanene wannan Mr Unknown d’in ba shima ki sakashi cikin jerin masu neman aurenki wa ya sani ko da Mr Unknown za’ai...” Ta k’arashe cikeda shak’iyanci....
Zulfah ta galla mata harara kana tace “Ai ke matsalarki kenan komai sai kin sako wasa ciki, wllhi dikdai wanda ya zamto mijinki nada aiki, ni ki tashi muje kafin su soma damun mu da waya...” Ta k’arashe tana gyara zaman mayafinta had’ida mik’ewa tsaye...
Dariya Atika keyi suna tafe tana kuma zolayarta da *Mr Unknown*
A haka dai har ranar ta k’are masu tinanin sak’o da wayar Mr Unknown kaman yanda suka saka mashi itada Atika bai k’yaleta ba... A hanya suna tafe suna neman adaidaita Manager ya k’araso, babu yanda baiyi ba ya rage masu hanya atafau Zulfa’u tak’i ala dole Manager ya k’yalesu badon yaso ba, haka Atika ta dinga mata mita a hanya.... Zulfah dai cewa tai taji amma wllhi bazasu shiga motar Manager ba... Kaman daga sama sai ganin Hafiz sukai gabansu tamkar wanda aka jefo... Take wutan fuskar Zulfa’u ya d’auke gaba d’aya, Atikar ma had’e rai tai tana watsa masa muguwar kallo....
Gaban Zulfa’u yaja ya tsaya yana wani huci shi kad’ai “Baba Alhaji ya sanar dani yanda sukaida Abbah... Zulfah kar mu bawa iyayenmu wahala, lokaci yayi da zaki daina wannan game d’in naki ki dawo gidan mijinki....” Kaman jira Atika take nan ya katsesa da fad’in “Wane mijin...? Ko tayi aure ne ban sani ba... Ko haka shi Baba Alhajin yace maka...?”
Da tsananin mamaki ya kaikaito yana duban Atika, lokaci guda ya d’aura hannayensa saman kunkuminsa yana k’are mata duba ta wulak’anci “Ke kuma wacece da ina magana da matata zaki tsoma baki... How dare you..?!”
Atika kaw dikda k’irjinta dake bugawa bata fasa aika masa harara ba tana fad’in “Ni ce bakinta idan ita bazata bud’e baki ta saka ka a yanda ya dace dakai ba... Ka fitar hark’arta ka daina wahalar da iyayenka don Zulfa’u ta maka wuya wllhi, ta riga tai maka nisa, nisarda har abada bazaka kuma hangota ba...”
“Ke...!!” Ya fad’i cikeda mamaki yana mai matsowa kusanta, daidai lokacin Zulfa’u ta shiga tsakaninsu, har lokacin fuskarta a tamke yake... “Ya Hafiz banson sauran mutuncin da nake ganinka dashi ya k’are, kaiwa Allah ka fita hark’ata ko ba don komai ba ko dan darajan Khausar dake kwance k’asa...!”
Mamaki ya cika Hafiz, bai daina huci yana duban Zulfah ba, fad’i yake “Ni kike cewa na fita hark’arki Zulfah... Kinajin abinda kike fad’i kuwa... Ni Hafiz kike cema na fita hark’arki... Toh waye kike so ki aura.. Wancan d’an iska karen farautar ‘yan siyasan ko kuwa wannan manemin matan banzan manager d’in naku kike so... Tell me waye kike so cikinsu...”
“Kan hanya muke Ya Hafiz, zaka iya adana rashin hankalin naka har mu bar bakin kwalta?...”. Bata kai aya ba ya d’aga hannu da niyyan kai mata mari yake fad’in “Ke ni kike fad’iwa magana haka saikace wani sa’arki....!”
Bai ankara ba sai ji yai an damk’e hannunsa ya gagara koda motsata.... Gaba d’aya suka kai dubansu gareshi don suma kansu basuji zuwan nasa ba....
Cikin dakekkiyar murya Akram Ke fad’in “If you dare lay a finger on her, zan nuna maka akwai banbanci tsakanin namijin K’warai da kuma namijin da ya rako mata duniya....”
Magaji dake gefe sai sannan ya k’araso yana janye Hafiz yake baiwa su Zulfa’u da Akram hak’uri.. Yana jan Hafiz d’in yake ci gaba da fad’in “Da ace nasan rashin daraja zakazo yi wllhi ban kawoka ba, Dan Allah kuyi hak’uri... Zulfa’u Kiyi hak’uri, laifina ne dana kawosa, bansan abinda zaizo miki ba kenan... A kullum nuna mana yake ya canza bansan har yanzu yana nan da halinsa ba... Kuyi hak’uri Dan Allah..”
Fincika Hafiz yai yana fad’in “Sai wani basu hak’uri kake saikace an masu wani abin... Baka ganine I’m the real victim here, wannan d’an iskan d’an siyasan shi yake hure mata kunne, kuma Zulfa’u k’anwata ce zan iya hukuntata a ko ina a kuma koda yaushe...”
Ya kuma fincika ya tako gaban Akram yana ci gaba da huci yake fad’in “Bari kaji na fad’a maka, ka rubuta ka ajiye kai Karen farautan ‘yan siyasa... Zaka iya hure mata kunne ta saurareka amma na sani kud’inka bazai tab’a sayan soyayyar Zulfa’u ba don abin duniya bai rufe mata ido ba ni zan baka shaida akan haka... Amma ka sani abinda har ka mutu bazaka tab’a samu daga gareta ba...” Yai wata murmushi har lokacin fuskarsa dab dana Akram kana yaci gaba da fad’in “I’m her first husband her first love... Na saka gudan jinina cikin jikinta tai wata tara ta fito duniya ta kuma raineta... Kar ka mance sunce da tsohuwar zuma ake magani...”
Murmushi da gefen baki kurum Akram keyi kana yace “Duk abinda ka fad’i are now in the past, and I promise you gabanta zaifi bayanta kyau, ka rubuta ka ajiye....!”Ya k’arashe maganar yana mai murmusawa cikeda k’asaita, k’asa k’asa suke maganar don tuni Yusuf ya bud’ewa su Zulfah da Atika mota sun shige...
Hafiz da zuciyarsa ke tsananin masa d’aci ya yunk’ura zai kai damk’awa Akram... Akram ya kuma gyara tsayuwarsa kana yace “And one more thing, kar ka kuskura ko labari na sake jin kana harassing d’inta,... Idan ba haka ba...?” Ya kuma yin wata murmushi kana yasa hannu ya d’an bubbuga kafad’an Hafiz yace “I’ll forget kaida ita kun had’a jini...” Daga haka sa kai yayi ya nufi mota...
Hafiz naci gaba da huci ya shiga bibbige yanda Akram ya dafasa... Magaji na janyoshi yana wani doguwa yake fad’in “Toh mai zaka min, ‘yan dabanku na siyasa zaka turo min ko mene... Kai naci uwarka a bariki barikaji mu mai license mukai...”
Dafasa Magaji yai yana mai ci gaba da sababi kana Magaji yace “Yanzu kuma da waye kake wai, baka ganin yayi gaba ne ya Barka da k’ura.... Abokina magana ta gaskiya lokaci yayi da zaka daina wannan haukar taka kaje gida ka rungumi Sawwamarka ku sasanta kuyi zaman lafiya, ka k’yale Zulfa’u ta auri wanda take so...” Ya k’arashe maganar yana k’unshe dariyarsa
Harara Hafiz ya galla masa kana yace “Ai na jima da sanin kaima hassadar dawowar matata kake min, kuma wllhi duk sai na baku mamaki sai na dawo da matata gareni... Wannan d’an siyasan da ‘yan daba yake tak’ama toh baisan da wa yake takara ba, zan nuna masa neman aure ba takaran kujeran mulki bane da ake saya da tsabar kud’i...”
Magaji na murmushi yake fad’in “Shima soyayyar akwai wanda ake saye da kud’i sai kai hattara...”
Hafiz na ci gaba da watsa masa harara yake fad’in “Wllhi banda Zulfa’u banida haufi akanta...” Yai murmushi yana mai shafa hab’arsa kad’an kana yace “Zan b’ullo masa ta yanda bai tsammani ba, badai gadaransa ‘yaniskan gari bane... Toh mu zuba nida shi... Sawwama...!” Yayi wata murmushi yana mai duban Magaji da bai fahimci nufinsa ba... Dafa Magani yai kad’an kana yace “Zata min amfani abokina... Tada babur muje kaji...” Shi kad’ai sai sakin murmushi yake yana ayyana yanda plan d’insa zatai aiki....
Magaji dai girgiza kai kawai yai kana ya tada mashin d’insa yana fad’in “Allah ya kyauta...”

***
“Bazan barta ta koma hannun wannan Animal d’in ba Yusuf... I must do something, ai kaji abinda yace, mahaifinsa Ke nuna iko akanta, I know Zulfa’u, nasan akwai abinda Ke holding d’inta back shisa ta kasa barina na turo... Amma wannan karon zan yi iyaka k’ok’arina naga ta bari iyaye Sun shiga maganan once and for all... She’s not safe da wannan lunatic d’inba tareda ita, d’an uwanta ne zai iya kasancewa da ita a koda yaushe... I really need to protect her... Bazan barta da wannan mahaukacin around ba...” Ya k’arashe cikin tsanin nuna damuwa yana mai zagaye parlorn...
Yusuf ya nusa kad’an kana yace “Toh miye abinyi...?”
Wani duba kurum Akram yai masa ba tareda cewa komai ba kana zira hannayensa cikin aljihu...

***
A can gidan su Zulfan ma itada Atika k’ulewa sukai k’uryar d’aki...
Atika ta rapka uban tagumi tana dubanta “Toh ko Aunty B zamu sanarwa, magana ta gaskiya Zulfah Hafiz baida hankali, kar watarana ya miki wani abin kinga yau k’iris ya rage bai mareki bakin kwalta ba, badon Allah ya kawosu Akram ba da bansan ya abin zai kasance ba... Wllhi nidai a nawa shawarin tun wuri gwara ki tsaida miji kafin wannan Baba Alhajin ya kuma zancen maidaki gidan Hafiz...” Ta k’arashe tana mai tab’e baki...
Siririyar iska Zulfah ta fuzar had’ida sauk’e gajeriyar ajiyan zuciya kana tace “Karkiceda Aunty Bara’atu komai, kinsan halinta da d’aukan abu da zafi yanzu sai taje har gidan Hajiya ta taka ma iyayen Ya Hafiz birki, shi kuma Baba Alhaji ba bari zai ba har gida zaizo ya sami Abbah ya d’aga mar hankali a banza... Kawai ki k’yaleni I can handle him...”
Atika dai dubanta kurum take baki a tab’e kaman daga sama suka jiyo ringing d’in wayar Zulfa’u ba kowa ke kira ba illa Akram...

***


KADUNA


Nik’i nik’i take shigowa da akwatin kayan nata sai faman haki take dan tin daga harabar gidan driver ya ije mata, Kubura dake gefen Ostriches tana jefa masu abinci sai cazgan dariyar Yesmin take tana ayyanawa cikin zuciyarta “Madalla Allah shi k’ara...” Ta kuma tintsirewa da dariya tana kuma jefa ma dababbobin abinci, sai Yesmin ta d’ago kai tana harararta sai Kubura tai kaman batasan da isowar nata ba... Yesmin tai k’wafa tana mai ci gaba da jan luggage d’inta....
Cikan murya kaman ta mai wak’a Kubura ke jifarta da habaici sanda ta iso daidai yanda take “Mutum yace bai yinka bai sonka, sai ka gane ka kama kanka... Shidai cusa kai babu k’warjini babban yawa ne... Anyiriri K angon K Khalid angon Kubura kana yafasu muna jin dad’i....”
Yesmin tai birki tana bintada kallon mamaki “Ke da waye kike...?”
Kubura ta shiga waige waige tamkar mai duba wani abin, Yesmin data dad’a k’uluwa tace “Dake nake k’aramar maras kunya, tsaban kin rainani kina ganina da kaya bakisan kizo ki amsa ba sabida kin sami d’aurin gindi daga wajen Ammi koh...?”
Dariyar rainin hankali wannan karon Kubura tai kana tace “Toh wama yasan da zuwan naki, ai ce nake dagani sai dababbobin nan ne a wajen nan...”
Yesmin ta kuma harzuk’owa tana fad’in “Ke ni kike kira dabba...?”
Kubura ta Kuma murmusawa tana wani jijjiga kana tace “Wlhi ba’a bakina kikaji ba...” Tayo kanta gadan gadan a daidai sanda motar Siyama ta sako hanci....
Tana ida parking suka fito itada Laila, dan yanzu kullum Lailar na lik’eda ita...
A guje Kubura ta tafi tana fad’ida Siyama “Oyoyo Aunty na sannu da dawowa..” Ta k’arashe tana amsar handbag d’in Siyamar...
Harara Siyama ta galla mata kana tace “Saikac banga rashin kunyar da kike tsulawa Yesmin ba, kin wani kwaso gudu kin taho nan...”
Yesmin tace “Wllhi cousin yarinyar nan d’aurin gindi ta samu daga wajen Ammi shisa take fetsararta san ranta, wai harda kirana dabba kiji fah...”
Kubura baki a ture tace “Wllhi Aunty Siyama ni bance mata dabba ba, aidai a bakinta kikaji...” Ta k’arashe tana juya idanu...
Girgiza kai kurum Siyama tai kana tace “Bani jakata ki d’auki jakan kayanta ki shigar mata...”
Kubura ta kuma b’ara fuska tace “Kut Aunty gani fah wannan tilin kayan ina zan iya...” Kallon da Siyama ta watsa mata ya sanyata d’aukan ta nufi cikin gida tana mai watsawa Yesmin muguwar kallo...
Siyama ya maido da dubantaga Yesmin kana tace “Wai dawowa kikai ne...? I thought Aunty tace sai bayan biki keda gidan nan...”
Yesmin tai kicin kicin da fuska tace “Wllhi bazan iya va cousin, I’m dying to see my Kay, bazan iya kwanakin nan ban ganshi ba...” Daidai sanda idanunta suka sauk’a kansa ya fito daga sashensa waya manne kunnensa, yana sanye cikin shiga ta k’anan kaya Red shirt da yayi tsananin fito da kyan fatarsa, gaban rigar an rubuta _Mango_ da ruwan zinari sai faded jeans, k’afafunsa sanye suke cikin takalmi k’irar sandals kalan bak’i.. Ya mata kyau matuk’a wanda har su Siyama da Laila suka shige cikin gida bata fahimci hakan ba....
Kaman wanda akace ya juya ya hangota ta kafa masa idanu tamkar tsohuwar mayya....



SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_



*82*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Cikin ranshi yake furta wannan yarinyar idan mayyace ta kama mutum toh harta b’argon dake cikin k’ashinsa sai ta lashe.... Kaman daga sama ya jiyo muryarta tana fad’in “My Kay badai fita zakai ba...?”
Mamaki ya hanasa furta komai, Yesmin ta d’an murmusa a hankali tana juya idanu kana tace “Yi hak’uri ko gaisawa bamuyi ba na tsareka da tambaya....”
Batakai aya ba ya katseta “Ke wai ke wata irin mayyace... Wai tsaya ma what’s your class of degree....?”
Ta dubesa da mamaki sai kuma ta murmusa ta mance tambayar da ya mata ta farko saita biyun take yunk’urin amsa masa “I graduated with second class upper...Ashe fah bakaje grad d’ina ba su Ammi ne sukaje....”Tai maganar tana kuma yauk’i had’ida juya idanu....
Gajeren murmushi yai wacce tafi kama data takaici kana yace “Aka sai maki result dai, don a ajin dak’ik’ai ban tab’a cin karo da babbar dak’ik’iya irinki ba, da kina gane karatu kaman yanda kikace da baki tsaya b’ata lokacinki wajen mutumin da sam baisan kinayi ba... And let me remind you this... Wllhi wllhi... Kinji na miki rantsuwar musulmi, kika kuskura kika sake ki yarda aka aura miki ni Khalid Mainasara a matsayin miji, sai kinyi nadamar da baki tab’a irinta ba tinda kika fad’o duniya.... So advisably ki sami Ammi tinda gaki nan Allah ya kawoki ko nace nacinki ya dawo dake, ki rok’eta ta taimake ki ta rufa miki asiri ta janye wannan auren shiriritan da take yunk’urin had’awa... Dan wllhi kika sake kika yarda kika biye mata akai wannan auren, na miki alk’awarin ganin dark side d’ina da duk duniyar nan babu wanda ya tab’a ganin sa.... It’s a promise...!” Yana ida fad’in haka bai jira cewarta ba yasa kai yai ficewarsa yana kuma making call....
Yesmin tabisa da kallo hawaye tab idanunta, wannan wulak’anci na Khalid ya isheta, inama zata iya ciresa cikin zuciyarta da

Please Login or Register in order to submit comment