Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaga dole na damu....”

Murmushi mai bayyana hak’wara yayi wanda yafi kama da dariya kana ya ciro wata k’aramar magnet cikin aljihun gaban rigarsa kafin ya janyo kujeran gefensa ya manna magnet din jiki kana ya d’ago ya dubeta itad’inma shi take duba...

Sameer yace “Kinga wani space between magnet d’in nan da k’arfen nan...?”

Girgiza masa kai tayi alamun a’a...

Ya d’an murmusa kafin yace “Well, yanda kikaga babu space sun manne da juna toh haka muke Partner, babu space d’in wata so ki kwantar da hankalinki kece Partner d’ina ta har abada har na koma ga ubangijina kinji koh....”

Hawayen da take mak’alewa suka soma zubowa, cikin sauri ta tashi ta isa kujeransa ta rungumesa.. Bata damu da sauran jama’an dake cikin restaurant d’in ba, Sameer d’inta shine mafarkin kowata d’iya mace...

Cikin muryar kuka take furta “I love you Partner.... I love you so much....”

Hannayensa ya had’e ya rungumeta kana yace “I love you more.....”

Ya jima yana tsaye yana dubansu zuciyarsa bata daina masa zogi da k’una ba, jijiyoyin jikinsa sun tashi hakan nan idanunsa sunyi jazir alamun k’unan rai... Cikin sauri ya fice daga restaurant d’in ya koma motarsa....

Wasu irin hawaye masu tsananin zafi suna gangaro masa k’irjinsa na kuma masa zafi idan ya tuna kalan soyayyarsu da ya gaza samun irinta a rayuwarsa....

Cikin sauri tamkar zai tashi sama ya finciki motar yana ayyana ta yanda zai tarwatsa wannan soyayya ta ko wata hanyace.....

***


Har ta iso unguwarsu bata daina ganin ana mammane garin da sababbin posters na Mutallab ba da alama rally d’insa za’ayi, har cikin ranta tanaso taga wannan rally d’in don ko babu komai itama tana d’aya daga cikin magoya bayan Mutallab, tabbas mutuwace kawai zata hanata fita ranar zab’e ta kad’a masa k’uri’a... Toh ya akayi bataji sanarwan wannan rally da magoya bayan Mutallab zasu gudanar ba domin kuwa sam shirye shiryen magoya bayansa a gidan Radio ta Magamar ‘yanci basa wuceta... Aiko bata ida tunaninba motoci suka soma shawagi suna wucewa sautin wak’ar MUTALLB na tashi cikinsu, abunka da mutum mai matasa yawa anyi tururuwarsu haka suke wucewa, wasu a babura wasu a motoci wasu kuwa a keke napep sai sannan ta lura keke napep d’in data shigama manne yake da hoton Mutallab, aiko wannan mutumi yabi ayarin mutane, tsaban farin ciki da Zulfah ke ciki batamayi la’akari da cewa ayarin masu rally suke biba domin kuwa har an shige k’ofar gidanta bata ankaraba....

Daga can kuwa wata hamshak’iyar Jeep ta doso wanda ko shakka babu contestant d’in ne cikinta, haba nan fah matasa suka kuma haukacewa... K’arshe me napep kasheta yayi ya fice a guje rik’eda poster yana fad’iwa Zulfah “Baiwar Allah kiyi hak’uri wllhi ga MUTALLAB....”

Ai Zulfah ma sai ta tsinci kanta da fitowa daga cikin adaidaita tana raba idanu ta ina Mutallab d’in yake...

Jama’a kaman anyi kasuwansu, maza da mata daga cikin gidajensu sai tururwan fitowa suke yara da manya.....

Bata iya hangoshi ba dukda ya fito da kansa ta saman motar saidai fararen hannayensa da tayita hangowa yana d’agawa mutane hannu... Babban abinda yafi burgeta ya kusan sakata kuka shine yanda taga mutane kaman yashi sun fito domin nuna goyon bayansu ga shugaban da ake masa tsammanin adalci...

Fitowarsa kenan daga kasuwa takaicin ‘yan rally d’in duk ya ishesa sabida sam ya tsani mutumin da ake rally d’in dominsa, sai tsaki yake yana kutsawa yana addu’an kada a k’ok’e masa sabuwar kimko d’insa da Alhaji ya basa.... Kaman ance ya kalli b’arin hagu ya hangota tsaye cikin ‘yan kallo.....



SameenaAleeyou 📚
[25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_................DA RABO_




*08*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*





Idan ran Hafiz yayi dubu ya b’aci, wane iskanci Zulfah keyi cikin dandatson ‘yan siyasa..? Sabida tsabagen rashin mutunci har nan ta fito kallon taron ‘yan siyasa.... Ya kad’a kansa ba tareda ya bari ta hangosa ba sannan yasa kai yayi shigewarsa...

Bayan wasu mintoci ta tsinci kanta tana mai fad’uwar gaba, innalillahi sai sannan tayi noticing layin da mai adaidaita ya ajeta bayan dandatson mutane sun d’an ragu... Hankali tashe ta koma jikin adaidaitan tana neman maishi ta bashi kud’insa koda da k’afane ta gangara tinda ba wani rata sosai bane tsakanin layin da nasu layin....

Mai adaidaita yana fad’in ta tsaya ya maidata inaa ko kulasa batayi tasa a fujajan ta shige ga lokaci da ya d’anja ba tareda tayi la’akari ba...

Har ta isa gida k’irjinta bai daina bugawa ba, hango abin hawansa da tayi ya kuma tsinkar mata da gaba, k’ila tuntuni ya dawo gidan bata nan bacin minti shabiyar kacal ya d’ibar mata taje ta baiwa Hajiyarsa hak’uri ta dawo gida tayi abincin rana....

A hankali Zulfah ta lumshe idanunta tana ambato sunan Allah cikin zuciyarta, tsaye tayi a farandar ta kasa dosa k’ofan parlornta, saida ta kwashi tsawon wasu mintoci a wajen tana zullumi kafin tayi k’arfin halin yin sallama a k’ofar don tasan tabbas jimawarta tsaye a wajen k’arin laifi ne....

Shiru ba’a masa mata sallamarta ba, tayi tsammanin hakan musamman data hango shi zaune a doguwar kujera fuskarsa a murtuke sai faman kad’a k’afa yake wanda d’abi’arsace idan ransa ya matuk’ar b’aci...

Zulfah tasha jinin jikinta, ta rasa da wanne zata fara, gaisheshi zatayi ko kuwa hak’uri zata basa ko kitchen zata fad’a ta soma girki, gaba d’aya sai ta nemi fushin da takedashi gameda abinda Sawwama da k’awayenta suka mata....

Cikin ‘yan kame kame ta soma fad’in “Ashe ka... dawo gida.... Sannu da dawowa barin.... Barin k’arasa kitchen.....”

Idan kujeran da yake bisa ya amsa toh kuwa shakka babu shima zai amsa....

Sosai ta kuma shan jinin jikinta kafin tasa kai zata shige d’aki ta rage kayan jikinta... Muryarsa ne ya daki dodon kunnuwanta a daidai sanda ta murd’a handle d’in k’ofar....

“Daga gidan uban wa kika fito....?!” Tambayar da ya jefo mata...

Cak ta tsaya had’ida rintse idanu k’irjinta naci gaba da bugu......

“Bakiji abinda nace bane.... Gidan uban wa kika fito...?” Ya kuma fad’i yana watsa mata mugun kallo.....

A hankali ta dawo da baya sanda tayi k’ok’arin saita kanta kana tace “Ban gane daga gidan uban wa na fito ba.... Daga gidan Hajiya nake....”

A fusace ya mik’e yana huci yake fad’in “Oh really... Bayan ganinki da nayi tsakiyan cink’oson maza har kinada bakin da zaki dubi tsaban idanuna kimin k’arya... How dare you Zulfah.....!” Ya k’arashe tamkar mai shirin kwasa mata mari....

Sauk’e ajiyan zuciya tayi kana tace “Kayi hak’uri Ya Hafiz wllhi hanyace tabi dani mai adaidaita yabi dani ta wajen amma wllhi gidan Hajiya na fito....”

Wata murmushin rainin hankali yayi kana yace “Hanyar gidan Hajiya ya koma bayan layin nan koh...?”

Shiru bata iya amsashi ba.....

Ya kad’a kansa kafin yaci gaba da fad’in “Bansan kin koma ‘yar siyasa ba ai sannan banji iyayenki ma sun sani kije gida zanzo na samu Abban....” Ya fad’i yana saka hularsa alamun ficewa zai kumayi....

Gabanta ya bada dumm! Innalillahi had’a da iyayenta zai kumayi.... Cikin sauri kafin ya ida ficewa ta janyo rigarsa tana fad’in “Ya Hafiz Dan Allah ka saurareni.... Wllhi ba abinda kake tunani bane, iyakacin gaskiyata na fad’a maka hanya tabi dani wajen....” Fuzge rigarsa yayi yana fad’in “Nayi imani da Allah kika kuma kama min riga zanyi wargazaki a gidan nan.... Idan munje gaban Abbah da Alhaji sai ki fad’a masu gidan uban da kika fito....”. Daga haka yasa kai ya fice yana dialing layin Sawwama da ya tadda d’inbin missed calls d’inta....

Durk’usawa tayi a wajen takaicin kanta na damunta zuciyarta na mata zogi, lokaci guda hawaye suka shiga kwaranya mata.....

Da k’yar ta iya mik’ewa ta kuma d’aukan mayafinta da jakanta ta ko zama bata kuma iyayi a gidanba ta fice sab’e da jakkarta tana hawaye....

Suna zaune parlorn Mamy suna lunch ta shigo tamkar wacce aka jefota....

A tare Nabilah da Marliya suka mik’e suna dubanta ganin yanayin da ta shigo....

Gijif ta zauna cikin kujera dafe da goshinta dake tsananin sarawa, Nabilah da Marliya suka kalli juna kafin Nabilah ta mata ido ta d’auki abincin ta wuce d’akinsu taci gaba daci....

Marliya tayi yanda tace d’in....

Kusan Zulfah Nabilah ta zauna tana mai k’are mata kallo...

“Addah lafiya....? Wani abin ne ya faru...? Naga dai d’azu kika mana sallama, lafiya Addah...?” Ta kuma tambaya cikeda kulawa....

Har lokacin idanunta a lumshe sannan hannunta dafeda goshinta, a haka ta furta “Mamy fah.....?”

“Tana sashen Abbah....”

Nabilah ta bata amsa....

Lokaci guda Zulfah taji sabon kuka na shirin taso mata, cikin sauri ta mik’e ta nufi uwar d’akin Mamy had’ida kullo k’ofar tana mai fashewa da wani irin kuka....

Nabilah ta bita da kallo had’ida rapka uban tagumi....

Mik’ewa tayi ta fice ta nufi Parlorn Abbah.....

Daga Mamy har Abbah dama Aunty Lami dake d’aya b’angaren sunsha mamakin ganin yanayin Nabilar wacce kaman an jefota......

“Ke lafiya...?” Mamy ta tambaya...

Nabilah da ta masu tsaye aka tace “Mamy dama Addace tazo and she seems not well....”

Abbah baice komai ba dama sunsan bazaice d’inba, gaba d’aya tinda d’ansa Ma’aruf ya b’ace ya dawo hakan, sai ya zamana tamkar bai damuwa da damuwar sauran yaransa sam basa gabansa, hakan sosai yakewa Mamy zafi, takanyi tunanin ko don su d’in ‘ya’ya matane kaman yanda Mamani ke yab’a masu maganganu ita sauran matan ‘ya’yan nata su Karima dasu Hajiya a cewarta duk sunzo sai aifan ‘ya’ya mata suke bacin ita kuwa uwar ‘yan maza ne domin kuwa duka ‘ya’yanta biyar maza ne... Hakan nan Mamani k’iriri take nuna masu tafison jikokinta maza wanda basu wuce uku ba, daga Hafiz wanda shine babba bayan b’acewan Ma’aruf(Alk’ali) haka nan take kiransa kafin ya b’ace saiko sauran biyun wanda duka ‘ya’yan Baffah Wada ne autansu Abbah.....

Zubawa Abbah abinci Mamy take ta kasa k’arasawa, Aunty Lami da zuciyarta tuni tayi haske, murmusawa tayi tana duban Abbah da tuni d’an sauran walwalar fuskar ta d’auke dukda kasancewarsa mutum maras yalwan fari’a...

K’arasowa Aunty Lami tayi ta amshi serving spoon d’in cikeda k’issa tana fad’in “A’a Mamy tashi kije kiji da ita zanjida Abbah....”. Ta k’arashe tana duban Abban da wutsiyar idanunta.... Aiko tamau ta hango fuskar nasa, ta saki murmushi a hankali....

Jiki babu k’wari Mamy ta mik’e ta kamo Nabilah suka fice....

Aunty ta gyara zama tana ci gaba da serving Abbah wanda yabi bada hankalinsa ga kallon tv...

D’an gyaran murya tayi kana tace “Na zuba romon kifin.....?” Kafin yakaiga bata amsa sukaji sallaman Mamani Hafiz na biyeda ita... Tindaga k’ofa take surfa ruwan bala’i....

“Inyi haka kawai, a d’auki alak’ak’ai a lanjab’awa jikana toh wllhi bazai sab’u ba, yo bacin zaman hak’uri da yakeda ita mai zaiyi da ita.... Idan baza’a hukunta ta ba toh wllhi ni da kaina zan guntule wannan aure jikana ya huta... Kan me yaro sai wahala da jarababbiyar yarinya yake wacce sam babu alkhairi tattareda ita....!”

Aunty ta mik’e cikeda nuna damuwa tana fad’in “Yi hak’uri Mamani kada jininki ya hau..... Allah baya son mutuwar aure ki daina fad’in haka, Zauna....” Ta k’arashe tana zaunar da ita bisa sofa tana mai ci gaba da tausarta...

Shiko Hafiz hula gaban goshi sai wani hure huren hanci yake yanajin ya isa.....

Abbah ya dubi Hafiz kana yace “Mai ta maka wannan karon.....?”

Babu kunya balle tsoron Allah Hafiz ya soma fad’in......

“Abbah jiya Zulfah har gida taje taci mutuncin Hajiyana itada k’anwar Mhaifiyarta Bara’atu, sosai ran Hajiya ya b’aci sanda take sanar dani amma ban d’auki wani hukunci kan abinba, yau nace taje ta baiwa Hajiya hak’uri toh shine ta d’ibi k’afa ta tafi taron ‘yan siyasa ashe dama wai itama har siyasan ta shiga tana tara min matan unguwa a gida idan bana nan.... Gaskiya Abbah ni na gaji da zama da Zulfa’u dama dai darajarka takeci....” Ya k’arashe yana mai d’aga kai sama...

Mamani ta kuma gyara zama daga saman sofa tana fad’in “Kaji koh ka daiji da kunnuwanka kuma idan har Hafizu ya saketa ina mai tabbatar maka babu mai kwasanta tinda shima jininta ya kasa da ita....”

Abbah da zuciyarsa ke masa matuk’ar k’una sauk’e ajiyan zuciya yayi kana ya dubi Mamani yace kiyi hak’uri Mamani amma abin baikai ayi saki ba ai.... Lami tashi ki kiramin Zulfa’u....” Ya k’arashe yana duban Aunty Lami...

Jiki na rawa ta mik’e ta nufi sashen Mamy, kafin ta isa sashen Mamy ta keb’e ta shiga neman layin aminyarta...


Wata uwar shewa suka sake daga cikin wayar kafin Aunty Lami taci gaba da fad’in “Na gaya miki Kakar ta tasosa gaba sun taho neman saki, amma fah kinsan banaso ayi sakin nan yanzu gwara tayita yawo a tsakani ita baga zawarci ba ita baga aure ba, bata a gidan uban bata a gidan mijin, kullum tana bisa layi....”

Suka kuma k’ek’yata dariya kafin Aunty tace “Zan kiraki anjima barin k’arasa kada suji shiru.....”



SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_..............DA RAO_





*09*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



Da sallama ta shigo parlorn kanta a k’asa Aunty Lami na biyeda ita.... Hafiz da Mamani suka rakatada mummunar kallo....

Abbah kuwa bayan abubuwan da Hafiz ya zayyano tayi ji yayi tamkar ya mik’e ya tufetada duka...

Cikinsu babu wanda ya amsa sallamarta dukda sanin darajan sallamar, daga can gefen carpet ta risina had’ida furta “Abbah gani nan.....”

Saida ya kwashe mintoci kusan uku kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Mai ya had’aki da mijinki...?”

Tasan maganan bazai wuce wannan ba dama, a hankali ta d’ago ta dubi sashen da Hafiz yake, hularsa gaban goshi saima shafa wayarsa da yake alamun babu abinda ya shalleshi, tausayin kanta ya kuma rufeta...

Muryar Abbah ta kuma tsinkayowa cikin fad’a wannan karon “Tambayarki nake, Mai ya had’aki da mijinki...?”

Kafin ta samu zarafin bada amsa Mamani ta cafe “Yo ina zata amsaka tunda tasan batada gaskiya, nidai kawai a sakarwa jikana mara a rabasa da annoba ehe....”

Bud’e baki tayi zatayi magana amma sai taji kuka yazo bakin nata, k’ok’arin saita kanta tayi dukda rawa da muryarta keyi kana tace “Abbah babu komai....”

Mamani ta daka shewa daga zaune kana tace “Kaji ja’ira yo dole kice babu komai tunda kinsan bakida gaskiya..... Munafuka kawai...”

Abbah ya kuma duban Hafiz kana yace “Maimaita abinda ka fad’i... Take Hafiz ya maimaita ko gizau babu a tattaredashi saima cewa “Abbah gaskiya aja mata kunne sosai don gaskiya banso ace na b’ata zumunta sabida taurin kunne irin nata....”

“Yo zumuntan ma ya b’aci mana sai mai me akeda annoba wacce tun haihuwarta babu alkhairi....” Mamani ta fad’i


Kasa daina dubansa tayi hawaye basu daina gangaro mata ba...

Cikin rawar murya ta furta “Ya Hafiz kaji tsoron Allah....”

“Da tsoronki zaiji.... Ja’irar banza...!” Mamani ta kuma fad’i yawa zata dunguro daga saman kujera....

“Zulfa’u da gaske mijinki ya hangoki cikin taron siyasa kuma bashi ya baki izinin hakan ba...?” Abbah ya kuma jefo mata tambaya...

Zulfah na hawaye take jinjina kai lokaci guda take fad’in “Eh Abbah da gaskene amma Abbah....” Cikin daka tsawa ya dakarta da ita kafin yaci gaba da fad’in “Wllhi wllhi kinji na rantse miki kika kashe aurenki bazaki zauna min a gida ba don bakida muhalli cikin gidan nan, muhallinki shine can d’akin mijinki, duk randa kika kaisa bango ya sakoki ki nemi wani gidan uban ba dai gidana ba kinji na fad’a miki.....”. Daga haka mik’ewa yayi ya wuce d’aki ba tareda ya kuma bi takan kowa ba....

Mamani da Hafiz suka mik’e a tare Hafiz na fad’in “Kin gani koh Mamani na fad’a miki wannan annobar bazan tab’a rabuwa da ita cikin dad’in rai ba, ni na sani Abbah hak’uri kurum zai bani.... Nidai kawai an cuceni wllhi....” Ya k’arashe yana ficewa had’ida bubbud’e hanci....

Mamani ta mik’e tana d’angwala k’afa ta isaga Zulfah dake nan durk’ushe a wajen ta shiga surfa mata bala’i kai kace rufeta da bugu zatayi, Aunty Lami sai faman dannar Mamani take cikin zuciyarta kuwa banda rawa da murna bata komai, burinta ya cika tunda bata tab’a haifa ba ita wacce ta haifa d’in dangin babu ne tunda babu mai k’aunar yaran, ta jima tana tsara hakan a rayuwarta bazata bari Mamy ta rik’e gida ba ta haifi yara sannan ta sami soyayya da kulawan kowa, ta d’au alwashi INDA RAI saita tarwatsa farin cikin da tadda Mamy da Abbah a cikinta, sai ta haifar masu da tashin hankali wacce batada ranar k’arewa, saita haifar da gaba tsakanin Mamani da ‘ya’yan Abbah tunda ita bata samu daman haifa mata koda jika guda ba, sannan sai ta zama tauraruwa a gidan dukda cewa itace batada tilon d’ah a gidan... Saita dasa soyayyarta a zuciyar kowa baga Abbah ba baga Mamani ba kai harma Mamy da yaranta sai ta sayi soyayyar kowa ta yanda zata zamto tamkar hasken rana a gidan wanda ke gusar da hasken lantarki, ya zamana ba’a ganin kowa sai ita....


K’iris ya rage Hafiz baiyi karo da Nabila ba wacce tayi k’ebebe a bakin k’ofar...


Banda uwar harara bata aika masa komai, yasan bazata gaishesa ba bazata kuma basa hak’uri ba koda zasu bagaji juna ne hakan yasashi rab’an ta gefenta zai wuce don sarai yasan wacece Nabila...

Har yakai bakin farandar ya tsinkayo muryar Nabila tana fad’in “Duk wanda bai daraja mace ba babban alamace cewa baya daraja uwarsa....”

Hafiz ya dawo da baya shaye da mamaki yake dubansa, shi Nabila ke fad’iwa magana a haka yana a matsayin yayansu gaba d’aya gidan koda ace baya auren Zulfah.... Dawowa yayi da baya yanda take nan a tsaye d’ankwalinta gaban goshi....

“Ke ni kike fad’awa magana...?” Ya tambaya yana faman huci...

Dad’a turo d’ankwalin gaba tayi had’ida basa k’eya kana taci gaba da fad’in “Idan mutum ya tsargu yasan halinsa ne toh shakka babu dashi ake...”

Hafiz ya tunzura ya d’aga hannu zai kwad’a mata mari tayi saurin duk’awa k’asa ya mari iska wanda saida k’arfin marin ta kusan aikasa k’asa badon k’ofa da ya dafe ba da ya tafi ya zube a k’asa...

Ya d’ago yana huci yake kuma k’ok’arin k’arasowa gabanta yana fad’in “Ni sa’anki ne Dan ubanki... Ni zakima rashin kunya...?”

Dariyan rainin hankali tayi kafin lokaci guda ta had’e fuska tace “Wllhi wllhi na girmi duka yanzu a gidan nan, kuma uba baifi uba ba Allah ka sake zagina sai na rama....”

A daidai lokacin da Zulfah ta k’araso wajen bata jira komai ba ta wanke Nabilah da mari tana faman huci, bata daina mamakin kalaman da taji k’anwar tata na fad’iwa mijinta ba wanda yake a matsayin Yayansu gaba d’aya...

“Addah kika mareni kan wannan ungrateful mijin naki....” Bata kai aya ba Zulfah ta fuzgo hannunta suka wuce tana fad’in idan batayi shiru ba zata k’ara mata....

Shi kuwa Hafiz har suka b’acema ganinsa mamakin Nabila yake, bai tab’a tsammanin rashin kunyar Nabilah ya kawo nan ba, lallai dole ya d’au mataki kan yarinyar nan don ko yayarta bata isa ta masa haka ba balle ita... K’ararramar yarinya da ita... INDA RAI sai ya cirewa Nabilah rashin kunyarta... K’wafa yayi kana yasa kai ya fice daga gidan zuciyarsa na masa k’una, dama ko yazo gidan iyakacinsa parlorn Abbah Mamy kuwa ba zuwa gaisheta mussamman yake ba dukda a matsayinta na sirkarsa saidai idan sun had’u a hanya ko a parlorn Abbah ya gaisheta amma bai tab’a taka parlornta da sunan gaisuwa ba...

Nabila ta dafe k’uncinta tana duban Mamy da Zulfah dake faman surfa mata fad’a kan rashin kunyar data kuma b’ullo dashi a ‘yan kwanakin... Kuka Nabilah keyi tana fad’in “Wllhi Mamy Allah baku kyautawa, ita fah Addah tsoron Yaya Hafiz take sai ta tsaya yana mata cin kashi da cin mutunci, Mamy bakiji abinda ya gama fad’iwa Abbah ai na lab’e bakin k’ofa naji komai, wllhi Mamy wulak’ancin da yayiwa Addah kare bazaici ba, ko shine autan maza sai taci gaba da zama dashi.. Idan Abbah yace zata bar masa gida babu gidansu Aunty B ne babu gidajen danginki ne Mamy, ina aka tab’a aure da cin zarafi.....”.

Zulfah ta katseta cikin daka tsawa “Babu ruwanki da rayuwar auren da nake sannan Ya Hafiz ba sa’anki bane da zaki masa rashin kunya da rashin mutunci, idan kullum muzguna mun yake babu ruwanki ban buk’atan damuwarki cikin rayuwar aurena kinjini koh....” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata...

Su duka biyun hawaye suke daga ita har Nabilan da bata daina hawayen takaici ba....

Zulfah taci gaba da fad’in “Allah na gani bai mance dani ba, sannan shi ya k’addara min wannan aure, kuma bana fata na zamto sanadiyan tashin hankalin Abbah... Inda rai da rabon wata rana Allah zai ya sarremun lamurana nayi imani zai sauk’ak’a min ta yanda banyi zato ba banyi tsammani ba kinji koh Sister... So please na rok’eki stop meddling, ki daina shiga kinji, wata matsalar kurum zaki kuma haifar mun.....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Rungumeta Nabila tayi su duka suna hawaye mai ban tausayi, Mamy tasa bayan hannu ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta shiga tsakaninsu ta janyosu suka nufi d’aki Mamy na rungume da kafad’ar ko waccensu....

Nasiha ta kuma yimasu gameda rayuwar duniya da matsayi da kuma ribar hak’uri, gaba d’aya yaran nata ta had’e ta masu nasiha harmada Marliya wacce take autarsu... Bayan magrib Mamy da Aunty Lami suka kuma tausar Zulfah suka umarceta da ta koma d’akinta kafin Abbah ya dawo gida ya taddata...

Aunty Lami ita tayimata rakiya har d’akinta ta kuma bata baki da nasihan hak’urin zama da miji musamman irin nata mijin... Sosai Zulfah taji dad’in shawarwarin Aunty Lami harda tayata daura abinci kafin ta wuce gida da shike ba itace da girki ba Mamy ce....

***

Bai tashi dawowa gidan ba sai wajajen 11:30pm lokacin har ta soma gyangyad’i a parlor wai donma tana kallon shirin fina finanfinan India da ake nunawa a tashan mbc bollywood....

Baiji mamakin ganinta ba don yasan zata dawo... Ya jima yana tsaye yana k’are mata kallon wulak’anci kafin ya daka mata wani uban tsawan datajisa uwa a mafarki...

“Ke!!! Ba cewa nayi kije gida ba sai na nemeki, mai kuma ya dawo dake....?”

Baccin da takeji ya watse itakam halin nasa ya daina bata mamaki saima tsoro...

Gyara kwanciyarta tayi kana tace “Wanda ka kai masa k’ara ne yace na dawo sanin kanka darajarsa kake ci nake zaune gidanka...” Daga haka juyawa tayi ta basa baya

Yayi k’wafa had’ida jinjina kai kafin ya fad’a d’aki, tana jinyo sanda yayiwa k’ofar sakata...

Tayi k’ok’arin danne k’uncinta tana duban sashen da abincinsa ke ajiye, a hankali ta gyara kwanciyarta had’ida lumshe idanu dukda baccin ya k’aurace mata...

A haka rayuwa taci gaba da wakana, a b’angaren su Sameer kuwa ana gobe zai taho Kano kusan kwana Siyama tayi tana zuba masa shagwab’a, gaba d’aya saiji tafiyar ta fice a ransa, ji yayi tamkar ya rubuta resignation letter ya zauna da Partner d’insa amma taimakon al’umma na d’aya daga cikin manyan burikansa na rayuwa....

Washe gari ma da k’yar suka rabu da juna yanda kasan wata uwa duniya zai tafi....

K’uri Sultan ya masu sanda Sameer ya kuma kirawo sunanta “Partner..!”

Juyowa tayi tana dubansa kana tace “Ka mance wani abu...?”

Saida ya d’ibi wasu dak’ik’ai yana dubanta kana ya kashe mata idanu guda kafin yace “I love you....”

Murmusawa tayi sannan tace “I know Partner... Drive safe....!” Ta k’arashe tana cuno masa baki gaba alamun kiss....

Kaman kar ya daina dubanta haka yakeji, shi kuwa Sultan dake zaune gaban motan idan ransa yayi dubu ya b’aci kai kace akansu aka soma soyayya, saikace wanda zasu shafe watanni ba tareda sunga juna ba sannan ya tabbata daren jiya kwana sukayi suna abu guda.... Cikeda takaici ya ciro wayarsa a aljihu yana shafawa....

Jiki a sanyaye Siyama ta dawo cikin gidan sai tanaji gaba d’aya ya mata girma, tsayuwa tayi gefen madubin console tana duban hotonsu dake cikin k’aramar frame a hankali tayi murmushi tana shafawa kana tace “Allah ya kaimun kai lafiya Partner.....”

Da dare tayima gaba d’aya sai taji babu dad’i, ta bud’e closet d’insu tana tunanin kayan baccin da zata saka, da ace yana nan k’ila da wannan zai zab’a mata, ko kuma wancan... Haka tayita tunani ko wanne ta d’auko sai ta mayar tana tunanin bashine Partner zai zab’a mata ta saka ba, gaba d’aya sai taji sabon tashin hankalin rashinsa na taso mata... haka nan a kitchen ma ta gama galantoyinta tana tunanin mai zataci, da ace Partenr na nan da ya dafa masu abinci mai sauk’i idan basuyi order ba....

K’walla suka ciko idanun Siyama sanda ta kwanta bisa gadonsu taji gadon ya mata fad’i.... Can k’arshen gado ta tak’ure had’ida rungume pillow hawaye na gangaro mata tsananin kewar mijinta na addabarta, ta mastu gari ya waye ta fice office ko zataji sanyi koda kuwa zata had’u da Khalid ne suyi fad’a...





SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_







*10*






Washe gari daga office koda ta dawo gida wasu ‘yan kayayyakinta ta had’a cikin k’aramar akwati kafin ta d’auki hanyar gidansu...,Kallo guda zaka mata ka fahimci tsan tsan damuwar dake tattareda ita..

Babu kowa a parlorn sai k’aran alarm ta dafuwar oxtail dake

Please Login or Register in order to submit comment