Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya maidoda dubansa gareta yana fad’in “Barin k’arasa ciki... Ina Naja’atu ya kawo min abinci na.... Ke Naja’atu....” Ya k’arashe yana bud’e murya alamun yana neman Najah.....

Sahariyya da akai komai a gabanta tsorone ya fara cika mata zuciya tana tunanin kardai abinda Hajiya ta shuka ne suka soma girba....

Da rarrafe Haule ta nufi d’akin mijinta tana fad’in “Amma Alhaji ka bani mamaki....”
Yana mai kwab’e babbar rigarsa ya katseta da fad’in “Da nayi mai....?”

Haule ta kuma sakin baki tana duban ikon Allah kana tace “Au bama kasan mai kayi ba Alhaji... Yanzu kai bazaka iya tantance makirci da akasinsa ba... K’iri k’iri kasan wancan shed’aniyar da d’iyarta makirici ne zalla ya kawosu ba komai ba.... Ko ka mance haka mukayi ma K’aninka da matarsa, ka mance irin wannan hak’urin muka basu.....”

Murmushin ko inkula Baba Alhaji yai mata kana yace “Banda abinki Haule shikenan kowa sai ya zama irinki... Sabida d’abi’arkice makirci shiyasa kike ganin kowa makiri ne.... Tinda sun gane kukurensu ni inaga ai shikenan Hafiz ya maida matarsa itama Zulfa’un sai ya had’esu duka biyu....”
Baikai aya ba Hajiya ta katsesa da fad’in “Wllhi k’arya kenan, wannan watsesstiyar d’ahna ya gama zaman aure da ita.... Wannan tsaf zata kar mutum... Wllhi badai Hafiz d’ina ba....”

Da wutsiyar ido ya dubeta kana yace “Akwai wani Hafiz d’in ne.....? Na gama magana Hafiz zai maida iyalansa don sakin baida wani alfanu cikinsa......” Daga haka band’aki ya shige ya bar Haule tana sallalami tana mamakin Yaushe Baba Alhaji ya soma mata musu... Lallai Magajiya bata zauna kurum ba da shiri ta shigo mata gida... Dik yanda za’ai ya zama dole ta tashi tsaye ta sami lafiya ta koma wajen bokanta kafin komai data mallaka su kufce mata.....

***

Gyara tsayuwarsa yai jikin mota k’afarsa a hard’e yana ci gaba da wasa da d’an makullin motar kana yace “Idan bazaki introducing d’ina wa Mamy ba, zan shiga nayi da kaina don dama kinsan wajen Mamani kam banida matsala.....”
Nabilah dai sai waige waige take duk a tsarge take jinta don bata saba tsayuwa da maza a waje ba kana tace “Kaga ni zan shige yanzu za’a fito masallaci sallan azahar, and banso mutane suyita kallona a nan suna wucewa....”

Ya d’an gimtse kana yace “teddy bear I’m serous, inaso family d’inki susan dani sabida bada wasa nazo ba.....” Yayi maganar babu alamun wasa a tattaredashi wanda saida ya haifarwa Nabilah da bugun zuciya.... Batasan mai zatace masa ba sai duban k’asa da tai..... Daidai lokacin Sameer ya fito daga gidan da niyyan tafiya masallaci....

Khalid yana hango Sameer ya saki murmushi don bai manta ba dama sun tab’a had’uwa a gidan saidai a wancan lokacin Sameer ya sanar masa cewa alak’asar da mutanen gidan sabo ne kawai sabida zaman unguwa guda, a halin yanzu baisan asalin alak’ar Sameer d’in da ahalin gidan ba....

K’arasowa Sameer d’in ma yai yana mamakin hango Khalid da k’anwarsa Nabilah a tare.....

“Aaa Dr ashe zan sameka a nan....” Khalid ya fad’i sanda ya shige Nabilah ya k’arasa ya baiwa Sameer hannu sukai masbaha....
Gaban Nabilah ya fad’i jin muryar Yayanta Ma’aruf suna gaisawa da Khalid.... Cikin sauri ta k’araso zata shige cikin gida, kai a k’asa taceda Sameer “Ina yini Yaya...”
Ya amsa mata a tak’aice bata kuma cewa komai ba ta shige cikin gida.....

Daga Sameer d’in har Khalid d’in kallo suka bita dashi har ta shige cikin sauri....

Sameer ya dubi Khalid yace “So you two know each other....?”
D’an shafa sumarsa yai kana tin kafin na had’uda kai a gidan nan nasan miss grumpy.....” Yai maganar yana murmushi....

Shiru Sameer ya d’anyi kana yace “Amma kasan alak’ar dake tsakanina da ita.....?”

Sai sannan Khalid ya d’ago yana dubansa with a serious face kana ya furta “Ban fahimceka ba....”

Dafasa Sameer yai yana murmushi kana yace mu k’arasa masallaci za’a shiga sallah.... Idan mun fito you’ve a lot to explain to me kasan bazan bari a yaudari k’anwata ba....” Ya k’arashe yana mai ci gaba da warware hannun rigarsa da yai folding wajen alwala

Khalid ya bisa da kallo yana mai nanata kalman k’anwata da Sameer yace har suka shige haraban masallacin


***

Yasmeen tai d’add’aya a parlorn tana ci gaba da aikin kuka wanda tin isowarta garin takeyi..... Mahaifiyarta kaw sai faman cika take tana huci, ita kad’ai takai mari takai bango tana mai jinjina rashin mutuncin da Khalid ya masu....
Cikin kuka Yesmeen taci gaba da fad’in “Momy Wllhi nayi imani Kano ya tafi wajen tsinanniyar can ya tafi tinda gashi Ammi tayi waya tana tambayar mun sauk’a lafiya... Momy nidai Wllhi bazan tab’a bari Khalid ya auri wata bani ba... Kigafah kalan wulak’ancin da yamin ya barni a train station yayi tafiyarsa.....” Ta k’arashe tana mai kuma jejjefa k’afafu tana kururuwa....



SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_


*71*




Mamakine ya cika Khalid jin cewa Iyayen Nabilah sune Iayayen Sameer na asali, wannan shine ikon Allah, who would’ve thought mutanen da Siyama ta tsana zasu juya su zama dangin mijinta....? Yai k’asaitaccen murmushi a hankali yana mai jinjina kai Don ko babu komai sosai abin ya masa zak’i.... Yana ganin kiran Ammi na shigo masa yayi biris yak’i d’agawa don yasan k’arshen zancen, k’arshe ma saka wayar yai a flight mode sanin cewa bazasu daina kiran nasa ba... Yana can sashen Mamani suna firan Yaushe rabo yayinda Sameer ke zaune parlorn Mamy suna tattaunawa kan batun Khalid d’in da Nabilah.....

Mamy ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Amma Ma’aruf kana ganin wannan al’amari mai d’orewa ne..? Banso azo ana samun sab’ani musamman da ya kasance d’anuwan matarka ne....”
Turowa kad’an yai daga cikin kujera kana yace “Mamy munyi magana sosai da Khalid kuma ya tabbatar min cewa da aure yake son Nabilah, sannan na yarda da halayya da d’abi’un Khalid Mamy... Yana dai da hali irin nasa na rashinji wasu lokutan but I assure you he’s a good person... Bawai don ya kasance dan uwa ga Siyama ba no, na sanshi tun yaranta yaron kirki ne Mamy... Amma saidai wani hanzari ba gudu ba...”
Mamy ta d’ago tana dubansa kana tace “Umhum ina saurarenka....”
Sameer ya d’an fuzar da iska kana yace “Mamy iyayen Khalid suna yunk’urin had’a aurensa da wata ‘yar uwarsa ce wanda sam shi bai k’aunarta... Kinji a yanda matsalar take, ni kuma sam bazan zauna a cutar da ‘yar uwata ko a k’untata mata ba, bazanso tai auren da zatazo tana shan wahala ba koma azo anacewa da an sani da ba’ayi ba....”
Jinjina kai Mamy tai kana tace “Wannan gaskiya ne Sameer, abinda yafi dacewa tun kafin maganan nan ya isa gaban Abbanku ka sami shi Khalid d’in kuyi magana, yaje yabi umarnin iyayensa yayi masu biyayya daga shi har Nabilar suyi hak’uri da juna, ni zan sami Nabilah nai mata magana, ka fahimta....”
Shiru ya d’anyi kaman mai nazari kana yace “A’a Mamy baza ai haka ba, idandai suna son junansu inaga bamuda hurumin datse masu farin cikinsu, komai d’an gwaji ne a rayuwa, inaga mu baiwa Khalid dama ya gwada nasa k’ok’arin wajen shawo kan iyayensa da nuna masu kuskuren dake cikin k’ok’arin da suke wajen auren da sam babu soyayya cikinta tinda kinga a nan gidan Auren Zulfa’u da Hafiz aya ce, ta zama izna ga masu yunk’urin irin wannan had’in da akeyi ba tareda baiwa yara daman zab’an abokan zamansu na rayuwa ba.. Aure is a lifetime commitment Mamy, one has to be very careful wajen deciding....”
Mamy ta jinjina kai cikeda gamsuwa da bayanan d’an nata kana tace “Haka ne Ma’aruf, kayi gaskiya Ubangiji ya maka Albarka....”
Sameer ya amsada Ameen Mamy kafin ya mik’e yana fad’in “Barin shiga na duba Mamani....”
Mamy tace “Toh a fito lafiya....”
Nabilah dake mak’ale jikin k’ofar d’akin Mamy taji komai, tsanin mamakine ya cikata, Wato wannan Siyamar itace matar Ya Ma’aruf... Kam bala’in can.... Matar datazo har cikin gidan nan ta gama rashin daraja ashe gidan sirakanta ne....? Aiko wllhi bataci bulus ba bashi taci Dan Wllhi wannan rashin darajan da tayi cikin gidan nan tsaf saita kwashesu ta maida cikin aljihunta saidai ba sunanta Nabilah ba... Ta saki murmushi a hankali tana hasasho ramuwar gayyar da zataiwa Siyama matar Ya Ma’aruf... Ita a halin yanzu ma bata ta tata da Khalid kawai burinta ta k’untatawasu Siyama ta huce takaicinta... Da wannan tunanin ta koma cikin d’aki ta haye kan gado ta lumshe idanunta tamkar mai bacci jin Mamy ta nufo cikin d’akin....

Sameer yana tafe sashen Mamani ya tsaya yana hangen k’ofar sashen Aunty Lami tamkar mai son tuna wani abin... Haka kurum kaman wanda aka umarcesa ya nufi sashen nata sallama saman bakinsa....
Aunty Lami dake k’uryar d’aki tana waya da Haule, Haule na labarta mata kalan rashin darajan da Magajiya tazo har cikin gidanta tai mata nan ta sinkayo muryarsa mai cikeda k’warjini yana sallama... Gaban Lami ya yanke ya fad’i tamkar wacce aka aje mata guduma... Gaba d’aya saima ta daburce ta shiga amsa masa sallamar nasa cikin in ina.... Daga d’aya b’angaren Haule da itama ta sauraro sallamar tasa wanda ko shakka babu itama fad’uwar gaban ya haifar mata, cikin sauri taceda Lami “Dama ta sameki ki gama mana shi duk mu huta da fargaba da fad’uwar gaba...” Bata jira cewar Lami d’in ba ta datse kiran....Da k’yar tai k’ok’arin saita kanta kana tai masa izinin shigowa.....
Aunty Lami harda karkad’e masa kujera tana fad’in “Lale lale Uban masu gida, shigo abinka....”
Murmushi saman fuskar Sameer ya shigo kana ya soma gaidata bayan ya daidaita bisa kujera mai d’aukan mutum biyu wato two seater... Gaba d’aya Lami ya kasa zaune ta kasa tsaye dikda d’ingishi da take sakamon fad’owa da tai jikin window sanda take lek’ensu Abbah da Mamy....
Kankace mai ta cika gaban Sameer da kayan ciye ciye da shaye shaye tana fad’in “D’an gidana kaci abinci please... Ko kana son wani abinne yanzun na had’a maka....”
A hankali ya d’an murmusa kana yace “Karki damu Aunty aima a k’oshe nake, dama cewa nayi bara na shigo na dubaki don jiya Mamy ke cemin bakiji dad’i ba kin samu buguwa a k’afarki....”
Aunty Lami ta kuma mik’ar da k’afar tana mai tamke idanu alamun zogi kana tace “Wllhi am Uban masu gida... Kaga waccan k’yauran kitchen d’in shine fah na buga dashi, ka ganshin nan ya jima a haka nan, toh Abbanku bai samun zama balle a gyara ga gidan sai ‘yanmata saima ka rasa waye zaka aika....”
Sameer ya d’an karanceta a hankali kana yace “Karki damu Aunty zan turo mai gyara anjima kad’an a duba in sha Allah... Allah ya baki lafiya....”
Ta amsada “Haba Uban masu gida, ayi haka... Kai na kuwa gode fah... Allah dai shi saka da Alkhairi.... Ohni Lami yau ga Ma’aruf d’in ya dawo garemu har mun soma ganin alfanunsa... Allah mun gode maka da ka bayyana mana shi....” Ta k’arashe tana mai kamo bakin zani tana share hawaye tamkar gaskiya....
Sameer shiru yai tamkar mai nazari don baiga abin godiya da kuka a nan ba, kana ya d’anyi gyaran murya yace “Babu komai Aunty, ki kwantar da hankalinki na dawo gareku in sha Allah kuma bazan sake b’acewa ba...” Yayi maganar yana mai dubanta with a straight face....
Aunty Lami da bugun k’irjinta ya k’aru a hankali ta saki zanin da take share hawaye dashi tana duban cikin idanun Sameer da baya fad’i mata komai sai tsan tsan tsoro da fargaba ga k’warjininsa da ya hanata sukuni tin shigowarsa.... Kakkaurar miyau ta had’iya da k’yar kana ta saki murmushin yak’e tace “Haka ne Uban masu gida... Toh ko ruwan kasha mana...”
Mik’ewa yayi hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa kana ya d’aura sassanyar murmushi saman kyakkywar fuskarsa yace “Na gode Aunty ban jima da shan ruwa ba next time in sha Allah...”
Aunty Lami ta bisa da kallo har ya fice tanaji cikin ranta tamkar yayi tuntub’e wajen ya fad’i gawa kowa ya huta, ta maidoda dubantaga ga contaminated drink d’in data kawo masa wanda ko kallo bai ishesa ba, tai k’wafa ta d’auka ta nufi kitchen dashi ta juye cikin sink, cikin ranta take ayyana cewa next time bazai tsallake ba idan ya tsallake wannan, tai murmushi sakamakon tuno abinda yafiso tun yana yaro wanda dashi zasuyi amfani su gama dashi kana tai k’wafa a fili ta furta “Muje zuwa Ma’aruf da sannu zaka fad’a tarkonmu...”

***

Jinge kansa yake jikin car seat d’in idanunsa a lumshe yana mai ci gaba da kad’a ‘yan yatsun hannunsa jikin steering wheel d’in motar.... Yusuf da duk tsawon lokacin karantarsa yake gyara zamansa ya d’anyi kana yace “We’ve been waiting here fo edges idan kanawa Allah muyi abu guda d’aya don wllhi na gaji....”
Da wutsiyar idanu Akram ya dubesa kana yace “Toh idan naje mai zance mata, kaina na kawo kokuwa Ogana nakema sharan fage...?”

Yusuf ya fuzar da iska a hankali had’ida tab’e baki kana yace “Rashin bin shawarinka ya janyo maka, saida na fad’a maka tun farko be frank with him, ka sanar dashi komai....”
Baikai aya ba Akram ya katsesa da fad’in “In sanar dashi mi... Cewa munyi tarayya wajen son mace guda kokuwa mai kakeso na sanar dashi...? Ni kama san abinda yafi damuna.... Wllhi ban sani ba if I can do this.... I’m not sure...” Ya k’arashe yana mai taunar lip d’insa na k’asa a hankali...
Yusuf yaci gaba da karantarsa a nitse kana yace “Alright here’s what you should do, amma shawarice....”
Akram ya dubesa da gefen ido kana yace “Ina saurarenka.....”

K’asaitacciyar murmushi Akram yayi bayan Yusuf ya gama basa shawarin hukuncin da zai yanke, wanda kuma sosai yayi na’am da shawarin abokin nasa da wannan matsaya suka nufi gidan Aunty Bara’atu kaman yanda Atika ta kwatanta masu.....

Kallon Atika da Aunty Bara’atu kurum take tana mamakin yanda suka tasata gaba sai tayi ado don zata fita zance... D’an turo baki gaba tai kana tace “Wllhi Aunty da dai kin daina biye Atika matsala ce bai ganta ba, ni ko zamanin da nake budurwa ma ai ban fita zance ba balle yanzu da nake bazawara....Kuma harda wani ado Aunty aima sai yace sonsa nake....”
Hararan da Aunty B ta narka mata ya sanyata yin shiru....
Atika ta k’unshe dariyarta sanda take ajiye had’edd’iyar doguwar riga ‘yar dubai mai launin ruwan hoda Wato peach saman gado, harara Zulfah ta rakata dashi had’idayin k’wafa na zan kamaki ne...
Atika ta kuma darawa kana tace “Aunty wannan ‘yar gidan naki saifa kinyi da gaske don wllhi ko a office haka nake fama da ita, duk wanda yace yana sonta sun b’ata kenan, harta Manager yanzu bata masa murmushin da take masa da, shi wannan abokin Yusuf d’in ma na tabbata don dai kin saka baki ne bansan ko gidan Hafiz takeso mu koma ba....” Nan ma harara Zulfah ta narka mata kana Aunty B ta tari zancen da fad’in “Ai Hafiz saidai yaga Katin gayyata da izinin Allah.. Mai ake da jinin Haule jinin tsiya....”
Zulfah ta marairaice fuska tace “Kai Aunty Hajiya fah tayi nadama...”

Muguwar kallo Aunty B ta kuma watsa mata kana tace “Idan Hajiya Haule zata shekara tana cewa ta tuba tayi nadama bazan tab’a yarda ba... Ke idanma ta tuban ba komawa gidan d’anta zakiyi ba kin gama zaman aure dashi....”
Atika ta mik’e tana amsa wayarta da ake bugawa... Ko ba’ace ba kasan bak’on nasu ne ya iso, nan Yusuf ke sanar da ita gasu sun iso... Aunty B tasa Zulai ta bud’e masu parlor k’ofan gaba...
Zulfa’u kaw gaba d’aya sai jinta take wani iri haka nan ga bugu da k’irjinta keyi, yau ita Zulfa’u ce zata fita wajen wani da sunan yazo neman aurenta, da gaske dai Ya Hafiz ba mijinta bane... Toh mai zatace, ya ma ake firan.. Abu ne da bata sanshi ba tun tasowarta tinda Hafiz ma rana tsaka akace an bata shi.... Tana tsaka da tunanin muryar Aunty Bara’atu ya katseta “Ki k’arasa shirinki a hankali Zulai ta kai masu abin tab’awa....”
Gabanta ya kuma bada sautin rasss... A hankali ta jinjina kai kana tace “Toh Aunty....”
D’aukar doguwar rigar tai tana k’are mata kallo kana ta zirata, ta d’ago tana duban kanta jikin mirror sosai ya mata kyau ya zauna a jikinta, zallan powder ta shafa shima don Atika ta tak’ura mata saiko d’an man baki data shafa, ta d’au mayafin rigar ta rufa akan sumarta wanda yake a tsefe ta tufkeshi a tsakiya mai yalwan cika dukda bai faye tsawo ba...
Atika tai tsaye tana dubanta kana tace “K’awata kin fito, babu wanda zai tunanin kin tab’a aure balle haihuwa... Masha Allah son kowa k’in wanda bai samu ba....”
‘Y’ar gajeriyar murmushi tai kana “Kedai kyaji dashi... Ni wllhi don dai kun tak’ura min ne amma harga Allah banyi shirin soma wani relationship yanzu ba....Not now gaskiya....” Ta k’arashe tana mai zama saman gado gijif..
Atika ta dara kana tace “Ni wllhi badani kike, Akram fah had’edd’en gaye ne na gaban goshin Governor to be d’inmu... Ni dama tinda Yusuf yace min program d’inki na kashesa nace za’a iso wajen.... Nidai Wllhi karki badamu ehe ki bari kawai musha biki, amma fah ina tausayin manager don Wllhi shima da gaske yake sonki....”
Hararanta Zulfah ta kumayi kana tace “Kedai kyaji dashi....”
Suna a haka Aunty Bara’atu ta turo k’ofan d’akin ta shigo ta dubi Atika tace “Haka akeyi kun k’yale bayin Allah sunata zaune... Ki lek’a ku gaisa kafin na taso k’eyar k’awar taki...”
Atika ta mik’e ta d’au mayafi tana mai darawa kana tace “An gama Auntynmu...”
***

A parlor Sameer ya bar Shamsu da Khalid suna firan ball ya shiga amsa kiran Mummynsa....
Koda suka gaisa Hajiya Fatahiyya sai cewa tai “Sameer, Son are you sure you’re alright... Daga muryarka inaji kaman wani abu na damunka... What’s wrong son.... please tell me...”
Fuzar da iska yai a hankali don yasan Mummy ta masa farin sanin da bazai iya b’oye mata damuwarsa ba.... Katse shirun nasa tai da fad’in “Is everything alright with your family...?”

Sameer ya d’an gyara zamansa sosai sakamakon tuno buk’atan Baba Alhaji da yayi kana ya soma fad’in “Mummy lafiya kenan zan iya cewa... Amma yanzu duk ba wannan ba Mummy... It’s Siyama.. Siyama itace damuwata a halin yanzu... Mummy I don’t understand her anymore... She’s something else, tinda ta tafi gida bata dawo ba and ko kiranta nayi wasu lokutan ta d’aga wasu lokutan bazata d’aga ba... Maganan da muke dake har yanzu batada labarin na sami biological parents d’ina talk less of introducing her to them... Mummy na fara doubting if Siyama really loves me...”
A hankali ta saki ajiyan zuciya kana tace “Sameer na sanka da hak’uri da barin abu ma zuciya, amma har idan zaka cutu bana goyon bayan kaci gaba da mata uzuri.... Amma mu bar zancen nan har mu dawo k’asar in sha Allah da kaina zanje na samu Faridar ayi mai yuwa idan Siyama zatai zaman aure fine, idan kuma bata shirya zaman auren bane sai mu sani... Ka k’ara hak’uri Sameer, in sha Allahu komai ya kusa daidaita kaji koh...”
Kaman tana dubansa ya jinjina kai kana yace “Mummy kar a mance ai mana addu’a jikin d’aki mai tsarki... Na gode k’warai Mummy na a gaida Daddy ace ina mishi add’uan samun lafiya... Allah yasa a dace ya kuma dawo daku lafiya...”

Ameen Son ta amsa masa dashi kafin ta k’arada “Ka gaishar mun da Mamy da Abbah and your siblings of course, Allah bai yi zamu had’u yanzu ba, amma da zaran mun sauk’a a Nigeria zamu had’u da yardar Allah tinda ta Kano zamu sauk’a... I love you so much Son, never forget that... Nida Daddynka muna sonka.... Allah ya maka albarka ya shige maka lamuranka...”
Cikeda jin dad’i had’ida peace of mind yace “Ameen Mummy nah....”
Sukai sallama har zai katse kiran ta kuma ambato sunansa “Sameer!”
Ya amsa a hankali yana mai jin zuciyarsa tai masa rauni ba tareda sanin dalili ba...
Mummy taci gaba da fad’in “Thank you for coming into our lives... Thnak you for making us happy... Thank you for completing our family... Thank you for giving me that chance to be a mother to you.... Thank you for being that son I always wanted to have.....”
Izuwa lokacin hawayene ke zubowa daga idanun Sameer ji yake tamkar ban kwana Mummy ke masa, a hankali yake furta “Mummy pls stop... Ki daina mun godiya, iyayena haifana sukayi but keda Daddy are my life... Most especially you Mummy, bazan tab’a iya biyanku d’awainiyar da kukayi dani ba Allah ne kawai zai biyaku.... I love you so much Mummy... So much....”. Ya k’arashe hawaye na gangaro masa...
A hankali itama ta goge hawayen da ya zubo mata kana tace “I love you too son.... Allah ya sadamu da Alkhairi...”
Sameer ya amsada Ameen Mummy nah... Jikinsa a matuk’ar sanyaye sukayi sallama... Kwanciya yayi rigingine bisa gado yana tuno rayuwarsa da Mummynsa tun tasowarsa kyakkyawan murmushi kwance saman fuskarsa....

***

Kanshi na bisa cup ya d’aura lips d’insa kenan da niyyan kurb’an ruwan ya sinkayo sallamanta cikin muryar nan nata mai dad’in sauraro, ruwan da bai iya kurb’a ba kenan ya d’go yana dubanta, ta masa kyau sosai har fiyeda lokacinda sukaje mata gaisuwar ta’aziyar rasuwar d’iyarta can gidan mahaifinta....

Shigowarta parlorn yayi daidai da bugun gate da ake, daga yanda suke suka soma sauraro muryan Hafiz....
Gaban Zulfa’u ya yanke ya fad’i... A hankali ta furta “Ya Hafiz.....”


SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_.................DA RABO_




*72*




Tinda ya hangi mota k’irar Mercedes a k’ofar gidan yaji hankalinsa sam bai kwanta aiko kaman jira yake Zulai tana bud’e masa ya soma tambayar ina Zulfa’u.... Zulai ta soma inda inda tama rasa mai zatace masa, tsawa ya darara mata tuni ta shiga ‘yan kame kame, saidi juyawan da zaiyi ya hangi takalman maza k’ofar parlorn, wani abu yaji ya sauk’a masa a k’irji tamkar an ije gingimemen dutse.... Ya watsawa Zulai harara kana ya shige fuuuu kaman zai tashi sama ya nufi parlorn... Kafin ya shige sai ganin Aunty Bara’atu yai gabansa tamkar wacce aka jefota “Karma ka soma wannan tunanin, shige mu tafi” ta nuna masa hanyar waje....
Banda huci da harararta Hafiz baya komai, Ita kuwa Zulfah a can cikin parlor gaba d’aya ta rasa sukuni, hankalinta yafi karkata wajen Aunty B da Ya Hafiz, dikda fira da Yusuf ke k’ok’arin janta dashi bawai fahimtarsa take ba, gaba d’aya ta kasa kunnuwarta ga sauraren tattaunawar Aunty Bara’atu da Ya Hafiz dikda cewa k’asa k’asa Aunty Bara’atu ke maganar...
A kufule Hafiz yace “Amma Aunty Zulfa’u fah da aurenta maiyasa zatake kula wasu mazan....”
Muguwar kallo ta aika masa kana tace “Kaine ka d’aura mata auren... Nace kai ka d’aura mata auren...?”
Hafiz yaci gaba da huci da kumbure kumbure....
Aunty B tai k’wafa kana tace “Shige nace kafin na sunkuceka aka na fiddaka.... Tsaya waima ban maka iyaka da gidan nan ba...?”
Wannan karon gajeriyar murmushi yai kana yace “Haba Aunty ashema Zulfah ta bar gidan nan kenan....”
Aunty B ta gyara tsayuwarta kana tace “Kaga Hafiz shige ka fice tin kafin raina ya b’aci...”
Ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Aunty B, ji yake tamkar ya shak’e matar nan data zamto masa shamak’i da farin cikinsa da kuma cikar burinsa... Yana sauraro muryoyinsu yanda suke fira cikin nishad’i da kwanciyar hankali, zuciyarsa taci gaba da masa zogi sanin cewa Zulfarsa ce cikin parlorn nan... Miyau mai d’ankaran zafi ya had’iya kafin ya furta cikin zuciyarsa “This is far from over..” Cikin huci yana mai aiakawa Aunty B duban k’iyayya ya juya kaman zai kifa k’asa....
Aunty B ta murmusa kana tace a hankali “Dama d’aya ce Malam Hafiz kuma kayi wasa da ita, mu zuba nidakai....” Bata bar wajen ba har saida ta tabbata Hafiz ya bar gidan....

Wani lungu ya samu ya mak’ale yana jiran fitowarsu, Aiko mintoci kad’an ya hango munafukar sabuwar k’awar nan tata Atika kaman yanda yake kiranta Munafuka, sun fito sunyoma samarukan nasu rakiya zuwa wajen motar tasu, daga yanda yake yana hango d’aya mai maroon d’in boyal d’in ya kafe Zulfa’u da idanu, zuciyar Hafiz taci gaba da tafrfasa, gashi sosai Zulfah ta masa kyau, tsantsan soyayyarta na kuma azalzalansa, idan za’a mutu bazai daina bikon matarsa ta dawo garesa ba, kuma wllhi da ko wanene ya shirya yak’in neman auren Zulfa’u a karo na biyu....

A hankali ya fito daga mab’oyar tasa ya nufosu, Atika da ba wani saninsa tai ba amma hangosa da tai saida gabanta ya fad’i don ba komai ta hango saman fuskarsa ba face tashin hankali tsagwaranta....
Cikin sauri Atika ta soma fad’in “Ka kar ka damu Oga Akram ka samu k’awata an gama in sha Allahu...”
Yusuf yai karaf yace “Yauwa k’anwata nasanki da k’ok’ari aci gaba da k’ok’arin shawo mana kan

Please Login or Register in order to submit comment