Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajen sahibarsa Sawwama.....

Tinda Aunty Lami ta d’auki wayar Hajiya ta fahimci babu lafiya.....

“Wai meke faruwa ne ni dan Allah ki sanar dani.....” Hajiya tace hankali tashe...

Aunty Lami ta samu jikin gado ta jingina kana tace “Haule anya kin tabbata Ma’aruf ya mutu...? Haule anya Ma’aruf ya zama tarihi kaman yanda muke tunani, anya Ma’aruf bazai dawo garemu ba....?”

Dukda bugu da k’irjin Hajiya keyi bai hanata dariyar yak’e ba kana tace “Haba Lami meye kuma kike neman maida mutane baya ana ci gaba a rayuwa, wane irin Ma’aruf...? Idan dai Ma’aruf d’an gidan Usman Mailafiya ne ya jima da mutuwa saidai mai kamanninsa, kinga kima daina sak’awa zuciyarki wannan mummunar zato don Allah....” Ta k’arashe tana zama bakin gado....

Girgiza kai kurum Aunty Lami take tamkar Hajiyan na dubanta kana tace “Inaga dai baki fahimci abinda nake nufi bane Haule amma idan da hali yau d’in nan mu had’u gidan Aminiyar sirri ta fad’i mana gaskiyar abinda tayida Ma’aruf Mailafiya don wllhi yau nikam nayi tozali dashi a raye....”

Jikin Hajiya ya d’anyi sanyi, gyara zamanta tai kana tace “Shikenan Lami mu had’u gobe gidan Aminiya tinda dai yaukam kinga dare yayi, ke nake jiyewa kinsan wannan baud’edd’en mijin naki ba bari zaiyi ki fice ba ni kuwa nawa mijin dama a tafin hannuna yake... Ma had’u goben....”

Aunty Lami ta amsada “Toh shikenan Alhaji na fita Kasuwa zan fito...”

Daga haka sallama sukayi ko waccensu tana sak’e sak’e cikin zuciyarta.....

***

Washe gari haka Nabila ta tasa Mamy gaba da tambaya ko tasan bak’in Abbah...

Mamy ta umarci Marliya data kwashe dankali cikin mai kana ta dubi Nabilah dake shirya wanke wanken plates cikin drawer tace “Kici gaba da tambayata abinda bai shalleki ba kar kiyi aikin dake gabanki....”

Nabilah ta turo baki gaba tace “Kai Mamy tambaya shikenan ya zama laifi ai da Marliya ce ko Addah suka tambayeki amsasu zakiyi, Mamy Dan Allah su wayesu...?”

Girgiza kai kurum Mamy tayi kana tace “Nabilah ban sansu ba hasalima ban shiga parlorn ba har dai suka tafi kina gani ai... Toh yaya za’ayi na sansu kin kuma san Abbanki kinsan wane irin mutum ne ba kasafai yakeso ana haurawa kansa ba musamman idan yana tareda bak’i, ballanata ma kinsan ba shigan zanyi ba idan ba shine ya buk’aci hakan ba... Wai me bak’in suka miki ne...?”

Ta k’arashe maganar tana mai jefo mata tambayar had’ida tsareta da idanu...

Girgiza kai Nabila tai cikin sauri don bataso Mamy ta fahimci wani abin kana tace “A’a basumin komai ba kawai dai na tambaya ne.....” Kan Mamy ta kuma jefo mata wata tambayar ya mik’e ta d’au markad’en kayan miya ta zuba cikin blender....

Girgiza kai kurum Mamy tai kana tace “Allah sa dai ba wani tsaurin idon kika masu ba don nasan halinki....”

Bata jira cewan Nabilar ba tai ficewarta...

Nabilah da Marliya suka kalli juna suna k’unshe dariya,Marliya tace “Mamyna case... Addah Naby kema dai Dan Allah ki daina tinzira Mamy sai kuyi zaman lafiya...”

Harara Nabila ta galla mata kana tace “Ke idan aka biyeta Mamy toh fah a gidan nan ma sai aci kashi akanmu, k’yaleta kawai haka zanci gaba da lallab’a kayana wataran zatai missing masifar nawa da taro mata magana...”

Da mamaki Marliya ke dubanta kana tace “Addah did I hear you right...? Kikace wataran Mamy zatai kewar fad’anki, uhm kodai kodai Mamy ta kusa yin sirki ne....”

Ludayin gefenta ta janyo zata kwad’awa Marliya, Marliya ta sukunya tana dariya kana tace “Kinga gaban mangyad’a nike kiyi hak’uri don Allah, nifah kawai tambaya nai.....”

K’wafa Nabilah tai kana tace “Dama baki sunkuya ba, wllhi Allah sawak’e na tsaya kula wani namiji bayan duk halinsu guda ne, ga Addah can tayi auren wahala bataji dad’i ba ga Mamy ma ba wani dad’in auren takeji ba Aunty Bara’atu mijinta kullum baya nan wayasan uwar mai yake tsinanawa a can barikin, zamana a gida gaban iyayena yafin zaman gidan wani gardi da idan yamin badaidai ba garin nan sai ya mana kad’an don wllhi da ace ni ce Ya Hafiz ke aure da tuni ya gama shiga taitayinsa...”

Sallaman Aunty Lami ne ya katsesu... Marliya ta amsa da sakin fuska yayinda Nabila ta tab’e baki taci gaba da abinda take...

Lek’owa kitchen d’in Aunty Lami tayi tana fad’in “A’a ‘yanmatan gidan ne a kitchen, iyye kaga yaran Mamy....”

Idan kayan miyan da take juyewa cikin tukunya sunyi magana itama zatai magana, Marliya ce dai gaisheta fuska fal fari’a kana tace mata Mamy na ciki...

Har saida Aunty Lami ta ambaci sunan Nabila kafin Nabilar ta juyo a tak’aice tace da ita ina kwana... Shikenan gaisuwar bata kuma cewa komai ba...

Jin muryar Aunty Lami yasa Mamy fitowa suka soma gaisawa, nan Aunty Lami d’in ke sanar da Mamy zata gidan Yayarta Rabi bataji dad’i ba....

Mamy tace “Ayya Allah ya bata lafiya, kinsan shigowar daminan nan sai a hankali yanayi ya canza sai ayiya cututtuka...”

Aunty Lami tace “Wllhi fah Mamy abin saidai addu’a...”

Mamy tace “Haka ne ki gaidata da jiki....”

Aunty Lami ta amsa da “zataji sai na dawo...”

Mamy ta amsa mata da “A dawo lafiya...”

Nabilah na kitchen tana kwaikwayon maganan Aunty Lami kana tai k’wafa tace “Salon munafunci...” Juyowa tai ta dubi Marliya dake dubanta da mamaki kana tace “Ke kuma idan ina waje kika kuma biyewa wannan munafukar matar tana wani jan mutane da wasa wllhi kema sai na daina miki magana tam...”

Dariya kawai Marliya tai kana tace “Um naga dai matar babanki ne don haka itada Mamy matsayinsu d’aya, besides Aunty Lami battada matsala tun tasowarmu haka muka gansu zaune lafiya da Mamy....”

Tsuka Nabila tai kana tace “Aikin banza wannan da gani ruwan munafukai ne da ita shiyasa sam tamu batazo d’aya ba... Nidai na fad’a miki idan ina waje kema kiyi banza da ita kafin na tunb’uke miki hak’orin gaba....”

Girgiza kai kurum Marliya tai tana dariya kana ta fice a kitchen d’in ta bar Nabilah da masifarta...


***

Wajajen biyar na yamma Khalid ya sauk’a a Kaduna dashikema bai fito da wuri ba saida ya tsaya ya kammala wasu abubuwan....

A parlor ya tadda Siyama da Yesmin first cousin d’insa d’iyar Yayan Ammi dake karatu a Cyprus, rabonsa da ita zaikai shekara biyu ko fiyeda haka idan bai mance ba...

Siyama na hangosa murmusinta ya k’aru kana tace “Speaking of the devil... Kinga gashi nan sauk’arsa kenan....”

Baice mata komai ba sai uwar harara da ya danna mata

Cikeda zumud’i Yesmin ta ajiye glass of lemonade dake hannunta ta juyo tana dubansa fuska fal fari’a.....



SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_



*20*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



“Ya Khalid sannu da zuwa, ya hanya...?” Yesmin ta fad’i cikin kashe murya....

Kallon kirki bata ishi Khalid ba yace da ita “Kina lafia...?” A tak’aice...

Nanma saida ta kuma murmusawa had’ida juya idanu kana tace “Lafia lou, it’s been a while...” Bai bari takai ayaba yace “As you can see I just got home, I’m pretty tired... would you please keep your greetings maybe for later....” Ya k’arashe yana d’aga mata giransa sama alamun Yes a gajjiye yake...

Nan fah jikin Yesmin yayi sanyi ta juyo suka had’a idanu da Siyama, sosai Siyama taji kunyar abinda Khalid yayiwa yarinyar nan Yesmin tasan za’a rina hakan kallon su Ammi kurum take idan taji suna mafarkin had’a Yesmin da Khalid, basusan Khalid wane irin baud’edd’en mutum bane shiyasa...

Har ya isa staircase Siyama ta d’an bud’e murya tace “Eyya shalelen Daddy sannu da hanya ko nazo na baka massage ne...?”

Rolling idanunsa yayi yana mai dubanta a kaikaice kana yace “Spare me your false sympathy Siyaam...” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai sa kai da yai yayi haurawansa sama...

Duban Yesmin Siyama tai fuska d’aukeda murushin yak’e kana tace “Ehen mai ma nake ce miki....?”

Girgiza kai Yesmin tai kana tace “Cousin anya Khalid zai soni kuwa...? Kiga fah abinda yayi...”

Murmushin Siyama ta kumayi kana tace “Kar ki damu cousin idan dai Khalid ne ya wuce haka, but I believe you can change him....”

Sauk’e deep breath Yesmin tai kana tace “But are you sure he doesn’t have a girlfriend...?”

Murmusawa Siyama ta kumayi kana tace “Wa... Wannan...?” Ta kuma d’an murmusawa kana tace “Dukda fad’a da muke yawan yi Khalid bai tab’a b’oyemin komai ba na rayuwarsa... Idan da ace yanada I’ll be the first person to know.. My brother is single... Shifah wannan baida lokacin ‘yanmatan ma pride d’insa bazai bari ya nemi budurwa ba shiyasa nace miki idan kinyi hak’uri you can win him over...”

Kurb’an lemonade Yesmin tai tana jinjina kalaman Siyama...

A b’angaren Khalid kuwa Haurawa sama da yayi yaji dama bai shigo sashen Ammi ba gaba da’aya, Aunty Hidaya ya hango mahaifiyar Yesmin Yaya ga mahaifiyarsa....

Cikin sauri yasa kai zai juya saidai tuni Aunty Hidaya ta hangoshi, bud’e murya tai cikeda far’a kana tace “A’a Son suk’ar yaushe....?”

K’ak’aro murmushi yayi yace “I just arrived Aunt.... Mun sameku lafia....?”

Aunty Hidaya ta kuma murmusawa kana tace “Lafiya lau Saifullahi... Ya aiki...?”

Murmushi Khalid yayi don ita kad’ai ke ce masa Saifullahi kana yace “Lafiya Aunt... Aunt Ammi fah...?”

Aunty Hidaya tace “Ta shige d’aki but tana fitowa... inaga bathroom ta shiga....”

Jinjina kai yayi kana ya mik’e a d’an gajjiye yace “Ok Aunt idan ta fito a ce mata na dawo... zan wuce d’aki na d’an kwanta before magrib...”

Dakatar dashi Aunty Hidaya tai da fad’in “Kaga k’anwar taka a k’asa koh... Jiya ta dawo daga sch ta gama gaba d’aya sauran karb’an result, she was so excited sanda taji zanzo don ko hutawa batai ba tace zata biyoni Kaduna....” Ta k’arashe cikeda gwad’a d’iyarta Yesmin....

Tak’aitaccen murmushi yayi kana yace “Aunt I’m exhausted, see you later....”

Yana ida fad’in haka ya fice cikin sauri ba tareda ya bari ta kuma janyo wani zancen ba....

Kallo tabi bayansa dashi k’asar zuciyarta tana furta lallai akwai aiki da wannan baud’edd’en yaron....

****

Yana zuwa d’aki wanka yayi ya rage kayan jikinsa zuwa masu sauk’i kana ya mik’e kan gadonsa... Wayarsa ya janyo ya shiga duban lambar da ya d’aukesa lokaci a garin Kano kafin ya samu don neman lambar ne ma ya dad’a zaunar dashi....

Kallon lambar yake yana murmushi lokaci guda ya shiga tura sak’o yana mai ambatawa cikin zuciyarsa

_Karkiyi tunanin Khalid ya mance... No never, you must pay for what you did..._

****

Nabila ta kuma duban Addarta Zulfah a karo na biyu kana tace “Addah donma bakiga how Mamy scolded me bane ranan da nazo na jima, is like Mamy gani take Aunty Bara’atu is nothing but a bad influence to her children, gani take wajenta nake koyo duk wani rashinji... Yanzu ma bance mata ga yanda zaje ba kawai tasan dai zan shiga sch registration ne dashike an koma....”

Zulfah ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana ta kamo hannayen Nabilah tace “Kiyi hak’uri Sis ni na janyo miki....”

Girgiza kai kurum Nabilah tai kana tace “A’a you don’t have to apologize, I’m your sister, when ever you need me.... I got your back....”

Rungumeta Zulfah tai cikeda farin ciki suka ci gaba da firansu....

Daga yanda Aunty B ke tsaye jinjina kai tai k’wayan idanunta suna kuma kad’awa, ‘yar uwarta Mariya bazata tab’a daina kallonta a matsayin mutuniyar banza ba, tun suna k’ana haka ta d’auketa har sukayi aure, har izuwa lokacinda iyayensu suka rasu suka barsu..... Hannu tasa ta goge hawaye guda da ya gangaro mata bata iya shiga d’akin ba sai juyawa da tayi da baya....

“Ya Kausar..? Kinje kin dubota...?” Zulfah ta tambaya damuwa kwance saman fuskarta....

Girgiza kai Nabilah tai kana tace “Banje ba tukuna amma In sha Allah daga nan zan biya...”

“Yaya Hafiz fah.... Yana zuwa gida...?”

Saida Nabilah ta aika mata wata kallo kana tace “Toh ni ina ruwana dashi da har zan fahimci yana zuwa ko bai zuwa....”

Zulfah bata kuma cewa komai ba tinda ta fahimci tambayar Hafiz ya sanya ran ‘yar uwar tata b’aci....

Mik’ewa Zulfah tai ta bud’e drawer ta zaro wasu ‘yan kud’ade kana ta mik’awa Nabilah tace “Gashi ki sai mata tsara idan zakije and please hug her for me... Kema ga wannan ki sai maku wani abin keda Marliya....”

Kallonta Nabilah tai ta kalli kud’ad’en kana tace “Addah save your money, now that you’ve to face another life zai maki amfani, nida Marliya bamu buk’atan komai, zandai karb’i na Kausar na sai maita...”

Girgiza kai Zulfah tai kana tace “Karki damu na karb’i alawee na ne na wannan watan, I’m still saving some, sannan babu abinda Aunty B bata min kinji koh so ki kwantar da hankalinki.... Inaso na kira Mamy but banso ta fahimci komai cikin muryata... Can you please hug her for me...” Ta k’arashe idanunta na rau rau....

Hannayenta Nabila ta rik’e cikeda tausayawa kana tace “Komai zai wuce Addah... Kar ki mance masu iya magana sunce INDA RAI DA RABO... Watarana zaki bud’e idanu ki tarar komai ya wuce, rayuwa ta zamto sabuwa mai dad’i, all your nightmares zasu gushe kinji koh... Never lose faith...”

Jinjina kai Zulfah tai kana tace “Allah yasa k’anwata...”

Nabila ta sakar mata sassanyar murmushi....


Sun jima suna tattaunawa kafin Nabilah ta d’auki jakarta da ‘yar folder d’inta ta makaranta tai masu sallama....

Tana tsaye tana neman adaidaita sak’o makamancin na jiya ya shigo mata daga lambar da bata sani ba...

Karancewa tai had’ida jan tsuka ta danna delete, bata kuma bi takai ba ta tari adaidaitan ta ta nufi gidan Hajiya.....

Saida ta tsaya bakin babban kwalta tai sayayyan kayan mak’ulashe na yara wa Kausar kafin ta nufi gidan...

Akayi sa’a bata tadda Hajiya ba, da alama harta yaran Hajiyan ma basa nan, Raihanah kawai ta tadda zaune bakin barandar Hajiya suna wasa itada Kausar...

Sosai Nabila taji dad’in ganinsu haka, tayi tsaye tana dubansu fuska fal fari’a....

Kausar ince ta fara hangota ta shiga d’aga hannaye sama tana dariya alamun ta ganeta....

A guje Nabila ta tafi ta d’aga yarinyar sama tana cillawa Raiha na dariyarsu...

D’an gefe dasu Nabilah ta zauna Raihana na mata sannu da zuwa...

Fuska a sake Nabila ta amsa kana tace “Yau ku kad’ai ne a gidan...?”

Jinjina kai Raiha tai kana tace “Sun fita gaba d’aya d’iyar k’awar Hajiya ta haihu yau ake suna....”

Nabila ta jinjina kai don taji dad’in hakan zata samu ta tambayi Raihana kalan goyon da ake baiwa d’iyar ‘yar uwarta.....

“Raiha ki fad’imin gaskiya please Ya rayuwar Kausar yake hannun Hajiya da iyalanta....?”

Take idanun Raihana sukai rau rau, lokaci guda tasa bayan hannunta ta goge hawayen kana tace “Addah Nabila ko ban fad’a miki ba kinsan irin rayuwar tsanar Addah Zulfah da sukai yayi tasiri ga rayuwar innocent Kausar... Addah Nabila banso Kausar tayi irin girman da nayi.... Inso taji dad’i ta rayu da mahaifiya tasan soyayya da shak’uwa irinta mahaifiya wanda ni na rasa tsawon rayuwata....” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata...

Nabilar ma k’walla ne suka ciko idanunta, tai k’ok’arin dannewa don k’arfafa gwiwan Raihana kana ta kamo hannayen Raihana ta rik’e cikin nata lokaci guda take furta “Komai zai wuce Raiha, komai zai zama labari.... Hak’urinki bazai tab’a tafiya kawai ba, zaki cimma wani mataki na rayuwa da yardar Allah.... Believe me INDA RAI DA RABO.....” Ta k’arashe tana k’ak’aro murmushin k’arfafa gwiwa....

Jinjina kai Raihana tayi had’ida sakin murmushi kana tace “Haka ne Addah Nabilah wataran komai zai zama labari...”

Nabila ta sakar mata murmushi kana ta mik’a mata ledar hannunta tace “Ga wannan sai ki adana mata please...”

Cikedajin dad’i Raihana ta amsa tana mai godiyawa Nabilar domin ita duk wanda zai k’aunaci Kausar ya gama mata komai, har cikin ranta takejin yarinyar...

Koda Hajiya da iyalanta suka dawo basusan anyi hakan ba, toh mai ma ya shallesu dasu, Hajiya ce ma mai d’an k’ok’arin kulada Kausar sabida jinin d’anta dake jikinta Najah kuwa ‘yar ko oho ce abinda Sahariyya ta d’aurata akai take bi, ita kuwa Sahariyyar tinda Hafiz ya mata kaca kaca akan Kausar ta kuma d’aukan karan tsana ta d’orawa yarinyar, batak’i ta wayi gari ta tadda yarinyar ta mace gaba d’aya ba, k’ila da har party saita had’a sabida farin ciki....

***

Shigowarta gidan kenan, dawowarta daga office ta hangi mota pake gefen flowers tamkar nasa, gabanta ya fad’i... For the first time da tab’a jin shakku cikin zuciyarta shin tana farin ciki ne da ganin Partner ko kuwa akasin hakan......


*SameenaAleeyou📚*
*INDA RAI*
_...............DA RABO_




*21*





*©Sameena Aleeyou...✍🏽*






Tijjani mai bayiwa flowers ta kirawo tana tambaya......

“Tijjani motar waye wannan....?”

Da tsananin mamaki Tijjani ke dubanta don a tunaninsa idan kowa zai mance kamannin motar Sameer ai ita bai kamata ace ta mance ba.....

Sosa kai Tijjani yayi kana yace “Hajiya ai motar Datta ne.... Bai jima da isowa ba .....”

Jinjina kai tai had’id lumshe idanu, da gaske Sameer na cikin gidansu, abinda ya faru last week ya shiga mata yawo a kwanya, tunanin ta yanda zata soma fuskantarsa ya addabeta, gani take tamkar Sameer zai fahimci wani abin....

Saida ta sauk’e deep breath kafin ta iya samun strength ta bud’e motar ta fice....

Kallo guda zaka mata ka fahimci tsananin sanyi da jikinta yayi, a hankali tasa hannu ta tura k’ofar parlorn, ba kowa sai Yesmin dake aikin kallo....

“Hi cousin...” Yesmin tace tana sakar mata murmushi...

Murmushin itama tai k’ok’arin maida mata kana tace “Are you alone....?”

Yesmin ta jinjina kai tana mai gyara zama saman sofa take fad’in “Eh Mummy da Ammi sun fita, Ya Khalid kuma yana tareda bak’o a sashensa.....”

Jinjina kai Siyama tai kana ta nufi upstairs don yin wanka, shiga tayi cikin sauk’ak’an kaya, doguwar riga mai laushin gaske as usual kai a bud’e....

Tsintar kanta tai da kasa fitowa daga d’akin sai faman sak’e sak’e take, bata tab’a tunanin cire cikin nan zai dameta irin haka ba, har cikin ranta take jin bazata iya fuskantar Sameer ba, what if ya ganeta..? What if ya tambayeta.... Mai zata soma ce masa....?

A hankali ta lumshe idanunta tana mai ayyanawa this is the best for the both of them.....

Parlorn ta nufo tana mai shafa samar wayarta a daidai lokacinda Khalid da Sameer suka shigo parlorn...


Daga can ya hangeta saman bene tai looking very pale kaman tai ciwo, gaban Sameer ya yanke ya fad’i cikin sauri ya nufi yanda take tsaye ta kasa motsa koda ‘yar yatsanta ne....

Khalid kam cikama rigarsa iska yayi musamman da ya hangi wannan yarinya mai uwar rawar kan a parlor, gaba d’aya ya fice daga gidan don dama Sameer ne ya zaunar dashi.....

Kallon juna suka shigayi tamkar wanda suka jima basuga juna ba, murya can k’asan mak’oshi Sameer yace “Partner...!”

K’wallan da Siyama ke mak’alewa ya gangaro mata... Sameer bai wata wata ba ya rungume matarsa tsam cikin jikinsa...

Fad’i yake “I’m here Partner... I’m here...”

Sosai Siyama ta kwanta cikin k’irjinsa tana sakin kuka a hankali, abinda ta rasa na ‘yan kwanaki... Batai zaton tayi kewar mijinta har haka ba...

Ita kuwa Yesmin yanda kasan ta sami tv haka take kallonsu, batai zaton ana irin wannan soyayyar a nigeria ba Nigeria d’in ma arewacinta.... Sun bala’in birgeta, Ita da Khalid kawai take hangowa cikin fuskokinsu, lallai cousin d’inta nada babban sa’a dama wannan shine mijin nata, he’s every woman’s dream... Gaskiya Siyama ta cab’a don babu macen da bazata so wannan had’edd’en gayen yake mutuwa akanta ba, gaba d’aya sun tafi da ita uwa wani duniya musamman data kuma jiyo muryar Sameer cikin damuwa yana furta

“Partner are you sure you’re fine... look, kalli fah.... kalli yanda kika koma... My goodness Siyaam have you been eating...? Talk to me...”

Ya k’arashe yana rik’e arms d’inta had’ida d’an jijjigata kad’an...

Harara ta d’an jefa masa kana tace “What do you expect Partner bayan ka tafi ka barni... So abinci ma bazanci da kyau ba....”

Murmushi ya sakar mata wanda ta jima bata gani ba kana yace “I’m sorry honey, zamu tafi tare wannan karon....”

D’an zaro idanu tai tana dubansa bata kai ga magana ba su Ammi sukayi sallama....

Sameer ya d’anyi k’ok’arin zare jikinsa daga na Siyama cikeda kunya yana d’an sosa k’eya ya nufo parlorn gaisar dasu Ammi...

Ammi fad’i take “A’a Dr sauk’an yaushe..? Sannu da zuwa lale...”

K’arasowa yayi ya zauna saman carpet yana mai gaidata...

“Mun sameku lafiya Ammi...”

Ammi tace “Alhamdulillah Sameer, ya aiki...”

Amsa mata yayi da angode Allah kafin Aunty Hidaya tace “Wannan ne sirkin namu..?”

Ammi tace “Gashi nan fah sirkin naki...”

Sameer ya duk’a ya gaidata itama cikeda karramawa, Ammi tai introducing Aunty Hidaya da d’iyarta Yesmin....

Yesmin ta mik’e a guje tabi bayan Siyama zuwa kitchen yanda ta tadda Siyamar ta saka Kubura ta markad’e masa lemun abarba...

Rungumeta Yesmin tai tana fad’in “Cousin kin gama dacewa kekam babu abinda ya miki saura,this kind love ku bar mana saura nida Khalid....” Ta k’arashe tana d’an daka tsalle...

Kubura da ta kafeta da idanu dariya ta kwashe dashi kana tace “Iska na wahalda mai kayan kara....”

Yesmin ta juyo a kufule tana dannawa Kubura muguwar kallo don dama tun zuwanta gidan jininsu baizo d’aya ba ta lura son gulma ne da ma’aikatan...

“Mai kikace...?”

Yesmin ta tambaya...

Kubura ta d’ago idanu kana tace “Au wai ni... Bance komai ba...”

Siyama ta danno mata mugun kallo kana tace “I know you Kubura mai kikace...?”

Kubura tace “Haba Aunty kinsan dai bana miki k’arya wannan yarinyar kawai k’aunata ce batai... Kuma ni naga ba son Khalid nake ba koh Aunty...” Ta k’arashe tana duban Siyama...

Siyama ta murmusa don ta lura har yanzu Kubura bazata daina haukan da take da wauta akan Khalid ba a baya ta zaci tsaban yarinta ne amma yanzu ta lura hauka kurum Kubura keyi, gashi ko hanyar da Khalid d’in ya taka idan ance tabi bazata bi ba tsaban tsoronsa da take...

Girgiza Siyama tai kana taceda Yesmin “Rabu da ita cousin haka take...”

Yesmin ta kuma galla mata harara kana tace “I heard her loud and clear fah wllhi tace wani abin k’ilanma zagina tayi...”

Kubura ta kuma watso wata maganar a hankali kafin Yesmin tai magana taceda Siyama “Aunty ga lemun yau dai zamuyi kewarki a gidan nan tinda Likita ya dawo gashi baki bani na kati ba yau.....”

Tak’aitaccen murmushi Siyama tai kana tace “Wai ke Kubura kullum sai an baki na kati waima waye kike kira....?”

Kubura ta zaro idanu kana tace “Aunty donma bakiga yanda a facebook samari ke bina ina masu wulak’anci ba sabida ni inada mijina gangariya ko kulasu banayi...”

Saida Siyama ta dara kana tace “Ko kuma kece iskan ke wahalwa... Kinga ki shirya yanzu ki tafi gidana kije ki kintsa gidan kafin mu k’araso.... Ki haura sama ki d’auko min handbag d’ina...”

Cikeda jin dad’i Kubura tace “An gama Hajjaju tamu Allah dai ya kare mana ke hasken zuciyar Dapta...”

Janyo hannun Yesmin Siyama tai suka fice tana fad’iwa Kubura “Ni ki wuce kafin daren ya idayi....”

Kubura sai murna take tasan yau tim Siyama zata cika mata aljihu.. Ta raka Yesmin da harara tana fad’i bayan sun fice...

“Kuji wannan abin meyema Khalid d’ina zaiyi dake..? Wllhi yafi k’arfin ajinki, nan gani nan bari akwatin maye... Duk barikancinki bazai k’yalla idanu kanki ba ehe... Banza kawai, ni yanzu daga Facebook ma makaranta zan koma sabida na lura Khalid d’ina asalin d’an boko da gayu ne ...” Ta k’arashe tana jan dogon tsaki had’ida sauya taku.....

Hhhhhh Wayaga su Kubura mata a gidan Khalid...

***


*Kano*


Banda taunar chewing gum bata komai sai wani d’add’aga idanu sama take tana tafiya tana bankad’a k’irji gaba, a yatsine ta k’araso teburin da yake kana tace “Ina saurarenka....”

Kallo ya bita dashi yanda tai masa tsaye aka kana yace “Ki zauna mana....”

Saida ta d’auki lokaci tamkar bazata zauna ba sai kuma ta finciko kurar ta zauna had’ida bashi baya tana mai ci gaba da taunar chewing gum...

“A haka ne zamuyi maganar...?” Ya fad’i yana yana mai d’an rank’ofowa....

Hannu ta d’aga masa cikeda tsiwa take fad’in “Kaga Hafiz nifa ba k’aramar yarinya bace da zaka nemi rainan wayo, idan magana kakeso muyi kayi maganar gaskiya ka turo gidanmu idan kuma ba haka ni kada ka sake zuwa wajena don wllhi bazan baka kaina ka watse dani a waje ba kaman yanda kayi da wancan ‘yar agwagwan ehe...”

Ta k’arashe tana mai danna masa aya.....

K’uri kawai Hafiza ya mata yama rasa mai zaice mata sai sunkuyar da kansa da yayi yana sosa goshi a hankali.....

Alhaji Tanimu mai kula da ginin da ake a gefen Kantin ne ya shigo yana faman washe mata baki, da gayya Sawwama ta mik’e ta nufesa cikin yanayin tafiyarta anayi ana rawa da k’irji ta isa gareshi tana fad’in “Alhajin kowa mai za’a kawo maka...?”

Bai daina yak’e baki ba yake fad’in “A kawo min tuwo ‘yar kyakkyawa...” Ya k’arashe idanunsa k’yam a k’irjinta...

A fusace Hafiz ya mik’e ya nufi Alhaji Tanimu zai kai masa naushi nan fah yaran Alhaji Tanimu sukayo kansa... Magajiya mahaifiyar Sawwama ta nufosu gadan gadan tana k’ok’arin rabon fad’a.. Sai fincika Hafiz yake yana fad’in Uban mai Alhaji Tanimu ke kallo jikin matarsa...

Sawwama bata tab’a sanin Hafiz na sonta haka

Please Login or Register in order to submit comment