Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace “Alhamdulillahi Allah ya kawoka, wato a gaskiya mun damu matuk’a da abindake wakana cikin gidanka, tun jiya abu yak’i ci yak’i cinyewa... Don munso kiran jam’ian hizba tun a jiyan amma wasu daga cikin committee na unguwa sukace mai gidan baya nan a bari nan da zuwa kwanaki uku idan har bai dawo ba sai a zattar da hukunci don bai kamata a apka masa gida kai tsaye ba dukda irin abubuwan dake faruwa cikin gidan....”

Hafiz da har lokacin yawun bakinsa a k’afe yake, da k’yar ya lalumo kalamai saman harshensa yace “Malam Sambo wani abu ne ke faruwa cikin gidan nawa....?”

Mutuminda ya kirada Malam Sambo bai kaiga basa amsa ba d’aya mutumin gajeren cikinsu yace “Kai kurma ne... Shin baka jiyo sautin kalangu da ‘yandaudu dake tashi cikin gidan... Kaga sam bazamu lamunci wannan abu ba, tarbiyan yaranmu muke jiyewa don haka dole ka tashi ka bar unguwar nan matuk’ar iyalinka zata maida gidanka gidan baje kolin shaid’anu... Haba ace an yini an kwana zubur ana abu guda tun jiya, babu dare babu rana babu sararawa balle sanin lokacin sallah, toh sam bazai yuwu ba mu bamu saba ganin irin wannan d’abi’a a unguwar nan ba, bazai yuwu a kawo mana gidan bori a unguwa ‘yan daudu da lalatattu suke mana safara ba, ya zama dole mu d’au mataki....”

D’ayan ya jinjina kai yace “Wannan hakane, unguwar nan an mana shaida mai kyau bazamuso rana tsaka wani ko wata ya kawo mana mishkila ba... Kuma tinda ka jima a unguwar hakan bata tab’a faruwa ba sai yanzu...”

Hafiz ya lumshe idanunsa a hankali hawaye masu d’umi suka zubo masa.... K’unci sun taru sun masa yawa a zuciyarsa.... Suna nan tsaye shida mutan unguwa wasu mazan suka fito daga cikin gidansa rungumeda ‘yanmata...
D’aya Dattijon ya furta “Subhanallahi... Ka gani koh, kaga irin musiban dake faruwa tun jiya a gidanka.... Toh ya zama wajibi ka d’auki mataki kokuma mu mu d’auka....” Daga haka tafiya sukai suka barsa nan tsaye yana mai bin’yandaudun da zasu shige cikin gidansa da kallo...

Da k’yar yake d’aga k’afafunsa ya nufi cikin gidan.... Hankalin Hafiz bai ida tashi ba saida yayi arba da masu kalangu da gurmi tsakiyar gidansa suna bugawa hayak’in kayan maye na tashi wasu watsattsu suna rawa maras kyaun gani.... Tuni wasu ‘yandaudun suka nufosa suna kai masa runguma, wannan ya jasa ta nan wancan ya janyoshi tacan....
Ganin bai kulasu ba da alama ma hankalinsa bai taredasu yasa d’aya d’andaudun gyara d’aurin k’irjinsa yana wani kareraye hannaye had’ida taunar chewinggum yake fad’in “Ohni ‘yar mamata shiko wannan kodai ‘yan matan basa gabansa ne... Kin gansa fah zalzal dashi...”
Baibi takansu ba ya shiga raba idanu ta yanda zai hango Sawwama, yana danna kai a parlornsa k’auri da hayak’in kayan maye suka kusa kifar dashi, nan ma wani kayan tashin hankalin ya tadda, banda watsewa babu abinda ake... Wa’iyazubillah...Bai ida ganin babban tashin hankali ba saida ya danna kansa a bedroom d’insa yanda ya hangi matarsa da mazaje kusan uku akan gadonsa.... Zuciyarsa ta buga da k’arfin gaske.... Yayi saurin kauda kansa yana mai rintse idanunsa, jiri mai k’arfin gaske yaji na yunk’urin kifasa... Innalillahi wa innalillahi raji’un... Shi tinda yake bai tab’a ganin musiba k’arara irin haka ba, duk abubuwan da yayi marassa kyau a baya bai tab’a cin karo da shed’anu irinta yau ba... Shi bai tab’a zaton Sawwama takai har haka ba.... K’afafuwansa ne suka silale sai jinsa kurum yayi ya zaune a k’asa a nan wajen, hannunsa dafe da k’irjinsa dake tsananin masa zafi....

***

Wurgi Siyama tai handbag d’inta saman kujera tana mai bin Nabilah da kallon k’yama.... Lokaci guda ta saki murmushi kana tace “You again.... Wato baki daddara ba koh.... Shine kika biyoshi har gida... Shin wai ana soyayya dole ne.... My brother doesn’t love, why is it so hard for to understand....”

Murmushi Nabilah ta saki kana ta mik’e tsaye ta tako gaban Siyama... Murmushin bai bar saman fuskarta ba take furta “Oh really?... The last time I checked ya zab’i ya rabu da family d’insa duk a sabidani.... So think kinyi kuskure a nan... Sannan ni kad’aice zan iya convincing Khalid ya dawoga iyayensa don nasan martaba da matsayin iyaye, idan ya zab’i wannan hanyar toh kuwa tabbas zaiyi nadama da danasani a gaba, bazanso ya kasance cikin masu hasara ba, domin kaw duk mai fad’a da iyaye yayi hasara....”

Siyama tana mai ci gaba da aika mata harara ta nufi sama tamkar zata tashi sama tana mai k’walla kirawa Ammi....

A daidai lokacin Alhaji Yusuf Mainasara yayi sallama cikin parlorn...

Nabilah tai saurin mik’ewa tsaye tana duban mai sallaman, Dattijon mutum cikin shiga ta kamala manyan kaya, tsananin kamanninsu da Khalid ta hango wanda ko ba’ace ba wannan shine mahaifin Khalid....

Tai saurin sadda kanta k’asa sanda Daddy ke k’arasa shigowa cikin parlorn yana mamakin baiga komai ba sai wata matashiyar budurwa duk yanda matarsa Hajiya Farida ta d’aga masa hankali cewa maza maza yazo parlornta, a zatonsa wani abinne ya faru ko kuma wani ne babu lafiya...


Ammi da Yesmin dake lab’e jikin staircase tsgege Siyama tai tana dubansu,
“What’s all this Wai meke faruwane...? Me wancan yarinyar takeyi a parlor... and naji kaman sallaman Daddy....?”Ta tambaya tana mai ci gaba da dubansu....
Cikin sauri Ammi ta toshe mata baki tanai mata alamu da yatsa cewa tai shiru.... Lokaci guda ta kwantar da murya a hankali tace “Tarkonmu ya d’anu, Yanzu abinda za’ai Siyama maza maza ki kira d’an uwanki ki fashe da kuka ki sanar dashi ga ‘yar iskan yarinyar nan ta biyo Daddy har gida har parlorn Ammi, make him believe yarinyar ‘yar hannu ce.... Oya Oya wuce mana.....” Ta k’arashe tana hankad’a Siyama d’aki... Siyama na fad’in “Haba Ammi ya zamuyi ma Daddy haka... You’ve gone too far gaskiya... Nidai bazan iya ba gaskiya....”
“Aw kinfi so ya aureta koh... Toh ai shikenan, kina dai gani wannan shine damarmu...”
Yesmin ta marairaice fuska tace “Haba cousin do this for me please... Ta haka ne kurum zan mallaki Khalid... Please...” Ta k’arashe kaman zatai kuka....
Juya idanu Siyama tai had’ida fuzar da iska kana tace “Alright fine naji...” Yesmin ta buga tsalle harda rungumeta don murna...

A can parlor kuwa tuni Nabilah ta durk’usa gaban Daddy tana gaishesa cikin murya mai taushi idanunta a k’asa.... Tinda yake tsakaninsa da ‘ya’yensa babu wanda ya tab’a masa irin wannan gaisuwar...
Daddy ya mata k’uri kana yace “Yarinya daga Ina... wajen Farida kikazo..? Ko wajen Siyama....?”

Nabila ta girgiza kai a hankali still idanunta na k’asa kana tace “A’a Daddy wajenka nazo....”

Gyara tsayuwarsa yayi da kyau kana yace “Wajena kuma....?”

Ta jinjina kai a hankali kana taci gaba da fad’in “Eh Daddy wajenka....”

Wannan karon zama yayi bisa kujera kana yace “Toooh... Daga ina kenan... Sannan maike tafedake...?”

Har lokacin Nabilah na durk’ushe gabansa kana tace “Daddy is about your son Khalid...”

Wannan karon annurin fuskarsace ta d’auke cak kana yace “Tooh... What about my son... Turoki yayi kokuwa dai kece yarinyar da ya bijire ma umarnina akanki....?”

Ta girgiza kai cikin sauri hawaye na k’ok’arin ciko idanunta take furta “A’a Daddy, Khalid baisan nazo nan ba, hasalima banason ya sani... Daddy Khalid mutumin kirki ne don Allah kada kayi fushi dashi, na sani wasu lokutan yanada nasa matsalolin but believe me he’s a good man... He’s only human, Please Daddy don Allah ka yafe masa ka dawo dashi gida, ka tuna girman fushin iyaye, ka tuna yardar iyaye na tareda yardar Allah... Daddy idan baka yafe mishi ba rayuwarsa tana cikin garari....”


SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_



62



*©️Sameena Aleeyou...✍🏻*




NOT EDITED




Daddy yai k’uri yana dubanta ba tareda ya furta koda kalma ba.... Tamkar wanda aka zabura ya mik’e ya shiga nuna mata k’ofa yana furta “Get out... Fice min a gida nace... Awho wato kinje ya tsaro maki abinda zakizo kice koh... Idan har da gaskene yana son yafiyata yazo da k’afafunsa ba Wai ya turo wani ba.... Zoki fice nace and don’t think of coming back.....”

Su Ammi dasu Siyama dake lab’e jikin bene a idanunsu komai ke faruwa...
Idanun Nabilah sukai rau rau... “Daddy Dan Allah hear me out....!” Ta fad’i tana mai kuma duk’awa k’asa....
Ammi ta dubi su Siyama ta k’yafta masu idanu, lokaci guda suka fito Ammi na fad’in “Tashi ki fice bamu son salon munafunci....” Ta k’arashe tana mai janyo Nabilah da hawaye ke zubo mata... Lokaci guda Ammi ta shiga hankad’ata bakin k’ofa yayinda Daddy ya haye sama yana nazarin yarinyar da maganganunta....

Har haraban gidan Ammi ke hankad’o Nabilah tana fad’in “Bak’ar munafuka baki tsaya kan d’ahanah ba harda mijin nawa shima tallata masa kanki zakiyi... Toh wllhi k’aryarki tasha k’arya, ke ni nan nafiki bariki wllhi... K’aryar rashin kunya kike...” Ta kuma hankad’ota ta fad’i har k’asa wannan karon....

K’afafun mutum ta gani tsaye gabanta, tai k’ok’arin d’ago idanu don gani ko wanene.... Ba kowa bane illa Khalid.... Fuskarsa ta sauya launi haka idanunsa...
Ammi bata daina huci tana jifan Nabilah da munanan kalamai ba yayinda Siyama ke tayata, itako Yesmin k’ok’arin b’oyewa bayan Ammi take sakamakon hango tsagwaron tashin hankali da tai cikin idanun Khalid....

“That’s Enough Ammi!!!” Ya fad’i yana mai duban mahaifiyar tasa...
Harara taci gaba da watsa masa kana tace “Awho kazo kabi bayanta ne bayan duk abubuwan da ‘yar uwarka ta sanar dakai a waya... Khalid shin kai wane irin shashasha ne... Maiyasa bazaka bud’e idanunka kaga kalan yarinyar nan na asali ba, ina ka tab’a jin budurwar arziki ta biyo saurayinta har wajen iyayensa, for once open your eyes and see what’s right....”

Girgiza kai Nabilah take tana duban Ammi, wannan karon da muryar tsiwa take magana dukda hawaye dake fitowa daga idanunta “Ni bashi na biyo ba, ni wajen Daddy nazo...”

Ammi da yaranta su Siyama da Yesmin baki sake suke dubanta kafin Ammi tace “Awho kaji koh... Kaji da kunnuwanka koh, mahaifinka ta biyo...”

Nabilah ta kuma rintse idanunta jin irin fassaran da Ammi take mata, Yesmin da Siyama suka shiga tafe hannaye suna salati suna taya Ammi...
Khalid da tuni ya gama zuwa wuya rasa abin fad’i yayi sabida wani irin zafi da zuciyarsa ke masa ganin yanda mahaifiyarsa take abunda sam babu girma cikinsa, ita dasu Siyama sam basuda maraba....
Lokaci guda Nabilah ta bud’e idanunta dake jik’e da hawaye jin munanan kalaman dasu Siyama suke jifarta da ita sunyi yawa ciki harda Daddynsu yafi k’arfinta saidai taje can ta nemi wasu love life d’in irinta ba Daddynsu ba ba kuma brother d’insu ba...

Fuskokinsu take duba kana ta goge hawayenta, cikin huci take furta “You know what... You should go ahead and believe whatever you want to believe... I don’t give a damn.... Ya rage naku..”
Ta maido da dubantaga Khalid kana taci gaba da fad’in “And you... Ya rage naka to fix your relationship with your parents..... Forget I ever exists...” Daga haka goge hawayenta tai kana tasa kai cikin huci zata shige....
Cikin sauri Khalid yasha gabanta shima hucin yake, su duka biyun suna aikama juna muggan kallo....
Fuzar da iska ya d’anyi kana yace “So tell me, mai ya kawoki gidanmu....? Huh talk to me...? What if wani abin ya sameki, just what were you thinking...??” Ya k’arashe Yana mai zaro idanunsa waje...

Murmushin takaici tai kana tace “Isn’t it obvious... Tinda kai baka san girman iyayenka ba, ni bazan bari ka zab’i hanyar da sam bazaikaika ga dacewa ba... Do you think I can leave my family for you...? Well no, bazan tab’a barinsu ba, idanda ace zasu zab’a min miji, ko wane iri ne zan amsheshi hannu bibbiyu matuk’ar zai faranta masu sabida na sani bazasu tab’a zab’a mun abinda zai cutar dani ba...” Muryarta ya soma rawa sosai sanda taci gaba da fad’i cikin taushi “So please just end this right now, ka basu hak’uri sannan ka karb’i zab’insu....”

Da tsananin mamaki yake dubanta wannan karon, he just couldn’t believe it, Teddy Bear ce take cewa su rabu for good...
“What did you say...?” Ya furta a hankali....

Jinjina kai tai kana tace “Yes you heard me loud and clear.... Don’t ever think of me again...!” Ta kuma sa kai ta shige cikin sauri hawayen da take dannewa na zubo mata... Tamkar wanda ruwa ya shanye haka Khalid yai tsaye a wajen... Ba Ammi kawai ba harta su Siyama tsaye sukai suna duban Khalid wanda ya koma tamkar ruwa ya shanye....
Ammi ta janyo hannayen yaranta su Siyama da Yesmin tana mai masu alamu da bakinta cewa suyi shiru su shige cikin gida kurum su k’yale Khalid da alama burinsu ya cika Khalid da Nabilah sun rabu rabuwa ta har abada....

Cikin sauri ya shiga bin bayanta yana furta “Hey hey!!...” lokaci guda ya finciko hannunta ta dawo da baya tana mai furta “Don’t touch me...!”
Tsaye kurum Khalid yai yana kallon yanda hawaye ke zuba daga idanunta.... Gaba d’aya sai yaji babu dad’i ya tuna a halinda ya risketa da mahaifiyarsa da kuma ‘yanuwansa, kalan wulak’anci da cin zarafin da ya tadda suna mata.... A hankali yake furta “Did they hurt you... Let me see are you hurt...?”

Cikin kuka take furta “Kar ka matso yanda nake, kaje kaji da iyayenka they’re all that matters....”
Hango hannayenta yayi yanda suka kukkuje... A hankali ya dafe kansa yana mai fuzar da iska lokaci guda yake furta “See, kin gani koh... Shiyasa bansan mai ya kawoki nan ba... Gashi nan sunji maki ciwo, do you think I can bear seeing you hurt...You know you’re so naughty....” Da zafi zafi yayi maganar...

Daddy dake tsaye balcony d’insa yana hangosu daga yanda yake, k’arasowa kusa sosai yayi yana mai sauraronsu...

Nabilah taci gaba da fad’in “Among the two of us who’s been naughty... huh? So kake Ina gani ka d’auko hanyar halak’a na k’yaleka... Do you even think zan barka ka zab’i hanya maras d’aurewa, hanyar da zai kaikaga halak’a... Well, no.... Ko mai zasumin I don’t care as far as hakan zaisa ka sami amincewa da yardar mahaifanka domin yardarsu na tareda yardar Allah ne...” Ta d’an sassauta murya kad’an kana tace “Please enough of this already.... Let’s go our separate ways...”

Murmushin k’arfin hali Khalid keyi kana ya matso da fuskarsa dab nata, lokaci guda yake fad’in “And who told you sabida ke na tafi na bar gida..? Oh c’mon give me break princess.... Kawai bazan tsaya amin auren dole bane, don har abada bazan tab’a son yarinyar da suke so na aura ba, I’ll rather die than na auri wannan yarinyar kin fahimta....?"

Nabilah tai shiru tana dubansa yanda yake huci, tabbas har cikin ranta taji babu dad’i da yace ba sabida ita ya bar gida ba.... Lokaci guda tai kicin kicin da fuska kana tace “Well, yayi kyau... Thank goodness cos I don’t want to be in the image.... Rayuwarkace kayi yanda Kaso da ita Allah ya gani na fad’i gaskiya na fita... And ka sanar da wannan abokin naka kada ya sake kirana....” Cikin tsiwa tai maganar wanda yasa Khalid murmusawa don ta juye masa Nabilar da ya soma sani had’uwarsu ta farko...
Ya bud’e murya yace “Fine naji... Zan amshi zab’insu...”

Cak Nabilah ta tsaya tana saurarensa lokaci guda yaci gaba da furta “And zan fice daga rayuwarki na har abada, badon komai ba sai don banaso wani cikinsu ya kuma hurting d’inki....”

Ta rintse idanunta hawaye masu d’umi suka zubo mata...
Khalid yayi k’arfin halin furta “Alright Miss Grumpy nayi binda kikeso ki tsaya muyi proper goodbye please....”
Bata tsaya ba saima sauri data k’ara tamkar zata kifeda k’asa.... Khalid yayi saurin bin bayanta amma ko kad’an bata bari ya cimmata ba....
A hankali ya furta “I love you... And I’ll always does....” Ya lumshe idanunsa siririyar hawaye ta sauk’o masa...

Daddy da komai ya faru akan idanunsa a hankali ya koma da baya ya zauna yana mai nazarin abinda ya faru tsakanin Khalid da yarinyar nan, idan ya fahimci wani abu shine yaran suna tsananin son junansu kuma dukansu sun sadaukar da farin cikinsu ne domin kare junansu, amma idan har abinda Farida take fad’i kan yarinyar gaskiya ne mai yasa baiji ajikinsa yarinyar tanada wani aibu ba....? Toh amma bijire masa da Khalid yayi fah...? Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ya dauk’i ruwa dake saman k’aramar table ya kurb’a...

Nabilah tana isa mota ta rungume Aunty B tana kuka sosai....
Aunty B jiki a sanyaye ta maida mata martananin rungumar kana tace “Let it out daughter... Yi kukanki....”

Saida tayi mai isarta kafin ta iya furta “Aunty na rabuda Khalid rabuwa ta har abada....”
Aunty B ta kuma rungumeta tana share mata hawayenta take furta “This is for the best Nabilah, hakan yafi tinda danginsu sam basa k’aunarki.... Kuma tabbas kinyi k’ok’ari da har kika taso kika nunawa Khalid rashin dacewan abinda yayi, k’arshen soyayya da zaki masa kenan ki nusar dashi kuskure babba da yayi a baya domin al’amarin iyaye nada girman gaske, Allah ya zab’ar maku abinda yafi zama alkhairi a gareku baki d’aya kedashi....”
Jinjina kai kurum tai ba tareda ta iya furta koda kalma ba kana suka d’auki hanyar gidan wata k’awar Aunty B domin su d’an yada gajjiya su kuma yi sallah kafin su d’auko hanya don basuso dare ya masu....

***

Tamkar maras numfashi haka Hafiz ke zube a wajen, koda motsa ‘yar yatsansa ne ya kasa, ya kwashe kusan sa’a guda zube a wajen gashi babu abinda aka fasa a cikin gidan saima wasu sabbin ‘yandaudu dake shigowa cikin gidan.... Ashe Wai hakance take faruwa idan d’aya daga cikinsu yayi aure toh fah sai sunzo sun had’a masa kalan tasu bukin shine sallamarsu tsakaninsu dakai, toh ita Sawwama ba’ai mata nata ba sai yanzu....
D’andaudu guda ne ya kusa tuntub’e da Hafiz ya doka salati yana dafe k’irji ganin mutum zube a wajen... Lokaci guda yake furta “Na shiga uku ni Lanti waye haka nan zai kadani k’asa ya tonan asiri ya ragen farashi.....” Ya shiga haske fuskar Hafiz sosai da d’an tocilan jikin wayarsa, lokaci guda ya saki shewa yana fad’in “Kai kai kai kuzo Yo ai ni na taki sa’a nai babban kamu, wannan zankad’ed’en saurayi haka...” Ya shiga shafa fuskar Hafiz yana kareraya... Maganganunsa ya janyo hankulan sauran ‘yan uwansa ‘yandaudun suka d’ungumo sukayo kan Hafiz kowa na masa nasa salon karya jikin....
D’ayan yana fad’in ku bari a bisa a sannu inaaa gaba d’aya sunyi chaa akan Hafiz har saida hankalin Sawwama yazo garesu, tayo kansu tana fad’in “Toh Lanti wa kuka samu haka, kwayi hak’uri ku barma guda d’aya ai.....” Batakai aya ba sukai idanu hud’u da Hafiz dake zube wajen yana numfashi da k’yar....
Sawwama ta dafe k’irji tana fad’in “Na shiga uku mijin nawa....”
Lanti yace “Aaaaah kice abin du namu ne... Ayyiriri gaskiya kin iya zab’e k’awata Yo dole kike b’oye mana shi ashe... Yau dai sai a barmu mu d’anah....” Ya k’arashe yana tafe hannaye....
Sawwama ta shiga turesu tana fad’in “Banson iskanci kunajina koh, kowa ya fice min a d’aki ku jira daga waje.....” Ta k’arashe tana k’ok’arin d’aga Hafiz....

Da k’arfin gaske ya fincike daga rik’on da ta masa yana mai tsananin huci dukda zogi da k’irjinsa ke masa.... Lokaci guda ya capko wuyanta ya shak’e da duka k’arfinsa, wasu irin ruwa suna fitowa daga idanunsa da suka koma tamkar jan gauta har saida ya danganata da jikin garu... Cikin wata irin dashesshiyar murya mai cikeda firgici yake furta “Wllhi yau sai na kasheki.... Matsiyaciya muguwa azzaluma.... Kin rabani da matata Kamilan mace natsestiya wacce batada kusanci da irin halayyanki, kin kashe Kausar, kin halak’amin rayuwa... Kaman yanda kika kashe mun aurena da d’iyata Wllhi sai na kasheki nima....” Ya kuma danne wuyanta sai zaro ido take tana yunk’urin yin nishi har saida’yan daduronta sukayo kan Hafiz suna yunk’urin janyesa... Wasu kuwa suka fice a guje don kar ayi kisa suna wajen, mai kalangu da garayama ya cika ma rigarsa iska a guje....

Da k’yar suka iya janye Hafiz daga shak’anda yayima Sawwama.... Yaci gaba da huci hawaye masu tsananin zafi suna ci gaba da zubo masa.... Fincika yake daga rik’on da suka masa yana fad’in duk wanda ya kuma zuwa kusansa sai ya kasheshi...
Sawwama ta mik’e da k’yar tana mai watsa masa harara take fad’in “Koda wasa kada ka saka ka kuma cewa ni na kashe maka aurenka da d’iyarka, ka fara zargin kanka kafin ka tuhumi wani don duk abinda yake faruwa yanzu are consequences of your actions, kuma da kake cewa na kashe d’iyarka da aurenka uwarka da ‘yanuwanka zaka soma tuhuma baniba don ni tayasu kawai nayi.... Sannan da kake cewa nida tsohuwar matarka mun banbanta naga nidakai duk kanwar jace, nasan baka fasa komai ba a halayyanka don haka koda wasa kada na kumaji ka zageni... Sannan bari kaji na fad’a maka babban kuskuren da zaka tapka shine kayi tunanin rubutamin saki don wllhi sai ka fice min cikin gida, Don idan baka sani ba ka sani a lokacin da baka a hayyacinka lokacin da asiri ke tasiri akanka tsaf na sakaka ka sauya takardun gidan nan zuwa sunana, kuma babur d’inka da aka sace ba sacewa akai ba nice nan na sa aka d’aukemin, harta kantinka da ya kama da wuta ba Wai tsautsayi bane, a’a nice nan na saka aka kwashemin kayan ciki na kuma bada umarnin a bankama kangon gini wuta sabida gudun rana irinta yau ranan da zakace zaka rabu dani... Domin ni nan daka ganni duk abinda kaga nayi toh fa sai idan zan sami riba a cikinta... Don haka ka tattara k’afafunka ka fice min a gida tun kafin nasa su lallasa maka bugu ko ka sakeni ko baka sakeni ba na saku don bakada sauran amfani wajena.... Kai kira saminu gurmi ya sake mana sabon kid’a.....” Ta k’arashe tana juyi yayinda sauran ‘yantashan nata suka tayata da ele da gud’a....

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un........ Abinda zuciyar Hafiz ke iya nanatawa kenan.... Wani hadiri hadiri da taurari yake hangowa cikin idanunshi, mai ya jefa kanshi ciki....? Shin anya Sawwama ‘yar adam ce...? Kenan gaba d’aya rayuwarsa ita ta kassara masa... Mai ya mata da tsananin haka....? Ya rintse idanunsa yana mai ci gaba da jefa k’afafunsa ba tareda yasan yanda ya dosa ba....

Suna tafe cikin motar driving kurum yake amma mind d’insa was somewhere else, Shamsu ya kula da hakan don ‘yan kwanakin sam baya gane abokin nasa, yasan definitely akwai abindake damunsa kuma koda bai fad’i mashi yasan it has to do with his wife, tinda yanzu Sameer ya samu iyayensa baida sauran damuwa da ya wuce matarsa, d’an dubansa Shamsu ya kuma ganin yanda yake driving d’in tamkar mai shirin barin gari, a hankali ya furta “Doc please drive slowly kasan banyi aure na ije iyali ba so banyi shirin mutuwa ba ka gane....”

Sameer ya jefa masa harara kana yace “Toh ai ita ba’a mata shiri, shiyasa idan kayi niyya maza kafin k’arshen shekara ka cikawa Mama burinta ka kawo mata sirka...”
Shamsu ya murmusa yace “Na fad’a maka ai na gaji da wannan gorin tsaf zan baku mamaki daga kai har Maman...”

Sameer ya tab’e baki yace “Ba fad’a a baki ba a dai aiwatar sai mu yarda....”

Nan ma murmushin Shamsu yayi kana yace “Yauwa speaking of aje iyali, Wai har yau Siyama bata dawo ba....? Sameer are you ba wata matsala....?”

Kallonda Sameer d’in ya jefa masa ne ya sanyashi d’an yin shiru kana yace “Look I’m sorry, I didn’t mean to intrude kawai na damu dakai ne shiyasa na tambaya....”

Sameer baice komai ba sai d’an duban gefen kwalta da yayi yana mai kuma k’ara speed....Sam bai kulada mutumin dake tafe tsakiyar kwalta d’in ba...
Shamsu ne ya soma hangosa ya shiga salati yana fad’iwa Sameer mutum gabansu.... Sameer ma salati ya soma yana k’ok’arin danna birki had’ida danna hannunsa gaba’a d’aya kan horn amma inaaa ya riga ya hauro saman kwaltan sosai ji kake k’iiiiii k’aran birki ga kuma mutumin da suka bige kwance gefen kwalta......

Cikin sauri suka firfito waje suka nufi mutumin da suka bige wanda ke zube saman kwalta bakunansu d’aukeda ambaton Allah


“Hafiz...!” Sameer ya furta a hankali...
Shamsu ya dubesa yace “Ka sanshi ne...?”

Jinjina kai yai kana yace “Cousin d’inane.... Taimaka min muyi sauri mukaishi asibiti...” ya fad’i yana mai nannad’e hannun rigarsa had’ida sunguman Hafiz Shamsu na taimaka masa, suka sakashi cikin mota kafin suka nufi asibiti mafi kusa.....




SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_




*63*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*


NOT EDITED



Mamy ta kuma jan gajeren tsaki a karo na biyu sanda ta kuma dialing wayar Nabilah tajita a kashe, ga magariba ta sako kai, bata saba kaiwa haka a

Please Login or Register in order to submit comment