Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fahimci yana cikin damuwa, ga Sawwama na tsananin fushi dashi sabida amanartarda sukaci shida aminiyarta ga matarsa bata nan.....

Ya jima a parlorn har baisan sanda bacci yayi gaba dashi ba yana nan rik’eda waya yana jiran ko kiran Sawwama zai shigo....

Bashi ya farka ba saida gari yayi haske sallah yayi kana ya shirya cikin sauri ya nufi gidan Abbah kafin Abbah ya tafi Kasuwa....

Ya kuwa taki sa’a Abban bai fice ba, Mamy ya tadda da Nabilah na tayata shirya kayan karin kumallo saman darduman Abban wanda yake cin abinci bisa....

Nabila tana ganinshi haka yaci uban wanka harda hula gabanta ya yanke ya fad’i domin kuwa sam bataso Ya Hafiz ya fara zuwa ba, bataso a soma jin zancen ta bakinsa don tasan yanzu sai ya iya canza zancen...




SameenaAleeyou 📚
[10/01, 19:22] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_...............DA RABO_



*16*





*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



Abbah bai daina bambamiba yana fad’in rashin kunya irinta yaran zamani da sam basu ganin girman dattijai....

Maganganun mutumin ya sanya Sameer saurin fitowa daga motar da niyyar basa hak’uri domin kuwa sam ba d’abi’arsa bace cin zarafin d’anadam ballantana har dattijo kaman wannan, sosai yake ganin girman nasa iyayen da bazaiso wani ya wulak’antasu ba don haka shima bazai wulak’anta tsohon wani ba...

“Baba dan Allah kayi hak’uri bada nufi nake maka horn ba kayi hak’uri don Allah......”

Wani irin bugu k’irjin Sameer yayi a sakwanni sanda sukayi eye contact da mutumin nan, a b’angaren Abbah ma babu sauk’i take yaji bugun zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, wannan k’wayan idanu tabbas yasan irinsu, wannan fuska tabbas yasan makamancinsa, tamkar an tsunduma a fridge haka jikin Abbah yayi sanyi, Sameer bai daina duban mutumin ba yanajin wani irin yanayi maras fasaltuwa a tattaredashi....

Ganin mutumin ma bai daina dubansa ba ya sanyashi matsawa baya a hankali ko zai samu sauk’in bugun zuciyarsa kayi... K’aran wayan salulan Sameer ne ya dawo dasu duniyar da tunaninsu ya barota....

Cikin sanyin jiki Sameer ya d’aga wayar yana satan kallon mutumin da ya kasa daina dubansa...

“Yes, yes gani nan zuwa In sha Allah....” Daga gani daga asibiti aka kirasa...

A hankali yasa kai zai koma ya shige motarsa Abbah yayi saurin k’arasawa ya damk’o kafad’ar Sameer guda.....

Shock d’in da Sameer ya tsinci kansa ciki har yafi na ganin Abbah da yayi....

A hankali yake kaikaito da kansa har ya sauk’e k’wayan idanunsa kan hannun Abbah yanda ya masa wani irin damk’a....

“Saurayi nan gaba ka dinga kula idan kana tuk’i....”. Cewar Abbah cikin dakewan murya...

A hankali Sameer ya jinjina kai kana yace “Na gode Baba...”

Daga haka cikin sauri yasa kai ya nufi motarsa Abbah bai daina duban yanayin tafiyarsa ba....

Har ya tada mota sai kuma ya juyo ya hangi mutumin nan dai na nan na kallonsa suka kuma had’a idanu....

Kashe motar Sameer yayi ya kuma fitowa ya nufi mutumin, ganin haka yasa Abbah saurin juyawa ya nufi motarsa data kasa tashi don dubata....

Yana tsaye jikin bonnet d’in motar Sameer ya k’araso ya tsaya dab gefensa, Abbah saiji yayi hannun saurayin nan saman nasa yana k’ok’arin amsar abin gyaran....

Abbah ya d’ago idanu ya dubi kafad’unsu yanda ya tsaya dai dai tsawonsu dai dai babu wanda ya d’ara wani, gabansa ya kuma yankewa ya fad’i babu wanda yazo zuciyarsa face d’ansa Ma’aruf, da ace yana raye da yana around shekarun wannan matashin ne, ya tuna Ma’aruf na yaro wani rana sun fita tun a lokacin Abbah yana caring and loving father kafin ya zamto abinda yake a yanzu, Ma’aruf na tsalle a wuyan Abbah yana furta “Abbah watarana zan kamoka tsayi idan na girma...?”

Abbah yaja hancinsa had’ida manna masa sunba a kumatu kana yace “K’warai kuwa masoyina, zaka kamoni tsayi harma ka k’etarani.... Amma bazaka k’etarani ba sai na tsufa sosai na koma tafiya a durk’ushe idan Allah ya ara mana kwana...”

Ma’aruf ya rungume mahaifinsa yana fad’in “Abbah na bazai tab’a tsufa ba...”

Abbah ya rungumeshi cikeda so da k’auna yanai masa shillo.....

K’aran tashin motarsa ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, Sameer ya sakar masa murmushi yana fad’in “Ta tashi Baba zaka iya tafiya yanzu....”

Abbah da tun b’acewar d’ansa ba kasafai yake murmushi ba sai gashi ya murmusa a hankali yana duban Sameer, k’arasowa yai zai shige motar kana yace “Na gode saurayi...”

Sameer ya jinjina kai yana furta babu komai Baba kana ya nufi nasa motar cikin sauri don yasan shi kad’ai ake jira a asibiti...

Har saida motarsa ta rab’a ta gefen na Abbah kafin ta shige ya kuma yin horn had’ida d’aga hannuwa Abbah shima Abban ya d’aga masa hannu yana mai bin motar tasa da kallo sai sannan Abbah ya tuna bai tambayeshi sunanshi ba....

Abbah ya kwanta jikin car seat had’ida lumshe idanu yana mai gargad’iwa zuciyarsa cewa wannan bazai tab’a zama Ma’aruf ba domin kuwa d’ansa Ma’aruf ya jima da mutuwa shi ya sani ya kumaji hakan a jikinsa, zuciyarsa ce dai mai neman kawo masa rud’ani yanda yake gab da shekarun girma..... Kasuwar da bai iya zuwa ba kenan a dole ya koma gida ya kwanta a d’akinsa...

Aunty Lami da fitowarta kenan daga kitchen nan ta hangi tamkar wucewar mutum sashen Abbah bacin tasan tuni Abbah ya fice kasuwa....

Cikin sauri Aunty Lami ta nufi sashen Abbah....

Ga tsananin mamakinta kishingid’e ta taddasa saman kujera a parlorn nasa, waje ta samu ta zauna daga gefensa tana tunanin anya lafiya....

***

Ammi ta kuma d’aga kwalin maganin dake gefen gadon Siyama, mummunar fad’uwan gaba ya sauk’ar mata, d’ago idanu tai ta kuma duban Siyama dake duk’unk’une cikin bargo tana bacci...

Ammi ta shiga girgiza kai tana furta “Oh no no no what have you done to yourself Siyama....”

Ta kuma bud’e drawer d’in tana d’add’aya da magungunan....

B’uruntun binciken da Ammi keyi ya d’aga Siyama daga bacci....

Cikin sauri ta shiga fuzge magungunanta hannun Ammi tana fad’in “Haba Ammi you know I hate it when people spy on me...”

Ammi ta girgiza kai tana dubanta kana tace “Siyama ki fad’a min gaskiya meye wannan, wato zancen da Kubura kemin tayi daidai... Siyama ciki kika cire...? Talk to me..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya...

A hasale Siyama tace da ita “Yes Yes Ammi I had an abortion....Ammi I’m not ready to take responsibilities for God’s sake... And please do not pressure me...” Ta k’arashe tana kuma nitsewa cikin lallausan blanket d’inta....

Girgiza kai kurum Ammi tai kana tace “Siyama mai kika zama kenan, ki kashe d’anki da kanki... Anya kinada lafiya kuwa....?”

Mik’ewa Siyama ta kumayi tana dubanta kana tace “Ammi please enough..... Abinda ya riga ya faru ya faru a ra’ayina babu haihuwa nan kusa maybe a gaba in the future.....”

Ammi ta jinjina kai cikeda tsananin takaici kana tace “Kinyi adalciwa mijinki...?”

Dubanta Siyama ta kumayi kana ta d’an tab’e fuska tace “Mijina always supports me, so na tabbata shima yaji haka babu abunda zai damesa... Ammi please understand ba kowa bane keda ra’ayin haihuwa, koda d’an nan yazo duniya bazaiji dad’in rayuwa da iyayensa ba domin kuwa zai kasance ne like a mistake so please ki daina damuwa Ammi, idan grandchildren kikeso Khalid zai haifa miki kinji koh...”

Girgiza kai kurum Ammi take tana duban Siyama da tuni tayi tunanin ba cikin hankalinta take ba kana tace “Don’t say I did not warn you, wataran d’an da kika ciren nan zaki nema da kud’inki, too bad lokacin bazaki samu ba...”

“And I don’t care Ammi...” Ta fad’i tana duban mahaifiyar tata....

Shigowar Khalid ya katse tartaunawar sun....

K’arasowa yayi ya d’an rungume Ammi kad’an kana yace “Goodmorning beautiful...”

Ammi ta murmusa had’ida jan sumarsa kad’an tace “Morning Son... An fito...?”

Jinjina mata kai yai yana kurb’an shayinsa a hankali kana yace “Yes Mamy, Abbah yace yana son sak’on ya isa Kano a yau...”

Jin ya ambaci Kano yasa Siyama dubansa...

Ammi ta jinjina kai kana tace “Toh Allah tsare hanya, ka kula da kanka kaji koh....”

“Insha Allah Ammi...” Khalid ya fad’i yana duban Siyama da tamkar batta a wajen....

Saida ya matso dab da ita kana ya d’an rank’wafo yace “Karki damu I’ll drove by and say hi to your husband... Sai kuma na sanar dashi rashinsa ya saki ciwo....”

Pillow d’in dake gefenta ta d’auka ta jefawa Khalid yai saurin kaucewa yana dariya nan suka soma kasa hali Ammi na rabon fad’a....

***

“Alhaji lafiya dai ko...?”

Aunty Lami ta tambaya tana duban Abban....

Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya yai kana yace “Lami shin idan mutum ya mutu yana dawowa...?”

Wani irin k’ugi da murd’a cikin Aunty Lami ya bada lokaci guda, gabanta yai mummunar fad’uwa...

Cikin inda inda take furta “Haba dai Alhaji ya kake irin wannan tunanin... Ina ka tab’a jin wanda ya mutu ya dawo...?”

Abbah ya jinjina kai kana yace “Haka ne...”

Daga haka bai kuma ceda ita komai ba sai mik’ewa da yayi ya fad’a uwar d’akinsa k’afafunsa na masa nauyi....

Wani irin kallo mai cikeda firgici da fargaba Aunty Lami ta rakasa dashi, dukda d’an sanyi dake kad’awa a garin bata daina jin gumi na tsartsafo mata ba... Tambayar kanta ta dingayi maiyasa Abbah zai mata irin wannan tambayar....

***

Zulfah ta kuma duban Nabila a karo na biyu tsananin mamaki kwance saman fuskarta... Anya Hafiz ne har zai mata wani halacci a rayuwarta... Kai kodai wani tuggun yake k’ulla mata...?

Muryar Nabila ya kuma katse mata tunaninta....

“Addah bansan maiyasa ya b’oyewasu Abbah ba amma dai ni a ganina ki sanar dasu kar yazo a gaba ya k’ulla miki wani sharrin...”

Duban Nabila tai sanda take maganar kana ta girgiza kai a hankali tace “Nabila idan har shi bai sanar dasu ba nima bazan sanar dasu ba sabida bashi Abbah zai la’anta ba ni zai tsinema ya kuma cireni cikin ‘ya’yansa, na tabbata bazakiso kiga rana makamancin wannan ba a matsayina na ‘yar uwarki...”

A hankali Nabila ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Toh baki tunanin Aunty ta fad’awa Mamy...?”

Girgiza kai Zulfah tai kana tace “Mun riga mun gama magana da Aunty B, zan zauna a nan tareda ita har lokacin da naji na sanar da mahaifana hasalima ni yin shirun da Ya Hafiz yayi yafimin... Idan na ida bautar k’asana har aiki Aunty tai alk’awarin samar min, sanin lafiyar Kausar ne kawai damuwata...” Ta k’arashe damuwa kwance saman fuskarta....

Hannayenta Nabila ta kamo kana tace “Kar ki damu Addah idan don wannan ne ni zanke dubo miki ita In sha Allah koda Hajiya dasu Sahariyya zasu hanani...”

Zulfah ta jinjina kai tana mai k’ak’aro murmushi had’ida rungume ‘yar uwar tata tace “Na gode Nabila...”

“Babu godiya tsakaninmu nidake abu guda ne..” Nabilah ta fad’i tana maida mata martanin murmushin nata...

A haka Aunty B ta shigo ta taddasu tausayinsu ya rufeta nan ta umarcesu su fito suje kitchen baki d’aya tasan hakan ka iya d’ebe masu kewa...

Yini zubur Nabila tai saida ta tuna Mamy ta haneta da yin dare kafin ta soma shirin tafiya...

***

Misalin k’arfe biyar na yamma bayan ya gama huta gajjiyan hanyarsa a hotel d’in Tahir guest in da ya sauk’a nan ya kira Sameer ya sanar dashi location d’in da zai samesa....

Tsaf Khalid ya shirya cikin k’anan kaya royal blue shirt ta amani da kuma bak’ar jeans sai watsa k’amshi yake as usual ya nufi motarsa ya d’auki hanyar da Sameer ya sanar dashi map na directing nasa daga cikin wayarsa...


Daga can mai adaidaita ya ijiyeta sai buga sauri take don tasan by this time Abbah ya dawo daga Kasuwa...

Bata ankaraba saiji tai ruwan tab’o ya wanketa har fuskarta....


SameenaAleeyou 📚
[10/01, 19:22] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_..............DA RABO_




*15*





*©Sameena Aleeyou...✍🏽*





Tsananin mamaki ya kama Nabilah da Mamy ganin Hafiz harda duk’awa yana gaida Mamyn abinda bai tab’a koda kwatantawa ba gaba d’aya rayuwarsa....

Yawa mutunin arziki haka ya sadda kai yana tambayan Mamy ko Abbah ya fice Kasuwa ne...

Mamy kaw cikeda jin dad’i tace dashi “A’a bai fice ba Yana nan tukuna....”

Hafiz ya jinjina kai yana d’an murusawa kana ya dubi b’angaren Nabilah da tayi sakare tana dubansa yace “Nabilah ya hutu ko har kun koma ne...?”

Badon Mamy na wajenba kuma bataso ta fahimci komai ba tareda ta gane nufin Ya Hafiz ba da ta k’wand’ara masa zagi ta ruga a guje....

Da k’yar ta furta “Umm bamu koma ba...”

Mamy tace “Ya Hajiyar taka...?”

Nan ma fuska a sake yace “Hajiya na nan lafiya, amma ban shiga ba ma dama sai na fice a nan ne...”

Mamy ta jinjina kai cikeda jin dad’i kafin Hafiz ya kuma duban Nabilah yace “Ya kamata kizo ma Addar taki d’an hutu ai kafin ki koma sch.....”

Da tsananin mamaki Nabilah ke was dubansa tama rasa abin fad’i, batakaiga bada amsa ba Abbah ya fito cikin shiri....

Gaba d’aya suka soma gaidashi, shi kanshi Abban ganin Hafiz da farar safiya ya sanyasa yin tunanin ko akwai matsala ne...

Koda suka gaisa da Abbah tambayar Hafiz d’in Abbah yayi ko lafiya ko akwai wata matsala ce...

Hafiz yace “A’a Abbah lafiya lau babu wata matsala....”

Abbah ya jinjina kana ya kuma fad’in “Yaya iyalin naka, da fatan dai lafiya kuke zaune...?”

Nan ma Hafiz jinjina kai yai yace “Lafiya lou muke zaune Abbah babu wata matsala...” Ya k’arashe suna mai had’a idanu da Nabilah...

Shi kanshi ya fahimci tsananin mamakin dake kwance saman fuskar Nabilah kuma ya fahimci Zulfah ba gida ta taho ba hasalima bata sanar da iyayenta komai ba, wannan shine kawai gatan da zaiwa Zulfah bayan zaman hak’urin data kwashe a gidanshi bazai tab’a bari iyayensu susan cewa aurensu ya k’are ba.....

Mamy ce ta umarci Nabilah da ta d’auko wa Hafiz plate da cup ya karya kumallo...

Nabilah ta fice jiki a sanyaye tana tunanin wannan kuma wane kalan tuggu Ya Hafiz ya k’ulla....

A daidai hanyar ficewa daga sashen Abbah Hafiz d’in ya cimmata, kiran sunanta da yayine ya sanyata tsayawa cak tana masa duba irinta bak’in munafuki....

“Ina Zulfah...?”

Tambayar da ya mata kenan....

“Ai kai zan tambaya mai kake shirin k’ullawa Ya Hafiz, maiyasa baka sanar dasu Abbah gaskiya ba....?”

Murmushi yayi kana yace “Nabilah kenan, ki tsammanin sanar dasu bazai raba tsakaninsu da Zulfa’u bane musamman Abbah....?”

Cikin huci Nabila tace “Toh meye manufar b’oyewarka, shin wannan bashine abinda kullum kake fata da burin ya sami ‘yar uwata ba yanzu da burinka ya cika mai zai hanaka jin dad’i kardai kacemin son Addah Zulfah kake...?” Ta k’arashe tana murmusawa....

Gajeren murmushi yayi kana yace “Idan kina tunanin zan tab’a son Zulfah kinyi kuskure... Iyakacin abinda zan mata kenan bayan hak’urin zama a gidana da tai shine na rufa mata asiri kada Abbah ya tsine mata bayan cutar farin k’afa da take fama dashi.... Amma kuma idan kuka bari akaji there’s nothing I can do, ki sanar da ‘yar uwarki ko a ina take, she decides for her life....”

Daga haka tab’e baki ya d’anyi had’ida d’aga kafad’a kad’an kafin ya koma parlorn Abbah hula a karkace....

Shiru tai tana dubansa ba wai don zuciyarta ya kwanta da abinda yake fad’i ba, itakam sam bata yarda da Ya Hafiz ba ta tabbata he’s up to something, mai zatai yanzu, tai shiru ne ko ta sanarda Mamy ne.... Toh ko dai ta soma kiran Addah Zulfah ne ta sanar da ita....?”
Jiki a sanyaye ta wuce kitchen...

Ita kanta Mamy canzawan Hafiz ya dameta Abbah dai dashike ba mutum bane mai yawan magana ko saka hankalinsa ya abu sam bai d’ago hakan ba, tun bayan b’acewar babban d’ansa Ma’aruf ya koma hakan, gaba d’aya sai ya zama wani irin murd’edd’en mutum and hard to deal with....

***

Fuskarta da idanunta sunyi luhu luhu alamun dare jiyan bata samu ta rintsa ba, a haka Aunty B ta shigo ta taddata gaba d’aya sai tausayin Zulfan ya rufeta, ta kasa daina tunanin laifin duk nata ne ita ta kashe mata aure....

Daga can gefen gado ta zauna tana mai k’arewa ‘yar ‘yar uwar nata kallo....

Zulfah ta d’ago kod’add’un idanunta had’ida k’ak’aro murmushi ta soma gaida Aunty B....

Aunty B ta amsa fuska d’aukeda murmushi zuciyarta kuwa k’unshe da tausayin Zulfa’un....

“Nasan daren jiya baki samu kin rintsa ba sannan shi aure ko yaya yake idan akace ya mutu dole rai ya sosu, Zulfa’u kiyi hak’uri, kiyi hak’uri don Allah wllhi ba ke kad’ai ba ni kaina banyi bacci yanda ya kamata ba, ki gafarceni don ji nake tamkar ni na kashe miki aure dukda ba son zamanki a gidan Hafiz nake ba.....”

Zulfah ta k’ak’aro murmushi had’ida share hawayen da suka zubo mata kana ta matso ta kamo hannayen Aunty B ta rik’esu cikin nata kana tace “A’a Aunty ko kad’an babu laifinki ciki hasalima haka Allah ya k’addara iyakacin wa’adin zamana kenan da Ya Hafiz.... Aunty damuwata Abbah... Aunty mai zance mishi... Shikenan tsinuwarshi zai bini... Aunty idan yace na tafi na nemi wani uban ina zanje....?” Ta k’arashe hawaye masu d’umi na kuma gangaro mata....

Rungumeta Aunty B tai tana shafa bayanta take fad’in “Let it out, kiyi kukanki Zulfah, sannan Abbah kuma kar ki damu I’ll take responsibilities of everything..”

Girgiza kai Zulfah tai cikin hawaye kana tace “No Aunty.... Bazan iya zuwa gidan ba don Allah ki barni na zauna taredake a nan please Aunty...”

Shiru tai tana duban Zulfan cikeda tausayawa kana tace “Idan hakan kikeso shikenan bazan tak’uraki ba sannan nima bazanso mahaifinki ya miki baki ba, amma baki tunanin idan shi mijin naki yaje ya fad’i komai, sannan al’amari irin haka ba’a shiru Zulfa’u.....”

Girgiza kai tai a karo na biyu kana tace “Nidai don Allah Aunty ki barni a nan koda zai sanar dasu...”

Jinjina kai Aunty B tai had’ida sauk’e nannauyan ajiyan zuciya, cikin kwantar da murya taceda Zulfah “Naji Zulfa’u In sha Allah zaki zauna a nan gidan iya lokacin da kikeso kika kumaji ki tunk’ari mahaifanki da batun nima na samu ‘yar tayin zama tinda Major yakan tafi can kudu ya shafe watanni, maza tashi muje kiyi breakfast....”

Zulfah ta k’ak’aro murmushi kafin ta mik’e tabi bayan Aunty B....

***

Shamsu na zaune parlor yana kallon tashan wasan k’wallon k’afa daga yanda yake zaune yana hango abokin nasa sai faman kai komo yake yana kuma shafa waya yana mannawa a kunnensa, ko ba’a fad’i maka ba kasan waye yake nema cikin wayar...

Shi kad’ai sai faman fuzar da iska yake yana fad’in “C’mon Partner pick up your phone.... What’s wrong what’s wrong what’s so wrong Siyaam...?”

Kaman daga sama saiji yai ta d’aga wayar....

Cikin sauri ya fice ya bar Shamsu na ihun team d’insu taci ball...

Murya cikeda damuwa yake furta “Siyama what’s all this, meyasa kika kashe wayanki... I’ve been trying to reach you for good two days Siyama... What have I done to deserve such punishment Partner...? My goodness I was so worried about you, and ban kira Ammi ba cos banso hankalinta ya tashi... Are you sure you’re alright Partner...?”

Ciza lab’e ta kumayi sabida mararta da har yanzu yake mata zogi kana tace “Oh really Sameer, did you really miss me...? Ko kuma kana can kanajin dad’inka acan ka k’yaleni a nan ba...”

Fuzar da iska yayi had’ida girgiza kai mai hali dai baya fasawa, shin yaushene Siyama zata daina samun doubts gameda shi.... Shin kalan nata soyayyar kenan...

A hankali ya furta “There you go again, Siyama yaushe zaki daina doubting d’ina, shin kinsan matsayin aure mai k’unshe da zargi....? Why Siyama.... Shin soyayyar da nake nuna miki ne na gaza ko meye laifina...?”

D’an lumshe idanu tai kana tace “I miss you Partner, yaushe zakazo...?”

A hankali ya lumshe idanu don ya fahimci topic d’in taso canzawa kana yace “Soon weekend in sha Allah.....”

K’irjinta ne ya bada wani irin sauti don bataso yazo ya fahimci wani abin tafiso ta zama fully recovered kafin yazo... Cikin d’an In ina tace “No karka tak’ura kanka, karka stressing kanka da yawa ka bari next weekend sai kazo nasan yanayin aikinka babu dare babu rana sannan har weekends ba wani hutawa kake ba, kadai bari next weekend sai kazo banso kayita jele saman kwalta ga yanayin hanyoyin namu a yanzu....”

Da k’yar ta k’arashe maganar sai faman tamke idanu take tana rik’e mararta...

Sauk’e ajiyan zuciya yai kana yace “Shikenan idan kince haka....” Seconds suka d’an gifta kana yace “Partner...”

Ta amsa da fad’in “Yes Partner...”

A hankali ya furta “Always remember that I love you... Ko a ina zan kasance inasonki....”

Jikinta ya d’anyi sanyi ba tareda tasan dalili ba, a hankali ta furta “Nima ina sonka Partner... Ka kula da kanka please...”

“You do the same...” Ya fad’i kyakkyawan murmushi kwance saman fuskarsa...

Suna ida waya da Siyama ya kira Mummynsa suka gaisa don through out yinin ranar bai samu ya kirata ba, sosai Sameer ke k’aunar iyayensa....

***

A b’angaren Siyama kuwa jigum tai tana duban pills d’in dake hannunta ta kasa afawa baki, gaba d’aya ta rasa sukuni cikin zuciyarta tun bayan faruwan wannan al’amari, da k’yar ta samu ta afa magungunan kafin ya kurb’i ruwa ta mik’e saman gadonta had’ida lumshe idanu ko baccin dole zai gaba da ita domin sam babu bacci cikin idanun nata....

****


Washe gari da sassafe Nabila ta soma shirin tafiya gidan Aunty Bara’atu, Mamy dai na hankalce da ita domin ta kula tun jiyan Nabila ta canza sosai tamkar wani abin na damunta, saida ta ida shirinta tsaf Mamy ta zauna gefenta had’ida ambato sunanta tareda jefo mata tambaya

“Nabilah kin tabbata lafiya ce zata kaiki gidan Auntyn ku da farar safiyar nan... Ki sanar dani idan akwai wani abinda ya kamata na sani...”

K’ok’arin saita kanta Nabilah tai dukda tsoro dake kwance k’asar zuciyarta gani take tamkar Mamy na iya reading mind d’inta... Saida ta d’an dara had’ida saka wasa wanda dama d’abi’artace kana tace “Kai Mamy yanzu bazanje gidan Aunty B ba sai babu lafiya.. Kawai nafison fitan safe ne sabida babu ‘yan sa ido sosai kinsan yanayin unguwar nan anjima kad’an zaki soma ganin suna fitowa da bencinansu....”

Mamy ta jinjina kai tace “Shikenan Allah ya tsare, ki d’aga posata akwai naira d’ari biyu ki d’auka kiyi kud’in abin hawa...”

Nabilah ta jinjina kai had’ida furta “Toh Mamyna na gode....”

“Ki gaida Bara’atun....”

Nanma amsawa tai da zataji kafin tasa kai ta fice cikin sauri...

Fitarta da kad’an Abbah ya fito da niyyan fita kasuwa...Bai bar katangar gidansa ba motarsa ta tsaya ta kasa tafiya abinka da sharrin k’arfe....

K’iris ya rage motar bayansa bata bugi bayan nasa motar ba....

Sameer da yaso makara sakamakon damunsa da waya da akai daga asibiti tuni ya danna hannunsa saman horn....

Iyakacin harzuk’a Abbah yayi, baisan sanda ya sab’a babbar rigarsa ba yasa kai zai fito daga motar yana faman huci yake “Wai maiyasa mutane sam basuda hak’uri ne, kazo kabi ta sama idan ka matsu.....”



SameenaAleeyou 📚
[12/01, 15:25] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_...............DA RABO_




*18*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Kallo mai d’aukeda alaman tambaya Mamy ta jefa mata wanda ya sanyata saurin cire hannu a abincin ga k’irjinta dake faman lugude....

Murya a shak’e taceda yaron “Kai jekace masa bata nan....”

Mamy ta wurga mata mummunar kallo kana tace “Kinsan wanene...?”

Baki a ture Nabila tace “Mamy yo zai wuce munafukan unguwar nan ne ‘yan saka ido, Mamy Allah nidai yaje yace bana nan koma kawai yace bazanzo ba....”

Mamy ta jinjina kai had’ida yin k’wafa, mik’ewa tai ta nufin k’ofar parlorn ta d’aga labulen k’ofar yanda ta hangi Almajirin rakub’e daga bakin veranda...

Har k’asa yaron ya duk’a ya gaida Mamy ta amsa kana ta k’arada

“Yau an baku sadakan abincin dare...?”

Girgiza kai yaron yayi kana yace “A’a Hajiya....”

Mamy ta nufi kitchen d’inta dubo sauran abincin rana ta basu don dama duk ran girkinta sai ta basu sadakan abincin sun wadata shiyasa suka maida k’ofar gidan wajen zamansu, ranar girkin Hajiya Aunty Lami ne da sauk’i wani sa’in sai sun karad’a unguwar neman sadaka....

Mamy ta fito da sauran abincin rana cikin flask ta juye masa kana tace “Kaje ka tambayo wanene shi mai sallaman...”

Almajirin ya jinjina kai cikeda murna yace “Toh Hajiya...”

Jim kad’an yaron ya dawo had’ida kuma kwad’a sallama, Mamy da Marliya ce kawai suka amsa Nabila kam tayi kicin kicin da fuska tana satan kallon Mamy jira kawai take taji wani mai asaran lokacin ne yazo wajenta... Wani irin yankewa gabanta yayi ya fad’i sanda taji abinda yaron ke fad’i...

“Wai mutumin da ya b’ata mata jiki d’azu ne, wai zuwa yayi ya bata hak’uri...”

Mamy ta kalli Nabilah itama Mamyn take duba zuciyarta na harbawa....

Ba tareda Mamy ta d’auke dubanta daga Nabila ba take fad’in “Jekace babu komai ya wuce ba sai ya bata hak’uri ba koh....”

Yaron tamkar mai tsoron juyawa yace “Hajiya Allah bazai tafi ba don tun d’azun yake jiranta...”

Duban Nabila Mamy tai kana tace “Banson dogon magana tashi kije ki sallameshi kafin Abbanku ya fito sallahn isha ya taddasa....”

D’an k’ara murya Mamy tai sanda take fad’iwa yaron “Jekace tana zuwa...”

Yaron ya juya cikeda jin dad’i yana mai amsawa...

Fuska a turb’une ta mik’e ta suri hijabin dake gefen Marliya ta nufi k’ofa....

Kana ganinta

Please Login or Register in order to submit comment