Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya Allah kada ka barnida iyawata, Ya Allah ka zamto majib’icin lamurana....!!” Ta k’arashe tana mai duk’a gwiwoyinta gaba d’aya k’asa cikin wani irin kuka mai ban tausayi....
Naja’atu ce ta k’araso ta d’ago Hajiya Haule... Najah na hawaye take fad’in “Allah zai kare Ya Hafiz Hajiya... Kici gaba da masa addu’a....!”

Hajiya ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Najah lokaci guda take furta “Najah gidan Mariya zan tafi... Dole naje na rok’i yafiyar Mariya... Naji da kunnuwana ko ta yafeni wala’alla zan samu sassaucin wannan uk’uba na rayuwa da nake ciki...!” Lokaci guda Haule ta zari mayafi tana hawaye ta nufi gidan Abbah....

Naja’atu ta maidoda dubantaga ‘yan daudun kana tace “Ku kuma Allah yasa wannan ya zamto wa’azi a gareku ku gane cewa wannan hanya da kuka biyo ba turba mai kyau bace... Ita wacce kuka aminta da ita take d’oraku akan mummunar hanya na fasik’anci da sab’awa mahaliccinku gashi ta tabbata cewa azzalumarku ce.... Shin maiyasa zaku bijirewa rahamar ubangijinku...? Shin Maiyasa zaku maida kanku mata bayan Allah yayi ku maza...? Shin da Allah yaso da sai ya halitto duniyar nan Duka mata ko duka maza... Amma ba haka yaso ba, ya rabamu jinsu mabanbanta domin ya cika rahamarsa a garemu, sashenmu su samu natsuwa da sashe... Wannan rahamarsa ce a garemu... Ina fata daku da masu wannan mummunar d’abi’a irin taku zaku wa’azantu ku tuba ku karb’i halittar da Allah Yai maku a matsayin rahama a gareku...!!”

Tinda Naja’atu ta soma magana jikkunan ‘yan daudun nan yai sanyi sosai.. Kan kace mai sun soma warware zannuwan da suke d’aure dasu had’ida d’ankwalayen kansu.... D’aya daga cikin su yana hawaye yake furta “Wllhi gaskiya kika fad’i... Mu d’in mun kasance masu bijirewa rahamar ubangijimu... Daga rana mai kaman ta yau na daina Daudu kuma zan koma gaban iyayena na rok’i yafiyarsu...!” Ya k’arashe yana mai jifa da zanin hannunsa had’ida goge gazal d’in dake girarsa....
D’ayanma yai jifa da takalmin k’afarsa ta mata yana mai furta “Nima daga yau na daina kamanceceniya da mata, iyayena sunmin iyaka da gidanmu dan haka zanje na mik’a kainaga hukumar hizba su zasu taimaka su dank’ani ga iyayena... Allahu Akbar su Shazali ashe Magajiya ce ta kashesu....!” Ya k’arashe yana mai kuma matse k’wallan da suka ciko idanunsa...

Haka ‘yandaudun nan suka dinga tuba suna fad’in sun daina kamanceceniya da mata da dik wani aikin assha da suke... Daka masu cewa zasu koma garinsu gaban iyayensu sai masu cewa zasu mik’a kansu ga hukumar Hizba...

Sahariyya ta k’araso ta rungume ‘yaruwarta Naja’atu hawaye na gangaro masu su duka biyun....

***

A can gidan Abbah kaw Haule duk’e take gabansu tana kuka na nadama wanda bata tab’a irinsa ba...
Mamy dake hawaye a hankali ta kamo kafad’un Hajiya Haule ta d’agota, lokaci guda ta rungumeta ba tareda ta iya cewa komai ba sai hawaye dake gangaro mata....

Baba Alhaji ya d’an kamo gefen rigarsa ya share k’wallan da ya mak’ale masa a idanu shima.... Lokaci guda yai k’ok’arin saita kansa kana yace “Zama a nan bai ganni ba dole na tafi ga jami’an tsaro domin ceton rayuwar Hafiz....”

Mamy dake share hawayen idanunta jinjina kai tai kana tace “Wannan haka ne Abban Ma’aruf...!”

Haule dake rakub’e tai saurin cewa “Usman zanso naje dakai can wajen jami’an tsaron, zamana a nan hankalina bazai kwanta ba....!”

Abbah ya d’an dubi Haule kana ya dubi Mamy lokaci guda yake furta “Inaga ku zauna a nan zaifi... Ni zanje na sami jami’an tsaron....”

Haule na hawaye take fad’in “Dan Allah ka barni naje Abbah... Ina matuk’ar son sanin halinda d’ah na Ke ciki..!!”

Abbah ya d’anyi Jim kana ya jinjina kai a hankali... Mamy tace itama zata tafi taredasu... Gaba d’aya su duka ukun suka d’unguma suka nufi ofishin ‘yansanda domin filing report...
Har yanzu Abbah ya kasa gasgata Wai d’an uwansa Baba Alhaji zai iya aikata hakan wa Hafiz, d’ansa na cikinsa da ya haifa... Gaba d’aya jikin Abbah a matuk’ar sanyaye yake yana mamakin shin Baba Alhaji wane irin mutum ne mai matuk’ar son zuciya... Ashe dik abubuwan da suka faru basu ishesa ishara ba.... Can wani b’angare kaw na zuciyarsa yana fad’a masa rashin imanin Baba Alhaji bazai kai nan ba... Allah sa ba hakan bane da gaske... Dan dik abubuwan da yai masa bazai so ya tab’e har haka ba...

***

A nan hideout d’in nasu kaw suka had’u gaba d’ayansu... Baba Alhaji sai muzurai yake cikeda firgici.. kana ganinsa basai ance maka hankalinsa a matuk’ar tashe yake ba... Magajiya ta kuma darara masa tsawa da fad’in “Ka shige nace... Kana wani tafiya kana lalumen hanya....!”
Suna cikin tafiya saiga Babba Duna ya fito daga cikin kangon ginin tamkar wanda aka jefosa....
Kallo guda zaka masa ka fahimci wannan anyi shed’anin k’arshen zamani wanda ya tsufa yana b’arna da fasadi a doron k’asa....

Baba Alhaji saida ya firgita da ganin Babba Duna...

Magajiya ta risina ta gaida Babba kana tace “Abokin huld’a kuna daji muna gari muna maku yak’i.... !”

Babba ya kuma kecewa da dariya kana yace “An gaida mai ‘yandaudu... Wannan shine sabon member da kikai masa register...?”

Magajiya ta jinjina kai tace “Shine wannan, mijina kuma mahaifiga Hafiz....”

Gaban Baba Alhaji ya tsananta fad’uwa a daidai sanda aka fito da Hafiz... Wani irin tsoro da firgici had’ida rud’ani suka d’arsar masa a zuciya ganin yanda azzaluman mutanen nan suka sauyawa Hafiz d’insa kamanni sabida tsananin bugu....

***

Bayan Sawwama kaw tasha da k’yar Daga hannun ‘yan daudun nan kaw take jami’an DSS d’in suka take mata baya ba tareda saninta ba, d’ayan ya shafi ‘yar k’aramar na’uran magana dake mak’ale kunnensa yana mai furta “Positive Sir, we need backup ASAP...!”




SameenaAleeyou📚





*INDA RAI*
_................DA RABO_



*108*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



NOT EDITED



A nan police station su Mamy sunyi jigum jigum suna jiran ba’asi daga jami’an tsaro, Hajiya Haule abin tausayi idan ka ganta dole ta baka tausayi, haka nan Mamy keta dannarta tana bata baki...
Wasu ‘yansanda ne suka fito daga wata k’ofa Abbah na biye dasu... Nan su Mamy ma suka mik’e ganin zugan ‘yansandan sun fice, jagaban nasu wanda da gani basai ance maka shine jagora ba waya yake yana fad’in team d’insa sun zama ready.... Hilox da motocinsu Jami’an tsaron suka nufa yayinda Mamy da Haule suka nufi wajen Abbah yanda wani jami’in tsaron ke kuma jadadda masa kada suyi yunk’urin bin bayansu sabida had’ari dake tattareda yanda suka nufa d’in...

Haule na hawaye take fad’ida Abbah “Ni dai Alhaji Usman ka taimaka ka barni na bisu... Inason sanin halinda d’ah na Ke ciki.... Ka taimaka ka k’yaleni na bisu Hafiz d’ina na can....!” Ta k’arashe tana mai had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o...
Daga Abbah har Mamy tausayi Haule tai mugun basu, bazasu iya k’yaleta a wannan yanayi ba, Abbah ya nusa kad’an kana yace “Inaga mubi bayan nasu...”
Mamy ta jinjina kai tana mai furta hakan yayi, nan suka nufi motar Abban kana suka take ma jami’an tsaron baya...

****

Girgiza kai kurum Baba Alhaji yake yana duban wannan tashin hankali da tinda yazo duniya bai tab’a ganin irinta ba.... Jikinsa har wane irin tsuma yake, ya dubi Magajiya dake tsaye yawa ‘yar gunda tana faman k’yak’yata dariya ganin yanda Hafiz ya koma abin kwatance.....
Cikin wane irin murya mai cikeda tashin hankali Baba Alhaj Ke fad’in “Amma Magajiya kedai babu zuciya cikin k’irjinki idan kuma akwai toh fah ta riga ta gama bushewa... Shin mai muka maki da tsanani...? Mai Hafiz ya maki da zaki jefasa cikin wannan mummunar tashin hankali irin haka....?!”

Banda uwar harara bata aika masa komai, lokaci guda taci gaba da fad’in “Kai saurara Alhaji nifa taimakon ka nake idan bazaka amshi kud’in fansar sassan jikin Hafiz ba nifa gaba Ta kaini, kuma da kake cewa mai Hafiz yamin, idan baimin ba ai yayiwa d’iyata dan haka ko a k’asar gyalena idan Babba yaga dama yai gunduwa gunduwa dashi yanzu gabanmu babu abinda ya shalleni matuk’a zan caske kud’ad’ena....!” Ta k’arashe tana watsa masa mugun kallo lokaci guda Ta shige k’ofar da Babba da wani yaron sa suka bi...
Cikin sauri Baba Alhaji jiki na wani irin kyarma ya k’araso zai kwance Hafiz.... A wane irin fusace Hafiz d’in yace dashi “Don’t ...! Kada ka kuskura kazo kusana... Kada ka yarda kai kuskuren tab’ani...!!!!” Yai maganar yana tsananin haki..

Baba Alhaji da hawaye ke gangaro masa kuma mik’a hannu yai kaman zai tab’a Hafiz d’in lokaci guda yake furta “Hafiz... Dah na ka yarda dani... Wllhi bazan tab’a aminta da shirinsu ba... Babu yanda na iya ne... Ka yarda dani Hafiz...!!!”
Tinda ya soma magana Hafiz ke binsa da wane irin duba wanda shi kad’ai yasan irin zogin da yakeji cikin zuciyarsa, ya kasa aminta Wai Uba zai yarda a had’a kai dashi a aikata wannan zalunci mafi muni ga d’an cikinsa....
Hafiz na Hawaye yake fad’in “Ban tab’a dana sanin aikata duk wasu munanan abubuwan da na aikata a baya ba irin yau... Kuma ko ba’a kasheni ba naji dad’i sosai a zuciyata sanin cewa kaida Hajiya yanzu kunji zafin a raba d’ah da iyayensa kaman yanda kukayima Abbah... Wannan bai isheku ba Baba kukayi kukasan yanda kuka had’a aurena da Zulfa’u da zigan Hajiya naita muzgunawa Zulfa’u ina azabtar da ita dan kawai cikan burinku na ganin kun cuzguna ma dik wani jinin Abbah... Wllhi nayi danasanin yi maku biyayya tin fari... Nayi dana sanin auren Zulfa’u balle ku samu daman muzguna mata, wllhi da ace tun fari nasan manufarku kenan da ban aureta ba na k’yaleta tai auren soyayya da wanda take so, amma bawa baya tara sani da Ubangijinsa.... Aurena da ita na cikin k’addarar rayuwarmu... Kuma Alhamdulillahi ko yanzu na bar duniya naji dad’i Zulfa’u zata samu rayuwa mai inganci fiyeda wanda tai baya....Haka kurum sabida san zuciya irin taku kuka tarwatsa mana ahali kuka jefa gaba a tsakaninmu....!” Hawaye basu daina gangarowa a idanun Hafiz ba yake ci gaba da fad’in “Yau ga sakamakon dik munan abinda kuka aikata ko nace muka aikata muna gani... Dan haka kada ka kuskura kai yunk’urin cetona... Idan taimako daga gareka ne ka sani bana so...!!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci daidai sanda Sawwama ta shigo a birkice... Takalma a hannu d’ankwali a hannu tamkar mahaukaciya sabuwar kamu.... Birki tai ganin Baba Alhaji duk’e yana kuka ga Hafiz nan gabansa magashiyan wanda badon Farin sani da taiwa Hafiz d’inba da zata iya rantsuwa akan bashi bane canzasa akai.... Wani irin jahilar birki Sawwama taja tana d’ora hannu aka... Dik rashin imaninta da futsararta saida ta firgita ta razana da ganin Hafiz... Take jikinta ya d’auki karkarwa.... Ta nufi Hafiz d’in cikin tsananin tashin hankali, lokaci guda take furta “Hafizi na....!!! Hafizina kaine haka... Haka suka maka..??!”

Banda jahilar duba da Hafiz Ke aika mata bai iya komai, hucin hakinsa kurum kake iya saurarowa sabida tsananin b’acin rai.... Tayo kansa gadan gadan... Daidai lokacin da ya ida tsinka igiyar da aka d’aure masa hannunsa da wata fashesshiyar kwalba da ya saci idanun yaran Babban Duna ya d’auka.... Yana nan likimo yana aika mata firgitacciyar kallo tamkar mayunwacin zakin dake kwanton b’auna ga dabban dake farauta..... Tana isowa Hafiz ya shak’o wuyarta da iyakacin k’arfin da Allah ya masa yana fad’in sai ya aikata lahira.... Yayinda Baba Alhaji ya mik’e yai kansa yana fad’in yazo su gudu kafin su Duna su k’araso... Fincika kurum Hafiz yake yana fad’in sai yayi ajalin Sawwama... Daidai sanda suka soma jiyo sautin jiniyan motar polisawa...

D’aya daga cikin yaran Duna ne ya shigo a birkice yana fad’in polisawa sunyiwa ginin nasu zobe.... Duna da Magajiya dake tattaunawa na sirri a wani b’angare dake cikin kangon ginin shak’o wuyar Magajiya yai yana fad’in “Kin shirya hakan da polisawa ne... Saida kika bari bamuyi fitowar shiri ba.... K’aryarki tasha k’arya babu wanda ya isa yaga k’arshen Duna...!!”

Magajiya na muzurai yake fad’in “Wllhi ban sani ba... Banida masaniya... Ta ya zan maka haka...? Dan Allah ka yarda dani Babba...!!”

Fincikota Babba yaci gaba da yi bakin bindiga manne gefen kanta har suka k’araso yanda su Hafiz suke... Har wannan lokaci Hafiz bai saki Sawwama ba Baba Alhaji na janyesa.... Yaran Duna kaw tuni Sun fita suna fafatawa da jami’an tsaro, sai bata kashi suke tsakaninsu.... Yau dai rana ta b’aciwa su Babba dan layun da suke amfani dasu su ciza bindiga bata shigarsu harsashi bai kamasu idan jami’an tsaro sun tink’arosu basu fito dasu ba, Take Duna ya kuma lalumar aljihunsa... Nan fah yaji wayam, sai yanzu kalaman Hafiz ke dawo masa cewa sai yayi sanadin Capkesa, Wato wannan shine nufinsa, sace layarsa yai sanda yake k’ok’arin shafasa da burin biyan buk’atarsa dashi... Lallai ya yarda Hafiz shu’umi ne na k’arshe.... Babba Ya Muna laluma yaji da gaske fah babu... Wani irin k’ara ya saki had’ida sauk’ewa Magajiya k’otar bindiga a tsakar kanta wanda saida ya sanyata zubewa a k’asa... Da alama dai dubun Duna ne ya cika....

Sanda ‘yan sanda suka k’araso cikin kangon ginin take suka saitasu da bingoginsu suna fad’in “Freeze... Hands in the air.... No body moves..!!!”

Gaba d’aya d’aga hannaye sukai alamun surrender banda Hafiz da ya zube wajen tamkar matacce... Baba Alhaji yai kansa yana ambato sunansa yana rungumarsa ba tareda yabi takan jami’an tsaro dake k’ok’arin hanasa yin hakan ba... Sawwama ma dai zube take wajen tana numfashi da k’yar sakamon shak’eta da Hafiz yai....

Su Magajiya dasu Duna dik haka suka d’aura hannayensu aka... Su Duna dai Babu layun da za’a ciza a gagari bindigar Jami’an tsaro sannan bata kashi da ‘yansanda sukai da yaransa sun kashe yaransa da dama...
Yau saiga Duna masu uniform sun taso k’eyarsa gaba, gashi d’an tsakurkuri sai shed’ana da mugunta... Gasunk’umin d’an ta’addan da ya gagari jami’an tsaro... Wannan shine fa INDA RAI DA RABO.... Engr dasu Detective Najib ne suka k’araso wajen... Kallo guda Engr yaima Duna zuciyarsa ta tsinke... Tabbas dikda tsufa da shekaru da suka nuna a Fuskar Duna bai mancesa ba... Shine dai wancan d’an ta’addan da yai sanadiyar tarwatsewar ahalinsu... D’an ta’addan da ya tarwatsa ahalinsu Ammansa... Tabbas bazai mance fuskar Duna ba sanda suke nemansu mota bayan mota a lokacin da yake rungume da Daula, hanyarsu ta dawowa daga Jada zuwa Kano.... Lokacin da ya fantsama daji shida Daula yana mai k’ok’arin nema masu tsira daga wajen wad’annan azzalumai...

Lokaci guda yaji k’walla na ciko idanunsa da tuni sun kad’a sunyi ja.... A daidai lokacin da Jami’an tsaro suka taso k’eyar babban d’an ta’adda wanda ya shahara ya kumayi k’aurin a fannin garkuwa da fashi da makami a fad’in k’asa baki d’aya Engr ya k’araso garesu had’ida masu umarnin su tsaya...
Babu musu suka tsaya suna masu bin umarninsa domin kaw shid’in shi yai dik k’ok’arinsa wajen ganin an capke Duna an kuma ceto Hafiz kaman yanda yaiwa Akram alk’awari....

Duna ya d’ago jajayen idanunsa yana duban Engr dasu.... Engr dake tsananin huci d’an rank’wafo da kansa yai kad’an dan Duna sam baida tsawo, hannayen Engr hard’e a baya yake furta “Ka gane ni...??!!”

Duna ya kauda kai gefe... D’aya d’ansandan ya buga masa bakin bindiga a k’eya yana fad’in “Yi magana mana..!!!”

Duna yai wani salo da harshensa irin yanda yakeyi kana yace “Ba kaine d’an takaran mujerar gwabna a k’ark’ashin jamk’iyar Adalci party ba...!”

Engr na tsnanin huci yake furta “Ba wannan nakeso ka tina ba...!”

Duna ya kumayin salo da harshensa tamkar tsohon maye ba tareda yace komai ba.... D’ansanda ya kuma darara masa tsawa yana mai buga masa bakin bindiga... Dakatar da d’ansanda Engr yai Ta hanyar d’aga hannu kana ya kuma duban Duna cikin tsananin karaji yake furta “Nasan zaka iya tina Wani Soja a can garin Jada wasu shekarun baya da yaso ya kawo k’arshen ta’addancin ka... Ka kasheshi kabi iyalansa zaka hallak’a... Nasan zaka iya tina Sanda Iayalansa suke tsere maka a tashar mota... Akwai wani yaro cikinsu da kuma k’aramar yarinyar ta goye... Nasan ka tina... Nasan ka tina komai yanzu..!!!” Ya k’arashe hawaye na tsarto masa...

Duna yabisa da kallo shaye da mamaki kana yace “So you’re that boy..!”

Engr ya jinjina masa kai kana yace “And that boy is your downfall... Yanzu zaka girbi abindaka shuka..!!! Ku d’aukeshi daga nan..!!!” Ya k’arashe yana mai kauda kai gefe had’ida k’ok’arin saita kansa sakamakon hawaye dake k’ok’arin ciko idonsa... Juyowar da zai sukai ido hud’u da Mamy wacce basu jima da isowa ba,da alama taji tattaunawarsu da Duna... Kuma itama taso ta ganeshi cikin wad’ancan ‘yanta’ddan...

Mamy na hawaye tana duban Engr, lokaci guda take furta “Ma’aruf... Shine wannan...Shine ya kashe Mahaifin mu... Bazan tab’a mance wannan bak’ar fuskar tasa ba... Shine..!!” Kuka yaci k’arfin Mamy yayinda Haule Ta matso ta rik’eta sosai jikinta a matuk’ar mace itama...

Jinjina mata kai Engr yai yana k’ok’arin daidaita kansa kana yace “Yes Mamy... Shine wancan d’an ta’addan... D’an ta’addan da yai sanadiyar rugujewar ahalinmu...Yau Allah ya kawo k’arshensa shima... Zai kuma girbe abinda ya shuka..!”
Ganin kukan Mamy na k’aruwa ya sanya Abba d’an janyo hannunta kad’an ya nufi mota da ita yana fad’in “Muje ki zauna Mariya... Kukan nan ya isa haka... Yau an kama wanda ya kashe Baba kuma za’a bi maku hakkinku.... Allah baya barin zalinci ya tabbata...!” Haka Abbah yaita bata baki har suka isa mota...
Yayinda motoci jami’an tsaro sukaci gaba da zarya a wajen...

Kasancewar jami’an tsaro sun gewaye wajen da igiyoyi na tsaro da gudanar da bincike yasa Haule bata samu daman tsallaka fence d’in ba.. Tana nan tsaye tana jimamin Ta yanda zata hango Hafiz d’inta.... Can ta hango wani kaman shi saman gado mai suffar keke irinta motar d’aukan majinyata Wato ambulance.... Haule ta rikice ta nufi wajen a d’ari tana ambato sunan Hafiz d’inta... Saidai sam kwance kawai Hafiz yake tamkar bai numfashi dan tuni ma jami’an lafiya dake taredashi cikin bayan ambulance d’in soma k’ok’arin d’aura masa na’urar oxygen dan ceton rayuwarsa... Haule hannaye bibbiyu aka take kuka... Yayinda Engr ke tsaye gefenta yana bata baki had’ida k’arfafa mata gwiwa cewa ta kwantar da hankalinta Hafiz zai sami lafiya da izinin Allah....
Haule dai kuka kurum take tana fad’in Hafiz kada ya tafi ya barta.. Can ta hangi Baba Alhaji dasu Sawwama dasu Magajiya an taso k’eyarsu hannayesnu rufe cikin handcuffs.... Tai kukan kura ta nufesu tana tsine masu albarka... Babu kaman Baba Alhaji da a cewarta dasa hannunsa aka tasamma hallak’a d’ansu...
Taci gaba da kuka tana fad’in “Bazan tab’a yafe maka ba Alhaji.. Ka cuceni ka zalunceni... Wannan shine sakayyar da zaka min bayan shekarun da muka kwashe muna tare... Mu k’ulla tare mu warware tare, amma rana tsaka kabi wad’annan tsinannun Allahn ka amince a salwantar da rayuwar d’anka gudan jinjnka... Allah ya isa tsakanina da kai...!!”

Baba Alhaji na kuka sosai yake fad’in “Haule wllhi ba laifina bane ki yarda dani... Wllhi tilasta min akai... Amma kinsan bazan tab’a yiwa Hafiz haka ba... Haule ina son d’ah na ina son d’anmu... Ki yafe ni Haule na...!!!”

Haule na kuka take fad’in “Kada ka sake kiransa d’anka dan babu uban da zaima d’ansa na cikinsa haka kan wata shashashar mace.... Wllhi nayi dana sanin aurenka da duk wasu muggan abu da muka k’ulla tare a baya...!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka....
Engr dai sadda kansa k’asa kurum yai zuciyarsa na masa rauni... Wannan shine k’arshen dik wanda yace zai gina rayuwarsa kan zalunci... Akwai darussa masu yawa a rayuwar wad’annan ahali ta ko wanne b’angare.... Tabbas mahak’urci yana tareda riba, yau gashi su Mamy da sukai hak’uri har k’arshen mutumin da yai sanadiyar mutuwar mahaifinsu da tarwatsewar ahalinsu Allah ya nuna masu... Gashi yau an capke Duna dik ta’addancinsa, yau ga Baba Alhaji da matarsa mutanen da suka tasamma salwantar masu da d’ansu yaron da baiji ba bai gani ba sabida son zuciya irin nasu yau gashi su da kansu suna tuhuman juna da d’aura alhakin salwantar da nasu d’an a wuyan juna... Kaico irin wannan rayuwa... Ubangiji ka kiyashemu aikin dana sani da son zuciya...Ameen...

Haka aka wuce dasu Magajiya aka jefasu bayan hilox yanda akewa criminals... Za’a haura da Baba Alhaji kenan ya hangi Abbah daga gefe idanunsa sunyi matuk’ar raunana... Baba Alhaji ya sadda kansa k’asa cikeda nauyin d’an uwan masa, lokaci guda ya rok’i d’an sandan cewa ya basa sakanni yai magana da d’an uwansa... Da k’yar d’ansandan ya k’yale Baba Alhaji yai magnar mintina da basufi biyu ba da Abbah...

Kai a k’asa Baba Alhaji ke furta “Ka yafeni Usman... Ka yafe min dik abubuwan da nai maka.... Hak’ik’a naso tarwatsa ahalinka sabida son zuciya da k’yashi da hassada irin nawa, sai gashi Allah ya tsare maka ahalinka sabida shi baya mulki da zalinci... Yanda naso tarwatsaka sharrina ya koma kaina... Na tarwatsa nawa ahalin da kaina... Babu wanda zaiso ya sake d’aga idanu ya dubeni cikin iyalaina... Babu wanda zai yarda cikinsu cewa bazan tab’a yiwa Hafiz haka ba...! Usman ka yafeni... Wllhi wannan hakkinka ne Ke bibiyata... Naso na salwantar da Ma’aruf tun yana k’arami... Na tilastawa Mamani ta tarwatsa farin cikin dake tsakaninka da matarka Mariya ta hanyar d’aurawa Mariya laifin b’acewar Ma’aruf... Na kuma tilasta mata had’a auren Hafiz da Zulfa’u ba don komai ba sai dan na tabbata ahalinka babu kwanciyar hankali a tattaredasu.... Usman duk wad’annan abubuwan ni ne nan na tilastawa Mamani yinsu, tsangwamar Mariya da yaranta idan har tana so sirrinta na cewa ba ita ta haifeka ba ya rufu... Idan ba haka ba zan sanar dakai komai... Ba komai yasa nai haka ba sai dan sanin cewa kana matuk’ar k’aunar Matarka Mariya kuma ta haka ne kawai zan ganka cikin k’uncin rayuwa... Idan har ka rasa kwanciyar hankali da zaman lafiya cikin gidanka da iyalanka nasan tamkar rayuwar kawai kake amma Farin ciki ya k’aurace maka... Na kuma had’uda mata shed’aniya irin Haule sai na kuma samun wata dama...!” Baba Alhaji dake kuka sosai ya kuma had’e hannayensa waje guda yana rok’on yafiyar Abbah da ko d’agowa ya kalli Baba Alhajin ya kasa... Shin mai ya tsare masa da tsanani a rayuwa da har zai masa irin wannan k’iyayya... Ashe d’an uwa zaiso ya jefa rayuwar d’an uwansa cikin garari irin haka... Kai kaicon rayuwa mai cikeda tarin hassada k’yashi da mugunta... Ko duban Baba Alhaji Abbah bai iya yi ba sabida zuciyarsa dake tsananin suya da d’aci had’ida rauni... Yana jin sanda d’ansanda ya tasa k’eyar Baba Alhajin... Bai daina bud’e murya yana fad’in Abbah ya yafe masa ba had’ida cewa “Usman kamin rai ka d’aukar min lauya kada ka bari a yanke min hukuncin laifin da ban aikata ba na rok’eka Usman..!!!”
Abbah dai rintse idanunsa kurum yai wasu irin hawaye masu d’umi suka gangaro masa....

Ganin yayi weak sosai yasa Engr K’arasowa ya tallafesa, gaba d’aya tausayin Abbah Mamy da Zulfa’u sun cika zuciyar Engr dan a gabansa Baba Alhaji yaita confessing muggan abubuwan da yaiwa d’an uwansa.... Ace d’an uwanka ne yai maka irin wad’annan abubuwan, baida buri face ya ganka ka tagayyara... Shin mai za’ai da k’iyayya hassada da gaba...Kaicon zuciya mai cikeda wad’annan cututtuka....

Engr bai bar wajen ba saida ya sanya one of his men ya maidasu Mamy gida... Itakaw Haule dama cikin ambulance d’in da aka d’auki Hafiz ta shige, sanin cewa magaifiyarsa ce ita shisa basu hanata ba... Tareda ita aka nufi asibitin...

Daga bisani ne su Engr suka nufi police station d’in yanda zasu bada nasu statement d’in, Engr ya kuma filing wani case akan Duna... Toh Duna kanma dama nemansa ake ruwa a jallo dan haka cases d’in dake bisa wuyarsa ma bazasu lissafu ba, D’an ta’adda ne da hukuncin kisa ya hau kansa koda ma ba’aje kotu ba ballantana kuma aje.... Tsabaragen ta’addancin Duna bazai yuwu a Detaining nasa a nan police station kafin a shiga kotu ba dole aka tafi da Duna prison dan ajesa a police station na nufin an basa lasisin escape ne....

Tinda Engr ya sako k’afa a k’ofar ofishin Zo Kaga yanda manema labarai kesonji daga bakinsa duba da yanda ya jajirce a matsayinsa na d’an k’asa mai kishin k’asarsa ya kawo k’arshen wannan d’an ta’adda da ya gagari Al’umma... Sam Engr bai b’oye masu cewa ba shi kad’ai yai wannan yak’i ba harda su Hafiz su Akram Wanda suka sadaukar da rayukansu dan a kame wannan hatsababibin d’an ta’adda....
Kame Duna ba k’aramin Martaba da d’aukaka ya k’arawa Engr ba, dan tuni labari ya karad’e ko ina, hartaga jamk’iyarsu sunyi matuk’ar alfahari dashi tin ma bai d’ale karagar mulki ba yake sadaukarwa da jajircewa wajen

Please Login or Register in order to submit comment