Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin yanda akai k’aryar mutuwa...” Ta k’arashe tana muzurai...

Hafiz durk’ushe k’asa rungume da kayan wasan yarinyarsa yake hawaye, lokaci guda yake furta “I only want to be with my daughter....” Wajen yayi shiru banda sautin fitar kukan Hafiz da kake iya jiyowa.... Ya d’ago idanunsa masu zuban hawaye yana duban mahaifiyarsa kana yace “Hajiya maiyasa akai mata sutura ba tareda an sanar dani ba.. Mai yasa aka kaita makwancinta ba tareda na mata addu’a ba... Mai yasa ba’a bari nayi bankwana da d’iyata ba...?” Ya k’arashe hawaye na kuma gangaro masa....

Fuska a tab’e Hajiya tace “Cikin abinda ka lissafa babu wanda ba’ayi ba, wayarka an kira yafi sau babu adadi kai har d’an aike an tura gidanka akaji gidan a rufe toh so kake a barta haka nan ayita jiranka sai sanda kaga dama ko mai...?” Bai kuma furta komai ba sai rintse idanunsa da yayi da k’arfin gaske...

Sahariyya dake lab’e jikin labule tana lek’ensa sai faman yatsina baki take d’igon tausayi ko nadama babu a tattareda ita

Fuskarsa jazir ya kuma d’agowa ya dubi mahaifiyarsa yana mai sakin huci a hankali, cikin dakakkiyar murya yace “Hajiya mai ya sameta... Mai yayi sanadin rayuwarta...?”

Sahariyya da Hajiya suka had’a ido Sahariyyan na aikawa Hajiya wani irin duba... Take Hajiya ta shiga inda inda tana fad’in “Yo mai kuwa ya kasheta banda ajali ko kashe maka d’iyarka zamuyi... inyi, ko rashin yardar naka takai haka ne...?”

Bai kuma cewa komai ba sai mik’ewa da yayi tamkar wanda ruwa ya shanye ya fice ba tareda ya kuma furta koda kalma ba... Naja’atu tabi bayansa cikeda tausayawa har ya fice kana ta maido da dubanta ga Hajiya da Sahariyya tanai masu muguwar kallo cikin sauri ta fice tana mai girgiza kai... Sahariyya ta rakata da muguwar kallo kana ta tab’e baki ta koma cikin d’aki tana mai danna earpiece a kunnenta ta saki sauti cikin kunnuwanta....

***

Zaune suke saman dakali k’ofar gida sai zuba zance suke irinta matasa, akasarin firan ya danganci siyasa ne da kuma wasanni k’wallon k’afa.... Daidai sanda mai amalanken rake yazo shigewa d’aya daga cikin matasan mai suna Auwalu ya tsaida mai amalanken, tuni mai rake ya gangaro yanda matasan ke zaune...

Auwalu ya dubi Akram da hankakinsa kega wayar salulansa yace “Yauwa ga mai raken na kira a saya mana muji dadin yin zance ko ya kukace...?”
Gaba d’aya sauran matasan sukace haka ne...
Akram ya d’an dube abokan nasa a kaikaice kana yace “Amma dai bani na tsaida mai rake ba...?”
“Koma bakai bane dole ka saya mana tinda mai gidanka na nema muk’ami idan ba haka ba mu hanaku k’uriunmu ko ya kuka ce..?” Nan ma suka amsa da wannan haka take, basu jira cewar Akram ba suka shiga zab’en rake mai rake na fere masu radio na kunnensa yana faman saurare...
Akram fad’i yake “Kaga Malam ko wanne cikinsu sai ya biyaka kud’inka....”
Mai rake na murmushi yake fad’in “Ai idan zasu zab’i MUTALLAB zab’in talakwa ko amalanken raken sukeso gaba d’aya sai na basu....”
Suka kekate da dariya gaba d’aya harda shi Akram d’in, tabbas ya sani Mai gidansa yanada magoya baya da dama wanda idan za’ayi zab’en gaskiya tsakani da Allah zai iyaci...
Akaci gaba da firan siyasa harda mai rake radio na bisa aiki, nan kuwa aka soma program d’in Muryar ‘yanci, Akram ya bud’e kunnuwa sosai yana jira yaji muryarta, baiji muryar tata ba sai na abokan aikinta daga bisani yaji d’aukacin ma’aikatan gidan radio d’in na mik’a mata sak’on ta’aziya na rashin d’iyarta da tayi... Tsananin mamaki ya cika Akram... Wai dama tanada aure harda yara...? Shi kad’ai yake tambayar kansa cikin zuciyarsa.... Bai kuma bi takan firan tasu ba har ya sallami mai rake ya basa kud’insa ya kuma ce ya rik’e canjin domin gudan dubu ne a aljihunsa... Matasan suka kuma ihu suna wasa shi suna fad’in sai Uban gidansa ko garin bakowa...
Akram dai gaba d’aya zuciyarsa ta tafi wata duniyar...
Abokinsa da suka taso tare a unguwar mai suna Yusuf shi ya fahimci nisan zango da Akram d’in yayi....
D’an dafasa kad’an yayi kana yace “Abokina akwai matsala ne...?”

Akram ya d’ago ya dubi Yusuf kana yace “Muje daga gefe...”
Babu musu Yusuf ya mik’e yabi bayan abokin nasa....
Daga can tsallake suka tsaya k’ofan gidansu Yusuf....
Yusuf yace “Akram lafiya dai ko...?”

Akram yace “Yusuf dama tanada aure...?”

Cikin rashin gane inda ya dosa yace “Aure... wace kenan...?”

Akram ya d’an shafi goshinsa yace “Zulfa’u Mailafiya ta gidan radion Muryar ‘yanci....”

Yusuf ya d’an murmusa a hankali kana yace “Aw dama baka sani ba...? Eh toh tanada aure batada aure...”

Akram ya dubesa da alaman tambaya kana yace “Ban gane ba what do you mean tanada aure batada aure...?”

Yusuf yace “From what I know sun rabu da mijin nata kwanakin baya can, kasan Atika abokiyar aikinta k’awar Saliha k’anwatace....”

Akram ya jinjina kai kana yace “I want to know more about her,...”

Yusuf ya d’an murmusa kana yace “Kar ka damu abokina zanyi k’ok’arina, zansa Saliha ta sanar da k’awarta zamu kaiwa Zulfa’u ta’aziya da sunan jamk’iyarku ko ya ka gani...?”

Akram ya d’anyi shiru kana yace “Amma kanaga bazatayi tunani siyasa ya kawo mu ba....?”

Yusuf yace “Haba Akram kasan MUTALLAB yanada magoya baya da dama yau ko siyasarce takaimu na tabbata bazamuji kunya ba duk yanda mukaje da sunansa....”

Akram ya d’anyi shiru na wasu dak’ik’ai kana yace “Shikenan Allah shi wuce mana gaba..”
Yusuf ya amsa da Ameen kana suka nufi cikin gidan gaba d’aya....

***

Tinda suka iso Kaduna suka had’a k’arya da gaskiya suka fad’iwa Ammi, Siyama harda cewa Khalid harda ita ya had’e ya daka...
Ammi ta dafe k’irji tana salallami...
“Khalid ne ya d’aga hannu ya dakeki...?” Ta kuma tambayar Siyamar...
Cikeda makirci Siyama tace “Aw mamaki kike sha Ammi, Toh wllhi Khalid ya shige duk yanda kike tunani, baiga darajan girme masa da nayi a haife ba yasa hannu ya dakeni nima don kawai nace ya rabu da wancan dangin mayun....”

Yesmin dake gefe da kumburarren bakinta tace “Wllhi Ammi ko shakka babu an juye masa kwanya bakiga yanda ya fice a hayyacinsa ba gaba d’aya....”

Ammi tai k’wafa tace “Dad na hanya ai shine kawai maganinsa don wllhi bazai janyo mana kayan kunya ba....” Ta k’arashe tana mai kuma dialing layin Khalid d’in

Kubura dake lab’e jikin staircase sai faman k’unshe dariyarta take tana kwaikwayan maganan Yesmin da yanda bakinta ya kumbura ya koma gefe guda, sai murna take tana tsallen Allah shi k’ara....

A daren Khalid ya dawo garin Kaduna saidai ko sashen Amminsa bai shiga ba, washe gari ma bai fito ba har saida ya tabbata mahaifinsa ya dawo don yana ganin sanda driver ya tafi airport d’aukosa, baiji mamakin ganin Khalid d’in baizo d’aukansa ba don tun a waya Ammi ta zayyane masa komai duk halinda ake ciki, shi kad’ai yake sakin huci har sai yafi Ammi fushi da lamarin musamman da shike an tab’o sanyin idaniyarsa Siyama wacce a duniya yak’i jinin yaga fushinta sabida tsananin sonta da yake....

Suna zaune gaba d’aya a parlorn ya sako kai, ko ba’ace ba yasan fitowarsa ake jira....

Kallo d’aya ya watsawa Siyama ya d’auke kai daga barin duban nata.... Can k’asa gefen k’afafun mahaifinsa ya k’arasa ya zauna...
A hankali ya furta “Daddy sannu da zuwa... Ammi ina kwana...?”

Baikai aya ba Ammi ta katsesa da fad’in “Da ban kwana ba zaka ganni...? Nace da ban kwana ba zaka ganni...? Ince kai ka zama sallamemme.... Ace tun jiya ka dawo gidan nan ka kasa lek’owa mu gaisa sabida ta zuba maka a ruwa kasha koh.... Harda wulak’anta ‘yan uwanka don kawai sun fad’i gaskiya...? Idan ka zab’eta sama da ‘yan uwanka ne sai ka tattara ka koma can ka zama cikakken sallamemme...” Siyama ta k’arada “Ahtoh fad’a masa dai Ammi..”

Daddy ya cafi zancen da ambato sunan Khalid...

“Khalid...!”

Khalid ya d’ago a hankali yana dubansa kana yace “Na’am Daddy...”

“Dad yaci gaba da fad’in “Khalid meke faruwa da rayuwar ka....?”

A hankali ya furta “I’ll explain everything Dad....”

Dakatar dashi yayi ta hanyar d’aga masa hannu kana yace “Ba sai ka min bayanin komai ba, mahaifiyarka ta sanar dani, ba kuma zan bari ka kawo mana abin fad’i a dangi ba, bazaka kawo mana yarinya maras cikakken asali ba da sunan mata, ga mata da yawa a duniya, kaje duk yanda kakeso ka kawo mace idan har family background d’inta nada kyau ni zan aura maka amma banda yarinyar da aka tabbatar batada cikakken asali balle tarbiya...”

Khalid ya dubi Ammi da Siyama da tsananin mamakin jin yanda suka had’awa Dad zance ya hau kai ya zauna... Ammi ta katse hanzarin nasa da fad’in “Ga k’awarsa Yesmin babu abinda ya rasa mai zai kaisa wani duniya neman mace...”

Daddy yace “Kaji koh... Inaso kamin rantsuwa babu kai babu wancan yarinyar sannan zaka auri ‘yar uwarka Yesmin....”

Khalid ya d’ago da mamaki yana duban mahaifinsa kana yace “Daddy rantsuwa fah kace....? Daddy it doesn’t have to reach this point...”

Ammi tace “K’warai kuwa it does ta hakane kawai zamu amince ka rabu da wancan tsinanniyar yarinyar.... Zaka rantse ne kokuwa...”

Khalid ya dubi mahaifiyarsa kurum ba tareda ya iya furta koda kalma ba...

Dad yace “K’yalesa tinda bazaiyi abinda mu muke so ba a matsayinmu na iyayensa muma bazamuyi abinda yakeso ba...”

Yakai dubansaga Khalid da kansa ke duk’e k’asa kana yace “Khalid inaso ka maido min da duk wani abinda na mallaka maka na jin dad’in rayuwa sannan ka tashi ka fice min daga gida kar ka dawo har sai ranar daka amince da buk’atarmu...”

Khalid ya d’ago a firgice yana duban mahaifinsa cikin rashin yarda da abinda kunnuwansa ke jiyo masa...
Baki na rawa yace “Daddy.....”

Dad ya kuma dakatar dashi da fad’in “Ka tashi ka fice mun a gida ka aje mabud’an section d’inka da na office d’inka.... I believe you can provide for yourself... Now..!!” Ya k’arashe cikin d’aga murya....

A hankali jiki babu laka ya mik’e ya nufi k’ofa.... Kubura dake lab’e bayan k’ofa hawaye suka shiga gangaro mata ji take kaman ta isa a guje ta rungumesa , ita kanta Yesmin d’in dake lab’e mab’oyarta sai taji babu dad’i ita ba haka taso ba bata zaci Daddy zai iya koran Khalid daga gidansa ba, ji tayi kaman ta ruga cikin parlorn tacewa Daddy duk abinda suka fad’i akan Nabila k’aryace.... Ta rintse idanunta tana hawaye... Tana ganin sanda Khalid ya dawo parlorn rik’esa keys a hannunsa da kuma suitcases d’insa biyedashi.... A hankali ya isa ya aje keys d’in gaban Daddy....
Siyama da Ammi mamaki ya cikasu ganin Khalid ya zab’i ya tafi akan yayi rantsuwa ya rabu da wancan yarinyar lallai da alama da gaske shanyesa tayi, jikin Ammi ya soma yin sanyin ganin Daddy da Khalid babu mai fasa k’udirinsa....

Har yasa kai zai juya Dad yace “Your car keys ajiyesu tinda suma ta dalilina ka samu....”
Khalid ya kuma duban mahaifinsa cikeda mamaki, lokaci guda ya sadda kai k’asa ya cirosu a aljihu ya aje saman center table... Dad ya kuma fad’in “Your master cards ajesu suma....”
A hankali Khalid ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya ciro wallet d’insa ya cire ATM cards d’insa ya ajesu saman table d’in....
Dad yace “Kar na sake ganinka k’ofar gidana balle k’ofar kampanina... Get out....!” Ya k’arashe yana mai nuna masa k’ofa....


SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_



*52*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




D’ago kai Khalid yai yana duban mahaifan nasa kaman zai magana sai kuma yai shiru baice komai ba, a hankali ya juya ya janye da suitcases d’insa, cikin wani irin yanayi yake d’aga k’afafunsa...
Zuciyar Ammi ta shiga tsinkewa ganin da gaske Khalid fita zai a gidan, tasan d’an nata da mugun zuciya amma batai zaton zai iya tsallake conditions d’in da mahaifinsa ya kafa masa ba ya fice....
Cikin inina takeceda mijin nata.... “Daddyn Siyaam don’t you think you’re going too far, kaga fah ficewa zaiyi, ina zaije shi, mai zaici..? Dan Allah kai hak’uri ka rangwanta masa....”

Wani mugun kallo Daddy ya watsa mata kana yace “Khalid baida muhalli a gidana until he’s learned his lessons...”

Ammi ta kuma kai dubantaga Khalid da har ya kusan ficewa daga parlorn, cikin sauri ta kuma duban mijin nata kana tace “Idan bazaka masa afuwa ba ko credit cards d’insa ka taimaka ka bashi mai zaici ina zaije....?”

A hasale Daddy ya kuma cewa “Nace maki har sai ya gane kuskurensa, babu abu guda a nan da zan basa sabida komai a nan ta dalilina ya samu, so idan har bazaiyi abinda ni nake so ba ya fice ya nema nasa da kansa yaji yanda ake nema da gumi....”

Duk maganganun da suke cak Khalid yai tsaye yana saurarensu zuciyarsa na kuma masa zafi... Cikin sauri yasa kai ya fice tamkar zai kifa k’asa....
Kubura tabi bayansa da kallo had’ida d’aura hannu bibbiyu aka tana kuka tana fad’in ta shiga uku...

Daddy bai kuma bin takan su Ammi da Siyama ba yai ficewarsa.... Harta Siyama saida ta sha jinin jikinta, ita kanta batai zaton abin zai kai nan ba, Daddy ya kori Khalid kuma Khalid baida niyyan janye ra’ayinsa, lallai abin ya girma....
Yesmin ne ta fito daga mab’oyarta a guje tana hawaye take fad’iwa Ammi “Aunt please talk to Daddy, he can’t send him away... Toh ina zaije shi.... Dan Allah ki masa magana”

Harara Ammi ta watsa mata ba tareda tace komai ba ta haye sama zuciyarta na mata zafi sosai.... Yesmin jiki a sanyaye ta maido da dubantaga Siyama murya har na rawa take fad’in “Cousin this can’t be, we must do something....”

D’an dubanta Siyama tai kana tace “Nima kaina abin ya dameni, amma karki damu don na tabbata Khalid bazai iya ba he would definitely give up, zai dawo ne sannan wannan shine kad’ai chance d’inki da zaku kasance tare, we should just keep an eye on Khalid, na tabbata Khalid baida abokin da ya wuce Baffah so definitely wajen Baffah zaje shi....”
Yesmin ta goge hawayen da suka gangaro mata kana tace “Shikenan hakan yayi, but I don’t want him to hate me even more...”

Siyama tace “Kedai nace miki ki bar komai hannu na a k’arashe Khalid baida zab’in da ya wuce ya yarda da duk wani condition da Dad ya kafa masa ciki kaw harda aurenki, so just chill kinji koh...” Ta k’arashe tana buga kafad’unta had’ida hayewa sama wajen mahaifiyarta....

Kubura ta fito daga mab’oyarta fuska duk hawaye yayinda ta hangi Yesmin itama fuskar tata jik’e yake da hawaye, nan sukai cirko cirko kowa tana aikawa juna muguwar kallo, tsuka Yesmin tai zata haye sama nan ta sinkayo muryar Kubura tana fad’in “Aikin banza wai harara a duhu, tusa kai babu k’warjini kuwa yawa ne, wllhi iska dai na wahal da mai kayan kara, mutum yace baya so baya so ko an tab’a soyayya dole ne... Billahillazi duk abinda ya samu Saifulllah mutum zaiji ne daga gareni....”

Cak Yesmin ta tsaya ta daina taka matakalan ta kaikaito shaye da mamaki tana duban Kubura, batasan sanda dariya ya kufce mata ba tace “I don’t have your time, you filthy made....!” Lokaci guda ta haye sama kaman zata tashi sama....

Kubura ta kuma yin k’wafa ta goge hawayenta ta fita ta nufi gate a guje ko zata hango Khalid.....

****

Ba shi ya koma gidan ba sai ana kiraye kirayen sallan isha....
Sawwama na zaune saman kujera tana kallon gidan talabijin na bollywood taji motsin shigowarsa, tana ganin sanda ya zube a veranda had’ida kifa kansa saman gwiwoyinsa, batace uffan ba bata tankasa ba saima tab’e baki da tai taci gaba da girgiza k’afafu d’aya bisa d’aya tana kallonta...
Tana jin sanda Hafiz ya busting cikin tsananin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare amma ko gizau Sawwama batai ba, saida aka kwashe kusan mintoci kaman biyar a haka kafin ta juya idanunta had’ida sakin gajeran tsuka ta mik’e ta isa gareshi tana faman tauna chewing gum tana wani jujjya idanu had’ida aika masa harara, ta kwashi dak’ik’ai a hakan kana ta d’an rank’wafo had’ida sassauta murya tace “Hafizi lafiya...? Meke faruwa na ganka haka cikin irin wannan tashin hankali...?”
A wahalce Hafiz ya d’ago yana dubanta, bai iya cewa komai ba sai rungumeta da yayi very tied yana kuma sakin kuka sosai tamkar wani k’aramin yaro, Sawwama ta rausayar idanu tana mai jin takaicin kukan nasa har cikin zuciyarta....
Cikin muryar kuka yake furta “Kausar Kausar babu Sawwama.... Kausar ta tafi ta barni.... Na rasa tilon d’iyata Sawwama....!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya mai ban tausayi....
Cikin zuciyarta banda tsuka bata komai, a fili kuwa tsan tsan damuwa ta nuna ta shiga salallami da kururuwa wanda kai kace gaskiyane har cikin zuciyarta ne...
“Allah sarki Kausar yarinyar nan ashe ba mai zama bace, badon Allah ya k’addara hakan ba da tana nan abinta a nan, ai banci ta zamaba Hafizina bara na shirya na tafi makoki...” Ta ida maganar tana maici gaba kuruwa....
Bai iya furta koda kalma ba sai zubewa k’asa gijif da yayi yana mai kuma dafe kansa....
A haka ta d’auko mayafi ta taddashi nan zaune wajen yanda ta barsa, ta tab’e baki tana kuma aika masa harara, lokaci guda ta saki murmushin mugunta kana tace “Hafizina ai hak’uri ai mata addu’a ni na wuce don bai kamata ana can ana makoki ba ni ina nan.....”
Nan ma Hafiz bai iya tankata ba har tayi ficewarta, shi kad’ai yasan abinda yakeji cikin zuciyarsa saiko mahaliccinsa....
Sawwama tana ficewa ta tari mai adaidaita tana kiran Alhajinta a waya....

***

A can asibiti wajen Raihana kuwa Mamani tayi zaune ta rapka uban tagumi tana kallon yarinyar, tsananin tausayinta na kuma ratsa zuciyarta, k’aunar yarinyar take har cikin zuciyarta, Bata tab’a zaton zata k’aunaci d’aya daga cikin jikokinta mata irin hakan ba, sai gashi Allah ya jefa mata k’aunan Raihanah cikin zuciyarta.... Tana a haka Dr Awwab yai sallama ya shigo nurses biyu biyeda bayanshi...
Mamani tana ganinshi ta soma sakin murmushi tana fad’in “Datta an shigo...”
Awwab murmushi kwance saman fuskarsa yace “Eh Baaba ya jikin jikar taki...?”

Mamani fuska sake tace “Toh Alhamdulillahi zamuce an auna arziki tinda da ranta...”

Awwab yace “Hakane Baaba... Emm nace ko zaki d’an jiramu waje munaso za’ai dressing...”

Mamani tace “Na’am d’an nan za ai mai kace...”

Nurse guda dake kwance drip tace “Baaba ciwon jikar taki za’a wanke...”

Mamani ta yab’e baki tace “Yo na ganki a nan ai amma na tambayeshi....”
Nurse tace “Allah baki hak’uri Baaba...”

Mamani ta tareta da fad’in “Amin hak’urin ta kawomu yanda muke yanzu... Kajimin kilibibi irinta yaran zamani....”
Dr Awwab ya k’unshe dariyarsa ya shiga baiwa Mamani baki lokaci guda ya shiga janta da barkwanci da shike gwani ne wajen barkwancin....
“Hajiya Baaba mu k’arasa daga waje mu barsu suyi aikinsu, banida round muje nai miki hira...”
Mamani ta d’an dara cikeda jin dad’i don tuni ta sake da Awwab ko don barkwanci irin tasa....
Suna tafe take tambayarsa “Niko nace ina abokin aikin naka shi wancan likitan...”
Awwab yace “Aw Sameer, ai shi aikin nasa da safe ne shiyasa ya tafi....”
Mamani ta d’anyi shiru tana mai son tambayan Awwab abubuwa da dama gameda wancan likitan, haka kurum takejin babban al’amari a tattereda shi tun sanda ta soma arba dashi...

Awwab zai kuma fad’in Baaba tace kirani Mamani kaji d’an nan...
Yai murmushi yace toh Mamaninmu
***

KADUNA


D’an savings d’in dake jikinsa yai amfani dasu ya kama madaidaicin d’aki a hotel mai sauk’in kud’i.... Gaba d’aya ya kasa sakin jiki a hotel d’in abinka da wanda bai saba da kwanan irin local hotels haka ba, sai faman d’aga kai sama yake yana bin d’akin da kallo wai shi Khalid yau shine dai zaiyi kwanan wannan hotel d’in... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da iska, kishingid’a yai saman gadon had’ida zaro wayar salulansa a aljihu ya shiga shafawa... Daidai kan lambar wayarta ya tsaya had’ida kafe wayar da idanu... Teddy Bear sunan da ya saving lambarta dashi ya furta a hankali....
Yatsunsa yakai kan lambar kaman zai dialing sai kuma ya tsaya yana kuma kallon wayar... Gajeren tsaki yai had’ida cilla wayar gefensa.... Ya janyo pillow had’ida danna kansa ciki ko baccin dole zatai gaba dashi....

Washe gari sassafe wayar Baffah ne ta tadashi tun kwanciyar bayan sallan asuba da yayi... Ya janyo wayar da k’yar yana kallon screen d’in wayar.... Ganin mai kiran nasa ya sanyashi sakin tsaki a hankali, k’arfe bakwai da rabi na safiya kaman yanda ya bayyana mashi a fuskar wayan... Bai d’aga kiran ba har ta stinke ya kuma maida kansa ya kwanta nan sautin wayar ta kuma tadashi, har ila yau Baffah amininsa ke kiransa...

Da tsaki ya d’aga wayar kana jin muryarsa kaji wanda bai sami wani wadataccen bacci a daren da ya gabata ba....

“Ka fad’a min idan bashi kake bina da zaka kirani this early...” Abinda ya soma fad’i kenan...

Daga d’aya b’angaren Baffah yace “Khalid kana ina ne...?”

“You haven’t answered my question... Why on earth zaka tasheni da sassafen nan... what for...?”

Baffah yai gajeren tsaki kana yace “Drop that ego for once in your life Khalid ba’a fad’a da iyaye... Idan har kana son albarka cikin rayuwanka kabi bayin Allahn nan sauda k’afa... Ta yaya zaka zab’i mace akan iyayenka... Akan mai Khalid....?”

Dafe kansa da ya masa nauyi yai kana yace “It’s too early for this.... I’ve headache already...”

Girgiza kai kurum Baffah yai kana yace “Tell me your location...”

Badon yaso ba sai don Baffah ya nace ya sanar dashi otel d’in da yake.....

Mintuna kad’an Baffah ya iso hotel d’in shaye da tsananin mamakin wai Khalid ke kwanan irin wannan hotel d’in...
Fuska a tab’e Baffah kebin ‘yar d’akin da kallo don shi ko wajen zama bai gani ba a cewarsa...
Khalid ya dubesa a kaikaice kana ya watsar....
Sanin cewa idan zai kwana wajen a tsaye Khalid bazaice masa ga wajen zama ba yasashi zama bakin ‘yar gadon....

K’uri Baffah ya masa kana ya girgiza kai a hankali yace “I never thought ban tab’a tunanin...kai not even in my dreams, the whole Khalid Mainasara the one that I know zai iya falling for wata mace ba waima har ya bar luxury life d’insa his family and everything yazo yana living miserable life irin haka ba... Khalid for crying out loud...!” Bai kai aya ba Khalid ya katse sa da fad’in “Cut it out please... Will you? Haba kazo ka sakani a gaba kana min lecture, wanda kayi a waya bai isheka ba... Look Baffah this is my life and I hate it when people try to intrude...” Katsesa Baffah yayi da fad’in “You can call me intruder or whatever amma bazanga kana abu maras kyau na k’yaleka ba Khalid... Quit this nonsense ka tattara ka koma gida and apologize to your parents...” Cikin tsananin b’acin rai yayi maganan wanda tinda ya soma Khalid bai kallesa ba saima wani gefen da yake duba...

A kaikaice ya dibeshi gira a sama yace “Are you done... Ka gama...?”

Baffah yayi shiru yana duban sa kurum sanda ya isa k’ofa ya bud’e masa yana mai masa alama da hannu yake fad’in “Get out please....”

Baffah yasan hakan ka iya faruwa yasan kafiya irinta Khalid mutum ne da sam bai tank’waruwa don haka bai Kuma cewa uffan ba sai mik’ewa da yayi jiki babu laka ya nufi k’ofa... Har ya isa k’ofar yaja ya tsaya, hannu yasa cikin aljihu ya ciro wallet d’insa ya zaro katin atm ya mik’a masa yana fad’in “One of your Bank cards Ammi ta bayar a kawo maka Incase you may need...”

Murmushi yai kana yace “Ka mayar mata bana buk’ata....”

Girgiza kai Baffah ya kumayi bai tsaya jan inja da Khalid ba yayi ficewarsa rai b’ace....

***

KANO

Zulfa’u na kwance uwar d’akin Mamy k’aramar alk’ur’ani rik’e hannunta tana karantawa Marliya ta shigo da sallama

A hankali ta goge hawayen da suka zubo mata kana ta dasa aya ma karatun nata ta amsa sallaman Marliya...

“Addah wai wasu bak’i ke sallama a parlorn Abbah zasu gaisheki....”
Da shike tunda akayi rasuwar parlorn Abbah ta waje na bud’e maza sukan shiga parlorn suyi gaisuwarsu musamman dangin Mamy dashike dangin Abbah wasu nacan gidan Baba Alhaji mahaifin Hafiz...

Zulfah ta dubeta da mamaki kana tace “ Bak’i kuma.... Baki sansu ba..?”

Marliya ta girgiza kai a hankali tace “Ban shiga ba Addah, Aunty B ce tace nai kiranki....”

D’an jim Zulfa’u tai kana ta mik’e ta zura hijab d’inta, hannun Marliya ta janyo da nufin tai mata rakiya...

A daidai k’ofar parlorn ta hangi Hafiz ya turo k’aramar k’ofan gate ya shigo cikin gidan... K’irjinta ya bada wani irin sauti, ganin Ya Hafiz ya sanyata shiga sabon tashin hankali domin kaw kamanninsa d’aya da d’iyarsa Kausar ne babu abinda yarinyar ta rage masa, take taji k’walla na neman ciko idanunta, tai tsaye ta kasa ci gaba da tafiya... Shima Hafiz d’in tinda ya hangeta sai ji yayi k’afafunsa sun kasa

Please Login or Register in order to submit comment