Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai jiyo sauk’an hannunsa tai saman nata ya rik’eta gam.... Idanun Sahariya suka sauk’a kan hannayensu yanda suke mak’ale cikin na juna... Zuciyarta yai wani irin tsinkewa k’afafunta taji sun gaza d’aukanta... Kasa tab’uka komai tai itama sai dubansu da take baki sake daga ita har mahaifiyarta Haule...


SameenaAleeyou📚






*INDA RAI*
_................DA RABO_



*98*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*


NOT EDITED!



Haule ta saki tukunya tana gyara d’aurin zani had’ida murje idanunta alamun tabbatarwa... Eh da gaske dai Raihanah take gani tarda Ma’aruf ba mafarki bane...
Sameer ya d’anyi gyaran murya kad’an kana yace “Kina mamaki ne...?”
Haule ta kuma matsowa kad’an tana nunasu da yatsa dan tama kasa furta koda kalma.... Lokaci guda labb’anta dake tsananin b’ari taji suna furta “Al... Alhaji... Alhaji fito kaga kayan al’ajabi... Ashe ga makirar da k’aninka ya aurawa d’ansa....!” Ta k’arashe tana kuma kururwa had’ida dannawa Baba Alhaji kira... A fusace ya fito Magajiya na biyedashi tana sanye cikin kayan bacci ‘yar kanti mai tsantsi ta d’aura zani sama sai wane yamutse fuska take alamun bata jima da tashuwa ba, Sai narkewa cikin jikinsa ake tana fad’in “Dalin Dalin dan Allah kaiwa matarka magana wllhi fitinarta Ke tadamu a gidan nan, sai taita biyewa yaran nan suna kokawa da farar safiya, kuma fad’ar bai wuce kan abinci, gaskiya Nidai Dalin Dalin ka taka mata birki kasan banson hayaniya..” Ta k’arashe tana narkewa cikin jikinsa ... Shiko Baba Alhaji tuni ya soma hura hanci yana fad’in “Wai ke Haule shikenan garin Allah na wayewa kinyi da kowa ken....!” Aya ya sakawa kalaman nasa sakamakon hangosu da yai tsaye tsakar gidan....
Haule kaw k’ek’ashe da idanu take duban Magajiya sai faman huci take, alla alla take dare tai Baba Alhaji ya bar d’akin Magajiya kaman yanda Shari’a ya tanada, ko banza wani k’uncin zai ragu mata... Lokaci guda Haule Ke fad’in “Ka nad’e a d’aki ana d’irka maka tsiddabaru kai a dole ga mai Amarya.... Toh sai ka fito ka ganema idanunka, an nad’e d’iyarka ma da sunan Amarya... Ka ganta nan... Ko kunya tana mak’ale jikinsa ta nuna mana ita cikakkiya ce.....!” Ta k’arashe tana hura hanci....
Raihanah da tuni k’walla sun ciko idanunta cikin sauri ta fuzge hannunta cikin na Sameer ta duk’a da saurin gaske tana k’ok’arin gaidasu saidai gaba d’aya ma kasa furta komai tai sabida kuka da yazo bakinta gadan gadan.... Sameer kaw da tsananin mamaki yake duban Haule, ko kunyar idanunsa bayan dik abubuwan da tai masu shida mahaifansa da ‘yar uwarsa Zulfa’u bataji ba.... Bai ida mamaki ba saida ya sinkayo muryan Baba Alhaji yana huci yake fad’in “K’yale ja’ira munafuka... Kina jina sai ya sakeki dan wannan aure bai d’auru ba dan dama Usman mutunci na yai niyyan ci....” Ya maido da dubansaga Sameer dake faman binsa da kallon mamaki kana yace “Kai kuma sai ka sakar min d’iya dan ba ita nayi niyyan baka ba, idan baka sakar min d’iya yanzu cikin salama a cikin gidan nan ba zaka amsa sammaci a kotu... Daga kai har Manu Billahillazi k’ararku zanyi....”
Sahariyya ta shiga doka tsalle tana murna Sameer zai saki Raihanah dan ko bata sameshi ba ta gwammaci dukansu su rasa da dai ace harma Wai Raihanah ce matar tasa....
Haule ta jinjjna kai tace “Ahtoh sai muji Uban da ya basu dama su aurar da yarinyar da ba tasu ba... Munafuka jibi yanda take mannewa cikin jikinsa kaman wata mage tana san san da kai na minafinci....”
A kufule Baba Alhaji yayo kanta yana furta “Zaki tashi Ki wuce ciki ne ko sai na jibgeki... Ja’irar banza.....!”
A d’imauce ta yunk’ura ta tashi tana k’ok’arin nufa d’akinsu saiji tai gam Sameer ya rik’o hannunta cikin nasa, idanunta masu zuban hawaye ta d’ago tana dubansa, ga tsananin mamakinta wane irin yanayi taga fuskan nasa ciki wanda zatai rantsuwa bata tab’a ganinsa cikin irin yanayin ba....
Haule ta wani zabura ita kad’ai tana duban yanda Sameer ya hana Raihana shigewa zuwa garesu... Shi kanshi Baba Alhaji da tsananin mamaki yake duban Sameer d’in... Lokaci guda yake furta “Eh lallai na yarda bakada mutunci baka gada ba... Sakar min d’iya dan ba kai ka haifa min ita ba, ba kuma ubanda ya aura maka bane ya haifa min ita... Sakarta nace....!”
Ga tsananin mamakinsa muryar Sameer ya sinkayo cikin wane irin dakewa yana furta “Babu yanda zata shige..!!!!” Yai maganar cikin tsananin tsimewa, had’ida rik’o hannunta...
Gaba d’aya suka zuba masa ta mujiya... Saida ya tabbata dik shi suke duba fuskokinsu cikeda tsoro kana Sameer yaci gaba da magana cikin tsimewa “Dama sallama mukazo muyi maku.... And to make sure bamu tafi da hakkokinmu akanku ba, amma ga dikkan alamu bakuda buk’atan hakan... Mun barku lafiya... Shige muje...!” Ya k’arashe yana mai janyo hannun Raihanah da har lokacin jikinta bai daina rawa ba...
Haule ta soma sallalami tana fad’in “Eh lallai kin cika Raihanah da har zaki zab’i namiji samada mahaifinki... Kin rik’a kin cika tabbataciya.....”
Maganganun Haule ya kuma sanya Raihanah fashewa da sabon kuka ta shiga k’ok’arin k’watan hannunta daga cikin nasa, amma saidai sam Sameer d’in yak’i sakinta saima damk’e hannun da yai sosai yana aikama Haule wani irin mugun kallon tsana da k’yama ya tina dik kalan abubuwa da Haule dasu Baba Alhaji suka masa shida Mamynsa harmada Abbah... Sai faman tururi kurum yake yana duban Haule da idanuniyansa da suka kad’a sukai jazir, ko sauraron Raihanah dake matuk’ar kuka tana fad’in “Ya Ma’aruf kai hak’uri ka barni naima Abbah biyayya na rok’i arzikinka... Shid’in magaifina ne...!!” Sam bai iya sauraronta saima ci gaba da duban Haule da yake cikin matuk’ar b’acin rai, kai kace sai taking out dik wani b’acin ran da ya shiga da k’unci a baya akan Haule.... Su Sahariyya sai murna ake Haule ma sai jijjiga take tana ayyanawa cikin zuciyarta cewa ko babu komai bazata tashi a 2 zero ba idan bataci wani yak’in ba taci wani, ko Babu komai idan ta murk’ushe auren Raihanah da Sameer yanzu a nan wani buri nata ya cika... Bata ankara ba sai ganin Magajiya tai ta tako gaban Baba Alhaji, lokaci guda Magajiya Ke dubansa, murmushi ta saki had’ida langab’e kai kad’an “Haba Alhajina... ‘Ya’ya dai duka naka ne, kuma ko shakka babu abun kunya ne dai kun riga kun tapkashi, mai sunan duk wannan borin da kake na cewa sai ya sakar maka d’iya...? Kokuwa rik’on saikainan kashin da kayiwa d’iyarka kakewa borin kunya kake cewa a saketa....?”
Baba Alhaji ya kasa furta komai sai muzurai... Haule tai karaf tace “Toh ke kuma uban wa ya kasa dake da zaki d’auka...?”
Murmusawa Magajiya tai kad’an kana ta dubi Baba Alhaji tace “Da kai nake Alhaji na...?”
Cikeda borin kunya ya soma fad’in “Toh ai toh ai fin k’arfi aka nuna min kan d’iyata.....”
Daidai nan Sameer ya k’araso gaban Baba Alhaji murya a shak’e wanda dagaji kasan maganar fita masa kurum yake, lokaci guda yake furta “Bayan dik abubuwan saka min, bayan duk abubuwan da kaima iyayena... And especially my father... Na yafe maka, kuma ina rok’on Allah ya yafe maka.... Amma kar kace na saki matata dan bani na zab’awa kaina ita ba sannan itama ba ita ta zab’eni ba, Allah shi yai hukuncinsa akanmu... Ina kuma fata hakan ya zama wa’azi a gareku akida matarka Hajiya Haule...!”Ya k’arashe siririyar hawaye wanda da gani na tafasan zuciya ne tana gangaro masa.... Gaba d’aya k’uri suka masa jikkuna a sanyaye...
Raihanah ta duk’a tana hawaye, lokaci guda take furta “Baba...! Baba..!!” Kuka yaci k’arfinta... Wajen yai shiru bakajin komai sai sautin kukan Raihanah, ga tsananin mamakin Haule sai gani tai Baba Alhaji ya dafa kan Raihanah, cikin murya mai tsananin rawa yake furta “Ki tafi tareda mijinki.... Ki tafi tareda mijinki.... Tashi kije..!!” Abubuwan da yake iya furtawa kenan...
Raihanah ta d’ago tanai masa duban mamaki... Baba Alhaji yaci gaba da jinjina kai yana furta “Ki tafi tareda mijinki...!!!” Yana ida fad’in haka ya juya ya nufi d’aki cikin sauri tamkar mai shirin kuka...
Tuni Sameer yasa hannayensa duka biyu ya d’agota... Cikin b’angaren jikinsa yai mata masauk’i yana mai share mata hawayen fuskarta... Sahariyya ta d’aura Duka hannayenta biyu aka tana furta “Na shiga uku Hajiya kina gani kuwa....? Shegiya k’onenniyar nan ce fah Wai matar tasa... Hajiya karki barta tabisa... Mutuwa zanyi...!!” Ta k’arashe tana kururwa...
Ko takansu Sameer bai kuma bi ba ya janyo hannun matarsa suka nufi k’ofa...
‘Yandaudu suka saki tafi suna yaba dacewa dasu Raihanah da Sameer sukaida juna... Yayinda Magajiya ta saki gud’a tana taya ‘yandaudunta kod’a Raihanah da Sameer....
Haule kam mutuwar tsaye tai a wajen tamkar wata gunki ta kasa yarda Baba Alhaji ya gwaleta irin haka... Ta bud’e murya yana fad’in “Alhaji barin Raihan kai ta tafi... Shikenan ka yarda ka sallamarta ma abokan gabanka.....? Na shiga uku ni Haule....!!!”
Sahariyya kaw tukunyar dake faman tafasa da ruwan zafi ta nufa ta d’auko a guje tabi bayan su Raihanah tana furta “Wllhi yau sai na k’arasa k’onaki mai gaba d’aya kowa ya huta... Saidai a daidai hanyar fita suka kusan yin karo da Hafiz da baisan tana zuwa ba aiko nan ruwan ya dawo kanta ya kware mata... Ta shiga talewa tana ihu tana tsalle had’ida birgima a wajen... Hafiz kaw ko d’auki bai k’ok’arin kawo mata ba sai matsawa gefe da yai yana kallon yanda take birgima a k’asa tana ihu sabida zafin k’unan dake ratsata... Murmushi ya saki kana yace “Alhamdulillah yau kinji azaban irin abinda kikawa d’iyata Khausar.... Allah shi k’ara...!” Daga haka yasa kai ya kutsa cikin gidan yanda ya tadda ‘yandaudu sunyi chaa wa mahaifiyarsa sun d’aura mata tukunyar tuwo aka suna rawa suna zagayeta Haule kaw sai cazgan kuka take har abin tausai.... Hafiz yai kansu a haukace tamkar sabon kamu.... Nan suke sanar dashi uwarsu Magajiya taima rashin arziki shisa suke ladabta ta dan dama Magajiya bata koda sa’insa da Haule saidai ta saka sojojinta ‘yandaudu su handling mata Haule... A d’ari Hafiz ya nufi d’akin Mahaifinsa yana fad’in ko ya saki Magajiya ko shi yaje ya saki Sawwama... Magajiya ta mik’e tana wuraga masa harara... “K’aramin maras kunya, ai bari kaji na fad’a maka zuri’armu sun zama d’aya billahillazi mutuwa ce zata rabamu... Uwarka kuma idan tana son zama lafiya toh tabi umarni na....”
Hafiz yakai dubansa ga mahaifinsa da ya kasa furta komai sai duba daga gefe.... Girgiza kai kurum Hafiz yai cikeda takaici kana ya fice a gidan tamkar zai kifa k’asa....

A hanya Najah ta had’udasu Sameer, Raihanah ta rok’esa yai parking suyi sallama da Najah, hakan kaw akai... Suka rungume juna suna hawaye... Najah tace “Kin cancanci Farin ciki Raihanah... Ki yafe mana dik abubuwan da muka maki a baya ‘yaruwata....”
Raihanah ta kuma rungumeta tana hawaye lokaci guda take furta “Allah ya yafemu gaba d’aya Naja’atu... Wllhi ban tab’a rik’eku ba tuntuni....”
Najah ta jinjina kai tana matsan k’walla kana taci gaba da fad’in “Hajiya ta zama ‘yar kallo a gidanmu... Mahaifinmu ya koma baida ta cewa... Gidanmu ya koma matattaran ‘yandaudu da duk wasu mutanen banza... Amma, abinda suka shuka ne... Ko da hakkinki kawai Allah ya bar Hajiya bazataga da kyau ba, balle d’inbin mutanen da suka sha wahala dik a sabida son zuciya irin nata... Raiha ki yafewa mahaifiyata kuma kice Addah Zulfah ma ta yafe mata ko ta sami sassauci cikin lamuranta...”
Raihanah ta kuma sa yatsunta tana share ma Najah hawaye kana taci gaba da fad’in “Allah zai kawo sauk’i cikin lamuran iyayenmu in sha Allah... Ko Babu komai Hajiya uwa ce a gareni domin kaw dik irin rik’onda tamin ta zab’i ta rik’eni bata salwantar dani ba, kinga kaw ita d’in uwace a gareni.... I love you so much Sis...!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Naja ta kuma rungumeta tana fad’in I love you too ‘yaruwata....” Cikin murya irinta mai kuka.... A haka suka rabu cikeda kewa da alhinin juna...
Isansu gida da kad’an Sameer ya fice ya d’aukosu Mummy yanda sukai sallama gaba d’aya suka d’auki hanya bayan su Abbah dasu Mamy sun kuma masu nasiha... Haka Raiha ta rabu dasu tana kuka musamman Marliya da yanzu sukai sabo sosai, gashi har suka tafi babu labarin Mamani....

****

ABUJA

Suna zaune Office d’in Dr d’in bayan ya ida sanar dasu condition d’in Daddy... Mik’ewa tsaye Khalid yai yana mai shafe fuskarsa da duk tafukan hannayensa cikin tsananin tashin hankali da dik k’ok’arin mai k’ok’ari bazai b’oyu ba.... Aunty Daula kaw kifa kanta kurum tai wasu irin hawaye na gangaro mata....
Khalid ya isa gaban Dr d’in lokaci guda cikin tsananin tashin hankali yake furta “No Dr.... There must be another way.... Can’t we take him abroad...?”
Dr ya girgiza kai a hankali kana yaci gaba da fad’in “I’m afraid you can’t... I’ll only advise you to continue praying for him... Chances d’in rayuwarsa.... Kad’an ne... I’m sorry I had to tell this...” Ya k’arashe yana mai girgiza kai a hankali had’ida zare glasses d’in dake mak’ale idanunsa....
Lokaci guda Khalid yake girgiza kai yayinda Aunty Daula ta k’unshe kukan da yazo bakinta gadan gadan jin kukan na zuwa mata da k’arfin gaske....
Khalid dake duban likitan da rikitattun idanunsa tamkar zai shak’osa haka ya rank’wafo daf fuskansa yana tsananin huci yake furta “How dare you say that... My father isn’t going die, you hear me...? So do everything, every possible thing you can to save my father...!”
Girgiza kai kad’an Dr yai kana yace “I’m sorry Khalid, but you’ve to accept the truth...!”
Khalid ya shak’o wuyarsa yana jijjigasa da iya k’arfinsa yake furta “Just do your damn job and save my father’s live, you incompetent...!!!” Cikin sauri Aunty Daula ta shiga janye Khalid tana hawaye take fad’in “Khalid ka nitsu ka ambato Allah cikin zuciyarka, kar ka bijirema rahamar Ubangijinka.... Allah shine mai warkarwa ba likita ba... Lets continue praying for him kaji....!”
Jiki a sanyaye Khalid Ke furta “Aunty Daddy can’t die... He just can’t..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya mai raunin gaske... Lokaci guda yasa kai ya fice daga office d’in cikin sauri... Nabila da Aunty B dake zaune reception nan sukaga fitowar Khalid ya gifta ya nufi waje cikin tsananin tashin hankali... A tare suka mik’e gabansu na tsnananta fad’uwa... Nan suka hango Daula ma ta fito tana matsan hawaye... Gaba d’aya suka nufeta... Aunty Daula ta rungume ‘yar uwarta Bara’atu tana fad’in “I don’t want to lose him... I love him with all my heart... I don’t want to lose my husband..!!” Ta k’arashe tana mai kifa kanta cikin jikin Aunty B... Ai a d’ari Nabilah tabi hanyar dataga Khalid yabi....
Wani Dr ne yazo ya shigesu ya nufi ofishin Dr Hameed babban likitan dake jagorantar team d’in likitocin da case d’in Daddy Ke hannunsa... Nan Dr Hameed yake sanar dashi halinda matarsa da d’ansa Khalid Ke ciki...
Likitan ya jinjina kai yana mamakin Wai dama Engr Mainasara yanada wata mata bayan mamar Siyama matar Sameer da sukai makaranta tare...? Abin ya tsaya masa a Rai... Da wannan tinanin ya ije report d’in dake hannunsa saman table d’in Dr Hameed kana yai ficewarsa....

Fitarsa da kad’an yaga wayan Sultan na shigo masa... Gaisawa sukai Dr Nazir na tambayarsa yau ya tina dashi ne...
Sultan yace daga d’aya b’angaren “Ai ni na fika mutunci Nazir tinda ni ina nemanka ko Abuja naje... What about you... Kana neman mutum ne...? If I haven’t forgotten the last time da muka had’u a auren Sameer ne...”
Nazir ya katsesa da fad’in “Hold on.. Speaking of Sameer.... Naga Father in-law d’insa a nan Abuja, yayi accident jiya, anyi rushing d’inshi wajenmu... Amma abin mamakin shine babu matar Sameer wajensa sannan babu mahaifiyarta saiko d’anta Khaleed da amaryar Baban nasu... Nasha mamaki sosai, dan ko idon Sameer ma ban gani ba....”
Sultan ya mik’e sosai yana furta “Wait, hold on..! Wai Ahmad Mainasara da nasani kake ce min yayi accident...? Ko dai wani daban kake nufi...?”
Nazir yace “How can I be mistaken bayan ina d’aya d’aga cikin Dr’s team da case d’insa Ke hannunsu.... Shisa nace maka nasha mamaki da naga babu Sameer babu matarsa babu kuma mahaifiyar matarsa dan to be honest with you jikin Engr Mainasara is getting worse.. I’m afraid he’s dying...”
Sultan da mamaki ya cikasa yace “And kace sai bak’in fuskoki kake gani wajensa...?”
Nazir yace “Of course yanda kaji....”
Sultan ya murmusa a hankali kana yace “Kaga kiranka da nai yayi amfani... Well, na gode da wannan information da ka bani.... Sai anjima Doc...!” Ya katse wayar yana shafa hab’arsa a hankali... Ko banza ya samu abinda zai amfani dashi ya sami yardar Siyama dana mahaifiyarta... Babu shiri ya shiga neman layin Laila yace tasan yanda za’ai ta kaisa wajen mahaifiyar Siyama yanada muhimmin abu da zai sanar da ita....

***

A can asibiti kaw jigum jigum sukai dan izuwa lokacin Aunty B tace ya zama dole a sanar da mahaifiyar Khalid halinda ake ciki, domin yin shirun ba komai zai haifar ba illa ya k’ara complicating abubuwa... Mai faruwa ya riga da ya faru, kuma ko mai za’ai hakan bazai canza baya ba, dan haka gwara kawai a sanar da ita....
Khalid ya numfasa a hankali kana yace “But Aunty how....? Ta yaya... I know my mother, idan taji batun nan komai ka iya faruwa regardless of my father’s condition... How am I going to do all of this Aunty... Just how...?!” Ya k’arashe yana fuzar da iska mai d’umin gaske....

Aunty B ta nunfasa kad’an kana tace “Maybe a samu wani wanda takejin maganan shi... Sisters, brothers... Or maybe friends...But we can’t wait any longer.... Magana ta gaskiya kenan...”
Mik’ewa tsaye yai yana mai fuzar da huci, lokaci guda yake zaga parlorn a hankali, shi kansa bai hasasho k’uran guguwa da tashin hankali dake tink’aroshi.... Toh waye ma zaije ya samu da wannan zance, waye Ammi ke sauraronsa... The only person da Ammi ke d’aukar magananta Aunt d’insa ce mahaifiyar Yesmin saiko dama dama Hajiya Fatahiyya momyn Sameer toh itama tinda ta soma yak’in raba Auren Sameer da Siyama suka daina shiri sosai, kuma ma ai Hajiya Fatahiyya bata nan... Last option d’in saidai fah yaje ya sami Mummyn Yesmin ne... Toh amma zuwa wajen Aunty Hanne Maman Yesmin yana nufin tada wani babban yak’in ne muddin taji cewa ya auri wata daban ba Yesmin d’inta dataci masa buri, kawai zai sake worsen situation d’in ne.....Dafe kansa yai kad’an yana ambaton Allah... Itadai Aunty Bara’atu da ta tatane da ita da kanta ta tari mahaifiyar Khalid da batun amma saidai wannan family issue ne bai kamata tai masu katsalandan ba, kuma idan har ta shiga batun toh fah saidai ta k’ara dagula abin ta kuma janyowa ‘yaruwarta Daula wani tashin hankalin wanda bata fatan hakan....
Gaba d’aya dai yinin ranan rasa abin yi sukai sai faman sak’e sak’e da warware ware Khalid yake....

***

A can Kano kaw neman Akram ake ruwa a jallo, lambar da yai amfani da itama da alama an gaza tracking layin, gaba d’aya hankalin Engr da na mahaifiyar Akram ya kai k’ololuwa wajen tashi, gashi a yammacin yau d’in ‘yansanda suka sami motar Akram d’in can wani gidan mai da aka jima da daina amfani dashi can hanyar fita gari....
Sanda suka kira Engr suka sanar dashi babu b’ata lokaci ya isa wajen, yai conforming cewa motar Akram ce, nan jami’an tsaro sukaci gaba da gudanar da bincikensu gameda abinda ya shafi motar had’ida baiwa Engr assurance d’in cewa bazasu huta ba har sai sun zak’ulo komai gameda b’acewar Akram, domin kaw tsintar motarsa da akai hakan na nufin Akram ba tafiya yai kaman yanda yace ba, dik yanda akai akwai wani abu a k’asa... Mai yuwa sacesa akai tinda ga motarsa an tsinta....

***

A can gidan Abbah kaw dik yanda suke tinanin zasu sami Mamani sunje amma babu Mamani babu labarinta, harta mutanen Kazaure sunce bataje can ba dan tin a biki da suka rabu da ita cikeda fushinta basu kuma jin d’uriyarta ba, hankalin Abbah dasu Baffah Wada yakai k’ololuwa wajen tashi, k’arshe dai Abbah cewa yai dole a bada cigiyan Mamani, ta ko ina abubuwa babu sauk’i, lokaci ne da ya zamto tamkar na farin ciki amma ta wasu fuskokin akasin Farin ciki ne... Wasu irin tashin tashin na hankula suka tsinci kansu ciki... A b’angaren Lami ma tashin hankali maras misaltuwa take ciki, itada shara a gidan basuda maraba, babu maibi takanta dan damuwan dake gabansu kad’ai ma ya ishesu... Haka takanyi jigum a d’aki tana tinanin abinyi, dik zaman gidan ya isheta ta gundura, ta tabbata har abada zaman gidan bazai kuma mata dad’i ba saidai ta mutu ita kad’ai a d’aki dikda cewa tayi imani dan hankalin Mamy bai tattareda ita ne a halin yanzu sabida b’acewar Mamani amma ta tabbata da yanzu Mamy tayita tausarta tana bata baki dikda ma ita akaima laifi, tasan halin hak’uri da kirki irin na Mariya... Amma wannan cin amana da tai mata da yawa take, harga Allah tana kunyar fuskantarta... Uwa uba Abbah da takeji kaman ta tattari i nata i nata ta tafi ta bar gidan Kafin ya saketa, Toh Wai idanma an saketa ita ina zataje tace an saketa a halin yanzu.. God’e god’e da ita sai ta hau tattaran k’afa taje tace an saketa... Ta share hawayen da suka kuma zubo mata... Tabbas yau d’in tana nadama da bata tab’a yin irinta ba tsawon rayuwarta...

***

A guje tabi bayan Hafiz tana kuma fuzgo rigarsa tana fad’in “Wllhi baka isa ba, mai kake tinanin zakai... So make a kamamu mu k’arashi rayuwarmu gidan Yari ko mi....?”
Hafiz ya fincike rigarsa bai daina huci ba yake furta “I’ll be very glad idan hakan ta kasance... Na tabbata idan aka kamaki da laifin garkuwa da d’an Adam mahaifiyarki zata had’iyi zuciya tinda Ke kad’aice d’iyarta, Kinga banida sauran damuwar ganinta cikin gidan mahaifina....” Ya k’arashe yana huci....

Girgiza kai Sawwama take lokaci guda take furta “Lallai na yarda baka cikin hankalinka Hafiz.... Idan kai wani abu foolish both nidakai will end up in jail... Haka kake so...?”

Hafiz ya murmusa kad’an kana yace “ Toh ni kuma wata rayuwa ce mai dad’i ta ragemin a halin yanzu... I’ve lost everything, every single thing... Na rasa d’iyata Khausar sannan na rasa Zulfa’u... What else... Ki fad’amin mai kuma nake tsoron rasawa...?!!”
Ya k’arashe cikin daka tsawa hawaye na tsartowa daga idanunsa, lokaci guda yaci gaba da fad’in “I have nothing to lose.... So Idan bazakije ki tilastawa mahaifiyarki ta tafi ta k’yalemin iyaye na ba... I’m gonna show you what I’m really capable of..!” Ya k’arashe yana mai ficewa cikin sauri...
Sawwama tabi bayansa tana doka masa kira amma inaa ko tsayawa baiba.... Sawwama ta koma cikin gida a guje tana lalumen wayan salulanta...

***
Hab’arsa d’aure saman hannayensa biyu da ya dunk’ule waje guda... Da alama yayi nisa cikin tunani... Lokaci guda ta aje masa ruwan tea d’in gabansa had’ida zama gefenta kad’an.... Ya sakar mata sassanyar murmushi had’ida furta “Na gode Matar....!”
Ta d’an saki murmushi a hankali tana mai sadda kanta, zata juya kenan taji ya ambto sunanta... Gabanta ya yanke ya fad’i, yauce rana ta farko data tab’a ji ya ambaci sunan nata... Ta juyo hankali tana mai amsawa...
Gefensa yai mata nuni dashi yace tazo ta zauna....
Gabanta ya kuma tsinkewa but she can’t say no to him... A hankali ta tako har kusan nasa... Before tai aune taji ya kamo hannunta ya zaunarta kusansa sosai... K’irjin Zulfa’u yaci gaba da bugu.... Shiko Engr k’uri yai mata yana babu ko k’yafta idanu, dik sai tajita ba’a sake ba, ya d’an kurb’i tea d’in kad’an da gaba d’aya ya mance da zafin tea d’in sabida yanda ya shagala da kallon amaryar tasa... Zafin da yaji saman harshensa ya sanyashi d’an sakin k’ara kad’an had’ida cire cup d’in daga bakinsa yai saurin ajewa k’asa, hakan yasa Zulfah tai saurin waigowa tana tambayarsa mai ya faru, daidai ya d’ago kenan bayan ya ije cup d’in fuskokinsu suka had’e waje guda... Tsinin hancinsu suka had’e su duka biyun suna jiyo hucin numfashin juna...... Wane irin yanayi ne maras fasaltuwa suka tsinci kawunansu ciki.... Zuciyoyinsu suka ci gaba da bugawa, so take ta janye fuskarta amma ta kasa, k’arar da wayarsa tai ya sanyata saurin janye nata fuskar zuciyarta bata daina bugawa ba... Engr yai k’ok’arin saita kansa had’ida janyo wayar saman table... Jin ya soma amsa waya ya sanyata tattaro duk wani strength d’inta tana k’ok’arin tashi amma sai ji tai hannunsa saman nata ya rik’ota, hakan ya hanata ci gaba da tafiya... Tai saurin

Please Login or Register in order to submit comment