Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makaranta ba ko dama da take kaiwa magariba computer practical take tsayawa, sannan idan tanada aji 4-6 takan fad’iwa Mamyn sabida karta damu.... Takai dubantaga Marliya da shigowarta parlorn kenan kana tace “Kin sami wayan Yusran...,?”

Marliya ta girgiza kai a hankali kana tace “Na kirata sau biyu bata d’aga ba.... Itama Nabilar na kuma kiranta bai shiga....” Mamy tai k’wafa kana tace “Wannan ai rashin hankali ne, idan ba rashin hankali ba Yo ko wayar k’awarta ba sai ta ara ba tace mana bazata dawo da wuri ba idanma nata babu chaji ne.... Zata dawo gidan nan ta sameni ne...” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye...
A k’ofa ta had’uda Zulfa’u wacce da alama daga sashen Mamani ta fito, ganin fuskar Mamyn kawai ya tabbatar mata hankalinta a tashe yake...
“Mamy Nabilar bata dawo ba har yanzu...?” Zulfah ta tambaya cikeda nuna kulawa...

“Inafah ta dawo... So take Abbanku ya kuma tambayana ko ta dawo gida... Wane irin karatu ne har yanzu bazata dawo gida ba, tayi ma kanta yace ta gama karatun...” Cikin fad’a Mamy ke maganar...

Zulfah ta d’an sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kiyi hak’uri Mamy in sha Allah lafiya lou take, kinsan wasu lecturers d’in sam basu san yakamata ba babu ruwansu da lokacin sallah wasu kuma ba musulmai bane so a mata uzuri Mamy...”

K’wafa Mamy ta kumayi kana tace “Ai bazasu hanata yin waya ba... Idan kuma Abbanku ya kuma tambayan ko ta komo gida sai kije ki masa wannan bayanin tinda ita batada hankalin ta d’aga waya ta kira mutane...” Ta k’arashe tana mai nufan kitchen bata daina sababi ba....

Marliya da Zulfah suka dubi juna suna masu jinjina lamarin....
“Bani layin Yusran na kuma kira....” Zulfa’u tace tana mai duban‘yar uwar tata... Cikin sauri Marliya ta mik’a mata wayar dake hannun nata...
Zulfah ta d’auki number d’in kafin ta soma dialing...
Wayar sai faman ringing take ba’a d’aga ba... Har ta kusa tsinkewa kafin aka d’aga, muryar k’aramar yarinyace take fad’in “Hello bata kusane ta saka wayar a chaji ne....”
Zulfa’u tace “Wannan ba wayar Yusrah bane....?”
Daga d’aya b’angaren yarinyar tace “Eh wayartace amma bata kusa ne...”
Zulfah ta jinjina kai tace “Ta dawo daga makaranta kenan...?”
Yarinyar tace “Eh tinda rana ta dawo...”

Duban Marliya da tai mata k’uri Zulfa’u tai kana tace “Toh shikenan sai anjima koh, idan Yusrah tazo kice mata Zulfa’u Addar Nabilah ce ta kira...”
Yarinyar ta amsa mata kana ta kashe wayar...

Jigum jigum sukai suna tunanin ta yanda zasu soma sanar da Mamy cewa k’awar Nabilah ta jima da komawa gida... Marliya tace “Addah kodai mu sanar da Mamy halinda ake ciki, kinga fah dare ya riga yayi, bamusan wane hali ‘yar uwarmu ke ciki ba....” Ta k’arashe fuska d’aukeda damuwa...

Shiru Zulfah tai tamkar mai tunani kana tace “Marliya na rasa ta yanda zamu fara b’ullowa lamarin ne, gashi anjima kad’an nasan Abbah zai kuma tambaya muddin bai ganta ba... Toh idan dai bata makaranta ina take... Toh ko kinada layin sauran abokan nata ne...?”

Marliya ta girgiza kai tace “Ai batada shirgin k’awaye kinsan halinta not everybody can stand her... Ita Yusrah dai itace d’aya k’awarta da na sani kuma coursemate d’inta ce komai tare sukeyi... Toh idan dai sun jima da tashi ita ina taje....?” Batakai aya ba muryar Mamy ya katseta da fad’in “Ban gane ba.... Ta baro makaranta tuntuni...? Toh ina ta tsaya....?”

Zulfah ta d’an gyara murya tace “Mamy ki kwantarda hank.....” Bata ida maganar ba wayarta ya d’auki ruri... Lambar Yusrah da yanzu ta kira ake kuma kiranta....

Zulfah tai saurin d’agawa cikeda damuwa... Daga d’aya b’angaren Yusrah tace cikin ‘yan kame kame bayan sallama “Em em ina yini Addah Zulfah...”

“Lafiya lou, Yusrah ce....?”
“Eh itace dama bana kusa ne d’azun...”
“Eh haka k’anwarki tace... Yusrah nace ko kuna tareda Nabilah ne... Munata kiran wayarta baya zuwa gashi dare ya sako kai already....”
Yusrah ta soma fad’in “Eh ai amma mun tashi ita sai ta wuce gidan Aunty Bara’atu.... Akan haka muka rabu, amma ku kira wayan Aunty B d’in suna tare....”

Nannauyan ajiyan zuciya Zulfah ta sauk’e kana taceda Yusrah “Toh shikenan mun gode Yusrah zan kira Auntyn yanzu....” Ta ida maganar tana mai duban Mamy da Marliya.....

Duk yanda sukaida Yusrah ta fad’i masu, ran Mamy idan yayi dubu ya b’aci, wace irin rashin hankaline wannan... Kan wane dalili Nabilah zata kama hanya ta tafi gidan Bara’atu ba tareda sanin kowa ba...? K’wafa ta kuma yi a karo na babu adadi kana taceda Zulfah tai mata kiran wayan Aunty B...

Zulfah ta danna nan ma bai shiga... “Bai zuwa Mamy....”
Jinjina kai Mamy tai kana ta nufi d’aki sauk’inta ansan yanda take yanzu...
Ita kaw Aunty Lami sai safa da marwa take tsakanin sashenta da sashen Mamy badon komai ba sai don ace ta nuna damuwarta itama....
Zulfah da Marliya dubanta kurum suke sam basuso Mamy tana fayyace mata cikinta gaba d’aya, don suma haka kurum bawai sun gama aminta da matar bane, tamkar tana b’oye wani abin haka suke gani....

Basu suka shigo garin Kano ba sai wajajen k’arfe takwas na dare, masallatai duk sun fito daga sallan lisha.... Kana ganin Nabilah zaka fahimci hankalinta a tsananin tashe yake, tasan a daidai wannan lokaci, lokaci ne da Abbanta ke zaune parlornsa kewaye da ‘ya’ayensa, idan baiga guda ba sai ya tambaya... Shikenan zata saka Mamynta a magana, donma yanzu Abbah ya sassauta da wasu halayyan nasa...
Aunty B takai dubantaga Nabilah wacce gaba d’ai take dame kana tace “Relax daughter, ki kwantar da hankalinki zan shiga naiwa Abbanku bayani ta yanda zai fahimta kinji koh....”

Nabila tai saurin dubanta kana tace “Aunty ce masa zakiyi ga yanda naje...?”

Aunty B ta girgiza kai tace “Ya za’ai nace masa haka, wannan between us ne, our little secret.... Ni dai kawai nasan mai zan fad’i masu daga shi har Mamyn taku.... Kinji koh... So ki kwantar da hankalinki idan Ina nan in sha Allah bazakuyi kuka ba...”

Nabilah ta murmusa tace “Na gode Auntynmu....”

***


A can asibiti kuwa har wannan lokaci Hafiz bai farka ba.... Gaba d’aya Sameer a dame yake, hankalinsa gaba d’aya na tashe... Duk wasu abubuwa da Hafiz yayima k’anwarsa bai hanasa jin tausayin Hafiz d’in ba musamman da shike shine ya bigesa....
Likitoci suna kansa yayinda shida Shamsu suke reception sai faman safa da marwa yake....
Shamsu ya mik’o masa ruwan gora yana k’ok’arin calming nasa....
“Doc try to calm down....”
Saurin katsesa Sameer yai da fad’in “How could you ask me to calm down.... Shamsu mutumin nan fah d’an uwana ne kuma ba fata ba yanzu idan hakan ta zamto silan ajalinsa zan jima inajin zafin hakan, domin gani zankeyi tamkar ni na kashesa.... Shamsu Hafiz can’t die.... He just can’t....” Ya k’arashe yana mai zama bisa benchi had’ida rufe bakinsa da duka hannayensa biyu cikin tsananin mutuwar jiki....

Shamsu ya zauna gefensa yana buga kafad’ansa guda a hankali yake furta “Bazai mutu ba in sha Allah.... Ka kwantar da hankalinka friend and pray for him kaji koh....”

Sameer ya lumshe idanunsa a hankali ba tareda ya iya furta koda kalma ba...

***

KADUNA

Daddy na zaune parlornsa Ammi na gefe faranti dambun kaza gabansa yanaci suna fira Khalid yayi sallama... Ammi ce ta amsa masa sallaman nasa kana ya shigo jiki babu laka...
Daga can gefe ya zauna kana iya hango d’an rama da duhu da yayi a ‘yan kwanakin... Kansa a k’asa ya soma gaida iyayen nasa.....

Ammi ce ta amsa masa Daddy kam ko kallon kirki bai ishesa ba....
Ya dubi Ammi tai masa alamu da idanu kan ya baiwa mahaifin nasa hak’uri...
Khalid ya d’an muskuta kana ya soma fad’in “Daddy kayi hak’uri....”
D’aga masa hannu yai alamun dakatarwa kana yace “Mai ya dawo dakai gidan nan....?”

Khalid ya had’iyi miyau da k’yar kana yace “Daddy hak’uri na dawo na baku, na sani abinda nayi ban kyauta ba... Bazan iya fad’a daku ba cos you’re my parents... I’m sorry Daddy and na yarda na amince zan karb’i zab’inku ma’ana na amince da auren Yesmin....”
Cikeda tsananin mamaki Ammi ta d’ago tana dubansa, shi kansa Daddyn duban mamaki yake masa...
Daddy ya gyara zama sosai kana yace “Ka tabbata da abinda kake fad’i...?”
Khalid yai k’arfin halin jinjina kai kana yace “Eh Daddy na tabbata...”

Alhaji Mainasara yace “Good...” Caraf Ammi ta cab’i zancen da fad’in “Ni dama nasan yarona mai biyayya ne kawai dai wancan watsetsiyar yarinyarce taso brainwashing d’insa...”
Wani duba Khalid ya mata kana yace “Ammi please ki cire Nabilah a batun nan, ku k’yaleta haka tinda nayi abinda kuke so, nima kuyi abinda nakeso ku barta haka kedasu Siyama please...”
Harara ta watsa masa kana ta mik’e cikeda murna tana fad’in dole taje taiwasu Yesmin da Siyama wannan albishir...
Daddy ya bita da kallo har ta fice kafin ya maido da dubansaga Khalid... Gyara zamansa ya kumayi had’ida d’an gyaran murya kana yace “Saifullah ka tabbata zakabi umarninmu...?”

Ya jinjina kai a hankali kana yace “In sha Allah Daddy.... fatana shine ku yafemin d’aga muku murya da bijire maku da nayi a baya....”

Nan ma jinjina kai kana yace “Babu damuwa ni dama nasan kanada biyayya da sannu rana irinta yau zatazo... Na yafe maka tuntuni, Allah ya maka albarka....”
A hankali ya amsada Ameen Daddy, suka d’an tab’a hiran company kad’an Daddy nata k’ok’arin shan cikinsa yaji ko don tak’ura da talauci ne yasa shi ya dawo yayi nadama amma shiru baiji hakan ba... Har saida Khalid d’in ya mik’e zai fice kana ya dakatar dashi da fad’in “You can now have access to your bank accounts... Ga sauran credit cards d’inka a drawer a can ka d’auka.... Sannan zaka iya komawa company office d’inka right away...”

Khalid ya jinjina kai yace “Na gode Daddy....” Ya d’anja fasali kad’an kafin ya dawo da baya ya kuma risinawa yace “Daddy banso ka dubi wannan da wata manufa... But to be honest with you.... I’ll like to resign from the company.... Zan applying neman aiki a wani wajen... Bawai don wani abin ba sai don Kawai inaso na zama independent ne.... I hope you’ll understand me Daddy...”

Shiru Daddy yayi na wasu ‘yan dak’ikai kana ya sauk’e ajiyan zuciya yace “Khalid ban fitar dakai waje karatu don ka dawo kayi aiki ma wasu ba sai don watarana ka zamto ka rik’e abinda zan bar maku koda bani a raye, domin kaw kai zaka gajeni a company d’in... Amma idan haka ka zab’a babu matsala ni zan sama maka aikin in sha Allah....”
Khalid ya d’anyi jim kana yace “Daddy dama dai da so samune na nemi aikin da kaina ba tareda taimakonka ba please.... I hope that’s ok with you...”
Shiru na d’an lokaci kana ya jinjina kai yace “Alright if that’s what you want... Bakada matsala dani, Ubangiji ya taimaka... Amma ka sani ko yaushe kaji kana son dawowa company d’in mahaifinka the door’s always open kaji koh....”
Ya jinjina kai a hankali kafin yayi sallama wa mahaifin nasa ya fice....

***

Abbah ya gama jin bayanan Aunty B tsaf kana yace “Bara’atu ba nak’i maki bane amma abinda Nabilah ta aikata sam ba daidai bane kuma ba tarbiyan gidan nan bane.... Mai amfanin wayar hannunta da ko mahaifiyarta bazata kira ta sanar da ita taje gidanki ba... Maima zaisa daga makaranta ta shige can gidan naki... Shin makaranta tace zataje kokuwa gidanki...?” Cikin kakkausar harshe yake maganan...
Aunty B ta kuma cewa ai hak’uri Abbah hakan bazata sake faruwa ba in sha Allahu.....
Kan Nabilah na k’asa ta kasa furta komai sai faman rakub’e rakub’e take.... Ita koh Aunty Lami idanunta k’yam kansu don bata yarda iyakacin gaskiyar ba kenan...
Daga parlorn Abbah acan sashen Mamy ma fad’a taitayi, daga Nabilar har Aunty B d’in bata k’yale kowa cikinsu ba....
Ita kaw Aunty Lami sad’ad’awa tai tabi bayansu don jin yanda zasu kaya da Mamy....
Aunty B da taga fad’an tai yawa da alama sosai ran Mamy ya b’aci don har tafi Abban nasu d’aukan zafi...
Gyara murya tai tace “Gidan Yaya Abida na kaita...”

Gaban Mamy ya yanke ya fad’i don rabonta da taji an ambaci wannan suna ta mance.....
Ta d’ago tana duban Aunty B d’in..... Aunty B ta jinjina kai alamun tabbatarwa....
Zulfa’u ma duban Aunty B d’in take lokaci guda k’irjinta na bugawa yayinda Marliya da Nabilah suka rasa gane wacece Yaya Abida.....
Ita kaw Aunty Lami dake lab’e jikin k’yaure dafe k’irjinta tai da duka hannayenta biyu.... Lokaci guda k’afafunta suka d’auki rawa.... Cikin sauri ta shiga jada baya da baya zuciyarta bai daina yankewa ba...


SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_


*64*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏼*



Mamy tai shiru ba tareda ta kuma cewa komai ba, Zulfa’u ce ta janyo hannayen k’annenta suka shige suka barwa Mamy da Aunty Bara’atu parlorn domin su tattauna....
Mamy ta kuma duban Aunty B kana tace “Gidan Yaya Abidah... Maiyasa kika kai Nabilah....?”
Aunty Bara’atu tai shiru na wasu dak’ik’ai kana tace “Na fad’a maki dama INDA RAI sai nayi silan k’ulla zumuncin da ya riga ya wargaje a baya, koda hakan zai zama k’arshen abinda zan k’ulla kenan a duniya....”

Nan ma shiru Mamyn tai batace komai ba sai duban Bara’atun da tayi, lokaci guda ta koma ta zauna cikin kujera jikinta a mace....
Ganin haka yasa Aunty B zama daga can kujeran gefenta....

A can d’aki kuwa Nabilah da Marliya ne suka tsare Addarsu Zulfa’u da tambayan wacece Yaya Abidah....
Marliya tace “Dama Mamy tanada wata ‘yaruwa shine bamu santa ba, koda wasa ko a labari bamu tab’a jinta ba....”
Dafata Zulfa’u tai kana tace “Marliya har abada babu sirrin da zai tabbata a rufe, a iya sanina shekarun baya can lokacin nima banida wayo sosai mukanje gidanta da Mamy, rana tsaka muka daina zuwa kuma koda na tambayi Mamy sai cemin tai Yaya Abida ta mutu bata raye, idan nai mata batunta sai tacemin ko sunanta kada na kuma ambata, ni kaina na mance da ita sai yanzu da naji Aunty Bara’atu na cewa gidanta sukaje da Nabilah.... Tabbas ni kaina nawa kan ya d’aure akwai wani sark’akk’iyar al’amari dake faruwa wanda iyayenmu basu fayyace mana ba....”
Marliya ta jinjina kai a hankali kana tace “Toh ko maiyasa Mamy tace ta mutu...? Maiyasa suka datse zumuncinsu...? Maiyasa bamusan da ita ba...?” A tare ta jero duka wad’annan Tambayoyin.....

Sauk’e ajiyan zuciya Zulfa’u tai kana tace “Mamy ce kawai zata iya bamu wad’annan amsoshin......” Tai maganar tana mai lulawa duniyar tunani...
Itakaw Nabilah gaba d’aya ba saurarensu take ba, hankalinta yafi karkata kan halin data baro Khalid ciki... Shikenan sun rabu rabuwa ta har abada....Anya tayi adalci ma kanta..? Anya hukuncin data yanke tai daidai ma zuciyarta da ruhinta...? Toh amma hakan shine daidaima Khalid, hanyar daya d’auka a baya bamai b’ullewa bane, ta gwammaci ta sadaukar da farin cikinta kan taga rayuwar mutum guda tak data tab’a so ya tagayyara.... Ta lumshe idanunta a hankali had’ida jingine kanta da ya mata nauyi jikin gado....

***
Mamy taci gaba da fad’in “Maiyasa kika d’auki Nabilah kika kaita wajen matar da kinsan cewa ta jima da mutuwa a babin rayuwata da iyalaina.... Maiyasa kike son tono abinda ya jima a rufe... Bara’atu maiyasa kike son dawowa da jiya yau....” Cikin tsananin rawar murya tai maganar...

Aunty B na hawaye ta taso ta durk’usa gaban Mamy had’ida rik’e hannayenta lokaci guda take furta “Wasu sirrikan suke bud’e kansu... Wasu sirrikan basu yarda su dawwama a rufe.... Ki sani’yar uwata ina sonki, ina k’aunarki ko mai zaije yazo, and I’ll forever be here for you.....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Lokaci guda suka rungume juna suna hawaye... Suna a haka wayar Mamy ya d’auki ruri, Sameer ne mai kirant, gaisawa sukai yanda Mamyn ta jisa a d’an birkice, tana tambayarsa ko zai shigo gidan ne kafin ya shige can gidansa sai ce mata yayi “A’a Mamy, ina asibiti dai tukuna...”

Mamy tasa yatsa tana goge hawayen da suka mak’ale mata had’ida gyara zama sosai kana tace “Toh... Lafiya amma...?”

Sameer ya d’an shafi sumarsa yace “Mamy Hafiz muka kawo asibiti ya d’an sami had’arin mota... But he’s out of danger now.. Amma dai bai farfad’o ba...”
Mamy ta mik’e tana furta “Subhanallahi, wani asibitin kuke Sameer.... Ka kira su can gidansu Hajiyar tasa...?”

Sameer ya sanar da ita asibitin da suke kana ya k’arada “A’a ban kirasu ba kece kawai na kira...”
“Toh shikenan, gamu nan zuwa zan sanar da Abban naka yanzu, zai kira Alhajin ya sanar dashi...”
Sameer ya amsada “Ok Mamy sai kunzo....” Sukai sallama kana ya katse kiran yana mai duban Shamsu da ya tallafi fuska da hannaye bibbiyu yana dubansa...

Jin Mamy tana fad’i ma Aunty B yanda sukaida Sameer d’in cewa Hafiz ne babu lafiya ya sami had’arin mota yana can asibiti yasa gaban Zulfa’u mugun fad’uwa... Cikin sauri ta d’aga labulen d’akin ta fito, fuska d’aukeda tashin hankali take ceda Mamy zata asibitin itama...

Aunty B ta galla mata harara kana tace “Kije ina...? Kije ki masa mai... Iyakaci addu’ace ince...? Toh ki masa ita daga nan....”
Idanun Zulfa’u sukai raurau... Ta kasa furta komai sai sadda idanun nata k’asa da tai....
Tuni Mamy ta fice sashen Abbah Aunty B ta mara mata baya... Aka bar Zulfah tsaye wajen tana kokonton halinda Hafiz ka iya kasancewa ciki... Marliya ta dafata kad’an kana ta kamo hannunta ta zaunar saman kujera, har lokacin Zulfah bata dawo daidai ba, mutuwar Kausar ya dawo mata sabo... Gani take kaman shima Hafiz d’in mutuwa zaiyi... Shikenan duk sun tafi sun barta... Bazatace ga abinda takeji gameda Hafiz ba amma can k’asan zuciyarta tanajin wani irin rauni had’ida tausayin kanta... Ta lumshe idanunta a hankali sanda ta tsinci zuciyarta na addu’an samun sauk’iga Hafiz... Mutumin da ya d’aid’aita mata rayuwa ya tagayyara....

***

Sanda labarin ya riski Hajiyar Hafiz bayan Lami ta gama labarta mata tashin hankalin dake gabansu ne.... Tabbas idan kan mata ukun nan Mamy da ‘yanuwanta ya had’e shikenan kashinsu ya bushe su kad’ai za’a bari a rana.... Tagajan magajan ta nufi asibitin tana kuka yanda ta riski su Mamy tuni sun isa can, cikeda tausayawa Mamy ta k’araso yanda take tana bata baki had’ida k’arfafa mata gwiwa....
Hajiya bata daina kuka tana furta Hafiz d’inta bazai mutu ba... Shikenan mata d’ah namiji.... Ta kuma d’aura hannaye aka tana kuka kaman wacce batai imani da k’addara ba...
A b’angaren Lami da Aunty B kuwa kowacce kallon kallo kawai suke aikama junansu....

Daga can Abbah da Sameer harma da Shasmu suna tafe tareda wasu likitoci guda biyu suna tattauna lamarin Baba Alhaji ya k’araso tagajan magajan sai sab’a babban riga yake... Abbah yaceda Likitocin ga mahaifin nasa ya iso.... Tuni Baba Alhaji ya nufesu yana tambayan ina Hafiz...? Ina d’ansa....?”
Dr guda d’aya ya dafasa yana k’ok’arin calming d’insa yake sanar dashi Hafiz zai sami lafiya da izinin Allah....
Baba Alhaji yakai dubansaga Abbah da Sameer kana yace “Ya akai ku kuka fara sani...? Meke faruwa...?”

Gaban Sameer ya fad’i don bai sanar dasu cewa shi ya buge Hafiz ba.... Baba Alhaji ya kuma fad’i cikin hasala...
“Usman ka sanar dani meke faruwa... Ya akai kaida d’anka ku labarin had’arin ya soma riska...?”
Dukda jama’a dake faman kai komo bai hana Baba Alhaji d’aga murya yana surfa bala’i ba....
Abbah ganin Yayan nasa zai tara masu jama’a ya d’an bud’e murya yace “Yaya baka fahimta ba... Sameer shine ya kiramu yake sanar damu kasan cewa shi ma’aikacin lafiya ne....”
Baba Alhaji yace “Wanene kuma Sameer...?”
Sameer ya d’ago idanu yana dubansa sanda Abbah yake furta “Dahnah Ma’aruf...”
K’are masa kallo Baba Alhaji yayi ba tareda ya furta komai ba kana ya kuma sab’a babbar rigarsa yabi bayan likitocin don jin bayanin hoton k’irjin da sukaima Hafiz.... A cewar likitocin ya sami rauni sosai ta cikin k’irjinsa dad’ida k’ari alamu sun nuna cewa yana cikin matsanancin tashin hankali da damuwa had’arin ya samesa wanda ya janyo zuciyarsa tai rauni sosai....

Sameer ya dafe kansa a hankali sanda Shamsu ya janyo hannunsa suka keb’e da abokin nasa....

***

Washe gari Nabilah na had’uwa da Yusrah a makaranta sai rungumeta tai tana kuka sosai, lokaci guda take furta “Yusrah ina sonshi... Wllhi ina sonshi, na kasa yakishe tunaninshi cikin zuciyata....”

Tausayinta ya cika Yusrah, rik’o hannunta tai da sauri suka fice daga ajin dashike babu malamin da ya shigo, nan suka keb’e yanda Nabilar ta labarta mata komai, duk yanda abin ya kasance....
Yusrah ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “K’awata ki kwantar da hankalinki ni wllhi inaji ajikina keda Khalid had’in Allah ne kuma d’an adam bai isa ya rabaku ba... Da sannu al’amara zasu daidaita bayan sunyi zafi... Kar ki mance duk tsanani na tareda sauk’i, kawai kici gaba da addu’a Allah ya kawo maku mafita....”
Jinjina kai Nabilah tai ba tareda furta komai ba...
Yusrah ta d’an murmusa tana dubanta kana tace “Ikon Allah da idan akacemin k’awa zata fad’a kogin love haka zance wllhi k’aryane... Where’s the tough Nabila that I used to know... Nabilar da maza basa gabanta... Mafad’aciya wacce baka gano lagonta da wuri... Lallai Khalid ya cire tuta cikin maza tinda har soyayyarsa ke neman canza wannan Nabilar daga mafad’aciya zuwa mai sanyi....” Dukan da Nabila ta kai mata ya sanyata shanyewa tana mai ci gaba da dariya...
Nabila ta galla mata harara tana mai tattare books d’inta take fad’in “Sai ki tashi muje ai gashi can ya shigo...”
Yusrah bata daina zolayarta ba har suka shige aji.....


A b’angaren Zulfa’u kuwa tana zaune ne kurum a office amma zuciyarta na wani wajen daban....
Atika ce ta shigo ta risketa a haka, janyo kujera tai daga can gefe ta zauna tana mai bud’e folder d’in dake gabanta had’ida ciro takardan da zasu gudanar da shirin yau.....




SameenaAleeyou 📚




*INDA RAI*
_................DA RABO_





*65*


Duk maganganun da Atika keyi sam Zulfah ba sauraronta take ba, ta ije takardun hannunta tana mai duban Zulfa’un.... D’an zungurinta da biron hannunta tai kana tace “Wai lafiya kike...?”

Nannuyan ajiyan Zuciya Zulfa’u ta sauk’e kana ta d’an shafi fuskarta tace “Lau nake.... Mu fara gudanar da shirin koh....”

Atika ta jinjina kai bawai don ta gamsu da amsar Zulfa’un ba kana tai alamu ga mai saka sauti da hannunta, suka rufe kunnuwansu da headphones su duka biyun ko wacce da takarda hannunta kafin suka soma gudanar da shirin......

****
Misalin k’arfe goma na hantsi Sameer ya shigo sashen Mamani, a parlor ya risketa ta ida shiri don dama ita yazo d’auka su tafi asibiti can wajen Hafiz.... Raihanah da Naja’atu na zaune daga gefe gaba d’aya suka gaidashi... Ya amsa cikeda kulawa sanda Mamani tai kiran Najah tazo ta duba mata takalminta maras nauyi parlorn ya rage saura Sameer da Raihanah, idanunsa naga ciwon Raihanan yana ganin yanda yake healing slowly... Gaba d’aya bata sakewa idan yana dubanta duk sai tajita ba’a sake ba haka nan, muryarsa ta kuma sinkayowa yanai mata yaya jiki, ta amsa a tak’aice... Ya jinjina kai kana ya k’arada “Salma tazo jiya....?”
Nan ma jinjina kai ta kumayi kana tace “Eh tazo...”
Ya jinjina kai a hankali ba tareda ya kuma furta komai ba.... Fitowan Mamani da Naja’atu ne ya katse firan nasu...
Mamani ta dubi Sameer tace “Ai sai muje koh... Ke Naja’atu ince kinzo mu tafi tarene...?”
Naja’atu tai saurin jinjina kai kana tace “Eh Mamani...”
Sameer yace “Bara naje na kunna motar sai kun fito...”
Mamani ta jinjina kai tana mai fad’in “Yauwa gamu nan fitowa....”

Sallama Raihanah tai masu kana ta basu sak’on gaisuwa su isar zuwaga Yayanta Hafiz da addu’an sauk’i a garesa.... Suna fitowa ne suka had’u da Marliya itama ta take masu baya suka d’unguma gaba d’aya...
Dashike Shamsu ne zaune gaban motar hakan ya sanyasu duka zama a bayan motar, a hanya Marliya ke tambayan Naja’atu jikin Sahariyya don tin dukan da Hafiz ya mata har yanzu bata sami ishesshen lafiya ba, hannunta guda ya karye haka nan ta sami rauni a k’afarta...
Gaba d’aya Hajiya Haule ba a hayyacinta take ba, abubuwa suna kan faruwa ba yanda taso ba ga babban abinda yafi bata mamaki shine tun jiya da aka kawo Hafiz asibiti matarsa Sawwama bata tako k’afarta ba, wannan abu sosai ya dami Hajiya, tai k’udirin da zaran wasu awannni sun shura bata ganta tazo ba toh zata garzaya can gidan Hafiz d’in ta duba ko lafiya ko mai ya hana matarsa kasancewa dashi a daidai irin wannan lokaci....

Isowarsu da kad’an suke samun labarin farkawan Hafiz d’in... Kalman Zulfa’u itace a bakinsa sanda ya farka... Hajiya Haule dake zaune gefensa wani k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi... Ta mik’e zunbur tana karanto hamdala had’ida tambayarsa mai yakeso.... Maimakon ya bata amsa sai sunan Zulfa’u da ya kuma kira.... Daidai lokacindasu Abbah da Sameer suka shigo d’akin...
Hafiz yaci gaba da fad’in “Hajiya ki taimakeni ki ceceni ki kirawo min Zulfa’u... Inaso na rok’eta gafara kafin na bar duniya.... Hajiya bazanso na mutu da hakkinta ba....” Ya k’arashe

Please Login or Register in order to submit comment