Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazataji ba ma I believe Aunty B can handle them kafin ta fito ta sallamesu.... Please ki zauna karki fito ina zuwa...” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye ta nufi tsakar gidan yanda Aunty Bara’atu taimasu Yesmin d’add’aya cikin salama...

Ko kad’an basu fasa rashin mutuncin da sukayo dakonsa suka shigo dashi gidan ba, haka dai da k’yar aka samu suka fice a gidan bayan sun gama zuba rashin mutuncinsu, gaba d’aya illahirin mutanen gidan babu wanda ya biyesu har suka k’araci tsiyarsu suka fice bayan Aunty B ta tilasta masu cewa ko su fice ko ta kirawo masu ‘yansanda....
Itakaw Marliya tas tayi video d’in su Siyama sanda suke zuba rashin mutuncinsu, suna ficewa ta koma d’aki wajen ‘yar uwarta....
A daidai lokacin da bak’i ‘yan office d’in su Zulfah suka zo mata ta’aziya...

***

Mamy ta kasa daina duban Sameer dake jikin window yana amsa waya, dukda cewa yau d’in tayi rashin jikarta d’aya daga cikin ahalinta sai gashi Allah ya maido mata d’aya daga cikin ahalinta, tabbas dole tai godiyawa Ubangijinta domin Shi d’in mai yalwata rahamarsa ce ga bayinsa, idan ya karb’e maka wani abin sai ya canza maka da wani abin domin ya zamto rahama a gareka....
Har Sameer ya ida amsa wayar Mamy bata daina dubansa ba wani irin murmushi ne wanda sam batasan tanayi ba shine saman labb’anta....
Sameer ya d’an kaikaito yana dubanta, wani sanyi da ya jima baiji ba cikin zuciyarsa yaji yana sauk’a masa a hankali..... Lumshe kyawawan idanunsa yai had’ida sakin sassanyar murmushi kana ya jefa wayarsa a aljihu ya k’araso gareta...
Daga can gefe da ita ya d’an zauna cikeda kunya da rashin sabo, itama Mamy din hakan ne ya faru da ita...
Murya a d’an k’asa Sameer yace “Ammm zan wuce zan koma asibiti...”

Mamy tace “Ita Raihan fah...? Jikin nata da sauki sosai...?”

Sameer ya d’anyi jim kana yace “Wayar da muka ida da colleague d’ina kenan, kar ku damu.... Please kar ki da’ga hankalinki In sha Allah zata sami sauk’i....”

Mamy ta jinjina kai a hankali kana tace Allah shi yarda, anjima Lami zata taho sai na biya na duba Raihanar kafin na shige gida sabida ‘yan gaisuwa sunata min waya a nan kuma Abbanku baisan da labarin ba har yanzu...”

Sameer ya jinjina kai kana yace “Hakane... Ya kamata a bar Abbah da batun sabida heart d’insa har yanzu weak ne sannan ga shock d’in da ya samesa na bayyanata... Zan wuce yanzu anjima sai nazo na d’aukeki....”
Mamy ta jinjina kai kana ta k’arada “Toh shikenan Allah shi taimaka ya kuma tsare su kuma ya basu lafia...”
Sameer ya amsada Ameen cikeda risinawa, daidai nan wayarsa ta d’auki ruri...
Lambar Mummy ya gani tana kiransa, ya d’an kai dubansaga Mamy kana ya d’aga wayar yana mai sadda kansa k’asa...

“Hello Mummy...” Kalaman da Mamy ta iyaji kenan kana Sameer yasa kai ya fice, ta bishi da kallo cikin tsananin sanyin jiki jin ya ambaci wata da Mummy wacce ko shakka batayi tasan Mahaifiyarsa ce data rainesa, d’ansu ya zamto mai iyayi hud’u... Ta k’arashe tinanin tana mai komawa zuwaga d’akin Abbah tamkar wacce k’wai ya fashema a ciki...

Daga d’aya b’angaren Mummy taci gaba da fad’in “Son, I was so worried, you haven’t been answering any of my calls... Kaga dole hankalina ya tashi...”

D’an jim yai yana mai karya steering mota kana yace “I’m sorry Mummy, I should’ve called to at least let you know na isa lafia, but mummy ever since I arrived here things haven’t been easy... I’m sorry for making you worried Mummy...”

D’an sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Alhamdulillah tinda kana lafia, but please next time kar ka sake irin hakan...”
In sha Allah hakan bazai sake faruwa ba... I’m driving right now, I’ll call you back kinji Mummy na...”

Nanma ta jnjina kai kaman na gannta... Har zai katse kiran ya kuma jiyo muryarta “Sameer.... I know by now iyayenka na asali sun fahimci wanene kai sun fahimci cewa you’re their long lost Son...”

Sameer ya d’anyi jim kana yace “Yes...Mummy.....”

Ta murmusa a hankali kana tace “I’m so happy for you Son, na maka murnar kasancewa da iyayenka na asali...”

Sameer yai murmushi a hankali kana yace “Na gode Mummy nah...”

Hajiya Fatahiyya murmushi saman fuskarta tace “Drive safe...!”

Har zata katse kiran Sameer ya katse ta da fad’in “Mummy.... I love you.... Always remember that...”

Cikeda jin dad’i k’walla na gangarowa Hajiya Fatahiyya tace “I know Son, and I love you more... Allah shi maka albarka...”

Sameer ya amsa da Ameen fuskarsa d’aukeda murmushi kana sukai sallama... Duk sai yaji jikinsa yayi sanyi tsananin tausayin Mummynsa ya tufesa a haka ya isa asibitin....

***

Fitowarsa kenan daga sashen Mamani, ya tsaya yana duban sashensu Nabila, gani yake tamkar zai hangota, dashike ‘yan gaisuwa sun d’an d’auke k’afa sabida almuru data sako kai...

Kaman daga saiga Marliya ta shigo daga gate dawowarta kenan daga rakiyan ‘yan ajinsu da suka shigo mata ta’aziya...

Tsaye tai tana duban Khalid da kacaukam hankalinsa kega kallon k’ofan sashensu... K’arasowa tai yanda yake bakinta d’aukeda sallama....
Khalid ya saita kansa had’ida amsawa Marliya sallamanta...
Ta gaisar dashi ya amsa da sakin fuska don sarai ya ganeta k’anwar Nabilah ce...
“Addah Nabilah kake jira...?”
Marliya ta tambaya...
Baikaiga bata amsa ba Marliya tace “Bazan b’oye maka ba wllhi idan zaka kwana a nan Addah Nabilah bazata kuma saurarenka ba bayan abinda sisters d’inka suka shigo gidan nan sukayi....”

Khalid ya kuma dubanta da tsananin mamaki kana yace “Sisters d’ina...?”

Marliya ta jinjina kai tace “K’warai Sisters d’inka... Ko basu ne wad’annan ba...?”

Ta k’arashe tanai masa nuni da video d’in data masu sanda suke zage zage da zuba rashin mutunci...

Tsananin mamaki ya kama Khalid sanda yake furta “Siyama... Yesmin....!”

Marliya ta katse video d’in kana taci gaba da fad’in “Now I believe you understand why I don’t want you for my sister, babu wacce zataso taga ‘yar uwarta ta shiga irin wannan family d’in, dan Allah kayi hak’uri kar ka saka ‘yar uwata cikin matsala, this family is going through a lot already, kafin labarin abubuwan dake faruwa su isaga iyayenmu dan Allah k’yale ‘yar uwata ko zata fice daga matsin naka ‘yan uwan... Babanmu wani irin mutum ne wanda ba kowa ke fahimtarsa ba kuma kaga ba lafiya ne dashi ba.. Sannan mahaifiyarmu sama da shekaru talatin kenan tana cikin alhini da damuwa na b’acewar Babban Yayanmu sannan Sister d’inmu babba tayi fama gidan miji ga kuma rashi d’iyarta da mukayi a yanzu uwa uba ga ‘yar uwarmu kwance gadon asibiti... Baka tunanin muna ciki matsaloli already... Dan Allah kar ka k’ara kan wanda muke fama dasu, na sani nayi shishigi wannan ba hurimina bane... I only care about my family ne kawai that’s all...” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Jikin Khalid yai sanyi sosai tamkar wanda aka tsoma a freezer.... Ya stinkayo muryar Marliya tana ci gaba da fad’in “I know I shouldn’t be telling you any of this...Maybe idan kaji ka rabu da ‘yar uwata....”

Da idanunsa da suka matuk’ar rinewa lokaci guda yake dubanta, zaka iya jiyo hucin dake fitowa tin daga k’irjinsa.... Dabda fuskar Marliya ya matso da nasa fuskar wanda ya sanyata tsanin tsoro da fad’uwar gaba, kaman zai magana sai kuma taji baice komai ba saima sa kai da yayi ya fice daga gidan cikin sauri tamkar zai kifa k’asa...

Marliya ta sauk’e ajiyan zuciya kana ta jiyo ta nufi cikin gida yanda sukai idanu hud’u da Aunty B....

***

Tafe suke shida Dr Awwab abokin aikinsa yanda Awwab d’in yaci gaba da fad’in “Already munyi moving d’inta to ward, tana room 3....”

Jinjina kai Sameer yai kana yace “Alright I’ll... check on her.... Thank you Awwab...” Ya k’arashe yana mai sa kai zai shige....

Saurin katseshi Awwab yai da fad’in “Dr are you sure you’re alright...?”

Kallonsa kurum Sameer yai kana yace “I’m fine... Why?”

“So why are you thanking me anyway... Aikina nake bai kamata kamin godiya ba....”

Sameer ya k’ak’aro murmushi da gefen bakinsa kana yace “Dukda aikinka kakeyi dole nai maka godiya cos I just found out she’s... She’s...”

Awwab yai shiru yana jiran yaji mai Sameer zaice, baikaiga bud’e baki ba Sameer ya k’arashe maganar nasa da fad’in “She’s my sister...”

Murmushi Awwab yai kana yace “Oh really... da munsan cewa k’anwarka ce tun a fari da bamu bari kayi mata aiki ba...” Ya k’arashe yana murmushi irinta wasa..
Murmushin shima Sameer yai kana yace “I’ll go ahead...”

Awwab yace “Alright Doc nima zan wuce gida tinda kazo...”
Sukai sallama Awwab ya wuce Sameer ya nufi room d’in da aka kwantar da Raihanah....

Lullub’e take cikin farin bandage kusan illahirin jikinta idan ka d’auke fuskarta....
Ya jima sosai yana duban fuskarta da tun shigowar sa idanunta ke lumshe tamkar mai bacci.... Yakai dubansa ga hannayenta wanda suma ba rufe suke cikin bandage ba alamun suma basu k’one ba.... Nan ya hangi yatsun hannun nata suna motsawa a hankali...
Sameer ya k’araso jikin gadon nata sosai yana dubanta yana mai tuna sanda suka soma had’uwa, yana cikin tunanin ne ya soma jiyo muryarta tamkar mai kuka tana furta “”Kausar... Kausar ina Kausar... Aunty Sahariyya kar ku k’onata please ku k’onani instead...!” Ta k’arashe tana fincika tamkar zata tashi daga gadon...
Sameer yai saurin rik’e hannunta guda ya hanata tashi.... Lokaci guda ta koma tayi lamo cikin gadon tamkar taci gaba da baccin, har lokacin idanunta a lumshe suke....
Sameer yai mata k’uri tsananin tausayinta na d’awainiya dashi... He was right all along... Da ganganci da son zuciya aka k’onasu tinda ya tab’a ganin irin azabtarwa da ukuba da ake masu a wannan gidan, tsanar Hajiya da ‘ya’yayenta ya kuma tasiri a zuciyar Sameer, idan kuwa har da gaske da ganganci aka kashe masa niece aka k’ona Raihanah he’ll press charges, sai yanda k’arfinsa ya k’are wajen karb’a masu ‘yancinsu... Ya k’arashe zancen zucin nasa shi kad’ai yana mai sakin huci...

****

Ta k’ure sautin tv tana cashewa tana celebrating nasaran da suka samu na raba Nabilah da Khalid kaman daga sama taji an banko k’ofar... Tamkar sauk’an aradu haka Yesmin taga Khalid tsaye cikin parlorn, fuskarsa da idanunsa sun koma jazir tamkar bashi ba...
Yesmin ta sandare sanda jikinta ya d’auki rawa, sosai ta razana da ganin yanayin Khalid, ta soma jada baya zata gudu, kafin tai wani aune saiji tai ya fincikota ya d’auketa da wata irin gigitacciyar mari, ta saki ihun azaba, bata gama susan b’angaren fuskarta da marin ya sauk’a ba ta kuma jin wata lafiyayya ta d’aya b’angaren... Yesmin ta kuma daburcewa tana sakin ihu... A gigice tasa kai zata fice a guje daga parlorn Khalid yai saurin sharb’e k’afafunta ta zube a k’asa, fincikar wayoyin kayan kallon yayi ya shiga labtawa Yesmin tamkar an aikoshi... Yesmin sai ihu take tana kiran cousin tazo ta taimaketa....
Siyama da fitowarta kenan daga wanka ta nufo parlor babu shiri jin ihun Yesmin yak’i k’arewa tamkar wacce ake zarema rai...

Baki kurum Siyama ta saki tana kallon ikon Allah yanda Khalid ke jibgan Yesmin, ta gyara d’aurin towel d’inta ta isa da sauri ta fincike wayar ganin Khalid zaiyi kisa...
A tsananin fusata Yesmin ke furta “Khalid meye haka, what do you think you’re doing... What’s gotten into you... Kasheta kakeso kayi....?” Ta k’arashe cikin tsananin huci...

Banda mugun kallo baya watsawa Siyama komai, cikin wata irin dakakkiyar murya yana mai nunata da d’an yatsa yake furta “Don’t let me lose the little respect I have left for you.... You better respect yourself Siyama...!”
Ya maido da dubansaga Yesmin dake zube magashiyan a k’asa tana nishi yace “Ke kuma ni ba sa’anki bane ban fara irin wannan wasan dake ba, this should be your first and last warning, don’t you dare meddle with my affairs.....!” Yana k’arashewa yai jifada igiyar wayan hannunsa ya fice tamkar kububuwar maciji.....


SameenaAleeyou📚




*INDA RAI*
_...............DA RABO_


*50*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Tabbas tafiya Kaduna babu shiri ya kamasu, domin kaw dole Ammi taji wannan labari, ko shakka babu yarinyar nan asiri taiwa Khalid, Ammi has to know about this idanma ta kama a nemawa Khalid taimako ne sai a masa... Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye ta nufi wardrobe ta shirya....
Nan ta fito parlor ta tadda Yesmin har lokacin kuka take....
Siyama ta d’an rausayar da idanu had’ida fuzar da iska kana ta nufi Yesmin d’in...
“Cousin ki daina kukan nan haka you’ll fall sick, dan Allah kiyi shiru haka nan...” Ta k’arashe tana dafe Yesmin d’in cikin sigar lallashi...

Idanu a kod’e Yesmin ta d’ago tana dubanta kana tace “Cousin ni Khalid ya buga haka, tinda nake my entire life babu wanda ya tab’a duka na haka, kai ko Mum bata tab’a zungirina ba sai gashi yau namiji wanda ko aurensa banyi ba ya tara min na jaki.... Haba haba cousin meye laifina don kawai nace ina sonshi...” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

K’wafa Siyama tai kana tace “Ki kwantar da hankalinki Cousin da gani ko ba’ace ba Khalid an juya masa kwanya ba haka kurum aka barshi da zaizo ya mana wannan cin kashin kan wata banza kucakar yarinya, kar ki damu Yesmina wllhi idan dai ina numfashi Khalid bazai auri yarinyar nan ba, gobe gobe zamu wuce Kaduna Ammi tace mun ma Daddy ma yana hanya goben gwara susan halinda d’ansu yake ciki...”
Da wannan Yesmin ta sami sauk’i cikin zuciyarta, tuni ta nufi d’aki had’a kayanta domin gobe asubahin fari zasu dira garin Kaduna....

***

Misalin k’arfe 9:30pm Sameer ya shigo gidan, babu kowa parlorn sai TV dake faman aiki shi kad’ai, ya d’auki remote control ya kashe kayan kallon, kai tsaye d’aki ya nufa yanda ya tadda Siyama na had’e kaya cikin suitcase.... Da tsananin mamaki yake dubanta dukda’ bai iya furta koda kalma guda ba sai dubanta yake faman yi, jin shigowarsa ya sanyata aje rigar hannunta cikin jakar kana ta iso gareshi fuska d’aukeda murmushi tana fad’in “Partner sannu da zuwa... Kasha hanya, naji mamaki da baka iso ba tuntuni, kodashike I guess asibiti ka wuce aiki ya rik’eka acan, are you hungry..? Muje nayi serving d’inka...” Ta k’arashe tana k’ok’arin janyo shi...
Har lokacin dubanta yake fuska d’aukeda alaman tambaya... Dakatar da ita yai da fad’in “No its ok, I’m alright.... Can you explain to me what this is for...?” Ya k’arashe yana nuni da suitcase d’inta....

Murmushi ta saki kana tace “Oh d’azu Ammi tai waya Dad yana hanya gobe, kasan ya jima baya k’asa so ya kamata naje mu tarbeshi, we are leaving to Kaduna first thing tomorrow morning nida Yesmin....”

“With whose permission...?” Yai maganar fuska babu alamun wasa yana mai zura mata idanu...

Kallo ta bisa dashi kana tace “Sameer ce maka nayi fah Ammi ce ta kirani so kake nace mata bazanzo ba, kar ka mance she’s my mother....”

K’uri kurum ya mata kana yasa kai ya shige yana mai rage agogon hannunsa yake fad’in “You’re not going anywhere....” Bai jira cewarta ba yasa kai ya shige bathroom...

Tirk’ashi! Kallo tabisa dashi har ya shige tana mai tsananin mamakin yanda gaba d’aya Sameer ya canza mata, da a bayane basai ta tambaya ba duk abinda tayi daidai ne amma yanzu wai har order da doka yake kafa mata, toh ko dai ya daina sonta ne...? Ta tambayi kanta, babu amsa, cikin sauri ta lalumi wayarta ta fice kiran Laila domin neman shawari....

***

Aunty Lami sai faman safa da Marwa take, takai mari takai gawro ita kad’ai, yau d’in ita zata kwana wajen Abbah, Mamy nacan zata duba Raihanah kafin ta wuce gida sabida masu zuwa mata gaisuwa, ita kaw Raiha Mamani ce a wajenta ita zatake kwana da ita dukda cewa ba wani abin zata iyayiwa mai jinya ba da naka a kusa yafi, ma’aikatan lafiyar suke komai a asibitin...

Zufa ya kuma ketowa Aunty Lami gani take tamkar Ma’aruf ya ganeta ya gane fuskarta tsaf itace matar data d’aukesa a kasuwa ta b’anb’are hannunsa daga na mahaifiyarsa a lokacin da Mahaifiyar tasa ta fice hayyacinta tana mai neman d’auki na jama’a sabida haihuwa data zo mata bagatatan... Ta kuma share gumin tana mai sakin numfashi da k’yar...
Abbah ya bita da kallo cikeda mamaki don batasan idanunsa biyu ba, kaman daga sama taji muryarsa ya ambato sunanta “Lami...”
Ta juyo a firgice alamun tsoro da firgici a tattareda ita....
Bata iya amsa Abbah ba sai zuba masa ta mujiya da tayi....
Abbah ya d’an gyara daga kwance zuwa kishingid’e kana yace “Lafiya kike tsaye wajen, mai ya hanaki bacci...?”

Tambayar da Abbah ya mata sai taji tamkar Abbah ya riga yasan komai, ta rasa mai zatace sabida lokaci guda taji tamkar harshenta ta zarge, da k’yar ta iya furta “La... lafiya kawai banjin baccin ne akwai wani abinda kake so ne....?”

Murmushi d’auke fuskar Abbah domin gaba d’aya yinin ranar annuri ta gaza d’aukewa a fuskarsa sabida d’imbin farin cikin da ya tsinta kansa ciki yace “A’a bani buk’atar komai, hasalima ni ji nake na warke banida wata buk’ata da ya wuce su sallameni a wajen nan haka na koma gida cikin ahalina mu kasance gaba d’aya tare....”
Zuciyar Lami ta kuma tsinkewa don ita kanta ta jima bataga Abbah cikin irin wannan yanayi na farin ciki ba....
Tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi kana ta k’araso gefen gadonsa ta zauna... Tana mai sakin murmushi take fad’in “Alhaji ga dukkan alamu kana cikin farin ciki...?”

Abbah ya jinjina mata kai cikeda aminta kana yace “K’warai Lami ina cikin farin ciki wanda na rasashi a baya, Ibangijina ya dawo min da wannan farin cikin...”

K’irjinta ya kuma bada Dam! Kardai sunsan cewa wannan likitan d’ansu ne Ma’aruf.... Idan kaw haka ne dole tasha cikin Abbah taji komai...
Ta kuma gyara zama murmushin bai bar saman fuskarta ba tana mai k’ok’arin gyarawa Abbah pillow da yake bisa tace “Alhaji halan wani abin ne ya faru...?”

Abbah ya kuma dubanta da fuskarsa mai k’unshe da tsantsan annuri kana yace “Babban al’amari ya faru Lami da sannu zaku fahimci hakan gaba d’aya...”

Tinda taji hakan tasan Abbah baiyi niyyan ya sanar da ita komai yanzu ba, tasan halin mijin nata domin kaw wani irin baud’edd’en mutum ne haka nan kalamansa wasu lokutan a baud’e suke zaiyi magana amma sai ka rasa gane inda ya dosa,idan kaw bazai fad’i mata ba ita zata sanar dashi mutuwar jikarsa idan yaso hankalinsa yayi gida komai ya fanjama fanjan kawai, ta gaji ta gaji da zullumi gwara ta sani idan Ma’aruf ya bayyawa iyayensa ne.... Ita a halin yanzu batama k’i Abbah ya mutu ba akan asirinta ya tonu....

Bata kuma cewa komai ba ganin Abban ya lumshe idanunsa tamkar mai bacci, bayan giftawan wasu dak’ik’ai data tabbatar yayi baccin ta fice kiran Haule domin susan madafa....

***

A b’angaren Siyama kuwa tas ta d’auki shawarin Laila cewa kada ta bari wani k’ato ya mata mulkin fir’aunanci a gidanta da sunan yana aurenta, idan ta riga ta sabar masa da sai abinda yaga dama za’ai shikenan ta zama wofi a cikin gidanta don shi namiji tankar yaro ne duk abinda ka d’aurashi bisa shi yakeyi don haka koda wasa kar ta bari wannan raini ya shiga tsakaninsu, tuni taci gaba da shirinta washe gari sassafe ko sallama Sameer baici arziki a masa ba don shi tuni yayi asubanci ya nufi asibiti duba yaya patient d’insa ta kwana, fitarsa da kad’an suma suka d’aga zuwa Kaduna....

***

A gidan Hafiz kuwa tinda garin Allah ya waye yake jinsa wani iri haka nan, wani ikon Allah safiyar ranar da tunani da begen d’iyarsa Kausar ya tashi domin kawa daren jiyan yayi mafarki da ita, yarinyar ta k’ara masa girma tayi kyau daga can nesa taketa k’ek’eta masa dariya saidai da ya nufota zai d’auketa sai ta b’ace ma ganinsa... Tinda ya farka daga wannan baccin kewar d’iyarsa ya damesa, baikobi takan Sawwama ba ya fice cikin sauri da niyyan ya soma zuwa Kasuwa ya duba shago daga nan ya d’an sai mata tsaraba yakai mata...

Yana isa Kasuwa dashike yanzu a kantin mahaifinsa yake zama don shi yanzu baida kantin baida jari baida komai a d’an zaman da yake a kantin Alhaji mahaifinsa yake d’an samun na kashewa.... A bakin kantin ya tarar da Tasi’u yaron shagon yanzu yakeda niyyan bud’ewa, suka gaisa da Tasi’u, nan Hafiz ke tambayarsa Alhaji bai iso ba....?

Tasi’u yace “A’a ai kaman rashi naji ana cewa anyi, nima dai banje ba domin jiya ma ni na kulle kantin a hannuna mabud’an suka kwana, daga nan nima dama can zan wuce....”

Hafiz ya dubesa da mamaki kana yace “Rashi...? Toh waye ya rasu....?” Badai Abban su Zulfa’u ba don yasan shine a asibiti...

Tasi’u yace “Wllhi nima dai ban sani ba amma ina tsamman ba babban mutum bane...”

Hafiz ya jinjina kai kana yace “Shikenan Tasi’u bari na wuce can gidan...”
Tasi’u yace “Toh Maigida a sauk’a lafiya, Allah jik’an musulmi....”
Hafiz ya amsa da Ameen kana ya shige yana tunanin toh kodai a mak’ota akayi rashin tinda da ace a gida ne da ko ba’a kira wayar salulansa ba za’a kira na matarsa... Da wannan tunanin ya hangi teburin mai kayan wasan yara, ya saki murmushi a hankali kana ya k’arasa ya sai doll baby da kuma dangin kacau kacau....

Sai buga sauri Hafiz yake ya isa gida yaji abindake faruwa ya kuma dank’awa Kausar tsarabarta, tuni ya tari babur ya d’ale yana mai sanar da mai babur d’in yanda zaya kaisa...

Babban tashin hankalin da riski Hafiz shine ganin taron mutanen a k’ofar gidan mahaifinsa suke....


SameenaAleeyou📚



*INDA RAI*
_...............DA RABO_


*51*


*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Da k’yar k’afafunsa suke iya d’aukansa, ji yake gaba d’aya k’afafun nasa suna masa nauyi, waye ya mutu a gidansu, makokin waye ake...? Meke faruwa ne...? Cikin sakanni zuciyarsa ta dinga jefo masa tambayoyi, daga can ya hangi Baba Alhaji mahaifinsa na masabaha da mutane suna kuma masa ta’aziya, zuciyar Hafiz ta kuma tsinkewa.... Yaci gaba da d’aga k’afafunsa da k’yar sanda ya nufo kusan mutanen sosai yaji ana cewa Allah shisa mai ceto ce....

K’afafun Hafiz suka d’auki rawa ba tareda yasan dalili ba... A daidai lokacin da sukai idanu hud’u da mahaifinsa sanda wani mutumi ke furta “Ga mahaifin yarinyar ma, sannu sannu kaji koh Hafizu Ubangiji ya baka masu zama yasa ita kuma mai ceto ce...”

Sam Hafiz bai iya amsa shi ba, hasalima bai fahimci mai yake nufi ba gaba d’aya ya zama lost and confused.... Duru duru yake ganin mutane yanda sukai chaa sunai masa gaisuwa, yana jiyo muryoyinsu tamkar daga nesa....
Yana ganin sanda mahaifinsa ya mik’e ya nufi cikin gida bayan ya rakasa da muguwar kallo....

A gigice Hafiz ya tsallake mutanen ya nufi cikin gida yana mai kiran mahaifin nasa.... Cak yaja yayi birki sanda yaga mata sun cike farandar mahaifiyarsa... Tamkar wanda ruwa ya shanye haka ya nufi dandatson matan yanaji kaman zai kifa da k’asa...
Naja’atu ce ta nufosa a guje ta rungume tana kuka sosai....

“Najah lafiya , meke faruwa... What is happening... Talk to me Najah... Ina Kausar.... Where’s my daughter...? Look I bought her a lot of toys, nasan zatai murna... Kin gani....” Ya shiga k’ok’arin bud’e ledar yana ciro kayan wasan.....
Ba Naja’atu dake rungume dashi tana kuka ba harta mutanen dake zaune farandar saida sukaji k’walla na zubo masu...
Cikin tsananin kuka Najah ke girgiza masa kai sanda yake kuma tambayarta d’iyarsa.... Cikin muryar kuka take furta “Ya Hafiz Kausar babu....”

Cak ya tsaya yana binta da wani irin duba cikin rashin yarda da kalaman da suke fitowa daga bakin k’anwar tasa yake furta “What do you mean Kausar babu... Mai kike nufi Naja’atu.....?”

Cikin Kuka Najah ke fad’in “Yaya Kausar ta rasu, mun rasa Kausar , Allah ya karb’i abinsa....”

Fuzgewa yayi daga rik’on data masa yana mai binta da wani irin duba yake girgiza kai kana ya shiga furta “No no no, my daughter is alive.... D’iyata tana raye..... I know she’s alive... Ni na sani... Ina Hajiya... Ina Hajiya nasan tana wajen Hajiya... Yanzu zan bata toys d’inta.....” Tamkar zararre haka shiga surutai, lokaci guda ya nufi d’akin Hajiya gadan gadan bai damu da matan da yake haye kansu ba shidai kawai yaga Kausar d’insa...

Wata Innar Hajiya ce ta rik’esa tana basa baki tana fad’in yayita karanto innalillahi.... Inaaa Hafiz sai fuzgewa yake yana tambayan ina aka b’oye masa d’iya... Fad’i yake “Hajiya nasan baki son zamanta a nan fine na maki alk’awari daga rana mai kaman ta yau kin gama rik’onta zan d’auketa na tafi da ita.... Ni zan rik’eta zan rik’e kayana... Please ki fito min da ita I know she’s in there ku bani d’iyata please....” Ya k’arashe yana nuni da uwar d’akin Hajiya....
Innar Hajiya ta kuma jaddada masa cewa d’iyarsa ta rasu ta rasu babu dawowa...., Hajiya ta cafe da masifa tana mai furta “Da kin k’yaleshi ya shigo d’akin ya duba tinda ya tab’a

Please Login or Register in order to submit comment