Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na amshi k’addarar na rasa Zulfa’u kai waye yace maka na rasata kenan... Wllhi sai yanda k’arfina ya k’are, ba yana gadara shi mai neman takaran kujerar governor ba idan shugaban k’asa ya tsaya takara Zulfa’u sai ta dawo gareni... Babu mutumin da ya isa babu wani d’a namijin da ya isa ya mallaki Zulfa’u bayan ni Hafiz not even wannan D’an siyasan, Ka fahimta...?!!!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye yana wani zazzaro idanu tamkar wani k’waro....Magaji ya murmusa a hankali kana yace “Abokina kenan, bakaci yak’i da yaron gida ba kana tinanin zakaci yak’i da uban Gida...? Hafiz lokaci yayi da zaka daina wannan damuwar, yanzu fah Zulfa’u ba sa’ar aurenka bace....!”
Hafiz dake faman danna masa harara jinjina kai yake kana yace “Na jima da sanin cewa baka k’aunar Farin cikina, bari kaji na fad’a maka tsaban kud’insa baya tsoratani, kyautar da yake ma ta riyace nayi imani dan ba har zuciya bane, wa ya sani ma ko d’an k’ungiyar shan jini ne ace a shekarunsa arba’in da ‘yan d’oriya ya mallaki irin wad’annan k’azaman dukiya aima dole ya tafiyarta ta hanyar siyasa tinda bata tsaftacecciyar hanya aka sameta ba dama... Ni dama ban tab’a sonshi ba tuntuni bak’in munafuki...!”
Magaji ya d’an murmusa kad’an “Hafiz kenan ya kamata kasan cewa ba duka ‘yan siyasa bane suka taru suka zama d’aya, komai da kake gani akwai na gari akwai na banza, ko wace irin hark’ace kuwa ba zallan siyasa ba harta cikin malamai akwai na kirki akwai na banza ‘yan kasuwanni ma’aikatan gwamnati da sauransu ka sani na gari basa k’arewa haka na banzan ma, toh ka dainayin kud’in goro kana zagin jama’a domin kaw Allah zai tsayar daku yai maku hisabi, kuma da kake cewa babu wanda yasan source d’in dukiyarsa ka mance shid’in gada yai daga mahaifinsa, ka mance sune masu Mutallab’s Mining company, kamfanin da gaba d’aya west Africa tayi zarra tayi fice bayan wasu manyan kafanonin da suke dashi, idan har zakai masa k’azafin d’an k’ungiyar asiri bakai masa adalci ba..”

A fusace Hafiz ya mik’e yana huci yake nuna Magaji da d’an yatsa “Zan maka kashedi na k’arshe daga yau kada ka sake cemin ga abinda zanyi tinda kai ba Ubana bane..!!!” Daga haka yasa kai ya shige fuuu tamkar zai kifa....
Jinjina kai Magaji yai cikeda mamaki had’ida tausayawa abokin nasa kana ya numfasa yace a fili “Eh lallai na yara kwanyarka ya tab’a Hafiz...” Magaji ya tina a da Hafiz ya sami Zulfa’u a b’agas dan dangin kyauta ya sameta yaita wulak’antata yana muzguna mata sai gashi yanzu da dik wani abinda ya mallaka bazai sameta ba, ta riga ta kufce masa, rayuwa kenan... D’an hakin da ka raina watarana shike tsole maka ido... Tabbas haka ne gashi ya faru kan abokinsa ya gani....

***

Har lokacin bai d’aga wayar ba saima k’ura ma wayar idanu da yai, shi harga Allah yanzu har tinanin d’aukan wayar Ammi yake, yasan maganar bazai wuce kan wannan mayyar yarinyar ba... Nabilah ta d’an dubesa taga yai k’urima waya, kaman ta tambayeshi ko lafiya sai kuma tai shiru had’ida maida idanunta kan yatsuna hannunta da taketa faman juya zoben dake yatsarta guda.... Tana a haka ta sinkayo muryarsa yana gaisuwa had’ida ambato Ammi.... Wani irin bugu k’irjinta yai tamkar an ije guduma, ta tuna karonsu da mahaifiyar Khalid gashi har yanzu basuyi wani tak’amaimen magana da Khalid d’inba balle taji ya matsayin aurensu wajen family d’insa.... Tana ganin yanda tin bayan gaisuwa ya k’urama waje guda idanu alamun daga d’aya b’angaren akwai abindake faruwa, dan shiru yai kurum yana saurarenta...

Ammi kaw taci gaba da bambamin masifa “Kan me zakai tafiya bazakai sallama da Yesmin ba, kuma tsaban wulak’anci da raini irin naka Khalid ka tafi har Abuja dik kwanakin nan ka kasa zuwa gidansu Yesmin ka gaida Aunt d’inka... Ya maka daidai, Allah ya baka sa’a kaci gaba da dik abinda kake....”
Khalid shaye da mamakin irin rainin dake tsakaninsa da Yesmin Wato ma k’ararsa takai wajen Ammi lallai yarinyar nan bata sansa ba har yanzu, amma ta nemi sanin ko shi wanene yanzu... Kasancewar ga Nabilah wajen kuma baiso ta fahimci akwai wata matsala ya sanyashi cewa “Ammi ban zauna bane, kiyi hak’uri zan kiraki back sai muyi maganar...”
A fusace tace “Khalid don’t you dare hang up on me, ban gama maka magana ba kana jina koh... Ba aiki ba idan uwar aiki ne ya tareka ka kirata ka bata hak’uri ku sasanta...”
Dunk’ule hannayensa kurum yake sabida tsananin tafasa da zuciyarsa keyi, wllhi sai ya cire rainin dake tsakaninsa da Yesmin hardai bata daina had’asa da mahaifiyarsa ba....
K’ok’arin saita kansa yai kana yace “Shikenan Ammi zanyi yanda kikace....”
Ammi tace “Yauwa yanzu dai naji batu... Allah shi maka Albarka.... Ga sets d’in akwatina da nai order sun iso, anjima Siyama zata d’auki pictures ta tura maka...” Bata jira amanarsa ba sukai sallama....
Shiru yai yana shafa wayarsa na d’an wani lokaci har saida Nabila ta d’an saci kallonsa, ko ba’ace ba kasan yanada damuwa dan duk k’ok’arinsa ya b’oye hakan zuciyarda ta damu dashi dole ta iya karanto hakan.... D’ago idanu tai tana k’ok’arin karatarsa Wannan karon idanunsu suka sark’e waje guda domin kaw shima d’in ita yake duba... Murmushi ya saki ganin tayi saurin maida idanunta k’asa, ya d’anyi gyaran murya kad’an yace “Wai ni teddy bear wannan sanne sannen da ake min na minene...? You know nafi sabo da masifarki, wannan sanne kai da shiru d’in duk ban saba dasu ba, ko sai mun tafi Kaduna ne a tsfeni ya k’arashe yana kwanto da fuskarsa dab nata.... Aiko kaman jira take ta jefa masa muguwar harara kana ta kuma kauda kai gefe...
Khalid ya murmusa kad’an yace “Yauwa better kinga da kika min wannan kallon yanzu na yarda teddy bear d’itace ba’a canza min ita ba...”
Wannan karon murmushi ta d’anyi ba tareda ta dubesa ba....
Shima murmushin saman fuskarsa yake dubanta kana yace “So Amarya ya taro...?”
A hankali ta amsa masada “Alhamdulillah..!” A tak’aice...
D’an gyara murya yai had’ida daidaita zamansa kana yace “Masha Allah...!” Gaba d’aya tattaro natsuwarsa ya kumayi kana yaci gaba da fad’in “Teddy bear... I know you’ve a lot of questions to ask, an saka bikinmu and you didn’t hear from me, banzo ba banyi waya ba, stuff like that... And you’ve every right to be mad at me... I’m sorry kinji koh... And I promise randa dik aka kaiki gidana I’ll explain everything to you kinji koh...”
Ita dai bata iya d’agowa ta dubesa ba har lokacin idanunta nakan zobenta da take juyawa... Idanun Khalid suka sauk’a kan abinda take, sosai lallen hannunta ya masa kyau special red one d’in da akai a fingers sosai suka masa kyau... Bata ankara ba saijin hannayensa tai saman nata... Tai saurin d’agowa tana dubansa shid’inma ita yake duba....
“kinji abinda nace...?” Ya tambaya yana tsareta da idanu ga k’irjinta dake matuk’ar bugu gashi yak’i sakin hannayenta saima murza yatsun da yake a hankali....A hankali ta jinjina masa kai alamun Eh dik wani iri take jinta, cikin dabara take k’ok’arin janye yatsun hannunta shiko Khalid yak’i saki saima dad’a d’an matsesu da yai ya nuna mata k’arfi kad’an... Ta d’ago idanunta masu cikeda tsoro wannan karon tana dubansa, Wato dai dik masifarta dai zai nuna mata k’arfinsu ba d’aya bane... Ya saki murmushi yana duban yanda dik ta wani daburce, kauda shirun yai da fad’in “K’unshin nan yayi kyau teddy bear... Yana gogewa a sake min wani dan inaso sosai...”
Harara ta d’an jefa masa wannan karon... “Ni ka sakemin hannu naje kafin a soma nemata....” Tai maganar tana turo baki....
Kallon d’an bakin nata da ya k’ware wajen iya tsiwa da masifa yake bai daina murza ‘yan yatsun hannun nata ba yake fad’in “Babu wanda zai nemeki sunsan da waye kike tare... Besides ko d’aukanki nai daga nan muka wuce babu mai tuhumata saidaima ace nayi daidai... Ko bazaki yarda ki bini bane...?” Ya k’arashe maganar sanda yake zame zoben da taketa wasa dashi a yatsarta...
Gajeran harara ta kuma galla masa kana tace “Tab, aiko kaini sukai yanzu bazan zauna ba dan sai na dawo na ida exams d’ina...”
Khalid ya murmusa yace “Meye a ciki kullum sai na kawoki kiyi ai... Saura nawa ne ki gama...?”
“Monday in sha Allah nake gamawa, saura last paper ne...!”
Khalid ya jinjina kai a hankali kana yace “Kinga zaman kano ya kamani.. Dan k’afarki k’afata bani barin garin nan without you teddy bear... So gwarama ki sakama ranki...” Ya k’arashe yana mai janyo wata k’aramar shopping bag dake gefen k’afarsa k’asa...
Ita dai kauda kanta gefe kurum tai, sinkayo muryarsa tai yana fad’in “Ni zan wuce, zan fara biyawa wajen Daddy first before na shige masauk’i tinda kink’i yarda ki bini.... Tashi muje Kimin rakiya...!”
Mik’ewa tai tana gyara mayafinta ta shiga bin bayansa a nitse... Saida suka kai k’ofa kana ya juyo yana dubanta yanda take takowa a natse da alama bata saba da d’aura zani ba, ya tako kusanta kad’an kana ya d’an rage murya yace “Being matar aure suites you teddy bear... Kinyi kyau sosai...” Nan ma bata amsa shi sai sakin murmushi da tai a hankali, Khalid ya kuma matsowa a hankali kana ya d’an rank’wafo saitin fuskarta, k’irjin Nabilah yaci gaba da bugawa jin d’umin numfashinsu kusan na juna, murya can k’asan mak’oshi yake furta “Anything for your Bear..?” Yanda yai maganar cikin salo na kashe murya saida ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba ga numfashinsa dab saman fuskarta, saurin janye fuskarta tai a d’an daburce tace dashi “Saida safe...!”
Khalid ya girgiza kai yace “Ba wannan ba...”
Bugun zuciyarta ya k’aru ganin yana kuma matso da fuskarsa kusan nata, ji tai tamkar ta hankad’asa amma batada wannan k’arfin, can k’asar zuciyarta kurum take addu’an abinda zai karkata hankalinsa... Aiko kaman daga sama wayarsa ta soma ruri, ya gyara tsayuwarsa yana mai zaro wayar... Wannan karon dagaji da abokinsa Baffah suke maganan dan taji yana cewa su had’u GRA yanzu zai tafi wajen Daddy..... Daga nan paper bag d’in hannunsa ya mik’a mata, tai kicin kicin da fuska alamun bata son amsa saidai yanda taga ya matuk’ar tsarewa ya sanyata amsa tana mai masa godiya dikda batasan minene ciki ba...
“Inda na isa masauk’i zan kira, and monday kar kowa ya kaiki sch zanzo na kaiki da kaina kinji koh...”
Jinjina masa kai kurum tai tana satan kallon yanda ya mak’ala ring d’inta a ‘yar yatsan hannunsa k’arama dikda haka bai isa k’asa ba tasan neman maganane kawai ya sanyashi yin hakan, can k’asan zuciyarta murmushi take ita kanta tasan itada Khalid hali yazo d’aya they’re both very stubborns ita kaw yanzu ko musu bata iya masa balle tsiwar data saba yi masa... Sukai sallama Khalid ya tafi da kewar matarsa...
Ita kaw har ta shige gidan k’irjihta bai daina bugu ba, Yusrah dake jiranta parlor nan ta sakata gaba da zolaya Nabilar na aika mata harara, batabi takan Yusrah ba dan cike take da haushinta, ta isa ta bud’e paper bag d’in kwalin wayace d’an ubansu k’irar Samsung hardasu sim da komai, ta saki murmushi had’ida lumshe idanu tana shak’an k’amshinsa da ya kama ‘yar jakar... A haka Yusrah ta shigo ta taddata..

***

A can gidan Haule fah? Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana... Mamaki ya cikata sanda ta kutsa cikin gidan ‘yandaudun nan sukai chaaa suna ele suna fad’in ga babbar Yaya ta iso a bata fili.... Suka janyo hannayen Haule dake binsu da kallon mamaki, tuni suka jefa Haule tsakiyar filin rawa suna gewayeta gurmi da garaya naci gaba da tashi... Can Haule ta hango Sawwama da d’aurin nan nata gaba na kallon yamma bayan na kallon gabasa sai karkad’a k’afa take tana jijjiga alamun rawa daga zaune....
Haule ta murmusa dan dik a zatonta Sawwama tayi haka ne ta kwaso ‘yan daudu da mai gurmi dan ta cazagawa Sahariyya bak’in ciki tinda an fasa bikinta.... Haule ta k’arasa gaban Sawwama tana huci tana nunata da ‘yar yatsa “Ke k’aramar kilaki, k’aramar shed’aniya ni nafi k’arfin kizo har cikin gidana kice zaki cazga min bak’in ciki... Naci uwarki a bariki barikiji na fad’a miki... Tin wuri ki tattari wad’annan ‘yaniskan ku fice min gida tinda ba bayan gari bane...!” Ta k’arashe tana kuma fincika....
‘Yan daudun nan suka shiga kame baki cikin salo suna fad’in “Aaaa Haba yayarmu tarban da zaki mana kenan... Kuma ma ai nan gidan Ubanmu ne zama daram babu fashe Billahillazi...!” Suka k’arashe suna tafe hannaye...
Kan Haule ya d’aure ta dubesu tace “Waye Uban naku....?!”
Salo sukai suna masu kame baki da tafe hannaye suke furta “Chaasss! Ayyye Lantana shafa mata...!” D’ayan yace
Wanda aka kirada Lantana gyara d’aurin k’irji yai had’ida rik’e hab’a kana yace “Waa ki rufa min asiri in mutu a d’aki maza su kaini... Ba’a ji mutuwar sarki a bakina ba wllhi....!”
Haule fah ta soma firgita da lamarin dan har yanzu bama ta lura da matar dake daga gefen mai garaya fuskarta lullub’e cikin mayafi ba.... Harta Sahariyya dake cikin nata damuwar gyara zama tai bayan ta ida birgimanta a k’asa tana kallon wannan show dake gudana a gidansu, kai kowa a wajen tsayuwa baima idanunsa abinci yai da ganin wannan ikon Allah...
Haule ta k’arasa a fusace ta finciko Sawwama tana fad’in “Ke dan uwarki me kike shirya ma d’ahna bak’ar mayya zuri’an jarababbu...” Batakai aya ba Magajiya ta mik’e had’ida yaye rufin kanta tai d’amara da gyalenta ta finciki d’iyarta Sawamma ta koma baya kana tai tsaye gaban Haule tana mai furta “Ke kada ki kuskura ki kuma tab’a min lafiyar d’iya dan wllhi kinji na rantse miki wad’annan mata mazan da kike gani su sauya miki kamanni....!”
Al’ajabi had’ida mamaki ya kuma kama Haule... Dariyar datafi kama data takaici Haule tai kana tace “Yo ai sai kuce min tafe kuke gaba d’aya, kuce bayan gari ne yau gaba d’aya a gidan namu, au ta kasa ne shine bari ta d’auko uwarta ta tayata... Yo ai kun bani kunya tinda kukayo zugan wad’annan asararrun... Ashe dai na cika aji shakkun tunk’arata...!”
Wannan karon murmushi Magajiya tai tana mai k’arema Haule duba daga sama har k’asa kana tace “Sauk’inki d’aya baki kai na zuba kishi dake ba, dan haka gwara ki saduda kiyi biyayya mu zauna lafiya...”
Haule fah bataji batun da kyau ba, mai wannan kilakin take fad’i ne....? Bata ankara ba tajiyo muryar Magajiya tana fad’in Mai gurmi yaci gaba da aikinsa, tana fad’i tana tik’an rawa daga tsakiya ashararrunta na tayata....
Su Amara k’irjin biki mai zasuyi itada k’awayenta banda dariya, harta Sahariyya saida taji dariya ya kufce mata ganin wannan drama dake faruwa a gidansu wanda yafi kama da wasan kwaikwayo tama mance itama cikin nata damuwar take, harta su Fa’iza k’awayen Sahariyya dariya Kawai suke suna fad’in saidai fah Sahariyya tai hak’uri amma wannan al’amari dole su dara su kuma kai gaba...
Haule da duniyar ta kuma juya mata a matuk’ar sanyaye ta isa gaban Magajiya tana fad’in “Mai kikace...?” Wannan karon cikin sanyin gwiwa sosai tai maganar...
Magajiya ta murmusa tace “Yafi miki da kika saduda da wuri... Ki jira mijinki shi zaizo yai maki sauran jawabi, kina iya shigowa fili mu taka a halin yanzu...” Ta k’arshe tana mai janyo hannun Haule tana sakata tai rawa tana bin sautin garayar tana furta “Rawa Haule rawa Haule....!”
Bibbiyu Haule ta soma gani... Itace Alhaji zai mata wannan cin kashin... Aure! Aure yai ba tareda saninta ba, aurenma ya rasa waye zai auro mata sai Magajiya... Take taji wani irin kuka na zuwa mata dan dik yanda takai da ganin ya d’aure bata isa ba bazata iya ba, tana jin yanda zuciyarta Ke fincika daga k’irjinta kaman zai fice... Itakam ta gwammci mutuwa da ganin irin wannan rana.... Zame hannayenta tai daga rik’onda Magajiya tai mata had’ida zama dirshan a k’asa ta jinginu jikin garu ta dafe kai tana furta “Na shiga uku ni Haule... Na shiga uku... Hafiz ya kawo mana annoba cikin zuri’a da ya auro d’iyar matar nan... Yanzu jarabawar bai tsaya akanshi kawai ba harda mijina... Na mutu, Haule k’arshenki yazo...!” Ta k’arashe tana mai sakin wani irin kuka da batasan ya kufce mata ba, suko su Magajiya da ayarinta basu fasa shagalinsu ba su Amara na tayasu....
A haka Hafiz ya shigo gidan ya tadda wannan kwamacala dake faruwa a gidan mahaifin nasa...

***

A can gidan Abbah kaw yanke shawarin had’uwa Washe gari sukai gaba d’aya a can gidan Babbar Yayarsu Abidah bayan kowa ya d’an sami natsuwa zuwa goben... Haka yayi masu gaba d’aya, saidai yau d’in sun kasa rabuwa da juna suka yanke shawarin kwana su duka hud’un a gidan ‘yar uwarsu Mariya, dan yau d’in ji suke tamkar kada su kuma rabuwa da juna, ga yaran Daula tuni sun sake suma sunata murna yau Mominsu ta had’uda family d’inta, tuni dama Daula tayi waya ma Daddy ta sanar dashi halinda ake ciki Farin ciki da al’ajabi ya cika Daddy, yace tai zamanta cikin ‘yan uwanta don da har zai turo driver ya d’aukosu zuwa masauk’i itada yara... Abin fah sai son barka ta ko wanne b’angare Farin ciki ne maras misaltuwa, daga bisani Engr da Sameer sukaima iyayen nasu sallama suka fice kaman kada su rabu da juna, nan Sameer yai rakiyawa Engr zuwa waje suna tafe suna kuma tattaunawa, bayan Engr ya wuce shima Sameer d’in sashen Mahaifinsa ya nufa yana mai zullumin halinda zai tadda mahifin nasa ciki bayan tulin abubuwan da suka faru a yau d’in....
Da sallama saman bakinsa ya nufo cikin parlorn sanda Abbah yai masa izinin shigowa... Ga mamakin Sameer murmushi ya gani kwance saman fuskan Abbah sam bazakace yanada damuwa ba sai ka karancesa sosai ka iya gano hakan....
“Shigo abinka, k’araso Ma’aruf... Dama ina nemanka akwai maganar da zamu tattauna....”
Sameer ya zauna daga gefen k’afan Abbah yana mai gaida Abban... Abbah ya amsa masa har lokacin murmushi ne saman fuskarsa wanda ko ba’ace ba kasan k’arfin hali kawai yake...
Bayan Sameer ya zauna Abbah yaci gaba da fad’in “Akan batun aurenka da d’iyar wajen Yaya...!”
Gaban Sameer ya yanke ya fad’i, dan shi har ya mance da batun wata Sahariyya.... Ya sinkayo Abbah naci gaba da fad’in “ Nasan mai yuwa kanada labarin an sauya aurenka da k’anwar Sahariyya...”
Wannan karon d’agowa ya d’anyi cikeda mamaki kana Abba ya jinjina kai yace “Da alama bakada labari... Ma’aruf..!” Ya kuma kiran sunansa cikeda kulawa...
Wannan karon jiki a sanyaye ya d’ago yana duban Abban...
Abba yaci gaba da fad’in “An maida aurenka kan ‘yaruwarka RAIHANAH... Bayan dik abinda suka faru nasan bakada wani tambayar da zakai gameda wannan al’amari... Kasan Raihanah itace matar da Allah ya zab’ar maka kuma inaso ka rik’eta amana, kada ka dubi abinda mahaifinta yai mana nida mahaifiyarka harma da kai... Ita d’in yarinyar kirkice, Allah Ubangiji yai maku albarka, ya azirtaku da ziri’a d’ayyiba... Ina labarin d’aya matar taka...?”
Sameer da ya tsinci zancen tamkar sauk’ar aradu dikda cewa yaji wani irin sanyi na sauk’ar masa cikin zuciyarsa sanda akace bai aure d’iyar Haule ba, saidai baima San mai yakeji gameda auren Raihanar ba, wani feeling ne da bai isa ya fasalta ba a halin yanzu... Muryar Abbah ya sinkayo yana fad’in “Kai nake tambaya Ma’aruf.... Ina labarin matarka...?”
Sameer ya d’an sosa kansa kad’an kana yace “Em Abbah dama... Dama sai naje Kaduna na dubata...”

Abba ya jinjina kai yace “Toh dama lallai lallai kaje ka duba iyalinka, ka had’e kan iyalanka ku zauna lafiya kaji koh..”
Sameer ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Zanyi yanda kace in sha Allah Abbah...”
Abbah ya murmusa kana yace “Allah shi maka albarka...”
Kai a k’asa ya amsada Ameen Abbah a daidai sanda Mamy ta shigo da sallama... Kallo guda zakai mata ka fahimci ta damu da damuwan mijin nata, Sameer yai mata sannu da shigowa kana ya mik’e ya basu waje, can k’asar zuciyar tinanin al’amran da suka saka shi a tsaka yake, ala dole ya amsama Abbah gameda maganan aurensa da Siyama dan bazai iya musama Abbah ba sannan a halinda Abbah yake ciki yanzu bai buk’atan k’arin tashin hankali, ya saki murmushi a hankali sanda ya tuna aurensa da d’iyar Haule Wai ya juye kan Raihanah... Al’amarin Allah kenan, haka yake gudanar da al’amaransa ba tareda shawartan kowa ba.... Ya lumshe idanunsa a hankali yana tuno tin sanda ya soma had’uwa da ita farkon dawowarsa Kano sanda ya kusan bigeta da mota tun kan yasan sud’in ‘yanuwan juna ne.... Ya kuma sakin murmushi a hankali kana yasa kai ya fice...

Mamy ta dubi Abba da yai shiru tin bayan shigowarta saima k’ok’arin kamo tashan labarai da yake... Saurin kai hannunta tai ta amshi remote d’in ta kai masa tashar NTA d’in dan lokacin labarun tara ne... Har lokacin nan Abbah bai dubeta ba saima maida hankalinsaga tv da yai dikda cewa da gani bama fahimtar labarun yake ba.... Mamy ta d’an sauk’e ajiyan zuciya sanda takai idanu kan tray d’in abincinsa dake gefe da alama ko tab’awa baiba tinda ita tana hidiman biki Lami ce ke kula dashi ta bata girkin ranakun... K’arasawa Mamy tai ta janyo tray d’in tana k’ok’arin serving d’insa Abbah ya katseta da fad’in “Karki zuba abincin nan Mariya a k’oshe nake...”
Mamy ta d’anyi raurau kana tace “Toh mai kaci ya isheka, gani fah baka ko tab’a abincin ba tintini...”
Jinjina mata kai yai kana yace “Ina sane, kawai na k’oshi ne...”
Mamy tai shiru dan tama rasa abin cewa gaba d’ai, sai sauk’e ajiyan zuciya da tai, a hankali ta d’an kuma muskutawa zuciyarta cikeda tausayin mijin nata lokaci guda take furta “Nasan kana cikin lokaci mai matuk’ar wahala a rayuwarka... Nasan hakan ba abu ne mai sauk’i amma ina rok’onka dan Allah kai hak’uri ka d’auki duk abubuwan da suka faru a matsayin k’addara kaji mijina...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya wanda ya sanya Abbah juyowa yana dubanta cikeda tsananin tausaya mata, shin wane irin kyakkyawar zuciya Mariya kedashi.... Bayan dik abubuwan dataji ta zab’i ta yafewa wad’annan azzalumai, lallai ita d’in tana zuciya mai kyau...
Sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an yana mai k’ura mata idanu... A hankali yakai hannayensa saman nata... Mamy ta d’ago tana dubansa cikeda tausayinsu su duka biyun.... K’wallan da Abbah keta k’ok’arin mak’alewa suka gangaro...
“Ki yafeni Mariya...!” Kalman data soma fita daga bakin Abba kenan...
Mamy ta girgiza kai tace “Dan Allah ka daina bani hak’urin nan haka dukanmu nan abin nan ya shafemu ba ni kad’ai ba, kuma mu godewaAllah da har ya warware mana komai...”
Girgiza kai kad’an Abbah yai “Ke d’in kece kikafi kowa a cikinmu, Mariya wala’alla hakkinki shine ya kamani har mutanen dana aminta dasu sukaimin cin amana mafi muni... A lokacin da Ma’aruf ya b’ace na biyewa son zuciyata naita zarginki da laifi nima, banyi la’akari da halinda kika tsinci kanki a natsayinki na mahaifiya ba, ban kasance taredake nai supporting d’inki ba saima biyema masu laifin da nai muka had’u muka cuzgunama rayuwarki... Zan jima inajin zafin wannan abun a raina...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Mamy da kanta Ke kife tana matsan hawaye itama, lokaci guda take furta “Wannan duk muk’addari ne daga Allah, mu d’auki hakan a matsayin k’addarar rayuwarmu... Sannan mu godewa Allah da ni’iman da yai mana a yanzu mu daina kuma duba baya...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Abbah yai mata k’uri yana godiya wa Allah can k’asan zuciyarsa da wannan baiwa da yai masa na samun mace irin Mariya...! A hankali ya matsa kusanta ya rungumota cikin jikinsa su duka biyun hawaye suke...!

***


A b’angaren Engr kaw tinda ya isa gida yake nazarin takardan da Akram ya bar masa, ya kasa aminta Muhibba can go this far, ta yaya zata masa haka... Kenan watak’ila tanada masaniya kan yanda Akram d’in ya tafi tinda she’s his accomplice.... Baisan kishin Muhibba yakai wannan peak d’in ba, a had’a baki da ita a yaudare mijinta, mijin da ya d’auki gaskiyarsa da yardarsa ya bata... Ya fuzar da iska a hankali yana mai had’e tafukan hannayensa waje guda... Kaman wacce aka wuntsilota haka ta shigo babu ko sallama bayan ta gama baccin asaranta, dan har ya dawo gidan bata sani ba saida ta tashi ta hangi motar da ya fita da ita a parking lot alamun ya dawo, dik yini zubur d’in nan da Engr yai a waje Muhibbah bata kira taji lafiyarsa ba dikda kasancewarsa mutum mai hada hada da yawa... Kallo d’aya yai mata

Please Login or Register in order to submit comment