Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jarumine yasan darajar kansa.�
Dariya tai ta ce“Ok bye.�
Katse kiran yay ya zura rigarsa ya nufi hanyar falon.
Kira ya shigo masa ya 'daga.
“What? Da gaske an kamasu? Wlh azim idan sunana ya fito mutuwace makomarku, ku kiyaye.�
Ya katse kiran yana wuci ya nufi 'kofar.
Bu'dewa yay yana sakin fuska ya ce“Ja'afar.
“Barka oga.�
Ya fa'da yana basa key d'in ya juya ya ce“ bon nuit.�
Ma'aruf ya ce“Gobe karka zo da wuri sai wajan goma ok?�
“Ok�
Ja'afar ya ce ya saka kansa ya fice.
Ma'aruf ya ce“Saura 'kiris Ka 'kwamuso min Rahma Abdul Majeed,nasan zaka iya jira nake na qarasa da mutanan can, ban ha'da abubuwa waje 'daya sbd tsaro.�
Ya qarasa mgnar ya na sheqewa da dariya.
Kiran Rabi'ah ne ya shigo wayarsa.
'Dagawa yay baice komai ba.
Daga can cikin kwarkwasa d kissa ta ce.
“Amincin Allah ya tabbata gareka ya ma'abucin fara'a my husband insha Allah.�
Sheqewa yay da dariya ya ce“Idan kinason na kulaki na baki ha'din kai aduk abinda kikeso sai kin bayyana min kanki da sunanki da garin da kike sbd naga kin 'boye numberki idan ba hakaba karki sake nema na, ban soyayya cikin duhu.�
'Kitt ya katse kiran.
Kanta ta dafe cikin takai ci ta ce“Zanyi hakan amman ba yanzu ba.�

Sosai likitocin suka du'kufa neman ceton ran Ibtisam, sunyi sa'ar tsayar da jinin, ta samu karaya 'kafa da hannunta, wanda zuwa anjima za'a 'dorasu.
sun mata 'dinki agoshinta da tsakiyar kanta. Har yanzu bata farfa'do ba, dan ba qaramin jimuwa tai ba.
Me taxi ahannu kawai ya karye sai 'dinkin goshinsa da le'bansa na qasa.

Rahma tin daga nesa ta hango Abie tsaye yana kai komo bakin 'kofar room 'din da aka shigar dasu.
Da sassarfa ta qaraso wajansa ta fa'da jikinsa tana kuka, ta ce“Abie! Allah yasa basu ji mugun ciwo ba.�
Hannayensa ya maida bayanta ya zagaye yana bugawa, ya sauke wahaltaccan numfashi.
Ahankali cikin lallashi ya ce“Bar kukan ummina kinji?�
La'bewa tai jikinsa ta lumshe idanunta ta 'daga kanta.
Zama sukayi, Abie 2 ya ce“Abien Rahmerh kayi tuqi da garaje ne ko? SBD ka fito bakada nutsuwa, don Allah ka ajiye hankalinka akan yaran nan, insha Allah komai zai zo da sauqi ka ban sati zan fara wata istahara.
Sannu Insha Allah komai zaizo da sauqi akan wa'dan da ka buge 'din, ka daina tuqi duk lokacin da kaji bakada nutsuwa.�
Abie ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Rahma wacce tai luf jikinsa idanunta arufe,kallo 'daya yay mata yasan hakan ba qaramin nutsuwa ta samuba, sbd tafi sati hakan bata ha'dasu ba.
Sake 'boyeta yay cikin jikinsa, ya fesar da zazzafar iska daga cikin bakinsa, ahankali ya furta.
“Abdulmajid bazaka ganeba ne Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi kawai.�
Ya 'karashe mgnar yana sauke wani irin numfashi mai wuyar fassarawa, sabida yadda hucin Rahma yake sauka 'kasan wuyansa.
Abie 2 ya ce“Yanzu ta ina za'a fara neman 'yan uwansu? Dan nasan zuwa anjima dole hankalinsu zai tashi a duk inda suke.�
Abie bai ce uffan ba, sbd kansa ya 'dauki chaji, addu'arsa yarinyar da yagani kamar gawa yasa bai mata babbar illah ba cikin rayuwarta.

Ja'afar yana isa gida, ya zauna dab da Harisu, ya ciro wayarsa ya kira Malam Adamu, suka sha fira sosai da Inna mai waina.
Bayan sunyi sallama, ya kira Ibtisam dan ya lallasheta wayar switch of.
Kansa ya dafe ya mi'kewa ya nufi 'kofa yana fa'din.
“Bari naje naga halin da take ciki.�
Kansan yaji ya sara yay saurin dafewa yana karanta duk addu'ar da ta zo bakinsa.
Harisu da Yahuza suka ce“Ya jikin Ibtisam 'din? Baba ya yi ta fa'da ya ce kun tafi asibiti ba sanin kowa.�
Ja'afar ya juyo zai mgna,
Baba Tsalha ne ya shigo bakinsa 'dauke da sallama ya ce“Wai ina kuka tsaya haka? Ina Ibtisam 'din?�
Ja'afar ya ce“Baba rabona da ita tin bayan sallar isha lokacin zan fita, ina take? Me ya sameta¿�
Baba Tsalha ya ce“Kaci gidanku ta ce tana tsamki nace taje ta fa'dama mutafi asibiti naji shiru nazo su Harisu sukace sunji kana mgna a 'kofa 'kila kun tafi ne.�
Ja'afar gabansa yay mummunar fa'duwa ya ce“Wlh Baba bamu fita tare ba banma san batada lafiya ba tin yaushe? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yanzu ina zamu nemonta.�
Baba Tsalha ya ce“Hasbunallahu Wa ni'imal wakil, zama bai samemu ba, ko dai ka mata wani abun ne don Allah me ya ha'daku?�
Ja'afar ya ce“Wlh ban mata komai ba, kawai taji dai ina wayane da Rahma kuma lfy lau muka rabu, na fita.�
Baba Tsalha ya ce“Wacece Rahma?�
Ja'afar ya sosa kansa ya ce“Allah ya ha'damu balarabiya ce, kuma wlh ina masifar sonta su biyu zan aura idan Rahma ta amince.�
Baba Tsalha ya zazzaro idanunsa waje ya ce“Ok muje bamuga zamaba ina zargin ta gudune mu fara zuwa tasha.�
Ja'afar hankalinsa ya yi masifar tashi jin Ibtisam ta gudu ne.
Baki 'dayansu suka shiga motar Baba Tsalha suka bar gidan Ja'afar sai wata irin zufa take keto masa.
Duk wata tashar mota da take cikin garin (Ndjamena) su Ja'afar sunje neman Ibtisam basu sameta ba.
Lokacin kuma 'yan sanda sun zo sunyi duk abinda ya dace, an 'dauke motar daga wajan shiyasa basu ga komai ba.
Ja'afar ya rasa inda zai sanya kansa sunata yawon neman Ibtisam har shabiyun dare ba labarinta.
Baba Tsalha ya tisasa gaba da fa'da akan me zaiyi waya da mace agabanta ga shina ta gudu 'kilama ta tafi cameron wajan 'yar uwan babanta.
Kasa ko motsi yay abin duniya ya damesa, shi fatansa duk inda take ta kasance tana cikin 'koshin lafiya.

Can kuwa asibiti sai wajan 1 na dare aka gama ma Ibtisam komai.
sai da suka saita kome aka d'ora hannun Ibtisam da 'kafarta, hankalin likitocin ya kwanta.
Har lokacin suna asibitin.
Abie yana ganin an bu'de 'kofar room 'din ya janye Rahma daga jikinsa wacce take bacci, ya kama hannunta suka nufi wajan Dr.
“Doctor wane halin bayin Allah suke ciki?�
Dr Salis ya gyara kwalar rigarsa yana sharce zufa ya ce“Alhmdllh! Mun saita komai shi wancan nasa da sauqi mun jima da 'dorasa mun 'dinke masa goshinsa, an 'Dora masa karayar hannunsa, yana bacci, muje sai na maka bayanin ita yarinyar.�
Abie ya jinjina kansa ya kalli Abie 2 ya damqa masa hannun Rahma ya ce“Kuje gida Yahaya maidaku insha zan taho kafin asubah,ummina kiyi bacci cikin amincin Allah da kariyarsa bye.�
Ya qarasa mgnar ya manna mata kiss a goshi.
Kai ta 'daga Abie 2 ya ce“Bari na kaita sai mu dawo ai bazamu barka ba kai 'daya.�
Abie “A'a don Allah je ka huta.�
Dole suka tafi shi kuma su ka nufi office 'din Dr Salis.
Bayan sun zauna ya ce“Yalla'bai yarinyar nan ta bugu dayawa, yanzu dai mun mata 'dorin hannu da 'kafa, 'dinki goshi da kai, amman mgnar gaskiya alamu sun nuna kamar ta yi doguwar suma, yanzu haka mun shigar da ita coma, amman karka damu komai na Allah shi keyin komai alokacin da yaso ba lallai bane yadda na'urori suka nuna mana ya tabbata ba, ko adaren yau Allah ya ga dama zai farfa'do da ita.
Dan haka za'a kula da ita, har lokacin da zata farfa'do, shi namijin yanada kyau 'yan uwansa zuzo jinyarsa.�
Abie ya tura hannunsa cikin yalwatacciyar sumar kansa, yana fa'din.
“Wa la haula wa la Quwwata illah billah! Hasbunallahu Wa niimal wakil. Ok ok, Dr Salis zan saka abazama cigiyar 'yan uwan bayin Allah nan zuwa gobe gidan Tv radio har asamesu.�
Dr kwantar masa da hankali ya shiga yida bayanai dalla² har yaji 'yar nutsuwa, sai 2 shi da securities 'dinsa suka nufo gida.
Acikin tsakitar Daren ya saka aka shigar da sanarwa duk wani godan radio da Tv da yake cikin garin Ndjamena.
Ja'afar kasa bacci yay adaren, ya shiga salloli da karatun Qur'ani akan Allah ya bayyana Ibtisam.
Rahma kuwa baccinta tai anutse, wanda da bayane ba zata ta'ba runtsawa ba Abienta na wani hali.
Yayin da Abie bai iya runtsawaba hakan ta saka shi 'dauro alwala ya shiga sallah.
Abie 2 kamar yadda yay alqawali zai duqufa da sallolin dare ya fa'dawa Allah akan Allah ya ganar da shi abinda yake son ganewa akan Rahma da Ja'afar, zai duqufa tsawon sati yana kaiwa Allah kukansa, kafin yay qoqarin cire musu aljanun sbd yasan Allah bai abu abanza, bai kamata yay garajen warware matsalar ba, sai ya kai kukansa gurin Allah.
Washegari kuwa gidan radio da Tv na Ndjamena, ko ina sanarwar Ibtisam ne dan tin tsakiyar daren me taxi ya dawo haiyacinsa ya fa'di sunansa da unguwarsu tin da safe Abie ya tura aka taho da matarsa da yaransa uku.
Baba Tsalha yana tsakar gida ya kasa fita radio ahannunsa kamar a mafarki yaji sanarwar, da 'karfi ya ce“Ba shakka Ubtisam ce Falmata taho muje mugani.�
Falmata ta ce“Allah yasa itace.�
Ja'afar ne yay parking a'kofar gidan zauwar kenan daga gidan Ma'aruf wanda yace yaje amso motar, ya fito ya shiga cikin gidan 'bangara Baba Tsalha ya nufa, ya shiga yana fa'din.
“ Baba naji sanarwa Hôpital général muje don Allah ko itace mugani ance acikin taxi hatsarin ya faru.�
Baba Tsalha ya ce“Muje.�
Su biyar suka nufi asibitin hankulansu atashe.
Jaddatu zaune tana balbala fa'da.
“Sbd Allah yaron ashe jiya ha'dari ya samu shine bazai fa'damin sai yanzu da safe.�
Hanan ta ce“Ummi dan kar hankalinki ya tashi ne ai, kiyi hkr ya ce anjima za'a kaimu lokacin Rahma ta tashi.�
Raiyana ta ce“Allah dai ya kare gaba nama rasa ina zaije adaren har yay tuqin ganganci haka, ya saka hankulamu tashi, dan wlh ni ban rantsa ba jin bai shigo ba, Ummi qarama sai 1 na dare ta iso. �
Jaddatu ta ce“Ya wuce damuwar rashin walwalar Rahma ne.�
Anutse take saukowa tana sanye da wata English Morocco maroon gown,tai masifar mata kyau, ta baza gashinta har tsakiyar bayanta,wani irin matsiyacin 'kamshi yake tashi jikinta. Wani hills ne aqafarta mai shegen kyau.
Wayarta (iPhone 13 pro max)
Ta Danna kiran Ja'afar wanda ya kirata tana wanka.
Bugu 'daya ya 'daga kiran lokacin sun shiga hospital.
“Hello Qalbina kiyi hkr zan kiraki anjima munzo hospital ne muna sa ran Ibtisam ce tin jiya ta 'bata.�
Rahma ta dafe saitin zuciyarta jin wani abu ya suki zuciyarta sbd jiya yace Ibtisam matar da zai aurace.
ta dafe qarfen benin cikin zafin kishi ta ce“Ni dai wlh yanzu nake son ganinka idan ka wuce 15 minutes sai dai ka isko gawata na mutu tinda baka sona wayyo 'kirjina zafi wayyo Allah na! Zan mutu!�
Ta 'karashe mgnar tana sakar masa kukan shagwa'ba.
Daga can Ja'afar ya dafe goshinsa kasancewarsa mutum marar son hayaniya, cikin raunin da jinnu suka saka masa ya ce“No! Ga ni nan Qalbi pls kar wani abu ya sameki wlh nima mutuwa zanyi.�
Su Baba Tsalha suka Saki baki da hanci suna kallon shi.😂
_(Allah dai ya 'debema Raiyana albarka ta maida mutane biyu wanda suka kasance miskilanci da izza ga kamun kaida rashin son hayaniya tamkar 'ya'yan sarauta. Amman yanzu ta saka an mayar dasu tamkar sakarkaru.)_
Ja'afad kai tsaye ya juya da sauri ba tare da ya tsaya ma su Baba Tsalha bayani ya fa'da mota ya fizge aguje yabar asibitin... *💃�'Yar aljin tubarkallah*

_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/14/22, 14:09 - Buhainat: ```D A```

```29&30```



_*Niger*_
(Tahoua)
Laraba tana zaune ta rabka tagumi, yau baki 'daya bata nutsuwa, sbd mummunan mafarkin da tai akan Ibtisam. Hankalinta sosai ya tashi, dan batasan halin da 'yarta take ciki ba.
Kuka ta fara tana fa'din.
“Ya Allah ka kawomin 'dauki kasa duk inda take tana hannu na gari, naji tsoron mafarkin, Ibtisam na yafe miki duniya da lahira, sbd ni ce silar faruwar komai, da ban kai sunan Dadda da Tanko wajan malam Wali ba da yanzu kina wajan iyayanki cikin aminci, dan nasan bazasu ta'ba ba Jamilu aurenki ba idan suna haicinsu. Astagfirullah wa'atubu ilaik.�
Ta 'karashe mgnar cikin kuka.
Taslim da take 'dakinsu yau ta tashi da ciwon mara mai 'karfi bata je école ba, ta fito aki'dime tana sakin kuka ta ce“Anna daman asirine kikawa Dadda da Baba sbd kawai a aura ma Aunty Ibtisam wannan tsohon birin?�
Anna da ta manta Taslim na gidan ta shiga rarraba idanunta ta ce“Don Allah Taslim ki rufamin asiri akan wannan mgnar wlh naji nayi nadama sosai, kuma ai asirin baiyi wani tasiri ba, ku'dina kawai akaci wlh bazan kumaba ki rufamin asiri, amatsayina na mahaifiyarki.�
Tanko ne ya shigo yana waya ya ce“Eh gatanan kusa.�
Wayar ya bata ta amsa tana goge fuskarta tana saita nutsuwarta tai sallama.
Daga can Cameron Karime zaune farar mace kyakkyawa sosai take kama da Tanko da Ibtisam, ta ce“
Laraba ya haqurinmu? Har yanzu ba labarin Ibtisam? Ai duk laifinku ne yaushe rabon duniya da auren dole yarinya 'karama kamar Ibtisam shekaru 17 kacal aduniya me ta tsare muku? Yaushe aka haifeta ma?�
Laraba ta Saki kuka ta ce“Wlh nayi nadama na yafe mata Allah yasa tana hannu na 'kwarai.�
Karime ta ce“Ameen ina jin ajikina duk inda take bazata ta'ba cutuwaba, Allah zai kareta, kunyi babban kuskure yaushe rabon duniya da auren dole, ga yaron namijine irin wacce kowace 'diyar mutunci zata so ace ta mallake shi kuka ma soyayyarsu karan tsaye, shi yanzu Allah ka'dai yasan halin da yake ciki.�
Laraba dai banda kuka ba abinda tana sake nadamar sanadinta 'yarta tabar gida.
Haka suka gama wayar Tanko ganin halinda Laraba take ciki ga Taslim na kuka ya ha'dasu yana lallashinsu duk.da shima juriya yake.

*Moray*
Inna zaune tana famar toya waina, sai washe baki take sabida cinikin da take.
Tana toyawa, Maimu na zubawa mutane, ta kalli Mahmoud da shigowarsa kenan cikin shirin tafiya school, zasu shiga lecture 9:30 am. ta ce“
Ya Mahmoud 'karfe nawa ne yanzu? Wlh sai nace Ya Ja'afar ya siyo min waya, Allah har kunya nakeji kamata banda ko rakani Masai.�
Inna ta ran'kwasheta akai, ta ce“Ubanki zai ci kinsan halinsa, har kikeda 'kwarin guiwar tinkarar ba'kin buzuna kice ya siya miki waya? Duk nawa kike shekaru 16.�
Mahmoud ya ce“Innata barta mana me kike tuna mata. Ba sai 10 zaku shiga lecture ba? Yanzu tara da sha bakwai, kije ki shirya, inna na tafi.�
Inna ta basa 300f cfa ta ce“Adawo lafiya Maimuna zuba masa wainar ya makara.�
Maimu ta zuba masa waina ya amsa ya fice yana fa'din “Allah ya qara lafiya innarmu ta mutunci.�
Inna ta washe baki tana kallon Hakim wanda ake zuba masu waina ta ce“Hakim sai kuka la'be kuna gulmar mu da 'yan unguwar geban zogi, akan yarinyar nan da ta nacewa Ja'afaru nah?�
Malam shigowarsa kenan yana mgna da Mahmoud da ya maidosa zai basa sako wajan mai gadin school 'dinsu.
Hakim zaiyi mgna Malam Adamu ya ce“Hakim daga yau na soke shigowa siyan waina ga dukkan baligin namiji, Ku tsaya a'kofar gida ku dinga turo yara.�
Cikin ladabi Hakim ya ce“Toh Baaba mun gode.�
Ya 'karashe mgnar yana amsar wainar hannun Maimu ya fice.
Inna zatayi mgna kallon da Malam Mal Adamu ya watso mata ya sakata shakkarsa ta ha'diye wani yawo sbd kwarjinin da ya mata.
Ta ha'de rai tana cigaba da tuyarta tana musmus da bakinta.
Mahmoud ya amshi saqon yana danne dariyarsa ya fice.
Malam Adamu yana tsaye aka sallami sauran mutanan ya musu kashedin kar wanda ya sake shigo musu gida su tsaya a'kofa.
“Ke! Maimuna maza ta shi ki shirya ki tafi makaranta idan ba asabar ko lahadi ba na sake ganinki kina aikin wainar nan kina makara zuwa makaranta zan sa'ba miki.�
Cike da ladabi Maimu ta miqe ta wanko hannunta ta nufi 'daki dan shiryawa.
Inna ta cika ta fammm amman baki ba damar mgna.
Deluwa dai tana sha'anin gabanta bata shiga harkar su.
Zai fita yaji tana ba wata yarinya ku'di tana fa'din.
“Jeki wajan Iliya kice ya min chap-chap na dala arba'in, bari na Kira Ja'afar.�
Kai Malam Adamu ya girgiza ya fice yana fa'din.
“Maimu ki iskeni panpo.�
Bayansa ta bi da harara.
Deluwa ta danne dariyarta kar rigimar ta dawo kanta.
Malam Adamu na zaune wajan ruwansa sai ga Tanko.
Bayan sun gaisa Tanko ya ce.
“Don Allah Mal Adamu asake binkitar Ja'afar idan Ibtisam na wajansa wlh zan aura masa, bansan kwanaki me ya sameni yarda da nayi na ba Jamilu aurenta, zan mayar masa da komai nasa, munyi mgna da yaya Karime.�
Malam Adamu ya sauke ajiyar zuciya ya ce. “Insha Allahu zan qoqarta bincikarsa wlh kuwa idan tana hannunsa Ja'afaru sai ya ha'du da fushina mai tarin yawa.�

*Tchad*
'Bangaran Rahma, Idanuwansu duk su Jaddatu suka zuba mata, su na kallon yadda take wayar har ta idar.
Rahma ganin Ja'afar ya rikice ya saka ta 'datse kiran tana, tana murmushin farin ciki, tasan yanzu zai taho wajantan.
tai fari da 'kananun kyawawan idanunta, ta nufo falon cike nutsuwarta take tafiya.
Tana isowa tsakiyar 'katon falon nasu ta tamqe fuska ba tare da ta kalli kowaba, ta zauna can gefe, ta 'dora 'kafa 'daya kan 'daya, tana latsa wayar.
Iman tazo ta haye cinyarta tana fa'din.
“Auntie kinyi kyau sosai za ki je gari dani?�
Rahma ta zuba mata idanunta, tana 'dan murmusawa, ta 'dagawa iman gira ha'di da 'dora 'dan 'karamin bakinta saman goshinta tai kissing 'dinta.
Ta kira “Latifa!�
Raiyana da mugun kallo ta bita a'boye
Hanan ta kalli bakin Jaddatu yadda yake musmus, tasan mgna take son yi ta kasa.
Latifa ta iso ta zube agaban Rahma.
“Uwar 'dakina ga ni.�
Rahma ba tare da ta kalleta ba, tana ha'de face ganin Jaddatu na shirin mgna, ta ce.
“Je ha'do abubuwan jiqa maqoshi, sai ki ha'da da tufa and dabino ki kai min falon saukar ba'ki, ki kunna turaren wuta ki fesa na fasawa ok¿�
“Toh an gama uwa 'dakina.�
Ta miqe da rawar jiki ta nufi hanyar kitchen.

'Bangaran Ja'afar kuwa yadda yaja motar da speed, ya bar hospital 'din. Baki da hanci Baba Tsalha, da su Yahuza su ka saki, wajan kallon Ja'afar har ya 'bacewa ganinsu, su kuma su nufi cikin asibitin.
Basu Sha wuya ba da tambaya aka kawosu wajan da za'a nuna musu Ibtisam su ga idan ita ce.
Abie suka hango zaune yana sanye da wata jallabiya milk colour hirami akansa yau sak shigar larabawan Saudiya yay, ya yi wani irin fitinannan kyau, kwarjininsa da haibarsa kwance kan fuskarsa.
Duk da yana cikin halin damuwa sam bazaka ta'ba ganewa ba, kasancewar sa mutum mai 'boye damuwa akan fuskarsa.
Gefansa securities 'dinsa ne, Abie 2 na gefensa, yayin da Abie1 waya yake da harshen turanci wanda zaka 'dauka shi idan cikakken bature ne yadda yake zuba turancin, zai baka sha'awa ya kuma burgeka.
Da sallama su ka qaraso wajan.
Yayin da Abbas da Khaleefa suka taresu daga isa wajan Abien wanda ya kawosu daga nesa ya nuna musu wajansu Abie ya juya.
Abie 2 ya ce“Ku barsu Abbas.�
Baba Tsalha cikin farin ciki ya qaraso, yabama Abie 2 hannu suka gaisa.
Ya ce“Daman yarinyar mu tin bayan isha jiya bamu ganta ba, sai mukaji sanarwa a radio shine mukace bari muzo mu duba ko ita ce.�
Abie 2 ya ce“Allah sarki bari ya gama waya sai muji.�
Yahuza takaicin Ja'afar ya cika masa zuciya, ya za'ayi ace yarinya tazo wajanka ana mgnar 'bata ko ha'dari amman ka tashi ka tafi.
Abie 1 bayan ya idar da wayan, ya fuskanci baba Tsalha bayan sun gaisa ya koro masa bayanin kamanninta, Abie yace.
“Bari zan roqi alfarma Dr ya kaimu 'dakin da aka killaceta sai ka duba.�
Wayar Dr Salis ya Kira cikin sa'a ya 'dauka, ya koro masa bayani.
Ba jimawa ya kaisu wanda dakyar Baba Tsalha ya gano Ibtisam ce, ga ta kwance kamar gawa duk na'urorine ajikinta.
Kukan tausayinta ya fara, bayan sun fito. Abie ya fara lallashinsa, da basa haquri.
Baba Tsalha ya fatar da majina ya ce“Tausayi ta bani...�
Kakaf ya fa'dawa Abie gaskiya akan Ibtisam da abinda ya sakata gudowa har hatsarin ya faru.
Abie ya ce“Karka damu nayi alqawalin tsayawa na nema mata lafiya ko million nawa za'a kashe, kamar yadda nai sanadin shigar wannan mawuyacin halin, zan fita da ita duk qasar da zata samu lfy, idan ta warke zan mayar da ita har gaban iyayanta.�
Ba Tsalha ba har Abie 2 sai da yay hawaye, da jinjinawa dattakun Abdul Majeed.
Wajan me taxi sukaje baba Tsalha dasu Harisu suka gaida shi.
Su ka dawo suka zauna suna jiran Ja'afar ta idan zai 'bullo.

Wayar Rahma ta 'dauki ringing, kallo 'daya tai mata ta miqe ba tare da ta 'daga ba.
Jaddatu ta ce“Inaga abinda ya girma sanina da tunani na, wannan abin sai anyi da gaske, dan wlh Rahma tai gamo da baqaqen aljanu tabbas.�
Rahma bata juyowa ta ce da iman da take binta.
“Koma ki zauna yanzu zanzo banson hayaniya.�
Jaddatu ta ce“Bita iman bita dan ubanta, me take 'kullawa a falon ba'kin da bataso aganta? Je Ku tafi, wai wannan masifar da Rahma ta kwaso daga ina?�
Hanan ta ce“A'a iman dawo tinda batason abita.�
Raiyana ta saki murmushin 'boye ta miqe tana fa'din “A'a iman zo yi zamanki kar Auntie beauty ta dakeki.�
Iman ta dawo tana sakin kuka ta fa'da jikin Hanan.
“Za ki tufemin baki ko sai na mareki uwar 'kwawa, wannna auntie taki yadda baqaqen jinnu suka mata caaaa ai sai fatan samun sauqi.�
Jaddatu ta 'kwalawa Latifa da Ummu Adnan kira.
Isowa sukayi cikin girmamawa suka zu'be gabanta.
“Yauwa maza kubi Rahma falon saukar ba'ki ku la'be ta window, ban yarda ko waye ba yazo wajanta, duk abinda idanunku suka gani kuzo ku fa'damin.
Ke! Latifa munafuka, sauran idan kun ke'be ki fa'da mata, sbd nasanki masifar gulma.�
Hanan tai dariya ta ce“Kai Ummi ke bakya son zaman lafiya, yanzu kiyi ta jikarki ma kafin kuci gaba da diramar Latifa.� Ummu Adnan ta amsa da“Toh Jaddatu Rahamu an gama.�
Latifa uffan bata ceba suka fice.
Jaddatu ta ce“Wlh kin kusa barmin gidana, tinda bakisan darajata ba.�
Raiyana ta qunshe dariyata, tana miqewa ganin mai kiranta.
Jaddatu ta bita da idanu.

Harabar gidan ta isa wajansa, ya fito yana tsaye gaban motar.
Tin daga nesa su ka qurawa juna idanu.
Sallama tai masa tana turo baki gaba.
Wani tsadaddan murmushi ya sakar mata, ya kashe mata ido 'daya.
Kanta ta 'dan sadda cikin sanyinta da ya saka ya koma ta ce.
“Muje ciki Habiby nah.�
Ba musu ya bita, yana zuba hannayensa duk cikin aljihun jeans 'dinsa.
Wajan zama ta nuna masa ya zauna ta zauna gefansa ta tsiyaya masa juice mai sanyi ta be'ka masa.
“Merci Qalbina.�
Ya fa'da yana kur'bar lemon, ya ajiye.
Apple ta yanko masa ta ce“Haaaaa Habibyna.�
Bakinsa ya bu'de ta saka masa. Latifa tafirfito da idanuwa waje, ta ce“Ikon Allah.�
Ummu Adnan ta ha'diye yawu tana yaba kyawun Ja'afar da cikar hallutarsa.

Ja'afar da Rahma dariya sukayi atare ya kashe mata ido 'daya yana tauna apple 'din.
Dabino ya 'dinci ya kur'bi ruwa ya ce“Alhmdllh! My Qalbi ga ni duk kinbi kin tayar da hankalinki, pls ki saurareni zan miki bayani wanda za ki fahimceni OK? �
Kai Rahma ta langwa'be tana kallon 'kwayar idanunsa mai sakawa 'yan mata mugun shakkarsa da kasala lokaci 'daya su rasa nutauwarsu.
“Ni dai Habiby idan mgnar wata ce banson ji kuka zanyi.�
Fuskantar ta yay,ya kamo hannayenta duk biyu ya riqe cikin nasa taushi biyu ya ha'du.
Kallon juna suke ba 'kiftawa.
Rahma sosai take ganin girmansa agabanta, yadda ya cika mata gaba , tabbas tasan shi 'din ba qaramin qato bane.
cikin kwantar da murya ya ce“Baby Rahmerh nah, ina sonki ki rage kishin Ibtisam OK¿ sbd ita....�
Ja'afar ya zayyanewa Rahma komai tin daga ha'duwarsu har soyayyarsu wacce dalilin irin son da take masa ta gudo tazo wajansa.
Rahma sosai kishi ya tokare mata 'kahon zuciya, hawaye ya 'balle daga idanunta kamar an kunna panpo.
“Oh! Ya Rabbi! Baby Rahmerh please ok.� ya qarashe mgnar yana kwantar da kanta gefe kafa'darsa yana shafa kanta ha'di buga bayanta, yanajin kukan nata har 'kasan zuciyarsa.
Cikin shasheqar kuka ta kirasa.
“My Habiby!�
Fuskarta ya tallafo ya amsa.
“Na'am my Qalbi pardon ok¿�
Idanuwanta ta lumshe ta tura fuskarta kafa'darsa tana sauke numfashi.
Latifa da tai tsuru² da idanu ta ce“Uhm soyayya da'di ko me yake cemata harda kukan shagwa'ba, shima ya rungumeta mana ya lallasheta ya wani kara kanta kafa'darsa...�
Ummu Adnan ta kai mata duka ta janyeta daga jikin window, ta ce“Bakida hankali, matarsa ce da kikeso ya rungumeta? Ko kafa'dar da 'dora kanta yana buga bayanta haramun ne, kekuma she'daniya kikeson ya rungumeta.�
Latifa ta ce“Toh dai ki iya bakin ki wajan Jaddatu.�
“Me wai? Ai wlh abinda ido ya gani shi zan zayyane.�
Aikuwa su na shiga parlor Ummu Adnan ta zayyanewa Jaddatu komai.
Jaddatu ta ce“Ikon Allah! Muje ki kaini wajansu wlh sai na 'daure yaron nan, wato shine zai lalata mana yarinya.�
Hanan bata hanata ba, dan sam itama hankalinta bai kwanta ba.
Idanunsa masu mutuqar kafi ya zuba mata, bayan ya janye kanta daga kafa'darsa, cikin sigar lallashi ya kirata“Baby Rahmerh please zanje hospital, kinyi breakfast kuwa?�
Ashgwa'be ta ce“Banyi ba kuma komai bazan ci ba yau.�
Tafin hannunsa ya sanya ya rufe mata baki yana ha'de fuska ya ce“Nakasata kikeson gani Qalbina¿�
Kai ta girgiza tana lumshe idanunta.
“Ok tashi maza

Please Login or Register in order to submit comment