Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rigimammiyata.�
Wani irin annurine akan fuskar shi ya lullu'beta ya shafi kanta harda tofa mata addu'a ya sakko ya kunna mata Ac ya shiga bathroom ya wanke fuskarshi sabida yadda ta goge masa lipstick.
'Kofar bedroom 'din ya rufo sai ya murza key a 'kofar falon, yabi hanyar da ya shigo ya sauka 'kasa ya nufi part 'din Abie 2, sai wani irin lallausan murmushi yake, yana shafa la'bbansa Babyn umminsa ta tsotsesu tass.

Da sallama ya shigo falon, suna zazzaune harda Ja'afar wanda zuwansa kenan.
Hannu ya basu sukayi musabaha, yana zama kusan Abie 2.
Ja'afar ya gaishesa cikin ladabi yana masa sannu da zuwa.
Abie ya amsa fuska asake yana fa'din.
“Ja'afar na sameku lafiya? Ya hkr?�
Aladabce ya amsa.
“Alhmdllh! Abie ga mota can compound ogana da na ma aikin tuqi ya ban Ku sanya min albarka acikinta nakeson mutafi Niger. �
Abie ya murmusa yana sosa sajan fuskarshi ya ce“Ma Sha Allah ubngiji ya sanya alkhairi muje nagani Ja'afar.�
Sosai Ja'afar yay murna shiyasa Abie yake burgeshi sbd baida girman kai.
Tanko ya ce“Abdulmajid ya gajiya sannu.�
Abie ya amsa da“Alhmdllh! Shamsu na sameku lfy? Mal Adamu ya ce“Lfy lau ya jikin Rahma? 'Dazu ta fita daga nan Ashe batajin Hausa inata tambayarta shirk daga 'karshema ta tafiyarta.�
Abie wani irin Smile yay yana fa'din.
“Mal Adamu ina Ummi zata koyi Hausa? Nima naci wuya kafin na koya .�
Dariya sukayi Abie 2 ya ce“Ya kamata muyi mgna Abdulmajid akan Rayyana kaga kowa anan yasan komai bare nace mu ke'be don Allah Adamu Shmsu Ku tayani basa hkr ya yafe mata yabarta yaci gaba da zama da ita, ka hkr tinda ta gane kuskurenta.�
Abie ya shafi sumar kansa yana shaqar 'kamshin babynsa da ya Kama jikinsa yana jin tamkar yanzu ne take wasa da harahenta cikin bakinsa tana zuqe dukkan yawun bakinsa tsabar yadda take mugun sonsa kome nasa so take.
Wani yammm! Yaji baida wani buri yanzu sai yaje ya shige jikinta ya lullu'besu da bargo yana shafarta har ta farka a baccin amman ina yanada uzururuka.
Abie 2 ya dafashi yana fa'din.
“Au sharemu kayi?�
Abie ya numfasa ya ce“Haba! Abien ummina kai yanzu aganin ka zama da irin wannan matar ya dace? Wlh inada tabbacin idan abinda yake shirin 'bullowa cikin satin nan ya 'bullo zatayi abinda yafi Nada muni, ba mamaki kwanciyar mage ta min, bandai sallameta ba amman zan sallametan akwai abinda nake jira na gama, zamuyi rabuwar arziqi da ita idan taso.�
Abie 2 a 'dan zaman da ya yi da Abie ya gano halaiyarsa mutum ne mai tsayawa akan mgna 'daya.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce“Toh Allah ya za'ba abinda yafi zama alkhairi.�
Dukkansu suka amsa da “Ameen.�
Abie yay gyaran murya ya ce.
“Yauwa Mal Adamu insha Allah jibi zaku wuce Ja'afar! Bar mgnar motarka har ka dawo jirgi zaku shiga daga nan har Niger, ka sake biyo jirgi ka dawo dan kawomin takardunka, muga yadda za'ayi.�
Tanko da Mal Adamu baki suka ha'da wajan godiya da masa fatan alkhairi.
Ja'afar yay 'kasa da kansa yana godiya ya ce“Amman Abie ni wlh cigaba da karatu ya fita akaina, a samomin aiki daidai dani akan kasuwanci yafi min.�
Abie ya ce“Ok ba damuwa kaje ka dawo, idan kuma kafi son Niger ka fa'damin gaskiya?�
Ja'afar ya ce“Wlh har zuciyata Tchad ta min zanci gaba da zama acikinta.�
Abie ya ce“Ma Sha Allah yaron kirki.�
Mal Adamu ya ce“Amman idan yaje zai kwana biyu sai anyi bikinsu sai ya taho da matarsa.�
Abie ya ce“Ok Allah ya sanya alkhairi za'a samoma gida insha Allah kafin su dawo an sanya musu kome aciki.�
Tanko harda kuka wajan godema Abie Mal Adamu sai albarka yake saka masa.
Wayoyin Abie dukkansu biyu atare suka 'dauki ringing, ya miqe ya ce“Ja'afar muje naga motar inada baqi yanzu.�
Miqewa Ja'afar yay suka fito Abie 2 na jeroma Abie addu'ar gamawa da duniya lafiya.
Tafe suke yana amsa wayar suka isa wajan motar Abie ya sanya masa albarka da fatan alkhairi, ya shige mota zuwa uzurorinsa.

★★★
Bayan kwana biyu.
*Gabon*
Aishatu jiki ya yi sauqi yau aka sallameta da safe, har yanzu tana kan bakanta akan sai Ma'aruf ya saketa.
Shi kuma ya ce tai masa alqawalin zata kwantar da hanaklinta, ba zata sanya tunanin aranta ba, sannan zata yafe masa ya yarda zai saketa.
Amman taqi bada amsa.
Zaune take a 'dakinta na gidansu saman 'katuwar katifa tana sanye diguwar Riga marar nauyi tayi tagumi tana nazarin duniya, bata ta'ba tunanin Rabi'ah zata ci amanarta ba!
Wasu irin hawaye masu 'dumi suka shiga ziraro mata akan fuskarta.
'Kamshi turarensa ya kawoma 'kofofin hancinta farmaki, tai saurin 'dago da kanta.
Tsaye yake 'kofar 'daki ya har'de hannayensa a 'kirjinsa, hawaye na zuba akan fuskarshi.
Kanta ta kauda ta ce“Natsani ganinka don Allah ka fita kaban waje please. �
Takunsa taji yana kusantota, ta waiwayo paper fara tass ta gani ahanunsa yana beqo mata, tsaye ta miqe zuwat 'kirjinta na bugun uku-uku....

A can Tchad kuwa
Abie ya gama shirya musu tafiya ayau flight 'dinsu zai 'daga 'karfe 2:30 na rana zuwa Niger Tahoua.
Abie yaba Rayyana ma'kuddan ku'di sabida sake gwadata, ya ce suje da Ummun Adnan tayoma su Tanko siyayya, cikin ikon Allah dala 'daya bata ciba, ta siyo komai tsakaninta da Allah, Abie kansa ya yaba da siyayar.
Ibtisam tana nan haukan son Abie na qaruwa cikin zuciyarta duk yadda taso yaqice shi, abun ya faskara da ganagan take wuni afalon wanda dole idan Abie ya fito zasu ha'du bayan amsa gaisuwarta baya sake kallonta, da ya gane dan shi take wuni sai ya fasa shigowa ta waccan hanyar yanzu yake fita, abinci ma sama Rayyana take kai masa, bakinsa da falon gaishe da mahaifiyarsa.
Rahma kuwa fushi take da Abie yaqi korar su Ibtisam, amman da gangan ya qyaleta sai sun tafi ya yi lallashi dan yana kewarta da 'dumin jikinta da zaqin yawunta, kawai shi dai haka yake mutum ne wanda idan baiyi ra'ayin abu ba, toh ba wanda ya isa ya saka shi ya yi, duk tarin son da yakema Rahma bazai ta'ba yarda ta saka shi ya wulaqanta mutum ba, ba tare da babban dalili ba, iyayansu Ibtisam yake dubawa ba wai Ibtisam ba, dan bata gabansa.
Rayyana an saki jiki Abie ya sauko duk da ba abinda yake ha'dasu sai gaisuwar mutunci amman tana qoqarin ganin ta goge laifinta.😂
Ja'afar bai sake shiga sabgar ibtisam ba jira yake su koma Niger ayi bikinsu ya koya mata hankali, tara ne yake.

Misalin 'karfe 1 na rana dukkansu sun gama shirin tafiya, har sunyi ma su Jaddatu bankwana suna 'bangaran su Abie 2. Ibtisam sai kuka take Laraba ta mata tambayar duniya ta ce kanta ke ciwo, nan kuwa kukan barin Abie take.
Jaddatu zaune Rahma kwance saman sofa ta yi matashi da cinyarta tana Sosa mata dogon gashinta, idanunta alumshe.
Sanye take da riga da zani na shadda Ash kala da ganin 'daurin zanin ba wai an iya bane.
Meerah na tausa mata qafafunta.
Latifa ta dire tray'n kayan marmarin da ta yanko musu.
Hanan agefe tana waya, Iman tana rungume ajikinta.
'Kamshin turarensa ya kawoma hancinta farmaki.

Da sauri ta bu'de kyawawan 'kananun idanunta, masu matuqar haske.
Shi da Rayyana ta hangosu suna saukowa anutse suke taka steps.
Idanunta ta runtse, lips 'dinta ta ciza da 'karfi, sai da taji zafin har cikin zuciyarta.
Kusan Jaddatu ya zauna yana amsa waya, ya gaisheta. Ta amsa cikin sakin fuska. Meerah ta gaishesa, ya amsa.
Rayyana ta ce“Ummi 'karama bacci kikeyi?�
Rahma muqus ta yi bata tanka ta ba.
Meerah ta ce“Eh inaga dai tayi baccin ne.�
Abie kallo 'daya ya mata yasan idanunta biyu.
Hannunsa ya 'dora saman goshinta.
Ajiyar zuciya suka sauke atare ya shafi fuskarta akaikaice ya tura mata, 'karamar yatsar shi cikin bakinta, ta tsinci kanta da lasa tana shirin tsotsa yay saurin janyewa dan kar a ankare da su, ya miqe yana fa'din.
Ummi ko zan dawo sai zuwa magarib yanzu sallah zamuyi mu shiga meeting, zanje muyi sallama dasu Mal Adamu. �
Ya 'karashe mgnar idanunsa akan Rahma wacce taqi bu'de idanunta, amman ji take kamar tabi Abienta.
Jaddatu ta ce“Toh adawo lafiya, wai ni kam me kayima takwara naga kamar fushi take dakai?�
Abie ya shafi sumar kansa yana murmushi ya ce“A'a banyi kome ba shagwa'barta ce ta motsa ace mata na fita idan ta farka.�
Rayyana harda su rakiya.

Ibtisam na la'be daman jiran Abie take ai kuwa tana hangosa cikin murna ta sake mannewa jikin bango.
Sai da ya kusa shigowa ita kumaa ta fito aguje kamar an aiketa tana fa'din.
“Toh bari na amso...�
Abie bai shirya ba yaji ya yi karo da mutum yana qoqarin matsawa yana fa'din “Subahanallahi!�.
Yaji ta shige jikinsa ta 'kam'kameshi ta tura kanta 'kirjinsa ta fashe da kuka tana fa'din.
“Wayyo Allah na!!�

_*Please 'yan team Rahmaa da Abienta kuyima Ibtisam hkr, wallahi kowane irin mutum akwai 'kaddarasa da jarabawarsa, ba wai ina goyen bayanta bane, A'a wallahi Ibtisam Allah ya jarabeta da mugun son Abie wanda duk yadda taso ta yaqice shi abin yaci tura, kuga barazanar da Tanko ya mata harda yace zai saki mahaifiyarta, amman kamar tunzurata ake matsalar da aka samu 'karancin shekarunta ta kasa ganewa babban zunubi take aikatawa son wani da auren wani akanta, ta jahilci kanta bayan tayi karatun addini daidai gwargwado, dan Allah Ku mata uzuri ta gamu da jarabawa wanda ta ha'du son zuciyarta. Allah ya yaye mata dan ko batada miji yadda Abie yake son Rahma zamansa da wata mace wlh zata cutu sbd zuciyarsa baki 'daya Rahma take so kenen ko agaban waye zai nuna mata so, duk da bance lallai bazai iya son wata koda bai kai na Rahma ba, sbd Allah shine yake zartar da hukuncinsa akan kowane bawansa yadda yaso, kenan baza'a ce bazai so wataba, Allah yasa mudace ya mana mai kyau Ameen.*_

_Rahmerh ladingo😉_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/25/22, 22:55 - Buhainat: ```D A```

```73&74```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

Not Editing


“Wallahi bana gani idanuna wayyo Anna Baba, idona zafi ka fasamin idanuna dan Allah ka kaini hospital.�
Ta 'karashe mgnar da yaren French cikin kuka tana sake qamqameshi, tanajin wata irin nutsuwa da sanyi na ratsa dukkan jikinta. (wa'iyazubillah.)
Abie cikin zafin nama ya 'ban'bareta daga jikinsa ya ingijeta ya jefar da ita yadda bazata ji ciwo ba! Yana fa'din.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Kidana hankali kuwa? Ke jahilar ina ce? Bakya jin tsoron Allah ne? Kina MATAR wani haka kawai ki kamani ni muharaminki ne? Sakara kawai.
Bu'de idanunki nagani wallahi ko yanzu na miki shegen duka na karya miki wuya ki mutu Ja'afar ya huta da zama da jahilar mace irinki sakara kawai, bu'de idanun maza nagani munafuka!�
Abie yay mata mganar cikin mugun 'bacin rai yana zaro mata manyan idanunsa.
Ai Ibtisam take ta shiga hankalinta ta miqe zaune daga wurgin da abie yay da ita, tana bu'de idanunta tana kuka, kallo 'daya tai masa tai saurin sadda kanta jikinta na mugun rawa, wani irin mugun kwarjini ya mata, ga tsoronsa da ya gama mamaye dukkan illahirin jikinta.
Abie da sassarfa yabar wajan yana dafe goshinsa, azahirin gaskiya ya tsani yarinyar sbd shi mutum ne mai 'kyamar abinda duk yake na haramun, sannan ya tsani mutum mai son kansa dayawa, ta gudo daga 'kasarsu domin Ja'afar sbd son da take masa, yanzu alamunta 'baro² ya nuna tana sonsa, me hakan yake nufi? Tsuki yaja aransa yana fa'din.
“'kasashen duniya dayawa ana ganin kimata, da darajata nafi 'karfin ki zubar min da kima wlh, sakaran yarinya kawai, da batasan me take ba!�
Nutsuwarsa ya saita ya shigo falon Abie 2 da sallama.
Amsawa sukayi, Abie 2 na murmushi ya ce“Wai baka fita wajan meeting 'din ba?�
Abie ya basa hannu sukayi musabaha ya murmusa ya ce“Wlh sai yanzu idan na fito daga masallaci zan wuce.�
Hannu yaba Mal Adamu da Tanko and Ja'afar yana fa'din.
“Ina muku fatan alkhairi Allah ya saukeku lafiya.�
Ya 'karashe mgna yana zura hannunsa cikin aljihun wando dakekiyar shaddar jikinsa Green ya zaro 'daurin 'yan
deux milles 'dauri uku ya be'kama Mal Adamu ya ce“Kaida Shamsu da Ja'afar kowa 'dauri 'daya ayi hidimar biki lfy sai munyi waya, Ja'afar ina jiranka fa!�
Baki 'daya 'kasan 'kafafunsa suka zube suna godiya, da masa addu'u sabida ku'dine wanda dukkansu kowa zai ishesa sabgogin bikinsa har agama ba wanda ya nemi wani abun.�
Sallama yay musu jin ana shirin tayar da sallah nan masallacin gidansa.
Laraba baki da hanci ta Saki tana kallon uban 'daurin ku'din da Abie yaba mazan ita banda ita ko meyasa ya hanata?
Abie ya ce“Ai sai mu hanzarta zuwa masallaci kar atayar da sallah da mun fito sai muwuce airport nayi rakiya.�
Cike da murna dukkansu suka fito domin zuwa masallaci daman sunada alwala.
Ibtisam kuwa tinda ta kalli Abie ta sadda kanta bata 'dago ba saida ta ga ya shige ciki ta miqe tana zubar da hawaye, ta nufi cikin, amman bata shiga ba sai da ya fito ta nufo ciki nan taci Karo dasu Abie 2 zasu masallaci.
Jikin Laraba ta fa'do ta fashe da kuka mai cin rai tana fa'din.“Amatsayinki na mahaifiyata kimin addu'a Allah ya yayemin abinda yake damuna dan Allah.�
Laraba ta ce“Ibtisam ki dawo hankalinki tashi kiyi sallah da sun dawo zamu wuce ni ina hutune.
Kinga mutumin nan ya rabamusu uban ku'di wlh ko sisin kwabo abi ban ba, ikon Allah.�
Ibtisam ta ce “Balarabe ko?�
Laraba ta ce“Eh amman nasan Babanki zai bani.�
Ibtisam ta share hawayenta ta miqe tayo alwala daman tana sanye da hijib madedeci tahau darduma ta tayar da sallah.
Abie ana idar da sallah ya shige moto tare da securities suka fice.
Yahaya ne ya kaisu Ja'afar airport Abie 2 'dan rakiya, shi daau Yahuza, suna nan sai da jirginsu ya cira sama suka nufi gida.
Ja'afar da Ibtisam wajan zamansu 'daya amman ko kallo bata ishesa ba, sabgogin gabansa yake.

*Gabon*
Aishatu sosai jikinta yake rawa gabanta yana fa'duwa, ganin paper 'din hannunsa tasan sakinta yay.
Danne abinda takeji tai ta sanya hannunta wanda yake rawa ta amsa tana fa'din.
“Allah yasa haka yafi alkhairi.�
Ta 'karashe mgnar zata zauna, taji ya fizgota ta fa'do jikinsa ya rungumeta ta baya, ya 'dora ha'bar akan kafa'darta, cikin kwantar da murya ya ce“Yanzu don Allah kinason na sakeki?�
Fizge jikinta tai tana nunasa da 'yar yatsa ta ce“Karka raina min hankali mana, kana nufin ba sakin nawa kayi ba?�
Sake damqota yay ya rungumeta ya ce“Wlh bazan iya sakin ki ba! Don Allah ki yafemin zan dai barki har lokacin da za ki sauko dawo gida wlh Allah ban ta'ba zina ba, abinda dai da na fa'da Munnira shine gaskiya wlh bana haiyacina komai ya faru ki fahimceni dan Allah.�
Jikinta ta janye ta zauna tana bu'de takardar, da abinda ta fara cin karo ya sanyaya mata jikinta.
BAN HKR MY AISHER��😭

HMM! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki.
INA SON
KASANCEWA A TARE DA KE HAR ABADA my Aisher.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan tab'a canjawa a kan hakan ba, don Allah ki yafemin my dawo kamar da nayi miki alqawalin zama dake bisa amana, ina sonki my Aisher.�

Ajiyar zuciya ta sauke a'boye amman azahiri tai kicin² da fuska ta miqe ta shige toilet ta banko 'kofar.
Murmushi yay ya juya ya tafi.
Rabi'ah wasa² tana cikin tashin hankali duk ta fige ta lalace komai baya mata da'di, sai tayi yin'kurin zuwa ganin Aishatu sai ta fasa gabanta na fa'duwa amman ta 'dauki alqawalin zuwa dubata da neman gafarata idan abun ya lafa.

*Niger*
Inna Hansatu an kasa zaune an kasa tsaye anata murna Ja'afar da babansa zasu zo, an yanke zabbi guda uku manya anyi farfesu an dafa macaroni da shankafa, an gyara musu salad da kwai anyi kunun gyad'a kai abun Masha Allah.
Sadiya tazo ta Kama mata girkin da Deluwa Maimou ta 'kwal'kwale gidansu tasa tana turaren wuta abin gwanin ban sha'awa ta share 'dakin Ja'afar ta goge an canza zanin katifa, Mahmoud ya wanke wanda yake kwana Asama.

Can ma Dadda da yaran sunzo sun gayara gidansu Laraba, Taslim Masha Allah, ta share 'dakunan ta goge ta kunna turaren wata, Dadda ta sayo zakatu biyu aka yanka ita da Taslim suka 'Dora girkin.
Dadda tana mota miyar Taslim ta ce“Don Allah Dadda ki daina zatayi 'karni fa!�
Aydah tai dariya tana fa'din.
Kince Dadda bata iya girki ba.�
Dadda ta ce“Barta Aydah 'Yar ashatta ko uwata ta gwadamin girki bari na kammala muci kuji.�
Taslim tai dariya ta ce“Yo abinda duk Rabin miyar nice ni da nafi Auntie Ibtisam ma iya girki.�
Dadda tace“Ai shagwa'bar ta barta iya girki ja'ira ai Ja'afar zai ga tab'ara.�
Dariya sukayi bayan sun kammala firkin bayan Maghreb sunyi sallah Dadda ta zuba musu sukaci suka 'koshi dam nan suka Kama hira dan Dadda na tare dasu sa iyayansu sun zo sai ta wucce gida.
Inna Hanssatu zaune an kakkame an sha wanka masha Allah ga 'kunshin gargajiya ansha 'kafa da hannu, gida ko ina sai baza 'kamshi yake.
Deluwa ma ansha kwalliya ba laifi tana 'kofar 'dakinta da yaranta.
Abinci Hansatu ta raba, Mahmoud na gefe ta kirasa.
“Mahamoud! Zo 'dauki naka kai da 'yan uwanka, Maimouna zo kema ga naku. Deluwa matso muci.�
Maimou ta ce“Yaufa akwai kwasar ganima, bari muci kafin su Baaba su zo suci su rage muci sauran.�
Inna Hansatu ta ce“Ai sai kici uwar cikin ci tinda ubanki ya bayar da ku'di.�
Deluwa tai gum da bakinta tana gun abincinta kar ta tofa tasha gori.

*Morocco*
Wata dattijuwa ce zaune a'kalla zata kai shekaru sittin da biyu, sai wata 'yar matashiya wacce bazata wuce shekaru 28 ba sai dattijo zai kai shekaru saba'in yana waya cikin harshen larabaci yana sakin murmushi.
Sai wasu kyawawan twins maza zasu kai shekaru 9.
Falon kawai zaka kalla kasan an tara dukiya.
Tv suke kallo tashar Aljazeera ana labarai, yayin da yaran nan game suke a wata Tv plasma suna tsereran jirgi.

Ummiterh ta ce“ Yaro kuzo ga Abien Ummi yau mu ko neman mu baiba wai sai mun koma can gidanmu, don Allah tinda Abbunku bayanan ai gwara mu cashe anan ko?�
Ai kuwa aguje suka nufo mahaifiyar tasu suna dariya, suka rungumeta suka bata Sumba suka miqe suka isa suka kewaye kakan nasu suna cewa ya basu wayan su gaisa da Abien ummi.
Zainabu dattijuwar ta kaima Ummiterh duka ta ce“Zahra bakyajin mgna wlh ke wai bakisan kin girma ba?�
Ummiterh tai dariya ta Abby kace uncle Abdul mun kusa zuwa Tchad. �
Wayar ya bek'o mata yana murmushi ya ce“Abdul Zahra da mayya ce idan ta kamaka kasheka zatayi.�
Abie daga can wanda yay luf bayan mota suna hanyar zuwa gida agajiye yake lilis ga yunwa ga bacci tin fitar azuhur bai dawoba sai yanzu kusan tara na dare, duk da tseraiya lokacin da take tsakaninsu.
Gyaran murya yay ya ce“Ai ni ummiterh ba ruwana dake matuqar bazaki koma gidanki ba, kinga na gaji ga bacci yunwa duk nakeji zamuyi mgna gobe OK?�
Ummiterh ta ce“Toh naji ga Twins na nemanka.�
“Ok ban Ammi muyi mgna sai ki bani su.�
Ammi ta basa sukayi mgna ta basa yaran suka ta'ba hira ya dates kiran.�
Abby ya ce“Toh fah lokaci ya yi Abdulmajid matarsa yakeso ta tare Allah ya jiqan Aliyu.�
Ya shafe 'kwallar idanunsa.
Zainabu ta ce“Hakan yafi ai amman ina dalili ace sai ta gama karatu ai da sauranta dukanta Rahma nawa take, yanzu zata San mune muka haifi mahaifinta.�
Ummiterh ta share 'kwalla ta ce“Damuwata da batasan suwaye 'yan uwan Ummul Aymana ba, duk da an barsa amatsayin kune Abby amman ai dole zata san gaskiya, 'yan uwan mamarta an kashesu a yaqi wasu kuma har yau ba'asan Inda suke ba.�
Abby ya ce“Zahra kin fiye mgna ai dukkanmu zamu tafi Tchad dole ayi komai agabanmu har bikin sai anyi zamu dawo Abdulmajid haka ya ce shi da Rahamu, amman ke ki tambayo mijinki idan y'a barki.�
Ummiterh ta zumb'uro baki gaba ta ce“Ai zai barni ma.�

*Tchad*
Zazzaune suke a falon tin bayan da suka gama abincin dare.
Rayyana acin ubansu kwalliya, sai baza k'amshi take.
Rahma sanye da wata riga maroon color ta yi kyau sosai rigar tabi jikinta kanta ko 'dan kwali babu, amman ta tuf'ke gashinta, ta yi kyau sosai duk rigar simple ce.
Doorbell aka danna Rayyana zuwat ta miqe ta tafi.
Rahma ta bita da kallo.
Hanan ta ce“Ummi! Ashe su Jaddatu Zainabu sun kusa zuwa?�
Jaddatu ta kur'bi shayi ta dire cup 'din ta ce“Eh munyi mgna da Abbyn Ummiterh.�
Hanan tai dariya ta ce“Kenan zata fashe? Anata min 'kumbiya² nasan komai wlh.�
Rahma ta rungume Jaddatu tana murna ta ce“Jaddati Ashe shiyasa 'dazu ummiterh ta kirani tana cemin tayi mafarki tazo Abienah ya korata kuji sharri.�
Dariya sukayi Jaddatu tana cewa “Ki share ummiterh ja'irace uwar banza.�
Rayyana tana bud'e 'kofar Abie ya bayyana.
Taso rungumeshi ganin yanayin yadda ya tsare gida.
Murmushi tai masa ta Kama hannunsa ta ce“Habiby barka da zuwa, fatan dai kana lfy? Ya gajiya? Wlh duk na damu tin azuhur da ka fita sai yanzu, hope lafiyarka k'alau?�
Ta 'karashe mgnar cikin nuna tsantsar damuwa idanunta har ya kawo ruwa.
Abie ganin yadda ta nuna damuwarta da shi yasa ya kamo 'dayan hannunta yana murmushi ya ce“Lafiya lau ai daman dai kinsan nakan zarta hakan wani sa'ain hope kowa lfy?�
Kai ta jinjina ya Saki hannun suka jera falon.
Rahma na jin takunsu ta waiwayo idanunta suka sauka akan nashi, tai saurin ha'de face ta juya kanta, tana 'ka'kalo murmushin yaqe ta Kama hannun Iman tana fa'din.
“Baby gobe za'a mana zanen henna me kyau kina so?�
Cikin murna Iman ta ce “Eh Auntie ina so.�
Murmushi Rahma tai ta sumbaci goshinta, ta kalli Jaddatu ta ce“Kema kina so ko Jaddati?�
Jaddatu ta ce“Allah rabani da abin kunya, ko ran aurenki ai irin na tsofaffi zanyi.�
Dariya suka sanya, sallamar Abie ta katse musu dariyarsu.
Jaddatu ta ce“Abien Rahma sai yanzu? Sannu.�
Kusan Jaddatun ya zaune yana amsar gaisuwar Hanan Iman na masa oyoyo ta zauna zaman cinyarsa.
Rahma ta dake ba tare da ta kalleshi ba ta ce“Abie sannu da zuwa.�
Taja bakinta ta tsuke.
Abie ya amsa yana tambayarta“Baby kinci abinci?�
Kai ta 'daga ha'di da cewa“Eh�
Rayyana sama ta haye domin ha'da masa ruwan wanka.
Hanan ta ce“Yayana ashe mun kusa baqi?�
Murmusawa yay ya ce“Wannan ummiterh 'karamar uwata akwai baki kamar aku. Hanan iyayan gulma mijinki dai ya kusa saukowa daga daji atattara atafi.�
Rahma kallonsa take cike da mugun sonsa da 'kaunarsa, take kallon yadda 'kananun la'bbansa ke motsawa yana mgna anutse.
Karaf idanunsa ya fa'da cikin nata, kauda kanta tai tana Kama hannun jiddatu, cikin saita nutsuwarta take fa'din“Jaddatu kalli faratanki sun fara tsayi.�
Abie kallonta yake cike da mamakin yadda ta sharesa, tana sambgogin gabanta.
Miqewa yay ya ce“Ummi na shiga zan watsa ruwa na kwanta sai da safe.�
Jafdatu ta ce“Abinci fa Abdul? �
Sajansa ya shafa ya kafe Rahma da idanu ya ce“Rayyana zata kawomin Ummi nagaji ne. Babyna sai da safe bye.�
Ya 'karashe mgnar yana juyawa ya fara tafiya.
Rahma ko kallonsa batayi ba, tana cigaba da hirata da Jaddatu.

Ya na

Please Login or Register in order to submit comment