Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

doctor kamar jiran fitarta take numfashin Rabi'ah ya tsaya cak bakinta na motsawa sam bakajin abinda take fad'a.
Aishatu idanu ta zuba mata ganin bata motsi jikinta ya d'auki rawa.

Dr yana dubawa ya ce.
“Kullun nafsin za'ikatul maut. Allah ya mata rasuwa kuyi hkr.�

Aishatu nan ta zube k'asa asume.
Mama kanta abun ya girgiza k'asa ta zauna dab'as ta dafe kanta wasu hawaye mai zafi ya zubo mata tana fad'in.
“Rabi'ah wallahi na yafe miki duk qamar da make nuna miki sabida ki gyara rayuwarki ba dan na tsaneki ba.�

Murta ya d'auki yaron Wanda har lokacin yana shan nonon uwarsa.
Idanu ya shafema Rabi'ah yana kuka kamar yaro.
Dr dakyar ya ceton ran Aishatu Wanda aka Kira Ma'aruf mutuwar Rabi'ah ta girgizasa matuqa.
Washegari da safe aka basu gawar Rabi'ah aka sallace ta aka kaita gidan gaskiya yaron na wajan Aishatu wani magani na gargajiya aka had'a mata ta Sha take ruwan nono yazo.
Aishatu bayan kwana uku ta saka aka tara dukkan families nasu ta musu bayanin abinda ya faru Wanda ta b'oye wani abun ta ce dai k'addarace kawai ta had'asu agidanta wani lokaci abisa kuskure cikin dare ya dawo daga tafiya Rabi'ah tazo tayata kwana har hakan ta faru Ashe rabone.
Kowa hakan ya d'auki maganar yamata addu'ar Allah ya bata ikon riqe yaron da amana mahaifiyasar Allah ya jiqanta.
Randa akayi sadakan sati aka sakawa yaron suna Umar Farook.
Kafin Arab'in yaro yayi mulmul sabida Gatan da yake samu Ma'aruf Allah ya jarabesa da son yaron ga wani irin bud'i da yake shigo musu Masha Allah.

★★★
Ibtisam cikinta na cikawa wata takwas Ja'afar ya shiriya musu zuwa Niger ya kaita haihuwa kwanansa biyar ya juyo wanda da zarna ta haihu zai dawo.
Toh masha Allah tana samun kulawa sosai cikin ya tsufa zama dakyar tashi dakyar an bata sati biyu Wanda ba lallai taci satin ba ma.

*Tchad*
Masha Allah Abie sunje Morocco sun memo auren Meerah an basu Wanda basu baro qasar ba sai da aka d'aura auren aka basu amaryasu.
anan gidan Abie akayi taron biki abin sai Wanda yagani b'angaran Abie2 aka zuba sabbin kaya dole idan ka shiga wajan ya burgeka, sai da Meerah tai kimanin kwana uku kenan da tarewar amman Abie2 ya kasa tab'ata, sai da tai kusan sati yaje ya zage ya fuskanceta aka b'arji amarci ya sameta cikakkan buduwar ta samu tattalin so fiye da yadda zan kwatanta Ashe Abie2 ya Iya love, cikin sati biyu sun murje sunyi qiba suna shan love kullun Rahma sai tazo ta zubama Abie2 shagwab'a ya lallab'ata kafin ta tafi.

Abie ya ce bayason Abie2 ya yi komai ya huta akan wuyar da yaci aduniya kusan shekaru ashirin da biyar.
Amman yaqi ya fara fita aiki companyn Ja'afar.

Rahma kuwa cikinta wata bakwai da 'yan kwanaki qalilan amman Masha Allah kace yau zata haihu dan tayi girman ciki.
Wata irin kulawa suke samu ita abin cikinta soyayyarsu da Abie sai qara hauhawa take.

Zaune take a falon nasu na qasa wanda suka tare d'akin k'asa.
Saman carpet tana cin mutumin nata strawberry.
Sanye take da doguwar riga shara-shara.
Idanunta akan TV.
Jin motsi ta waiga.
Abie ta gani cikin shirin fita ya ha'da cikin wasu irin kayan Pakistan masu uban tsad'a yana baza k'amshi ba abinda yafi burgeta irin hular kansa da takalmin k'afarsa da glass d'in da yake manne akan kyakkyawar fuskarsa.

K'ananun kyawawan idanunta ta qura masa tana kallon tsadadiyar agogon da take d'aure a tsintaiyar hannunsa, yana dubawa.

Qarasowa yay gabanta ya rusuna yana sakar mata tattausan murmushi ya shafi fuskarta ya d'ora hannunsa saman k'aton cikinta ya shafa ya rusuna ya kai guiwowinsa k'asa ya sunkuya ya sumbaci cikin ya ce.
“My babies ya kuke?�
Ya d'ago yana d'aga mata gira ya ce.
“My ruhi ya dai kina son sanin Inda Abienki zaije koh?�
Ashagwab'e ta turo bakinta gaba tana sanya masa strawberry abakinsa ta ce.
“Wayyo My Abieh kayi kyau sosai zan bika, dan Allah karma bari matan banzan su kalle min kai kaji...�
Wani irin ihu ta Saki lokacin da taji marata wani abu ya sokaeta kamar allura ta damqe damtsam hannun Abie.
Arikice Abie ya ce.
“No! My Baby meye haka idan bakyaso nafita na barki zan jira har kiyi bacci OK?�
Rahma bayanta taji ya riqe cikinta yay wani irin murd'awa take taji yaron cikin na zillo ga azabar da marata take cikin seconds goma har zufa ta karyo mata, cikin fitar hayyaci ta ce.
“Wayyo Abie zan mutu bayana marata cikina wallahi ba wasa nake ba, ka kaini wajan Jaddatu.�

“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Babyna ko naqudace ai lokacinki baiba na shiga uku.�.
Ya qarashe mganr yana ciccib'arta sama ya nufo babban falon, yana kiranta Babyna kiyi haquri yanzu zamuje asibiti qila juyawar yarone.�
Hahaha Abie inaga zaka zama ubane fa yau

Whtspp number😊
_*+22796515805*_

_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
6/7/22, 19:48 - Buhainat: ```D A```

```106```

_Rahmerh Ladingo😉_



*ALHAMDULILLAHI��* Masoya Ngode sai mun ha'du JIKAR BULAMA, nan kusa kujirani da zafinsa zai fito, Tabbas wannan tafiya ta daban ce.😹 tabbas idan kin karanta Dattijon Arziqi toh JIKAR BULAMA ya shafeshi a dad'i da soyayyar cikinsa da darusan cikinsa da makirci da darasi da komai fatana ku biyoni muje zuwa, wannan da zafinsa yake tafe sannu-sannu nake tafiyar da salona, bana takurawa bana gaggawa amman na tabbata za ki/ka ku anfana wannan shine burina wa makaranta.��
Ya ALLAH duk labarin da ya kasance babu darasi acikinsa ko fad'akarwa karka bani ikon rubuta shi.��


Jaddatu zaune tana kallon tashar Aljazeera, tana Jan casbi taga Abie d'auke da Rahma hakalinsa a tashe yana doso falon.
Jaddatu ta miqe tana fad'in.
“Innalilalhi wa'inna ilaihir raji'un! Abdul me ya faru da Rahma?�
Gabanta ya iso ya ce“Ummi ki kwantar da hankalinki inaga juyin cikina ta ce maratan da bayan da cikinta suke mata ciwo...�
Jaddatu ta matso tana kallon Rahma ta ce.
“Maza muje asibiti haihuwace ba juyawar ciki bane.�
abie bai jiraba me zatace yay gaba cikin sauri jin yadda Rahma ta cikuikuiyeshi tana kiransa.
“Abie! Marata bayana.�
Sannu kawai yake mata.

Jaddatu ta kiraUmmu Adnan da Latifa sukanzo cikin sauri suna zubewa gabanta.
“Yawwa Maza zo ki had'ado kaya ki samemu mota, Latifa ke kuma kiyi qoqarin had'ama farfesun hanta da k'oda da kunnun madara.�
Ta k'arashe mgnar tana gyara mayafin kanta tana tokara sandarta ta nufi k'ofar fita.
Ummu Adnan ta shiga ta had'o kayan haihuwa wanda daman su suka jera a d'akin da yake kallon na Rahma da Abie, ta had'o komai ta fito ta rufama Jaddatu baya.

Meerah ta fito da niyar shiga wajan Rahma taga ko lafiya yau bata shigo, ta hango Abie d'auke da Rahma ya nufi parking spaces.
Cikin tashin hankali ta bisa tana tambayarsa.
“Abie me ya sameta?�
Abie ya ce“Inaga haihuwace.�

Meerah ta koma ciki da gudu ta d'auki wayanta, ta Kira Abue2 ta sheda masa zasu asibiti Rahma na naquda.

Abraham daga nesa ya hango Abie d'auke da Rahma, yay saurin isa rumfar ajiye motocin ya fito da wata baqar Jeep.
Baya shigar da ita shima ya shi ya zauna yana rungume da ita.
Meerah da Ummu Adnan suna gaba Jaddatu baya wajansu Abie suka d'unguma zuwa hospital.
Sosai suke tausaya ma Rahma ganin irin azabar da take Sha, sai damqe Abie da Jaddatu take tana cizon lips d'inta, Abie sai sannu yake mata.

Suna isa asibitin aka amsheta cikin gaggawa aka nufi labor room da ita, Wanda Abie yaji tamkar ya bita suyi naqudan tare.
Jaddatu suna zazzaune sunyi jugum² suna zaman jira.
Abie ya aksa zaune ya kasa tsaye sai kai kome yake.
Jaddatu ta kalleshi ta ce.
“Don Allah Abdul ka zauna, adsu'armu kawai take buqata.�
Goshinsa ya dafe yana hango yadda aka shiga da ita labor room.

Dab da ita ya zauna yana danna casbi da yake maqale atsarsa, bai iya cewa komai ba.
Abie2 ya iso suka gaisa da Jaddatu ya zauna kusan Abie1 yana fad'in Allah ya bud'e idanu lafiya.
Jaddatu da Meerah suka amsa da.
“Ameen.�
Abie aqasan labb'ansa ya amsa da Amin.

Kusan awa biyu Rahma tana famar naquda, taci uwar azaba kafin Allah ya sauketa lafiya, ta haifo yaranta kyawawa mace da namiji, macan babu abinda ya rabata da Rahma har 'kananun idanunta sak, haka namijin ba abinda ya rabasa da Abie, ma'ana dai yaran baki d'aya Abie ne macan ce ta 'dauko idanun Rahma.
Yaran bakwaini ne 'yan mitsi² dasu, suna fitowa duniya bayan agyarasu aka sakasu a kwalba, aka kaisu wajan da za'a dinga kula dasu tsakaninsu da Rahma sai idan zata shayar dasu, sai da aka gama shirya Rahma tsaf baccin wuya ya d'auketa kafin aje sanar dasu Abie.

Lokacin da nurse ta fito bada albishir Rahma ta haihu, Abie na hangota jikinsa ya d'auki rawa bakinsa na makyarkyata ya ce.
“Ya don Allah har yanzu?�

Nurse tai murnushi ta ce.
“Alhmdllh! Aqa'idar asibitin nan bama sanar da kowa nasa ya haihu sai an gyara yara da uwarsu sai mu fito mu sanar yadda zakaga naka cikin farin ciki.
Madam ta sauka lafiya ta samu mace da namiji amman suna kwalba sabida basu isa haihuwa ba.�
Abie ya ce.
“Alhmdllh! Allah Kaine abin godiya da ka azurtani da Yara biyu lokaci d'aya haqiqa kinada babban tukuici.�

Jaddatu ta rangad'a gud'a ta ce.
“Alhdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!!! Yau Rahma ta saukewa Abdul Yara biyu.�
Sai ta fashe da kuka, Abie ya rungumeta yana murmushi ya ce.
“Ummi don Allah ki daina kukan haka muje anuna mana yaran.�
Abie2 ya ce.
“Masha Allah, D'iyar albarka tai k'ok'ari sosai Allah ya bata lafiyar shayarwa.�
Meerah tana kallonsa ta amsa da.
“Ameen ya Allah.�

Wajan Rahma Nurse ta fara kaisu.
Kwance take tsaf abinta tana bacci, tamkar ba ita bace ta gama yaqi.
Abie ba kunyar kowa ya isa ya zauna bakin gadon ya riqo hannayenta yana murzawa ya rankwafo dab da fuskarta ya sumbaci goshinta ya ce.
“My baby sannu Allah ya miki albarka ya baki lafiyar shayarwa, Ngd sosai baby Ummi kinyi qoqari Allah ya albarkaci yaranmu.�
Su Abie2 suka amsa da.
“Ameen.�
Jaddatu zauwa tai ta rungumeta tana saka mata albarka, ita kam baccinta take bata San me suke ba.
Jaddatu ta Kira Latifa awaya ta ce maza tayi sauri ta kawo farfesun Rahma ta samu taci.

Wajan yaran aka kaisu masha Allah kayawun yaran abun kallone 'yan k'ananu dasu.
Abie yay musu addu'a tare da kiran sallah ya rad'a musu suna.
Namijin Abdulwahab suan mahaifinsa macan UmmulAymana.

Duk yadda zan fad'i dad'i da farin cikin Abie da zuri'arsa suke ciki akan wannan haihuwar toh bazan gayi daidai ba sabida gabaki d'aya kafofin sadarwa ba Inda Abie baiyi shelar haihuwar ba, kowa murna yake tayasa jama'a nesa dana kusa kiransa sukeyi taya murna.

Ja'afar har iyayansa ya Kira ya gayamusu suka Kira Abie sukayi masa barka harda Tanko hakan ba qaramin kima ya qarama Ja'afar wajan Abie b dan aduniya Wanda zai nun k'aunarsa da yaransa ko Rahma da Jaddatu toh ba qaramin masoyinsa yake kallonsa ba.

Kusan kullun asibitin cike take ga abokan arziqi mazu zuwa ganin Rahma da yaranta Wanda aqalla yanzu kusan kwana goma kenan, yaran suna samun kulawa sosai Rahma Allah ya jarabceta da son yaranta matuqa ba kamar macan da tai irin idanun mahaifiyarta.

*Niger*
Misalin k'arfe d'aya na rana Ibtisam zaune ta bararaje, tana cin wake da shinkafar da akayi, tana ci tana turo baki.
Laraba ta ce.
“Wai baqin ran me kikeyi yau Ibtisam? Me aka miki? Ji yadda kike cin abincin kamar dole kodai bakya so ne?�
Ibtisam ta qaqalo murmushin k'arfi tai ta ce.
“Kai Anna wlh ni bawani baqin rai da nakeyi kawai banajin dad'in yanayin ne.�
Anna tai shiru kamar batasan naquda ta fara.
“Taslim ku qare cin abincin kije ki kirawo mun Dadda.�
Taslim ta amsa da.
“Toh Anna.�

Ibtisam ta yamutsa fuska tana ciza lips ta ce.
“Me zata miki Anna? Ni kamar ma natafi can.�
Laraba ta ce“A'a ki zauna ai zatazo.�
Ibtisam batace komai ba tana tura Wake da shinkafar kamar dole.
Suna gamawa Taslim ta tafi gidan Dadda kiranta.
Kamar wasa Taslim na fita naquda ta tasoma Ibtisam gadan-gadan, ai kafin su Dadda suzo Laraba ta Kira Tanko a waya yazo da mai taxi suka nufi asibiti.

Cikin hukuncin Allah suna zuwa Ibtisam bata huce 30 minutes ba Allah ya sauketa lafiya ta haifo k'aton d'anta mai Kama d Ja'afar sak har baqin ba abunda ya bari.
Wai kai karkuso kuga murna wajansu Inna Hansatu mai waina, Mal Adamu tsabar farin ciki shi ya Kira Ja'afar ya gayamasa.
Ja'afar rasa idan zai saka kansa yay dan murna lokacin da Mahmoud ya tura masa hoton yaron.
Tabbas wannan zuri'a sunyi farin cikin haihuwar Ibtisam.
Ita kanta tana mamakin dangin Ja'afar haka suke son Ja'afar.

Tin ranan Ja'afar ya fara shirin tafiya su Harisu sukace bazai barsu a motarsa zasu zo wacce aka dubata sabida yasan abanza zasuci kwana uku ahanya.

Lokacin da yazoma Abie sallama zai tafi ba qaramin alkahiri Abie ya masa ba duk wata hidima da za'ayi ta suna ya d'aukar masa nauyinta komai ya basa yaqi karb'a sabida ayanzu yannada rufin asirinsa, amman ganin Abie ya b'ata ransa dole ya amsa, yay godiya.
Ai kuw kwanansu uku ahanya kafin su iso.
Inna sai tattalin Ja'afar ake an kasa zaune an kasa tsaye.
Ibtisam na shayar da yaron taji daga tsakar gida Laraba tna fad'in.
“Ah Ja'afar zauwar yaushe?�
Zazzaqar muryasa taji yana gaisheta ya ce.
“Yau d'azu muka shigo Anna fatan mum sameku lafiya ya masu jiki?�
Laraba ta amsa da lafiya bismillah ka shiga tana d'akinsu.�
Ibtisam tai saurin zarema yaron nono ta kwantar da shi tai saurin kwnciya ta rufe idnunta.
Da sallamaa ya shogo d'akin kallo d'aya yay mata ya gane baccin qarya takeyi.
Murmushi yay ya d'auki yaron ya zauna dab da ita.

Idanu ya qurama yaron sam baiga wani banbancinsa ba da yaron, komai nasane yaron ya d'auko.
Bakinsa ya manna kunnen yaron yay masa addu'a duk da yasan anyimasa, sannan yay masa huduba da sunan mahaifinsa Adam.
Kuka yaron ya tsala, yay saurin mirgino Ibtisam ya janye rigarta ya saita masa abincinsa ya kuwa kame yana tsotsa.
Ibtisam ta qyalqyale da dariya ta ce.
“Idanuna biyu fa! Mon amour sannu da zuwa ya gajiya?�

Rungumeta yay ya ce“Hahaha nasani Mon cherie, sannunki nagode sosai fa kinyi qoqari haifomin gwarzon namiji Allah yasa bad'i warhaka ki qaromin twins... �
Dukan wasa ta kai masa tana kwab'e fuska ta ce“A'a gaskiya...�

Masha Allah ranan suna anyi suna mai qayatarwa, suna yayi armashi Ja'afar da iyayansa sunyi komai na bajinta anci ansha, kowa na son barka yaro yaci sunan mahaifin Ja'afar Adam, ana kiransa da Rafael.
Ja'afar satinsa d'aya ya koma tchad wajan aikinsa Inda ya tafi yabar Ibtisam da iyayansa da 'yan uwansa da kewarsa.
Haka Ibtisam taci gaba da wankan ruwan zafi tana samun kulawa sosai ita da yaronta Rafael.

Acan kuwa Chad.
Rahma nada sati biyu da haihuwa akayi suna, an yanka raguna anyi abinci an raba sadaka tinda Rahma da Yara na asibuti anabasu kulawa.
Sai da suka kwashe wata biyu a hospital ana kulawa da yaranta wandan ayanzu sunyi mulmul sunyi wani irin qiba kamar ba bakwaini ba amman doctor ya ce baza'a sallamesu ba sai yaran sun cika wata uku sunga ba wata matsala.

Rayyana cikin wata hud'u da aure tayi wani irin kyau sabida wani irin so Nafi'u yake mata, sabida yadda ta kwantar da hankalinta tana binsa sau da k'afa, tana bin matansa a kullun sai ta shiga b'angaransu sun gaisa haka tana son yaransa hakan ba k'aramata kima yay wajansa ba.
Yau ita ce me girki tin k'arfe uku ta shiga kitchen ta fara shirya masa dadd'an abinci.
Misalin k'arfe 9 zaune take a falonta Wanda yasha turaren wuta sai qamshi yake, taci kwalliya tsaf abinta, sai yamutsa fuska take sabida mugun tashin zuciyar da ya sakata gaba tin yamma dakyar ta kammala girkin da yamma.
Kanta taji ya Sara mata ta dafe tana fad'in.
“Washhhh! Anya ba ciki gareni ba?�
Ta tambayi kanta tana miqewa tsaye jin qaran buga qofar falonta.
Tana bud'ewa suka had'a idanu da Waheeda, wani irin tsalle tai ta dire gefe ta ce.
“A'uzubillahi minan shed'anin rajin bismillahi rahamanir rahim. Dan ubanki fitarmin agidana.�
Waheeda ta zube qasa tana riqe k'afafun Rayyana tana fashewa da kuka ta ce.
“Don Allah ki yafeni wlh naga jarabawar ko nace miki naga sakayya bakiga yadda nakoma ba wlh alhakinku ne na qara nadamane Ajiya labarin irin hukincin da Allah yayima Malam yanzu haka yana yawo tsirara kasuwa² yana fad'in abubuwan da shuka arayuwarsa don Allah ki yafeni bazan sake ba na tuba wlh kowa guduna yake dan Allah ku yafemin...�

Rayyana ta ingijeta da k'arfinta tace.
“Bani bake karki sake kallon titin gidana ma, kije na yafe miki amman babu alaqa ko ta gaisuwa tsakanina dake.�
Rayyana ta qarasa mgnar tana turata ta janyo qofarta ta murza key taji zuciyarta na tashi ta nufi toilet aguje ta fara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta.

Awahalce ta fito tana maida numfashi taji ana knocking.
Awahalce ta isa ta bud'e.
Ganinsa ta afka jikinsa tana sauke numfashi.
Alhaji Nafi'u ya tarairayota jikinsa yana fad'in.
“Subahanallahi Habibiya bakida lafiya ne?�
Kai ta d'aga masa tana narkewa ajikinsa.
Alhaji Nafi'u duk ya rud'e sai tattab'ata yake ya ce.
“Muje ki saka hijab muje hospital.
Rayyana bata musaba tafison ta tabbatar da zarginta.
Aikuwa suna zuwa asibiti gwajin farko Rayyana na d'auke da cikin sati hud'u.
Wai karkaso kuga farin ciki wajan alhaji Nafi'u tamkar yau za'a fara masa haihuwa, kaf iyalansa ba wanda baiji ba wannan cikin, hajiya Sha'awanatu har mamaki take duk da tasansa mutum mai son 'ya'ya sosai.
Wannan dare sun rayasa cike da wata irin soyayya ko motsi tai zai tambayeta me takeso, Rayyana banda godiyar Allah ba abinda takeyi, dan ita kanta tazan ta samu mijin da kowace macs zataso mallakarsa.

*Gabon*
Aishatu zaune a falo tana shirya Farook yaro d'an kusan kimanin wata 4 yayi wata irin qiba me burgewa fari Tass da shi masha Allah.
Sai yakushin Aishatu yake yana dariya, tsantsar kamarsa ta sake bayyana da Ma'aruf.
Kumatunsa taja tana dariya ta ce.
“Idan ka ciremun idanu naga wa zai maka wasa ja'irin d'ana kawai...�

Shi dai dariya yake ya fara qoqarin sanya hannunsa cikin rigarta.
“Uwani! So don Allah kamamun yaron nan naje na shirya mutafi kasuwar nan.�
Ta k'arashe magana tana sanya masa takalmi.
Uwani ta iso tana sanya hannu zata d'aukesa ya qamqame Aishatu ya sanya kuka.
“Ai kam kin sansa da naci bazai jeba je abinki Dadynsa zai fito yanzu ne.�
Ta k'arashe mgnar tana janye rigarta ta fara shayar da shi.
Uwani ta tattare kayan da aka ciremasa ta gyara wajan ta tafi.

Ma'aruf ya fito cikin shirnsa yayi kyau sosai ya zauna kusan Aishatu yana sumbatar wuyanta, ya ce.
“Eh lallai zaku hau taxi kuwa tafiyata zanyi idan kin biya D'an nan naki komai bazakiyi ba!�
Ya fad'a yana Jan hancin Farook, ya saki Maman yana b'angala masa dariya.
“Yauwa toh riqesa ban 5 minutes na shirya.�
Ma'aruf kallonta yake cike da tsantsar k'aunarta ya riqe fuskarta da tafukan hannunsa yana fad'in.
“Haqiqa da na rasa amatsayin matata nayi babbar asara wlh samun irinki aduniyar nan ta yanzu akwai wahala, banida bakin da zan miki godiya sai da na miki fatan gamawa da duniya lafiya, ubangiji ya bamu zuri'a dayyaba.�
Ya qarasa mgnar yana sumbatar bakinta.
Aishatu ta ce.
“Ameen ya Allah Abban Farook mijin AISHA. �
Dariya suka sanya suna rungume junansu, yaronsu na tsakiya shima dariyar yake b'angalawa, Aishatu ta ce.
“Oya je wajan Abba na shirya.�
Ta k'are mgnar tana beqawa Ma'aruf shi ta shiga ta shirya ta Kira Uwani suka tafi akasuwa ya ajiyesu ya wuce shagon gwanjonsa Wanda yanzu abun ya bunqasa yaransa ma mutum biyar ne sari d'aurin dila kawai yake bayarwa an daina siyar da guda².
Daga kasuwa suka biya gidansu Rabi'ah sun jima sosai acan kafin daga can suka wuce gidansu Ma'aruf, qarshe suka yada zango gidansu Aishatun sai dare Ma'aruf yazo ya tafi dasu gida.

Rahma yadda suke samun kulawa da yaranta abin ba'a cewa komai ita kanta tayi mulmul sai kewar soyayyar Abienta ke d'awainiya da ita, sabida bakinsa da ita sai gaisuwa Jaddatu da Ummu Adnan suke kula da ita yaran kuwa likitoci bakinsu da ita susha nono.
Ahaka Jaddatu tayi qoqarin sake shirya Rahma ta mata gyara sosai a asibitin dan tasan Ana sakinsu ba saurara mata Abie zai ba.
Abie ya qara bud'e makarutun boko da islamiyya, sadaka da manyan masalllatai biyu da sunan 'ya'yansa, an kammala ginin asibitin Rahma an zuba makaita k'wararrun likitoci, Abie ya soke karatun Rahma ya ce baya buqata ba magnar idan yaranta sunyi wayo taci gaba.
Sadaka kamar yadda ya Saba duk juma'a k'ofar gidansa acike take har gobe hakane baya fashi hakan ba qaramin d'aukakasa ya qara yiba.

Yau 'diyan Rahma suka cika wata uku cif yau aka sallamesu daga hospital idan kaga murna wajan Rahma da Abie abin baya fad'uwa.
idan kunga yadda Abdulwahab wanda suke kiransa da Dady UmmulAymana kuwa da Mamy suke kiranta masha Allah idan ka kallesu sai ka kuma bazaka tab'a cewa bakwain ne ba sunyi wani irin girma da wayo gasu da dariya Dady kuwa akwai shan yatsa.

Ibtisma ma ayau suka iso Chad Ja'afar yaje ya kawosu, masha Allah ita da 'danta sunyi wani irin girma yaron tamkar yakai wata hud'u katone sosai ga shi baida kuka.

Tinda suka iso taba Ja'afar Rafael ya kaisa gidan Baba Tsalha ita kuma ta shiga gyaran gidanta kafin yamma tsaf ta gyara ko ina ta d'aura musu girki.

Ibtisam ta fito daga wanka d'aure da towel take jiyo kukan Rafael, murmushi tai ta ce“Ai kam yaron nan yayi qoqari ai kam da ya bari naje.�

Qaran bud'e k'ofa taji ta waigo,tana goge jikinta da qaramin towel.
Idanu suka had'a da J'afar ya shigo d'akin yana rungume da Rafael, yana tsala kuka.
Dariya tai tana fad'in.
“Mon Amour haka ake reno? Ka wani matse yaro.�
Wani irin kallo mai cike da so da sha'awa da k'auna yake aika mata.

Fari tai da idanu tana d'aga masa gira.
Da sassarfa ya qaraso wajanta ya had'asu da yaron ya manne aqirjinsa.
D'an qara tai tana kallonsa.
Gira ya d'ga mata ya ce“Kinci bashi zuwa dare, oya basa abincinsa.�
Amsarsa tai tana zama gefen gado ta fara shayar da yaron ashagawab'e ta ce.
“Mon amour yaushe zamu je gaishe da da Baba Tsalha da Jaddatu daga can nagano auntie Rahma?�
“Zuwa gobe insha Allahu, yau sai kin biya bashi.�
Ya k'arashe mgnar yana sumbatar wuyanta yana shafa fuskarta.
Dariya kawai take masa ganin yadda ya wani sakata gaba yana matsata ita dai yaronta take shayarwa.

Rahma tinda sukazo gida tai wanka ta shirya cikin riga da skirt na material tayi wani irin kyau tamkar Dady da Mamy ba daga tsatsonta suka fito ba.
Zaune suke a babban falon tana kallon yadda aka sake canza komai na falon, Merrah na wasa da Many tana b'angala dariya, Dady kuwa na wajan Jaddatu ta Hana kowa d'aukanta yaron baya gundurata.

Abie ne ya shigo yana waya.
Idanu suka taurawa juna shi da Rahma.
Kai ta langwab'ar tana tutturo masa bakinta, da idanu tana take masa magana.
Murmushi mai taushi ya sakar mata, yana d'aga mata gira ya qaraso falon ya nufi wajan Mamy tana harba k'afafu ya sunkuya ya amsheta hannun Meerah yana murmushi ya sumabceta ya ce“Aymana wayo koh?�
Meerah tai dariya ta ce.
“Masha Allah kamar sunyi wata hud'u ko biyar.�
Murmushi yay ya nufi wajan Jaddatu ya zauna, yana kallon Dady yanajin tsananin k'aunar yaran har cikin jininsa.

“Ok Mustapah karka wani damu komai zaiyi daidai insha Allah, ngd ok bye zuwa jibi inada meeting a mexico da na dawo za'a San abunyi.�
Jaddatu ta ce“Allah ya qara rufa maka asiri ya mama albarka.�
Rungumeta yay ita da Dady ya amsa da.
“Ameen Ummina.�
Ya k'arashe mgnar yana kallon Rahma wacce ta shagwab'e fuska tana kallon Mamy na harbe-harbenta, Meerah na mata wasa.
Miqewa Rahma tai irin tayi fushi Abie yaqi mata mgna ta haura sama.
Jaddatu ta ce.
“Takwara ina zaki? kije da Aymana ki bata Tasha, kinji doctor ya ce kar abarsu suna jin yunwa naga baki basu mono ba tinda mukazo madaran ma basu shaba sosai.�
Rahma ta dawo ta zauna ta ce.
“Ummi da kwanciya zanyi kaina naji yana ciwo kad'an.�
Abie danne dariyarsa yay yasan k'arya take fushi tai.
Jaddatu ta ce.
“Subahanallahi sannu to ki shayar dasu ki barsu sai kije ki kwanta, Abdul d'auko mata magani.�
Rahma ta mashi Mamy ta fara shayar da ita.
Yarinyar tana Sha tana kallon Rahma k'urrr Rahma ahankali ta ce.
“Mamana kallo koh?�
Karaf akunnen Abie.

Tana shayar dasu ta barsu ta haye sama bedroom d'insu wacce basa Iya rabawa ita da Abie ta shiga ta Mirza key tai kwanciyarta tanajinsa yazo taqi bud'ewa Abie abun dariya ya basa shi ssam baiga abinda ya mata ba Har dare Rahma fushi take da Abie,
Bayan yaran sunyi bacci Rahma kwantar da kowane saman gadonsa taje tai wanka ta shiyar cikin wasu irn kayan bacci masu masifar kyau, tana wani irin k'amshi.

Abie na falo zaune waya yake yana Danna laptop.
Wani irin qamshinta ya daki hancisa yay saurin d'ago da kansa ya kalleta.
Kai ta d'auke tana turo baki, sai wani irin taku takeyi jikinta ko ina motsawa yakeyi kayan jikinta na bacci basuda maraba da tsirara, gabansa tazo ta gifta tana qoqarin nufar hanyar fita.
Da sauri Abie ya miqe yana fad'in.
“Hamza! Wani uzuri

Please Login or Register in order to submit comment