Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inason kiyi breakfast yanzu bari kawai na koma gidan tinda bakya son naje hospital 'din.�
Cikin farin ciki ta kamo hannunsa ta ce“Allah Habibyna¿�
Gira ya 'daga mata ya miqe tsaye yana miqar da ita murmushi 'dauke kan fuskarsu.
Tsawa sukaji Jaddatu ta daka musu.
“Sakar mata hannun dan ashatar uwaka, wannan wace irin masiface ta kinno mana kai? Amatsayinka na bahaushe, hausar ma ba'ki kakeson yarinyar mu, harda koya mata ta'ba jiki tsabar masifa da jarabar da kake son koya mata, daman ba'kar fata akwai nacewa jar fata, toh wlh Rahma tafi 'karfinka, saketa dan babanka munafukin yaro, kaga wannan 'katuntakar ina yarinya 'karama mai shekaru 18 zata iya kwasar wannan masifar.�
Ta qarasa mgnar tana nufosa da sanda.
Ja'afar ya saki hannun Rahma ransa amugun 'bace yay hanyar fita yana zura hanunsa cikin aljihun wandonsa, ya tsani wulaqance bai 'kaunar azagi asalinsa ko jansinsa.
Jaddatu wani irin muggun kwarjini Ja'afar ya mata yadda ya ha'de fuska ya nufo hanyar da take shirin isa wajansa kansa tsaye babu alamar tsoro a fuskaraa, takunsa yake tsaf yadda ya Saba tamkar 'dan wani sarki.
Jaddatu hakan ya sake harzuqata ta qara sauri ta nufosa tana fa'din.
“Shin kai 'dan uban waye anan 'kasar Tchad da har zaka shigo mana gida ka rungumemin jikata, bayan ina mgna ba alamar ban haquri kake nuna min kai d'in jinin sarautane....¿�
Raham ganin da gaske Jaddatu zata bugawa Ja'afar sandar hannunta aka 'kawatata da kwalliya kusan rabinta azurface.
Da gudu ta iso gaban Jaddatu wacce zata sauke masa sanda jikinsa,ta saurin shigewa jikin Ja'afar wanda yake quqrin kauceta kar wannan mur'de'diyar sandar ta sauka jikinta, amman ina tuni Jaddatu ta sauke sandar akan Rahma wacce ta saki gigitaccan 'kara sbd azabar da ta ratsa tsakiya kanta. Sai ga jini, ihu Ummu Adnan ta saki ganin Rahma jini na zuba kamar an yanka (zakara) ko (kaza) idanunta suna lumshewa, ta yi luuu jikin Ja'afar wanda ya rungomata, ya shiga jijjigata, ya kira sunanta da mugun 'karfi “Rahmerh nah!� Yana watsama Jaddatu wani irin mugun kallon da yasaka Jaddatu sakin sandar hannunta........

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/17/22, 19:21 - Buhainat: ```D A```

```31&32```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

_Assalamu alaikum._
_Don Allah kuyi hkr, wlh uzurine ya riqeni kwana biyu shiyasa kukaji shiru Ngd�._

Sosai kallon da Ja'afar yake jifan Jaddatu da shi, ya bata mugun tsoro Wanda hakan ya sakata sakin sandar, gabanta na mugun fa'duwa ganin Rahma kanta na zubar da jini, hankalinta yay mugun ta shi ta saki kuka tana qarasowa wajan tana 'fadin.
“Latifa ce Yahaya ya fito da mota muje hospital. Na tsaneka mugun yaro kana neman ruguza mana rayuwar farin cikin mu zuwa baqin ciki.
Ja'afar ya ciro handkerchief, daga aljihun wandonsa ya rabasa biyu jikinsa na rawa ya 'daurama Rahma kanta daidai wajan da jini yake fita.
“Cikin 'bacin rai ya ce“Karki kuskura ki ta'bata, bayan kin mata illa, me zaki ce? Zan iya komai akan Qalbina.�
Ya 'karashe mgnar yana sunkutar Rahma wadda ta jima asume ya fice da ita cikin zafin zuciya yake tafiya, yabar falon.
Jaddatu ta fashe da kuka tai zaman 'yan bori atsakiyar falon, tana fa'din.“Ummu Adnan maza ki sanar da securities kar abarsa ya fita da ita daga gidan.�

Ummu Adnan cikin jimamin abinda da yake faruwa,ta fice da gudu tabi bayan Latifa, dan isar da saqon.
amman tana fita compound 'din gidan taga Ja'afar yaja motar da speed, yana zuba horn megadi ya bu'de masa ya fice.
Latifa ta hango ta fa'dawa Yahaya direba saqon Jaddatu ta juyo tana dawowa.
Ummu Adnan ta iso ta kama hannun Jaddatu ta ce.
“Kiyi hkr muje ciki ya tafi da ita asibiti.�
Jaddatu tsabar takaici ya hanata mgna, ta miqe suka fito.

Rainatu da take la'be bayan window kaf komai agabanta ya faru, tin bayan shigarsu Jaddatu falon ta tintsire da dariya, tana fa'din.
“Kowa yaci tuwo dani miya yasha, wlh duk sai na tarwatsa rayuwarku na mallake Abdul Majeed ni 'daya.�
Ta 'karashe mgnar tana dialing 'din number Abie.
Tana ta ringing bai 'daga ba, har kusan sau biyar kafin ya 'daga, bai ce mata komai ba.
Kukan kissa ta saki tana fa'din.
“Abien umminmu don girman Allah ka gaggauta aurama Ummi yaron nan sbd zasu iya rasa rayuwarsu su na son junansu sosai, ga Ummi babba tasaka su agaba, harda dukan Rahma ga ta can ya 'dauke a mota sun nufi hospital dan Allah ka ban izinin bin bayansu.�
Ta 'karashe cikin wani irin kuka.
Abie ya miqe tsaye hankalinsa atashe ya ce “What? Wane asibitin?�
Dai dai lokacin yaga Ja'afar da nurses an wuce da Rahma saman gadon 'daukar marasa lfy, an nufi wata 'kofa da ita.
Da'bas ya zauna ya 'kurama Ja'afar manyan fararen idanunsa masu matuqar haske da lumshewa amman lokaci 'daya sun riki'de sunyi jajir, bai iya furta komai ba banda bakinsa da yake motsawa alamar sunan Allah yake Kira.
Abie2 ne ya miqe da sauri ya kalli Ja'afar hankalinsa a tashe ya ce“Me ya sameta Ja'afar yaushe kaje gida muna nan?�
Ja'afar ya kalli Abie 2 ba kowani 'dar ya zayyane masa abinda ya faru.
Baba Tsalha ya kalli Ja'afar takaici ya cikasa ganin irin cin amanar da yay Wa Ibtisam.
Harisu da Yahuza ma kasa masa mgna sukayi bare Abie 1.
Ja'afar ya matso kusan Baba Tsalha ya ce“Baba dan Allah ina Ibtisam take? Fatan bataji ciwo dayawa ba?�
Ba wanda ya tankasa ko kallon arzi'ki bai ishasu ba.
Abie 1 ne ya ha'diye wani yawu me masifar 'daci bayan ya jajirce wajan tattaro dukkan nutsuwarsa,ya Kira shi.
“Ja'afar! zo zauna.�
Zauwa ya yi ya zauna kusan Abie hankalinsa duk atashe, kallo 'daya zaka masa kasan baida wani sukuni acikin rayuwarsa.
Hannunsa ya kama ya riqe ya kafeshi da ido ya kasa mgna.
Abie 2 ya dafe kan Ja'afar ya 'kura masa idanu yana qara nazarta wasu a'amura masu girman gaske.
Kallon Baba Tsalha yay ya ce“Wannan fa ayanzu bazaku ta'ba iya fahimtarsa ba, abu 'dayane addu'a itace zamu musu ahannu suke Wallahi duk abinda yake baisan me yake ba.�
Baba Tsalha ya ce“
Ban gane me kake nufi ba?�
Zayyane musu komai yay. Ja'afar ya mi'ke ya isa 'kofar room 'din da aka shiga da Rahma ya tsaya ransa a'bace jin ana cewa jinnu garesu kawai dan kar a aura musu juna.

Raiyana jin Abie ya 'kyale baice komai ba, ya saka tai shiru, ta katse kiran cike da farin ciki ta nufi 'bangaransu.
Jaddatu ta share hawayen fuskarta ta ce“Hanan ta shi muje asibitin nasan wane hali Rahma take ciki.
Ya Allah ka kawo mana 'dauki cikin gaggawa.�
Hanan ta Kira Abie taji ko Rahma nan hospital 'din da suke.
“Eh�
Ka 'dai ya iya cewa.
kama hannun Iman ta ce“Muje wannan masifar Allah ka kawo mana 'karshenta idan da saka hannun wasu magautan ne ya Allah ka toni asirinsu ka Hana kowaye kwanciyar hankali.�
Ummu Adnan da Latifa suka amsa da “Ameee.�
Rayyana aranta ta ce.
“Ba Amin ba.
Azahiri ta amsa da “Ameen muje hospital mugani wannan yaron kawai a aura masa Ummi ko ma samu kwanciyar hankali.�
Wani mugun kallo Jaddatu ta mata ta ce.
“insha Allahu bazata auresa ba Rahma nada mijinta wlh lokaci ya yi yanzu ko Rahma na aman jini bazamu aura mata jansin da ba namuba, bayan hakan zuciyarta da wanda take so yake sonta bazamu aura masa ita ba.�
Rayyana jin abinda Jaddatu ta ce, ta zazzaro idanunta gabanta na fa'duwa ta ce“Ayyah! Ummi bansan tanada wanda take so ba amman yana wace 'kasa?�
Kai tsaye Jaddatu ta ce“ Morocco. �
Wani yawu Rayyana ta ha'de tana wani irin nazari me yasa tin farko bata tsaya taji kan abu ba taje ta ha'da wannan qazamar soyayya wacce take ganin gaba 'daya lamarin kamar sam baiyi ba.
Murmushin 'boye tai tana canza shawara akan zataje wajan malam ta ce awarware lamarin sai a ha'data da wancan ya 'dauketa subar qasar ma zatafi nutsuwa Inda bata ganinta.
Su uku suka nufi asibitin.

Tsaitsaye suke abakin 'kofar room 'din da aka kwantar da Rahma.
Dr Salis ne ya fito tare da wata nurse.
Abie da Ja'afar rigai² tambayar Dr.
“Dr ya jikin nata?�
Dr Salis ya ce“Alhmdllh! Ta farfa'do daman taji tsoro sosai ne lokacin da taji an buga mata kome meye akanta, shine yay nasara 'dauke numfashin mun tsayar da jinin, wajan bai kai 'dinki ba an mata dressing.�
Abie ya ce“Zamu iya ganinta?�
“Eh muje.�
Kai tsaye Dr Salis ya fa'da.
Dukkansu suka nufi room.
Rahma na zaune tana hawaye tana kiran Ja'afar.
Da sassarfa ya isa wajanta yana fa'din.
Na'am Qalbina ga ni sannu ya jikin?�
Ya 'karashe mgnar yana zama dab da ita, ya kamo hannunta yana jera mata sannu, ya shafa wajan da aka mata dressing.
Wa ni irin murmushi take sakar masa ganinsa akusanta ta kwantar da kanta 'kirjinsa tana sauke numfashi.
Abie 1 sandarewa yay atsaye ya kasa ma isa wajan idanunsa dishi-dishi suke gani.
Ganin hakan Abie2 ya kamasa suka fito nan 'kofar room 'din
Yayin da Baba Tsalha dasu Yahuza sukayi mutiwar tsaye wajan.
Abie 2 nutsuwarsa ya tattaro waje 'daya yana kallon Abie 1 ya ce.
“Pls ka nutsu na maka alqawalin zanyi iya qoqarina na rabasu da wannan masifar da aka ha'dasu da ita.�
Abie 1 ya saki murmushi mai ciwo yana fa'din.
“ba wai ina 'kin lamarin bane, A'a ina duba wasu lamurane wanda bayan bikin idan sun dawo hayyacinsu zai biyo baya, ba wai lallai su so juna ba, nasan wace ce ummina, shima wannan yaron tabbas yana son yarinyar nan da na bige amota, me kakeji idan ya dawo hayyacinsa bayan na aura masa ummina? Wlh itace abin tausayi duk da bansan gaibu ba, bazan so asako min ita ba wannan shine abin da zai iya buga zuciyata na mutu.�
Abie 2 ya shiga lalla'bashi da nuna masa hakan ma bazata faru ba.
“Yanzu mu nuna musu zamu aura musu juna dan su nutsu na tabbata kafin lokacin insha Allahu 'kullin da aka musu zai warware.�
Kai Abie 1 ya jinjina suka koma ciki.
Abie idanunsa ya runtse ganin Rahma ta lafe 'kirjin Ja'afar.
Abie 2 ya ce“Daga yau idan kuka sake ko ta'ba hannun juna bazamu aura muku juna ba, Ku Saki juna sai bayan aure�
Rahma ta matsa da sauri tana ha'de hannayenta alamun ta tuba.
Baba Tsalha dasu Harisu 'kwarai sun shaida Ja'afar baya hayyacin sa, sanin waye Ja'afar 'din.
Rahma ta kalli Abienta ta shagwa'be tana beqa masa hannunta tana fa'din.
“Abiena mutafi gida kaga Jaddatu ta buga min sanda.“
'Kayataccan murmushi ya qaqalo, yana kamo hannunta ya kalli Ja'afar ya ce“Karka damu na baka aurenta amman sai kun nutsu kun daina riqe hannun juna ok?�
Ja'afar cikin murna ya ce“Wallahi Abie mun daina muna godiya.�
Dr Salis ya sake duba kan Rahma ya ce“Bata wata matsala, ga maganin da zaku siya mata ta Sha shi kenan zaku iya tafiya tinda waccan baiwar Allah bata buqatar mai jinya sai bayan ta farfa'do, ahi kuma mai taxi yanada iyalinsa kusa da shi ana kulawa da shi.�
Abie ya ce“Alhmdllh! Zan basu dukkan wata kulawa na 'dauki nauyin iyalinsa ci da sha da komai har sai ya warke ras na saka ayo masa order 'din sabuwar taxi.�
Dr ya jinjinawa dattakun Abdul Majeed sosai.
Ja'afar ya amshi takardar da aka rubuta sunan maganin ya fice da rawar jiki.
Rahma ta visa da kallon so tana murmushi.
A harbar asibitin suka ha'du dasu Jaddatu suka nufi gida wanda Rahma ko kallo Jaddatu bata isheta ba.
Har su Baba Tsalha sukazo gidansu Rahma wanda suka gigice da ganin makeken gidan da tsaruwarsa kamar a'kasar larabawa.
basu ta'ba saka ran ko amafarki zasu ta'ba shiga irin gidan ba.
Falon Abie 2 aka zazzauna baki 'daya.
Abie 1 yay gyaran murya ya ce“Ummi don Allah karki tayar da hankalinki akan wannan lamarin kinga halin da kika saka Ummi, ni bazan qi aura masa ita ba, abinda nakeji shine bayan sihirin ya sakesu ba lallai su zauna da juna wanda hakan tamkar nine aka nakasa bayan nan ga baiwar Allah can kwance wanda bamu san lokacin farkawarta bare musan matsalar kuma itace zabinsa, kawai mu dage da addu'a insha Allahu ba abinda ya gagari Allah, idan mun fa'dawa Allah al'amura basu sauya ba kenan aurensu shine alkhairi sai muga iyayansa ayi komai itama waccan zan fita da ita waje bayan ta warke zamu roqe iyayanta su aura masa ita sabida itace za'binsa.�
Dogon numfashi yaja ya kalli Ja'afar ya ce“Me sunan wacce yarinya?�
Ja'afar ya ce“Ibtisam.�
Rahma ta hararesa tana turo baki gaba.
Da idanu ya bata hkr.
Kanta ta 'dauke ta mi'ke tana fa'din “Wallahi banson kishiya Habibyna.“
Ta fice aguje tana sakin kuka.
Ja'afar ya miqe jikinsa na rawa.
Abie ya ce“Idan ka bita zan hanaka aurenta fa!“
Cak ya tsaya, yana runtse manyan idanunsa wanda suka riki'de, zuciyar shi na masa 'kuna.
Abee ya ce“Ban number mahaifin Ibtisam, da ta mahaifinka.�
Ja'afar ya ciro wayarsa daga aljihun ya duba ya fito da ita ya shiga zayyanawa Abie yana 'dauka ya saving, ya sanya wayar cikin aljihun gaban rigarsa ya ce“Kuje insha Allahu komai zai dawo normal.�
Baba Tsalha godiya sukayi suka miqe.
Jaddatu ta ce“Allah ka tsinewa wanda ya ha'da wannan masifar Allah ya saukar masa da aya cikin gaggawa ya tozarta shi fiye da yadda ya tozarta mu.�
Abie miqewa yay ya Kama hannun Jaddatu suka nufi ciki.
Raiyana hankalinta atashe yake, ta Kira malam bata samunsa bare ta masa bayani, ta kira Wahida bata gari tayi tafiya.
Rahma sama ta haye ta fa'da saman bed 'dinta ta saki kuka mai ciwo.
Abie sai da ya kwantarma Jaddatu hankali shi da Hanan, kafin ya haye sama.
Wanka yay ya sanya wasu fararen kaya na shan iska ya nufi wajan Rahma.
Kwance take ta na'de cikintattausan bargo tana kuka marar sauti.
Tin daga falonta yake jin kukanta wanda yake masifar masa ciwo har can 'kasan zuciyarsa.
Bedroom 'din ya shige, ya nufi 'katon Royal bed 'din Nata ya nufa ya zauna bakin gadon ya janye bargon ya sanya santala-santalan hannunsa ya janyota ya zaunar da ita dab da shi har suna shaqo numfashin junansu, ya 'dago fuskarta ya matso da fuskarshi dab da tata, ya sauke mata wani irin 'dumamenman numfashi mai fitar wani irin 'kamshi, ya kirata cikin taushin murya.
“Baby ummina!�
Kallonsa tai ido cikin ido tana lumshe 'kananun kyawawan idanunta masu lumshewa.
Ta zum'buro bakinta gaba ashagwa'be ta ce“Abiena fushi Rahma take ka hanata za'binta.�
Ahankali ya 'Dora bakinsa saman goshinta ya sumbata ya kashe mata ido 'daya dab da kunnenta ya ce“Karki damu nasan abinda kika fi so aduniya rasa shi zai miki illa, zan baki abinda kikeso ok Baby?�
Cikin farin ciki ta fa'ada jikinsa ta qamqameshi tana dariyar farin ciki, ta 'dago ta kamo fuskarshi da dukkan tafin hannunta ta fara kissing 'din kumatunsa zuwa goshinsa hancinsa.
Da sauri ya janyeta ya riqe hannunta yana mata wata wani irin sihirtaccan kallon da ya sakata runtse idanunta tana riqe kafa'dunsa cikin sanyin murya ta ce“Abiena kaina ciwo bacci kaji.�
Wajan da aka mata dressing yay kissing ya kwantar da ita ya miqe ya 'dauko bottol 'din water ya 'ballo magani ya zauna ya 'dago kanta dab da kunnenta ya ce“Pls Baby banson musu karki bu'de idanunki haaaaaa zan baki sweet abaki ok?�
Rahma langwa'be kai tai, ashagwa'be ta ce“Abiena duk lokacin da kace sweet ba sweet bane magani ne wollah.�
Sumbatar hancinta yay da ha'barta yana shafa 'dan cm'karamin bakinta jajir irin nasa, ya ce“Oya haaaa Abie zai baki sweet, idan ba haka ba bazan aura miki Ja'afar ba.�
Cikin rawar jiki ta damqe hannunsa bakin ta bu'de ya jefa mata maganin ya 'dora mata gorar ruwan.
Anutse take shan ruwan, tana ha'de maganin ya jan ya kwantar da ita ya lulu'beta, ya mata ra'da.
“Oya Baby ummina bacci.�
Zaune yake yana shafa kanta hannunsu sarqe da juna har bacci ya 'dauke.
Zare hannunsa yay, ya rage mata gudun Ac ya miqe ya fice yana rufe mata 'kofar bedroom ya rufe ta falo ya sauko.

Rayyana tana hayowa sama shi yana sauka zaije zasuyi mgna da Jaddatu.
Kallonsa tai tana kamo hannunsa taji 'kamshi Rahma na tashi ajikinsa.
Wani 'katon abu taji ya tokareta a 'kahon zuciya, baqin ciki ya sauka azuciyarta, amman tuna 'yarsa ce sai ta 'danji sauqi.
Wani kallo ya watsa mata da ido ya tambayeta lafiya?
Raiyana susucewa tai ta shige jikinsa tana sauke numfashi ta ce“Wlh ina sonka Abien Ummi.�
“Hummm kinsan wani abu?
Da sauri ta 'dago ta kalleshi gabanta na fa'duwa.
Zan fa'da miki ba yau ba.�
Ya 'karaahe mgnar yana janyeta gefe ya 'karasa sauka ya barta sake da baki.

Ja'afar bayan sun tafi gida hankalinsa ya kwanta sosai jin za'a basa Rahma da Ibtisam. Baba Tsalha ya amsa nasiya sosai duk da yasan baya hayyacinsa.
Motar Ma'aruf ya shiga ya mayar masa.
A farfajiyar ya iskoshi tare da wasu baqi bayan sun gaisa ya basa key ya tafiyarsa.
Ma'aruf sheqe da dariya ya kalli Habu ya ce“Sauran qiris na gama da Tchad. �
Habu ya ce“Har yanzu kana nan da qudirin Rahma Abdul Mjeed 'din?�
“Yes yes Habu.�
“Ok Allah ya temaka.�
Ma'aruf zaiyi mgna yaga Kira ya 'daga ya miqe ya shige flowers.

Kafin zuwa dare duk wasu manyan malamai da Abie ya Sani suke mutunci harda wanda yanar gizo ne ya ha'dasu irin su (Twitter Facebook Instagram telegram) duk ya musu bayanin abinda yake faruwa da roqon su tayasa addu'a akan A ya karya al'kadarin abin.
Kuma kowanen su ya aika masa ma'kuddan ku'di sabida sun ce sauka za'ayi sau 3 koma meye sai ya karye da izinin Allah.
Abie 2 ma can tsakiyar dare yay shiri mai kyau cikin fararen kaya ya fara ibada yana fa'dawa Mahaliccinsa buqatarsa yana kuka akan ya tarwatsa wannan sihiri da yake jikin bayainsa.
*Bayan kwana 6*

Maa Sha Allah dubun al'aumma ne suka dage wajan saukar Qur'ani mai girma akan lamarin Rahma da Ja'afar.
Wanda su kuma suna gefe sunata kwasar love 'dinsu ta waya idan yazo gidan kuma hira Abie 2 na tsakiyarsu har su gama ya tafi.
Rayyana ta gigice da jin mgnar da Malam yay akan idan zai karya sihirin nan dole sai ya yi tarayya da ita, idan ba haka ba jinnu kanta zazu dawo, kuma ba mamaki hauka zasu sakata mafi muni, sai ta za'ba wanda hakan ya yi mugun d'agaren hankalinta dan bata ta'ba zina ba bata fatan yinta kuma, hakan ya saka ta shiga tsaka mai wuya, sabida batada wata mafita bayan ta bari a aurama Ja'afar Rahma can su qarata ba ruwanta, ita Rahmar ce kawai batason gani kusa da mijinta.
Hakan ya saka ta 'dan sakawa kanta nutsuwa, ta fara Jan Rahma ajikinta, yadda Abien zai 'dan sassauta mata ya saurareta ta samu wai matsayi azuciyr sa duk da tasan baya sonta auranta kawai yay.
Can Niger ba qaramin gigicewa Tanko da Malam Adamu sukayi ba jin Ibtisam na Tchad.
Abie ya aika musu wadataccan ku'di ya ce su taho akwai mahimmiyar mgnar da zasu yi, ba 'bata lokaci suka shiru suka nufo Tchad ba tare da sun fa'dawa matansu gaskiya su na son sai sunga abinda yake faruwa.
Ai kuwa sun tardo tashin hankali halin da Ibtisam take ciki da soyayyar da Rahma da Ja'afar suke, wanda ya 'daga hankalinsu, sai da Abie 2 ya musu bayani kafin su samu sasaaucin 'Kunar zuciyar,amman duk da haka Malam Adamu ko gaisuwar Ja'afar baya amsawa sbd ha'intarsa da yay cewa baisan Inda Ibtisma take ba bayan tana wajansa.
Gidan Abie suke zaune jiran tsammanin farfa'dowar Ibtisam, sun samu kulawa ta musamman wajan Abie sosai sunyi mamakin karamci irin na Abien.

Rahma tsaye gaban dressing mirror, Raiyana na gyara mata uban tulin gashinta, wanda yake fitar da wani irin 'kamshi, sai 'kyalli yake.
Sanye cikin da wata irin doguwar Riga, Ash kala taji adon sequence stones, masu azabar kyau suna fitar da 'kyalli.
Wata sarkace sirirya ta gold a wuyanta wani irin azababban kyau ta yi.
Fuskarta sai wani irin annuri take.
Rayyana ta kame gashin dukkansa da band ta saki jelar tsakiyar bayanta.
Cikin siririyar murya ta ce“Ammi Ngd da yadda kike 'kaunata da Ja'afar na matsu ayi bikinmu mu wuce Espagne, naci gaba da karatuna ga shi hutuna ya 'kare kusan dati 'daya kenan.�
Ta 'karashe mhgnar tana ka'da 'kananun idanunta, masu matuqar kyau. Raiyana cikin murna ta ce “Daughter karki damu insha Allahu za ki samu abinda kike so zan tsaya muku.�
Rungumeta Rahma tai tana godiya.
“Yanzu dai ki 'karasa kimtsawa kafin Habibynki ya iso, bari naje na saka Latifa ta shirya masa abin motsa baki, kubi asannu surukanku na gidan banda rashin kunya fa'din kalaman soyayya a gabansu.�
Raham ta langwa'bar da kanta gefe ta ce“Ammi ai munada kunya fa!�
Dariya sukayi Raiyana ta fito ranta fass.

Tana bu'de 'kofar falo zata fito tai karo da Abie zai shigo.
Sanye yake da wani shegen yadi coffee brown, 'dinki yay masa masifar kyau, wani irin fitinannan kyau yay ga 'kamshinsa na musamman mai da'di na tashi ajikinsa.
Wani malalacin kallo ya watsa mata ya ra'bata zai shiga ciki ta ri'ko hannusa tana marerece fuska ta ce“Tana shiryawa ba kayan 'kwarai ajikinta.
Wani malalacin murmushi ya sakar mata wanda ya kusa tafiya da dukkan numfashinta kawai ta zube jikinsa.
Da sauri ya janye jikinsa Hannunta ya kama suka koma 'bangaransa.
Fuskantarta yay ya ce“Idan Baby Rahmerh ta dawo hayyacinta ta auri abinda take so zan dawo gareki na fuskanci zamanmu amman yanzu pls ki ban lokaci banda nutsuwa, duk wanda yay wannan abun yana ga kamar hakan sauqi ne toh shine babban kuskuren da yay acikin rayuwarsa, sannan matsalar da zai shiga arayuwarsa wlh babu ranar fitarsa,ni ban d'aukar fansa akan dukkan abinda ake min, amman lamari idan ya shafi Baby ummina banda da'di sam ta wannan fannin bana yafiya.�

Raiyana ta kalleshi ta fashe da kuka ta ce“Wato zargina kake ko me? Na rantse da girman Allah Abdulmajid idan nasan wani abun akan matsalar Ummi qarama Allah ubangiji ya.....�.cikin zafin nama ya 'dora tafin hannunsa saman bakinta
ya zaro manyan narkakkun idanunsa yana kallonta ya mata wani kallon sai da taji zata shi'de masa, ya Saki 'kayataccan murmushi ya janye hannunsa da sauri ya matsa gefe ya zura hannayensa cikin aljihun wandonsa ya 'dage gira 'daya yace“Mata kenan. Yaja dogon numfashi ya nuna mata yatsarsa alamar ta fice.
Cikin rawar jiki ta fice sabida yadda yake ladabtar da ita da narkakkun idanunsa.
Wayarsa ta 'dauki ringing.
Ganin Dr Salis ya saka gabansa mummunan fa'duwa, ya saita kansa yay masa sallama.
Dr Salis ya amsa ha'di da furta..........
*'Yar ajin tubarkallah💃�*



_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/24/22, 16:50 - Buhainat: ```D A```

```35&36```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

Dr Salis ya miqe tsaye ya na kallonta ya ce“Zakiyya lfy? Me ke faruwa?�
Ya tambayeta Cikin ru'duna yana sake bin hannunta da kallo.
Sake nuna masa hanyar take, cike da tsoron halin da ta ga Ibtisam aciki.
“Dr yarinyar nan wacce take room 10 wlh ta farka abin ya motsa....�
Bai jira ta 'karasa mgnar ba, ya kwasa aguje, suka biyo bayansa.
Nurses ukune kanta tsaye suna qoqarin sake mata allura, hakan ya gagara sabida masifar 'karfin da ta nuna sai fizge² take tana kai musu duka, tana wawurasu da cizo, duk ta birkice idanunta.
Dr Salis ya qaraso dab dasu ya ce“Ku dakata! Wa ya saku sake mata allura?�
Ibtisam jin mgnar yasa ta 'dago kanta tana zazzaro idanunta tana musu wani irin kallo, ta kwaikwaiyi mgnar Dr Salis ta shiga jifansu.
Tanko yana ganin halin da 'yarsa take ciki, ya nufi wajanta yana sakin kuka.
Abie yay saurin riqo shi ya na fa'din “Astagfirullah! Haka ta koma Dr?�
Ibtisam ta kalli Abie ta ce “Astagfirullah haka ta koma Dr?�
Abie ya dafe goshinsa.
Yay saurin sakin Tanko shi da Malam Adamu kusan tare su ka isa bakin gadon, nurses na rirriqeta, asannu sbd 'dorin hannunta da 'kafarta.
Dr Salis cikin wayo da daraba dakyar ya mata allura da zata kashe mata sassan jikinta, bazata iya kokowa ba ko jefe jefe.
Curewa tai waje 'daya tana binsu da kallo, yadda Abie yake kwaranto mata addu'a yana tofa mata tsakiyar kanta.
Bakin Abie take kallo yadda yake motsawa, sannu ahankali.
Itama ta shiga motsa bakinta bata me zatace ba kawai dai kwakwayonsa take.
Ganin batada 'karfin kokowa ya saka suka zazzauna bakin gadon.
Tanko ya riqo hannunta yana fa'din.
“Ibtisam nine babanki kin ganeni kuwa?�
Fizge hannunta tai tana hararansa ta saki dariya tana kwaikwayon mgnar sa.
Abie ya kamo hannunta ya ce“Toh ni fa kin ganeni?�
Cikin kasala ta kalleshi ta ce.
“Toh nifa kin ganeni?�
Tana kallo hannunsa ta fara qoqarin zare zoben hannunsa, na diamond sai 'kyalli yake.
Janyewa yay ta fashe da kuka tana qara ruqumqume hannunsa.
Dr ya

Please Login or Register in order to submit comment