Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya iso wajanta ya Kama hannunta ya zaunar da ita bakin gadon ya shiga goge mata jikinta da qaramin towel yana qoqarin shafa mata mai ta riqeshi tana kuka.
“Don Allah ka rabu dani bana so zan shafa hakan haramun kakeyi.“
Bai kulata ba ya juya mata baya ta shafa man ta 'dauki kayan ta saka ta yafa mayafin ta sanyan takalmi ta ce.
“Muje na gama ka sadani da iyayena.�
Shiru tai tana murgu'da baki ganin yadda ya tsare gida.
“Zo zauna kici abinci muje su miki bayani da Kansu.
“Zatayi mgna ya 'dora yatsa bakinsa.
Ya kamo hannunta.
Dan karta 'bata masa lokaci ya shiga bata abaki, fafur taqi ci sai da ya zaro mata idanu.
Sosai ta sha tea 'din taci farfesun hufzah 'daya taci.
Da kansa ya goge mata bakinta da tissue ya kwashe kayan yakai kitchen ya dawo.
Miqar da ita yay ya riqo 'kugunta yana mata sahihin kallo.
Baki ta zum'buro gaba tana qoqarin cire hannunsa ajikinta.
Sumbatar wuyanta yay wanda saida taji wani yamm.
Akunne ya ra'da mata.
“Ja'afar 'dinki kika tsana um?�
Kuka ta sanya masa tana 'daga kai alamar Eh.
Murmushi yay mai tsada ya goge mata fuskarta ya kama hannunta suka fito.
Ibrisam kusan ru'dewa tai ganin falon duk sai ta qara tsorata tana qamqame jikinta ta ce“Kawai na mutum wlh siyar dani kayi.�
Dariya yay marar sauri ganin falon ba kowa shiru yay saurin sumbatar la'bbanta ya zaunar da ita saman sofa ya kunna Tv ya zauna nesa da ita.

Abie fitowarsa daga wanka kenan ya ji wayarsa na neman agaji.
Abraham ya gani ya amsa kiran.
Cikin mutuntawa suka gaisa yana tambayarsa.
“Abraham! Baby ummina ta tafi ne?�
Cikin girmamawa daga can ya amsa, da.
“Eh Yalla'bai ai anfi awa....�
Nan ya zayyanewa Abie dukkan abubuwan da suka faru ya 'dora da cewa.
“Har an sallame shi ya tafi yana godiya da alkhairin ka gare shi.�
Abie ya shafi kwantaccan gashin 'kirjinsa wanda yake baqi qirin, ya furta.
“Alhmdllh! Amman banji da'din tonon asirin nan ba gaban jama'a, Allah ya kyauta ya qara mata lafiya, Abraham zan fita meeting zan kira ka insha Allah.�
Sallama sukayi.
Agaggauce ya shirya sabida zai gana da wasu baqi zasuyi meeting.
Tsaf ya shirya cikin suit Green sun masa masifar kyau, sai baza qamshi yake.
Kira akaro na 4 ya shigo.
Goshinsa ya dafe ya isa wajan wayar.
Sunan Jaddatu 'baro² yana yawo akan screen 'din wayar, ya rubuta *Sweet Ummina.*
Da sauri yay picking call 'din.
Da sallama ya fara yana gaisheta.
Daga can yaji Hanan tana fa'din.
Don Allah Ummina karki fa'damasa ki tayar masa da hankali bari ya dawo.�
“Ke! Hanan wlh xan cin miki mutunci fa! Sai na fa'da ban fiki son 'Dana ba ni na haifi abina duk wanda zai so bayana ne. Wa'alaiki salam Abdul kana jina?�
Abie yay gyaran murya wanda Jaddatun ta ankare.
Cikin nutsuwa ya gaisheta yana fa'din “Ummina don Allah ki kwantar da hankalinki nasan komai daman karki damu idan na dawo za'asan abun yi.�
Jaddatu daga can ta ce“Abdul so nake wai da su kwashi tsunmakaran kayansu subar mana gidanmu.�
“No! Ummina abari har na dawo har yanzu ita d'in zaman mata take gareni insha Allah idan nazo zakiga irin hukuncin da zan yanke.�
Sosai ya kwantar mata da hankali jin ta fara kuka tana fa'din ta rasa me yawa mata kowace idan ta Shigo shi da Rahma suke son ganin bayansu.�
Dakyar ya samu ta bar kukan ya shiga bata labarin irin temakon da ajani yama Ja'afar akan Ibtisam.
Toh sai ta manta wacan mgnar ta shiga mamakin lamarin daga nan ta basa Hanan suka gaisa.
Can falo kuwa Tanko ne ya fito kamar amafarki ya ga Ibtisam tsaf cikin shiri zaune tana kuka qasa².
Tanko ya kirata.
“Ibtisam!�
Aguje ta isa wajan mahaifinta ta qamqameshi tana sakin rikitaccan kuka, tana fa'din “Don Allah Baba kayi hkr na tuba ku yafemin kuskuran da nayi na guduwa na barku da damuwa.�
Janta ya yi suka zauna.
Lallashinta ya shiga yi yana tambayarta da jikinta me takeji yanzu?
Laraba ce jin muryar 'yarta ta fito aguje tana kiranta “Ibtisam!�
Rungume juna sukayi suna kuka.
Abinda ya janyo hankalin Abie ya fito.
Cike da farin ciki yake fa'din.
“Ma Sha Allah Ibtisam an farka Alhmdllh sannu ya jikin?�
Sai lokacin ta waigo tana kallonsa.
Tinda take arayuwarta zata iya rantsuwa da Allah bata ta'ba ganin namiji mai kyawunsa da cikar zatinsa ba, ga shi balarabe kyakkaywar fuskarsa mai zagaye da saja ga wata 'kazumba mai kyau, ga gemu mai 'dan tsayi, doguwar fuskar shi wacce ta 'dan saka fa'di ka'dan 'dauke take da manyan idanu farare masu lumshewa,da siririn hanci mai tsayi, sai 'dan 'karamin bakinsa jajir kamar na jariri. Dogone sosai mai cikar zati ga faffa'dan 'kirji, duk da ya fara manyanta amman tamkar ayanzu ne yake cikin zamaninsa sbd kyawun jiki ga jin da'di wanda yake bayyane afatar jikinsa.
Aranta take ta yabonsa haka tana mamakin daman za'a iya samun namijin da ya kere Ja'afar dinta akomai?
Idanu ta tsira masa babu ko 'kiftawa.
Abie yay saurin janye idanunsa cikin nata aransa yana fa'din wannan kallon na 'kauyanci fa? kamar wata halitta kiga gani.� duk acikin zuciyarsa yake mgnar.

Sam Abie bai fiye son kallo ba.
Tanko ya ce “Ibtisma bakya jin Ana miki mgna ne?�
Firgigit tai tana sadda kanta ta gaishesa.
“Ina yini?�
Tana mamakin ya akayi ya iya hausa duk da taji hausar ba rass bace.
Abie ya amsa yana tambayarta da jiki.
Ja'afar wani irin haushinta yaji akan yadda ya ga ta qure Abir da idanu.
Ja'afar ya sake gaishe da Abie.
Zama Abie yay yana amsawa cikin sakin fuska yana fa'din.
“Ja'afar barka da arziqi Allah ya qara tsarewa, bari na dawo daga meeting sai muje a qara duba lafiyarta idan ba wata matsala kawai sai mu juya gida idan kun huta kwana biyu.�
Ya qarashe mgnar yana sauke numfashi yana kallon wayarsa kira na shigowa.
Bai 'daga ba.
Gyaran murya yay ya ce“Yauwa Shamsu sai kama yarinya bayani yadda zata fahimta.�
Tanko ya gyara zama yana amsawa da “Toh Alhaji.
Ya fuskanci Ibtisam, ya mata bayanin dukkan abubuwan da suka faru har aurenta da Ja'afar.
Ya 'karashe mgnar da fa'din.
“Dan haka banson sake jin wata fitina daga gareki ki amshi aurensa da hannu biyu, daman sbd shi kika fito Allah ya yi daman can shine mijinki dan haka karki 'kullace shi ba yin kansa bane.�
Ibtisam ta fashe da kuka tana fa'din.
“Baba ni fa wlh tin ranar da na kamashi yana waya da wata yana fa'da mata maganganun soyayya naji ya ficemin araina, ni ba shi nake so ba araba auren kawai...�
Bakinta Tanko ya buge mata ya daka mata tsawa “Tashi kiban waje shashar banza marar hankali.�
Miqewa tai tana kuka ta kalli Abie wanda kansa yake ak'asa yana tura wani saqo a email, yana mgna ahankali.
“Please Shamsu abita hankali yarinya ga batada lafiya, ayai hkr insha Allah zasu daidaita da mijinta.�
Sautin kukan ta qara tana diddira 'kafafunta, ta ce “Don Allah balarabe kace su raba auren bana so wlh har zuciya pls ka temaka min kaji balarabe na roqe dan Allah.�
Abie yay saurin 'dagowa ya kalleta ya girgiza kansa ya ce“Ja'afar kamata don Allah kuje ka lallasheta.�
Da gudu ta bar wajan Laraba ta miqe tana fa'din “Don Allah ku duba lamarin nan fa yarinyar nan da gaske take.�
Tsawar da Tanko ya mata ne yasa ta bi bayan 'yarta tana harare-harare.
Ja'afar wanda ya dafe kansan da tafin hannunsa yana runtse idanunsa zuciyarsa na wani irin zafi tamkar zata faso 'kirjinsa ta fito jijiyoyin kansa sunyi wani irin ra'do-ra'do.
Ransa ya yi masifar 'baci wanda kallo 'daya zaka masa kasan kalaman Ibtisam da na uwarta sunyi mugun baqanta masa rai, wai ta daina sonsa ba shi take so ba toh wa take so?
Abie ganin halin 'bacin ran da Ja'afar ya shiga ya saka shi dafa kafa'darsa ya ce“Kayi hkr don Allah komai zaiyi daidai karka fito da fushinka akanta ka cije ka jata jikinka kana lalla'bata zata sauko kishine yake damumta wlh tana sonka.�
Ja'afar ya ce“Abie na gode ba fushi nake ba mamaki nake. �
Tanko ya ce“Kayi hkr dan Allah idan dai nine ubanta wlh bata isa ta sakani jin kunya akaro na biyu ba, ka Saki ranka Ja'afar ban Sanka da bayyana fushinka ba 'boye shi don Allah.�

Kansa ya sadda yana murmushi sbd kalaman Tanko.
Abie ya miqe yana fa'din lokacin sallah ya gabato zan fita sai na dawo zamuje hospital, don Allah idan an kammala girki kuci ku qoshi.�
Sallama sukayi Abie ya fita.
Securities tsaitsaye a compound 'din gidan, kowa da bindiga ahannunsa tamkar gidan gwamna.
(Gaskiya Abie babban mutum ne)
Cikin mutunci suka gaisa aka bu'de masa wata shegiyar baqar mota ya shige suka fice daga gidan, yana amsa waya.

Laraba na can tana lallashin Ibtisam akan ta kwantar da hanlinta dole Ja'afar sai ya saketa tinda bata sonsa. jin hakan ya saka ta daina kukan, Abie kawai yake mata gizo shi kawai take gani yana mata murmushi, duk wani gefen tana jin Ja'afar aranta.

Tanko da Ja'afar su na zaune suna mgna sama² kowa ransa ba da'di.
Lokacin sallah yana yi Tanko ya shiga ya koro Ibtisam tana kuka ta nufi 'dakin.
Tsaye ta iskosa yana fesa turare zai tafi masallacin da yake jin ana shirin tayar da sallah.
Baki ta zumb'uro tana gunguni.
Kallon arziqi bai mata ba, ya sanya kansa ya fice cikin takunsa na 'kasaita.
Tsaki taja ta nufi toilet 'din.

Yamma liqis jirginsu Rahma ya sauka a 'kasar Espanol, cikin babban birninsu (Madrid) .
Direbanta tare da masu tsaron lafiyarta sukazo tarbarta.
Sanye take cikin wata dark blue din abaya wacce taci uban adon stones, ta yane kanta da mayafin rigar tana sanye da baqin glass wanda ya qarama farar kyakkyawar fuskarta kyau.
Wani shegen rufaffan takalmi ne blue aqafarta wanda ya mata kyau matuqa, tana rataya da handbag 'dinta ta fara saukowa daga matattakar jirgin, tana jin wani irin farin ciki na ratsata.
Cikin harshen larabci cikin siririyar muryata mai da'di ta 'daga hannayenta tana fa'din.
“I miss you Espanol na dawo Alhamdllh Allah.�
Kai tsaye wajan kayanta ta nufa bayan ta kammala duk abinda ya dace taja babbar trolley 'dinta ta nufi wajan da tasan ana jiranta.
Tsaitsaye ta iskosu, Aslim na riqe da wata farar babbar takarda mai kauri an rubuta *Welcome Rahmatullahi Abdulmajid Abdulwahab.*
Kyakkyawan murmushi tai musu ta 'daga musu hannu alamar ta gode, sbd daman ita dai ba gwanar mgna bace, hirata Abie sai Jaddatu Hanan su Ummita 'yan Morocco sai Anee Rafeeq ma ba wani mgna take masa ba sai katari.
Mota suka bu'de mata ta shige suka rufe, aka sanya trolleyn ta both, direba da securities biyu na kusansa haka suka bar airport 'din.

*Gabon*
Aishatu ahalin da ta samu Ma'aruf yasa tai shiru bata tanka masa ba, ta kwanta gefensa, haka suka kasance har kwana biyun Ma'aruf bai wata nutsuwa ko walwala.
'Bangaran Rabi'ah ta dage da 'karfi sai Ma'aruf ya sota ya aureta har ta shiga bin malamai.
Zaune suke anata kiran wayarsa yaqi 'dauka.
Aishatu ta ce“Dan Allah ka 'dauka bakasan alherin da yake cikin kiran ba...�
Tsawa ya buga mata yana fa'din.
“Uban wa yace miki alkhairine?�
Idanu ta zazzaro jin ya zageta.
Wani kiran ya kuma shigowa.
Cikin fusata ya 'daga kiran yana fa'din.
“Dan kutumar uban uwar babanka Inusa karka sake kirana agidana...�
Daga can aka katse ko me aka ce masa ya miqe tsaye yana fa'din.
“What?�......

_💃�'Yar Ajin Ma Sha Allah🥰_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/5/22, 18:19 - Buhainat: ```D A```

```51&52``

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

Ficewa yay daga cikin falon yana kirta ruwan masifa.
“Wai me kake fa'da ne haka? Ba nace adakatar da komai ba, har na nemeku? Toh dan kutumar ubanku ku mayar da kayan muhallinsu, tare da kiyaye dokokina wlh idan aka samu akasi! Hummm! Adakatar da komai nace bana buqatar komai me yasa ba kwaji ne? Na ce mgnar Rahma abarta,ta kowa ma�
Ya 'kare mgnar cikin 'daga murya yana huci. Ko me aka ce masa ya sauke ajiyar zuciya, yana fa'din.
“Ok nima ina tafe jiya naso zuwa akwai dalilin da ya tsayar dani.�
Bayan sun gama wayar, ya kira wata number, bugu 'daya aka 'daga ya ce.
“Duk na tsayar da komai asakesu cikin sirri.� cike da bada umarni yay mgnar yana katse wayan, zai koma ciki sai ga kiran Rabi'ah.
Tsaki yaja ya kashe wayar baki 'daya.
Inda ya barta nan ya iskota zaune ta yi tagumi.
Zama yay ya rungumota jikinsa yana shafa cikinta, ha'di da kissing 'din wuyanta.
Kuka ta sakar masa tana fa'din.
“Ma'aruf yau ni kake zagi ko?�
Matseta yay yana fa'din.
“No! Masoyiyata wlh aharzuqe nake bake na zaga ba kiyi hkr, bakisan halin da nake ciki bane, idan na zageki iyayena na zaga tinda ni dake abu 'dayane.�
Zatayi mgna wayarta ta 'dauki ringing.
Ganin Rabi'ah jikinta na rawa ta 'daga kiran.
Ma'aruf yaja tsaki yana fa'di.
“Kibi asannu makashinka na tare da kai!� baki ta saki tana kallonsa ha'di da amsa wayar.
“Hello 'kawata ykk? Kwana biyu kin 'buya?�
Daga can Rabi'ah ta ce.
“Uhmm! Bari kawai, y bbyna? Hope kina lfy? Ke 'daya ce nazo yanzu?�
Aishatu ta kalli Ma'aruf wanda idanunsa suke rufe ya miqe saman sofa ta ce“A'a ogan na kusa idan ya fita zan kiraki ko kuma ma kizo ai baida matsala.�
Rabi'ah tai kicin² rai 'bace ta ce“No! Ki barshi kawai sai anjima.�
'Kitt ta kashe kiran.
Aishatu tai dariya ta ce“Au yau 'yan kunyar ne da naga kina zuwa idan yana nan.�
Ta 'karashe mgnar tana ajiye wayar.
Ma'aruf ya ce“Bakida wayo sai duniya ta koya miki hankali.“
Ashagwa'be ta kwanto jikinsa tana sakin kukan takaicin kasancewar shi 'dan kidnapping da safaran mata.
“Dan Allah karki qaramin zafi kiyi shiru me ya faru? Cikin kuka ta ce“Damuwarka nakeson sani?�
Kai ya girgiza aransa yana fa'din.
“Kwanciyar auren mu da duk wani abu da zan miki na kyautatawa, da akasin hakan, sai kin shelawa duniya bare wannan gagarumin lamari.
(Haba Ma'aruf wa ya ce maka Aishatu bata san sirrinka ba?😂)
“Ni ba abinda yake damuna ki tayani da addu'a kawai.�
Kai ta girgiza ta Kama hannunsa suka shiga daga ciki, sosai ta jiyar da shi da'di marar misaltuwa sbd sun jima basu ha'duba. Bayan sunyi wanka sun nutsu suka shirya suka bar gidan zuwa yawo duk 'ko'karinta na son ta ga ta cire masa damuwarsa.
Rabi'ah kuwa sai kai komo take ranta 'bace wulaqancin da Ma'aruf yake mata, takaicinta asirin da ta masa har yanzu shiru bai kamasa ba, Malam ya ce da kansa zai kawo kasan kirane zasu masa.

*Tchad*
Raiyana tajima sosai tana baccin na ban mamaki kafin ta farka.
Da idanu take bin 'dakin da kallo, 'dakin baqi na 'kasa.
Idanunta ya sauka akan auntie Saro wacce ta rafka uban tagumi, hawaye na zabu akan fuskarta.
Raiyana ta zabura tana fa'din.
“Aumtie Saro lafiya? Me nake a'dakin saukar baqi? Me ya faru dani?
Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Shi kenan wani abin ya sameni ko auntie Saro?�
Cike da jin haushinta da 'kyamar halinta, auntie Saro ta ce.
“Tirr da halinki Raiyana iyayanmu basu bamu gur'batacciyar tarbiya ba, me kika nema kika rasa aduniya agidan bawan Allahn nan, da har kika yarda kika fa'da halaka, kike son nakasa masa rayuwar 'yarsa 'kwaya 'daya? Ashe duk yadda nake baki shawara baki 'dauka ba? Kika shiga bin bokaya da 'yan tsubbu, kina sa'bon Allah kina shirka kawai dan ki 'batawa Rahma rayuwa.
Shin me ta miki ne? Ai yanzu wa gariya ya waya, ke samun namiji irin wannan ba abin alfaharinki bane...�
Raiyana ta fashe da kuka tana 'Dora hannunta akai tana zazzaro idanunta ta ce.
“Na shiga ukuna! Wa ya lanqayamin sharrin wannan?�
Saro cike da takaici ta ce“Aljannu da kika tura musu suka dawo kanki...�
Kakaf ta bata labari.
Raiyana kanta ta saddda cike da kunya tana kuka tana fa'din.
“Kaicona da rayuwata Abien Rahma da kansa ya nemomin magani na warke? Allah sarki na zalumci kaina amman auntie Saro ba laifi na bane wlh kishin Rahma nake duk da tana 'yarsa natsani kulawar da yake bata, ina sinsa kamar na ha'diye shi, kulawar da yake bata, wlh tana min ciwo sosai, shiyasa nayi hakan dan na nisantasu ni banyi dan na cutar da ita ba...�
Auntie Saro ta ce“Humm! Mamaki ai cutarwa ta nawa kuma Raiyana ka gama mutum da baqin aljani kace baka cutar da shi ba?�
Raiyana ta fashe da kuka tana fa'din.
“Yanzu kowa yasan abinda nayi kenan? Wayyo Allah na! Na cuci kaina da rayuwata, auntie Saro ya sakeni ko? Wlh mutuwa zanyi ku tayani basa hkr.�
“Ni ban saniba wannan sai ki jira shi, yazo baya 'kasar kije ke kika sani dan kin gama cutar da kanki, ni kinga zan tafi tinda kinji sauqi, bazan iya da kayan kunya ba, Allah ya jisehemu alkhairi.�
Auntie Saro ta miqe ta shiga ha'da kayanta.
Raiyana tai tagumi tana kallonta har ta gama ta kalleta ta ce“Ni zan tafi.�
Raiyana ta miqe tana 'dauka hijabin da ta gani gefen gado ta saka jikinta ba 'kwari ta ce“Bari nazo.�
Fitowa tai.
Jaddatu suna zaune ita da Hanan Iman na game awayar Hanan suka ga Raiyana tana nufosu.
Jaddatu kallo 'daya ta mata ta 'dauke kanta, tana karka'da sanda.
Raiyana jiki ba kwari cike da kunya ta zube tana gaida Jaddatu.
Ada'kile ta amsa, ba tare da ta kalleta ba. Hanan ta ce“Masha Allah Raiyana ya jikin? Sannu Allah ya qara sauqi.�
Raiyana kanta a'kasa ta amsa.
“Da sauqi Amin Ngd.�
Miqewa tai ta haura sama Jaddatu na binta da harara.
Hanan ta ce“Don Allah Ummi ba ruwanki ki saka musu ido ita da Ya Abdul.�
Tsaki Jaddatu ta ja batace komai ba, ta maida hankalinta kallon Tv tashar Aljazeera.
Raiyana 'dakinta take bi da kallo ya fara 'yar 'kura alamun kenan ta kwan biyu akwan? Hawayen fuskarta ta share ta kwaso sabulu da turare da mayuka da ku'di da turaman atamfa biyu ta sauko.
Jaddau na binta da kallo bata tanka ba.
Auntie Saro taqi kar'ba ba yadda Raiyana batayi ba, ta ce“Ko ya kike ke jinina ce ba dan ki biyani ba nayi jinyarki na tafi Allah yasa hakan ya zama darasin Rayuwa agareki Allah yasa kin shiryu, yanzu kin gane Wahida ba 'kawar arziqi bace.�
Tana gama mgnar ta fice.
Sallama ta wa su Jaddatu ta tafiyarta.
Raiyana tana kuka wiwi ta gyara 'dakin tsaf ko ina ta sanya turare ta kwashi kayanta ta nufi sama, tana cikin tashin hankali da mugun tsoron tararrabi take bata san irin hukucin da Abie zai 'dauka akanta ba.

*Espanol*
Wani tamfatsetsan gidane na gani na fa'da, wanda aka ha'da jin da'din duniya, gidan ya ha'du matuqa wanda yake mallakin Rahma a'kasar ta Espanol, Abie ya Gina mata tin lokacin da ta za'bi 'kasar da zatayi karatu, sbd baida burin ta zauna amakaranta ko Kama gidan haya duk irin arziqin da Allah yay masa.
Dole idan mutum yaga tsarin gidan ya burge shi tsabar kyau, ya 'kayatu da shuke².
Falon yanada girma sosai yasha kayan alatu, tamkar gidan amarya ba 'yar makaranta ba.
'Dakuna kwana ukune manya biyu d'auke da manya gadaje na zamani irin na turawa, sai 'dayan wanda ba komai cikinsa sai katifa da carpet da Tv gefen kitchen yake, nan Meerah mai aikin Rahma take, biyun kuwa sai abin wani corridor ake zuwa ajere 'daya na kallon 'daya tsayawa fa'din tsaruwar 'dakaunan da kujerun ciki da sauran abubuwa 'bata lokacine.
Suna isa gida Rahma ta fito ta nufi hanyar falonta.
Meearh ta gyara ko ina sai 'kamshi yake tai mata dadda'dan girki sosai suka gaisa cikin mutunci, tana ma Rahma sannu da zuwa da jan trolley bakin 'kofa wacce direbanta ya shigo mata da ita.
Rahma tai murmusa lokacin da shiga 'dakin ta ga komai agyara ta murmusa ta ce“Thank you Meerah.�
Kai ta jinjina ta ce“Ayi wanka azo aci abinci pls.“
Kai Rahma ta 'daga ta wuce ciki ta fara fatali da kayan jikinta ta 'dauki remote ta kunna Ac ta nufi bathroom.
Ruwan 'dumi ta ha'da sosai, tai wanka ta jima kafin ta fito 'daure da towel, kyakkyawan jikinta mai kyan surah na 'digar da ruwa, sanyin Ac sosai yake ratsata.
Amman bata wanke gashinta ba dan da safe katin tafiya ta wanke shi.
Saloli ta rama ta shirya ta fito falon ta 'dan ci girkin da Meerah ta mata, ta dawo falon ta kunna Tv plasma.
Ta zauna tana latsa waya zata kira Jaddatu, sai taga message 'din Abie.
Murmushi mai kyau kan fuskarta ta shiga wajan message 'din.
_“Hello Babyna ykk hope kina lfy kin iso lfy? I miss you muahhhhh sai na kiraki ina busy bye🥰._
Cikin murna ta shiga mayar masa da amsa.
_“Alhmdllh lfy nazo, A'a banida lfy Abie rashin ka ya saka min kasala inata kewarka, Abie rabin raina pls ina jiranka jibin Allah ni kuka zanyi tayi naqi cin abinci idan baka zoba.😢_

Tana tura masa ta kirasa tana ringing ba'a 'daga ba, sai taji wani iri.
Ranta ba da'di ta kira Jaddatu suka Sha hira.
Kiran Anee ya shigo wayarta ta 'dauka tana lumshe idanunta asanyaye ta ce.
“Habibty Anee ykk?
Daga can Anee tai tsalle ta dire tana murna ta ce“ina lfy barkan ki da zuwa Habibty, wlh tin 'dazu Rafeek yake damuna yana son ya ganki ya takura min da kira sai munzo.�
Rahma ta saki sansanyen murmushi tana dafe goshinta ta ce“Uhmm! Ni wlh Anee acikin ru'du nake shiyasa ban basa fuska, sbd gudun abinda zaije yazo, shiyasa nake baya² amman bari Abie yazo zanyi qoqarin masa tambaya cikin nutsuwa idan na tabbatar da mgnar gaskiyace ba zai yuba naci gaba da kulashi, duk da daman sama² ne nake kulashin, sbd kar na zurma dayawa na dawo na cutu.�
Anee ta ce “Me yake faruwa? Ko dai mgnar ce akan kinada aure?�
Rahma ta numfasa ta ce.
“Eh ita fa! wlh, dan Abie wannan Karon ma ya tunatar dani.�
Anee ta ce “Wlh nafi jin wayo yake miki dan ki tsaya kiyi karatu, karki fara soyayya, amman nawa kike da har za'ace kinada miji da 'da'dewa.�
Rahma ta numfasa ta ce“Eh hakan nima nafi zargi, amman ki rabu da shi gobe zamu ha'du a makaranta...�

*Australia*
Abie sai kusan magarib ya samu ya dawo gida, wanka yay suka tafi masallaci su uku, basu dawo ba sai bayan isha'i.
Laraba da Ibtisam zaune atsakar 'daki.
Laraba ta ce“Ince dai babu abinda ya miki?�
Ibtisam ta zaro ido tana girgiza kanta ta ce,“Tabb abinda sai wani shan 'kamshi yake min, wai dan nace ban sonsa, wlh Anna yaban haushi wai ke kinga ranan, yadda yake mata kalaman soyayya ko tsoron Allah baya ji, na baro ku na gudu naje wajansa sbd son da nake masa na tsakani da Allah. Anzo an lanqayawa aljannu qarya hummm!�
Laraba ta ce“Ai maganinki kenan ba yau nake ganemiki baqin yaron bazai yi wani abun arziqi ba, amman kika nace wa gari ya waya ga shi yanzu an 'daura aure, toh ke da ubanki wa kikeso yanzu?“
Ibtisam ta zum'buro baki gaba tana rau-rau da idanu ta ce“Ni wlh wannan babban balaraban wanda ya kawomu Allah Anna bakiji yadda nakeji ba akansa sai naji ashema Ja'afar abaya banso shi ba...�
Wani irin bugu taji abakinta sai da ya fashe jini take ya fara bin gefen bakinta.
Ibtisam kuka take sosai tana 'boyewa bayan Laraba, wadda ita kanta ta gama tsorata da lamarin Tanko.
Cikin zafin rai ya ce“Laraba na rantse da Allah idan kika kasowa Ibtisam aurenta aranar zan sakeki karki ce ban gayamaki ba, kiji kuma tsoron Allah adukkan lamarunki, wlh idan kika tunzura yarinyar nan tai abinda Ja'afar ya saketa bani ba ita bake ke na yafe wlh wlh wlh kinji na rantse sau uku na fita daga rayuwarku har abadan idan kinaga barazana nake bismillah Laraba zaki san waye Shamsuddin. ke agidan uban wa kika ta'ba ganin anyi hakan? Kinada miji kice kina son wani? Wanin wanda mafarkinki ma bazai kai can ba, ke ko tsoron Allah bakyaji Ni za ki wulaqanta? Wato duk bayanin da aka miki baki gamsu ba?�
Ibtisam ta shiga gorgiza kanta tana kuka tana ha'de hannayenta.
Laraba sosai tsoron ganin yadda Tanko ya koma lokaci 'kalilan.
Masifa yake sosai kamar ya Ari baki yana 'Kara musu kashedi, daga 'karshe ya ce“Ku tashi Ku ban waje idan kunga dama kuci abinci idan baku ganiba ku kuka sani ke Ibtisam daga nan har mutafi karki sake shigomin 'daki ki zauna wajan mijinki.�
Cikin rawar baki ta amsa da“Toh Baba.�
Suka fice sumi-sumi.

Zaune Abie yake saman sofa ya lume yana waya murmushi 'dauke saman kyakkyawar fuskar shi.
Yana sanye da wani yadi mai shegen kyau da tsada fari 'kal, 'dinki ya amshe kyakkyawan jikinsa.
“No! Ummiterh wlh sam yau ban zauna ba, yanzu haka hospital zamuje nayi waya da Dr za'a duba yarinyar, koda Baby ban samu nayi waya ba naga kiranta nasan akwai rigima yau ni da ita.�
Abie ya 'karashe mgnar yana 'yar dariya ya beqa hannunsa ya 'dauki cup glass me 'dauke da coffee zai kai bakinsa karaf idanunsa suka sauka akan Ibtisam da ta qureshi da idanunta tana matsar 'kwala tana goge gefen bakinta yana fitar da jini.
Idanunsa ya janye yana mamkin

Please Login or Register in order to submit comment