Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta wuce sumsum batayi mgma ba tai shirin bacci, tai kwanciyarta kusan Jaddatu.
Jaddatu ta ce“Zanga ta imda zaku sake ha'duwa tinda ke sakaryace, ina gyaraki kina zuwa yana lalubeki koh?�
Rahma ta runtse idanunta, aranta tana fad'in.
“Innalillahi! Abie ka jamin ya zanyi? Ashe ban masa zance Abie 2 da Meerah ba.�
Hanan dariya kawai take abinta, Rahma kuwa ta cure waje 'daya kamar ruwa ya cinyeta.

Abie kuwa ransa fess ya kwanta, ba jimawa bacci ya 'daukesa, sbd tashin da yake so ya yi na cikin dare.

★★★★★★
*Bayan kwana 5*

Niger
Duk tsayin kwanakin nan Ja'afar bai sake kusantar Ibtisam ba, yana kulawa da ita, sosai har ta warke ras ganin bai sake neman komai wajanta ba, ta saki jikinta da shi, sbd yadda yake bata kulawa, ga yanayin yadda yake romantic nata, bai wuce iyaka sai ta Fara rage tunanin Abie Sam yanzu bai dameta ba kamar da, datake wuni tana tunaninsa.
Tsaye yake a 'kofar falo cikin shirinsa mai k'ayatarwa, 'kananun kaya jikinsa ya yi masifar kyau, sai baza 'kamshi yake, yana amsa waya.
“Eh Abie insha Allah gobe muke tasowa.�
Daga chan Abie Wanda yake harabar asibitin Rahma, ya amsa da.
“Ok Ja'afar Allah ya kawoku lfy, an shirya komai agidanku, insha Allah idan kazo kahuta sai muyi mgnar aikin ka, tinda kace bazaka cigaba da karatu ba!�
Cike da girmamawa Ja'afar ya ce.
“Ok Abie insha Allah Ngd Allah ya qara rufa maka asiri, sai munzo.�
Abie ya amsa da “Ameen ya Allah Ja'afar.�
Katse kiran Ja'afar yay bayan ya masa sallama, ya kalli qofar jin takun Ibtisam.
Sanye take cikin wani danqarere lace, amman ba wai me ku'di dayawaba daidai wadaida ne, baqine me adon pink ya Mata kyau sosai 'dinki Riga da zani.
Idanu suka ha'da tai saurin kauda kanta, tana murmushi qasa², ganin yadda yake kallonta kamar zai lasheta, amman ya wani waske yana shan 'kamshi.
Dab da shi ta tsaya kamar zata shige jikinsa, ta 'dan kalleshi ta ce“Mon amour na shirya.�
Hancita yaja, ya matsota jikinsa, ya rankwafo, dab da fuskarta, ya 'dago kanta bai tsaya wani batuba ya ha'de bakinsu ya sumbaceta, tare da tsotsar harshenta.
Ibtisam ta zare bakinta ashagwa'be ta ce.
“Don Allah muje kaji.�
Da yake miskilan na kusa bai sake mgna ba, ya Kama hannunta suka fito ya rufe qofar falon, suka tafi.
Keke napep suka hau.
Tafe suke acikin keke napep, Ja'afar yana latsa wayarsa, message suke da wani abokin Haroun.
Kallonsa Ibtisam tai ta ce“Mon amour ina zamu fara zuwa?�
Kallon yay ya shafi sajansa ya ce.
“Uhmm! Gidanmu mn, daga Chan sai ki wuce da dare zanje na kawoki.�
Hannunsa ta kamo tana wasa da yatsun hannun tana murmushi.
Kallonta kawai yake, yadda ta dawo Ibtisam d'insa ta da.
Murmushi yay aransa ya ce“Mon cœur anji maza anyi hankali.
A 'kofar gidan Mal Adamu keke napep ta ajiyesu, Ja'afar ya biyasa ku'dinsa suka shiga.
Acikin soron qofar Ibtisam ta riqe hannun Ja'afar tana sunne kanta, ta ce“Mon Amour inajin kunyar Inna wlh.�
'Yar dariya yay, ya rungumota ya ce“Tabbas dole kiji kunyarta 'danta kin Nuna bakya sonsa, yanzu kuma ya kaiki duniya ta daban kin dawo haiyacinki...�
Da sauri ta sanya hannunta ta rufe masa baki, tana narai² da idanu ta ce“Please Mon amour za'a gamun muje.�
Fuskarta ya shafa ya saketa tai saurin yin gaba, cike da kunyar irin yadda yake nuna mata tsantsar 'kauna, tin Randa suka zama abu d'aya.

Inna Hansatu mai waina, suna zazzaune a rumfa tsakar gida, anata hira hankalinta wajan lissafain ku'din wainarta, taji sallamar Ja'afar da Ibtisam.
Deluwa ta amsa sallamar cikin sakin tana fad'in.
“Sannunku da zuwa kune da rana tsakiya?�
Ja'afar ya ce“Eh wlh umma mun fito sallama ne.�
Inna ta ce“Au ashe gobene tafiya Allah sarki baqin buzuna.�
Ibtisam ta tsuguna tana gaishesu cikin girmamawa.
Inna ta amsa fuska sake tana bata hannunta, ta qarasa ta zauna kusanta cike da jin nauyinta.
Maimou ta ce“Ya Ja'afar kamar nabiku, auntie Ibtisam ko nazo mu tafi ne?�

Ibtisam kanta 'kasa ta murmusa ta ce“Eh Maimou.�
Ja'afar ya ce“Ina wasa dakene?�
Inna ta ce“Maida wuqar yayarta take tsokana ah toh.�
Deluwa tai dariya ta ce“A'a fa kinsan halin Maimuna idan ta samu zuwan yi zatayi.�
Ja'afar ya miqe ya ce.

“Bari naje wajan Baaba na dawo, sai ki tafi Chan gidan.�

Ibrisam kanta a 'kasa ta amsa da.
“Toh�
Inna ta ce“Kaga kuwa abincinsa can yanzu za'a kai, jeka da shi.�
Ja'afar ya amsa da.

“Toh innah.�

Yana fita innah ta miqe da kanta ta zuboma Ibti abinci, dakyar tai hannu biyu sbd tsabar kunya da takeji, Maimou na janta da hira.
Sai kusan qarfe uku Ja'afar yazo ya rakata gidansu, daga can ya shiga sabgogin shi tare dasu Harisu dan tare zasu koma.

Laraba tinda Ibtisam tazo da kallo take binta, ganin cikin kwanaki 6 ta yi kyau tsaf abinta, fatarta taqara murjewa, kamar ma ta yi 'kiba haka take gani.

Taslim tai dariya tana kallon Laraba ta ce“Kai Anna sai kallon Auntie Ibti kikeyi halan ta canza ne?�
Aydha tai tsalaf ta ce“Eh wlh ta yi kyau abinta.�
Ibtisam ta zabga Mata harara ta ce“Ni ban son baqin surutu fa! Wai nayi kyau.�
Laraba ta ce“Wlh sai yau da naganki hankalina ya kwanta, kinga yadda kika sauya kuwa? Allah ya qara Baku zaman lfy da kwanciyar hankali, dan Allah Ibtiam ki kwantar da hankalinki, kibi mijinki sau da 'kafa, kinga 'kasar wasu zakuje banda iskancin nan da kika tsira na baya ni dai wlh ba ruwana.�
Ibtisma ta zumb'uro baki gaba ta ce.
“Anna ki daina tunamin wlh tallahi ba yin kaina bane alokacin, kuma ai komai ya wuce insha Allahu zanma roqeshi gafara, da zaran mun isa lafiya.�
Ta 'karasa mgnar tana goge hawayen da suka silalo kan fuskarta.
Taslim ta ce“Ai wlh auntie kinyi dacen miji dan Allah Ku zauna lfy kinji?�
Ibti tai murmushi ita kunya ma takeji sbd Taslim ta fita hangen nesa.
“Anna bari naje gidan Dadda na dawo.“
“Toh ki gaisheta Karime kuwa jibi zata tafi kije kuyi sallama.�
Tanko ne ya shigo bakinsa d'auke da sallama.
Ibtisam ta miqe aguje ta tarbesa tana rungumesa cikin murna ta ce“Baba nayi kewarka dayawa.�
Tanko ya saki baki da hanci yana kallon Ibtisam, da gaske yaga tayi kyau sosai harda 'yar 'kiba ma.
Hannunta ya kamo yana washe baki.
“Kai masha Allah Ibtin babanta naji dad'in ganinki haka sosai Allah ya qara muku zaman lafiya, ince dai ba matsa masa kikayi ba, akan ya kawoki ba koh?�
Tana maqale da hamnunsa ta ce“A'a Baba, wlh shi ya ce muzo muyi bankwana gobe zamu tafi Tchad. �
Kai masha Allah, naji dad'i Allah ya Baku zaman lfy ya kaiku lfy, dan Allah ki nutsu kisan bautar Allah kikaje yi, sannan dan Allah karki jamana abin kunya bake ba bawan Allah nan kinga kinada auren wani akanki, kiji tsoron Allah aduk Inda kike ki tuna idan bakya ganinsa shi yana ganki.�

Ibtisam ta ce“Wallahi Baba na muku alqawali ba bainda zai faru sai alkahiri, insha Allah. �
Tanko ya ce“Alhmdllh naji dad'i sosai Allah ya miki albarka, ya albarkaci aurenku.�
Laraba ta amsa da
“Ameen ya Allah. �
Ibtisam bayan iyayanta sun gama mata nasha mai shiga jiki ita da Aydah da Taslim suka tafi gidan Dadda domin mata sallama.

Ja'afar sai kusan 9 na dare suka tafi gidansu, bayan sunyi sallama da dukkan 'yan Uwa da abokanan arzik'i.
Su na isa gida suka fara shirin tafiya dan gidan bus zasu kwana 'karfe 4 na asuba bus d'insu zata tashi zuwa damagaram.
Bayan sun gama dukkan shirinsu sukayi wanna suka shirya.
Ja'afar ya kalli Ibtisam na hamma.
Hannunta ya kamo yana murzawa ya ce“Muje toh ai zakiyi bacci a can.�
Langwab'ewa tai ajikinsa ta ce“Ai ba wani bacci hayaniya ta yi yawa awajan Mon Amour.�
Murmushi yay iya labb'ansa yaja hancinta ya ce“Oya muje dare fa ya yi kar murasa abin hawa.�
Manyan idanunta ta zaro waje tana 'Dora hannunta saman 'kirjinsa ta kallesa ta ce“Mon Amour Wlh na manta fa! Ai shi kenan muje 'din wlh bacci inaji kamar me.�
Fuskarta ya tallafo da hannunsa 'daya, 'dayan a 'kugunta yana Mata wani shu'umin kallo Wanda ya saka taji fa'duwar gaba, ta lumshe idanunta tana tura kanta tsakiyar 'kirjinsa.
Bakinta ya sumbata ya Mata ra'da akunnenta.
“Je t'aime bébé, kinci bashi dayawa fa! Zaki biya a Tchad. �
Ibtisam ta 'kwace jikinta ta koma baya tana maqale kafa'da.
Kai ya girgiza yana zura hannunsa cikin aljihun wandonsa, ya fita kiran adaidaita sahu.

Aikuwa suna zuwa gidan bus (3stv) ya rakata 'bangaran mata ya wuce wajan maza, bata jimaba bacci ya 'dauketa duk da kuwa qaran TV bai hanata baccinta ba.

★★★★★★
Washegari misalin 4:30 na asubah bus d'insu ta 'daga daga Tahoua.

Tchad
Duk tsayin wannan kwanakin da gaske Jaddatu ta hana Abie ganin Rahma ta amshe wayanta ko awaya basa ha'duwa, hakan ba qaramin takura rayuwarsu yay ba su duka biyun sunyi missing 'din junansu, Rahma kuwa tai alk'awalin bazata bi kowace hanya ba dan ganin Abien, zata hkr har ayi bikin tinda yazo.
Jaddatu Abie2 kawai take Kira a waya taba Rahma su gaisa, ko idan yazo gaishe da Jaddatun ta basa umarnin shiga wajan Rahma susha hirasu nan kawai take samun sassauci, Abby da zainabu sunata dariya dan sunga Jaddatu abun na gaske ne.

*Gabon*
Ma'aruf duk yabi ya rame, ya sakawa kansa damuwar abinda sukayi da Rabi'ah, Uwa uba ga ciki ajikinta, abun ya tab'asa sosai ga shi Aishatu ta ce yabar komai ahannunta, haka ya barwa Allah ikon sa.
Cikin shirinta ta fito tayi kyau tsaf sai uwar ramar da take damunta.
Hajiya ta kalleta ta ce“Aishatu wai me kike nufi da Ma'aruf ne? Toh wlh yau gidanki za ki koma kya qarasa warkewa agidanki, shifa Aisha zaman aure 'dan hkr ne, wlh duk macan da bata iya hkr da mijinta tabbas bazata iya zama da kowa aduniya ba, Ma'aruf fa 'dan uwanki ne koda wani abun ya miki hkr zakiyi ki yafe masa sannan idan Wanda zakiyi qoqarin sanya shi hanyane ki jajirce kiga ya bari ne, ba wai ki guje shi ba, ke da yake 'dan uwanki kin guje shi ina kuma bare?�
Aishatu ta zauna kusan mahaifiyarta ta kamo hannunta ta ce“Insha Allahu zan koma ni bai min wani abu na gujewa kawai naji haushine wani lamari da ya faru amman insha Allah na yafe masa kuma idan na koma zanzo na muku bayani wlh :kaddarace kuma bata wuce kan kowa, zan shairya cikin kwanakinnan kafin sati biyu zan koma, bari na qara warwarewa.�
Kallonta mahaifiyarta tai ta ce“Ni bazan matsa miki naji tsakaninki da mijinki ba, dan haka Ku gyara tsakaninku Allah ka'de fitina tsakaninku.�
Aishatu ta amsa da.
“Ameen Uwa tagari sai na dawo.�

Kai tsaye Aishatu tana fita ta hau taxi ta tafi gidansu Rabi'ah dan bata yarda da ita ba, tana gudun ta zubar da cikin.

Rabi'ah zaune tsakiyar falonsu qasa tana shan iska, sanye da doguwar Riga atamfa, duk ta rame sai uban fari tai cikin ba qaramin laulayi take sakata ba.
Hannunta riqe da cup tana shan ruwan tsamiya.
Aishatu ta shigo gidan da sallama.
Maman Rabi'ah ta amsa tana shanyar kayan da almajirinsu ya wanke ya bari igiyar ta cika.
“Ah Aishatu kece da rana haka?�
Aishatu ta rusuna ta gaisheta tana ajiye baqar ledar hannunta, ta amshi shanyar tanayi.
“Wlh nice mama ina Rabi'ah kuwa?�
“Tana ciki kawo nayi dan Allah Aisha ki bari kema ba lafiyar kirki gareki ba.�
A'a mama zanyi.�
Bayan ta qarasa ta Mata jagora suka shiga d'akin.
Rabi'ah jin murya Aishatu ya saka duk ta diririce.
Dakyar ta amsa sallamar tsabar kunyarta.
Aishatu ta zauna kusan Rabi'ah ta ajiye ledar ta ce“Rabi'ah barka da rana ya jikin?�
Rabi'ah ta fashe da kuka ta rungume Aishatu tana kuka mai cin rai ayanzu arayuwarta ba abinda tafi so irin mutuwa duk da tasan bata tanadi abinda za'ace taso mutuwa ayanzu ba.

Aishatu ta janye ta matsa gefe tana tab'e baki, ta ce“Uhmm! Nazo na sake garga'dinki ne wlh karki kuskura ki zubar da cikin nan, yadda bakiji kunyar abinda kukayi ba har Allah ya Baku kyauta toh idan dai Allah ya yarda sai kun haifesa ya taka doron k'asa, sbd bakusan me zai zama ba nan gaba ko ta zama ba, dan haka kuji tsoron Allah karki zubar da cikin nan.�
Rabi'ah ta ce“Insha Allahu dan Allah Aisha ki yafemin.�
Baki Aishatu ta tab'e ta ce“Wlh da ban yafe muku ba Sam bazaku tab'a sake ganina arayiwarku ba, ni na tafi Allah ya qara lafiya.�
Rabi'ah kunya ta hanata rakiya tana kallon Aishatu har ta fita.
Sallama ta ma Maman Rabi'ah ta tafi.
Tana fita Rabi'ah ta fasa kuka me cin rai tana qara nadama abin da tayi, tabbas ta yarda son zuciya b'acinta.

★★★
Rayyana zaune ta yi tagumi tana tuna rayuwarta agidan Abie.
Hawaye ya silalo mata tai saurin gogewa ta mai fad'in.
“Astagfirullah wa'atubu ilaik, ya Allah ka ciremin son abinda yamin nisa na har abadan.�
Auntie Saro da take shigowa d'akin ta amsa da.
“Ameen ya Rabbi, wlh Raiyana ki fitar da Abdulmajid aranki ki fawwalawa Allah komai ki Saki jikinki ki mori 'kuruciyarki dan wlh har yanzu da sauranki, karki bari tunanin abinda bazaki samuba ya nakasaki, fa! Ki Saki jikinki kinga ba iddah akanki ki dinga daukan wanka kawai idan sabga ta samu muna fita insha Allahu za ki samu miji, amman idan kinyi tuba domin Allah. �
Rayyana ta share hawayen da kuma silalowa saman fuskarta, ta sauke ajiyar zuciyata, ta kalli Saro ta ce“Uhmm! Bazaki ganeb wlh son so nake ma Abie, amman ba komai zanci gaba da addu'a, Allah ya ban Wanda zai soni.�
Very good my sister, insha Allahu yanzu ki tashi muje tsakar gida musha iskar Allah ga Badiya qawata can tazo karki sake taga alamaun damuwa a fuskarki.�
Rayyana ta miqe tai murmushi ta ce“Kai Auntie Saro bakida dama dole dai so kike kiga na sake koh?�
Hararata tai ta ce“Eh mana.�
Aikuwa Badiya tin daga nesa take kallon Rayyana Sam bataga alamar damuwa ba sai 'yar Rama da tayi.
Cikin fara'a Rayyana ta ce“Oyoyo Auntie Badiya barka da zuwa.�
Badiya tai murmushi ta amsa.
“Yawwa Rayyana wlh naji dad'in ganinki zuciyarki fess mutuwar aure ba kanki farau ba, sai dai fa samun mini kaar takine ya sakeka haukama kayi wallahi.�
Auntie Saro ta tsiyaya Mata lemo tana zama ta ce“Ah toh gayamata dai kawai ta manta baya ta Kama abinda yake gabanta duk Allah ya zab'a mana abinda yafi alkahiri...�

★★★
Masha Allah yau su Ja'afar suka iso Tchad lfy, kwanan su biyu ahanya.
Kai tsaye Abie ya tura direba aka 'daukosu a tasha aka nufi gidansu 'dan madedeci mai shegen kyau, tsaf nacin amarci, ya zuba musu komai na anfanin abinci, motarsa ta wajan Ma'aruf na 'yar rumfar ajiye motar gidan.
Ja'afar zaune kusan Ibtisam, sunyi muguwar gajiya, dukkansu jikinsu ciwo yake musu.
Ja'afar ya shafi fuskarta ya ce“Beby gajiya ko?
Idanunta ta lumshe tana kwantar da kanta saman kafad'arsa, ta ce“Wlh kuwa Mon amour ko ina ciwo jikina yake min.�
“Sorry bari na duba naga toilet na ha'damana ruwan wanka kiyi wanka ki kwanta ni fita ma zanyi.�
Ibtisam ta janye jikinta tana miqewa tsaye ta ce“Muje ka nunamin sai na ha'dama toh idan ka fita sai nayi.�
Murmushi yay ya ce“Ai wlh yau ba Inda za ki sai na fanshe gajiyata ai na raga miki.�
K'walla ta taru mata a idanunta ta ce“Dan Allah ka bari koda bayan wata 'dayane nida bana sallah ma tin jiya...�
Hannunta ya kamata ya ce“Beby kalli wannan gida wai namune Allah kenan mai yadda yaso alokacin da yaso Allah ya kare Abie da dukkan family's nasa albarkar Annabin tsira.�
Ibtisma ta ce“ameen mon amour.�
Bedroom ne guda biyu ajere kowace akwai gado madedeci tsaf masha Allah.
Ibtisam ta ce“Mon amour gsky bawan Allah nan ya gama mana komai wai 'dakin ma kowa da nashi...�
Hannunta yaja suka shiga bathroom, ya ce“Eh fa na zab'i wannan ha'damin ruwa ki tafi naki ko zamu zauna tare?�
Kunya taji ta ha'da masa ruwan gumi sbd zaman da tai gidan Abie da Australia ta koyi abubuwan wayewa.

Bayan ya yi wanka ya shirya ya shiga motarsa ya nufi gidan Abie, dakyar Ibtisam ta barsa ganin ya koma Mata Ja'afar d'inta dan ta ce tsoro takeji, dan da faeko ta d'auka wasa yake ba Inda zaije, ganin hakan yasa ya lallab'ata ya fice.
Wanka tai ta nufi 'dakinta ta kwanta kasancewar tin jiya bata sallah sai bacci.
Can kuwa Ja'afar da Abie sun keb'e bayan sun gaisa, Ja'afar ya basa dukkan takardun makarantarsa, ya duba, daga nan suka nufi company'nisa na sarqoqin zamani masu masifar kyau zaka rantse gold ne, sam ba gold bane ana sarrafasu ne dan masu 'karmin k'arfi amman ina har masu 'karfin rububin siya sukeyi.
Wanda hakan ya saka ba qaramin ku'di ake samu wajan ba, suna isa wajan ya mayar da Ja'afar manager. Ja'afar kasa mgna yay sai hawaye kawai, na farin ciki nan take ya Kira gida yana sanarwa da Mal Adamu Wanda shima ya cika da farin cikin lamarin.

Bayan kwanaki.
Yau ta kama Alhamis ya zama auren Abie da Rahma sauran kwana 3, fa'din kyawun da Rahma ta yi da yadda suka maida mata, jikinta wani matsiyacin laushi, duk da daman jikinta laushi kamar auduga tofa yanzu abin yaci uban na baya, wani irin tsumi Jaddatu da Zainabu suke mata ga na wajan Hanan da Haleesa, abin ba'a mgna ga shegen 'kamshin turaren tsumi da na jikin da ya gama kamata ko cup 'din da tasha ruwa ko lemo ka d'auka masifar k'amshinta yake, matsalarta biyu rashin ganin Abie da jin muryasa sai yadda taga tana tsiyaya yanzu kam pant baya mata pad take sakawa sabida zuba take sosai, da farko kuka ta fara duk ta gigice, tama Hanan da Haleesa bayanin abinda yake faruwa da ita, Hanan ta ci dariya sosai ta yarda Rahma yarinya ce, zaunar da ita sukayi sukayi mata bayani yadda zata gane sai lokacin ta daina kukan.

Kowa yasan bikin 'yan gata ake sabida yadda aka qara k'awata gidan masha Allah duk wani ma'aikaci na gidan Kama daga secretary's masu wanki mota na kaya direbobi masu ba flowers ruwa mai kulawa da tsuntsayen gidan tin daga kan baru 'kwa'kwa jimuna talatalo aku 'dawisu. Kai kowa na gidan an musu 'dinkunansu na kece raini Wanda zasu saka ranan biki Latifa da Ummu Adnan, ba'a cewa komai Uwa uba Meerah da take jansin su.

Rahma zaune cikin bedroom 'din Jaddatu, Meerah na kusanta zaune tana gyara Mata faratanta.
Rahma ta ce“Auntie Meerah kiyi hkr karkiji shiru akan mgnar da na miki har yanzu bamu samu lokaci ni da Abie ba zan masa bayanin insha Allahu kinji? But ke dai ki kasance cikin shiri insha Allah, kin kusa shigowa cikin family's nawa.�
Meerah kunya taji sosai sai ta qara qasa da kanta, ta ce“Haba! Rahma ba komai ai daman har a gama biki ki nutsu.�
Rahma tai murmushi ta ce“Uhmm! Ba haka ba kawai Abien nawa ne ya yi tsada, wlh nafi 'karfin kwana 11 ban gansa ba da ko giftawarsa.�
Meerah ta ce hakan shine daidai ai.�
Murmushi tai ta d'aga kanta tana kallon qaton hotonsa manne a bangon d'akin Jaddatu.

Abie kwance saman makeken gadonsa daga shi sai singilet da wando iya guiwa, Ac na ka'dasa ta ko ina, waya manne kunnensa, murmushi d'auke kan kyakkyawar fuskarshi mgna yake, shi kansa ya qara wani irin kyau sbd ya fasa fita kwana biyu hutawa yake abinsa, shima ya b'oyewa kowa ganinsa, sai 'yan gidansu, auma basa wani ganinsa.
“Ok Nasir ba damuwa idan kana ganin zuba hannun jarin companyn mai nasara bazai zama matsalaba za'a zuba but yanzu banda lokaci ka bari har na nutsu nan da kwana 3 jirgina zai 'daga Turkey (Istanbul) zan yada zango, daga chan zan shiga zagayen qasashe, but zan nemaka naji yadda za'ayi Ok?�
Alhaji Nasir daga chan yay murmushi ya ce“Tabbb zan dai saurara idan ka gama cin amarcin zan waiwayeka mu dai atemaka mana shigar da kud'inka companyn mai nasara akwai qaruwa sosai wallahi sbd kowa rububin ka zuba dukiyarka companynsa suke, sun san komai naka domin ilahi kakeyi.�
Abie ya miqe zaune yana shafa kwantacciyar sumar kansa mai laushi tana fitar da k'amshi.
“Ok..OK! Nasir zamuyi mgna ka bari na nutsu insha Allahu.�
Sallama sukayi, yana ajiye wayan ya miqe ya sauko daga bed domain shiga bathroom kiran Ja'afar ya shigo wayarsa , ganin Ja'afar ne ya sanya ya dawo ya 'daga kiran.
“Hello Ja'afar kana ina?�
Cikin girmamawa Ja'afar ya ce“Abie ina company don Allah idan da dama kazo yanzu...�
Abie ya ce“Ja'afar ba nace maka ba na ajiye komai sai na dawo daga tafiya tsawon wata 3 ba? na jiye komai na amince ma kaida matemakinka Sadi da Kamal komai na wannan company kuyi komai amana na baku Okay?�
Ja'afar ya dafe goshinsa yana shirin mgna yaji an fizge wayar hannunsa.........!

Whtspp number😊
_*+22796515805*_

_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
5/17/22, 22:52 - Buhainat: ```D A```

```96```

_Rahmerh Ladingo😉_


Ja'afar ya 'dago da kansa ransa amugu b'ace, ya kalli Alhaji Dauda ya ce.
“Ban wayata ka fa Kama girmanka, bana shiga sabgar kowa, akan aikina nake komai, taya za'a dinga baku kaya akan farashi mai sauqi sai kuje kuna linka ku'da'dan kaya, bayan kunsan dokar da mai dukiyar ya sanya?�
Cikin hasala Alhj Dauda ya ce“Kai D'an talakawa 'karya kake wlh, waye ubanka a 'kasar nan da har zakayi sa'insa dani?�
Murmushi Ja'afar yay ya ce“Ba kowa bane sai nagartaccan mutum Wanda yaban tarbiya,da ba dan haka ba...! Ban wayana kaya dai bari mai shi yazo wlh ba za'a baka sarinsu ba.�
Abie da yake jin komai ta wayar Ja'afar, wacce take hannun Alhj Dauda, ya furta.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Me yake farune?�
Kiran ya katse ya sake kiran wayar Ja'afar.
Alhj Dauda ganin kiran yana surfa ruwan masifa yay wurgi da wayan yana huci.
Ja'afar ya 'dauki wayansa, yay picking call 'din, yana murmushi.
Abie daga Chan ya ce“Ja'afar meke fatuwa ne?�
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce“Abie Alhj Dauda ne wai sai dai abasa sarin sarqoqin nan akan qasa da farashin da akebawa 'yan uwana talakawa, bayan kanata sanarwa cewar bakayi dan masu da shi su sare suna muzgunawa talakawa ba, inada labarin yadda yake business 'din sarqoqinka a zaman gold Anya hakan yayi kuwa? Shine dan na Hana abasa sarin yazo ya tisani gaba, shiyasa nace kazo da kanka zai fi.�
Abie ya dafe kansa, ya sauke numfashi me zafi ya ce“Ok bani Daudan.�
Wayar Ja'afar ya beqa masa, ya fizgeta kamar zai tizga masa hannu.�
Cikin masifa ya ce“Alhaji AbdulMajid! Wane matsiyacine wannan ka d'ora akan kayanka?�
Abie ya ce“Subahanallahi haba Alhj Dauda ya zaka kirasa matsiyaci bayan kaine babban mataiyaci, ta ya na bu'de company Ana sarrafamin Abu na 'kwarai domain bayin Allah marasa k'arfi su siya su saka masu sari su Sara su sayar ban hanaba amman ba irin ku ba, na kuma ce duk Wanda yake mai qarfi yazo yay basaja ya siyi sarqoqina yaje ya siyar da mak'uddan ku'da'de ban yafe ba, shine kai Ashe kana siya ya ganoka ya hana zaka cimasa mutunci?�
Dauda ya ce“Ta ya zaka bu'de company irin wannan kayi zaton zamubar talakawa su anfana su kad'ai? Humm! Toh ni dai ba wannan ba don Allah abarni na Sara daga wannan karon ba qari.�
Abie ya ce“Ban bada dama ba, bashi wayan.�
Ja'afar ya amshi wayan.
Abie ya ce“Ban Baku damar siyarwa masu ku'diba sbd zalumci dayawa sukeyi suna siyar da sarqar a zaman gold. �
Ja'afar ya ce“Wlh Abie inayi daidai gwargwadona, ina kuma kamosu.�
Wayar Abie ya katse Ja'afar ya ce“Sai kayi hkr bazamu bayar ba.�
Alhj Dauda ya ce“Ni kukawa cin mutunci zaku gani daga kai har uban gidan naka wallahi na rantse da Allah.�
Ja'afar ya ce“Muga alkhairi, addu'ar iyaye na tare damu, indai akan gaskiyar mune, toh ba mutum ba sai dai Allah.�
Alhj Dauda ya fice azafafe yana nuna masa yatsa, ya ce“Zaku gani kuwa.
Ja'afar ya ka'da kafa'da, ya ce“Tawakaltu Alallahi.�

Abie bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito ya shirts cikin wani lallausan yadi blue ya sauko k'asa ta 'kofar baya.

Da misalin qarfe 8 na dare
Abie2 dawowarsa kenan zaune yana Jan casbi, yana kallon Tv tashar Al'jazeera, Abie1 ya shigo da sallama.
Cikin sakin fuska ya amsa yana fa'din.
“Ango kasha 'kamshi.�
Abie ya murmusa ya basa hannu sukayi musabaha, ya zauna.
Abie2 ya Ce“Fatan kana lfy?�
Abie ya amsa da“Lafiya lau Alhmdllh! Yau duk bamu ha'duba, na hangoka masallaci.�
Abie2 ya sauka qasa saman carpet ya ba cicciro kayan abincin da Meerah ta kawo masa yay serving d'insu shi da Abie.
Sai da sukaci suka idar Abie 1 ya fuskanci Abie2 ya ce.
“Am inaga fa yanzu ya kamata ka ajiye iyalai zaifi, ya za'ayi zaka zab'o ko na zab'omaka?�
Ya 'karashe mgnar yana tsare Abie2 da manyan idanunsa, yana son ya ga wace irin amsa yama mgnar.
Abie2 ya kurb'i ruwa ya ce“Uhm! Na baka zab'i, toh ni ina nake zuwa bare nasan matar aure.�
Murmushi Abie yay ya ce“Ok good zan duba, na wuce Allah ya bamu alkhairi.�
Abie ya miqe ya rakasa har qofa ya dawo.

Zazzaune suke a falo, kowa na nan banda Rahma tana d'akin Jaddatu mab'oyarta.
Da sallama ya shigo yana binsu da kallo.
Ummiterh tsabar tsokana ta

Please Login or Register in order to submit comment