Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

abanza, ke tsabar munafurci ke 'dawainiya dake.â€
“Toh Jaddati ai munafurci ma dan ka ku'butar da hanyar neman abincin ka halaline, kiyi hkr wlh ni ina sonki.â€
Ta 'karashe mgnar tana ficewa aguje.
Hanan me zatayi idan ba dariya ba.
Raiyana da take saukowa murmushi ta ke, ta iso ta zauna tana fa'din.
“Ummi baku tafi yawon bane? Ummi babba kunata dirama keda mutuniyar?â€
Rahma batace kome ba, kai ta 'daga tana dafe goshinta, ta mi'ke ta nufi sama.
Jaddatu ta ce“Rahma wai meke damunki ne? Suwa za'a gyarama can 'bangaran wajan ne?â€
Juyowa tai tana kwab'e fuska ta ce“Jaddati zamuyi mgna wlh ciwon kai nake.â€
Hanan ta ce“Toh ummina maza je kisha magani.â€
Kai ta 'daga“Toh ammina.â€
Raiyana ta bita da kallon mamaki ta rasa me taiwa yarinyar nan da zafi ta tsaneta.....?â€
Raihana ta ce“Hanan bansan me zanma Ummi ta soni ba?â€
Jaddatu ta ce“Kinga Raiyana banson harakar munafurci, rabani da gulmar mutum bayan idanunsa, tsakani da Allah fa! Toh me tai miki? Idan ba kinso gulma ba fa'di agabanta mana.Wa kikaga tawa mgna da ta shigo? Raiyana ina rabaki da shiga sabgar Rahma.â€
Hanan ta kyalkyale da dariya tana mi'kewa ta ce“Iman muje ciki kar cikina yay ciwo.â€
Jaddatu ta ce“Humm ko kuma tusar za ki kiyi ta nuska mun a'daki ba, Hanan Allah shiryeki.â€
Raiyana ta ce“Ummi tusa kuma?â€
Hanan tai dariya ta ce“Bakya daddara.â€
Jaddatu ta ce“Raiyana don Allah ki zabomin dabino a fridge masu taushi ya fiye miki zaman gulma.â€
Raiyana aranta ta ce“Humm duk zan rama ne wlh muje zuwa.â€
Azahiri ta ce“Toh Ummi bari na za'bo muku.â€

Rahma key ta 'dauko ta bu'de bedroom 'din Abienta.
Wani 'kamshi ya daki hancinta irin na Abienta kamar yana garin.
Ajiyar zuciya ta sauke, ta bu'de tafkekiyar wardrobe 'dinsa, wacce take sha'ke da kayan sakawa iri².
'Bangaran shaddah ta za'ba kala 'daya jallabiya kala biyu yadi kala 'daya kayan bacci kala biyu.
'Bangaran takalmi d'aya ta 'dauka ta zube kayan saman makeken gadon Abie ta haye gadon.
Kiransa tai video call.
Ta 'dan jima tana ringing kafin ya d'aga.
Daga can Abie ya ce“Uhmm! Baby ummina I miss you, kice kina 'dakin Abienki? Wannan tilin kayan fa na gabanki? Ko duk kewar Abie ne?â€
Rahma ta shagwa'be ta zuba masa idanu tana bek'a masa hannunta.
“Oya zo toh ga ni baby.â€
Kukan shagwab'a ta sanya masa.
“Abienah! Ni bazan qara zuwa Hutu ba tinda barina kakeyi.â€
“Ya Salam! Baby sauran kwana 2 na dawo yi shiru karki hanani sukuni kinji, ina Raiyana dasu Hanan?â€
Ashagwa'be ta ce“Abiena nutsu kaji. Daman 'dazu ne da muka fita wlh na ha'du da wani bawan Allah...
Ta basa labarin dalla².
Abdul Majeed ya ce“Baby bakya tsoron acutar damu? Wlh naji fa'duwar gaba, amman tinda kince mu temakesa shi kenan Allah yasa nagari ne.â€
Rahma ta ce“Abiena wlh shima kamar balarabe ne da larabci muke mgna wuyace ta saka ya fara duhu kuma bazai wuce warinkaba, amman rashin gata ya saka fuskar tasa tsufa kamar ya haifeka insha Allahu bazai cutar damu ba.â€
“Ok Baby duk abinda kikeso inaso oya je ki kai masa kayan ya canza, Muahhh ina sonki ummina bye....â€
“Wayyo Abiena tsaya don Allah karka kashe.â€
Ta k'arashe mgnar tana turo bakinta gaba.
“Ok na tsaya.â€
“Abiena ina sonka dayawa² kai ta tunanina 'diya 'daya tilo wajan Abienta.â€
Wani sansanyan murmushi ya saki mai kyawun gaske ya ce“Dole wannan Baby. â€
Kashewa tai tana masa gwalo, ta mi'ke zaune, ta kwashi kayan ta sakko daga bed 'din ta fice.
Falon shiru ba kowa lokacin ana kiran magarib, agaggauce takai kayan har lokacin Latifa na gyaran falon.
Sosai dattijon ya sanya mata albarka yana kuka,Rahma ta lallashesa yay shiru, sai da ya tayar da sallar magarib suka fito ita da Latifa, ta na bata umarni idan ta yi sallah ta zuba abinci ta kai masa.
Bayan sallar isha'i su Ja'afar zaune sun idar da cin abinci kenan kasancewar Ja'afar ya iya girki sosai shi yake dafa masu, aresho 'din da suka siya, su zasu gyara kayan miya, da siyowa shi ya dafa musu haka sukeyi.
Ja'afar ya dafe kansa da yaji ya sara masa, yana kiran sunan Allah.
Baba Tsalha ne ya turo 'kofar ya shigo da sallama.
Su ka amsa. “Yauwa Ja'afar Allah ya amince an samu tu'ki wlh awani 'katon gida, amman zakayi ne zuwa wani lokaci kafin direban su ya dawo, mahaifiyarsa ke fama da larura mai tsanani jinyarta zai tafi, muje suna son ganinka.â€
Ja'afar ya zubawa Baba Tsalha manyan lumsassun idanunsa wa'danda basu fiye fari ba, 'kwayar sun sanya kalar brown ya sauke numfashi cikin dadda'dar muryasa ya ce.
“Baba badan kun ce akwai mai yiba da nace A'a amman ba kome Allah ya sanya yazamo alkhairi.â€
Baba Tsalha ya ce“Ameen wlh alkhairi ne ma, mutumin baida matsala.â€
Ja'afar ya ka'da kansa ya mi'ke ya ce“Toh ku sai mun dawo.â€
Yahuza da Harisu atare sukace.
“Fatan alkhairi na wajanmu angon Ibtisam adawo lfy.â€
Ja'afar ya 'dan murmusa yana zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa, suka fice........!

_💃ðŸ»Yar Ajin Tubarkallah🥰_

*DATTIJON ARZIK'I* N300 katin MTN ta wannan number *+22796515805*



SULTAN
mss flower

BAK'AR FATA
AUTAR MANYA

TSINTACCIYA
Nimcyluv

Gaba É—aya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218


*Real Ladingo+22796515805* For more information😇

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
2/2/22, 18:46 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_


*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_

*🔥FITATTU HUƊU🔥*


_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_

_Sauran Ku page biyu na gama free page, ku 'kakka'be zani ku gyara zama tafiyar ta musamman ce wallahi.💃ðŸ»ðŸ¥°_


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


_*cнapтer 17&18*_


*Niger*
Laraba kamar yadda tai al'kawali bayan magarib, taje da kanta ta siyo musu gasashen nama.
Ibtisam zaune su Aydah anata cin gasashen nama, sai surutu suke, ita kam tana gefe juyin duniya Ibtisam ta'ki cin naman. Taslim ta ce“Wai aunty Ibtisam meyasa bazaki ci ba?â€
Laraba ta ce“Dan ubanta karta ci, shegiya me mugun hali, kuma wlh aure anyi an gama, sai dai idan bai ce abasa ba. Tafi son shegen ba'kaâ…” can, matsiyaci bai da taro bare sisi, satinsa nawa baya garin? Uwar me ya ta'ba aiko miki?â€
Ibtisam ta saki kuka ta mi'ke hankalinta mugun tashe, ta fice aguje ta bar gidan.
“Ibtisam ki dawo wlh zan wulaqanceki.â€
Ibtisam kai tsaye keke napep ta tare ta shiga sai gidansu Ja'afar, domin ta yi mgna da Mahmoud, tasan shi ka'dai zai iya temakon ta.
Dab da kwanar gidan ta sallami me napep cikin ku'din da Ja'afar ya bar mata.
Tana tafe sai ga motar Alhj Jamilu kamar an tunku'do shi. Gabanta ya sha da motar.
Dole ta tsaya, ta ri'ke 'kugu tana jiransa ya fito.
Baki ya washe ya fito da kwalin waya ya ce“Amman me kike nema nan unguwar? Kinga saqonki nazo amsa, sai 'dazu wayoyin su ka iso.â€
Tsaki taja ta ce“Ban bu'kata don girman Allah Baba ka fita daga sabgata, karka rabani da masoyina.
“Naji amshi wayan zamuyi mgna.â€
“Wlh bana so.â€
Ta qarashe mgnar tana barin wajan.
Da kallo ya bita yana lashe 'katon wargajejan bakinsa ya ce“Allah ya kai damo ga harawa.... Aure ni dake ba fashi ke matar manyace.â€
Ibtisam a 'kofar gidan ta la'be ta kasa shiga sai share hawaye take.
Cikin ikon Allah Mahmoud ya fito yana sauraron waqa, da jarkar mai ahannunsa alamun Inna mai waina ta aikesa amsar mai na wainar gobe kanti.
Sam bai lura da itaba, sai da ta kirasa.
“Mahmoud! â€
Juyowa yay ya na waige-waige.
â€Lah! Ibtisam! Ke ce? Amman kika qi shiga?â€
“Wlh Mahmoud tsoron Inna nakeji karta koreni.â€
Dariya yay ya ce“Mutum da surukarsa, muje ciki toh ki zauna na siyo mata mai nazo.â€
Cike da tsoro ta ce.
“A'a muje tare daga can sai na wuce.â€
Mahmoud ya gane mgna take son yi da yayansa.
“Ok muje.â€
Ya fa'da ya na lalubo number Ja'afar ya danna masa Kira, su na ci gaba da tafiya.
Can kuwa Tchad.
Unguwar clemate
Wani gida ne mai kyau babu laifi ya ha'du, kana ganin gidan kasan me shi ya tara ko ba yawa.
Baba Tsalha bayan sun shiga gidan suna tsaye jiran Lawi me gadi ya kirawo mutumin, dan daman shine ya saka ya masa cigiya.
Ja'afar kasan 'kasa yana danna wayarsa ko wasa bai tsaya kalle² gidan ba.
Wayar hannunsa ta 'dauki ringing.
Ja'afar ganin number Mahmoud ya 'dan tsotsi ba'kin lips 'dinsa na qasa mai taushi yay picking call 'din ya kai wayar kunnensa tare da sallama.
Daga can Mahmoud ya ce“Ya Ja'afar ka kirana Ibtisam ce gatanan.â€
Ja'afar ya lumshe manyan shayayyun idanunsa ya ce“Ok ok...ok!â€
Ya datse kiran ya duba yaga sauran ku'din zasu masa hira 3 minutes.
Kira yay kai tsaye.
Mahmoud ya 'daga kiran ya be'kama Ibtisam ya ce“Toh je jikin bishiyar can ku zanta bari na hanzarta na amso mai nazo.â€
Cikin farin ciki ta 'daga kanta, ta nufi gindin bishiyar dogon yaro.
Sallama tai masa cikin sanyin murya.
Daga can Ja'afar ya amsa, yana mi'kewa ya koma jikin wata flowers ya kira.
“Mon cÅ“ur tu me manque beaucoup , fatan yau lfy ta b'oye min ke?â€
Ibtisam wani irin magana 'disun son Ja'afar taji ya kuma fizgarta, taji ruwa da iska bazata iya rayuwa babu Ja'afar ba.
Ta fashe da kuka ta kirasa.
“Mon amour! Don Allah kayi wani abu kar arabani da kai...â€
Kuka yaci 'karfinta ta kasa 'karasa mgnar.
Ja'afar ya dafe goshinsa, ya ce.
“Subahanallahi! Baby menene? Kiyi shiru wlh har 'kasan zuciyata nakejin kukan ki, nutsu kima Sahibinki bayani, ku'din basuda yawa karsu 'kare, muahhhh! Ina sonki babu abinda zai rabamu sai mutuwa.â€
Ibtisam tai luf abinta ta lumshe idanunta tana sauraron dadda'dar muryashi, taja dogon numfashi ta narkar da murya ta shagwa'be ta ce.
“Mon amour yo ba wani tsoho bane d'azu....â€
Tsaf ta masa bayanin komai bata 'boye masa, har naman da aka siyo da ku'din ta'ki ci, da tareta da yay yanzu ya bata waya ta'ki amsa.
Ja'afar ransa ya yi masifar 'baci zuciyarsa ta harzu'ka matuk'a manyan idanunsa suka riki'de lokaci d'aya sukayi jajir jijiyoyin kansa suka fito ra'dau-ra'dau. Mur'da'ddan jikinsa ya soma rawa, ya kasa mgna sai bakinsa da yake motsawa alamar sunan Allah yake anbato.
Ibtisam cikin kunnuwanta banda hucin numfashinsa batajin komai sai ajiyar zuciya ajre².
Kuka ta saki ta kirasa.
“Mon amour!â€
Dakyar ya motsa labb'ansa ya amsa.
“Na'am Baby mon cÅ“ur, maza yi shirunki na sanki nasan bazaki gujeni ba sabida ku'di saïi dai ni ma bazan zugaki ba ki bijirewa iyayan ki, ina Baba?â€
Ibtisam ta ce“Ya tafi Bouza sai gobe zai dawo don Allah mon amour ka kirasa kaji.â€
“Ok baby karki damu yanzu ni nutsu insha Allahu muna tare, kinga ku'din sun 'kare gobe zamuyi mgna, yanzu Mahmoud ya rakaki har 'kofar...â€
Ku'din suka 'kare bai ida mgna ba.
Kansa ya dafe, jarumta yake yasan wannan abun babban abune, amman tuna mahaifin Ibtisam atsaye yake sai yaji sanyi aransa.
Dai-dai lokacin da Ja'afar ya dawo ya zauna.
Ma'aruf ya fito daga falon, sanye yake da 3 quarter sai wata jibgegiyar rigar sanyi mai hula, ya yi kyau sai baza 'kamshi yake, yana tafe yana waya.
“Haba! Aishatuna kin fiye rigima, da mitar tsiya kullun cikin waya muke. sati 3 kawai zanyi na dawo, naga lafiyar ki da ta baby na koma. Hope kina lfy?â€
Daga can Aishatu ta turo baki gaba ta ce“Uhmm! Da dama dai, ya tarin 'yan mata da aka tara acan?â€
Ma'aruf ya yi tsaki ya ce“Ban saniba masifafiya kawai, shi kika iya.â€
'Kitt ya tsinke kiran.
Yana tafiya cike da gadara, yana bubbu'de hanci. Kasancewarsa mutum mai shegiyar gadara.
Tin daga nesa yabi su Ja'afar da kallo. Gabansa yay mummunar fa'duwa, sabida yanayinsa kamar yaron da ya ta'ba marinsa shekaru biyu baya,jinsa da ganinsa suka 'dauke na wani lokaci Tahoua,ya zubamasa ruwan kwata me tsami, mafarin da ya haramta masa shiga niger. ta'be baki yay aransa yana fa'din ai kuwa da ya shiga masifa ramuwa mai zafi zan masa.â€
sai da ya kusa yaga Ja'afar ingarman namiji tsayayye mai sufar 'karfafa, ajiyar zuciya ya sauke aransa ya ce“Yes! Wannan shine na goma kuma shine zai Iya. Kuma wlh shine ya mareni ramuwa har gida. Wannan Irin mazan nake son su na driving na, da kuma 'dayan aiki tabbas wannan shi zai iya fito min da.....†wani shu'umin murmushi ya saki, ya ce“Zan sakar maka masu gidan rana, sai na gama business 'dina da kai na rama abinda kamin.
Bakisan d'auke da sallama ya iso wajansu, yana bek'awa Baba Tsalha hannu.
Ja'afar ya amsa sallamar. Lokacin su ka ha'da idanu. Ja'afar Sam bazai gane Ma'aruf ba, sbd ranan bada fuskarsa ta asali bane.
Ma'aruf ya tsorata da kyan Ja'afar, sai yaji ya raina kansa agaban Yaron, sbd abaya ransa a'bace bai ga kyansa ba.
Gaisawa sukayi, Lawi ya ce“Yalla'bai ga su sai ku dai-
dai-ta.â€
Ma'aruf ya ce“Ok Ngd gobe da safe sai kazo, duk Inda zanje kaine zaka kaini sai aike idan inada, amman kafin direbana ya dawo, maybe har zanje Gabon na dawo Ok? Sannan awuni kakeson ku'dinka ko sati? Ba lallai ka kai wata ba?â€
Ja'afar ganin yadda Ma'aruf yake komai agadarance, sai kace wani ubansa ya saka ya ce“A'a barsa asatin ko kuma har wancan ya dawo.†ya na fa'din haka yaja bakinsa yay gum, shi damuwarsa ma ta ishesa.
Ma'aruf aransa ya ce“Tabb yaron nan 'dan jin kaine.â€
ya ka'da kafa'da ya ce“Ok ba damuwa kazo da sassafe.â€
Ja'afar ya ce“Ok.â€

Ahanya komawane Ja'afar ya ce“Anya Baba wannan mutumin zan iya aiki 'kasansa?â€
Dariya Baba ya yi ya ce“Haba! Yarona ai tinda ka baro 'kasarka ka shigo wata 'kasa domin neman halak 'dinka toh fa sai kakai zuciya nesa, kayi hkr ka 'kas'kantar da kanka har ka samu abinda kake so, kaima kaje kaci gashin kanka.â€
Ja'afar ya ce“Insha Allahu Baba Ngd. â€
Su na zuwa gida yama su Harisu bayani komai, suka tayasa murna. Lokacin ya saka Kati ya gwada kiran layin Tanko mahaifin Ibtisam amman baya samunsa, sai Mahmoud 'kaninsa shima bata shiga, ya so ya ji ko ya raka Ibtisam 'din.

Can Niger kuwa Ibtisam sosai taji sanyi aranta, mgna da tai da Ja'afar.
Mahmoud ya isowa yajata suka tafi, ta tsaya awaje ya kaima Inna manta ya fito ya raka Ibtisam har gidansu sai da ta shiga gida ya tafi.
Kamar munafuka da ta shigo.
Laraba ta ce“Kinje kiyin waya da ubanki Ja'afar kin fa'da masa koh? Toh wlh rubuta ki ajiye sai na aura miki Alhj Jamilu ai yazo yanzu ya fita yakuma gayamin Inda ya ganki ga wayarki nan.â€
Ibtisam Sam yanzu batada damuwa tinda ta yi mgna da masoyinta, shiyasa uffan bata ce ba.

Anutse take taka matattakalar benin, tana saukowa, hannunta ri'ke da wayarta. video call take fuskarta cike annuri, sai dai hankalinta wajan saukar gudun kar ta goce ta gangaro, dan idan tana tare da Abienta komai zai iya faruwa. Sanye take da riga da wando Pakistan, maroon colour ta 'daure dogon gashinta irin na asalin larabawa, ya sauka har tsakiyar bayanta.
Sai da ta sakko a matattakalar 'karshe ta tsaya, tana kallon wayar ta shagwa'be tana turo jajayen la'bbanta gaba.
Dariya Abienta yay, ya 'beko hannunsa ta cikin wayar kamar zai iya kamata, ya ce.
“Kamota nan kamota nan Baby ummina.â€
Rahma ta 'kyal'kyale da dariya tana kallonsa ta 'daga hannayenta ta ce“Ga ni nan ga ni nan Abiena, akamani akaini wajan Abiena. Amman yau Abiena duk ka canza mi fa!â€
Ta 'karashe mgnar tana kwa'be fuska.
Daga can ya zaro manyan kyawawan idanunsa, ya ce.
“Ya Rabbi! Baby mene? Oya ta shi ni kije falo mu gaisa da su Ummi sai kije ki kawai ba'kon na gansa, dan hankalina ya'ki kwanciya.â€
Ashagwa'be ta kira shi.
“Abiena!â€
“Uhmm Baby Na'am muahhhhh je t'aime, oya.â€
Mi'kewa tai tana kallonsa tana son saka masa kuka, ya girgiza mata kai. “Lal-lah baby ummina.â€
Murmushi tai ta nufi falon.
Jaddatu da su Hanan zaune suna fira, basu jima da kammala lunch ba.
Raiyana ta zubawa Rahma idanu har ta iso wajansu.
Dab da Jaddatu Rahamu, ta zauna ta rungumota, jikinta tana nunawa Abienta.
Jaddatu ta ce“Au abinda ya hanaki sakkowa kici abinci ko?â€
Abienta ya ce“A'a Jaddatu Baby lashe² tai asama, ta ce bata son cin abinci yau.â€
Jaddatu ta watsame hannu, alamar da'kuwa ta ce“Ga taka kai da Rahmar.â€
“Godiya nake ummina. Ashe Rahma ba'ko ta rakito mana?
Jaddatu ta zaro idanu ha'di da tambayar yaushe? Na shiga uku! Ba'ko awannan zamanin?â€
Abie yay dariya ya bata labarin komai yadda Rahma ta basa.
Jaddatu ta ce.
“Shi kenan wayyo Allah gamu gareka! Wlh ni dai zuciyata batai na'am ba, don Allah kace ta sallame shi dan nasan kai 'daya zaka hanata.â€
Abie ya ce“Haba! Ummi ako yaushe mu kasance da kyakkyawar niya ta temako azuciyar mu, ba wai mu saka zargin zamuyi temako acutar damu ba? Sannan mu kasance masu tawakali da Allah, ba maiyi sai Allah ba mai hanawa sai Allah, idan har Allah ya 'kaddara mutum sai ya cutar da kai bayan ka temakesa, toh fa sai ya cutar dakai. Idan kuma Allah bai 'kaddara ba duk yadda yaso ya cutar da kai Allah zai kareka da dukkan sharrinsa.â€
Jaddatu ta ce“Toh naji ai kaifa kome wannan tilon ta ce shine, ni dai ina jin tsoro amman tawakaltu ilallah.â€
Rahma tai dariya ta warce wayarta ta ce“Matsa matsoraciya, me zai samu bawa bayan daman can ubangiji ya rubuto sa cikin kundin 'kaddarasa, ni inaji ajikina wannan mutumin babu cuta babu cutarwa zuciyata 100% ta yarda da shi, jinsa nake kamar Abiena wallah.â€
Abie daga Inda yake tsaf yana kallon komai ya lumshe idanunsa yana jin wani matsanaicin yanayi mai wuyar fassaruwa, ya bu'de d'an 'karamin bakinsa, ya murmusa ya bushi dadda'dar iska ya fesar yana motsa la'bban nasa.â€
Rahma ta ce“Abiena kajita ko.
Toh ga ammi da ammi ku gaisa.â€
Raiyana da ta gama sha'kewa ta mi'ke ta ce“A'a ku gama ina zuwa zan shiga toilet. â€
Hanan ta amsa tana dariya ta ce“Ya Abdul munata kewarka fa!â€
Murmushi yay ya ce“Sha kuruminki ina tafe, ina Angel Iman?â€
“Ta yi bacci.â€
Bayan sun gaisa ya ce maza taje ta kawai ba'kon su gaisa.
Mi'kewa tai anutse tana tafiya, Jaddatu na fa'din.
“Allah ya rufa asiri wannan gadon jajibe² irin Abdul Majeed da ta gado.â€
Hanan tai dariya, tusa na kubce mata.
Jaddatu ta ce.
“Ta shi ki ban waje, Hanan ke kam buni ya ciki wlh albasa batayi halin ruwaba, babu abinda kika ajiye sai tusa, cikin 'katon 'duwawunkin nan, tirrr. Ko ni tsohuwa da 'duwawuna suka ru'be wlh ban sakin tusa ina sane sai dai idan ku'buce min tai, ko cikin bacci, amman ke ba kunya abu 'burrr-'burrr-'barrrattt, sai kace budari.â€
Raiyana da take lab'e dariya ta ku'buce mata, ta toshe baki, ashe Latifa na can dining area, tana guga ta jiyo Jaddatu duk yadda taso toshe bakinta abin yaci tura ta 'kyal'kyale da dariya, tana toshe baki.
Jaddatu ta shiga tafa hannayenta.
“Ikon Allah! Raiyana! Latifa! Ni kukewa dariya? La'be kuka koma?â€
Raiyana, aguje ta haye beni dariya take over, duk haushin da ta sha'ka ya kau, wata irin dariya take, ta toshe bakinta.
Latifa ta yi duk yadda zatayi ta ha'diye dariyar abin ya faskara, Allah ya sota ta kammala gyaran dining 'din tai saurin rugawa aguje ko tsoron tayis 'din mai wal'kiya kamar muduba batayi ya kayar da ita batai ba.
Jaddatu ta ce“Wlh zamu gauraya daku, Hanan duk kece kika sakani su'bul da baka.â€

Rahma jikin 'kofar falon tai tsaye tana bubbugawa.
Zaune dattijon yake afalo saman carpet.
Sanye da jallabiya sabuwa fara 'kall, ta masa mugun kyau, yau d'aya kyawunsa ya fito, sai dai jikinsa yafi fuskarsa kyau . dadda'dan 'kamshin turaren Abdul Majeed da yake jikin jallabiyar ya kama masa jikinsa.
Tin bayan da yay sallar isha'i, yake Jan tsohon casbin sa, ya zubawa Tv idanu.
Jin ana buga 'kofar ya sanya ya mi'ke ya nufi 'kofar.
Ya na bu'dawa tana tsaye.
“Abba ga Abiena ku gaisa muje ciki.â€
Cike da dattakunsa ya murmusa ya ce“Sannu 'diyar albarka, insha Allahu za ki gama da duniya lafiya.â€
Rahma ta Kama hannunsa ganin yana 'dingisawa suka nufi wajan kujerun tana amsawa.
“Allah ya amince Abba.â€
Zaunar da shi tai saman kujeran ta zauna 'kasa dab da 'kafafunsa ta be'ka masa wayan.
Sallama yay yana 'dagawa Abie hannu.
Abie ya ce“Sannu ina yini? Ta min bayanin komai idan na dawo zamuyi mgna. Bawan Allah me sunanka?
Dattijo ya ce“ Abdulmajid Idris.â€
“Abie ya zaro idanunsa waje ya ce“Ma sha Allah! Amman bai ce shima haka sunansa ba!â€
Rahma ta ce.
“Yeee ashe ba banza ba naji 'kaunar dattijon ashe mahaifine. Kaga Abie zan kashe wayar ga Abiena na biyu kusa da ni zamuyi fira, kai bari idan na dawo sai muyi waya.â€
'Kitt ta yanke kiran ta ajiye wayan gefe.
Ta zubawa dattikon idanu, ta ce“Abiena pls ka fa'da min me yasa gaka kyakkyawa amman bakada kowa kuma ba wanda ya temakeka?â€
Ta 'karashe mgnar tsakaninta da Allah kallon Abienta take masa ta kamo dukkan hannayensa ta ri'ke tana zubar da hawaye.
Jikinsa ya 'dauki wani irin 'bari cikin maganarsa wacce kanaji kasan harshensa akarye yake ya ce“Karkiyi kuka toh 'diyata kiyi hkr kowa da irin 'kaddarasa. Yay saurin zame hannayensa sabida abinda yakeji wani abu na masa yawo asassan jikinsa.
Rahma ta zum'boro baki gaba ta shiga harba 'kafa ta ce“Abie kai ba irin waccan Abien bane baka sona shi kenan bari na tafi.â€
Ta fara 'ko'karin mi'kewa.
Sai ya ga kamar bai kyauta mata ba, amman wani fannin sai ya ga yau fa kawai su ka had'u, ta ya zai iya sakin jikinsa da ita.
Hannunta ya kamo ya ce“Yi hkr 'diyar albarka Wa yace bana sonki? Ai duk duniya mai sonki bayana ne, kece kika nunamin abinda duniya ta kasa nunamin wanda najima ina kwad'ayin na kasance na samu wanda zai soni ya kula dani, nasan akwai na Allah, sai yau Allah ya kawo ranan Wa zanso sama dake?â€
Cikin farin ciki Rahma ta ma'kale hannunsa saman 'kirjinta, tana kalkonsa haka kawai take mugun jinsa har 'kar'kashin ranta.
Da sauri ya janye hannunsa wanda yake ta'bo 'kirjinta, acikin ransa yana fa'din.
“Ya Allah!â€
Rahma ta ce“Abie 2 menene? Kake rude idanunka? Yauwa Ngd Abie2 ka riqemu Amana, kaci abinci ka 'koshi koh?â€
Kai ya jinjina.
“Na ci Allah ya miki albarka, maza je ki kwanta, kiyi bacci kinji?â€
“Toh shi kenan Abie2 kaima tahi kwanta, gobe zan saka asamo mai kulawa da kai.â€
Hannunsa ya zare cikin nata ya ce“An gama 'diyar albarka,amman ban son kowa ya kula dani zanji da kaina, ga ki kin wadatar.â€
Murmushi sukawa juna ta fita ya rufe k'ofar falon ita kuma ta rufe masa gate da key, sabida 'karamin gate ne, tinda akwai key wajansa.
Jaddatu ta isko tana famar surta masifa sai fa Latifa tabar gidan da kyar ta samu ta rarrasheta, Hanan na musu dariya.
Rahma da wuri tai bacci yau ko wayar batayi da Abienta.
Tsakiyar dare misalin 'karfe 2 na dare Rahma ta yi 'dai-daya tana sharara bacci, mai masifar da'di tana rungume da 'katon Teday 'dinta.
Ga shinta ya bazu ya lullu'be mata fuska.
Kamar amafarki ta ji ana.........!

_💃ðŸ»Yar Ajin Tubarkallah🥰_

*DATTIJON ARZIK'I* N300 katin MTN ta wannan number *+22796515805*



SULTAN
mss flower

BAK'AR FATA
AUTAR MANYA

TSINTACCIYA
Nimcyluv

Gaba É—aya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218


*Real Ladingo+22796515805* For more information😇

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
2/3/22, 11:42 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_


*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_

*🔥FITATTU HUƊU🔥*


_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


_*cнapтer 19*_



Wayarta nata ringing, kasancewar bata sakata a silent ba.
Ahankali ta fara motsawa, tana sake 'kan'kame 'katuwar Teddy 'din da take rungume a'kirjinta.
Bu'de shanyayyun 'kananun idanunta tai ahankali, wanda suke cike da bacci jin anqi daina kiran wajan karo 4.
A hankali mi'ke zaune tana murza idanu, bakinta na motsawa alamar addu'a take.
Matsowa tai sosai ta be'ka hannunta, ta 'dauki wayan da take a gefen bedside drower, ajiye tana neman agaji.
Ahankali ta furta.
“Abie! Lfy kuwa?â€
Ta 'karashe tana picking call 'din, ta manna wayan akunnenta.
Ashagwa'be ta ce“Wayyo Abie I miss u jiya bamuyi fira dare ba, bacci wallah.â€
Murmushi mai taushi ya yi, ya ce.
“Uhmmm! Babyna ni ai na kasa inata tunaninki na ce sai na kira naji lafiyar tilon 'ya Ummi baby. Amman jiya ko 'dazu dai za ki ce.â€
'Kyal'kyalewa tai da dariya tamkar ba daga bacci ta farka ba, ta ce.
“Abie na manta na zata asubah ne video call pls naga farin cikina.â€
“Wayyo Baby kiyi hkr oya bacci dare ya yi sosai 'karfi biyu fa!â€
Kukan sangarta ta sanya masa yana ji tana harbe-harbe, wanda ga shinta ya gama rufe mata fuska.
“Ya Salam! Ok bari na kira video call 'din.â€
Kira yay ta 'daga tana murmushi da guntin hawaye, ta janye gashin da ya rufe mata fuska.
Hannu ya me'ka ya ce“Sai na mare ummina, rigimarki Abie mgnarki Abie ko?â€
Idanu ta 'kura masa ta turo baki “Toh Wa gareni bayan Abie nah?â€
Murmushi yay ya ce“kwanta ki lullu'ba muci gaba da mgna.â€
Kwanciya tai sunata fira har kusan 3 'barawo bacci ya saceta.
Abienta yay murmushi ya datse kiran...

Washegari Ja'afar da wuri ya shirya, ya ma su Yahuza sallama, su sai tara zasu fita aiki.
Ya na zuwa Lawi me gadi ya ce ya shiga.
A 'kofar falon ya tsaya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment