Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

jinta kwance cikin 'kirjinsa ya nufi hanyar bedroom 'dinsa da ita.
Bai direta ko ina ba, sai tsakiyar makeken royal bed 'dinsa ya kwantar da ita ya lulu'beta da wani tafkeken lallausan bargon wanda yake fitar da dadda'dan 'kamshinsa, ya rankwafo ya mata kiss agoshinta, ya ga yadda take kallon lips 'dinsa tana matsar kwalla.
Waskewa yay ya ce“Oya Babyna bacci, bari na shirya zanje hospital 'dinki na dawo, ance wani bawan Allah yana nema na.â€
Ya shafi fuskarta, yana barin wajan.
Idanunta ta runtse bata iya furta komai ba, sbd bazata iya mgna ba, adaidai wannan lkcn nan, sam bazata iya ba, ayanayin da take ciki.
Kamar bayan 25 minutes cikin baccin da ya 'dauketa mai da'din gaske taji tattausan lips 'dinsa saman kumcinta ya manna mata kiss, 'kamshinsa mai azabar da'di ya mamaye dukkan 'kofofin hancinta, ta sauke numfashi mai wahala, asanyaye cikin baccin da yake cinta ta kirasa.
“Abiena! Pls.â€
“Na'am Babyna! Pls me um?â€
Kai ta girgiza dakyar ta iya fa'din.
“Jibi mukeda jarabawa ya kamata gobe na wuce.â€
Ta 'karashe mgnar tana bu'de shanyayyun 'kananun idanunta masu haske, ta kalleshi yadda ya rankwafo sai taga sosai ya cika mata gaba.
Hannunta ta 'dora saman fuskar shi tana ta'ba sajansa, zuwa gemunsa ta ja dogon hancinsa ta 'dora yatasarta saman jajayen lips 'dinsa wanda sak baida banbanci da nata.
Sosai take kallon tsantsar kamarsu da Abienta, ta ha'diye wani irin yawu ashagwa'be ta kira shi “Abiena bacci nakeji sosai.â€
Ra'da ya mata ya na sakin murmushi.
“Ok Baby oya bacci ko na kawo miki shayi me zafi? Idanunta ta rufe ruf, kai ta girgiza tana hamma, still idanunta rufe. Murmushi yay ya sake kissing 'din kumatunta ya ce “Ok bye ki tashi lfy Baby.â€
Ya 'karashe mgnar yana janye kansa dab da ita ya juya ya fara tafiya, hasken 'dakin ya rage mata, ya rage gudun Ac.
Sai lokacin ta bu'de kyawawan lumsassun 'kananun idanunta wanda suke cike da bacci, kallonsa take cikin 'danyar shaddah me suna (Annur) brown coffee, 'dinkin ya fito da dattakunsa sosai, wata irin tafiya yake mai cike da kamala.
Har sai da ya fice ya rufo mata 'kofar kafin ta janye idanunta daga 'kofar.
'Katuwar ajiyar zuciya ta sauke ta shige cikin bargon, tana shaqar 'kamshisa asakalce ta furta.
“Wlh daman ace mijina halaiyarsa da dattakunsa da kominsa irin na Abiena ne, amman gaskiya banjin zan wani sosa tinda Abie ya min alqawalin raba auren idan bana sonsa, Abiena Allah ya baka mace tagari, Allah sarki ummatah Allah ya jiqanki da rahamarsa.â€
Ta 'karashe mgnar tana goge hawayen da batasan yadda akayi suka zubo mata ba. Ahaka baccin ya sake saceta.

Jaddatu zaune suna mgna da Hanan, Abie ya sakko waya yake cikin nutsuwa, ya na murmusawa.
Kusan Jaddatu ya zauna har ya kammala wayan, ya miqe ya ce“Ummina zanje hospital 'din Ummi qarama nazo.â€
Jaddatu ta beqa masa ruwan addu'ar da Abie 2 ya kawo ta ce“Ka bata ta sha ka shafa mata ajikinta, ah toh wannan aikin ai sai kai.â€
Abie ya furta.
“Masha Allah bari toh na bata sai na tafi.â€
Ya amsa yana nufar corridor 'din zai kai shi bedroom 'din da take dan ya haramta mata sama.
Kwance take sai wata irin mimmiqewa take tana ihu wanda muryata ta dishe bata fitowa sosai.
Auntie Saro na gefe tana mata addu'a tana hawaye.
Da sallama ya shogo 'dakin.
Auntie Saro ta amsa tana matsawa gefe, tana gaishesa cikin girmamawa.
Amsawa yay yana fa'din.
“Ayyah! Abin ya motsa? Tin yaushe ta farka?â€
Cikin kuka ta ce“Bata jima ba, naje kitchen maida plate 'din da naci abinci na isko ta farka.â€
Zama yay saman bed 'din ya kamota tana fizge² ya daka matsawa wanda hakan yasa tayi la'kwas ta bar abinda take tamasa 'kurr da idanu.
Murmushi yay ya rungumeta jikinsa ya riqeta sosai ya bata ruwan addu'ar, ganin ya na son shafa mata Saro ta bar 'dakin tana jinjinawa 'karfin imanin Abie ace yana kulawa da ita hakan bayan taji yana wasu maganganu irin Raiyana ta cutar da shi sosai.
Gabaki 'daya kayan jikinta ya cire mata ya shafe mata jikinta, da ruwan addu'ar ya mayar mata da kayanta, ya shiga karanto ma addu'a cikin kunnenta wanda ba'ayi 5 minutes ba bacci ya 'dauketa.
Ficewa yay daga 'dakin.
Abie 2 na zaune 'dakinsa falonsa 'dauke da Qur'ani ahannunsa yana karatu.
Abie ya shigo da sallama.
Amsawa yay bayan yakai 'karshen aya, lokacin Abie har ya zauna dab da shi.
Ya murmusa ya ce“Abien Rahmerh karatu ake?â€
Kai Abie ya jinjina yana murmushi, ya ce“Yau duk banga 'diyar albarka ba?â€
Abie ya shafi kwataccan sajan fuskar shi ya ce“ Bacci na barota tana yi may be idan ta farka ka ganta, muna godiya da karamcinka garemu Allah ya saka da alkhairi, ya jiqan magabata bari naje hospital na dawo, na fara shirin tafiya.â€
Ya miqe.
Abie 2 ya ce“Bari na muje yau duk ban leqosu ba.â€
Abie ya ce“A'a ba can ba hospital 'din 'yarka Rahmerh wajan gini fa!â€
“Ok muje kawai.â€
Ya rufe Qur'anin ya maidata ma'ajiyarta suka fice suna hirasu cikin raha.
Dukkansu suna bayan motar Abraham yaje suka tafi motar securities bayansu.

Ja'afar su na zuwa gida wanka yay ya canza kaya, ya tafi gidan Ma'aruf ya kai masa motarsa ya ba me gadi key 'din ya ajiye masa, yanata kiransa awaya ya fa'damasa da zaran taji sauqi zai dawo kan aikinsa, bai samu Ma'aruf 'din ba. Daga can hospital ya koma.

*Gabon*
Ranan da Aishatu ta fa'dama Ma'aruf labarin 'kawarta, ya shiga ta shin hankali. Ya na fita ya kira yaransa akan su tsayar da komai akan sai yazo, ya kashe wayoyinsa baki 'daya ya shiga nazarin rayuwa, da randa ya fara wannan mummunar sana'ar, a 'boye ba wanda ya sani a danginsa, haka nakusa ma da shi bai yarda ya saniba.
Cikin kwanakin baki 'daya baida nutsuwa, kullun yana gida kusanta ya na qara tsorata da lamarin, barin irin yadda yaji malaman suna wa'azi tabbas idan mutum baiyi gaggawar tuba ba 'karshensa baya kyau, dan zaiyi mutuwar wulaqanci.
Zaune suke ta yi matashi da cinyarsa tana kallonsa, shi kuma yana shafa cikinta.
Cikin sanyi murya ya ce “Wai lfy kika 'kuramin idanune?â€
Muskutawa tai ta ce.
“Uhmm! Ba kome naga kawai kwana biyu ka nutsu ba yawan fita ba yawan waya, kayi sanyi ka daina tsokanata, lafiyarka kuwa?â€
“Wlh lfy lau kawai yanayin rayuwane.â€
Damuwarta ta danne ta miqe zaune ta kamo hannayensa tana murzawa, tana kallonsa ta ce“Don girman Allah Ma'aruf ka fa'damin damuwarka na maka al'kawalin ba mai ji mu kashe mu binne, kai mijina ne kuma 'dan uwana idan na fallasaka kaina na fallasa, haka family 'dinmu na tuzarta, tare da 'ya'yan da zamu haifa, pls idan wani abune ka fa'damin na baka sharawa wacce zata fishemu.â€
'Dan guntin tsuki yaja ba tare da ya kalleta ba ya ce“Malama ba komai kinji.â€
“Shi kenan tinda ka ce haka idan damuwa da kake ciki nima na sakawa kaina damuwa idan mun rasa babynmu ai ka huta.â€
Ta 'karashe mgnar cikin kuka.
Rungumeta yay hankalinsa atashe ya shiga lallashinta.
Zaiyi mgna aka fara danna doorbell 'din falo, ya goge mata fuskarta ya ce“Pls je wanke fuskarki ba mamaki daga gidane wasu sukazo.â€
Kafa'da ta maqale tana hawaye.
Jin an qara dannawa ya nufi 'kofar ya leqa ya ga waye.
Ta hudar ya leqa Rabi'ah yagani cikin shiga mai kyau anci ubansu kwalliya.
Tsuki yaja ya bu'de 'kofar ya yi babakere ya tare hanyar yana ha'de fuska.
Ganinsa ya saka Rabi'ah washe baki tana wata irin karairaya ta gashesa.
Fuska ba walwala ya amsa ya ce“Bata nan.â€
Cikin murna ta ce“Yauwa sai muyi mgna na wuce ko? Tinda na kiraka ban samunka duk hankalina ya tashi, shiyasa nace bari nazo.â€
“A'a banda lokaci yanzu kije zamuyi waya.â€
Yana gama fa'damata haka ya maida qofa ya rufe, ya barta tsaye sororo da mamaki.
Aishatu ta kalleshi ta ce“Lafiya kai da waye?â€
“No! Karki damu wani ne yazo nemana nacema megadi ya ce bana nan, kaina yake ciwo bazan iya doguwar mgna ba, na tafi na kwanta, jibi zan wuce Tchad amman bazan sati inaga zan dawo.â€
Da kallo ta bishi har ya shige bedroom.
Tagumi tai tana tunanin ko ta nuna masa ta sani idan yaso suyi mgna.
Miqewa tai tabi bayansa.

*Tchad*

*Unguwar MOURSAL*
Tamfatsetsiyar hospital ne da ake ginawa da sunan Rahma, wacce aka sakawa suna.
( *RAHMA HOSPITAL TCHAD*)

Tinda motocin suka shigo hankalin ma'aikatan ya koma wajansu Abie.
Securities na bu'de masu mota ma'aikatan manya da 'kananu sukayi caaaa! Kowa na biqa gaisuwar ban girma wajan Abie.
'Dayan bayan 'daya sai da Abie yay musabaha da su fuskarsa sake yana tambayarsu ya aiki.
Mu'az ya iso yana fa'din.
“Tinda kun gaisa kowa ga koma bakin aikinsa.â€
Abie ya murmusa ya ce“Mu'az ya hkr da jama'ah?â€
“Yalla'bai Alhmdllh! Gini ya kusa zauwa 'karshe insha Allah. Bismillah mushiga.â€
Cikin office suka shiga bayan sun qara gaisawa Mu'az ya ce.
“Yalla'bai bari na kira mutumin sai kuyi mgna.â€
Bai jima da fita ba suka shigo da wani magidanci zai kai kimanin shekaru 37 ahaife, fari yafi ruwan zubin fulani, yanada kyau, ba laifi babu makusu ajikinsa, kallo 'daya zaka masa kasan idan ya samu Hutu namijine ba laifi duk da baikai Ja'afar ba bare Abie akyau amman tabbas namijine, cikakke.
Har 'kasa ya zube yana gaishe da Abie cikin girmamawa.
Abie ya amsa cikin sakin fuska yana kamasa ya miqe ya zaunar da shi kusan shi, yana fa'din.
“Ance ka jima kana nema na, Allah yasa lafiya?â€
Kansa 'kasa ya ce“Eh Alhaji Abdulmajid na jima ina nemanka amman ba na samunka, don Allah don darajar Annabi Muhammad.â€
Abie 1 and 2 da Mu'az suka amshe da fa'din.
“S.A.W.â€
Cikin kamalarsa Abie ya ce karka damu yaro ina jinka fa'di abinda kake so ka fa'daâ€
Kansa 'kasa ya ce.
“Don Allah Alhaji kayi min alqawalin zaka temakamin da abinda zan roqeka, sannan ka fahimcine ka kalle da idanun rahamar da Allah ya maka? Sannan ka yarda da mgnar da zqn fa'da maka.â€
Abie ya kafeshi da manyan fararen idanunsa, ya girgiza kansa ya ce“Ni ba mutumin banza bane, ba zanyi alqawalin abinda bansan meye ba, na amsa ma nazo na kasa cikawa na shiga layin mutane ukun da Annabi ya lissafoi, fa'di karka damu idan wanda zan iyane zan maka.â€
Kansa 'kasa ya fara mgna.
“Ni sunana Hisham Tahir har'do bafulatanin Cameron ne, munada arzi'ki irin namu na fulani arzi'kin shanu da raguna tumakai.
Kwanaki mun shigo garin nan kenan munzo wajan auren 'yan uwanmu da suke nan, saman titi munzo tsallakawa naga wata yarinya ta fito daga mota, ta nufi wajan wani dattijo da niyar taimaka masa wanda....â€
Abie 2 ya katse shi ta hanyar cewa“Kai!....â€
Abie 1 ya katse shi ta hanyar cewa.
“Please Abdulmajid barsa ya yi mgna, ina jinka me ya faruwa da dattijon........?â€

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/1/22, 18:08 - Buhainat: ```D A```

```45&46``

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

_🥺Hajiyoyi Ba Editing😔_

Hishm kansa ya girgiza ya ce. “A'a ba wai dattijon yay wani abubu, muna tsaye ne muna ganin yadda ta nuna tausayinta wanda agabanmu duk abinda ya faru ya faru, na temakon da ta masa wallahi bazan 'boye makaba na kamu da matsanaiciyar 'kaunarta, tin daga ranar ban sake zama lafiya ba, duk da kallo 'daya na mata nasan ba tsarata ba ce, ba jansin mu 'daya ba, amman na nace sai da nayi bincike akanta.
mun bisu har gidan a mota wanda tinga gate nasan tabbas tamun mugun nisa, amman na kasa hkr inata bincike aka fa'damin min 'yarka ce kai kuma daman mun sanka a Tv sunanka ya zaga duniya da hotonka kowa yasan kai mai temakone mai jin 'Kaine zakayi komai domin kaga wani ya kasance cikin jin da'di, yanzu kusan wata biyu kenan ina famar nemanka wlh yanzu ko gate 'din gidanka sun hanani zuwa ance sai an harbeni, nan ma nasha zuwa amman ban ta'ba samunka ba. Dan Allah ka temaka ka ban auren Rahma karka duba tazarar da take tsakaninmun.â€
Ya 'karashe mgnar cikin kuka yana riqe 'kafar Abie.
Abie wani irin bugu yaji zuciyarsa nayi kansa ya shiga sarawa, cikin jarumtarsa yay azamar tattaro nutsuwarsa ya 'ka'kalo murmushi wanda bazaka ta'ba gane yadda yake ji acikin zuciyarsa ba, kasancewarsa mutum wanda yake me 'boye abu zaiyi wuya ka fahimci halin da yake ciki na damuwa.
kamo hannun Hisham yay yana kallonsa cike da dattakunsa ya ce.
“Haqiqa naji da'di nayi farin cikin 'kaunar da ka nunawa tilon 'yata guda.
Sai dai kash! Wallahi tanada aure, an jima da aka 'daura mata aure, sai ta gama karatunta za'ayi bikinta, kayi hkr don Allah mun gode da 'kaunarka garemu.â€
Abie 2 da kallon mamaki! Yake bin Abie 1. Yayin da Hisham yake fa'din.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una! Haqiqa nayi kuskura acikin rashin sani na kamu da soyayyar abun da yake haramun agareni. Astagfirullah don Allah ku yafemin, rashin sanine zan roqi Allah ya cire min sonta azuciyata.â€
Ya 'karashe mgnar yana kuka kamar wani yaro 'karami.
Abie lallashinsa yay tare tare da cewa.
“Kayi hkr Hisham, tabbas da batada aure da na aura maka ita matuqar tana sonka.â€
Sosai Hisham ya ji da'din yadda Abien ya nuna kulawarsa akansa.
Godiya yay ma Abie ya tafiyarsa cike da damuwa cikin zuciyarsa, dan ba qaramin so yakema Rahma ba.

Sosai Abie ya nunawa Abie 2 asibitin mai girman gaske kafin su nufi hospital wajansu Malam Adamu.
Yanzu ma Ja'afar ne zaune saman kujera gefen gadon, Ibtisam na bacci yayin da su Mal Adamu suke waje zazzaune.
Da sallama su Abie suka iso wajansu.
Bayan sun gaisa Abie yake tambayar ya me jiki,duk suka amsa “Da sauqi.â€
Abie office 'din Dr Salis ya nufa.
Bayan sun gaisa ya ce“Dr yarinyar nan haka zamu tafi da ita idanunta biyu? kasan fa! Irin abubuwan da take nunawa.â€
Dr Salis ya ce“A'a yalla'bai anjima idan tafiyarku ya kasance bai fi 1 hour ba zan mata allura insha Allah har kuje bazata iya komai ba, daga baya zatayi bacci mai yawa.â€
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce“Ok hakan yayi Allah ya nuna mana.â€
Sallama sukayi, ya
fito ya shiga room 'din da Ibtisam take kwance.
Ja'afar ya amsa sallamarsa ya gaishesa cikin girmamawa.
Abie ya ce“Ja'afar ya me jiki? Allah ya qara sauqi, ya kamata kaje ka shirya lokaci na qaratowa, idan ka shirya sai ka taho muku da kayan sakawa harda na Ibtisam,idan kazo suma sai su tafi da mun dawo 'daukarku ne zamuyi muje airport.â€
Ja'afar ya amsa da “Toh Abie Allah ya saka da Hairan. â€
Abie ya fita yana amsawa da “Ameen ya Rabbi.â€
Abie na fita Ja'afar ya koma bakin gadon ya rankwafa ya sumbaci kumatunta da hancinta ya shafi fuskarta, dab da kunnenta ya ce“Allah ya baki lfy.â€
Kwanciyar ya gyara mata ya fito.
Mal Adamu ya ce“Kaje ka shirya idan kazo sai mutafi su Tanko su shirya, ni gobe zan wuce niger.â€
Ja'afar yay musu sallama ya fita ya samu taxi ya shiga ya tafi.

Tafe suke dukkansu abayan mota, Abie yana leqa wani saqon email.
Abie 2 ya ce.
“Abdul Majeed daman 'diyar albarka ka jima da ka mata miji? Haba! Shiyasa ka tashi hankalinka, ka saka idanu sosai tsakaninta da Ja'afar kullun ina tsakiyarsu idan suna fira, amman ban ta'ba ganinsa ba.â€
Abie ya ajiya phone saman cinyarsa ya kalli Abie 2 yana murmushi ya shafi sajan fuskarshi, tare da 'Yar 'kasumbarsa wacce tai masa kyau, yana Jan gemunsa, ya ce.
“Uhmm! Tin tana shekaru 12 aka 'daura auren tin mahaifina na raye wanda dalilin auren da ya 'daura mata Naja'atu ta kasheshi, wata 'daya bamu sakeyi ba 'kasar morocco.â€
Ya qarashe mgnar cikin 'kunar zuciya yana dafe goshinsa tun tuni jijiyon kansa sun fito ra'do² alamun ransa ya 'baci, jikinsa ya shiga tsuma tsanar mata ta mamaye dukkan sassan jikinsa.
Ganin halin da ya shiga Abie 2 ya rikice ya riqeshi yana fa'din “Subahanallahi! Kisa mahaifinka? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!â€
Har suka iso gida Abie bai dawo normal ba.
Bayan sun fito daga motar Abie 2 ya ce“Dan Allah kayi hkr Abdul Majeed wlh bansan irin wannan 'kuncin zan tuna maka ba, da bazan tambayi mijin Ummi ba, Allah ya jiqan Abbu yasa ya huta, ai kai kaji da'dinka ka girma da iyayanka ni kuma da ban sansu bama tin ina tsuman goyona suka rasu.â€
Abie ya ce“Lah! Ba komai karka damu, sannu Allah ya jiqansu, ai fa ka shirya mata zan maka nan kusa, amman ka za'ba ka darje zaifi bari na shiga ciki lokacin la'asar ya gabato.â€

Jaddatu zauna Latifa na zuba mata shayi, sai mita take batajin 'kamshin kanafari yana tashi sosai.
Latifa ta ce“Wlh Jaddatu kamar yadda nake sakawa kullun ne.â€
Baki ta ta'be ta ce“Yo Allah na tuba Latifa rantsuwa da tana kasheki ai kin jima da mutuwa. Ki fa'dawa ummu Adnan ta min dambu nama na rago kinga na shanun ciwon 'kafafu suke sakani.â€
Latifa ta amsa da “Tom.â€
Ta danne dariyarta ta tafi.
Hanan na musu dariya.
Abie ya sallamo ya shigo falon.
Kusan Jaddatu ya zauna, tana masa sannu da zuwa.
Amsawa yay ya tsiyayi shayin yana kur'ba.
Jaddatu ta ce.
“Ya naga yanayin ka ya canza?â€
Cikin zafi² yake shan shayin ya ajiye cup 'din ya miqe yana fa'din.
“Kaina yake ciwo bari nasha mgani, Hanan ba gaisuwa? Ina baby Iman?â€
Ya 'karashe mgnar yana tafiya.
Hanan ta amsa da “Wlh Ya Abdul na gaisheka naga kamar baka cikin nutsuwane Iman bacci take, sannu Allah baka lfy, wai ina ummine?â€
Da “Ameenâ€
Ya amsa yana tafiya ya ce“Tana bacci na barta, ban saniba ko ta tashi ta tafiyarta.â€
Kofar falon ya mur'da ya shigo da sallama, shiru alamar bata farka ba.
Bedroom 'din ya nufa.
Kwance take ta yi 'dai-'daya saman royal bed 'dinsa,ta yaye bargon da ta rufa, ga sanyin Ac ya kama 'dakin sosai sai rawar sanyi take.
Idanunsa ya sauka kanta santala² fararen cinyoyinta matasa duk awaje.
'Kafarta mai 'daure da sarqar zinari ya kalla duwatsun sai walqiya sukeyi, yanayin yadda take rawar sanyi ya sanya 'kafarta me sarqar take sakin qara cakasss tamkar tana tafiya.
gashin kanta ya barbaje ya rufe mata fuska, ta rungume pillow saman 'kirjinta.
Murmushi 'dauke kan fuskar shi yay saurin isa dab da 'kafafunta, ya sanya hannunsa ya cire mata sarqar qafarta ahankali yadda bazai tasheta ba.
'Kafar ya sumbata ya ajiyeta 'dam, ya 'dora sarqar saman bedside drower, ya 'dauki remote ya kashe Ac ya kunna na'urar 'dumama 'dakin.
Ya qarasa bakin bed, ya zauna ya sanya tattausan ya 'dauki kanta ya 'dora saman cinyarsa, motsi ta fara ahankali.
Leqo fuskarta yay, yaga bacci take tana cinno 'dan 'karamin bakinta.
Guntin smile yay, ya tattare mata gashin da ya rufe mata fuska, ya 'daure shi.
Awarwaron hannayenta ya shiga zarewa ahankali, ha ya zarosu.
Sarqar wuyanta ya cire mata, har 'yan kunnen, ya mayar da ita ya kwantar yadda zatafi jin da'din baccin.
Sumbatan la'bbanta yay yana jan siririn dogon hancinta, ya manna mata kiss saman idanunta.
Ya nufi bedroom.
'Kananun kyawawan idanunta ta bu'de tabi bayansa da kallo tana sakin murmushi.
Sai da ya shiga ta ce“Abiena tin fa kana ciremin sarqar 'kafata na tashi.â€
Cikin bargon ta shige tana shaqo 'kamshinsa mai sakawa taji nutsuwa.
Abie alwala ya 'dauro lokacin da ya fito ana kiran sallar la'asar.
Kallonta yay ya ga ta rufe dukkan jikinta.
Fita yay zuwa masallaci idan ya dawo sai ya tasheta.
Yana fita ta miqe zauna, tana miqa ta sauko, bathroom ta shiga ta cika bathtub da ruwan 'dumi ta shige ciki ta kwanta.
Ta jima sosai kafin tai wanka ta fito, ta 'daura alwala.
'Daure da towel ta fito tana riqe da kayanta.
Motsi Abie taji afalo duk sai ta rikice.
'Katuwar wardrobe 'dinsa ta bu'de wacce take shaqe da sutturo iri² 'bangaran jallabiya ta kalla ta ciro wata ruwan toka sabuwa dal tai saurin sakawa jikinta ba tare da ta cire towel 'din ba, hirami ta janyo shima sabo ta rufe masa wardrobe 'dinsa.
Turarensa ta fesa ta cire towel 'din ta ajiye saman bed ta hau darduma ta tayar da sallah..
Abie na zaune falo yana waya, ya kai 20 minutes kafin ya gama ya miqe ya nufo bedroom 'din.
Ta gama sallar karatun Qur'an take.
Murmushi yay ganin kayansa jikinta sunyi mata kyau sosai, duk da rigar ta mata mugun yawa.
Bai mata mgna ba ganin tana karatu, ya shiga ha'da kayansa, kala 4 ya 'dauka sai na bacci kala 2 sbd kwana 2 ne zaiyi ya juyo. Sai da ya gama shirya kayansa cikin 'karamar trolley ya 'dauki duk abinda zaiyi anfani da shi, ya zauna saman kujera yana duba saqonnin email.
Rahma anutse ta gama karatunta tai addu'a ta shafa ta miqe ta maida Qur'an wajansa, ta linke dardumar ta ajiye ta muhalinta, ta gyarama Abie bed 'dinsa tsab.
Awarwaronta da sarqar wuya da ta qafa ta kwashe ta nufi wajan Abie.
Kusansa ta zauna, ashagwa'be ta ce.
“Abie rabin raina ina bacci ka ciremin kwaliyata, maida min toh.â€
Kallonta yay ya kwaikwayi mgnarta.
Kumatunsa ya beqa mata.
Tasan me yake nufi.
Fuskarshi ta riqe ta manna 'dan 'karamin bakinta saman kumatunsa ta sumbata, itama ta basa kumci.
Sansanyar Sumba ya mata akumatunta,wacce ta maqale masa ta tura kanta cikin 'kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya.
Anutse ya sanya mata sarqar da awarwaron ya sanya mata ta qafar ya sumbaci 'kafar, 'dan kunnen ya sanya mata, yana gyara mata bichons 'kananun 'yan kunnen wanda ya kasance tilla ukune jera akunnenta, biyun sai ta saka 'yan mitsi² 'yan kunne na gold.
Ashagwa'be ta riqe hannunsa tana fa'din “Aushhhhh! Abiena zafi kawai ka cire min toh.†hura mata wajan yay yana shafawa ahankali ya ce.
“No! Baby sunyi kyau barsu idan naje Australia zan siyo miki mask kyau na diamond.
Baby ki kace gobe kike son wucewa ko?â€
Cikin murna ta amsa tana kallon 'dan 'karamin jajayen la'bbansa tana langwa'bar da kanta.
Kallo 'daya yay mata yay saurin Janyeta jikinsa ya na miqar da ita tsaye, yana murmushi sbd ya lura da ita ba abinda take so irin tai ta ma sa kiss le'bensa.
Hannunta ya kama ya 'dauki wayarta suka fara tafiya.
Ashgwa'be ta ce“Abiena bakece komai ba?â€
Kwaikwayonta yay ya 'dora da cewa“Za ki tafi baby ummina muje kici abinci.â€
Asakalce ta ce“Wayyo Abiena wlh banjin yunwa pls ka barni nayi fira bankwana da kai.â€
Kallonta yay ya kashe mata ido 'daya yana sakar mata 'kayataccan murmushi.
Baki ta turo.
'Kasa suka sauko tana maqale da hannunsa.
Jaddatu da Hanan suka bisu da kallo.
Jaddatu da gaza gani ta ce“Oh! Yau shagwa'bar saka kayan Abienki ne?â€
Rahma ta ce“Eh kuma dasu zan zauna har gobe wlh bazan cire ba.â€
Dariya Jaddatu tai ta ce“Ma Sha Allah MATAR manya 'yar manya.â€
Hanan ta kalleta Jaddatu ta ce“Wlh Hanan masifar gulma gareki ai fatan alkhairi nai mata kuma 'diyar Abdul Majeed ai 'Yar manyan mutane ce.â€
Abie baice komai ba yaja suka tafi kan dinning area, zaunar da ita yay.
Ya shiga ha'da mata lafiyayyan girkin.
Ashagwa'be Rahma ta ce“Abiena kanaji matar manyan mutane ce ni, halan ba yaro bane mijin nawa rabin raina ni dai gaskiya bazan xauna da babba idan ma irin halinka gareshi.â€
Rankwafowa yay ya sumbaci la'bbanta da gashin idanunta wanda suke gazar².
Akunnenta ya ra'da mata.
“Babyna bazaki iya son duk abinda na baki ba? OK ai mun gama mgna nace idan bakyaso dole zai sakeki.â€
Ya 'dago ha'barta yana sakar mata tsadaddan murmushi.
Kanta ta samu da fa'duwar gaba ta shafi fuskar Abie tana Jan tsinin karan hancinsa, tai raurau da ido tana son ta yi mgna ta kasa.
Kumatunsa ya bata.
Ahankali ta manna masa Sumba tana kwantar da kanta kafa'darsa.
Da kansa ya ciyar da ita yana mata waqa mai da'din gaske wacce tin tana yarinyar 'yar shekaru 3 idan yana mata take samun nutsuwa sosai.
Ai kuwa sai gata tana 'kyal'kyala dariya ta 'dare saman cinyarsa tana kallon bakinsa yadda yake waqar cikin 'kwarewa.

Misalin 'karfe 6 su Abie suka gama shirin tafiya, sosai sai da yaba Raiyana kulawa, da barmusu duk abin buqata, da wanda za'a tarbi malamin da zaizo mai maganin aljannu, kafi yabar gidan.
Rahma harda kukanta Abie ya samu dakyar ya lallasheta ya ce zai biya wajanta ya kwana kafin ya dawo Chad.
Har airport Rahma tai rakiya, su Baba Tsalha Harisu Yahuza Mal Adamu Abie 2 duk suna airport, sai da jirgin su ya cira sama suka nufo gida.
Mal Adamu da Abie na rarrashin Rahma tanata kuka kamar Abien ya tafi kenan.

Acikin jirgi kuwa Ja'afar bai ta'ba hawa jirgin sama ba aman cikin ikon Allah sam baiyi 'kauyanci ba, sbd aganinsa komai sa kaine.

Sa'bani Laraba da ta dinga 'kurma ihu tana fa'dun.
“Wlh ni daman nasan duk abinda aka ha'da da yaron nan Jafaru sai an ha'du da masifu acikinsa.... Wayyo Allah kaina na juyawa zanyi amai...â€
Tanko cike datakaicin ya ishesa ya buge mata baki, ganin jama'a na kallonsu.
Kasancewar kusan Abie suke dan dukkansu Vip ya biya musu.
Kai Abie ya girgiza yana mamakin halaiyar Laraba.
Tanko fa'da ya fara mata kamar ya ari baki.
“Wlh badan jirgin ya tashi ba, da mun FASA tafiyar nan Ja'afar ya isa ya kula da matarsa, tinda ko munje
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment