Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

agaskiya bazan d'auki wulak'ancin uba ba na d'auki na d'iyarsa, haba! Abin yayi yawa, yarinyar nan jiji da kai gareta, ke muma fa jansin larabawane, banga wata d'agawa da zasu mana ba, dan suna larabawan Marooco ...�
“Ke! Raiyana ki rufawa kanki asiri ki zauna gida mafi daraja da miji mai kima da daraja da dattaku,yanzu kaf layin unguwarmu da gidanmu ake kwatance, ko kinfi son kizo mu zauna mu had'u muna zawarci ana zaginmu a unguwa? Bakya tausayin kanki, shekaru talatin da d'oriya baki aura ba Allah yaji k'anki ya miki gyad'ar dogo, amman kikeson watsar da ni'imarsa ki kaso auren? Toh wlh ba ruwana, wannan yarinyar da ba damuwa tai da lamarin mutane ba me zata miki?�
Raiyana jikinta yay sanyi ta ce“Uhmm! Auntie Saro bazaki ganeba, tsakani da Allah dan dai najima banyi aure ba nayi shine sai na d'auki cin fuska? Ni fa bansan me na mataba take shareni.�
Saro ta ce“Dan Allah ki sawwaqa ma kanki da damuwar mutanen gidan nan, zauna kici arzik'i iya cinki idan kinci kin tara bai kusancekin ba sai musan yadda zamuyi akwai hanyoyi masu sauqi fa!�
Raiyana ta ce“Nifa mugun sonsa nake ba wai kud'in kawai nake so ba.�
Auntie Saro ta kwantar mata da hankali tana fahimtar da ita abubuwa daban-daban tabi asannu har ta fahimci wasu abubuwan ta watsar da mgnar Rahma.

Jaddatu tin daga nesa take fad'in.
“Taje ta shiryo miki k'arya ko? Latifa akwai naci wlh.�
Rahma zama tai dab da Jaddatu ta kwantar da kanta kafad'arta ta rungumeta tana sakin murmushi, ta shafi fuskarta, tai mata kiss akumatu ta ce“Ina sonki Jaddatina.�
Ta kalli Latifa ta ce“Jeki karki damu.�
Latifa ta zube gaban Rahma ta ce“Ngd Allah ya tsareki da tsarewarsa uwar d'akina insha Allahu miji mafi daraja da tsad'a za ki aura.�
Ta mik'e ta tafi cikin murna.
Jaddatu bata ce komai ba, ta sumbaci goshin Rahma ta ce“Je kiyi abinci, meyasa kika kashe wayanki Abdul Majeed ya buwayeni da Kira? Me Raiyana ta miki kika shareta?�
Rahma ta yamutsa fuska tana rau-rau da k'ananun idanunta, ta turo jajayen k'ananun labb'anta gaba ta ce“Yo ni me nayi?�
Daga wannan mgnar bata sake magana ba, ta janye jikinta ana Jaddatu ta nufi k'aton dining area d'in mai d'auke da kujeru 12.

Bayan ta idar da cin abincin ta dawo falon, Raiyana da Jaddatu sunata hirasu.
Bata ce musu komai ba, daman sunsan bazata ce ba, ta shige jikin Jaddatu ta canza channel, zuwa MBC 2 tana kallon wani film na larawa. Sosai ta shiga kallonsa atsanake.
Raiyana ta kamo lallausan hannun Rahma ta ce“Baby ummi! Abienki ya ce idan kin ta shi kinyi abinci muje akai mu ki zagaya k'afafunki.�
Rahma ta juya kyawawan k'ananun idanunta, ta ce“No! Ammi Thanks bari sai gobe.�
Raiyana ta amsa da “Allah ya nuna mana.�
K'asan labb'anta ta amsa da.
“Ameen�
Abdul Majeed aranan bai samu kansa ba sai dab da magarib ya shigo gida, acan b'agaransa na k'asa yay alwala ya tafi had'add'an masallacinsa da yake game da gidan, wanda k'ofofinsa suke daga waje, wanda, bai fito ba sai da akayi sallar isha'i, shima yana fitowa ya taras da bak'o ak'ofa wanda masu gadi sun hanasa shiga sun ce ba'a fad'a mu su bak'o zai zo ba.

*Niger*
Su Ja'afar sai kusan goma na dare suka shigo garin damagaram, agajiye sabida sosai direbansu yay gudu.
Bayan bus ta saukesu nan cikin k'aton gidanta na ( *Sonef*) akwai bandaki wajan wanna ga bokatai nan da panpo.
Bayan sun yanki ticket d'in zuwa diffa, wanda bus d'in zata tashi k'arfe 4:30 am na asubah, wanka sukayi su ka siyo abinci sukaci, daman sunyi sallolinsu ahanya, suna gama cin abinci suka kwanta.
Ja'afar ya kasa bacci sai juyi yake yana tunanin iyayansa da Ibtisam.
“Ya Allah!�
Ja'afar kira cike da damuwa kwance akan kyakkyawar bak'ar fuskarshi.
Wayansa ya zaro tuna lokuta da dama, Ibtisam na kwana da wayan Babanta, wajanta, idan ya bata tai game, sabida yanada waya mai yin WhatsApp sabida 'yan uwansa nan Cameron.
Ta nan suke samun suyi zumunci sabida kud'in kira tsada.
Cikin k'warin guiwar samun Itibsam Ja'afar ya kira number Tanko.

*TAHOUA*
Ibtisam wunin yau sakoko ta yisa sabida rashin Ja'afar d'inta, tin Laraba na masifa bayan ta jibgeta ta ga dai abun na gaske ne, tsoron karta kwanta musu jinya dan ciwo ba wuya ba ne wajan Ibtisam ya saka ta shiga lallashinta.
Kamar lokuta dayawa yadda Tanko ya saba bata wayan yauma ya bata, ta yi game, amman bata yi ba, ta gwada kiran number Ja'afar yafi sau talatin bata shiga.
Haka tai ta kuka ab'oye tana rungume da wayan, har b'arawo bacci ya saceta.
Cikin baccinta taji ringing d'in wayan.
Ai kuwa ta zabura ta mik'e zaune tana bud'e manyan idanunta wanda suke cike da bacci, tana murtsikesu, tana fad'in.
Ya Allah kasa Mon Amour ne.�
Ta k'arashe mgnar tana kallon screen d'in wayan.
Cikin farin ciki ta d'aga kiran tana kai wayan kunneta, ta kalli k'aninta bacci suke sosai, daman tafi tsoron Aydah mai shegen bakin qarya.
Cikin zallar shagwab'arta ta sakar masa kuka k'asa-k'asa, tana kiran.
“Mon Amour! Kewa ina kewarka ya zanyi?�
Daga can Ja'afar ya mik'e yabar wajan dan kar ya shiga hakk'in masu bacci, cikin tausasa murya da amon muryasa mai dad'in sauraro ya kirata.
“Mon cœur! Svp ki daina kukan nan kinji, yi shiru kiji ke bakya murna na samu ganawa dake?�
Ibtisam ta had'iye kukan nata ta langwab'ar da kanta kamar tana gabansa, ta shagwab'e ta fara mgna cikin rauni.
“Toh Mon amour na yi shiru, don Allah kana ina yanzu? Fata duk inda kake kana cikin lafiya da makwanci mai kyau?�
Ta k'arashe mgnar tana sakin sabon kuka mara sauti.
Goshinsa ya dafe yana takunsa cike da izzarsa wacce sam bazaka tab'a cewa shi ba wani bane ak'asar nan, bayan suturun jikinsa da su ka nuna ko shi waye.
“My Ibtisam! Haba! Tawan pls ki daina wlh idan ba haka ba, bazan kuma kiranki ba...�
Katse shi tai ta hanyar sakin siririyan dariyar k'arfin hali ta marerece murya ta ce“Kayi hkr toh Mon amour na daina, bani labarin kana ina?�
Laraba da fitowarta kenan daga makewayi sabida tuwan tsakin da taci ya tab'a mata ciki, karaf taji mgnar Ibtisam k'asa².
Butar ta ajiye ta nufo d'akinta tana tura k'ofar cikin sa'a ba sakata ta fad'o d'akin, ta warce wayan tana kai kunnenta, taji mgnar Ja'afar tace“Iyeeeee! Ba shakka! Daman hakan ka koyama d'iyarmu?�
Ja'afar jin mgnar Laraba gabansa ya fad'i ya tsinke kiran dan yasan ba sauraransa zatayi ba.
Ibtisam kuka ta sanya ta ce“Ba laifinsa bane Anna ni na kirasa...�
Duka Laraba ta kai mata, ta ce“Kimin shiru dan ubanki zanga wanda zai qara baki wayan, ai duk laifin ubanki ne, zo maza rufe k'ofar waton ahaka kuka kwanta ba sakata ko?�
Ibtisam tana kuka ta mik'e bayan Laraba ta fita ta rufe k'ofar ta fad'a saman yaluluwar katifarsu kusan Aydah ta kwanta tanata ruzgar kuka harda majina.
Cikin masifa ta fad'o d'akin tana shiga buga k'afar Tanko.
“Malam tashi wlh idan yarinyar nan ta lalace kaine sanadi! Ashe wayan da kake bata ita wancan miskilin yaron suke raba dare suna waya? Sbd Allah ka kyauta ka d'auki babban waya kabawa d'iya budurwa cikin talatainin dare tana waya da k'ato.�
Takon ya mik'e zaune yana amashe wayansa, ya ce“Shine dan d'aukan hankali irin naki kika ta sheni? Nasan wacece Ibtisam shiyasa na bata wayana na yarda da ita insha Allahu addu'ar da nake ma yarana ba wani abun mai muni da zai faru dasu ba! Na sani tana waya da Ja'afar mak'iyinki ba, zo ki kwanta.�
Ya k'arashe mgnar yana koma ya kwanta. Har tai masifarta ta gama bai tanka ta ba sabida yasan tana tsoron yarinyarta ta lalacene.
Ja'afar haka ya kwanta zuciyarsa cike da k'unci yasan har dukanta sai Anna tayi shine ya damesa.

*Tchad*
Rahma yau fushi ta yi da Abienta ko da su ka had'u akan dining area wajan dinner, bata kula shi ba, ya mata mgnar duniya tai bazan da shi k'arshe ma ta sanya masa kuka.
Jaddatu da Raiyana ne masu lallashinta, tana gama cin pizza ta d'auki k'aramin jug wanda Ummin Adnan ta had'a mata fruit d'in 'ya'yan itatauwa masu dama ta haye sama, tana kiran Latifa ta zo ta mata tausa.
Jaddatu ta kalli kyakkyawan agogon da yake manne jikin bango, ta ga 10 na dare ta d'an wuce, tai ta dariya tana fad'in.
“Yau gaskiya Abdul ka tsayar damu sosai ashe dare yayi haka? Duk da sai 9 ta wuce muke dinner amman yau mun makara.
Yau fa wlh mugun halin take, Raiyana kinga ni ko ke har kika damu kanki, halin Rahma sai ita mai rikicin gan gan.�
Raiyana ta kalli Abdul Majeed wanda ya maida hankalinsa akan wani had'anda'an system na company iPhone.
Sanye yake da fararen kaya riga da wando na sanyi masu taushi, sai wani irin fitinannan k'amshi yake tashi ajikinsa. Farin glass manne akan kyakkyawar fuskarshi, mai fitar da annuri.
Cup d'in glass mai kyawun gaske ya d'auka ya kai daddad'an shayin bakinsa, ya kurb'a ya ajiye.
Da tsinin ido yake kallon yadda Raiyana ta k'ure shi da ido.
Hankalinsa ya maida wajan Jaddatu ya ce“Ummi Afuwan wlh tinda na fito daga sallar isha nayi bak'o daga Jos ta Nigeria dole zanji da shi, ba kiga sai Kira nai aka kai masa abinci, kuma yau ya juya yanada kyau dukkan mutumin da ya d'auko k'afar shi yazo daga wani garin ko wata k'asa ka saurare shi ka masa tarba mai kyau, sabida kai ma gaba bakasan ko zaka nemi wani temakon wajansa ba ko wajan wani shak'ik'insa, bare wannan harakar kasuwanci ta had'amu. Uhmm! Bari naje biko Baby Ummi, na mata bayani yanda zata fahimceni, ba lallai ta yi baccin kirki anata fushi da Abienta, na rasa wa baby ummin ta biyo rigima?�
Raiyana aranta ta ce“Wannan gyatumar taka mana, kaima ai kanada kuji shi d'an ak'ida kawai, sai na cinye jarabawarka, insha Allah.�
Jaddatu ta ce“Jeka maza, nima bari naje na kwanta.�
Hannun mahaifiyarsa ya kama suka nufi b'angaranta.
Sai da ta kwanta ya ce“Abokiyar kwan naki dai jibi zata dawo.�
Dariya Jaddatu tai ta ce“Ai kam asha rigima Allah ya nuna mana da ran da lafiya.�

Baiga Raiyana ba a falon sai Tv take surutu, ya rufe dukkan k'ofofin ya kashe Tv da fitulun falon, ya d'auki system da wayoyinsa ya haura sama, kai tsaye beni na 2 ya wuce wajan Rahma bai tsaya ajiye kayansa ba!..._*Yar Ajin Tubarkallah🥰*_



*DATTIJON ARZIK'I* N300 katin MTN ta wannan number *+22796515805*


TSINTACCIYA
Nimcyluv

SULTAN
mss flower

BAK'AR FATA
AUTAR MANYA



Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218


*Real Ladingo+22796515805* For more information😇

_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/2/22, 09:18 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_


*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_
🔥FITATTU HUƊU🔥*


_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_


_Labarin nan zan iya kiransa da *BAKANDAMIYATA🥰* tabbas. Kusan meyasa nace hakan? Humm! Muje zuwa. Tabbas salon labarin cike yake da zallar k'auna da soyayya mai rikitarwa, shak'uwa iya shak'uwa, akwai rikita-rikita, da_ chakwakiya _wacce duk iya tunanin mai tunani ba lallai yaje inda nake son zuwa ba. akwai abubuwan k'aruwa darusan rayuwa salon love mai tsafta mai_ _tsuma zukata, hajiya karki yi jinkiri wajan siyan labarin nan, ki cije ki shigo daga ciki adama dake, ni dai bakina da taba, tabbas bazan baku k'aran hasken komai ba ayanzu, kune za ku d'auka alokacin da free page yazo gangara,👌�latsa nan hajiya kai tsaye ki sadu da marubuciyar_ *dattijon arzik'i🥰*. Don girman Allah idan ba siya zakiyi ba karki tab'oni.��
👇�
*Http://wa.me/+22796515805*



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


_*cнapтer 9&10*_

A k'ofar d'anki ya tsaya ya na knocking, had'i da kiranta, cike da tausasa muryasa me nutsuwa da kamala.
“Baby Ummina bud'e ga Abienki yazo ya lallashe ki.�
Rahma wacce take kwance saman tamfatsetsan royal bed d'inta, ya sha lafiyayyar shimfid'a sanye take da riga da wondo na bacci, wandon iya guiwarta rigan doguwa har k'asa, mai bud'add'an gaban.
Wani irin kyau ta yi, dogon gashinta mai samtsi da laushi, ya baje saman k'aton pillow'n yayin da rabinsa ya rufe mata fuska.
Ahankali take jin sautin daddad'ar muryar Abienta na ratso ta falon ta, kai tsaye ya zarce har bedroom d'inta, ta shige dodon kunnenta.
D'an k'aramin bakinta ta turo gaba, had'i da muskutawa, yayin da ahankali ta fara qoqarin bud'e k'ananun kyawawan shanyayyun idanunta, wanda sun b'ata lokaci a lumshe, tana aikin janyo numfashinta wanda yake sama yana qasa.
Tar ta bud'e idanunta had'i da yink'urawa ta zauna saman bed d'in, jin har yanzu daddad'ar muryan Abienta na ratso dodon kunnenta.
Gashinta da ya rufe mata fuska ta janye gefe, ta yink'ura ta sauko, ta d'aure rigar baccinta da igiyoyin gaban rigan, ta sanya silipas ta nufi hanyar falon tanata qoqarin fizgo numfashinta wanda yake ta mata farazanar d'aukewa ba tare da k'wak'waran dalili ba.
Key ta murza ta bud'e k'ofar, ba tare da ta kalli Abien nata ba, ta kalli k'asa tana wasa da zara² fararen yatsunta wad'anda suka Sha zanen Jan lalle.
K'afafun Abienta ta kalla farare tass sanye da silipas, dab da su system d'insa ne ya ajiye ya d'ore wayoyinsa a sama.

Abdul Majeed ya zubawa 'yar tasa narkakkun idanunsa, ya saki wani irin guntin smile, ahankali ya tako zuwa dab da ita, wanda fitinannan k'amshinsa ya buwayi hancinta.
Tattausan hannunsa ya sanya ya janye mata dogon gashinta,wanda ya rufe mata kusan dukkan fuskarta, ya d'an rankwafo ya lek'o fuskarta, yana sakin smile.
idanunsa akanta ya kusanto fuskarshi dab da tata, har suna jin hucin junansu atausashe ya kirata “Baby ummina! Oya zo naji me Abien ya yi um? D'ago mana baby ummiterh.�
Jin muryasa dab da kunnenta daddad'an k'amshin da yake fitowa daga bakinsa, ya mamaye mata dukkan k'ofofin hancinta.
Dad'in k'amshin ya sanyata jan wani irin wahalallan numfashi, wanda taji lokaci d'aya yana qoqarin barin gangar jikinta. Da iya kacin k'arfinta take janyo numfashinta da yake son tsaya iyakacin k'arfinsa.
Hakan ya sanya zuciyarta wani irin matsanecin rauni, wanda ya janyo zuciyar ta fara bugu da dukkan iya k'arfinta, jikinta ya fara wani irin b'ari, yayin da wani irin fitinannan sanyi ya kawoma dukkan illahirin jikinta farmaki, lokaci d'aya, sanyi ya fara bin gab'ob'in jikinta, da dukkan wata k'ofar mahudar gashin jikinta, sannan tin daga cikin tafin k'afarta zuwa har k'wak'waluwarta, sanyin yake ratsa.
Abienta ya ce“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ummina! Bakida lafiya ne?�
Ya k'arashe maganar ya janyota cikin jikinsa ya rungumeta k'am-k'am, ya d'ago fuskarta yana shafawa yana hura mata d'umamanmiyar iskar bakinsa mai fitar da wani irin d'umi had'e da k'amshi marar misali.
Numfashinta da yake barazanar tsayawa ta fizgo da k'arfin gaske tana sanya dukkan hannayenta ta zagaye bayansa, ta fashe da wani irin rikitaccan kuka, cikin fizgo numfashi ta kirasa.
“Abiena zan sha ruwa mai d'umi.� ta k'arashe mgnar cikin shashek'ar kuka.
Abdul Majeed ya rikice yana famar buga bayanta ya ce“Ya Ilahi! Baby wai me na miki? ji yadda zuciyarki take bugawa. Ok naji muje na had'a miki tea me zafi, don Allah ki daina min kuka zo kiji yadda zuciyana ke bugun uku².�
Ya k'arashe mganr yana kamo lallausan hannunta ya d'ora tsakiyar faffad'an k'irjinshi.
Rahma jin yadda zuciyar Abienta yake bugawa iya k'arfinta, ya sanyata tattaro nutsuwa ta k'arfi ta fara shafa k'irjin nasa ta tura kanta tsakiyar k'irjin nasa, tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, ta kira shi asanyaye.
“Abiena!�
Ya amsa da “Na'am zuciyar Abienta! ke d'aya k'wal ubangiji ya mallaka min aduniya, banga anfanina ba idan har zan barki acikin damuwa.�
Ya k'arashe maganar ya na d'aukarta cad'ak kamar baby ya juya ya fara taka matattakalar benin.
Rahma ta had'iye kukanta sbd kalamansa sun saka mata tausayinta, ta tura kanta tsakiyar k'irjin Abienta tana sauke ajiyar zuciya, ajere².
K'asa ya sauko da ita ya zaunarta saman kujera, ya manna mata kiss saman kumatunta, yaje ya kunno fitilun falon masu haske, ya shige kitchen.
Rahma ganin bai dace tabar mahaifinta ya yi mata aiki ba ya sanya ta mik'e cikin sauran d'an kuzarinta da ya rage mata ta iskosa kitchen.
Ashagwab'e ta ce“Abiena kawo na had'a.�
“No! Ummina!�
Kai ta d'ago ta kalle shi tana kwab'e fuska, gira ya d'aga mata yana sakar mata lallausan murmushi.
Itama murmushin yak'e tai dan ta rasa abinda yake damunta, bayan abinda Raiyana tai wa mahaifinta tabbas akwai damuwar da ta kasa gano meye.
Tayi nisa cikin tunani taji tattausan hannun Abienta ya rik'e nata yana janta tare da fad'in.
Muje naji me ke damun ummina.�
Zaunar da ita yay ya zauna dab da ita, yana hura mata had'add'an tea d'in da ya mata da bakinsa.
K'ananun kyawawan idanunta ta zuba masa, tana sanya yatsarta aramun dimple d'insa, wanda yake lob'awa, sbd yadda ya dage yana hura mata tea d'in da Iskar bakinsa yana murmushi, ya ce“ Oya zo ki sha.�
Ya k'arashe mgnar ya na tallafo gefen fuskarta, ya kafa mata cup a mitsitsin bakinta.
Marerece fuska tai tana kallonsa.
Fuska ya had'e ya ce
“Oya.�
Luf ta lab'e ajikinsa ta lumshe k'ananun fararen idanunta tana shan tea d'in, cike da nutsuwa da kwanciyar hankalin da ta samu ayanzu², wanda take ta tafi duniyar tunanin abun da batasan meye shi ba.
Dariyar Abienta ta dawo da ita daga duniyar tunanin.
Kyawawan k'ananun idanunta ta bud'e ta tsurama kyakkyawar fuskar Abienta ido yadda yake mata dariya yana rik'e da fuskarta, ya nuna mata cup d'in vide ma'ana ba komai, ya shanye tea d'in amman sai famar rik'e hannunsa take tana kai cup d'in bakinta.
Fuska ta kwab'e tana tura yatsarta a ramin dimple d'insa, tana matsar k'ananun lumsassun idanunta.
“Sorry mah baby ummina muje ki kwanta, yau busy nayi dayawa ba shareki nayi ba kinji bugun zuciyata ummina.�
Rahma ta zumb'uro k'aramin bakinta gaba, cikin sanyita da rauninta akan Abien ta ce“Abiena! Ko kirana baka d'aga ba fa! Ga shi gobe zaka tafi tsawon kwanaki ban ganka ba Abiena!�
Ta k'arashe mgnar cike da rauni wanda ya bayyana qarara akan kyakkyawar fuskarta, har k'walla sun fara taruwa, tai saurin mayar da k'wallar, ta daure batayi kukan ba!
Wani irin wahaltaccan numfashi ya janyo da k'arfi, ya feso da iskarsa waje, saman fuskarta, tare da shafa fuskarta a raunace cike da tausayin 'yarsa d'aya tilo kamar tsoka d'aya acikin miya, ya ce “Afuwan Baby ummiterh zanyi qoqarin dawowa akan lokaci domin na baki dukkan kulawar uwa da uba suke bawa d'ansu,na ji dake na tarairaye ki na baki lokacina fiye da kowa har sai hutunki ya qare kin koma Espagne, oya muje ki kwanta kinji Babyn Abienta.�
Cike da rauni ta jinjina kanta tana janye jikinta.
Kama lallausan hannunta yay suka nufi wajan kashe makullan fitulun falon wanda k'wayayen sun kai guda 12 kala² hannunta ya sanya saman ma kashin fitulun ya danna yatsotsinta falon ya gauraye da duhu, yay murmushi k'asa² ya ce“Oya dodo Kama ummina...�
D'an guntun qara tai ta fad'a jikinsa ta k'ank'anme shi cike da zallar shagwab'a ta ce“A'a fa dodo oya tafi sha'aninka Baby na tare da Abienta ba wani abin cutarwa da zai iya cutar da ita.�
Ta k'arashe mgnar tana murmushi.
Ba sake mgna ba yay murmushi ya kunna fitilun haske ya bayyana, janyeta jikinsa ya kama hannunta suka nufi sama.
Ak'ofarta ya saki hannunta ya mata kiss agoshi ya ce“Oya ummina bacci mai dad'i ki kasance cikin amincin Allah har zuwa wayewar gari.�
Ya k'arashe mgnar ya d'auki wayoyinsa da system d'insa.
Rahma ta ce“Abiena kaima ka kasance cikin duk abinda ka lissafomin fiye da hakan, I love u Abiena bye.�
Ta d'aga masa hannu tana shigewa ciki ta murzawa k'ofar key.
Juyawa yay ya fara tafiya wani irin sihirtaccan murmushi d'auke akan fuskarshi.
Yana saukowa daidai k'ofar d'akin Raiyana yaji motsi, hakan bai saka shi waigawa ba, ya gifta ya ji muryan Raiyana, tana kiransa.
“Abien Ummi inada mgna.�
Waigowa yay ya fad'ad'a murmushin fuskarshi, ya ce“Ok inaji�
K'arasowa tai tana danne mugun haushinsa da takeji, ta marere fuskarta kalar tausayi, ta ce“Sbd Allah tin yaushe wajan Ummi kake? amman ni kuma kamar ba matarka ba? Gsky gatan da kakewa...�
Da sauri ta had'iye abinda zata fad'a ta waske ta gyara kalamanta ta ce“Allah ya qara maka lfy ya barma kai nida Ummi babba da Ummi 'yar lelen Abdul Majeed, kana son 'yar dayawa gaskiya, nima Allah ya bani haihuwa da kai.�
Ta k'arashe maganar tana qoqarin rungumeshi.
Bai hanataba ta wani shige jikinsa ta k'ank'ameshi tana shak'ar daddad'an ni'imataccan turarensa, wanda ya gauraye da turaren Rahma.
Can k'asa ya ce“Hankalinki ya kwanta? sakeni toh, Sam bakida kunya har kin manta tijaran da kika min?�
Ya k'arashe mgnar yana zamewa ya juya ya nufi bedroom d'insa.
Raiyana sororo ta tsaya tana kallonsa har ya shiga ya rufo k'ofa.
“Hummm Abdul Majeed zaka shigo hannune da izinin Allah.�
Ta fad'a tana shigewa ciki.
Rahma kai tsaye saman bed ta fad'a ta shige wani irin lallausan bargo mai fitar da sihirtaccan k'amshi,ta rungume k'atuwar Teddy d'inta, tana mai karanto addu'o'in bacci.
Minti 7 bata cike ba wani irin dadd'an bacci yay awon gaba da ita.
Abdul Majeed yana shiga, shirin bacci yay ya shirya cikin wasu kayan bacci masu masifar kyau da laushi, ya kashe dukkan wayoyinsa yabi lafiya royal bed d'insa, bakinsa bai daina karanto addu'a ba har bacci ya d'auke shi mai cike da nutsuwa.

*Washegari.*
Niger Diffa

K'arfe 5 saura na asuba bus d'insu Ja'afar ta cira daga garin damagaram zuwa Diffa.
Tafiya ta tsawon 7 hours sukayi acikin bus, kafin su iso garin Diffa.
Suna sauka daga gidan bus suka shige rumfuna da aka tanada dan bak'i, suka zazzauna bayan sun huta sunyi abinci sunyi sallah, sun nutsu.
Ja'afar ya kalli wayansa yana jujjuyata zuciyar ba dad'i tun jiya, dan tabbas yasan Ibtisam d'insa tana cikin damuwa.
Manyan idanunsa ya lumshe ya bud'e ya kalli Yahuza da Harisu abokan tafiyarsa, sai hirasu suke cikin walwala, sunata dariya.
Tsuki yay ya shafi sumar kansa, ya ce.
“Kufa ku tashi musan nayi hutun ya isa haka.�
Harisu ya ce“Uban gidana kak'i fad'in garin da zamu dosa kai tsaye, tsakanin Tchad da Cameron? Ko muje Tchad idan baja sai mudawo Cameron ko?�
Ja'afar ba tare da ya kallesu yana danna wayasa, yay dialing d'in number Baaban sa, ya ce“Inaga muje Tchad zaifi ko?�
Yahuza ya ce“Wlh nima nan nafi kwad'aituwa, Allah yasa mu samu aiki na k'warai acan.�
Ja'afar ya amsa da
“Ameen. Oh! Na rasa Baaba�
Ya fad'a yana sake kiran number mahaifinsa bata shiga.
Harisu ya mik'e ya d'auki jakarsa ya ce“Muje zama ba namu bane.�
Basu musaba suka mik'e kowa ya d'auki jakar matafiyansa suka fito nan k'ofar sonef suka shiga keke napep.
Ja'afar yace ma me napep.
“Yauwa don Allah tashar mota zaka kaimu inda zamu samu motar Tchad. �
Me napep ya ce“Akwai kuwa amman yanzu kwanan hanya zakuyi dan akwai tafiya.�
Ja'afar ya ce“Ok muje mun gode fatanmu mu sauka lafiya shine kawai.�
Nan me napep ya nufi babbar tashar motocin, ya kaisu har layin motocin Tchad, cikin ikon Allah mutum ukune daman suka rage sai ga su Ja'afar. Nan suka shiga mota kamasho ya amshi kud'insu ya sallami direba nan mota ta tashi jama'ar ciki kowa na addu'a, cikin nasara yanzu Ja'afar ya gwada kiran mahaifinsa ya sameshi.

*TAHOUA*
Unguwar Moray

Malam Adamu yana tsakiya da cin abinci, wanda kullun sai yayi sallar azuhur 2 yake zauwa cinsa agida, ko kusa baya cin abinci wajan sana'arsa.
Kiran da ya shigone ya sanya shi saurin kai lomar abincin bakinsa, ya d'auki wayan da take gefensa ajiye.
Ganin Ja'afar ne ya fad'ad'a fara'arsa, ya d'aga kiran tare da sallama, yana fad'in.
“Ma Sha Allah Ja'afar yanzu kuna ina? Tin jiya wayan take kashe na barta a chaji yanzu na cirota.�
Ja'afar wanda motarsu ta fita daga cikin Tasha, ya ce“Baaba ina yini? Asamu cikin addu'a gamu zamu Kama hanya, abani innata idan tana kusa.�
Malam Adamu ya ce“Allah ya saukeku lafiya ya rabaku da sharrin dukkan abin k'i Allah ya baku sa'ar tafiya, bari na kaiwa Hansatu wayan.�
Daga can Ja'afar ya ce“Ameen Baabana Ngd. �
Malam Adamu ya fito wayan akunnensa sai addu'a yake jeroma Ja'afar.
Inna Hansatu tana zaune a inuwan dalbejiya, ita da Deluwa tana lissafin ribar da ta hayo mata ayau sai washe baki take, sabida kusan d'ari uku taci riba, ta ce“Ina laifi sbd Allah ga shi anata cin ta sadaka agida ai na zaune baiga gari ba wlh.�
Deluwa ta ce“Allah ya qara albarka hannu ya kuma k'aro kasuwa. Hansatu kinyi mgna kuwa da Ja'afar?�
Inna ta ce“Ameen fa kam tinda ana cin ta sadaka sosai. A'a wlh ni da wayana taci battery sai an siya, kekuma an sace taki, sai ta Malam...�
Isowa yay yana fad'in.
“Yauwa ga iyayan naka zaune, anata lissafi, Delu amshi ki masa fatan alkhairi.�
Deluwa ta amsa tana kara wayan akunnenta, tare da sallama.
Ja'afar ya gaisheta, ta amsa tana masa addu'a, ta bek'awa inna mai waina.
Inna bayan ya gaisheta ya fad'a mata suna hanya, ta shiga kwararo masa addu'a akan Allah ya

Please Login or Register in order to submit comment