Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga motar su ka tafi.

Rahma sanye da wata tsadaddiyar doguwar riga bak'a,wadda taci uban adon duwatsu jajaye, kallo d'aya zakama rigar kasan akwai tsada.
Sosai ta mata mugun kyau ta yane kanta da 'dankwalin riga, sai wani irin fitinannan k'amshi yake fita daga jikinta. cikin sassarfa take saukowa daga saman benin, fuskarta ba annuri ko kad'an.
Dai-dai 'kofar Raiyana sukaci karo da ita ta fito zata sauka k'asa.
Wucewarta tai tana jujjuya wayanta ahannunta. Rainaya ta ce“Ummi barka da dare, kunyi waya kuwa Abienki?�
Rahma taja ta tsaya tana waigowa, tana kwa'be fuska kamar zatayi kuka ta shiga danna wayar hannunta hawaye ya shiga silalowa saman kyakyawar fuskar. Kai ta shiga girgizawa Raiyana had'i da cewa“A'a Ammi bamuyi ba, ba'a samunsa.�
Ta k'arashe mgnar cikin sanyin murya wadda take rawa, ta juya ta fara tafiya.
Rainaya ta toshe bakinta sabida dariya da ta kamata, ta bita da harara aranta ta ce“Ke ya dama uwar me yake tsinana min, idan yana garin? Banda shan k'amshi mtswwww!�
Amman azahiri ta biyo bayanta tana fad'in. “Ai zai kira k'ila ya gaji ne zuwa gobe zamuji shi.�
Har su ka sauka Rahma batace uffan ba.
Jaddatu zaune tana kallon Tv.
Rahma ta shigo falon, Raiyana na biye da ita.
Tana tafiya ta ce“Jaddati zan fita shan iska gidan zafi yake min bye.�
Jaddatu ta ce.
“Ke! Rahma! Ina zakije awannan lokacin dare ya soma yi? Dawo. Wato mu nan duk ba mutane bane, sbd mahaifinki baya gari shiyasa gidan ya 'dumame miki da zafi ko Rahma?�
Rahma ta 'dan ciji jajayen labb'anta had'i da fad'in.
“Karki damu zan zagaya ba ni 'daya zan fita ba, tare da direba and security. �
Ta 'karashe mgnar ta sanya kanta ta bi corridor d'in zai fitar da ita daga falon.
Jaddatu ta kalli Raiyana wadda take tsaye, tabi Rahma da kallo har ta 'bace mata.
Ke! Rayyanatu! amatsayin ki na uwa bakisan yadda za ki lallashi Rahma ki kwantar mata da hankali ba, ta zauna ko? Watobkwaliya ta biya kud'in sabulu, yanzu ba ruwanki da 'diyarsa? Ahaka kike son Abdal Majeed d'in? Bakya kulawa da tilon 'yarsa?�
Ta 'karashe mgnar tana 'daukar wayanta tai kiran number Yahaya direba. Cikin sa'a ta sameshi. sallama ya mata had'i da gaisheta.
“Yauwa kanaji Yahaya karka tuk'a Rahma duk abinda zatayi. Da Khalifa da Abbas aka tafi Gabon ko sunanan?�
Yahaya cikin girmamawa ya ce“A'a Ummi su na nan dan tsaron Ummi qarama.�
Jaddatu ta ce“Yauwa! Ka ce nace karsu barta ta fita.�
“Ok an gama.�
Datse kiran tai tana kallon Raiyana wadda ta wani zube gaban Jaddatu, cikin kukan kiss a ta ce.
“Wlh Ummi na hanata amman bataji ba, ya zan mata? Banason 'bacin ranta.�
Jaddatu ta ce “Shi kenan Raiyana.�

Rahma kai tsaye wajan Yahaya ta nufa.
Ma'aikatan gidan sai gaisheta suke tana amsawa. Tare ta gansu dasu Khalifa.
Wajansu ta iso da sallama.
Atare su ka amsa.
“Zan fitane.�
Ta fad'a cikin sanyinta.
Abbas ya ce“Hajiya dare ya yi kiyi hkr sai gobe.�
Wani irin kallo tai masa bata ce komai ba, ta kalli Yahaya direba ta ce“Zakayi driving d'ina ne?�
Kai ya Sosa ya ce“Ummi qarama ki bari sai gobe.�
Batayi mgna ba ta juya ta nufi wata had'add'iyar rumfar shak'atawa, ta zauna ta had'e kai da guiwa ta saki kuka mai ciwo.

Ja'afar uffan bai ce ba yana jin yadda me taxi d'in ke basu labarin garin Tchad kamar sun tambaye shi.
Yahuza da Harisu suka biye masa sai hira suke, har suna tambayarsa yadda zasu samu aiki, ya ce zuwa gobe zasuyi maganar. Sai da suka tsaya hanya suka basa kud'i ya siyo mu su abinci.
Unguwar hausawa wani 'dan madedecin gidane irin ginin talakawa amman ba laifi shafe yake da siminti Baba Tsalha me taxi yay parking, ya bud'e k'ofar ya fito yana washe baki ya bud'e mu su ya na fad'in.
“Bismillah mu shiga ku kaga d'akin idan ya muku.�
Firfitowa sukayi, rataye da jakukkunansu na matafiya, su ka nufi cikin gida.
Gidane me kewaye daban² wajan kashi biyar, akewayen farko su kaga ya ciro makulli daga cikin aljihunsa ya bud'e k'ofar.
Baki ya washe ya ce“Mushiga kuka idan ya muku.�
Harisu ya ce“Ya ma yi baba.�
Ja'afar bai ce komai ba har ya gama nuna masu komai na gidan,dakine 'daya 'kwal da toilet da filin tsakar gidan baida wani yawa, sai qaramar kitchen ko ina fas ashare na gidan.
Harisu ya ce“Nawa zamu bayar duk wata?�
Baba Tsalha ya ce“Kud'inku jaka ashirin CFA, ai kunga d'aki mai kyaune, sai Ku kawo na wata uku yanzu.�
Harisu ya fito da kud'in Aljihunsa duk basukai jaka talatin CFA ba, ya basa jak ishirin ya ce“Baba rik'e wannan kafin mu samu aiki, sauran abinci zamuci.�
Baba Tsalha y'a amsa ya basu mukullan ya ce“ Akwai tabarma sai kuyi qoqarin siyan katifa, ni na koma wajan sana'ata, nima anan gidana yake gobe dai na muku sauran bayani.� ya mu su sallama ya tafi.
Ja'afar ya jinjina kansa ya nufi d'akin.
Wankakkun kaya ya ciro ya fito ganin jarkar ruwa da bukiti, cikin sa'a akwai ruwa, haka cikin uban sanyi Ja'afar yay wanka, sabida mugun 'kyan'kyamin sa Sam bazai iya bacci ba, ya kwana da kaya ya wuni ajikinsa.
Su Harisu sun ce su kam bazasu iya wanka ba da uban sanyin wannan. Bayan sunci abinci suka rufe d'akinsu kowa ya nemin makwancinsa, da abin rufarsa, jeruwa sukayi saman tabarma.
Lallausan bargonsa ya ciro sabo dal ya shimfid'a rabi ya rufa da rabi, yana jinsu suna surutu amman shi kam uffan bai cewa, agajiye yake ga tunanin iyayansa da Ibtisam.

Washegari.
*Gabon*
(Unguwan Alibandeng)
Wani narkeken gidane wanda yaji kayan more rayuwar duniya, gidan ya tsaru matuk'a, tin daga qofar zaka sheda hakan. bare cikin gidan, zuwa falon wanda yasha manyan kujeru masu laushi da tsari, ga carpet mai taushin gaske, malale atsakiyar falon.
Ba'ki ne a falon wajan mutum biyar an cikasu da kayan motsa baki da ruwa da lemo. wanda Abdul Majeed ya bada umarnin su zauna zai tattauna da su akan kasuwancin nasu, . Kusan 20 minutes amman bai fitoba sbd daman baison wulak'anta mutane ne shiyasa ya ce a barsu su shigo tinda sun san yana 'kasar.
Kwance yake saman tamfatsetsan gado ya nad'e cikin bargo yanzu zazza'bin ya sauka tinda qarin ruwan ya qare Dr Anwar ya cire masa ya koma.
tin jiya da yazo baida lfy qarin ruwa ake masa.
Wahalallan numfashi ya janyo fesar da iskar waje, ya bud'e gajiyayyun narkakkun idanunsa bakinsa na motsawa sannu ahankali alamun tasbihi yakewa ubangijinsa.
Bargon da ya lullu'be dukkan jikinsa ya janye, ya mik'e zaune ya janye wayarsa (iPhone 13 pro max).
Kunnata yay. Tana kunnuwa kai tsaye ya kira number Jaddatu Rahamu.
Tanata ringing ba'a daga ba.
Kira uku yay ba'a d'aga ba.
Cikin rauni da alamun nuna rashin lafiyarsa qarara, ya furta.
“Ya Rabbi! Ko lfy?�
Daga can kuwa wayan tana bedroom yayin da Jaddatu take cikin falo, sai dai Rahma na d'akin tin d'azu ta shigo ta kwanta tana juyi wayan na silent, bata luraba.
Number Rahma ya kira, bugu d'aya ta d'aga kiran ta sanya masa kuka harda shashek'e. Ta kirasa “My Abie lafiya kuwa? Ka barmu cikin damuwa tin jiya ba'a samunka, nadamu sosai.�
Idanunsa ya runtse da 'karfin gaske, ya dafe goshinsa wanda jijiyoyin kansa suka firfito sukayi ra'do-ra'do, sbd ciwon da kansa yake masa, ga kukan yana sukar har 'kahon zuciyarsa.
Ahakanli ya kirata.
“Baby ummina! Pls kiyi hkr tin jiya da nazo banda lfy, banson ku tashi hankalinku shiyasa na kashe wayoyina, amman yanzu naji sauqi.
Hope baby ummina tana lfy?�
Rahma daga can ta sauke ajiyar zuciya ta ce“Wlh Abie jikina sai da ya ban kamar ba lfy ba kake be, yanzu don Allah ya jikin naka? Bari na kiraka video call na ganka kaji?�
Abienta ya ce“Naji ummina na bari na kunna data.�
Cikin murna ta kunna data ta shiga IMO ta kirasa video call ya d'aga.
Kyakyawar fuskarshi ya 'kawata da murmushi yana kallon ya 'daga mata hannu“Hi ummina.�
Rahma ta langwa'be kanta ta marerece fuska, ta ce“Hi Abiena I miss u sannu ya jikin naka? Wlh har kayi 'yar fuska.�
Murmushi yay ya shafi sumar kansa ya ce“A'a Baby ban rame ba, ina amminki da Jaddatu na kirata bata d'aga ba?�
Fuska ta kwa'be ta ce“Tana falo Abie Allah baka lfy kasha magani kaji, jiya kamar zanyi hauka Jaddati ta hana in fita da dare.�
Dariya yay ya bek'a hannun waya ya ce“Bari na cire kunnen rashin ji ai na hana fitar dare.�
Ashagwa'be ta ce“Wayyo Abie zafi ka ciremin kunne zafi.�
Kyawawan idanunsa ya waro yana murmushi ya ce“Uhmm! Ummina sai kuwa na ciresu da nadawo, karki manta cizo uku zan musu idan kin min kuka na musu sau6. Baby bye inada ba'ki afalo zan kiraku an jima ki gaishemin da su kafin na kira je t'aime muahhhhh!�
Ya katse ta wajansa sabida yasan rigima zata masa sosai.
Saukowa yay jikinsa ba 'kwari ya shiga bathroom ya watsa ruwa, ya fito ya shirya cikin wata lafiyayyar shaddah fara 'kall qoqari kawai yake yi.
Da sallama ya shigo falon ya be'ka mu su hannu suna musabaha 'daya bayan 'daya.
Kafin ya zauna.
Hamid ya ce“Ashe zazza'bi ya rufeka? Wlh bamu saniba ai da zamu barka zuwa gobe, Allah ya qara sauqi.�
Abdul Majeed ya amsa da “Ameen ba komai Ngd.�
Daga nan ya basu dukkan lokacinsa suka fara tattaunawa akan abinda ya kawosu.
*Unguwar Haut de gué gué*
Aishatu zaune a falonta, ita da wasu mata uku sai hira suke suna dariya, kayan ciye² agabansu.
Aishatu ta ce“Humm Rabi'ah ki bari kawai, Ma'aruf 'karshene wlh ina son mijina yana jiyar da ni da'di ta kowane 'bangare, ashimfid'a sai dai ni nagaji ba shi ba. Wajan abinci ya wadatani da komai sutura haka, abin hawa matsalata da shi 'dayane, rashin zama sai ya zagaye 'kasa uku zuwa 4 kafin ya waiwayo gida, a'kalla za'a kwashe kusan wata biyu baya nan, kin sanni ni kuma da jaraba,duk da banda juriya dayawa.�
Dariya sukayi suna tafa hannayensu.
Hudah da Kabeera su ka had'a baki wajan cewa“Ai kefa wlh kinyi dace miji ga gayu ga kud'i ga iya soyayya. Duk cikinmu babu tsaranki sai mijin da zai auri Rabi'ah kawai yafi mijinki kyau, soyayya ce bamu saniba.�
Rabi'a ta yamutsa fuska ta ce“Shegen jiji da Kaine da shi l, kai ba wani kud'i ba, bari zai shigo hannu.�
Aishatu ta daketa ta ce“Kama mijinki yarinya mata warce suke fa!�
Dariya sukayi, Rabi'ah ta ce ina samun mai money wlh zan daina aurensa...�
Hudah ta ce“Nadama zakiyi kuwa dan ubanki.�
Dariya Rabi'ah tai.
Aishatu ta ga wulgin uwani, ta kirata.
“Uwani! Zo nan.�
Cike da tsoro da farga ba uwani ta tura wayanta cikin bra, ta fito tana rarraba idanu.
Zubewa taigaban Aishatu ta ce“Ga ni hajiya.�
Aishatu ta ce“Kutumar ubancan la'be kike mana ko me?�
Uwani ta zaro idanu ta dafe 'kirji ta ce“Ni shegiya! Me zanji hajiya? Kufa duk matane 'yan uwana, wlh naji kamar kin kirani ne, sai nafito ganin kuna hira ya saka na juya na koma kiyi hkr.�
Aishatu ta ce“Kinci sa'a tashi kije.�
“Ngd hajiya Allah ya qara girma.�
Ta mik'e ta tafi.
Rabi'ah ta tab'e baki ta ce“Wlh nifa banson 'yar aiki Tab.�
Kabeera ta ce“Dallah ja can masu kyau ko? Amman yo irinsu uwani ko guda 'darine me ruwana.�
Aishatu tai dariya ta ce“Yauwa 'kawata gayamata dai, nima da macan 'kwaraice ai bazan bari ba, Ma'aruf idon garine ba'a barinsa da mace mai aji.�
Haka sukaci gaba da hirasu, yayin da uwani ta kashe kunne tana 'daukar ma ubangidanta rahoto.

*Tchad*
Baba Tsalha tinda safe ya bugama su Ja'afar 'kofa. Bayan sun bud'e ya shigo sun gaisa ya musu bayanin irin wururuwan da ake samun aiki na ginin gidaje company asibiti dako tura baro da tuk'i, idan akwai wanda yakeda parmi acikinsu.
Ja'afar ya ce“Baba inada parmi na iya mota sosai, amman kasan sha'anin masu kud'in nan sai a slow, wani motar tana 'baci ahannunka za'a sakaka ramuwa, wani kuma yasan asara. inda zan samu aikin ginin wanda akullun za'a dinga ba ni hakk'ina nafison hakan.�
Baba Tsalha ya ce“Amman da ka samu tuk'in yafi 'dana kona company ne.�
Ja'afar ya jinjina kansa ya ce“Ok Allah ya za'bamana abinda yafi alkhairi. Ku me kuka zab'a tinda na nace ku koyi mota kun k'i?�
Dariya Yahuza da Harisu sukayi sukace.
“Muje dai duk inda zakayi aikin muna wajan.�
Haka suka shirya Baba Tsalha ya kwashesu a taxi 'dinsa suka fita.

Wajan guri biyar sukaje cikin rashin sa'a an tsayar da d'aukan masu aiki.
Na shidda ne suka dace wani companyn turare, amman kud'in baida wani yawa, sannan Ja'afar bai samu tuk'in ba, hakan ma ya saka albarka.
Nan su ka yini sai yamman lik'is aka sallame su, Baba Tsalha yazo ya 'dauke su suka nufi gida.

★★★★★★★★★★★

*Bayan sati d'aya.*

Ahankali Yahaya direba yake driving, ya mik'e babban titin ( *rue de 40*)
Yayin da Rahma tana baya zaune, ta nad'e cikin wata tsadaddiyar Lufaya, Ash colour, abinka da farar mace ba'a mgnar kyau. Wani irin fitinannan k'amshi ke tashi ajikinta yayin da ya gauraye motar baki d'aya.
Waya take latsawa tana sakin tattausan murmushi.
Dai-dai danja ta tsayar da su ta 'dago da kanta,tana murmushi idanunta basu tsaya ako ina ba sai akan...........!

_💃�Yar Ajin Tubarkallah🥰_

*DATTIJON ARZIK'I* N300 katin MTN ta wannan number *+22796515805*



SULTAN
mss flower

BAK'AR FATA
AUTAR MANYA

TSINTACCIYA
Nimcyluv

Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218


*Real Ladingo+22796515805* For more information😇

_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/2/22, 09:19 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_


*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_

*🔥FITATTU HUƊU🔥*


_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_


_Ba wai tarin zallar soyayya ba ce kawai acikin wannan tafiyar, akwai tarin abubuwa tare da sarqaqqiyar mai wuyar warwarewa, akwai abubuwan anfanuwa masu tarin yawa cikin labarin dattijon arzi'ki. Sai dai A 'Bangaran soyayyar kuma abin akwai dagula lissafi, amman... Kuma fa zata 'kayatar zata burge zata bada citta matu'ka.🥰_


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


_*cнapтer 15&16*_


Wani dattijo ne gefen titin zaune fari ne, sa dai alamun datti ya zauna jikinsa sosai. kayan jikinsa duk sun tsufa sun fara cirewa, ya lullub'e rabin jikinsa da wani tsohon bargo. Robace irin ta almajirai da suke bara agabansa, da sandarsa ya na 'dagawa alamar bara yake, abin gwanin ban tausayi.
Rahma ta 'kura masa kywawan 'kananun idanunta, cike da mugun tausayin sa, ta ce.
“Ya Allah! Wannan bawan Allah ina family's 'dinsa yake zaune anan neman sadaka? Yahaya idan danja ta sakemu ka zaga wajan wancan tsohon zan basa sadaka.�
Ta 'karashe maganar cikin shashe'kar kukan da bata san ma ya akayi ya su'buce mata ba.
Kasancewarta mai tsananin tausayi.
Yahaya ya ce“Hajiya meye toh na kuka? Kiyi hkr, jifa² idan nabi nan na kan gan shi.�
Abbas ya ce. “Kawo akai masa ba sai kin fita ba.�
Rahma ta girgiza kai tana fad'in.
“A'a muje dai.�
Danja ta sakesu Yahaya ya zagaya da motar dab da inda dattijon yake zaune, yay parking.
Abbas ya fito ya bu'de mata 'kofar.
Handbag 'dinta ta bu'de ta ciro ku'di 'yan (1000 fran CFA).
Sun kai na jaka 20 ta fito ta isa wajan dattijon da sallama.
Abbas na tsaye abayanta.
Tsohon ya amsa sallamar.
Rahma ta rusuna gabansa da harshen larabci ta ce“Abba ina dangin ka kake bara anan? ai kayi tsufa sosai zamuje ka kaimu gidanka naga iyalinka zan 'dauki nauyin abincin ku da abin shanku.�
Kuka ya saki yana magana irin tamasu karyayyan harshe.
“Allah sarki banda 'da banda jika banda mata, iyayena sun rasu tin bansan kaina ba, banda kowa sai Allah anan nake wuni na samu sadaka na siyi abinda zanci na koma kangon da nake zaune.�
Rahma ta saki kuka ta kama hannun dattijon ta ce“Ta shi muje gidanmu daga yau kayi 'yan uwa da kowa...�
Abbas ya ce.
Hajiya ki barsa ki dai basa sadaka don Allah mu tafi.�
Rahma ta ce“Ba damuwarka bace malam ka kula da lafiyata akace ba wai ka tirsasani ba nabar abinda nayi niya. Temako nayi niyar yi meye toh aciki? duk abinda na zarta nasan ya zartu Abie bazai tab'a 'kin abinda na kawo da zumar na temaka masa ba.�
Dattijon ya ce“A'a ngd barni naci gaba da rayuwata ahaka har lokacin mutuwa ya riske ni.�
Rahma ta ce“Abbas kamasa muje gida na fasa ma zuwa yawon.�
Abbas badan ransa yaso ba, ya kama dattijon ya mi'ke suka nufi mota.
Jama'a sai kallonsu suke dan basu ta'ba ganin wanda yazo 'daukarsa ba, sai dai abasa sadaka idan magarib ta yi ya tafi yana dogara sandarsa dan bai ko ganin kirki haka mutane suka fuskanta.
Bayan motar ya sanyasa Rahma ta zauna kusansa, Abbas ya koma mazauninsa. Yahaya yaja motar yana fad'in.
“Ina zamuje yanzu?�
Rahma ta ce“Gida mana.�
Yahaya ya ce“ Amman Hajiya da kin nemi izinin Yalla'bai.�
Rahma takaici ya saka bata sake magana ba, kasancewarta marar son maimaici akan mgna, yanzu zata harzuqa tamkar mai jinnu, shiyasa ta sharesa, ta 'dauki wayanta, ta dannawa Abienta Kira.

Daga can Gabon Abie da yake tsaye 'kofar company, suna sallama da ba'kin da suka gudanar da taro.
Bugu 'daya ya 'daga kiran tare da sallama, yana sakar mata Sumba ta wayan.
“Muahhhhh! Baby I miss u so much. �
Ya qarashe mgnar ya na ke'bewa daga cikin jama'ah.
Rahma ta karkatar da kanta ashagwa'be ta ce.
“Uhmm Abie ba yanzu muna chart ba, kace na jiraka ka sallami ba'ki? na sauka zan baka labari mai da'di Abie nawa.�
Ta 'karashe mgnar tana murmushi.
Daga can Abie ya shafi yalwatacciyar sumar kansa, zuwa gemunsa ya Saki 'kayataccan murmushi ya marerece kamar wani matashi 'dan kimanin shekaru 25 ya ce.
“Baby ummina pls gayamin menene um?�
Rahma ta ce“Naqi Abie sai mun ke'be ina cikin mota na fasama zuwa yawon mun juya gida.�
Daga can Abienta ya waro idanunsa waje ya ce“No! Baby pls mana kije kinji?�
Rahma ta ce“Wayyo Abie na fasa bye.�
Ta tsinke kiran ta mayar da wayan cikin Jakarta.

Ja'afar Masha Allah ba laifi suna samun ku'di ka'dan², cikin satin da sukayi a Tchad.
Baba Tsalha na nema masa aikin tu'ki har yanzu dai ba'a dace ba, shi Ja'afar bai wani son driving 'din.
Ya siyi layi suna gaisawa da 'yan gidansu, harda Ibtisam, ta wayan Tanko.
Yau da wuri suka dawo daga wajan aiki, wanka yay ya sanya jans da t-shirts, sai 'kamshi yake, ya gyara sumar kansa, Masha Allah, su Ja'afar ba'kin buzu akwai kyawu.
Zaune suke a tsakar gidansu, sai zuba suke, shi kuma yana gefe waya ri'ke a hannunsa, ya na latsawa duk ta ko'de.
Kiran gida yake baya samu.
Tsaki yaja “Mtswww!� cikin dadda'dar muryasa ya ce“Na tsani rashin network 'din nan fa, ku tashi mu zagaya a'kafa muga gari.�
Harisu yay dariya ya ce.
“Duk rashin jin Ibtisam 'din ne?�
Idanuwansa ya lumshe ya bu'de ya mi'ke ya zura hannunsa cikin aljihunsa,ya ce“Allah ya mana bu'di na alkhairi na tura mata ku'di ta siyi waya, muje zagaye don Allah.�
Dariya suke masa, da tsokana bai kuma tanka su har suka bar gidan suka fita zagaye.

*Niger*
TAHOUA

Ibtisam zaune ta yi tagumi yau duk bataji muryan Ja'afar ba, batada nutsuwa Babanta baya gari sun tafi (Bouza).
Laraba tana fifita wuta ta 'dora girkin dare. “Ibtisam! Zo nan�.
Baki ta turo gaba tana matso 'kwalla ta mi'ke ta taho kamar wacce 'kwai ya fashewa aciki.
“Ga ni Anna.�
Ta 'karashe da murya kamar zatayi kuka.
Laraba ta ce“Gyara min kayan sai kije kiyi ta famar ba'kin tunanin ba'kin yaron can tinda Allah ya 'dora miki jaraba.�
Ashagwa'be ta ce“Ni Babana nake tunawa, ai da yana nan da mun gaisa da Ja'afar...�
Maka ta kai mata, ta goce aguje ta nufi 'daki.
“Dawo ki gyara min kayan miyi ko wlh na jibga miki tsinannan duka, ai jarabarce ta hanaki zuwa islamiyya kikace kanki na ciwo Aydah ta fa'dan lafiyarki lau. Munafuka
tinda ke bakisan inda yake miki ciwo ba.�
Ibtisam ta fito tana goge hawayen fuskarta, rashin jin Ja'afar ayau ba 'karamin tayar mata da hankali yake ba.
Tana tsakiya da gyaran kayan miyar ne wani yaro ya shigo da sallama, ya ce“Ana sallama da Ibtisam.�
Ibtisam ta ce“A'a wlh ba dai ni ba...�
Laraba ta ce “Sai ubanki ko? Ta shi dan ubanki. Kai waye me sallamar?�
Yaron ya ce“Wlh ban sansa ba amman alhajine aqatuwar mota.�
Laraba ta gwagwalo idanu ta dafe 'kirji ta ce“A me? Mota fa?�
“Eh wlh mota.�
Ya fa'da yana fita.
Laraba ta warci mayafi ta nufi qofar.
'Dam ta le'ko karaf idanunta sukasauka akan wata jibgegiyar mota fara kirar Ferrari, wani mutum tsaye zai kai kimanin shekaru arba'in, wankan tarwa'da mai bu'dadd'an hanci bakin wannan gari guda idanunsa kamar na biri😂.
Laraba ta dafe 'kirji ta ce“Shi kenan ubangiji ya amshi ro'kona, yarinya zata shiga gidan huta haka babban mutum wanda yasan darajar mace.�
Aguje ta iso ta ce“Maza dan ubanki jeki babban kamune, wlh idan kika masa rashin kunya ni dakene.�
Ibtisam ta fashe da kuka ta ce“Wlh kowaye ban sonsa Ja'afar 'dina nake so.�
Laraba da qarfin tsiya ta saka Ibtisam fita wajan.
Daga nesa Ibtisam ta tsaya tana addu'a dan ita tsoronsa ma take ji.
Baki ya washe ya ce“Ba gaisuwa baby? �
Ibtisam ta ce“Baba ina yini? Kayi hkr babana baya gari.�
Alhj Jamilu ya ce“A'a ni ban haifeki ba, zance nazo, wlh ina sonki inada mata da yara uku, mgna nazo muyi ta fahimta kinji.�
Ibtisam ta ce“Don Allah kayi hkr inada wanda nakeso yana sona Allah ya baka agaba.�
Ta na gama fa'din haka ta shige ciki yana kiranta ya bata Ku'di ta'ki komawa.
Ashe laraba tana lab'e tako shiga jibgarta tana fa'din.
“Wlh sai kin aure shi bazaki mana asaraba shegiya uwar ba'kin ciki.�
Ibtisam taci kukanta har ta gaji dan ta daku. Yaro aka turo da 'katuwar leda shaqe da kaya. Laraba baki yaqi rufawa lokacin da ta bu'de taga kayan lashe², harda turaruka sabulu da ku'di jaka arba'in.
Ihu tadinga yi ta shi'de tukunyar tuwon ta ce“Wallahi gasashen nama zamuci da lemon Oriba, jaka arba'in afarkon dance?�
Baki 'daya Laraba ta ru'de sabida murna, yayin da Ibtisam ta la'be tana kallon ikon Allah wajan uwar tata.

Unguwar Moray
Inna mai waina zaune gindin murhu tana girkin dare, Deluwa na wanki salad su na ta'ba hira. Mahmoud 'kanin Ja'afar ya shigo da sallama ya be'kawa inna mai waina waya.
Amsa tai tana washe baki ta ranga'da sallama.
Ja'afar ya gaisheta daga can, ya 'dora da fa'din. “Inata nemanku yau shiru innata fatan kuna lafiya?�
“Yaron kirki duk lfyrmu lau wayan babanka ruwa ta fa'da yau ta'ki tashi shiyasa baka jimu ba. Fatan kana lafiya?�
Ya amsa mata“lafiya lau, ya kowa da kowa? agaishemin su.�
“Zasuji ya aiki? Har yanzu ba'a samu mai 'kwari ba? Allah ya temaka ya yi bu'di na alkhairi.�
Deluwa ta ba wayan su ka gaisa tai masa fatan alkhairi, yama Mahmoud sallama ya ce zai kira zuwa dare idan Babansu ya dawo gida...

*Tchad*
Yahaya na parking Rahma ta fito ta temakawa dattijon ya fito, ta kalli Yahaya ta ce.
“Kamashi don Allah muje naga 'bangaran da zai zauna asamo wanda zai dinga kulawa da shi har ya murmure.�
Yahaya ya jinjina kai kasada irin ta yarinyar duk da shima tsohon ya basa tausayi. Ciki ta nufa mintinan da ba sufi 10 ba ta fito da makulli ta ce
“Muje.�
Wani 'bangare suka nufa.
'Kofar ta sanye key ta bu'de.
Kewayene 'dan madedeci flowers ashuke ko ina filin.
Key ta sanya ta bu'de 'kofar falon.
Ma Sha Allah tsaf falon 'dakuna na bacci guda biyu.
“Yauwa Yahaya bari yanzu na turo Latifa tai mopping muje ka nuna masa wajan wanka don Allah ya yi wanka bari akawo masa kayan sawa bari na za'bo masa cikin na Abiena.�
Tshon ya Saki kuka ya ce“Allah ya albarkaci rayuwarki ya saka miki da alkhairi ko amafarki ban ta'ba zaton zan samu masu temakona ba, sabida najima ina gararin rayuwa.�
Rahma ta ce“Ameen ba kome daina kuka.�

Jaddatu zaune wata matashiya a'kalla zatayi shekaru 27 ahaife, kallo 'daya zaka mata kasan jininta ce sabida tsabar kama da take da Jaddatu da Abie, kyakkyawace sosai balarabiyar asali, sai wata yarinya bazata wuce shekaru 7 ahaife ba, saman cinyar mamar tata tana zuba shagwa'ba.
Jaddatu tana kur'bar shayi, sai surfa masifa take.
Hanan sai dariya take ta ce“Don Allah ummina ki dinga hkr da Latifa, wai me laifinta?�
Jaddatu ta ce“Hanan Latifi ta ciki munafurci ne acikin dukkan lamuranta wlh.�
Iman ta ce“Jaddati ban shayin.�
“Amashi makwa'daiciya wlh nasan daman shine kike ninnik'ewa jikin uwarki.�
Rahma ta shigo ta zauna a falo tana kallon wayata 6 na yamma.
Lumshe 'kananun idanunta tai tana girgiza 'kafafunta, ta shiga kiran Latifa. sai gata aguje ta zube gabanta ta ce“Ga ni uwar 'dakina barka da dawowa.�
Rahma ta ce“Kije 'bangaran yamma kusa da 'bangaran ma'aikatan gidan, wanan 'kofar za ki ga 'kofar bud'e ki shiga har falon mopping zakiyi mai kyau ki goge har Tv da kujeru.�
Latifa ta ce“An gama insha Allah.�

Jaddatu ta ce“Latifa anji munafurci ashe 'dazu bakece kika dafa shayin ba?�
Latifa aranta ta ce“Ya Allah ka shiga tsakanina da tsohuwar nan me neman ganin bayana agidan nan?
Azahiri ta rusuna ta ce“Jaddatu Rahamu wlh Ummu Adnan ce ta ce na bari zata dafa naje na gyarawa Uwa d'akina 'bangaranta.�
“Ai da kika kawomin nunawa kikayi kece kika dafa, har na yabeki

Please Login or Register in order to submit comment