Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba mune zamu bata lfy ba, Allah ne zai bata, haba ina anfanin zabur da kima cikin jama'ah...�
Abie ne ya ajiye jaridar hannunsa yay gyaran murna.
Tanko yaja bakinsa yay shiru.
Anutse Abie ya ce“ kayi hkr harda rashin sabo.�
Tanko ya ce“Shi kenan Alhaji Ngd sosai Allah ya biyaka da gidan aljanna.�
Abie ya amsa da “Ameen.�
Ya 'dauki jaridarsa yana karantawa.
Ja'afar takaicin Laraba kamar zai kashesa, duba da yadda larabawa da turawa suke kallonta suna dariya.
'Karamin tsaki yaja a 'boye ya na mamakin halaiyar Laraban, wai shine yake janyo musu musifu.

Kallon Ibtisam yay yana riqe da ita jikinsa, bata iya ko 'daga 'Yar yatsarta sbd alluran da aka mata,shiyasa tai lamo jikinsa tana famar zaro idanunta cizonsa take so ta yi ta kasa sbd batada kuzari ko guntu atare da ita.
Hancinta yaja ta hararesa tana zaro masa idanu.
Guntin murmushi yay yana 'daga mata gira.
Karaf akan idon Laraba, wacce ta takure waje 'daya.
Ta ce“Lah ha ilah illallahu! Me zan gani Jafaru iskancin da yasa ka nace ka biyo mu kenan? Yarinyar ba lafiya keke neman koya mata iskanci? Toh meye idan ba iskanci ba 'daga ma mace gira....�
Wawan bugo Tanko ya kaima bakin Laraba tai saurin kaucewa tana rufe bakin nata.
Abie kunya ta saka bai 'dago kansa ba yana mamakin matar matuqa.
Ja'afar ransa ya 'baci sosai amman yay shiru bai ce komai ba.
Tanko cikin kwantar da murya yaba Ja'afar hkr.
Ya kalli Abie ya ce“Don Allah Alhaji daga munje an bata 'daki idan zaka dawo zamu biyoka wlh MATAR nan bazata bari azauna lafiya ba acan shi ka'dai zai iya jinyar matarsa daman ai ba yarda take damu ba.�
Abie ba tare dare da ya yi mgana ba ya jinjina kansa hakan ma ya yi.

Rahma ma tana can tana shirin tafiya Espagne gobe insha Allah.

Sai tsakiyar dare suka shigo 'kasar Australia.
Tinda airport Ja'afar yasan lallai wannan 'kasar babbar 'kasa cikin manyan 'kasashen duniya.
Laraba 'kauyanci 'kiri² ta dinga nunawa.
Wasu manyan motoci guda biyu akazo tarbarsu da ita.
Lallai Abie babban mutum ne wanda duniya ta san da zaman sa.
Ba hotel suka nufa ba, wani tamfatsetsan gidane wanda yake mallakin Abie 'din.
Tinda wajan gidan zakaji sha'awar ina ma ka kasance acikinsa.
Suna shiga falon wanda ya gaji da ha'du suka zazzauna.
Pa 'din Abie nan Australia ya shiga musu sannu da zuwa bayan ya jido kayansu.
Abie ya ce “Nadeer yanzu dare ya yi sosai zuwa gobe sai muje asibitin kaje kaima ka kwanta sai da safe.�
Cikin girmamawa Pa Nadeer ya amsa “Allah ya huta gajiya Oga.�
Babban kukan Abie wanda idan yana 'kasar shine ya shirya musu daddan girki nan falon saman carpet ya shimfi'da wata babbar lade mai kyau ya jera musu abincin.
Sai da sukaci suka nat Abie yama Tanko da Laraba jagora Inda zasu kwana.
Yazo yama su Ja'afar wanda Ibtisam 'din bacci take.
Abie ya ce“Kaje da abinci idan ta farka cikin dare sai ka lalla'ba ka bata, ka dinga kiyayewa kar ka ajiye duk abinda kasan idan ta gansa zata iya 'dauka ta buga maka.�
Ja'afar yay godiya yana qara ganin kima da darajar Abie 'din.
Abie bayan ya rufe falon ya shige bedroom 'dinsa mai girman gaske ta tsaru. Wanka yay ya 'dauro alwala ya shirya yana baza 'kamshi ya Rama sallar magarib da isha, ya miqe ya fara nafila.
Ja'afar ma hakance bayan ya kwantar da Ibtisam yay wanka ya rama sallah ya shiga nafila dan tin rada ya dawo haicinsa bai sake cikakken baccin dare ba sosai.
Abie sai 'karfe uku ya gama bayan ya jima yana ma Allah kirari yama mahaifinsa da Ummu Aymana and Aliyu addu'a, ya miqe ya cire jallabiyar ya sanya kayan bacci kwaso wayoyinsa yana dubawa kasancewar layinsa na Australia har biyu.
Ganin kiran Rahma yay har miss calls 6 a'dayar layin miss calls 7 da message 2.
'Kwan filar 'dakin ya kashe ya bar na gefen gadon ya 'Kara gudun Ac kasancewarsa mutum mai son sanyi sosai. kwanciya yay yana dafe goshinsa Allah ka'dai yasan halin da take ciki.
Message 'din ya duba.
_😭“Abiena Allah yasa kana lfy ina kiranka ka qi ka 'dauka na kasa bacci ina son naji lafiyarka, ya gajiya? I miss you so much Abiena.😢_
Kansa ya dafe yana fa'din.“Oh! Babyna ina fa lfy gajiya ce kawai.

Bai kirata ba ya tura mata message.
_😔“Wayyo Babyna yi hkr Abienki ya gaji ne, sosai ina lfy, gobe zan kiraki nasan yanzu kinyi bacci, kina maqale cikin zuciyata ban manta dake ba, gajiya ta saka ban kira ki ba, miss you too baby ummina.😘_

Dr Moha ya kira sukayi mgna akan gobe suna shigo asibitin.
Har tsawon 5 minutes yana jiranta shiru yay murmushi daman yasan ta yi bacci.
Addu'ar kwanciya bacci ya karanta ya rufe rabin jikinsa da blanket, ba jimawa bacci yay awon gaba da shi.

Ja'afar uku bata qarasa ba, ya kammala ibadarsa ya miqe da jallabiyar ya kwanta yana rage hasken 'dakin.
Jikinsa ya jayota ya rungumeta tsam yana kallon kyakkyawar fuskarta, yana shafa gashin kanta wanda bai fiye yawa ba.
Addu'ar kwanciya bacci ya karanto musu.
Yaji Ibtisam ta fara motsi sai yaji ta shige cikin 'kirjinsa sosai ta 'kan'kame shi.
Ajiyar zuciya ya sauke ya sake matseta gam yana shafa bayanta alamar lallashi.
Cikin baccin gajiyar da ya 'daukei shi yaji wata irin iska mai 'karfi kamar guguwa.
Azabure ya bu'de idanunsa bakinsa 'dauke da addu'a.
Abienda idanunsa suka gane masa'ne ya yi masifar gigitashi.....!!

_💃�'Yar Ajin Tubarkallah🥰_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/2/22, 22:41 - Buhainat: ```D A```

```47&48``

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

Sosai Ja'afar yake zaro idanunsa, wanda suka numa zallar tsoronsa akan abin al'ajabin da ya gani.
Duk da ya kasance jarumin namiji marar tsoro amman lamarin na yau ya yi mugun tsorata shi, wanda ya nemi addu'ar da yake cikin bakinsa lokacin da ya farka amman ya kasa, sakkamkon abinda yake tsaye gabansa.
Yawun bakinsa ya ji ya 'kame baki 'daya. Da sauri ya rarumo Ibtisam ya rungumeta gam a 'kirjinsa, yana kallon ikon ubangiji.
Yaron nan makaho da ya temakawa sanye da wasu irin kaya ya yi shiga irin ta 'ya'yan sarauta, sandar da take hannunsa kallo 'daya zaka mata kasan ta zinarince.
Sai wasu irin manyan halittu masu 'kirar 'karfafa, kallo 'daya zaka musu kasan ba mutane bane.
Gabansa ya 'karaso yaga cikin halittun biyu wanda yafi tsayi da girman ya beqa dogon hannunsa wata lafiyayyar kujera ta lu'u-lu-u ya ajiye agabansa sai walqiya take ya zauna dab da gadonsu.
Cikin sansanyar murya ya ce.
“Assalamu alaikum Ja'afar.�
Ja'afar 'yar zufar da ta karyo masa ya goge yana sake rungume Ibtisam jikinsa.
Numfashi mai 'karfi ya fizgo cikin jarumtarsa ya amsa.
“Wa'alaika salam, bawan Allah ba kai bane wanda na tsallaka saman titi? Shin ya akayi kazo nan? Sannan wannan halittun fa!?�
Hussain yay murmushi ya ce.
“Ya kai bawan Allah Ja'afar haqiqa nine wanda ka temakawa, ni musulmi ne mu 'yan biyune 'dan uwana Hassan ba ruwansa da rayuwar bil'adam, ni kuma haka na taso da son bil'adam, da son temaka musu amman na 'kwarai fa!ni ba mutum bane aqalla yanzu inada shekaru dubu 'daya da 'dari biyu da goma sha 'daya da kwana 17 yau cif aduniya.
Najima ban samu wanda ya temaka min ba irinka, tinda nazo duniya cikin wannan shekarun nawa kaine mutum na tara da ya temakeni cikin mutane duk da ba wai ina buqatar temakon ba, inayine kawai dan ware bil'adam irinku masu Neman temako, mu tarbi inda mukasan zaku wuce da zaran kun temaka mana sai muma mu temakeku. Akwai wa'danda zakaga suna cikin halin neman temako ko wata gagarumar matsala,muke fitowa mu tarbesu mu nuna atemake ko abinci ko sutura ko halin rashin lafiya ko Neman sadaka ko atsallakamu titi, kawai sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, wataran harda mari ana nuna mana 'kyama bayan mu'din cikin jansin mu ma babbar sarauta garemu mun gama samun duniya lahira muke nema. Amman duk da haka ni ban ta'ba 'daukan fansa ba akan kowa temakon ne kawai bazan ma wanda bai min ba, idan ka mareni nasan agaba zaka ha'du da daidai kai sabida nawa mahaifin bazan ta'ba cutar da bil'adam ba. �
Ja'afar sosai yake atsorace amman ya jure yana kallon Hussain ya ce.
“Ai ni kuma aganina ban maka wani temako ba da ya cancanta ka sakamin, ai ba komai yiwa kaine toh da me zaka sakamin?�
Hussain yay murmushi yace bari kaga yanzu na dawo asalina.�
Yana qarashe mgnar yay wata irin girgiza take ya riki'de ya dawo Hussain 'dinsa sak babba kuma cikakken aljani.
Ja'afar ya ce.
“Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahamnir rahim.�
Hussain ya ce “Ai banzo da niyar cutar da kai ba, zan temaka maka akan matarka dan wlh kafin Ku samu maganin da zai warka da ita zaku jima duk da ba abinda ya gagari Allah.�
Ja'afar jin ya ce Ibtisam zaima magni cikin murya ya ce“Amman da naji da'di.�
Hussain ya ce“Insha Allah 'dago kanta.�
Ja'afar jikinsa na rawa ya 'dago kan Ibtisam, Hussain ya beqa hannun ya dafe goshinta.
Wani irin haske hannunsa ya fara idanunsa arufe bakinsa na motsawa.
Kusan 30 minutes, ahakan, kafin Ibtisam ta fara wata irin rawa jiki da kyarrrma numfashinta na sama da 'kasa.
“Karka ji tsoro Ja'afar sai mun cika awa 'daya cif.�
Kai kawai Ja'afar yake 'dagawa.
Sosai ya girgiza da lamarin yadda Ibtisam take zanzana.
Sandar hannunsa ya 'daga ya fara karatu yana tofawa, wanda goshinsa ya fara fitar da zufa, ya buga atsakiyar kan Ibtisam, wanda atake ta 'kurama ihu ha'di da fa'din “Wayyo Allah nah! Ja'afar ka cuceni, zan mutu ban nemi gafara iyayena ba! Na tsaneka bana sonka...!�
Sai kuma tai shiru tana sauke numfashi alamun bacci.
Hussain ya ce“Alhmdllh! Tana farkawa bacci lafiya zata farka sai dai baccin zai jima zata ita kwana da wuni ahaka karka damu tana tashi komai ya wuce Insha Allah, dan haka karku kaita asibiti dan batada wata matsala yanzun, na barku lfy ina muku fatan alkhair ki bi sannu ka saddo 'kasa ka 'kas'kantar da kanka ka lallashi yarinyar ka bata kulawa karka yi girman kai cikin lamarin sannan karka yi fushi ka biye mata ka yanke hukunci cikin fushi duk zakuyi nadama daga baya, idan kunbi son zuciya, da kuma 'bacin rai, ka riqe mganata ka rungumi matarka tana sonka da zaran ka ajiye jiji da kanka ka lallasheta komai zai wuce fatan alkhairi .�
Ja'afar da'di ya rasa inda zai tsoma ransa sai godiya yake ma Hussain.
Iska da guguwa mai 'karfi wacce tafi ta farko ita ce ta turniqe 'dakin kafin giftawar idanu sun 'bace.
Kumaa daidai lokacin ake kiran sallar asubah.
Ja'afar ya kwantar da Ibtisam ya zuba mata idanu cikin farin ciki wai ta warke.
Miqewa yay ya shiga toilet yay wanka ya 'dauro alwala ya fito ya sanya jallabiya ya tayar da sallar raka'atanil fajir.

Abie amakare ya farka dan lokacin an fara sallah, masallaci, agaggauce yay wanka ya 'dauro alwala yay sallah.
Bayan ya gama ya fara azkhar.
Bayan ya idar ya miqe ya fito falo yana Jan cazbi.
Da mamaki yake kallon Ja'afar da Tanko zaune falo suna magana cikin zallar farin ciki wanda ya ga Laraba sai washe haqora take.
Sallama yay musu suka gaisa cikin mutuntaka.
Abie ya ce“Ya dai ko an samu wani ci gabane wajan Ibtisam?�
Cikin farin ciki Tanko ya ce.
“Alhaji daman zaman jiranka muke bai kamata kana hutawa atasheka ba,Allah ya dubi kirkin ka da temakon ka, ya ragema wahala, jiya cikin ikon Allah cikin tsakiyar dare......�
Tsaff ya labartawa Abie yadda Ja'afar ya labarta masa daga kan temakon da yawa yaron makaho zuwa zauwarsa da abinda yama Ibtisam zuwa ihunta da kiran sunan Ja'afar da tai da yadda Hussain ya ce da zaran ta farka zata tashi normal kar aje asibiti abari har ta farka.
Abie ya sauke ajiyar zuciya zaiyi magna kiran Rahma ya shigo wayarsa.
Bai 'daga ba ya kallesu ya ce.
“Ma Sha Allah Alhamdllh! Abu ya yi kyau toh ba damuwa zamu jira muga farkawar tata amman duk da haka zamuje aqara dubata idan ta tashi.�
Ja'afar cikin murna ya ce“Abie Allah ya qara girma da bu'di.�
Abie ya 'daga wayar yana amsawa da “Ameen ya Allah Ja'afar.“
Wayar ya kai kunnensa yana miqewa ya nufi bedroom 'dinsa.
Zazzafan numfashi ya sakar mata ta cikin wayar ha'di da sauke ajiyar zuciya, cikin sansanyan murya ya mata sallama.
“Assalamu alaiki Ya Baby Ummina.�
Rahma daga can ta turo baki gaba tana amsa sallamar, ha'di da cewa.
“Abiena I miss you fatan kana lafiya? Ya gajiya? Jiya nayi bacci marar da'd, pls Abie ka biyo Espagne na ganka pls karka wuce Chad.�
“Alhmdllh Babyna hope kina lfy ya shirye² tafiya? Na miki alqawali zuwa nima bazan iyaba nayi kewarki sosai Habibaty Ummi�
Ashagwa'be ta ce“Uhmm! Anjima ka'dan ne Abie zamu tafi, ok sai kazo, rabin raina.�
A tausashe ya ce“Masha Allah babyna sai na shigo jibin insha Allah ki kularmin da kanki zan kiraki OK? Pls kici abinci nasanki bakya cin komai cikin jirgi.�
Asanyaye ta ce“Ok Abiena bari na kwanta ka'dan bye.�
Murmushi yay ya sumbaci wayar ya ce“Allah saukeku lfy bye baby Abienta.�
Asakalce ta kirasa.
“Abienah!�
“Na'am babyna! Oya kwanta kiyi bacci ki huta kafin lokacin tafiyarku.�

Abie Dr Moha ya Kira ya ce ya ya qara hkr zuwa dare ko yamma zasu shigo hospital. Daga nan ya Kira Jaddatu da Hanan and Abie 2 suka sha fira.
Misalin 9 Abie ya kirasu Tanko duk suka fito sukayi breakfast wanda kukun Abie ya musu breakfast mai da'di da ha'daddan tea, bayan sun gama Abie ya ce suje su kwanta su huta, su jirayi tashin Ibtisam.

*Tchad*
Misalin 'karfe 11 na safe jirgin su Rahma ya 'daga zuwa 'kasar Espagne, bayan ta yi sallama da 'yan gidansu Latifa harda kukanta.
Abie da Hanan har airport suka rakata sai da jirginsu ya tashi suka dawo gida.
Jaddatu zaune tana mitar tafiyar Rahma.
“Wlh gidan yau ba da'di duk da daman sai ta ga dama take zama 'kasa amman banajin da'di. Oh! Wai Latifa harda kuka samun waje.�
Ummu Adnan da take yanka mata kanka da apple ta gintse dariyarta tana fa'din.
“Jaddatu sabo akace tirken wawa.�
'Karan doorbell na falo ne ya Hana Jaddatu mgna ta ce“Je ki bu'de.� Abraham ne tsaye bayan sun gaisa ya ce.
“Yauwa ka ce da Ummi baqon malamin yazo an sauke shi ya jima na bari ya hutane yanzu sai amasa iso ya ga marar lafiyar.�
Ummi Adnan ta amsa da“Toh ba damuwa.�
Gaban Jaddatu ta zube tana mata bayani.
Jaddatu ta lunquma kankana bakita ta ce “Toh toh ba laifi je kicema Saratu ta shirya sai afito da ita falo ayi komai agabanmu kamar yadda me gidan ya fa'da.�
Ummu Adnan ta amsa da “Toh an gama.�
Miqewa ta nufi bedroom 'din.
Raiyana zaune Saro ta shiyarta da kyar, sai wasu irin fizge² take tana zabura tana taune bakinta, tana jujuya idanu duk ta ko'de ta rame.
Da sallama Ummu Adnan ta shigo.
Amutunce suka gaisa da auntie Saro, ta mata bayanin komai.
Saro ta ce“Ok kamata muje tinda ashirye take, naga kamar da sauqi jiya zuwa yau gaskiya.�
Afalon suka zauna da ita saman carpet.
Jaddatu ta tsira mata idanu tana tauna tufa ta girgiza kanta tana fa'din.
“Wallahi Raiyana kin cutar da kanki matuqa na miki sha'awa zama da Abdul. Ummu Adnan je kice su shigo, amman kira min Hanan idan kuma bacci take barta karki tasheta.�
Cikin girmamawa ta amsa ta nufi corridor 'din da zai kaita bedroom 'din Jaddatu. Bacci ta iske sunayi ta fito ta sanar da Jaddatu ta tafi kiran Abraham da baqon.
Abie da Mal Adamu tsaye suna mgna da Abraham akan baqon.
Ummu Adnan ta sanar da Abraham su shiga.
Abraham ya Kira baqon.
Masha Allah babban mutum ne kana kallonsa kasan malamine wanda yasan abinda yake ba muna malami ba, Qur'ani ce ahanmunsa da wata roba mai 'dauke ruwan addu da bulala lafceciya wacce taji addu'in ayoyin Allah.
Sallama yay musu suka amsa sukayi musabaha, Abraham ya masa jagora zuwa ciki har da Abie sbd idan ta Kama ya temaka masa sai ya temaka masa.
Mal Adamu ya koma ciki ya zauna wanda Abie ya roqi alfarmar ya jirasa har ya dawo.
Suna shigowa falon cikin kamilalliyar muryasa yay sallama.
Raiyana ta zabura ta 'kurma wani irin ihuui jikinta na rawa ta arta aguje tana neman wajan 'buya.
Jaddatu ta ce.
“Maza Saro Ummu Adnan akamota.
Malam ya ce“A'a Ku barta.
Wata irin tsawa ya daka mata ya ce“Maza kuzo nan kumin bayani kafin yanzu jikinku ya fa'da muku.�
Raiyana da ta shige 'kasan kujera jikinta ma rawa ta fito ta nufo wajansa ta zube gabansa tana ha'ada hannayenta........
*Pls kuyi manage ina busy ne.*
_💃�'Yar Ajin Tubarkallah🥰_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/3/22, 15:25 - Buhainat: ```D A```

```49&50``

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

Cikin wata irin murya marar da'din sauraro, ta fara mgna tana sake ha'de hannayenta.
“Mun tuba malam karka 'karasu duk an 'konemu, karka 'karasamu.�
Malam ya zauna ya na kallon Raiyana baiyi mgna nazartar ta yake sosai, tabbas aljannun gaskiya ne ba na 'karya ba, addu'a ya fara ya bu'de roba me ruwan addu'a ya 'dan watsa mata.
Ihu ta saki tana qoqarin tashi amman ta kasa dan ya 'dauresu tam awajen.
“Kukuwa me ya kawoku jikin baiwar Allah nan? Lallai ku fa'damin gaskiya idan ba haka ba zaku 'kone tsaf zan 'kone ku 'kurmus.�
Ya na idar da mgna bai jira komai ba ya bu'de Qur'ani ya fara karatu.
Rawa jikinta ya fara tana wata irin lauyewa azaba suke sha sosai, daman an 'kone musu rabin jikinsu lkcn suna jikinsu Rahma.
Wani ihu suka saki suna fa'din.
“Zamu fa'da zamu fita karku rabamu da 'ya'yanmu.�
Dakantawa Malam yay ya ce.
“Muna jiranku me ta muku?�
Cikin azaba da fitar hayyaci suka zayyanewa malam dukkan abinda ya faru tiryan-tiryan.�
Malam ya ce“Subahanallahi! Haba! Me yasa za'a ha'da baki daku acuci 'yan Adam? Jansin mu ba 'daya ba da ku, dukkanmu Allah ya haliccemu ne dan mu bauta masa, amman dayawa daga cikinku bakuda komai sai zalumci sai cutar bil'adam. Toh yanzu abinda nakeso daku kuji tsoron Allah ku tuba ku koma ga Allah, ku daina ha'da baki da bokaye dan bazan Kira malamin tsubbu malami ba, ku daina shiga jikin mutane kuna cutar dasu.
Ku fita fita ta har abadan baku ba ita.�
Kai Raiyana ta shiga 'dagawa alamar yarda.
Bulala ya zuba mata sau uku, tai wani irin 'kara ta zube kwance wajan tana atishawa ba qaqqautawa ajere wajan sau hamsin wani irin baqin hayaqi ya dinga fita bakinta da hancinta da wasu irin ruwa masu yauqi su ba blue ba su ba baqi ba.
Shiru kakeji sai bacci Raiyana take tana sauke numfashi.
Malam ya ce“Alhamdulillahi! Komai yazo 'karshe insha Allahu bazasu dawo ba, ga wannan ruwan idan ta tashi abata tasha, insha Allah bazu sake cutar da ita ba...�
Jaddatu ta fashe da kuka tana fa'din.
“Amman mu ai ta cutar damu, Allah ya isa Raiyana wlh kinyi asara Allah da nasan kece kika ha'da wannan masifar tsakani takwara da Ja'afar bazamu barki ki zauna agidan nan ba, wlh yau 'din nan sai kun fita kun barma na gidanmu Ashe ba dan Allah kike zaune damuba kema irinsu Zuwaira da Hanifa ne daman Naja'atu ba yauba Allah ya tsine mata albarka, dan ta kwashe kayanta daga gaban ma'aiki.
Tin bayan Naja'atu sai da yaron nan ya ce ya haramta aure naqi nake tirsasa masa har ya sake sau uku amman kowa da mugun nufinta kafin ya gama jarabasu sai Allah ya tona musu asiri toh wlh yanzu an qare matarsa zata bayyana ta Abadan nagaji da abinda ake masa.�
Ta 'karashe mgnar cikin kuka sosai.
Abie 2 hkr yake bata Hanan ta fito ta zauna tana binsu da kallo ta rungume Jaddatu tana tamabyarta.
“Wai ummina me ya farune?�
Hanci taja ta face majina tana fa'din.
“Hanan ashe duk mugun abun da ya samu Rahma kwanaki wannan annamimiyar wacce na 'dauka MATAR arziqi na saka ya aureta itace tahaddasa komai.�
Malam yay gyaran murya ya ce“Ayi hkr dan Allah addu'a zaku mata Allah yasa ta shiryu sanadin hakan, Allah ya kiyaye gaba, Abraham muje zan wuce insha Allah.�
Ya qarasa mgnar yana miqewa.
Har Abie suka fito suna jimamin abinda Raiyana ta yi toh me take nufi da hakan.
Saro kuka take kamar zata ha'di zuciya, ga kunya ta lullu'be ta yi da ta sanin kasancewar Raiyana 'yar uwarta sabida iyayansu basu 'dorasu akan turba marar kyau ba.
Jaddatu ta ce“Wlh ko kukan jini kike sai kunbar gidan nan yanzu munafukai azalumai...�
Hanan ta rufe mata baki ta ce“Haba! Ummi kiyi hkr aka kashe miki miji ma kika hkr bare wannan, sannan don Allah ki bari wanda ya ajiyeta yazo sai kiji irin hukincin da zai yanke ba ruwanki dasu, Saro kamata ku shiga ciki.�
Ummu Adnan ta kamata mata suka cicci'beta suka nufi bedroom.
Jaddatu sai kuka take dakyar Hanan ta lalla'bata.
Abraham ya sallami Malam yana masa godiya har tashar mota ya kaisa.
Abie 2 ya jima yana mamakin al'amarin akan me Raiyana ta ha'da Rahma da Ja'afara soyayya?

*Australia*
Misalin shabiyu Ibtisam ta farka.
Ahankali ta fara qoqarin bu'de manyan idanunta, wanda taji sun mata nauyi sosai ga wani irin zafi da sukeyi.
Jinta manne ajikin mutum ga wani irin 'kamshi mai masifar da'di ya mamaye dukkan 'kofofin hancinta tai saurin qarasa bu'de idanunta.
Basu sauka ako ina ba sai saman kyakkyawar baqar fuskar Ja'afar, yana manne da ita ya zagaye 'kugunta fuskarsu dab da juna suna jin bugun numfashin juna sosai.
Baccinsa yake anutse.
Manyan idanunta ta zaro tana fa'din.
“A'uzubillahir minan she'danir rajim! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! me kamin? Ina ne nan kamar na mutu ina aljanna? Wayyo na shiga uku ina ka kawoni bayan ka gama zalumtata? Wayyo Anna wayyo Baba ku yafemin sakammakon bijire muku anci amanata, an 'batamin rayuwa�.
Ta 'karashe mgnar tana fizge jikinta cikin zafin zuciyar da bata san tana ita ba.
Amman ko gezau ta kasa amshe jikinta daga Ja'afar.
Tattausan hannunsa ya sanya ya rufe mata baki, ya mata rumfa da faffa'dan 'kirjinsa.
Wani irin kallo ya watsa mata wanda abaya yake sakawa ta shiga hankalinta.
Sosai taji tsoronsa, amman sai ta dake tana ture shi tana dukan 'kirjinsa hawaye yana shatatowa kan fuskarta.
Fuskarta ya riqo da hannunsa ya zuba mata kyawawan idanunsa, wanda suke rikitata, cikin sansanyan murya ya fara mgna yana shafa lips 'dinta.
“Mon cœur kiyi hkr kinji, ba da gangan naci amanarki ba,ki yafemin sanin kanki ne ni bazan ta'ba cutar dake ba ko kwanciya waje 'daya dake ba tare da kin halatta agareni ba.�
Ya 'karashe mgnar yana sumbatar goshinta da idanunta yana lashe mata hawayen fuskarta, wanda hucin numfashinsa yake sauka saman fuskarta tana shaqo 'kamshin bakinsa.
Ture shi ta shiga yi tana kuka, tana fa'din.
“Kai macucine na tsaneka sakeni bana sonka na tsaneka...!�
Baki ya rufe mata cikin zafin nama yana mata wani mugun kallo amman sam Ibtisam bataji bata gani ta dage sai wani irin kuka take tana son raba jikinta da na shi.
Cak ya 'dauketa ya nufi toilet.
Tana bayansa sai yakushinsa take ya ha'da mata ruwan wanka ya direta fuska ba wasa yana jafa idanunsa cikin nata ya ce“Wuce maza kiyi wanka kizo na kaiki wajan Baba.�
Bai tsayaba ya wuce.
Jin abinda ya ce ya sanya tu'bewa tana kuka tana kallon bathroom 'din wai wajan wankane nan kamar 'daki, zoben hannunta ta kalla yana walqiya kamar diamond, ta zaro idanu tana fa'din “Ina na samu wannan zoben mai kyau?�

Ja'afar doguwar rigar atamfa wace ya dinka mata ya ciro mata da pant daman yaga ba saka bra take ba, ya feshe kayan da turare madedecin mayafin ya ajiye mata gefen bed, ya fita domin ha'do mata abinda zata ci.
Cikin sa'a falon ba kowa ya wuce kan dinning ya ha'do mata tea mai kauri ya zubo mata soyayen dankali da kwai da naman rago wanda akayi farfesun sa ga hufzah gefe ya 'daukar mata biyu, yaje kitchen ya 'dauko tray ya jera ya koma 'dakin.
Wanka tai sosai taji da'din jikinta ta 'dauro alwala ta 'daura towel amman ta kasa fita kuma daman can Ibtisma idan ta cire kaya tayi wanka bata iya maidasu jikinta sbd 'kyan'kyami gareta.
Ja'afar jin shiru ya saka ya biyota.
Tsaye take tana rarraba idanu hawaye nabin fuskarta.
Bai mata magana ba ya kamo hannunta, tana tirjewa cikin kuka ta ce.
“Ina ka satoni ka kawoni? Wacce duniya ce nan Ja'afar na tsaneka ban son ganinka...�
Wata irin rikiracciyar tsawa! ya daka mata wacce tasaka Ibtisam rawar jiki ta qame waje 'daya tana shasheqar kuka.
“Wlh idan bakimin shiru ba zanyi maganin ki zo nan.�
Kanta ta sadda 'kasa taqi zuwa wajan nasa dan ta 'dauki alqawali sai dai ya kasheta bazata sake soyayya da shi ba.
Kai ya girgiza

Please Login or Register in order to submit comment