Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'kanwarsa.
Rahma tana tsaye sai da Ja'afar yaja motar ya tafi yana 'daga mata hannu tana 'daga masa ta jiya ta koma wajan Abienta.

*Gabon*
Misalin 'karfe 8 na dare jirgin su Ma'aruf ya shiga Gabon.
Nura direba yazo 'daukarsa, kai tsaye gida suka nufa.
Rabi'ah kuwa murna sosai take jin Ma'aruf ya ce wajanta zai fara zuwa, girkin da Aishatu ta turo masa shine ta tanadar masa sai lemuka da ta ha'da masa, da dambun nama.
Aishata najin tsayuwar mota ta miqe cike da murna ta leqa ta window.
Anutse yake tafiya waya manne da kunnensa.
Tin kafin ya iso ta bu'de 'kofar yana shigowa ta 'dare samansa tana fa'din.
“Oyoyo masoyina.�
Sama yay da ita yana 'kyal'kyala dariya ya ce“Aishatuna iyayan rigima ya babyna?�
Kumatunsa ta sumbata ta ce.
“Wlh kaji yana motsi kamar yasan kana nemansa.�
Sauka tai ta Kama hannunsa suka nufi saman kujera.
Zaunar da shi tai ta tsiyaya masa lemo mai sanyi ta basa abaki ya Sha.
“Thank u my life. �
Murmushi tai ta Kama hannunsa suka nufi ciki taje ta ha'da masa ruwan wanka suka tafi ita ta temaka masa yay wanka ta shiryasa tsaf suka nufi kan dining area.
Sosai ta cika masa cikinsa da dadda'dan girkinta.
Rungume take ajikinsa yana kissing 'dinta hannunsa saman cikinta yana shafawa, bata hanashi ba.
Akunne ya mata ra'da “Fa'damin kinyi kewata sosai?�
Kai ta 'daga masa sbd yadda yake lalubarta da kissing 'dinta ya gama kashe mata jikinta.
Wayarsa tai ringing yay sallon kallonta ya 'dauke sbd kar Aishatu taga sunan Rabi'ah.
Janyeta yay, ya ce.
“Masoyiya zanje gida na dawo.�
Rigima ta kafa masa sai sun tafi tare, baida za'bin da ya wuce ya tafi da ita sai ya barota gidan nasu daga can yaje wajan Rabi'ah ya dawo ya 'dauketa.
“Ok je ki shirya mu tafi.�.
Cikin murna ta nufi bedroom'dinsa sbd mafi yawa kayanta na nan.
Tana fita sai ga Uwani da gudu ta iso cikin girmamawa ta zube gabansa ta beqa masa wayar da take record mgnar Aishatu idan 'kawayanta sun zo ko tana waya. Ta 'dora da cewa “Bata wani yawo yalla'bai duk Inda ta tambayeka toh can take zuwa Nura direba na kaita.“
Cikin sauri ya ce“Ok! Ok jeki ngd zan saurara.�
Miqewa tai ta fice.
Shi kuma daman cikin shiri yake ya leqa bedroom 'dinsa dan ya ga nan ta shiga.
'Karan ruwa yaji ya ce“Wai wanka nema kike? Pls my life ki zauna gobe sai muje na tafi.
Kuka yaji ta saka masa, ya bushe da dariya ya ce“Wasa nake miki ina mota.�
Yana zauna cikin mota ya fara sauraren irin ta'bargazar sakin zancan da take sam batasan rufawa aurensu asiri ba.
Kai ya girgiza ya ce“Wato Rabi'ah da wannan damar ce zatayi anfani ta shigo rayuwarmu? Toh 'karya kike wlh zan koya miki hankali.�
Aishatu tana cikin shiryawa 'karamar wayar Ma'aruf ta fara ruri bata 'dauka ba, sai da aka Kira sau biyar ta 'daga da niyar cewa baya kusa taji abinda ya kusa 'dauke numfashinta.
'Kasa ta zauna jikinta na tsuma tana jin kalaman mutumin tamkar zasu tafi da numfashinta.
Saurin kashe wayar tai baki 'dayanta ta miqe dakyar ta shiga toilet taci kukanta ta wanke fuska ta fito da qudirin insha Allah sai Inda 'karfinta ya qare wajan ceto mijinta dan bataji 'digon sonsa ya ragu ba.
Sosai ta sanyama kanta jarumta ta 'ka'kalo murmushi ta shiga motar yana Jan hancinta ya ce“Kin 'batamin lokaci.�
“Sorry.�
Kawai ta iya fa'da.
Gidansu ya ajiyeta bayan ya gaisa da iyayasa da 'kannensa ya nufi gidansu Rabi'ah wanda da kwantaccan yazo har qofar gidan.
Har falon baqi wanda yake 'dan qarami sbd basuda wani 'karfi nan ta ajiyesa ta jera masa komai na ci gabansa tai serving 'dinsa
Ma'aruf ya 'kyal'kyale da dariya ya ce“Wai kina nufin irin girki matata kika min? Gaskiya na qoshi ta cika min cikina dam, sannan me ya saka kika za'bi kici amanarta bayan ta yarda dake?�
Rabi'ah kukan kissa cike da takaicinsa ta saki tana fa'din.
“Ba laifina bane ba zuciayta ke sonka.�
“Ok naji bari kuka amman abinda nakeso dake ki bari idan ta haihu sai ki tinkareta ki nemi alfarma kice ta amince na aureki idan ta yarda ba matsala zan temka miki kiji abinda ta kwa'daita ki da shi, idan kuma bazaki iya tunkartaba karki sake kirana.�
Yana gama fa'damata hakan yasa kai ya wuce daga falon.
Rabi'ah ta duqe tana sakin kuka mai ciwo, amman ta qudirta aranta sai ta 'dauki mataki akan Ma'aruf.

*Tchad*
Misalin goma na dare Tanko da Laraba suka shigo Tchad cikin garin Ndjamena.
Yahaya direba Abie ya tura ya 'daukosu.
Laraba tinda motar ta shigo tamqameman gidan na Abie ta fara zaro idanu tana dafe 'kirjinta ta ce“
Na shiga ukuna! Baban Ibtisam ina aka kawomu nan? Karfa siyar damu akayi.�
Yahaya dariya ta ku'buce masa yana fitowa ya bu'de musu qofa suka fito.
Laraba jikinta ko ina rawa yake tana kallon ko ina haske ra'dau tamkar Rana sbd waau irin 'kwayayan fitulu masu haske da bada Kala.
Malam Adamu ya taresu ya musu jagora har ciki ya nuna musu 'dakin wanda yake ware ya ce“Abie ya ce Ku zauna anan kafin ku tashi tafiya wajan, sannuku ya hanya?�
Tanko ya amsa “Alhmdllh! Muje sai kiyi wanka ki huta.�
Abie 2 ya iso yana musu sannu da zuwa ya kira Rahma awaya ya ce Latifa ta kawo musu abinci.
Rahma tana falon cikin sa'a ta kira Latifa ta saka ta kai musu abinci.
Adaren Abie ya musu jagora zuwa asibitin Ibtisam na barci Dr ya ce su koma dan basa buqatar kowa kusanta akwai ha'dari hakan.
Washegari tin safe Abie ya fita dasu domin ayi musu passport.
Cikin ikon Allah kwana uku kacal an gama passport Abie ya nema musu biza aka fara shirin tafiya wanda jirgin dole sai zuwa jibi zai ta shi zuwa Australia.
Laraba tin tana kukan halin da Ibtisan take ciki har ta hkr ta barwa Allah, dan jiya dukan tsiya ta mata wanda taurin kanta ne ya janyo mata, sbd ance tabar shiga idan ba bacci take ba Abie kawai yake iyamata sai Dr.
'Bangaran gidan ma tin tana 'kauyanci har ta saba da wannan 'katon gida har lambu take zuwa batada aiki sai tsinko lemu da guiba da magwaro.

Zaune take a falo tana sanye da abaya pink, ta yane kanta da mayafin fuskarta sam ba walwala.
Jaddatu ta kalleta ta ku'bi shayi ta ce.
“Yo Allah na tuba mu za'awa shan 'kamshi.�
Abie na danna laptop ya 'dago yana kallon Rahma ya murmusa ya ce“Zo baby fa'damin nine ko Ja'afar ne? Ko Ummina ce? Nasan hanan da Raiyana basa tsokanarki.�
Asakalce ta ta taso ta nufo wajansa ta zauna dab da shi tana kallonsa tana narai-narai da 'kananun kyawawan idanunta.
Raiyana takaici kamar zata ha'di zuciya ta mutu.
Abie ya ce“Bazaki fa'di wa ya saka min ke fushi ba?�
Ashagwa'be ta ce“Yo Abie ba wani bane ya takura min tin 'dazu an nkusa awaya ina baccina me da'di ya kirana sai masifa yake min wai sai na fa'da masa yaushe muka qulla soyayya yaga numbata an saka sunan Qalbina wayasa, kuma wlh ni ban sansa ba kuma naga sunan Habiby nima wayata Allah ban san shi ba shine nace yazo ayi qurayya muga juna, kuma fa bayajin larabci sosai sai français, na kwatanta masa gidan, ya ce zai zo.�
Jaddatu ta ce“Alhamdulillahi! Allah abin godiya, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halittun duniya Annab S.A.W.�
Abie ya ce“Ja'afar 'din kika manta Babyna�?
Rahma ta tsira masa idanu ta ce“Wlh Allah ban San shi ba waye¿�
Miqewa yay ya miqar da ita yaja hannunta suka nufi hanyar barin falon.
'Bangaran Abie 2 suka nufa sai yaga motar da Ja'afar ya danno cikin gidan. Tsaye Abie yay har Ja'afar yay parkint ya fito ya nufi wajan masu gadi.
Gaisawa sukayi cike da izzarsa murya 'kasa ya ce“Pls Rahma nake tambaya.�
Masu gadin abin ya basu mamaki. Hango Abie da Rahma suka nuna masa.
Bai ce 'kalaba sbd halinsa na shiru ya nufi wajan cike da takunsa na 'kasaita.
Rahma ta kalleshi ta waro idanunta waje cikin sanyinta na asali da ya dawo ha'di da zafin zuciyar da gareta idan taga abinda ya 'bata mata rai.
Hannayen Abie ta damqe sosai ta ce.
“Abiena wannan yaron nan ne da ya ta'_ba bugar mana mota kwanaki me yazo yi gidanmu?�
Abie ya lakaci hancinta ya ce“Baby ban sanki da fushi ba ki nutsu.�
Ja'afar da sallama ya iso wajan ya gaishe da Abie ya ce“Don Allah kece Rahma?�
Hararansa tai ta kwantar da kanta kafa'dar Abie ta ce.
“Ban saniba kaje Inda ka samu number tawa sai ka tambaya yaro kayi gaggawar goge numbata...�
Abie ya rufe mata baki da tafin hannunsa, ya mata ra'da akunne ta saki kukan shagwa'ba tana diddira 'kafa.
Ja'afar tsabar haushinta da takaicinta ya saka ya juya ya fara tafiya cikin zafin zuciya ganin marar kunyar yarinyar nan ce yana goge number ta, sauri yake yabar gidan dan ya tsani shiga gidan masu ku'di Sam.
Number Ibtisma ya kira akshe ya dafe goshinsa yana sake sauri.
Abie ya kirasa Ja'afar! Dawo ga mahaifinka nan fa!�
Idanuwa Ja'afar ya waro waje yana juyowa cike mugun tsoro da ki'dima kar dai ace babansa ya gane Ibtisam na wajansa?
Juyowar da yake yaga Tanko malam Adamu Abie 2 Laraba gefe.
Badan namijin gaske bane da ya zube 'kasa sabida muguwar ka'duwa da abinda ya gani agabansa.
Idanunsa ya murza da kyau tsaf yaga malam Adamu mahaifinsa tsaye yana Jan casbi.
Adaidai wannan lokacin Aljannun da malam ya turama su Ja'afar suka dira gaban Malam Rabin jikinsu a 'kone halittar tasu ba kyan gani.
Malam ya ce“Maza kuje wajan wacce ta ta 'dauki alhakinku ba niba.�
Wanda adaidai wannan lokacin Raiyana da take ganin abinda yake faruwa, tana la'be sulalewa tai 'kasa sumammiya tsabar bugawar zuciyarta, da tuno sharu'dan malam...........!


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/24/22, 16:54 - Buhainat: ```D A```

```39&40```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

_Wai 'yan *Fitattu 4* me yasa kuke fitar min da littafina? Ko dan kunji nace bazanyi Allah ya isa ba? Ku tuna haqqina ne fa! Don Allah kuyi hkr ku daina sbd wlh Nagano kune ba 'yan paid group 'Dina bane, sbd shedar da nakeyi. Wlh bana so har can 'kasan zuciyata ban ta'ba roqonku ba yau na roqa ku daina, don Allah wlh idan nagansa bakusan yadda nakeji ba, ku daina pls.��😭_


Jaddatu da Hanan da suka biyo bayansu Abie, su ga meke faruwa ne suka saki salati, ganin Raiyana ta zube 'kasa sumammiya.
“Hanan yi sauri kawo ruwa.�
Robar ruwan da take hannun iman Hanan ta amshe ta shafama Raiyana afuska ta zuba mata saman 'kirjinta.
Ajiyar zuciya ta sauke, wani irin 'bari jikinta ya fara.
Jaddatu ta ce“Mun shiga uku! ke! Raiyana lfy kuwa? Kike abu kamar mai ciwon farfa'diya?�
Raiyana sai shure² take bakinta na fitar da wani irin baqin ruwa, idanunta sun firfito waje duk sun juye baki 'daya.
Sai lokacin hankalin su Abie yay wajansu, sbd abinda Jaddatu take fa'di. Gudun zargi ya sanya Abie yaja hannu Rahma suka nufi wajanta.
Su malam Adamu ganin kamar MATAR gidan ce ba hijab mayafin kanta ya fa'di suka qi zuwa Abie 2 ya ce.
“Mu shiga ciki har su gama Allah ya bata lfy, Ja'afar bismillah shigo.�
Ja'afar har lokacin idanunsa kan mahaifinsa mugun mamakin abin yake.
Jin abinda Abie 2 ya fa'da, ganin sun shiga ciki harda mahaifinsa yana masa wani irin kallon da bai ta'ba masa ba, yay saurin binsu abaya hankalinsa a mugun tashe, shi bai damu da kallon tsanar da Laraba take masa ba.
Abie kallo 'daya yay ma Raiyana ya gano tabbas 'kai'kayine ya koma kan masheqiya.
Baice musu komai ba, ya sunkuya ya riqe hannunta ya fara karanto mata addu'a yana tofa mata.
Rahma duk sai ta tsorata ganin abinda Raiyana take yi, ta koma bayan Jaddatu ta la'be.
Anjima sosai kafin jikinta ya daina rawa ya sanya tattausan hannunsa ya 'dauketa ya nufi ciki da ita.
Nan wani 'daki da yake 'kasa ya sanyata saman wani lafiyayyan gado ya kwantar da ita, ya juya ya fice.
Zauna ya gansu falo sunyi tsuru².
Jaddatu ta ce“Wai daman Abdul Raiyana ciwon aljanu gareta ka kwaso mana?�
Abie kallon mamaki yama mahaifiyar tashi, kamar ba ita ta matsa ba ya aureta.
“Ummi wlh ban saniba yau nagani, insha Allah za'a mata mgani da ayar Allah ta warke. Baby taso muje.�
Rahma ta maqale kafa'da.
Hanan ta ce.
“Duk tsoron ne? Jaddatu ta kalli Abie ta ce“Kamata kuje ina mai maka tuni lokaci ya kusa, na fara gajiya da wahalar da kake Sha fa!�
Abie ya murmusa ya ha'de hannayensa�, cikin taushin murya ya furta.
“Afuwan ya mahaifiyata, ki bari don Allah...�
Katse shi tai ta ce“Kamin shiru Abdul, banson maganar banza, kai wace irin zuciya gareka ne¿�
Rahma ta kalli Jaddatu ta kalli Abie ganin yanayinsu ya canza.
Ashgwa'be ta ce“Wai Jaddati meye kike matsawa Abiena?�
Jaddatu ta harareta ta ce“Gata nake muku Rahmata.�
Abie hannun Rahma ya kama ya miqar da ita yajata suka tafi.
Hanan ta ce“Wane irin gata Ummi?�
Jaddatu ta ce“Aikin ki kenan gulma da shegen bakinki kamar tsutsa, ni wlh idan so samune kar Rahma ta koma Espagne.�
Tafe suke Rahma ta kalli Abie zatayi mgna ta fasa.
Murya shi taji yana fa'din.
“Baby ummina yi mgnarki kai tsaye.�
“A'a Abiena babu komai fa!�
Kai ya jinjina.

Ja'afar gaban mahaifinsa ya zube ya riqe 'kafafunsa ya ce.
“Don girman Allah Baaba kayi hkr ka yafemin na tuba bazan sake ba, wlh banqi bayyana muku Ibtisam na wajena ba, da wata manufa sai dan....�
Laraba ce ta katse shi ta hanyar fa'din.
“Qarya kakeyi baqin munafuki da gangan ka...�
Tanko ya rufe mata baki ya ce“Wlh kina sake mgna zan baki mamaki.�
Adamu ya ce“Ja'afar ka ban mamaki wlh banzaci hakan daga gareka ba, yanzu gashinan ka janyoma yarinya mummunan ha'dari dalilinka.�
Manyan idanunsa ya firfito yana fa'din.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!�
Ja'afar ya miqe hankalinsa atashe ya kira baba Tsalha awaya sukayi mgna ya kirasu Harisu duk sukayi mgna ya fice ya shiga mota yabar gidan.
Abie 2 ya ce.
“Adamu wannan yaron sai an masa uzuri abubuwan da suka faru, baya haiyacin sa, daga shi har Rahma kuma nasan kasan hakan, wannan ma shedace.�
Abie suka shigo da sallama, yana duddubawa baiga Ja'afar ba.
Lura da hakan ya sanya Abie2 ya ce.
“Yana zuwa.�
Zama yay, yayin da Rahma ta koma wajan Abie 2 tana son masa tambaya ta kasa ta shiga bin kowa da kallo.
Ja'afar bai rufe 30 minutes ba sai ga shi dasu baba Tsalha.
Bayan gaishe² Baba Tsalha ya shiga basu labarin Ja'afar tin randa ya 'daukosu daga tashar mota, har zamansa gidansa suna haya da zuwan Ibtisam wadda ta zauna ahannunsa wajan matarsa, da neman shawarasa da yay,akan zai maidata gida.
Ya 'dora da cewa.
“Wlh Ja'afar ba lalataccan yaro bane, sbd ana gobe zamuje Cameron wajan yayar mahaifin Ibtisam, wannan Iftila'in ya sauko musu.�
Kowa ya yarda da mgnar baba Tsalha sbd kakaf ya girme musu shekaru nesa ba kusa ba, ga kuma su Harisu awajan sun bayar da shaidar hakan.
Abie 2 ya 'dora da fa'din.
Alhmdllh! Kawai zamuce amman yaran nan sun ha'du da sharrin jinnu wanda yake na ture ne ya shigesu sun qulla alaqar soyayya wacce basa haiyacinsu, lura da hakan yasa muka shiga kai kukanmu wajan Allah akan ya warware lamarin, idan kuma wani alkhairine sanadin hakan ya tabbatar mana da shi, toh Alhmdllh Ja'afar and Rahma kunji yadda kukayi soyayya ba tare da kun sanma kunyi ba ayanzu daman akin sihirine yay tasiri.�
Ja'afar ya furta.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakil,la haula wala quwata Inna billahil alliyul azeem! Ibtisam ki yafemin ki yafemin natuba haqiqa na cutar dake acikin rashin sani.�
Gaban Tanko ya rarrafa ya riqe 'kafafunsa ya ce“Don Allah baba ka yafemin wlh sanin kankane idan ina haiyacina babu wata 'diya mace da zan kalla da sunan so bare har na juyama Ibtisam baya, don Allah Ku yafe min.�
Tanko ya rungume Ja'afar ya ce“Wallahi ban ta'ba jin haushinka ba, tinda nasan me ya faru nakuma San kana son 'yata dan haka wlh na baka ita duniya da lahira, da zaran ta warke za'ayi bikin Ku.�
Ja'afar ya shiga ma Tanko godiya.
Mal Adamu ya ce.
Ai ba nan gizo yake saqar ba Ibtisam fa yanzu da mutum 'daya take yarda Abdulmajid.�
Abie gabansa yay damm, sai ya saki murmushi ya furta.
“Ai wannan ba matsala bane yanzu dai tinda abubuwa sun warware Shamsu muna nemawa 'danmu auren Ibtisam a 'daura ko zuwa gobe ne sai muje da shi akwai dubarun da za'ayi insha Allah sai ya dinga saka mask irin fuskata yana kulawa da ita.�
Sosai kowa yay na'am da mgnar, banda Laraba da ta tsani Ja'afar.
Ja'afar ya riqe qafafun Abie yana masa godiya. Ya na fa'din.
“Wlh ban ta'ba zaton akwai masu ku'di irinka ba aduniya.�
Abie ya ce.
“Karka damu wlh na 'daukeka tamkar 'dan cikina sbd kanada hankali cikin samarin yanzu da wuya asamu irinka mai tsoron Allah da riqe amana.�
Haka taron ya tashi kowa na sakama Abie albarka temakon da zaiyi Ibtisam ta dinga kallon Ja'afar matsayin Abie.
Washegari kuwa bayan sallar juma'ah a babban masallacin wanda yake mallakin Abie, bayan waliyan ango da amarya sun bayyana da shedu bayan anyi komai akan tsarin musulumci aka 'daura auren Ja'afar da Ibtisam akan sadaki mafi daraja wanda Abie ya bayar, basu bar masallacin ba, sai da aka kuma sauke Qur'ani mai girma.
Duk wanda ya ga Ja'afar ayau yasan yana cikin farin ciki da samun abinda yafi so ya mallaka, sai dai wani gefe ganin halin da Ibtisam 'dinsa take ciki yana 'daga masa hankali..

Cikin kwana 'daya da wuni Abie ya shiga ya fita, abinka da mai ku'di, har an samu passport 'din Ja'afar har biza.

*Niger*
Inna Hansatu mai waina sai suntiri take tsakanin bayi da waje.
Bata wucce minti goma cikakke, sai ta koma aguje, sbd zawo take tin lokacin da Mahmoud ya kawo mata waya, Mal Adamu ya fa'da mata an 'daure auren Ibtisam da Ja'afar ta sanya musu albarka.
Yanzu ma aguje ta shige tana gwalo idanu waje.
Sadiya da Nuratu 'ya'yanta sun shigo kenan, suka hangota har suna ha'da baki wajan cewa.
“Inna lafiya kuwa?�
Deluwa da take zaune ta ce.
“Ina fa lafiya daga jin labari ta tayar da hankalinta sai zawo take, taqi kuma tasha magani.�
Zama sukayi suna fa'din.
“Subahanallahi!�
Maimou ta ce“Dan Allah su aunties idan ba rigimar inna ba, meye dan Ya Ja'afar ya auri Ibtisma tana halin jinya? Duk ba dalilinsa bane hakan ta sameta ai, ba wanda ya cancanci zama da ita sai Ya Ja'afar ko?�
Inna da take fitowa tai jifa da buta tana tafe a 'dan duqe ta ce.
“Inji uban waye yace 'dana ya cancanci zama da ita? Uban wa yace taje can ta iske shi? Wlh Allah yana gani ni wannan auren ina baqin cikinsa banyi farin ciki ba, yaro qarami ya qare ajinyar mahaukaciya sbd Allah. �
Nuratu ta miqe tana kwance goyen 'danta Ra'ees ta bama Deluwa ta amsa tana masa wasa.
Ta nufi wajan inna da ta ra'be 'kofar bayin tana surfa ruwan masifa.
Nuratu ta kamota tana bata hkr.
“Haba innarmu kiyi hkr ba'aja da lamarin ubangiji don Allah kiyi shiru bari fa'din mugun alkaba'i akan auren 'dan lelenki. Ke! Maimou amshi siyo mata 'dan hakkin da ka raina ta Sha yanzu zawon zai tsaya da izinin Allah.�
Zaunar da inna tai saman tabarma tana lallashinta, ba wanda yay qoqarin saka baki masifar ta dawo kansa.
Bayan Maimou ta kawo maganin inna ta sha dakyar Nuratu ta bada ku'di aka siyo mata indomie da kwai ta shiga ci tana santi.
Sai da ta nutsu Nuratu ta ce“Innata dan Allah karki sake cewa komai akan auren nan, kinji?�
“Inna ta ce“Wai daman shine abinda ya kawoku?�
Sadiya ta ce“A'a Inna ba shi bane kiyi hkr dan Allah.�
Nuratu ta kira Ja'afar cikin sa'a ta same shi, ganin ita ce ya katse kiran ya kirata.
Da sallama ta fara.
Ja'afar ya ce“Inada niyar kiranki anjima yau da dare muke tafiya. Kinga innata bata 'daukan kirana fa!�
Nuratu tai murmushi ta ce“Ya Ja'afar barka Allah ya sanya alkhairi yaba Ibtisam lafiya, ya kaiku lafiya, ga innar ta huce yanzu zata sanya albarka insha Allahu.�
Ta mannawa inna wayar akunnenta.
Ja'afar cikin kwantar da murya ya ce.
“Assalam ya mahaifiyata ki daina fushi da 'dan lelenki.�
Inna ta buntsiro baki kamar yana ganinta ta ce.
“Kaci sa'a ina sonka na hkr amman wlh idan wannan sakarar uwar tata ta nuna 'kiyayyarta gareka zan 'dauki mummunan mataki, Allah ya albarkaci aurenku ya kaiku lafiya ubangiji yasa adace kayi hankali fa! kar ta jiyata min kai.�
Ja'afar ya ji da'din addu'ar sosai yay murmushinsa wanda daman bai fiye wa kowa shi ba, daga innarsa sai Nuratu ko Ibtisam itama bai fice sau uku ba tin ha'duwarsu.
Ya shafi yalwatacciyar sumar kansa ta asalin baqaqen buzaye ya ce.
“Ngd innata, agaishe min da kowa da kowa, ban Nuratu.�
Wayar ta ba Nuratu sun 'dan ta'ba hira Sadiya ta amsa tai masa barka Deluwa ma suka gaisa Nuratu salin halin yayan nata tai masa sallama tare ta fatan alkahiri, ya katse kiran.
Inna aka washe baki akace“Allah mai iko wai yau Ja'afaru na zai hau jirgin sama kai jama'ah.�

Dadda na zaune tana tsafema Aydah kanta Taslim tana musu girkin rana, Fu'da da Nadra sunata wasansu.
Wayar Dadda ta 'dauki ringing.
“Toh mutan Tchad ne ko Cameron?�
Ramadan ya ce“Allah yasa Babane.�
Dadda ta 'daga kiran tana rabka sallama.
Tanko ya amsa daga can yana gaisheta.
Dadda ta ce“Shamsu jiya shiru bamu jika ba yara duk sun damu, ya me jikin?�
Tanko ya amsa“Da sauqi ya yaran? Yauwa dadda dan Allah kiyi min kyakkyawar fahimta na kira Karime munyi mgna yanzu...�
Tsaf ya zayyanewa mahaifiyarsa komai game da auren Ibtisam da Ja'afar da aka 'daura jiya juma'ah, ya 'dora da cewa.
“Jiyan wlh duk hankalina ba kwance ba shiyasa ban kiraki ba kiyi hkr dan Allah.�
Dadda ta ce“Masha Allah wlh naji da'di hakan sosai shima yaron ya yi halacci na kuma gamsu da 'kaunar da yake mata, shi kuma wannan balarabe Allah ya saka masa da gidan aljannatul Firdausi, Inda Ana samun irinsu dayawa aduniya wlh talakawa da basu shiga wani hali ba.
Allah ya basa dukkan abinda yake nema gidan duniya da lahira, gaskiya yanada kirki irin wannan temako haka? Duk da shine yay sanadin shigarta mawuyacin hali amman ya yi jihadi sosai.�
Nan ta ba yaran 'daya bayan 'daya wayar suka gaisa da mahaifinsu suna masa fatan sauka lafiya.

*Gabon*
Aishatu tin abinda ya faru ranar da taji abinda aka fa'da cikin wayar sai ta zamana bata aiki sai saka channel 'din da ake wa'azi mafi yawa ma wa'azi akan 'yan kidnappings da 'yan safaran mata.
Ma'aruf abin yakan basa mamaki, sai ya Sha jinin jikinsa ko matarsa ta gano abinda yake ne sai yaji hankalinsa ya tashi.
Zaune suke afalo yanzu ma wa'azin ne ake nunawa tashar sunnah Tv.
Ma'aruf hankalinsa wajan aikin da yake cikin wayarsa sbd ya hana kowa kiransa awaya yanzu sai idan shi zai Kira.
Aishatu ta ce.
“Wlh ba abinda na tsana aduniya irin yaudara ko zamba cikin aminci idan na Kama mutum da irin laifin nan toh wlh duk son da nake masa zan ajiye shege na dates duk wata alaqar da take tsakaninmu ta har Abadan, me ake da mutane masu fuska biyu, ai zama dasu ma haramun ne wlh.�
Ma'aruf ya kamota zai rungume yana fa'din.
“My life duk me ya kawo mgnar nan ne?�
ta fizge jikinta tana matsawa gefe.
(dan tun ranan bata kuma yarda wani abu ya shiga tsakaninsu ba, ciwon 'karya ta tsira, shi kuma ya yarda sai riritata yake sbd yana masifar son cikinsa da ita kansa.)
Wayancewa tai tana yamutsa fuska.
“Wlh masoyina wata qawatace da take 'kasar Egypt saurayinta har an sanya musu ranan aure ashe ya ha'inci iyayansa da ita dama duk wani masoyinsa, Ashe ba aikin da Allah ya zabar masa ba yake yi ya za'bi musgunawa iyayan wasu 'ya'yan wasu kakannin wasu ta hanyar safaran yaran mutane ana kaisu wata 'kasa dan lalata dasu, da kidnapping Ana basu ma'kuddan ku'da'de.
'Karshe ya rasa ransa ta hanyar kamasa da aka je ya gudu aka harbeshi.�
Ta 'karashe mgnar cikin kuka mai tsuma zuciya.
Ma'aruf zufa ce ta karyo masa mugun tsoro ya shigesa ya kalli Aishatu da cikinta wanda ya shiga wata na shidda ya fito ba laifi.
Aransa yace“Kar fa aje nima na mutu cikin irin 'kazamar harakan nan?�
Rungumota yay ya ce“Bari kukan dan Allah kiyi hkr bari zan fita yanzu zan dawo kinji?�
Kai ta 'daga masa, ya mata kiss a lips 'dinta ya kwashi wayoyinsa ya fice daga gidan hankalinsa atashe zufama take karyo masa ta ko ina dan yaji tsoron labarin, shi fa bai son mutuwa ayanzu.
Hnnayenta ta 'daga tana kuka tana roqon Allah yasa Ma'aruf ya shiryu ya daina wannan mummunar harakan, tin duniya bata gama shaida sa ba, tana son mijinta 'dan uwanta uban abinda zata haifa.

*Tchad*
Abie sosai ya tsaya akan ciwon Raiyana, anata mata addu'a harda saukar Qur'ani, wanda Auntie Saro

Please Login or Register in order to submit comment