Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga Rayyana tana 'ko'karin fitowa, sukaci karo.
“Wayyo sorry ban ganka ba! Shiga kayi wanka sai muje kaci abainci.�
Kai ya jinjina ya ce“Ngd ki kawo min nan nayi ko spoon 3 nayi, ki ha'domin coffee mai da'di please.�
Cikin murna ta ce“Ok an gama afito lafiya.�
Ta sumbaci hannunsa ta fice, shi kuma ya shiga bedroom.
Kayan jikinsa ya rage ya shiga bathroom.

Rahma sai kallon Rayyana take tana kai komo wajan ha'dawa Abie abinda zaici, ta jima tana dafa coffee kafin ta juye cikin cup glass me kyau, taje man dining area ta ha'do komai a tray ta haye sama.
Abie ya jima yana wanka kafin ya fito da towel 'daure a 'kugunsa, qaramin towel yana goge jikinsa.
a falonsa ta ajiye tray'n saman center table, ta zauna jiransa salin halinsa batayi gangancin shiga bedroom ba.


Acan Niger kuwa 'karfe 9 na dare jorginsu ya sauka, taxi suka shiga Mal Adamu da Ja'afar taxi 'dinsu daban kasancewar su ba 'daya ba.
Fa'din farin farin ciki wajan Inna Hansatu ba'a magana ganin yadda Ja'afar ya qara zama qato ga wani irin haske da baqar fatar sa ta yi.
Can ma Dadda kamar ta goya Ibtisam ganin yadda ta ciko ta sake fari.
Ammaan sai taga Ibtisam 'din Sam batada walwala.
Bayan sunci sun sha Dadda ta qarama Laraba da Tanko ban gajiya ta ce.
“Ta miqe ta ce“Ibtisam zo muje can gidana mu kwana sai musha hira.�
Aikuwa kamar jira take ta miqe cike da zumu'di ta ce“Daman akwai labaein da zan baki Dadda...�
Tanko ya ce“Mama ki 'kyaleta ba Inda zata.�
Dadda ta ce “Toh shikenan mai 'diya.�
Tanko ya ce“A'a ba haka bane zan miki bayani gobe insha Allah.�
Dadda ta musu sallama ta tafi Ibtisam ta fashe da kuka ta nufi 'daki tana fa'din.
“Ni daman ba'a 'kaunata.�
Laraba ta ce“Oh Allah ni Laraba naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba! Tanko yarinyar nan anya tana hankalinta kuwa? Wlh inaga kamar bata dawo hankalinta ba?�
Tsuki yaja ya ce“Dallah rufemin baki tin ban wulaqantaki cikin 'diyanki ba! Wa yaja duk abinda yake faruwa?�
Muqus Laraba tai bata sake mgna ba.

Ja'afar tsabar gajiya yana gama con abinci yay wanka ya rama sallah ya kwanta, yanajin Mahmoud na basa labari yay banza da shi dan buqatar hutu yake.

A can Tchad kuwa Rahma ganin Rayyana ta koma sama 'dauke da tray wani irin abu ya tirniqe Rahma ta kasa control kanta ta miqe tama Jaddatu da Hanan sallama, daman Meerah ta jima da tafiya.
Dab da zata iso 'kofar falon Abie ta ji mgnar Rayyana tana fa'din.
Please My Habiby ka 'dan qara spoon 'daya kaji,daure don Allah haaaa na saka maka.�
Wani dammm! Rahma taji 'kirjinta ya buga da sauri, ta rumtse idanunta wani irin zafi takeji wanda yake tasowa daga 'kasan zuciyarta.
Shirun da taji hakan ya tabbatar mata Abie ya bu'de sweet 'din bakinsa Ammi na basa abinci aciki 'kilama ta dinga lashe masa wanda ya 'bata masa baki.
Da Sauri ta bu'de idanunta ta dafe bango ta fara tafiya taji sautin muryar Rayyana tana tafa hannu ta ce “Bravo! habibina muahhhhhhh! Toh amshi coffee ka Sha.�
Zamewa Rahma tai 'kasa dab'as ta wanda sai da bayanta ya bugu da qofar falon wacce take rufe ta bada sautin alamun an bugu da ita, ta saki 'dan qara tana dafe 'kugunta tare da cewa“Ushhhhhhhh! Bayana.�
tana toshe bakinta kar ajita...........

_Rahmerh ladingo😉_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/29/22, 16:56 - Buhainat: ```D A```

```77&78```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

Washegari Abie ya na fitowa daga masallaci, ya biya dan tashin Rayyana ya isko tana sallah, ya ji da'di sosai ya zauna ta idar suka gaisa ya ce“Yauwa zanje Cameron amman ayau zamu jiyo komin dare, 'karfe 8 flight 'dinmu zai tashi.�
Ya 'karashe mganr yana miqewa.
Rayyana ta ce“Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, zanyi missing 'dinka. Please zanje gida idan ka amince da rana don Allah habiby?�
Abie ya 'dan kalleta ya ce.
“Ameen amin Shkuran, Ok kije ba damuwa, agishe da su Saratu.�
Godiya tai masa harda rakoso bakin 'kofa riqe da hannunsa.

Zaune ya isko Rahma sanye da jallabiyarsa fara 'kal sabuwa ta mata kyau ta yane kanta da hiraminsa tana karatun Qur'ani.
Sosai hakan ya masa da'di ya shiga ya watso ruwa, ya fito 'daure da towel a'kugunsa, yana goge murdadd'an jikinsa mai cike da gargasa, Masha Allah Abie yanada kyan fata Sam bazaka ta'ba cewa ya yi shekaru 40 ba bare 50 cif.
Rahma tana gama karatun ta 'daga hannu tana addu'a tana zubar da hawaye.
Bayanta ya sunkaya ya'dauka Qur'ani ya kaita ma'ajiyarta ya dawo ya zauna bayanta ya sanya hannayensa ya zuro ya ha'de da nata yana amsawa da “Ameen Ya Allah Babyna.�
Rahma yadda Abie ya kanainayeta ya rungumeta, danshin ruwan jikinsa na shigarta yana goga mata sajan fuskar shi, agefen fuskarta yasa bakinta ya bara farawa, tsikar jikinta sai yamm take, dakyar ta 'karasa addu'ar tana hawaye suka shafa.
Ya juyo da ita gabansa ya na wasa da hawayen fuskarta.
Rahma idanunta ta runtse sbd kallon Abie fa'duwar gaba yake sakata Sam bata Saba ganin ba Riga ba, duk da tasan yanada babban 'kirji batasan cike yakeda gashi haka ba.
Can 'kasan maqoshi ya furta“Ya Salam! My Baby yanzu ni kam me na miki? Daga masallaci nake fa! Please Ruhina ki daina min asaran hawayenki na tuba, Oya fa'damin me nayi yanzu zo na shanye hawayen sai naji dalili. Oya sanya hannunki ki zagaye bayana rungumeni gam kinji My Baby.“
Ya 'karashe mgnar yana tallabo fuskarta da dukkan hannunsa biyu, ya mata qurr da shanyayyun idanunsa, baisan wani irin so yake mata ba, jinta yake tabbas idan babu ita bazai ta'ba rayuwaba.
Rahma sanya hannunta duka biyu ta yi ta zagaye bayansa, ta rungumesa gam, tana fa'din“Abie nah me yasa nakeson koda yaushe na kasance da kai kuma ajikin ki? Bayan nasan hakan bai dace ba amman na kasa Hana kaina, Abie wane irin so nake maka don Allah?�
Ta idar da mgnar cikin shasheqar kukan zallar shagwa'ba.
Abie ya ra'da mata akunnenta.
“My baby kul kiyi kuka maza had'e hawayenki, banson kukanki farin cikin ki na har abadan yakusa, insha Allah. Irin son da nake miki kike min My Baby.�
Ahankali ya shiga lashe mata hawayen ya tura hannunsa cikin dogon gashinta yana caku'dawa, sai ajiyar zuciya take saukewa.
Ahankali ya ra'da mata.
“My Baby kina son kiyi breakfast da sweet lips 'dinki?�
Kallonsa tai ta zaro hannunta 'daya tana shafa fuskar shi tana Jan dogon hancinsa, ta sauke yatsunta biyu saman lips 'dinsa ta shafa ta zura masa yatsarta manuniya cikin bakinsa ahankali cikin yanayi na shaukin so da yake kwasarta ta ce.
“Abie Rabin raina! Cijeshi please. �
Yanayin yadda tai mgnar da yadda take juya yatsarta bakinsa tana nemon yawunsa ta yi wasa ya saka shi jin wani irin yanayi mai girman gaske.
'Dan ciza yatsarta yay ta kalleshi tana lumshe idanunta tai 'yar dariya ta ce“Abeinah qara cizawa wlh kamar Susa naji sam ba zafi.�
'Kara jizawa yay ahankali.
Ta sake tura masa yatsu biyu suka zama uku ta manna bakinta saman kunnensa ta ce“Abienah so nake ka ciza da 'karfi pls Rabin raina kamin abinda nake mana.�
“No! Baby wlh bazan iya ba.�
Kukan shagwa'ba ta sakar masa acikin kunnensa tana sake qamqamesa.
“Wayyo ni Abdul Majid dole dai mu tarkata kayanmu tafi honeymoon baby rigima zatayi sosai tabbas.�
Rahma kuwa tsabar rigima da yake cinta sam bata ji me Abie yake fa'da ba.
Miqewa yay da ita jikinsa, yana 'dan cicciza yatson hannun nata yana tsotsarsu kamar sweet shiru tai tana sauke ajiyar zuciya.
Kwantar da ita yay saman bed, ya shigar da ita jikinsa yana famar tsotsar yatsun nata, tana 'yar dariya tana shafa fuskar shi.
Fuskata ya tallafo ya ce“Oya kiss me my baby.�
Rahma ta ha'de face 'dinsu cikin shaukin begensa ta ce“Abie idan ka sabamin ya zanyi bayan ka aurar dani? �Gira ya 'daga mata ya birkitata ya sakar mata nauyi yana mata cakulkuli, ha'di da sumbatar wuyanta.
Dariya take 'kyal'kyalawa tana maqalqaleshi tana fa'din “Abie nah ka bari wayyo Abie nah cikina zai 'kulle.�
Sai da ya ji ta gaji li'kis tana son sakin kuka ya barta yana dariya, da Jan dogon hancinta.
Mirginawa tai ta haye saman 'kirjinsa ta yi 'dare² tana qamqameshi tana sauke numfashi ashagwa'be ta ce.
“Abienah 'kishi ma nakeji bari naje nasha ruwa na dawo.�
Abie ya maqaleta yana mata ra'da akunnenta.
“No! Baby bari na kawomiki akwai a falo Bby zanje Cameron yau zan dawo komin dare kalli agogo bakwai ta gota 8 flight 'dinmu zai 'daga kiyi breakfast da wuri pls kinji babyna.�
Ya 'karashe mgnar yana sumbatar kunneta ha'di da hura mata iskar bakinsa yana wasa da dogon gashinta da ya baza shi, sosai yake son gashinta koda yaushe 'kamshi na musaman yake ga samtsi da tsayi.
Rahma ta maqaleshi cikin sanyin murya ta ce“Abienah an bika.�
Tai mgnar yara, dariya Abie yake ya ce“ Please babyna ai bazan kwana ba, wai an bika oh baby ummina.�
'Kin barin jikinsa tai dole tana jikinsa yaje falon ya bata ruwan ta Sha suka dawo ya kwantar da ita yana lallashinta har ta barsa ya shirya tsaf cikin wata dakekiyar shaddah Coffee brown, wacce ta fito da asalin kyawunsa da cikar zatinsa da haibarsa, Uwa uba kwarjininsa.
Yana fesa turare Rahma ta rungumeshi ta baya tana shaqar 'kamshinsa.
Ashagwa'be ta ce“Abienah ka ha'du wlh.�
Juyo da ita yay ya rungumeta gam ya sumbaci tsakiyar kanta, ya ce“I love you My Baby, ki kularminda kanki har na dawo, pls kici abinci ayau sosai OK? �
Kai ta 'daga tana son sakin kuka.
“No! Baby pls oya smile.�
Murmushi tai ta ce“Abienah duqo ka'dan kaji.
“Tsawonsa ya rage sukayi daidai yana ri'ko 'kugunta gam.
La'bbansa ta kamo tana tsotsa ahankali tana shafa sumar kansa.
Abie ya lumshe idanunsa yana murza 'kugunta aransa yana fa'din.
“Wayyo Allah na!! Baby karki kawomin aiki.�
Jin ta kamo harshensa kafin ta fara ya kamo nata yana tsotsa ya fara susutata da special kisses 'dinsa tayi lak'was tana sauke numfashi.
Ahaka ya samu ya mata dubara ta koma bacci ya lullu'beta yana dariya ya 'dauko sabuwar da ya siya mata irin wacce iPhone 13 pro Max number 'yan Morocco da lambobinsa sai na Jaddatu da Hanan da Abie 2 ka'dai aciki, ya ajiye mata saman bedside drawer ya sumbaci goshinta, ya ajiye mata key kusan wayar ya bu'de drawer ya zaro ku'di masu yawa ya fito ya janyo 'kofar bedroom 'din.
Yana fitowa falon Rayyana tana shigowa 'dauke da tray.
Fuska asake ta ce“Har ka shirya? Pls kasha koda tea ne karka tafi haka.�
Ta 'karshe mgnar tana dire tray'n saman center table.
Abie wanda ya kara waya a kunnensa ya zauna kusanta, yana gyaran murya, ya mata nuni da ta ha'da masa tea 'din.
“Wa'alaika salam Abraham a fito da mota zuwa airport na shirya a hanzarta na makara wani uzuri ya riqeni.�
Abraham da ga can ya ce“Yalla'bai ai motoci sunfi awa Ana jiranka muna tunanin lafiya ma, sauran minti 20 jirgi ya tashi a hanzarta yalla'bai.�
Abie ya dafe kansa aransa yana fa'din.“Laifin Babyna ne toh ya zanyi da rigamammiyata.
Azahiri ya ce
“Ok�
'Kitt ya datse kiran.
Number Abbas ya kira yana 'dagawa ya ce“Ku shirya ganinan.�
'Kitt ya 'dates kiran.
Rayyana ta beqa masa tea wanda yaji kayan 'kamshi yasha madara da Milo.
“Ngd�
Ya furta ya amsa ya yi kur'ba sau uku ya ce“Zan tafi na makara lokaci ya shige amshi kima su Saratu tsaraba Yahaya direba ya kaiki bance kiyi tuqi ba.�
Amsar ku'din tayi me uban yawa tana kwararo godiya ta ce“Abien Ummi ku'din sunyi yawa.�
“No! Ba yawa na tafi muje zan rufe 'kofar.�
“Habiby ka bari na gyarama bedroom da nan falon.�
“A'a Rayyana ki barsa pls ki matsawa baby taci wani abun idan ta fito.�
Rayyana ta 'dauki tray'n ta ce“Ok habiby an gama Allah ya dawo dakai lafiya.�
Da
“Ameen.�
Ya amsa suka fito ya murzawa 'kofar key ya zare ya jefa aljihunsa suka sauko 'kasa da Rayyana suna magna.
Parlour'n ba kowa agurguje ya biya wajan Jaddatu ya gaisheta ya mata sallama ya fito ya tafi.
Abie tsabar makara yau bai tsaya amsar gaisuwar ma'aikatan gidan ba hannu kawai yake 'daga musu ya shige motar suka nufi airport.
Minti uku da zuwan Abien jirginsun ya 'daga zuwa Cameron.

*Niger*
Misalin 'karfe 10 na safe, Ja'afar tsaye cikin shigar 'kananun kaya, yana fesa turare mai sanyin da'din 'kamshi, wayarsa ta 'dauki ringing.
Ganin Harisu ya saka ajiye kwalbar turaren ya 'dauki wayar yay picking call 'din tare da sallama.
Daga can Harisu ya ce“Abokina fatan kun sauka lafiya? Ga Baba Tsalha nason magana dakai.�
Ja'afar ya amsa sallamar yana fa'din.
“Alhmdllh! Oh! Mon dieu! Pardon Harisu, wallahi tin safe bacci nake, tinda na dawo daga masallaci, yanzu ma Inna ce ta tayar dani, fatan kuna lafiya! Ina Yahuza har yanzu baku fita ba? Bani Baban.�
Harisu ya ce“Lafiya lau eh yanzu zamu fita, ga Baban. �
Ja'afar ya gaishesa cikin girmamawa baba Tsalha ya ce“Daman dan muji kun isa lafiya ya gajiya?�
Ja'afar ya ce“Baba ina tune daku da anjima zan saka Kati na kiraku, Alhmdllh! Baba.�
Sun 'dan ta'ba hira sukayi sallama, Ja'afar ya jefa wayarsa cikin aljihun wandonsa,ya fito ya nufi cikin gidan nasu.
Innah mai waina ana zaune bakin nan awashe kamar gonar auduga, Mal Adamu ya baje musu tsaraba, ma'kota sai shigowa barka dazuwa ake.
Mal Adamu ya Innah Hansatu turaman atamfa biyu masu kyau da takalmi da mayafi biyu, sai turaren wuta na jiki da na 'daki.
“Oh! Allah haihuwa me albarka Ja'afaruna ya janyo mana alheruruka Masha Allah Malam mun gode Allah ya qara rufa asiri.�
Mal Adamu ya amsa da “Ameen Hafsatou.�
Ya beqama Deluwa nata kamar yadda yaba Innah Hansatu haka ya bata.
Godiya take tana fa'din.
“Ubangiji ya qara arzi'ki da hanya ta alkahiri.�
“Ameen ya Allah. Maimunatu ga naki abayace da lufaya keda 'yan uwanki duk 'iri 'daya ne sai ki ajiyemusu duk wacce tazo ki basu.�
Ja'afar ne ya shigo da sallama.
Maimou ta miqe tana murna ta rungumeshi tana dariya, ta ce“Ya Ja'afar ashe haka ka zama Allah jiya kallon duhu namaka, sannu da zuwa Ya Ja'afar kalli kayanmu da Baaba ya kawoma.�
Janyeta yay yana hararata ya ce“Ke banson iskanci ji yadda kika cikuikuiye min rigata.�
Inna Hansatu ta ce“Ai wlh baqin buzuna ni wannan 'dabir ta runguma ma bana sonta sai kace wasu larabawa.�
Murmushi Ja'afar yay ya ce“Inna idan basu rungumi yayansu wa zasu runguma? Baaba ina kwananku?�
Mal Adamu ya amsa shi da Deluwa fuska asake Deluwa na tambayarsa “Ya gajiya Ja'afaru?�
Zama yay kusan Innarsa ya ce“Tabi jiki Umma.�
'Yan 'kanninsa suka gaishesa ya amsa yana tambayarau karatu.
Innah ta 'dauko masa shayin da ta ha'da masa yaji madara an sayo masa biredi ta soya masa wainar 'kwai.
Ja'afar ya fara ci yana danna waya.
Mal Adamu ya ce“Hafsatu da Ja'afar har kwai aka soya masa mu aka soya mana awara da kunu.�
Dariya tai ta ce“Haba! Ina laifi.�
Murmushi yay ya ce“Ja'afar idan ka kammala sai leqa ka gaka ya MATAR taka ya ta kwana ko?�
Fuska ya ha'de shi fa ya fita sabgar yarinyar bai ta'ba zaton Ibtisam zata iya sauya halinta ba, amman ba mamaki tinda tin farko ita ta nuna masa so yay saurin tarar numfashinta amman sai ga shi tana son raina masa hankali zai koya mata hankali.
“Tom Baaba insha Allah.�
Ya amsane amman ba wai zaije bane.
Innah Hansatu ta ce“Ka gaisheta da jiki idan kaje.�
Deluwa ta ce“A'a baza'ayi haka ba zamuje ni dake mu dubota dan Allah Hafsatu.�
Mal Adamu ya ce“Kwarai kuwa zakuje.�
Ja'afar yana gama breakfast 'dinsa ya miqe ya fice zai zaga gari, ya dawo ya ce yaje.

Ibtisam tinda ta tashi yau batajin da'din jikinta, wani abu takeji ya danne mata 'kirjinta, daurewa kawai take, haushin kowa takeji yau agidan, tin safe ta fito tai breakfast ta'ki.
Tanko ne ya shigo da sallama hannunsa 'dauke da baqar leda 'danyan kifini ya siyo da kayan miya.
Laraba suna zaune saman tabarma sunata kallon kayan da Tanko ya fito musu tsaraba yaran harda nata Tasha mamaki dan bata San dasu ba,bakinta yaqi rufuwa.
Taslim ta ce“Baba sannu da zuwa gaskiya Baba kayanmu sunyi kyau Masha Allah, mun gode kowane na gwada sunmin gaskiya wannan 'kasar akwai kaya masu kyau.�
Tanko ya zauna yana fa'din.
“Madallah Taslim Allah miki albarka.
Laraba ga kifi amana farfesun kifi sai adafa shinkafa 'yar Cotonou. Ina Ibtisam?�
Laraba ta ce“Tana 'daki taqi cin komai wlh ba yadda banba.�
Miqewa yay ya nufi 'dakin.
Kwance take ta du'kun'kune waje 'daya ta 'daga kanta sama tana kalon silin 'daki.
Tanko ya shigo yana kiranta.
“Ibtisam!�
Za'bura tai ta miqe zaune tana rarraba idanu.
“Wai Ibtisam kasheni kikeso kiyi? Me ya sauyaki haka lokaci 'daya? Wallahi kibi duniya asannu ina jiye miki nadamar da batada anfani wlh kin ban mamaki kin jahilta kanki kina Neman hallakar da kanki kina son wani da auren wani akanki? Kin kyautama kanki ke yanzu dan Allah idan ba daliliba me ha'dinki da babban mutum kamar Abdulmajid mutumin da Jar fatarma masu ku'din maza da mata ba da kowa yake alaqaba, idan ba dalilin dalili ba ina za ki gansa? Mutumin da jansin Ku ba d'aya ba kike neman jefa kanji halaka, wlh ki dawo hayyacinki tin kafin na 'daukar miki hukuncin da zai miki tsauri, tashi kije kici abinci, wallahi ina kan bakana matuqar kikayi abinda yaron nan ya sakeki Allah bani bake sakara marar tunani.�
Kuka take tana basa hkr ya ce“idan kina son na hkr ki saki ranki kamar da kar na sake ganinki ahaka.�
“Insha Allah Baba zanyi ka tayani da addu'a.�
Hannunta ya Kama suka fito da kansa ya zuba mata abincin ta fara ci ba dan tanajin 'dan'danonsa ba, dan ta farantawa mahaifinta ne, ga 'kirjinta na ciwo.
Tana idarwa ta daure ta saki jikinta suna sake duba kayan.

Acan Tchad kuwa sai shabiyu Rahma ta farka daga bacci, ta shiga tai wanka ta fito da towel ta goge jikinta ta shafa lotion 'din Abie ta zura jallabiyarsa sai lokaci idanunta suka sauka akan sabuwar wayar waccan baqa ce wannan kuwa pink kala ce.
Tsalle Rahmaa tai ta ce“Wow! My Abie sabuwar waya ka siyamin? I love you Rabin raina I kiss you My Abie.�
Ta 'karashe mgnar tana sanya santalelan farin hannunta ta 'dauki wayar akunne take an cikata da charge, ta shiga contacts taga lambobin family 'dinsu ne kawai, kuma sabon layine.
'Yar dariya tai ta yi far da 'kananun idanunta masu matuqar kyau da haske.
Number Abby Morocco tai dialing.
Bata jima ba tana ringing aka 'daga tare da sallama.
Rahma ta nufi falo tana amsa sallamar ta ce“Tsoho mai ran 'karfe matarka ce nayi sabon layine sabuwar waya kasan kuma aikin waye.�
Daga can kyakkyawan dattijon mai nutsuwa da kamala ya ce“Aff ya wuce Sojanki, ga Zainabu tana nemanki wai yaushe za ki zo?�
Rahma ta karkatar da kanta gefe ta ce“
Abbyn Ummana kace Zainnunu me ta ajiyemin wlh zan shigo wannan satin idan Rabin raina Abie ya yarda. Yaushe Auntie Saleeha zata dawo da Yemen ne?�
Dariya ya yi ya ce“Zai ma yarda amman muma ai munkusa zuwa, Auntin ki sai azumi fa ta ce anan zatayi azumi nna da wata hu'du kenan.�
Rahma ta ce“Pls Ku jira nazo sai mudawo tare ina Ummiterh ne dasu Irfan iyayan surutu?�
Abby ya ce“Basa nan sun fita, ga Zainabu.�
Rahma ta amsa tana tsokanarta sun jima suna hira ta tsinke kiran ta kira numbers Abienta duk basayi kamar ta yi kuka ta nufi 'kofar falon ta bu'de taji gam da key.
Sai lokacin ta tuna ta ga key kusan wayan, ta koma ta 'dauko ta ajiye saman center table ta koma bedroom 'din ta wanke toilet tas ta fesa turaren toilet ta gyara masa bedroom tsaf daman ba alamar datti, ta gyara shimfi'dar gadon ta goge TV plasma, ta kunna turaren wuta ta fesa na 'daki, ta koma toilet ta zuba kayan acikin (machine à laver) ta wanke masa kayansa na jiya wanda su ka d'aine masu datti sai na barcinsa ta shanyasu a abin shanyar toilet, ta fito ta rufe bedroom ta fito ta gyara falon tsaf nan ta kunna turare ta goge TV'n falon da fridge, tsaf komai a muhalinsa sai 'kamshi kawai ke tashi ta bu'de 'kofar ta fito ta murza key ta zare ta haye sama.
Agurguje ta shirya cikin Riga da wando jeans da wata crazy 'din riga yellow ta mata kyau kamar yadda jeans 'din ya zauna Masha Allah sai 'kamshi take ta sanya slippers a qafarta ta fito.
'Dakin Meerah ta buga taji shiru ta gane tana 'kasa.

Jaddatu ta hango zaune tana waya sai washe baki take.
Kallo 'daya tama Rayyana ta kauda kanta, tsaf shirinta tana cikin blue shadda tayi kyau komai blue ne ajikinta har jaka.
Hanan ta ce“A'a kaga Autar Abienta yau fa kwalliya ta yi kyau.�
Iman ta tarbeta da gudu Rahma ta 'dagata tana murmushi ta ce“Abbyn ummina na gaisheki keda Jaddatu da ammi Hanan.�
Ta 'karaso falon ta, zauna tana ajiye Iman ta ce“Ammi Rayyana barka da safiya .
Ammi Hanan ina kwana?�
Ta 'karashe mgnar tana kwantowa jikin Jaddatu ta sumbaci kumatunta ta ce“Masoyiya Jaddatu fatan kina tashi lafiya? Da wa kike waya?�
Rayyana cikin sakin fuska ta amsa gaisuwar ta ce“Baby zaki rakani gida mu yini?�
Kai ta langwa'bar ta ce“Kashhh! Ammi da Abienah na nan ne sai muje kinga kuwa ban ta'ba zuwaba wataran zanje.�
Murmushi Rayyana tai ta ce“Ai kuwa zamuje wataran ummi qarama.�
Rahma ta miqe tana amsa gaisuwar Meerah ta ce“Meerah pls a 'dan gyaramin 'daki wlh na gaji na Abie na gyara. Latifa! Pls zo kuje ki Kama mata.�
Ta 'karashe mgnar ta nufi corridor 'din da zai sadata da dining area.
Rayyana baki da hanci ta saki tana kallon Rahma har ta 'bace mata, lamarin yarinyar na bata tsoro matuqa, sai ta dinga mata gani² kamar ba matar uabanta ba, tamkar kishiya haka take ganin abinda Rahma take mata.
Meerah da Latifa suka haye sama dan cika aikin uwar gidan tasu.
Jaddatu na gama waya Rayyana ta ce“Ummi zanje gida amman bazan kai dareba.�
Jaddatu ta ce“Ikon Allah ashe dai har yanzu da saura toh agaida mutanen gidan.�
Rayyana jiki asanyaye ta amsa sukayi sallama da Hanan ta fita.
Hanan ta ce“Iman jeki wajan Auntinki ta baki chocolate.�
Cikin murna ta tafi.
Hanan ta ce“Kai Ummi don Allah ki daina mata hakan shi wanda ya ajiyeta idan yana bu'katar zama da ita fa!? haba!�
Sandar hannunta ta d'aga zata kwa'da mata ta matsa nesa tana dariya.
“Ke! Jiddah bana son magnar banza wato kece munafukarta ko? Wlh zan sa'ba miki korar kare zan miki ki tattara ki koma Morocco kafin mijinki ya dawo munafuka na tsani matarnan wallahi idan ma zama zaiyi da ita ya rabamu ai yanada gidaje bana son ganinta Sam.�
Hanan tai muqus taja bakinta ta tsuke sanin halin uwar tata.
Rahma tana gama breakfast ta dawo falon ta zube jikin Jaddatu tana nuna mata wayar da Abie ya siyamata sabuwa.
Jaddatu ta ce“Yauwa 'dan albarka ya kyauta, kuma ta yi kyau sosai.�
Rahma na murmushi ta shiga camera suka fara salfie.
Sama ta koma ta nemo number Anee a cikin kundinta na ajiye numbobi, ta sanya ta Kira tana zubewa saman sofa a falonta, yayin da su Meerah Duke aikin goge-goge har sun gama.na bedroom.
Cikin sa'a kiran ya shiga.
Anee lokacin suna tare da Rafeek a compound 'din gidan Auntie ta, ya zo mata magiyar ta ha'dasa da Rahma har wata 'yar rama ya yi,duk ya susuce rashin samun layin Rahma.
Anee ganin number kamar ta Chad ta 'daga tana “Hello! Waye?�
Rahma ta 'kyal'kyale da dariya ta ce“Habibiyarki ce dallah can yau Rabin raina Abie ya siyamin sabuwar waya, ya amshe waccan har layin, kinsan My Abie akwai rigima, ni *Baby Abie rigimata* ma zan dinga cemasa wollah.�
Ta 'karashe mgnar tana 'kyal'kyala dariya.
Anee ta ce“Innalillahi! Wallahi Rahma bakida mutunci Allah ganinan inata nemanki kamar nayi hauka bana samunki kuma banda number Abienki bare na kirasa hope kina lafiya? Wai yaushe kika zama 'yar iska baban namu zakina cema Baby rigima? Yau kam Habibyta a farin ciki kike, meye sirrin Rahmatah?�
Anee ta tambayeta itama tana sakin dariyar farin cikin samun 'kawar tata.
Rafeek jin Anee ta ambaci Rahma ya warce wayar cikin zafin nama ya kai kunnensa cike da 'dauki da farin cikin samunta.......!
_😩Duk yadda naso naje Inda nakeson zuwa banzo ba yau, dole na hkr, wai nagaji wlh Tabb rubutu masifa ne.🤣_

_Rahmerh ladingo😉_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/29/22, 16:56 - Buhainat: ```D A```

```79&80```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_


Cikin 'daukin samunta da son jin muryata, Rafeek ya bud'e baki zaiyi mgna,yaji zazzaqar murya Rahma tana siririyar dariya.
Dan bata san meke faruwa ba, ta sake sakin siriryar dariya, ta ce“Wlh Anee Abie ne ya bani irin wani farin ciki yau, inajin nisha'di

Please Login or Register in order to submit comment